Complete Hausa Novels

Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Rawanin_Zalinci_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 20 of 24

Cigaba da wurga mata wannan matsiyacin kallo ta yi tare da cewa. "Ke É—in wacece ke? Ke É—in banza ke É—in hofi, babanmu dai zaki iya aikansa ya je ya dawo kamar yadda kika faÉ—a É—in, dan kin shanyesa, amma ni dai wlh nafi karfinki algunguma kanwar shaiÉ—an kawai!!".

Cikin fushi tare da jin zafin kalaman nata Hauwar ta yi kanta zata daketa. Da sauri maman Zainab ta shiga tsakaninsu ta mayar da Zainab ɗin bayanta. Cikin ɓacin rai ta fara magana. "Wlh Hauwa idan kika ɗaura hannunki a jikin Zainab sai kin gane baki da wayo, sai na tuno maki da lokacin da muke zuwa Islamiya!".

Khadija dai tana tsaye shiru tana ganin wannan iko na Allah, ita kanta ma ciwo yake yi mata, ta gaji da tsayuwa tana son ta zauna.

Birki Hauwar ta ja, cikin kunan rai ta juya fuuu kamar wata kunfa ta nufi ɗakinta in da baban Zainab ya shiga kenan, da alama tana matuƙar tsoron yin faɗa da maman Zainab ɗin, duk da ta san cewa baban Zainab yana nan kuma zai tare mata faɗar, sai dai tasan kafin ya fito ya tare mata ɗin maman Zainab idan ta yi mata duka ɗaya sai ta yi jinya, hakan yasa bata yarda ta yi faɗa da ita idan baban Zainab ɗin ya matsa ko kaɗan ne.

"Zainab ku shiga wancan É—akin da ta ce naku É—in ku zauna ina zuwa, ku fa rufe kofa idan kun shiga, kuma ko an buga kofar kada ku buÉ—e har sai idan ni ce na dawo". Cewar maman Zainab.

Cikin wani irin kasalalliyar murya mai sanyi Khadija ta ce. "Mama ina zaki je?".

Nisawa ta É—an yi kafin ta ce. "Ba zan yi nisa ba, yanzu zan dawo, idan na dawo zan gaya maki in da na je". Tana kai karshen maganar bata jira jin me zasu sake faÉ—a ba ta nufi waje da sauri.

Su kuma suka nufi cikin É—akin a hanzarce kamar yadda ta umarcesu, suna shiga kuma suka dannawa kofar key.

Da shigansu É—akin ba'afi da minti É—aya ba sai ga Hauwa da baban Zainab sun fito daga nasu room É—in. Sai cika Hauwa take yi tana batsewa, da alama wani munafurcin ta je ta haÉ—a, ta kwashi karya da gaskiya ta sanar da shi, bawan Allah shi kuwa da already an rigada an shanye mashi ruwan kansa, sai yazama kamar wani yaronta, duk abin da ta faÉ—a shikenan ya yarda, haka kuma zata taso shi a gaba zalo zalo yana biye da ita, duk abin da ta faÉ—a ya hau kai ya zauna da shi yake aiki.

Ganin babu kowa a parlourn ne yasa Hauwar ta fara surfa uwar masifa a kan ita lallai ba zata yarda ba sai baban Zainab ya daki Zainab É—in dan ta yi mata rashin kunya.

Shi kuwa bawan Allah sai hakuri yake ta bata babu kakkautawa, kafewa ta yi a kan lallai sai ya gurzan mata bakin Zainab har sai ya yi jini. Allah sarki Zee baiwar Allah, babanta bai taɓa ɗaura hannunsa a jikinta da sunan duka ba, baya dukansu sai dai rarrashi da lallama tare da nuna soyayya, amma yau Hauwa tana son lallai sai an dirzan mata bakin Zee, akwai cakwakiya kenan.

Sai hakuri yake bata yana gaya mata ai shi bai ga su Zainab ɗin ba, tun da kuma basa nan ta yi hakuri kawai. Sam bata san sun shiga cikin ɗakin ne sun rufe kofa ba, da ta leƙa ɗakin da ta baiwa mamar tasu taga ba kowa sai ta yi zaton fita suka yi, bata yi yunƙurin leƙa ɗayan ɗakin ba.

Ita kuwa maman Zainab tana fita kai tsaye bakin titi ta nufa, da yake gidan nasu bashi da nisa da bakin babban titin.

Yau a karo na biyu Maman Zainab ta sake fita ba da izinin baban Zainab ba, hakan kuma ya faru ne saboda tsananin kunan rai da take ji, idanunta sun rufe bata ji bata gani, shiyasa ake son bawa a kowani lokaci ya rinƙa yawaita addu'ar Allah yasa ya fi karfin zuciyarsa, sannan ku kasance a duk lokacin da ranku ya ɓaci ku yawaita istigfari kuna ambaton sunan Allah, hakan zai sa duk ɓacin ran da zaku shiga ba zaku taɓa yin aikin danasani ba, dan haka ni dai shawarata a gareku ƴan uwana mata har ma da maza, kada ku bari zuciyarku ta fi karfinku, duk wuya duk daɗi kuma kada ku bari ambaton sunan Allah ya kubce daga bakunanku, yawan ambaton Allah ya kan sa ku fi karfin zuƙatanku, kuma yakan kai ku ga nasara tare da cinma burikanku da kuma samun babban rabo duniya da lahira, dan haka kada ku yarda ambaton Allah a kowani irin yanayi ne ya kubce daga gareku!!.

Abin hawa ta hau ba tare da ta gayawa kowa ba ta nufi bayan gari. Zuciyarta tafarfasa yake yi mata tamkar zai fasa kirjinta ya fito waje, ranta ya yi bakin kirin, idanunta sun rufe sosai, burinta kawai ta isa in da take da buƙata, sai sauke wani irin ajiyar zuciya take yi wanda da gajisa kasan na tsananin ɓacin rai ne, wai ace Hauwa ce ma zata zaɓa mata in da zata zauna ita da gidan mijinta, gidan mijin nata ma wanda ta sha wahala ta juri komai dan su gina gidan? Abin da ciwo kam matuƙa, duk kuma macen da aka yi wa haka ba lallai ta iya ɗauka ba, za'a tara mata ɗari da wuya a samu biyu da zasu iya danne irin hakan su shanye, akwai matuƙar ciwo sosai.

Kai tsaye bayan gari suka nufa, ba tare da ɓata lokaci ba ta yi wa mai mashin ɗin kwatance wajen wannan boka na Hauwar, sai kutsawa cikin dajin yake yi ita kuma tana kara yi mashi kwatance. Da kyar dai suka iya isowa wajen dutsen.

Sauka ta yi ta ce ya jirata bari ta je ta fito, dama sun yi da shi tun kafin ta hau a kan zai kai ta ne ya kuma dawo da ita, hakan yasa ya samu waje ƙarƙashin wata bishiyar kuka mai girma ya yi zamansa bayan ya kashe mashin ɗin nasa kenan. Zuciyarsa cike tab da tunani tare da tarin tambayoyi haɗe da mamaki a kan maman Zainab ɗin.

Bai san wacece ita ba, amma ta bashi mamaki yadda ta ce ya kawota wannan ƙungurmin dajin, tunani ya rinƙa yi tare da tambayar kansa me ta zo yi a nan? Sam bai san da cewa a saman wannan dutse ta baya akwai wani la'anannen Allah ba wai shi boka, wani tsinanne wanda wutar jahannama ke jiran gangar jikinsa idan bai tuba ba, shi dai mamaki yake yi kawai na me zata yi a daji, tunani ya yi ko dai ya salallaɓa ya bi bayanta ya je ya leƙa me zata yi ne domin ya samu abin labartawa a gari.

Hakan kuwa a ka yi, ya miƙe daga zaunen da yake ya fara salallaɓawa ya haye saman dutsen shi ma. Tun bai ƙarisa zuwa wajen ɗan kogon da ya gani a wajen ba ya fara jiyo muryarta tana magana kamar haka.

"Ba ni ce na kawo maka aikin ba dama? Ai kuÉ—ina na biya, dan haka na ce ka warware wannan aiki, idan kuma ba haka ba zan shigar da kai kara ga hukuma, macuci kawai azzalumi, wlh da kai da Hauwa ba zaku ga annabi idan baku tuba ba".

Yana daga zaune saman ɗan buzunsa na tsafin ya amsa mata da. "Ke ɗin ganin annabin zaki yi ne aka ce maki? Nasan kin san da cewa idan mutun ya je wajen boka ba tare da ya yi aiki da abin da bokan ya faɗa ba, zuwa kawai ya yi sallarsa ta kwana arba'in Allah baya karɓa, kin san da haka kuma ai kika zo nan har kika yi amfani da abin da na faɗa na kuma baki, ke muma fa ba wai jahilai bane, bari ki ji in gaya maki gaskiya kafin ka zama cikakken boka sai kana da hadda Alqur'ani mai girma a kanka, sannan sai ka san fassarar ayoyin cikinta, babu wanda Allah ya kafurta a Alqur'ani mai girma har sau biyar sai boka!! Mun san komai kawai take sanin muke yi domin biyan buƙatar kanmu! Kuma hakan ce kaddararmu, Alqur'ani da kike ganin nan tun daga farkon duniya har karshenta akwai magungunar duk wasu cuta da suke a duniya a zamanin da ya shuɗe da kuma yanzu har ma da cutar da zata bayyana nan gaba wadda namu sani ba, Allah bai saukar da cuta ba sai da ya saukar da maganinta, kowacce aya a cikin Alqur'ani da kike ganin nan tana da dalilin sauketa, dan haka ki sani ba wai da ka muke komai ba, duk wani sihiri da zamu haɗa in dai da gaske so muke taci to dole sai da Alqur'ani, dole sai da wasu ayoyin da Ubangiji ya saukarwa mutanen da suka gabata domin kawar da matsalarsu, to mukuma da ita muke amfani domin hassasa matsala cikin al'umma, sihirin da yake jikin mijin kurciya ce, sihiri mai wuyar warwaruwa kenan, ba kamar sauran sihiri da kika sani wadda zata yi kwana arba'in ko makamancinta ta kwance bane, wannan babban aiki ne, dole idan za'a kwanceta sai an dawo da kurciyar, sannan tsakanina da Hauwa akwai amana, dan tana mun abin da ba kowa ba, sai dai idan zaki yi mun abin da take yi mun sai na duba na gani.......".

Zaro ido maman Zainab ta yi tun lokacin da ya fara jawabinsa, kenan dama sun san gaskiya shegu?. Ni kuwa na ce kwarai kuwa babu abin da basu sani ba, shiyasa idan Allah ya tashi kamasu suke cin ubansu! Domin da sanin komai suke aikata duk abin da suke aikatawa, Allah baya kama bawa a cikin aikin rashin sani, amma ka sani ka take sani babban laifine wanda idan Allah ya tashi kamaka baya yi maka ta daɗi, babu wani ɗan iskan boka da ya isa ya yi sihiri ba tare da ayoyin Alkur'ani ba, dan haka ilimi ne da su sarai la'anannun tsinannu, kafirtasu da Ubangiji ya yi har sau biyar a cikin Alqur'ani ma duk sun san da haka shegu, sun karanta kuma sun karanci tafsiri, sun san fassarar ayoyi da dama, wasu ma sun san fasarar kowace aya shegu, amma a haka suke take sani suna cutar da bayin Allah, su yi asiri su ɗaurawa wata cuta, wata su haukatata ta shiga duniya a sake samun wasu la'anannu su yi amfani da ita a haukace dan biyan buƙatarsu suma, kuma duk bokayen ke saka hakan, ga shi nan dai abubuwa kala kala, ga cin zarafin Alqur'ani mai girma da suke yi, wata zasu rubuta mata suratul ali'imran su haɗa da magungunansu su ce ta wanke gabanta da shi, wannan ɓangaren sun fi yiwa karuwai wai dan su kara ɗanɗano, kun ga laifi kan laifi, ga bokanci ka taimakawa zinace zinace ta kara yaɗuwa, wani lokaci su rubuta wata sura daga cikin Alqur'ani mai girma su wanke suce mace ta yi wanka da shi, haka zata je cikin toilet wajen najasa ta yi wannan aiki, wani lokaci da jinin al'ada kazanta zasu rubuta Alqur'ani mai girma su wanke su bawa mace ta baiwa namiji, wani lokaci su rubuta wata sura a paper su ce mace ta sanya a gabanta, aiki dai kala kala na cin zarafin Alqur'ani mai girma duk yinsa suke yi, kuma sarai sun san hukuncin da yake jiransu na yin wannan ɗanyen aikin, amma da yake sheɗan ya yi wa Allah alkawarin sai ya samu parsinjoji na tafiya wutar jahannama, sai ya bi ya yi ta kaɗa masu gangan a kunne yana gaya masu cewa kada su damu su yi ta aikata fin hakan ma, idan sun zo mutuwa sai su tuba, haka sheɗan yake ruɗarsu, su yi ta tsula siyarsu a zuwan zasu tuba kafin mutuwa, sai su fake da cewa ai Allah gafurun rahim ne, sai dai sun manta shi Allah ba'a yi mashi wayo, wane mutun, san da zasu mutu ma basa sani bare har su tuba, time da zai kamasu ma basa sani bare su tuba shegu!!!.

Ganin maman Zainab ta zaro idanu tare da luluƙawa duniyar tunani ne yasa bokan ya sake ce mata. "Kada ki damu mu wannan ita ce kaddararmu da Allah ya kaddaro mana".

Wani irin matsiyacin kallo ta bishi da shi kafin ta ce. "Kuka dai kaddarawa kanku, Allah kam bai É—aura maku wannan kaddara ba, kowani É—an iska sai ya gama shirga iskancinsa, ya tsula tsiyarsa son ransa sai ya ce kaddararsa da Allah ya kaddaro masa kenan, to shi dai Allah baka isa ka yi mashi karya kuma ka zauna lafiya ba, azzaluman banza kawai..........."

Dakatar da ita ya yi ta hanyar daka mata tsawa ba tare da ya bari ta gama amayar da zafafan zantukan da suke ƙunshe a cikin cikinta suna cizonta ba.

Maman Zainab akwai karfin hali, ko tsoron wannan boka bata ji ba, ɓacin rai yasa ta fara zazzaga mashi masifa ba tare da jin tsoron kada ya yi mata wani abin ba, bugu da kari tana zaune a cikin muhallinsa tana kwashe mashi albarka.

"Dakata Hajiya, idan maganganu marasa daÉ—i kika zo gaya mun to tun wuri ina umartarki da ki fita a cikin wajen nan tun ban sauya maki halittar jikinki ba, sha sha sha kawai, ke har kin isa ki zo har in da nake ki ce zaki gaya mun magana? To idan ba aiki zaki kawo mun ba kada na kara ganinki a nan, idan ba haka ba kuma sai na mayar dake kwaÉ—o ko kunkuru". Yana maganar yana wani irin muzurai da ido, yadda kuka san kwarton da soja ya kama a gidansa, irin shi zai tsoritatan nan, ga idanun nasa jajir da su kamar mutun ya kwakwalesu ya jefar saboda muninsu, hancin nan nasa ba'a magana, a bage yake a saman fuskarsa kamar kan fanfo, ga shi bakin kirin kamar zunubi, bakinsa kamar waga.

Kasancewar ta zo ne domin a kwance wannan aiki da hauwa ta yi wa baban Zee, sai ta ɗane zuciyarta, ta daure ta sassauta muryarta tare da ƙoƙarin kawar da ɓacin ranta ta fara magana a nutse. "Ni ba dukka wannan ne ya kawoni ba, aikin da ka yi wa mijina kawai nake son ka kwance shi kamar yadda ka yi".

To kun san bokaye basu da sirri, dan haka sai ya ce mata. "Ni da Hauwa akwai amana a tsakaninmu, amma idan zaki bani abin da take bani sai na warware".

Da sauri ta amsa mashi da. "E zan baka menene?".

Ba wani ɓoye ɓoye bare kunya ya baje mata komai a faranti. Kanta zata bashi, dan shi ne abin da Hauwa take bashi yasa ya riƙe mata amana, har da wani ɗaurawa da cewa. "Ke kin ma fi Hauwa sura da kaya, kin ga da kin bani sai na warware aikin, kuma zan riƙe maki amana".

Ni kuwa nace wani amana kuma? Na tabbata ita ma Hauwa hakan ya ce mata idan ta bada kanta zai riƙe mata amana, amma ga shi yanzu saboda yaga maman Zainab ta fi hauwa komai da komai har ya tonawa Hauwar asiri, kuma idan da maman Zainab zata bashi kan nata tsab zai iya kwance aikin nan da ya yi wa Hauwar, kun ga kuwa a nan ina amana fisabilillahi? Ko da yake duk aikin da aka ce maka ya saɓawa Allah da Manzonsa ai babu wani amana da tausayi a cikinsa face danasani da nadama maras amfani!!.

Wani irin mahaukacin razana maman Zainab ta yi da jin maganganunsa, nan take ta ji wani irin jiri yana neman kwasanta, wa'iyyazubillah ta furta kusan sau uku. Wani irin tsinanne kallo ta fara bin bokan da shi, wani ƙazami da shi, ai wannan da ta haɗa shinfiɗa da shi gwara ta mutu, da wasu garmar hakwaransa da baya brush kamar na shanu. Wani irin muguwar tsanan Hauwa haɗe da baban Zainab ɗin ne dukka ya kamata, ji ta yi wlh zata iya hakura da baban Zainab har abada tun da ya haɗa shinfiɗa da Hauwa da ta sallamawa wannan ƙazamin la'anannen Allah kanta, waye ya sani ma ko yana ɗauke da wata cuta tun da ya nemeta hakan yana nufin ba da iya Hauwar kawai yake kwanciya ba, yana keta mutuncin mata da dama, daga gani halinsa ne, da wuya kuma idan bai da wata cutan.

Wani irin ƙululun bakinciki ne ta gangaro mata har wuya, kanta dake sara mata tun ɗazun ne ya fara yi mata barazanar tarwatsewa, sam bata san lokacin da zafafan hawaye suka fara bin ƙuncinta ba, ita kanta bata san hawayen me take yi ba. Cikin kunar rai ta juya da sauri kamar zata kifa ta fice daga cikin wajen ba tare da ta sake ce mashi ko uppan ba.

Unexpect wannan mai mashin ɗin da yake yi masu laɓe ya ganta a gabansa, bai yi tunanin zata juya tafito cikin ƙankanin lokaci haka ba, ya saki baki yana kallonsu kuma ya afka duniyar tunani a kan cewa kenan mata idan suka je wajen bokaye haka suke yi? Dama haka ake abin, bawan Allah bai taɓa gani ba sai yau, ya luluƙa duniyar tunani kwatsam ya ganta a gabansa ta fito.

Cikin hanzari ya ɗaga jikinsa daga jikin dutsen ta bakin kofar kogon in da ya samu damar leƙan nasu. Ƴan kame kame ya fara yi irin na marasa gaskiya.

Bata bi ta kansa ba ta yi saurin wucewa zata sauka kasan dutsen. A hanzarce ya rufa mata baya. Da kyar ta iya jiransa har yazo ya hau mashin ɗin ya tayar, kamar zata faɗi ƙasa zaboda jirin da take gani. Tsana da kyamar Hauwa da baban Zainab ne cike fal a ranta, bata da tabbacin cewa baban Zainab ɗin ya taɓa kwanciya da Hauwar, amma da yake zuciya bata da ƙashi sai ta ɗaurawa har da shi ma karan tsana.

Kunna mashi mai mashin É—in ya yi suka bar wajen, suka nufi hanyar da suka zo domin komawa, sai sake sake take yi a cikin ranta, tana ta tufka da warwara...........

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

🏞️FOREST🏞️🕊️🌹

Sosai Kamran ya sha wahala wajen yawo a bakin wannan tekun domin neman hanya, sai dai kash bai iya samun hanyar da yake ganin e ya aminta da ita ba, ya samu hanyoyi da dama a wajen, sai dai duk yana ganin kamar zasu yi mashi wahalar bi, sannan yana ganin kamar ba za su ɓille mashi ba, domin kuwa dukka hanyoyin daji ne gaba daji baya, babu kamshi alamar gida ko motsin wata halittar ɗan adam, hakan yasa yake ganin kamar har yanzu bai samu hanyar da ta dace ya bi ba.

Komawa ya yi wajensu Pretty jiki duk ya yi tsami saboda wahalar neman hanya, a kasale yake tafiya, yanayi yana tunanin mafita.

Lokacin da ya koma wajen nasu Pretty tana barci, ita kuma Sweetie tana karatun husnul Muslim da kai ba tare da littafi ba.

Kasancewar Prettynsa ta yi barci sai ya ji babu daÉ—in zaman wajen nasu, domin kuwa babu abokiyar rigimarsa, babu wanda zai tsokana ta yi mashi rigima ko kuka ya rarrasheta, hakan yasa ya ce da Sweetie bari ya je wajen mammarsa kada ta nemesa.

Sam Sweetie bata so tafiyarsa ba, ta so su yi hira sosai, amma ina ba dama.

Da okey ta amsa mashi kawai, daga jin yadda ta amsa mashi kuma kasan ba har cikin zuciyarta wannan okey É—in yake ba, ta dai amsa ne kawai rai bai so ba.

Miƙewa ya yi ya nufi hanyar fita. Yana tafiya yana waigo Pretty dake kwance, ji yake yi kamar ya mayar da yarinyar nan cikin cikinsa ko zai huta da irin kaunarta dake azalzalar zuciyarsa. Ita kuma Sweetie ji take yi kamar da sanya hannu ta buɗe idanunta ta fara gani domin ta ga mutumin da take jin tana kauna a duniya sama da komai nata a halin yanzu.

Yana fitowa ya cikaro da Rocky ya dawo daga yawonsa. Bai kula shi ba yasa kai ya yi gaba, baya Rockyn ya rufa mashi suka cigaba da tafiya kamar yadda suka saba, a haka suka nufi gida wajen mamma.

Pretty kuwa tana barci tana mafarkin Kamran ɗin, ita kuma Sweetie idanunta biyu tana tunaninsa, shi kuma yana tunanin Pretty tare da tunanin babansa da kuma yadda za'ayi ya samanwa Sweetie maganin idanun nan nata, yau ya ƙuduri niyar tambayar mamarsa maganin, in ta gaya mashi kuma tabbas ko a ina ne komai wahalar da zai sha wajen nemowa zai nemo mata, a cewarsa ya gaji da ganinta bata gani, so gara ya nemo mata maganin idanunta zu buɗe ko dan su rinƙa zuwa yawo a tare. Wani ɓangare na zuciyarsa kuma yana tunanin meyasa Mamma take ɓata rai sosai a duk lokacin da ya yi maganar addinin su Pretty? Wato a duk lokacin da ya yi mata wata kalma da ta danganci musulunci irin su Alhamdulillah da dai sauran word's da yake tsinta a bakin su Prettyn..........

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

KINGDOM OF POWER 💪🔥💘

"Yah Jawad meyasa zamu ɓuya to?.....".

Bata ƙarisa maganar ba ya yi saurin sanya tafin hannunsa ya rufe mata baki yana mai kallon cikin idonta, har yanzu basu dai'na sauke ajiyar zuciya ba daga shi har ita.

Ƙura mashi ido ta yi tana jiran ta ji me zai ce, tana kuma mamakin meyasa suka ɓuya? Meyasa bai bari ta yi magana ba ya rufe mata baki.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

Share fisabilillahi 👏

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍

🔥CROWN OF INJUSTICE🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)

🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 10/9/2024.....✍️📚🌹

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E____________48🔥

KINGDOM OF POWER 💪🔥💘

Ƙura mashi ido ta yi tana jiran ta ji me zai ce, tana kuma mamakin meyasa suka ɓuya? Meyasa bai bari ta yi magana ba ya rufe mata baki.

Matsowa kusa da ita sosai ya yi, cikin murya wadda za'a iya kiransa da kamar raÉ—a, in a low sosai kenan ya fara magana. "Kada ki sake yin magana kin ji ko?". Ya yi maganar tare da zame hannunsa daga saman bakin nata. Sai binta da wani irin kallo yake yi.

Ƙasa sosai ita ma ta yi da murya kamar yadda ya yi. "To Yah Jawad meyasa muka ɓuya?".

Bin É—an bakin nata da kallo ya yi kafin ya ce. "Because of Akka mana, kin san wannan tsohuwa da bala'i, yanzu sai ta samun hawan jini, so stay quiet har sai ta tafi zamu fita, don't let anyone to know abin da ya faru".

"Har da Auta?". Ta faÉ—a tana É—an zaro ido.

Hannu ya kai ya É—an matse É—an bakin nan nata har sai da ta ce wash. "If i say don't tell someone anything about me and you doesn't means har da Auta a ciki, i know kece Auta, sannan Auta ce ke, dan haka ki dai'na raba kanki da ita, coz nasan ma ko na ce kada ki gaya mata sai kin faÉ—a É—in, so is better na ce ita kam a gaya mata". Yana magana yana É—an wurga mata hararar wasa.

Zata yi magana suka ji motsin mutun yana tinkaro dressing room É—in wanda ko basu ga waye bane sun san King ne, dan sun san ya shiga wanka.

Jawad ba zai damu sosai ba idan kin ya gansu, saboda shi da daddyn nasa kun san yadda suke ai, gwara mashi King ya yi ta ganinsu a haka sau dubu a kan Akka, Akka ce matsalarsa shi.

Cikin hanzari ya sanya hannu ya toshe mata baki dan kada ta yi maganar, sannan ya fara matsawa a hankali kusa da ita, ita kuma ta fara ja da baya a hankali har suka matsa daga wajen glass ɗin suka ɓuya a bayan wani shirgegen drawer dake shaƙe tab da haɗaɗɗu kuma tsadaddun King shoes kala kala.

Cikin nutsuwa King ya shigo room É—in waist É—insa na'a É—aure da wata tsadaddiyar towel sky blue mai haske, yana shigowa cikin kuma yana magana a in da yake ce da Akka ta jira su je a tare, bari ya sanya kaya five minutes yana zuwa.

Mannuwa da jikin bangon wajen Chuchun ta yi, a hankali ya zame hannunsa daga saman bakin nata, sannan ya kara matsowa kusa da ita sosai, ya yi mata runfa da faffaÉ—ar kirjinsa a in da suka bawa King baya kenan.

Cikin nutsuwa shi kuma ya fara shirinsa tare da fitar da kayan da zai sa, sai dai yana yi yana É—an yin sauri saboda ya tsayar da Akka a kan ta jirasa.

Sosai Yah Jawad ya kura mata ido, ita kuma hankalinta na can wajen tunanin daddyn nata dake a cikin room ɗin, dan ma Allah yasa room ɗin yana da matuƙar girma, sannan wajen jera takalmar sakawarsa har drawer kala uku ne, kuma ba'a waje guda suke ba, dukkansu suna da ɓangarori daban daban, haka shi ma glass na jera watch ɗin nasa ma manya manya ne har guda uku, dukkansu kuma a shaƙe suke da tsadaddun agoguna kala kala, mafiya yawancin komai da yake cikin room ɗin guda uku uku ne, da alama wannan tsarin su Momma ne, shi kuma dan ya yi adalci ya biye masu kowacce ta jera nata kalar abubuwan da take buƙata ya rinƙa yi mata kwalliya da shi, ranar da yake wajen Momma sai ta shirya shi da kalar kayanta da ta sanya aka shirya mashi, haka idan yana ɗakin su mama kenan, yana ƙoƙarin kamanta adalci kam, shi ne yasa komai nasa uku uku ne kala daban daban, kowacce da kalarta, kuma kowacce a ranarta duk kalar da ta zaɓa mashi baya reject koda baya son wannan kalar, dan zaman lafiya, yana hakuri ya nuna yana matuƙar so ya kuma yi amfani da shi fuska ba yabo kuma ba fallasa!!.

Shiru ya ɗan dakata daga ƙoƙarin zura ash color arab jallabiyarsa da yake ƙoƙarin yi, kunnuwansa ne suka jiyo mashi kamar alamar motsi a cikin room ɗin. Ƴan waige waige ya fara yi da mamaki fal a saman fuskarsa.

Jin haka yasa Yah Jawad ɗin ya ƙara matsawa kusa da ita sosai ta yadda har suna iya jiyo sautin numfashin juna, dan gudun kada King ya gansu, still idanunsa yana a kan face ɗinta ya kasa kawar da kallonsa, ɗan rage gudun sautin fitar numfashinsa ya yi ta hanyar ɗan rike numfashin da yake yi kafin daga baya ya ɗan saki a hankali, duk gudun King ya gansu ne, yanzu sun ji ya fara waige waige dan yana ɗan jin motsi, so sun san zai iya ganosu, kuma fitar sautin numfashin a wajen da ya kasance babu hayaniya yana bada sauti mai ɗan karfi da har mutun zai iya ji kamar motsin wani abin!.

Ganin bai ga alamar komai bane yasa ya cigaba da yin shirinsa cikin natsuwa.

Daga karshe dai jawota jikinsa mai gabaɗaya ya yi tare da rage tsawonsa kaɗan, sannan ya sunkuyo da kansa izuwa kunenta, cikin raɗa ya ce mata. "Ki rage sautin fitar numfashinki, ki rinƙa sakin numfashin a hankali hankali......".

Still wannan ɗan magana da ya yi yasa King ya sake jin alamar motsi a karo na biyu, a lokacin kuma yana sanya alkyabba a saman jallabiyar jikinsa. Dakatawa ya yi shiru, cus cus ya ji yo kamar ɓera na fasa ledar indomie, mamaki ne ta kara bayyana sosai a saman fuskarsa a in da ya fara waige waige a karo na biyu, sai kuma ya ajiye rawanin da ke hannunsa a saman wani haɗaɗɗen show glass dake shake da hatiman masarautar wadda suke dukka iri guda ne masu kan zaki kenan. Fara ƴan dube dube ya yi ko zai gano ta ina yake jiyo wannan ɗan motsin.

Jin ya zo ta kusa da drawer da suke É—in ne yasa Jawad É—in ya kara mannata da jikinsa sosai suka yi wani tsit kamar babu wata halitta mai rai a wajen. Yan dube dubensa King ya gama yi tsab, sannan ya juya ya koma wajen da yake shirinsa.

A hanzarce ya ƙarisa shirin dan Akka na jiransa kuma ya ɓata lokaci wajen tsayawa da ya yi ta yi dan jin motsin da ya yi, dan haka sai ya ƙarisa shirin a hanzarce ya fice daga room ɗin.

Yana fita a tare suka sauke wani irin nauyayyar ajiyar zuciya, kara ƙanƙameta ya yi yana fitar da numfashi da sauri da sauri saboda rike numfashin nasa da ya yi ta yi dan kada King ya gansu.

Ita ma da sauri sauri take sakin numfashin tata. Hannunsa É—aya ya É—aura a saman bayanta dai'dai tsakiya. "My Jannat mun tsalleke rijiya da baya, da Akka ko daddy sun ganmu am in trouble wlh". Ya faÉ—a da wata kasalalliyar murya kamar mai jin barci.

"To Yah Jawad meyasa kake gudun su ganmu? Ai naga sun saba ganinmu a tare, bare ma shi daddy da a can baya kai da Yah Jaish kuke zuwa cin abincin a dining room ai kullum suna ganinmu a dining room É—in a tare ko?....."

ÆŠaga kansa sama ya yi tare da jinginta da jikin drawer, a wahalce ya ce. "Banda irin wannan kallon kam, ai idan suka ganmmu a irin wannan yanayi akwai matsala, musamman Akka sai ta saka mun hawan jini...."

"To meyasa?". Ta tambaya da mamaki sosai a saman face É—inta, ta kuma yi maganar tana É—an É—ago kanta daga saman chest É—in nasa.

Slowly ya sauƙo da kansa daga ɗagata da ya yi, ya zamana suna fuskantar juna sosai saboda ta ɗan ɗago kanta ita ma. Kura mata idanu ya yi kamar wani ya ce zai kwace mashi ita. A hankali ya motsa lips ɗinsa wajen furta. "Kina son sanin dalili?".

Da sauri ta gyaɗa mashi kai haɗi da cewa e. Rankwafo da face nasa dab da tata ya yi, ɓangare ɗaya na zuciyarsa tana azalzalarsa da ya faɗa mata kawai, ya furta mata saboda yana sonta ne, ɗayan ɓangaren kuma yana ƙoƙarin hana shi yin hakan ne ta hanyar bijiro mashi da tunanin cewa zata rai'na shi, zakuma ya samu matsala da Jaish da dai sauran tunani marassa kan gado.

"Yah Jawad ka faÉ—amun mana". Ta katse mashi tunanin da yake yi.

Ji yake yi kamar ya yi kissing É—inta idan tana magana a kusa da shi, kuma ji yake yi kawai ya daure ya gaya mata yana sonta. Amma ina ko kusa ko alama ba zai iya yin hakan ba.

Nisawa ya yi tare da sumbatar goshinta, sannan ya É—an ja baya kaÉ—an tare da raba jikinsu.

"Wani lokaci zan gaya maki, but now come let us go". Ya kai karshen maganar tare da riƙo hannunta cikin nasa da nufin su fice daga room ɗin.

Ba musu ta bi bayansa, hankalinta yanzu gabaɗaya ya karkata izuwa room ɗinta, tana son ta koma can ta je ta cigaba da yin waya da Yah Rizwan wanda yanzu shi ne tauraronsa yake haskawa a idanunta tun daren jiya, ya tsarata ne da wasu shegun love word's, shi da yake cewa Jawad a yanzu ba shi da lokacin mace, amma kuma ashe ya iya zafafan kalamai masu tsayawa a rai, ko daga ina ya koyo? Allah masani sai kuma shiɗin haɗi da alkhalamina........💘

A cikin room na King suka tsaya, hannun nata ya saki tare da juyowa gareta da kyau. Zuba mata idanun ya yi na Æ´an mintocin da basu wuci biyu ba, kafin ya nisa tare da cewa. "Jeki room naki".

Da sauri ta juya zata ta fi, har ta kai tsakiyar room ɗin kamar a mafarki ta tsinkayo muryar can ƙasa ƙasa ya furta sunanta. Da sauri ta juyo tare da dakatawa daga tafiyar da take yi.

Siririn murmushi ya sakar mata mai matuƙar ƙayatarwa wadda idan aka yi maka shi dole ka mayar da martani ko kana so ko baka so, dan time ɗin da martanin zai bayyana a saman fuskarka ma ba zaka sani ba sai dai kawai ka ji ka yi. Ita ma kuwa hakance ta faru da ita, sam bata san lokacin da ta dawo mashi da martanin nata siririn murmushin wadda ya kara jefa shi cikin yanayi ba.

"Ki kula sosai my sister, bana son dai mu rabu, amma ki je ni zan je wajen Jaish tun jiya yake nemana ban samu mun haÉ—u ba". Ya faÉ—a yana kallon cikin idonta.

"Tom Yah Jawad zan kula sosai". Ta yi maganar tare da juyawa, yanzu tana jin Yah Jawad É—in nan nata a matsayi na musamman a cikin zuciyarta, haka kawai take jin daÉ—in ganin fuskarsa musamman idan yana É—an murmushi. Zuciyarta cike tab da tunanin Yah Rizwan É—inta ta nufi kofar fita.

Tsareta da kallo Jawad ya yi babu ko kyaftawa, ita kuma tana tafiya tana tunanin zafafan kalamai Rizwan bare ma yadda ya rinƙa yabon kyanta tare da nuna mata ya mace a kanta, hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba, tana son taga ana nuna mata so ana kuma yabon duk abin da ta yi, ta wannan hanya Rizwan ya yi nasarar sace zuciyarta, kuma a nan ne suka sha banban da Jawad, shi Jawad koda yaushe sai faɗa ya iya yi mata a kan kada ta yi kaza ko idan ta yi kaza sai ya bata punishment, amma shi Rizwan jiya da ta ce mashi zata je wajen Momma da daddare, cikin nutsuwa ya tambayeta da kayan barcin zata fita? Da e ta amsa mashi, ƙasa ya kara yi da murya tare da kara nutsu kafin ya ce mata a'a shi bai yarda ba yana da kishi sosai, ta sanya hijabi har ƙasa, kuma me zata je yi a wajen Momma da daddaren nan?

Gaya mashi ta yi zata je ɗebo turaruka. A sanyayye ya ce mata ta bari sai da safe mana, shi yanzu gaskiya ba zai iya hakura da hiran nan nasu ko na minti ɗaya ba, bai shirya dai'na jin zazzaƙar voice ɗinta ba, ta yi hakuri ko dan soyayyarsu ta bari sai zuwa da safe. Cikin rarrashi da nuna soyayya ya yi mata magana ba kamar yadda Jawad ya ce idan ta sake fitowa da kayan barci sai sun ɓata kuma ya bata punishment ba, wannan shi ne banbancin da yake a tsakaninsu, Rizwan da daɗaɗan kalamai yake amfani wajen hanata yin abu.

Sai da ta kurewa kallonsa da kamar minti biyu sannan ya rufa mata baya, kai tsaye part É—in Jaish ya nufa.

Ga mamakinsa sai ya ga É—an uwan nasa sai shirga aikin shiri yake yi alamar zai yi tafiya.

"Travel without telling me, why? And where are you going?". Ya yi maganar tare da zama a gefen gado idanunsa na'a kan É—an uwan nasa babu ko kyaftawa.

Sai da ya kammala zuba kayayyakin da yake zubawa a cikin haÉ—aÉ—É—iyar echolac É—insa mai bala'in tsada kafin ya juyo da kallonsa izuwa kan É—an uwan nasa.

"How do you expect me to tell you that I want to go to somewhere bayan gabaÉ—aya you're totally useless now, wai ma ni this two day's what's wrong with you? Where are you going that very important better than my issues?......"

Katse shi ya yi da cewa. "Woooo zaka fara halin naka ko Jaish? To wai ni mema na yi ne? Am with you bro, i didn't give anyone my attention or my time, kawai dai lokacin haÉ—uwarmu mu tattauna a kan issues É—in naka ne bai yi ba........".

Hararar da Jaish ɗin ya wurga mashi ne yasa ya dakata da yin maganar yana son fahimtar wani abu, shin da gaske ran ɗan uwan nasa ya ɓaci ne? Ko dai wasan da suka saba yi ne?.

"Since day before yesterday nake binka a kan kazo mu yi magana, amma you're always try to show me you're busy, you don't have my time, you're doing something or you go to somewhere, you're not around and some miscellaneous excuse".

Cikin zolaya ya ce da Jaish É—in. "Meyasa ba zaka tambayi uzurin nawa ba? Do you know maybe I fall in love with someone ne yasa am going up and down since that time you said?".

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.