Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Rawanin_Zalinci_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 4 of 24
Part na family'n king, wata shirgegiyar benece mai hawa huɗu, ga wata haɗaɗɗiyar elevator da take kai komo tana ɗaukar mutane izuwa sama or ƙasa, ba sai na faɗa ba kun sani gini ne da aka kerashi da tiles and glass, kasancewar KING ZUHAIR architecture ne, shi ya fitar da zanen tsarin gidansa ta yadda ya ja hankulan dubbanin jama'a, dan kuwa wani irin tsari ya zubawa ginin nan nasa wanda ko a ƙasashen turawa da wuya a samu mai irin tsarinsa, tsarin ta fita ne iya fita, dan idan aka bar mutun da kallon wannan tampatsetsen gidan ma kawai sai ya wuni ya kwana yana kallon iya waje kawai.
Ƴaƴan KING kowa da bedroom nasa na daban, kowa kuma bedroom nasa aljannar duniya ce, musamman auta da ta kasance sanyin idaniyar babanta, kuma jika ga sarkin Dubai wato kakanta wanda ya haifi mamanta, kuma ta kasance jika da kakan nata ya fi kauna, ita na ta ɗakin ma idan ka shiga sai ka yi tunanin ba a duniya kake ba, saboda tsantsan tsaruwa da kawatuwa, KING ya zuba mata makudan kuɗaɗe a ɗakin nata, haka zalika kakanta, daga Dubai aka kawo komai na cikin ɗakin.
Sanan ko wace mace fa wato su mummy kenan, ko wace Part nata daban ita da Æ´aÆ´anta, sai dai part É—in daddy wato KING yana a tsakiya ne, hakan yasa aka yi kofofi da zata sada ko wani part da part É—in na daddyn a hawa na uku kenan, a nan suke haÉ—uwa su yi hira, su ci abinci a babban parlourn KING. Wannan a takaice kenan tsarin KINGDOM OF POWER.
Cikin wani katafaren garden mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali, garden ɗin ya ji komai na more rayuwa, luntsuma luntsumar sofas dake ciki farare kal da su gwanin ban sha'awa, sai tashin wani daddaɗar kamshin flowers garden ɗin yake yi.
Daga can gefe guda wajen wani kyakkyawar tsadadden grass carpet, wasu kyawawan ƴan mata farare tas da su kamar wasu tattabaru ne suke zaune a wajen, saman grass carpet ɗin dai'dai in da suke a zaune shinfiɗe yake da wani irin Turkey carpet mai matuƙar laushi, ga wasu manya manya throw pillows dake a saman carpet ɗin masu matuƙar kyau.
Waɗan nan ƴan mata su huɗu ne, kyawawan gaske ne, farare tas dasu, tamkar ka taɓa jini ya zuba.
Sun kasance kamanninsu É—aya ne sak, da gani ba tambaya kasan jini guda ne, dukkansu babu wacce zata kai shakaru 17 a cikinsu, Æ´an mata ne caras cas da su.
Sanye suke cikin shiga ta ƴaƴan sarakuna, shiga ce mai matuƙar ɗaukar hankali, doguwar riga ce fara kal wadda ta sha kwalliyar duwatsu golden color masu bala'in ɗaukar idanu.
Daga samar rigar tayi masu cif a jikinsu, daga ta wajen plat tummynsu rigar ta yi wani uban buÉ—ewa tamkar umbrella har kasa, dukkansu rigar tasu tana ja har kasa.
A saman rigar tasu kuma sun É—aura wani dankareriyar shegiyar alkyabba mai bala'in kyau da tsada, launin golden color mai haske.
Uku daga cikinsu waɗan da suka fi manyata suna sanye da hular alkyabbar a kansu, ɗaya kuma dake zaune a ɗan gefe saman throw pillow, ita sam bata sanya hular alkyabbar a kanta ba, ta bar kanta babu ɗan'kwali, ga gashin kan nata gwanin ban sha'awa, bakinkirin da shi, ya zubo mata har gadon bayanta, sai kyalli yake yi, duk cikinsu ita ce ƙarama, kuma ta fi su kyau nesa ba kusa ba, dan ma dai jini ba wasa bane yasa kamannin jini ya bayyana a tsakaninta da su, bacin haka ita ɗin daban take a cikinsu, harta yanayin hasken fatarta ba irin nasu bane, ita ɗin fatarta tamkar madara haka yake, su kuma jajir suke kamar tsada.
Dukkansu suna da dogayen hanci masu matukar kyau da É—aukar hankali, sannan waÉ—an nan ukkun dukkansu lips nasu ya kasnace pink color ne, da yake suna da hasken fata, sai kalar lips É—in nasu ta bayyana sosai tamkar sun saka lips stick, ita kuma karamar cikin nasu lips nata red color ne mai bala'in kyau, ya yi red sosai gwanin burgewa, har wani shining yake yi.
Duba da dara daran idanu farare kal kal tamkar audiga, kwayar idanunsu bakin kirin har yana wani walwali, eyelashes nasu zara zara sosai like gashin doki. Ita kuma ƙaramar cikin nasu kwayar idanunta ba baki bane, hazel eyes ke gareta, kasancewar idanun nata fari ne tas, hakan ya bawa launin kwayar idanun nata damar kara fitowa sosai.
Wasu shirga shirgan dakarun yaki masu ji da lafiya da karfi ne a tsaye a ɗan nesa kaɗan da waɗan nan ƴan'matan, da alama bodyguards nasu ne, dan kamar yadda suke su huɗu a wajen, dakarun yakin kuma su uku ne a wajen, da alama kowacce jarumin sadaukin dakare ɗaya ne yake gadinta duk in da zata je, saboda yanayin yadda dakarun suka tsaya tamkar wasu saƙaguna, kowannensu yana fuskantar mace ɗaya, hakan ce zai baka tabbacin cewa kowanne da wadda yake gadi, sai ita kuma karamar cikinsu babu wani dakare da ya fuskanceta a wajen, da alama nata dakaren baya wajen ko kuma wani abin makamancin haka.
Sai hira ƴan mata ukun nan suke yi cikin harshen larabci, ita kuma ƙaramar tana zaune rike da wani hoto a hannunta tana kallo, ta ƙurawa hoton idanu sosai, kome take kallo a ciki?. Daga karshe ma sai ta sauka daga saman throw pillow da take zaune, ta koma saman carpet ɗin ta zauna, tare da kishingiɗa a jikin pillown tana mai cigaba da kallon hoton.
Wani cikakken gwarzon namiji ne ya shigo cikin wajen, sanye yake a cikin kayan yakinsa shi ma, baka iya ganin face nasa saboda hular kayan yakin nasa dake a kansa, yana tafiya ne irin na cikakkun gwarazan maza, ga tafiyar tasa cikin wata iriyar nutsuwa da kamala, sam babu hayaniya a tattare da shi, sai wani irin dake a tare tattare da shi, yana buƙe kamar wani zaki.
Hannunsa na rike da wata kyakkyawar kwando mai ɗauke da fruits a cike a cikinta, fresh fruits ne mai matuƙar kyan gani a idanun. A gaban ƙaramar cikin nasu ya zo ya tsungunna tare da ajiye mata kwandon fruits ɗin a gabanta, cikin girmamawa ya ce.
"Ranki ya daÉ—e ga shi nan".
Ƴar yarinya da bata wuce 11 to 12 years ba, kanta ta ɗago daga kallon hoton da take yi tare da sauke dara daran Hazel eyes nata a kansa.
Cikin sauri ya kara risinar da kansa ƙasa alamar girmamawa.
"Banace maka ka daina ce mun ranki ya daÉ—e ba? Ka kira su Aunty MieMie da ranki ya daÉ—e, ka kira su Aunty chuchu da ranku ya daÉ—e, nima da nake Æ´ar yarinya sai ka wani ce mun ranki ya daÉ—e? To ni bana so, kawai kace mun auta ta ko kuma ka kirani da baby kamar yadda uncle Taheer yake ce mun".
Ta yi maganar cikin kwararriyar laraɓcinta, ga ta da zaƙin murya sosai, voice nata gwanin daɗin saurara.
"Kiyi hakuri ranki ya daÉ—e, zan gyara". Ya bata amsa da yaren da ta yi mashi magana, ya yi maganar a sanyaye cikin nutsuwa.
"Ba zaka gyara bakam, ga shi yanzu ma ka sake ce mun ranki ya daÉ—e, to shikenan tun da ba zaka canza hali ba".
Ta kai karshen maganar tare da É—aukar Æ´ar wukar da yake a cikin kwandon fruits É—in da kuma Apple guda É—aya da nufin ta fara yankawa ta ci.
Waɗan nan ƴan mata guda ukun da suke wajen har suna rige rigen karɓar wukar daga hannunta tare da Apple ɗin, shi ma wannan dakaren nata ya yunkura zai karɓi wukar ne sai ya ga ƴan uwanta sun riga shi, hakan tasa sai ya koma ya nutsu.
"Ke auta so kike yi ki yanke hannunki uncle Taheer da daddy su bamu hukunci ko?".
Cewar Æ´an matan, sun yi maganar har suna haÉ—a baki.
"Kai Aunty Chuchu ni fa yanzu na iya yanka fruits, baki ji uncle Taheer ya ce yakamata nima na fara koyan takobi bane? Ya ce na girma yanzu".
Miƙewa tsaye dakaren nata ya yi tare da tsayawa a ɗan gefenta kaɗan, kamar wani mutun mutumi, kun san haka dakarun yaki suke tsayuwa dama, cike da jarumta sosai, musamman idan aka basu kula da mutun mai mahimmanci, ai sam basu zama, Auta tana da matuƙar mahimmanci sosai ga kowa da yake gidan, ƴa ce ga Gimbiya Rahilarh, wato amaryar King Zuhair kenan, ƴar ta ce, shi ne yasa ma ta fisu kyau, dan ita gaba da baya dukkan jinin larabawa ne babu mix, kada ku manta mamanta ƴa ce ka sarkin Dubai, King Zuhair ma nasan baku manta tushensa ba, so ita auta bata da mix ko kaɗan, suna ji da ita, suna sonta sosai, shi ne ma yasa King Zuhair ya wakilta assistant commander mayakansu wato HOORAIN da ya kula da ita, ya zama shi ne mai bata tsaro, tsabar son da yake yi mata ne ya yi mata wannan gata, duk sauran ƴaƴansa normal mayaka ne suke tsaronsu, amma banda ita auta, ita assistant commander da kansa ne yake tsaronta, da da dama ma da commander za'a sanya ya yi tsaronta, duk wani motsin da zata yi ya kula da ita sosai, idan ta yi koda tuntunɓe ne zai sha hukunci.
(Kai irin wannan soyayya haka, to Allah muma ka yi mana arzikin da zamu yi wa ƴaƴanmu fin haka ma🤲)
"Ba wani girman da kika yi, ki bari mu yanka maki ko a kira kuyangu su yanka maki ki sha".
Cewar É—aya daga cikin Æ´an'matan, wadda aka kira da Aunty Chuchu kenan.
ÆŠan turo baki ta É—an yi kafin ta ce. "Amma Aunty Chuchu kin san ni bana son na kuyangu ko?"
GyaÉ—a mata kai Aunty Chuchu É—in ta yi alamar e ta sani
"Tom shikenan, ni bari ma na je wajen daddy a faÉ—a kafin ku gama yankawa, dama nace mashi zan je hutu wajen Mai rankarfe, this time Dubai zan tafi, bari na je na tuna mashi da batun hutu nawa, dan gobe nake son a kai'na". Still cikin harshen larabci ta yi maganar tata, da voice nata na yara mai shegen daÉ—i.
Ta kai karshen maganar tare da miƙewa tsaye, tana da tsawo dai'dai gwargwado, ba gajera bace ba, kafarta na sanye da cover mai bala'in kyau launin gold color miƙewarta tsaye yasa tsananin kyanta ya kara bayyana sosai, kyakkyawa ce ajin farko.
Wucewa gaba ta yi HOORAIN ya rufa mata baya, yana taku na kikakkun jarumai waÉ—an da jininsu yake a tsananin tafashe, Hoorain baya magana, tamkar wani kurma haka yake, sai iya cika aiki cikin zafin nama.
Da kallo su Chuchu suka bita da shi har ta fice daga cikin wajen.
Duk in da ta zo wucewa sai manya manyan dakarun yaki sun sunkuyar da kansu ƙasa alamar girmamawa a gareta, idan kuma bayi ne sai sun zube gwiwowinsu a ƙasa haɗe da sunkuyar da kai dan girmamawa, ba zasu ɗago kansu ba har sai ta wuce, gata wata ƴar firitu a wajen, amma haka ake bata wannan girma dan dole, kun san yadda gidan sarauta take, musamman sarauta mai cike da girma irin haka, girmama ɗan sarki dole ne ga bayi, koda kuwa jariri ne.
Tafiya take cikin nutsuwa har izuwa kofar tampatsetsen babban fadar mahaifin nata, wasu jiga jigan zataran matasan dakarun yaki ne suke gadin kofar shiga fadar, suna shirye cikin kayan yakinsu, tsayawa zayyana maku haɗuwa da kyan kofar shiga cikinta kawai ma ɓata baki ne, dan ba zata faɗu a baki ba.
Fada ce irin na hamshaƙan sarakuna masu faɗa aji a duniyar mulki, sai dai kuma wannan fada ta fita daban a duk cikin fadojin da kuka sani a duniya, saboda fada ce ta manya.
Tun da auta ta saƙo kafarta, da Sallama ta fara cin karo, Sallama wani bawan sarki ne wanda kamar matsayin PA yake, duk wani mai son ganin sarki in ma a cikin gida ko kuma a waje or a fada to dole sai ya bi ta hannun Sallama, idan ba haka ba ba zai sami damar ganin sarki ba, kun dai san yadda matsayin PA yake ko?, To haka matsayin Sallama a cikin fadar sarki yake.
Ganin Gimbiya auta ce tasa Sallama ya fara washe baki tare da fara zuba mata kirari.
"Takawarki lafiya Æ´ar sarki jikan sarki, mace mai farar aniya tare da farar zuciya, farar mace alkyabbar mata, tauraruwa a cikin taurari, Æ´ar gata kuma Æ´ar lelen kowa dake a cikin masarautar nan, Queen Zunaira taka a sannu masu kasar Dubai da kewaye".
Yana zuba mata kirarin ne tare da É—aga hannunsa É—aya sama alamar jinjina, ya kuma sunkuyar da kansa kasa alamar girmamawa.
Duk wanda yake son zaman lafiya a cikin KINGDOM OF POWER to ba shakka dole ya kaunaci Gimbiya Zunaira, dan King Zuhair ya fi kaunarta sama da yadda yake son kansa, hakan tasa sallama ya zage yake ta zuba mata kirari babu kakkautawa, dan ya faranta ran sarki.
Da yake kamar yadda Sallaman ya faɗa, ita ɗin macece mai farar zuciya, ga kyauta kamar babanta, ga san jama'a da saukin kai, duk ƴaƴan KING ZUHAIR suna da masifar jiji da kai haɗe da izza ta gidan sarauta, kunsan yadda jikin sarauta suke, iya fadanci, nuna tsantsar isa da takama, izza da nuna fifiko, to duk haka ƴaƴansa suke except auta, ita kaɗai ce mai saukin kai tare da ɗaukar mutane da daraja a cikinsu, sai kuma Gimbiya Chuchu wadda ita sam bata da wata matsala, bata da jiji da kai, bata ma da yawan magana, in kaga tana magana to da su Gimbiya Zunaira ɗin ne, ban da haka ita bata kallon mutane ma bare ta yi masu walaƙanci, ita kuma auta tana tsayawa ta saurari mutane ɗaya bayan ɗaya, yanzu ma tsayuwa ta yi tare da kai kallonta cikin ainahin fadan, sannan ta furta cewa a bawa Sallama kyautar kujerar Makka, daga haka ta wuce ciki abinta, da sauran ƴan uwanta ne ko kallon arziki sallama ba zai samu ba bare har su yi mashi magana, akwaisu da izzar bala'i, musamman ma wata yar autar mai suna Gimbiya SAREENA, ta fi kowa iya jiji da kai tare da nuna izzar sarauta, isa da taƙama, kamar ba zata mutu ba
Kai tsaye saman stage da mahaifinta yake auta ta nufa, sai faman duƙar da kai ƙasa duk wasu mayakan dake a matsayin bodyguards a cikin fadar suke yi, alamace ta suna girmamata.
A saman wajen stage da sarki yake daga ta bayansa akwai wasu dakarun mayaka guda biyu wanda ake kiransu da sunan sarakan Figini, su ne masu yi wa sarki firfita da maficin gashin jimina, sai fifita suke yi mashi da wasu tampatsetsa tampatsetsan maficin gashin jimina.
Daga ta can gefen kujerar sarki da iyalansa kuwa, wasu hamshaƙan sofa sets ne a wajen, su kuma kujerune waɗan da aka ware na zaman malam liman, wato limamin Fada, sai Galadima, yana cikin majalisar sarki, Madaki, Yana daga cikin ƴan majalisar sarki shi ma, sai Sarkin Dawakin tsakar Gida, ko ban faɗa ba kun san shi ne mai jagorantar masu kula da dawakan gidan sarki.
Daga kasar stage ɗin ma akwai wasu sofa sets tantsama tantsama, wasu daga cikin manyan fada ne suke zama a kai, irinsu sarkin gida, mai jagorantar masu shige da fice na cikin gidan sarki kenan, sai sarkin hatsi, mai kula da wajen ajiye kayan abinci, shi ne kuma mai fitar da zakkar sarki idan lokaci ya yi, duk wata sadakar kayan abinci da za'ayi dole sai da saninsa, komai dai da ya danganci abinci shi ne mai kula da shi, ko in ce jagoran ma'aikatan da suke kula da su, akwai ɗan iya, mai rerawa sarki waƙa kenan, yana da zazzaƙar murya, dan mai murya sosai ake nemowa, mai kuma ilimi sosai, sannan akwai sarkin bayi, ko ban faɗa ba kun san shi ne mai kula da duk wasu bayi da suke a cikin wannan Masarauta, sai Kasheka, wanda shi ne yake kasancewa a tare da sarki kullum, duk in da sarki zai je dole Kasheka ya kasance a tare da shi, sai amintattcen sarki, wanda wannan muƙami ne da ake bawa wanda sarki ya aminta da shi sosai, still akwai kilishi, kilishi wani bawan sarki ne wanda alhakin yi wa sarki shimfiɗa ya hau wuyansa. A duk gurin da sarki zai zauna, to kilishi ne yake yi masa shimfiɗa, imma a cikin Masarauta ko a wajenta, sai sarkin mayaƙa wato commander ZAFAR, shi ma a cikin fada ya fiya yawan zama, domin idan za'a fita yaki ko wani abin ya sani.
Akwai dai muƙa mai da dama a cikin fadar sarki, amma waɗan nan sune manyan muƙaman, na kawo maku su ne kuma dama dan ana karatun littafi ne domin a samu karuwar ilimi, so ko baki taɓa shiga fadar sarki ba idan kika karanta littafin nan zaki san abubuwa da dama da suka danganci sarauta, shi ne amfani karatun dama, shi ne kuma yasa nake ƙoƙarin ganin na faɗaɗa maku komai dan ku sani ku sami karuwar ilimi.
Kasancewar wajen zaman sarki waje ne da kowa ya sani na daban ne, tampatsetsan kujera ne na alfarma mai zaman mutun biyu, sai kuma na iyalansa dake a gefe da gefen nasa, wanda idan sun zo cikin fada zasu zauna a kai, babu wanda ya taɓa zama a saman kujerar sarki sai sarkin, koda kuwa matansa ne basu zama, shi kaɗai yake zama abinsa, amma saboda son da yake yi wa Auta, idan ta shigo a gefensa take zama, saman kujerar tasa.
Yanzu ma da ta shigo a gabansa ta zo ta tsugunna, cikin girmamawa tare da ladabi da biyayya ta sunkuyar da kanta ƙasa, cikin sanyin murya ta yi mashi barka da hutawa, while shi kuma Hoorain yana waje bakin kofar fadar yana jiran fitowarta, dama baya binta ciki idan suka zo, a waje yake tsayawa abinsa.
King Zuhair duk da yana jikin naÉ—in farar RAWANIN sarautarsa, ya sha alkyabbarsa mai bala'in tsada, hakan ba zai hana ka ga madarar kyau ba, kyakkyawar gaske ne shi É—in, namiji mai cikar haiba da kamala, ya hakince a saman kujerar nan tasa yana gudanar da mulki bisa gaskiya da amana tare da adalci.
Ƙasa ƙasa ya yi magana ta yadda ko masu yi mashi fifita na bayansa ma basu ji me ya ce ba, duk da cewa yana cikin naɗin RAWANIN mai kamar nikaf. Auta dake a gabansa ne kawai ta iya jin abin da ya faɗa, dan haka sai ta miƙe cikin nutsuwa ta koma kusa da shi ta zauna tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya.
"Me yake tafe dake Mamana?". Ya sake yin magana ƙasa ƙasa cikin nutsuwa, harshensa akwai kaifi sosai, maganarsa tana da kaifin da idan ta ratsa dodan kunne sai ganganjiki ta amsa, dama akwai masu irin wannan murya a cikin jama'a, sai dai ba kasafai aka cika samunsu ba, mutun ne da zaku ji muryarsa mai kaifi, idan ya yi magana koda cikin nutsuwa ne sai masu sauraronsa sun shiga taitayinsu, koda kuwa raha yake yi da su, saboda kaifin harshensa sai kaga suna tsoron yin magana da shi, ko da ba mafaɗaci bane, bare kuma shi King Zuhair da ya kasance jinin Modarawa, ai kunsan faɗa dole, zafin rai dole, dan a jinin Modarawa dai babu rago mara zuciya, wannan yana ɗaya daga cikin dalilan da yasa KING baya magana da ɗaga murya, dan tsaro, shi kansa yasan yana da kaifin harshe, so ɗaga muryarsa ga al'umma haɗari ne babba, zata iya sa wani da bai ji ba bai gani ba ya mutu saboda tsoro.
"Daddy dama na zo ne na gaisheka".
Ta faÉ—a a nutse.
Ba tare da ya kalli in da take ba, dan suna jere ne wajen guda, cikin sanyin murya ya amsa mata da.
"Anya kuwa autana gaisuwace ta kawo ki?".
ÆŠan guntun murmushi ta yi wadda sai da dimple nata suka lotsa, fararen hakwarantan nan suka bayyana, ga wani É—an siriri wushirya a tsakanin hakwaran nata, kyau iya kyau ya kara bayyana dalilin wannan murmushin.
"Kai daddy shi na zo yi mana". Ta faɗa a ɗan shagwaɓe.
"Ai nasan halinki ne, haka kawai rana tsaka baki zuwa wajena, keda wani lokaci ma sai na sanya an nemo min ke, to yanzu dai gaya mun kawai me kike so kika zo a dai'dai wannan lokacin?".
ÆŠan kwanto da kanta a saman shoulder É—insa ta yi tana mai cigaba da murmushi, daddyn ya gama ganota
ðŸ¤ðŸ”¥ð—¥ð—”ð—ªð—”ð—¡ð—œð—¡ 👑 ð—ð—”ð—Ÿð—œð—¡ð—–ð—œðŸ”¥ðŸ¤
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
ð— ð—”ð—Ÿð—Ÿð—”ð—žð—œð—¡
â¤ï¸â€ðŸ”¥FATEEMA ZAHRA MUSA â¤ï¸â€ðŸ”¥
(â¤ï¸A-K-A ð‘·ð‘¹ð‘°ð‘µð‘ªð‘¬ð‘ºð‘º ð‘»ð‘¬ð‘¬ð‘´ð‘¨ðŸ”¥)
Writer of DUK KARFIN IZZATA, TRIPLETS, and now RAWANIN ZALINCI.
🔥ðŸ¤T🔥ðŸ¤T🔥ðŸ¤W🔥ðŸ¤......💻
â¤ï¸ð‘«ð‘¨ð‘»ð‘¬ 6/7/2024.....âœï¸ðŸ“šðŸŒ¹
ðŸ¤ð‘ºð‘»ð‘¬ð‘· 1......âœï¸ðŸ“šðŸ”¥
اللَّهÙمَّ صَلّ٠عَلَى Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯Ù ÙˆÙŽØ¹ÙŽÙ„ÙŽÙ‰ Ø¢Ù„Ù Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯ÙØŒ كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ وَعَلَى Ø¢Ù„Ù Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ، Ø¥Ùنَّكَ ØÙŽÙ…Ùيدٌ مَجÙيدٌ، اللَّهÙمَّ بَارÙكْ عَلَى Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯Ù ÙˆÙŽØ¹ÙŽÙ„ÙŽÙ‰ Ø¢Ù„Ù Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯ÙØŒ كَمَا بَارَكْتَ عَلَى Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ وَعَلَى Ø¢Ù„Ù Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ، Ø¥Ùنَّكَ ØÙŽÙ…Ùيدٌ مَجÙيدٌâ¤ï¸
E____________8🔥
ÆŠan kwanto da kanta a saman shoulder É—insa ta yi tana mai cigaba da murmushi, daddyn ya gama ganota.
"Daddy dama batun zuwana wajensu mai rankarfe ne fa".
Ta yi maganar kamar wata mai in'ina.
"This time kuma can kike son zuwa?". Ya faÉ—a yana fitar da hannunsa É—aya dake a cikin alkyabbar tasa, lallauran kumatunta ya fara shafawa.
"Daddy ba Mummy ta ce Yah Omar zai kammala secondary school É—insa this time ba? Kuma ta ce yanzu zai dawo nan da zama idan ya kammala, shi ne zan je mu dawo a tare da shi ai".
"Ya kammala dai ba zai kammala ba mamana, shirye shiyen dawowa ma yake yi, sai dai ki je ki tarosa ku dawo a tare".
Shiru ta É—an yi kafin ta sake cewa. "To daddy yanzu a nan zai cigaba da karatu ko?".
Jinjina mata kai ya yi alamar e, da alama bai cika son yawan magana sosai ba, dan daga yanayin amsa mata É—in da yake yi zai nuna maka cewa sam baya son motsa bakinsa, dan ma ita ce, ba dan haka ba da ba amsawa zai yi ba.
Wani dakakken jarumin mayaki ne ya shigo cikin fadan, cikin girmamawa ya duƙa dan gaisuwa ga sallama, sannan ya sanar da shi cewa Sarkin yammaci yana son ganin sarki.
Cikin hanzari sallama ɗin ya ƙariso gaban stage da King yake a kai, a nutse ya haura sama, a daf gabansa ya zo ya zube gwiwowinsa a ƙasa, cikin girmamawa tare da zubawa King kirari kafin nan ya sanar da shi cewa Sarkin yammaci yana neman iso a gare shi.
Shiru na Æ´an mintocin da akallah zasu kai uku King ya yi, da alama fa King jinin mulkin nan ta ratsa shi sosai, dan izzar bala'i ke gare shi, magana cike da class, maganar mai sifirin ce, ana yi kamar ba'a son yi, ana yi kuma ana hutawa.
"Daddy in tafi ko?". Cewar auta, dan ita sam bata son hayaniya, yanzu ta san idan sarkin yammacin nan ya shigo sai an yi ta zuba mashi kirari, kuma sarkin yammacin matsayin wa yake ga marigayi King ABDUL MALIK BADEEN, dan dai a tsarin mulki idan mutun ya fika matsayin kujera to ya fika ne, ba dan haka ba ai da King Zuhair ɗin ne ma ya dace da ya je ganin Sarkin yammaci ba wai shi ya zo ba, idan kuka yi duba da kasancewar Sarkin yammaci a uncle na King Zuhair ɗin kenan, amma da yake kujerar yammaci tana a ƙarƙashin mulkin king Zuhair ne, dole sarkin yammaci ya zo da kansa idan yana da buƙatar ganin King.
"Kin gaji da zama ne?". Har lokacin kallonsa yana fuskantar cikin tsakiyar fadar, bai juyo gareta ba.
"Daddy ai naga kaka zai shi go ne, shi ne yasa zan tafi, sai can yamma ai zan dawo".
Jinjina mata kai kawai ya yi, ba dan yana son ta bar kusa da shi ba, sai dan kawai zai so ya gana da uncle É—in nasa ne cikin nutsuwa da mutunta juna ya kuma bashi hankalinsa waje guda.
Har lokacin Sallama yana duƙe a saman gwiwowinsa yana jiran amsar da king zai basa, dama a tsarin KINGDOM OF POWER wlh babu wanda ya isa ya shigo fada ta kofar can taba family ba ba tare da izini ba sai, mulki mai karfi ke garesu, kuma suna gudanar da mulkin nasu ne bisa ga bin dokokin da suka tsarawa masarautar, idan kun san abin da ake cewa ba sani ba sabo, to shi ne yake aiki a cikin dokokin wannan masarauta, babu sani kuma babu sabo, duk wanda ya yi ba daidai ba hukunci kawai ake yanke mashi, koma waye shi, hakan kuma ita ce adalci, ita ce dai'dai, wannan dalilin ne kuma yasa masarautar ta tara ɗinbin makiya na kin karawa, ba'a taɓa masarauta wadda ta tara maki a tarihi ba irin wannan masarauta, dama kun san idan mutun ya ce zai yi aiki bisa gaskiya da amana, zai yi mulki kamar yadda ta zo a Shari'ance, to ba shakka zai tara makiyan da shi kansa sai ya ji ya tsani duniyar ma gabaɗaya, dan duk in da ya juya makiya ne ta ko'ina, burin kowa kawai ya kaisa ƙasa, saboda kawai wannan gaskiya tasa, zata zamana harta makusantarsa ma basu barshi ba, wata kila ya taɓa hukuntasu dan sun yi laifi, suma sai su shiga sahun makiyansa, to a takaice dai haka King Zuhair yake da waɗan nan tarin uban makiyan ta ko'ina, sai dai shi mutum ne da ya riki Allah hannu biyu, sannan kuma mulki yake gudanarwa dai'dai da koyarwar addini, baya damuwa da kowa da komai, koda ɗansa ne ya yi laifi sai ya hukunta shi, adalci kawai ya sani, kuma duk wanda yasan tarihin modarawa dama yasansu da wannan ɗabi'ar, suna da adalci, basu taɓa mutum haka kawai sai in har shi ya taɓosu, idan kuwa ya yi gigin taɓosu fa sai dai mu ce sunansa sorry, dan gangan ma sai ta fishi dakuwa, gari sai ta fishi niƙuwa, MODARAWA No be wasa Wlh!!.
Miƙewa auta ta yi tare da cewa sallama ya sanar da Hoorain ita zata bi ta kofar nan da zai sadata da part nasu, ba zata fita ta kofar da kowa yake shigowa ba, wato kofar da ta shigo kenan, da yake kunsan da akwai kofar da zai iya sadaka da part na King a cikin fadar, dayawan lokuta ta nan ma family suke shigowa cikin fadar.
Kun san dai yadda tsarin mulki take, kuma ku daga gani kunsan madarar mulki ziryar ake bugawa a cikin wannan masarauta babu wasa. Dan haka ƙasa auta ta duƙa dan yi wa mahaifin nata sallama, wannan ma ɗaya ce daga cikin dokokin masarautu, ko da mahaifinka ne a kan mulki dole ka bashi girma fiye da tunaninku, kamar dai yanzu ita auta da ta zube gwiwowinta a ƙasa, ƴa ce mafi soyuwa a wajen babanta, amma dole ta bi dokar masarauta, shiyasa na ce maku king Zuhair harta ƴaƴansa idan suka yi laifi yana hukunta su, ba sani ne kuma babu sabo.
Sai da King ya bata izinin tafiya, sannan ta miƙe tsaye, cikin tsantsar so da kauna ta manna mashi kiss a kumatu kafin ta juya ta nufi step na sauka ta bayan King ɗin, dan kofar tana ta baya ne ba ta gaba ba.
Dawo da kallonsa a kan sallama dake tsugunne ya yi, cikin sanyin murya tare da magana É—aya ya furta an bashi izini, daga haka ya mayar da hannunsa da ya fitar daga cikin alkyabbarsa dan shafa kumatun Auta, sannan ya mayar da kallonsa a kan tsakiyar fadar.
Kirari sosai Sallama ya fara zuba mashi tare da ɗaga hannu sama ya dunƙuleta yana aikin zuba mashi jinjin da kuma faɗar kyawawan fararen halayensa.
Yana dake a saman kujerar nan bai ko motsa ba, ya hakince abinsa. Almost 2 mins Sallama ya ɗauka yana zuba wannan kirari kafin ya miƙe ya nufi kofar fadar dan ya isar wa da sarkin yammacin saƙon King.
A bangaren ita kuma Auta, tana fita cikin ainahin part nasu ta koma, ta baro su Chuchu a garden suna aikin yanka mata fruits. Akwai bayi sosai da suke ta faman safa da marwa a part ɗin nasu, kowace baiwa da aikin da take yi, duk idan auta ta zo wucesu sai sun tsugunna mata ƙasa alamar girmamawa.
Kai tsaye wani babban part ta shiga, tun daga kan yanayin tsarin wajen kasan wajene na mutane na musamman a cikin masarautar, saboda tsari ne mai matuƙar kyau da aka tsara shi, harta kwalliyar jikin bangon ginin wannan part ɗin kwalliya ne na musamman.
Ciki ta shige abinta, a babbar parlourn ƙasa ta tsaya, parlourn ya tsaru iya tsaru, dukiya ta yi kuka a wannan waje, komai na cikin parlourn launin dark blue and gold ne, kalar kuma ta yi matuƙar bada abin da ake so, dan ta kara bayyanar da cewa lallai nan gidan sarauta ne.
Kuyangu ne suke ta faman aikace-aikace na gyara a cikin parlourn, Æ´an mata ne su huÉ—u, kowacce da abin da take yi, daga mai gyara shinfiÉ—un alfarma dake saman kujeru, sai mai shirya pillows, É—ayar goge wajen Tv take, É—ayar kuma goge katafaren parlourn take ta faman yi.
Suna ganin auta suka zube gwiwowinsu a ƙasa tare da sunkuyar da kai ƙasa.
"Inan Akka?". Shi ne tambayar da autar ta jefa masu.
Cikin girmamawa har suna haÉ—a baki wajen cewa. "Akka tana sama".
Da sauri ta haye saman ba tare da ta sake bi ta kansu ba, wajen kyakkyawar elevator ta nufa, sama ta haye, sai faman farinciki take yi kamar wadda aka yi wa wani kyauta mai girma, daÉ—i take ji yayanta ya kammala secondary school zai dawo.
A hawa na ukku ta tsaya, sauka ta yi ta nufi cikin katafaren parlourn saman, cikin wani katafaren bedroom mai girman gaske ta shiga.
Wani shinfiɗaɗɗen king bed na alfarma ne a cikin wannan ɗaki, bed ɗin yana da girma sosai, kayin wannan King bed ɗin ya kai kusan taɓa sama, dan ya fi rabin bango, kuma iya wannan bed ɗin ne kawai a cikin wannan katafaren bedroom ɗin, sai wasu gajerun luntsuma luntsumar Dubai carpet dake shunfuɗe a kasar floor na ɗakin, tiles na cikin ɗakin gabaɗaya launin sky blue ne, sun sha gyara, sai ka ce kafa bai taɓa bi ta kansu ba, saboda tsafta, ga wasu triplets door masu kyau a jere ta ɓangaren dama a cikin ɗakin, ɗaya door ɗin toilet ne, ɗayan kuma na balcony, ɗayan kuma dressing room ne.
Akwai kuyangu guda biyu a cikin É—akin da suke yi wa mamallakin wannan É—akin hidima, Æ´an mata ne kuyangun masu jini a jika.
Wata kyakkyawar farar balarabiyar dattijuwa ce ke kwance a saman wannan katafaren bed É—in, kuyanga É—aya tana aikin matsa mata fararen kafafun nata, abinku da jiki na tsufa, É—ayar kuyangar kuma tana matsa mata hannunta, ita kuma tana kwance shiru abinta.
Hayewa saman bed É—in auta ta yi bayan ta gabatar da sallama kenan.
"Akka, Akka tashi ki ji wani labari". Shi ne abin da autar take ta faÉ—a.
BuÉ—e idanuwanta wannan dattijuwa ta yi, kwayar idanunta sak irin na autar, duk da take tsohuwa kyakkyawar gaske ce.
"Wani labari ne wannan haka Auta?". Ta yi maganar tana ƙoƙarin miƙewa zaune.
Cikin hanzari kuyangun nan nata suka ja da baya kaÉ—an tare da cire hannayensu daga tausan da suke yi mata.
"Akka Yah Omar ya kammala secondary school, kuma daddy ya ce zai dawo nan"
Akka zata yi magana sallamar Gimbiya Chuchu ya katse ta.
"Wato ke auta a nan kika zo kika yi zamanki kin barmu muna ta jiranki a garden ko? To ga can Aunty Fanan tana jiranki da fruits a hannu, ni ba zan iya ba na taho na yi wanka". Cewar Gimbiya Chuchu kenan.
"Aunty Chuchu ni fa na fasa shan fruits É—in, kuma ba yanzu zan koma garden ba, yanzu ina nan tukun nan". Ta kai karshen maganar tare da kwanciya a saman bed É—in ta tada kai da cinyar Akka.
Juyawa Gimbiya Chuchu ta yi ta nufi waje tana faÉ—in. "Ke dai kika sani, ni kinga wucewata, bari naje bedroom É—in can na yi wanka hai". Ta kai karshen maganar tata ma a kofar waje, dan tana tafiya ne tana maganar.
Bedroom na kusa da na Akka ɗin ta shige, tana shiga kuma ta hau cire kayan jikinta kamar wadda take sanye da ƙaya dama. Toilet ta nufa dan yin wanka, kasancewar wannan part ɗin na kakansu ce, Akka ita ce ta haifi King Zuhair, so kowa daga cikinsu yana da damar shigowa cikin wannan part ɗin ya yi abin da yake so, babu wanda zai yi mashi wata shamaki.
Ita kuwa auta, ta yi kwanciyar suka cigaba da hira a tare da Akka, shi kuwa Hoorain ya koma cikin mayaƙa ƴan uwansa, dama sai ta fito yake kula da ita, idan ta koma ciki shi ma komawa wajen ƴan uwansa mayaka yake yi.
Shi kuma King Zuhair suna can suna tattaunawa da Sarkin yammaci a kan yanayin halin rayuwa da al'umma suke a ciki, suna ta faman neman mafita, dan samawa mutanensu saukin wahalar rayuwa da ake ciki.
Idan muka waiwaya gidansu Zainab kuwa, and kafin mu waiwaya let me tell you one think about me and my story, ina son ku sani kowace marubuciya a duniyar nan da yanayin tsarin salon rubutunta wadda ta tsarawa kanta, kowacce da abin da ta fi karkata a kai, to abin da nake son ku sani a kai'na shi ne, ni salon rubutuna yana tafiya ne a kan part, part! Wato labaraina suna da ɓangarori da dama, nasan da dama daga cikin waɗan da suka karanta littafin TRIPLETS sun san yana da parts parts daban daban, a fita wannan a shiga wannan, idan ban yi karya ba a kallah akwai parts mabanbantan sama da guda 13 a cikin littafin TRIPLETS, parts nasu Abba ne, nasu Abbi daban daddyn jelly da dai sauransu, kuma kowani part kun sani da nashi roll ɗin da yake playing a cikin littafin, ba'a banza nake sako parts da dama ba, so ni haka salon nawa rubutun yake, kowacce writer da nata salon, ina maku albashir da cewa shi ma littafin RAWANIN ZALINCI tafe yake da parts mabanbanta da zasu ƙayatar da ku matuƙa, duk da cewa ba lallai ya kai yawan parts na TRIPLETS ba, sannan kowani parts da nasa cakwakiyar, kuma duk wanda kuka ga sako a cikin labarina da rawar da zai taka, ba haka kawai nake sakosu dan jin daɗin kai'na ba, fatan kun gane?.
â¥â¥â¥â¥â¥â¥â¥â¥â¥â¥â¥â¥â¥â¥â¥â¥â¥â¥â¥â¥â¥â¥â¥â¥
GIDANSU KHADIJAH🧡
A yanzu Khadija an zama ƴan'mata, kyau ya kara bayyana, ga surar jiki komai masha Allah, su Zainab iyayen san kyalliya ma an zama ƴan'mata, mamansu tana matuƙar kula da su, kamar yadda kuka sani ne babansu yana kula da su sosai, kuma tun daga kan Zainab mamansu bata sake haihuwa ba har yau, dangin miji sun sakota a gaba a kan cewa shiru shiru bata sake haihuwa ba, dama su jama'a ba'a iya masu, ka haifi dayawa ace ka cika haihuwa, idan kuma Allah ya dakatar maka da haihuwar, nan ma su isheka da shirun ya yi yawa yakamata ka kara, sai kace akwai wanda yake bada haihuwa ne a duniya, wlh jama'a muji tsoron Allah, ban cire kowa ba muji tsoron Allah! Mu dai'na takurawa waɗan da basu haihuwa da wuri ba ko kuma waɗan da basu samu haihuwa ba kwata kwata, domin kowa yasani cewa babu wanda ya isa ya bada haihuwa sai Allah mahalicci mai kowa mai komai, amma saboda son zuciya sai a murje idanu ayi ta takurawa baiwar Allah wai har yanzu bata haihuwa ba, to kada dai a manta mai bada haihuwar yana sama yana jin duk abin da ake yi kuma yana gani, ku ta cin zarafin yarinya idan bata haihu da wuri ba, a dai rinƙa jin tsoron Allah, wata ma idan ta haifi maza ace ta cika haifar maza, ta cikawa mutane gida da maza, idan kuma mata ne nan ma ace ta cika gida da ƴaƴa mata kamar dai Maman Zainab a yanzu, su maman Haidar sun sakota a gaba wai ta tara ƴaƴa mata kuma daga su ta lafe shiru ba kari, to gaskiya su shirun ya yi masu yawa, ko ta kara haifar wasu ko kuma baban Zainab ya karo aure daga cikin family, abin mamakin kuma duk wannan bala'i da maman Haidar ɗin take yi fa ita ma ƴaƴanta biyu rak, amma saboda son zuciya bata duba nata ba ta sakawa wata ido, da yake dama ba kaunar maman Zainab ɗin suke yi ba, dama ance laifi tudu, ka taka naka ka hango na wani, wannan matsala ta haihuwa ko rashinsa yana ɗawainiya da mata dayawa, to wlh mu ji tsoron Allah, mu sani Allah shi ne mai iko da komai, shi haihuwa idan Allah ya tsara ga lokacin da zai zo to fa babu uban da ya isa ya hana shi zuwa, ko uban magani kike sha dan hana ɗaukar ciki, wlh idan lokacin da Allah ya rubuta zaki haifi ɗan ya zo duniya, to fa ba makawa sai kin haife shi a lokacin, and lastly su ƴaƴa ai ba'a ƙayyadewa kai ga iya adadin da ake so, sai dai bawa ya faɗa kawai dan jin daɗin bakinsa, amma Ubangiji ya riga ya tsara maki ƴaƴa nawa zaki haifa a rayuwarki, dan haka ba sai kin wahalar da kanki ko kin wahalar da ƴar wasu a kan zancen bata haihuwa ba! Ki sani kema watara zaki iya haifar ɗiya mace, nasan babu wadda zata ji daɗi a sako ƴarta a gaba da cin mutunci a kan rashin haihuwa, to ki sani alkawari ne duk abin da kika yi wa ƴar wani sai anyi wa taki.
Ita dai Maman Zainab kome za'a faÉ—a sai dai ta kawar da kai tamkar bata san suna yi ba, dan ba yadda za ta yi da su, yayyun mijinta ne, dama kannensa ne to da sai ta iya saka baki, amma yayyunsa ne da mahaifiyarsa, dole ta ja bakinta ta yi shiru.
Wani babban abin bakin cikin kuma a nan shi ne, wai Haidar yana son Khadija, mamarsa kuma ta dage sai shi za'a bawa ita, kwata kwata yanzu fa shekarun Khadijan 17 years, shi kuma Haidar a yanzu yana da 27 years, amma haka yaron nan ya kafe wai sai ita yake so, yaga ta zama Æ´an'mata yanzu, komai zam zam, gata da tsafta da son kwalliya, dan tun suna yara mamansu ta saba masu da kwalliya idan baku manta ba, so yanzu abin ya bi jikinsu, tsaf tsaf da su.
Khadijah sam bata son shi, dan idan baku manta ba a baya tun suna yara yake kyararsu, baya kyautata masu, kun san yaro kuma da iya rike abu, to Khadijah dai bata manta da irin harara, mari tare da zagin da ya rinƙa yi masu tun shekaru goma zuwa shaɗaya a baya ba, dan haka sai ta tsane shi sosai.
Bugu da ƙari Khadijah bata son shi ne saboda rashin iliminsa, kunga dama shi bai yi karatu ba, to yanzu ita kuma tana Ss2, ganin wani iri wawa ma take yi mashi, dan ko sunaye bai iya rubutawa ba, idan an kira shi a waya sai ya tambayi Sadiq wanene mai kiran nasa, Sadiq ɗin ne yake gaya mashi sunan mai kiran nasa, ko saving number mutane a kasuwa Sadiq ɗin ne yake tallafa mashi ya rufa mashi asiri ya yi masa, babu abin da ya sani, shiyasa Khadijah ta yi mugun rai'na mashi wayo take ganinsa a very local, ga shi kuma kakanta wadda ta haifi babanta da kuma maman Haidar ɗin sun zage a kan tabbas shi zata aura tun da ya nuna yana sonta ai ba zasu bawa bare ba. Tirƙashi!! Yau ake yinta.
Kullum cikin kuka take yi baiwar Allah, har abin ya fara shafan karatunta, da babanta ya fahimci haka shi ne ya ce ta yi hakuri In Sha Allah ba zata auri Haidar ba, zai yi magana da mamar tasa, wato kakansu kenan, sannan ta rage zuwa gidan kakan nasu dan ta É—an huta da zancen Haidar É—in da ake yi mata, ita kuma kakan ta rike wuta a kan lallai Khadijah É—in tana gama Ss 3 sai aure kawai. Babbar magana, ko yaya wannan aure zai kasance? To mu dai namu ido.
Zainab dai sai dai ta bisu da ido abinta, babu ruwanta da su, a maimakon Haidar ɗin ya ce Zainab yake so tun da ita ce kara ma kuma ta fi Khadijah kyau, sai ya nace ya khafe lallai shi Khadija yake so, kuma ba komai ne yasa ya kafe sai ita yake so ba face surar jikinta, Zainab yanzu take girma, halittar jikinta bai bayyana sosai ba, su tula tula duk basu ciko sosai kamar yadda yake so ba, ita kuma Khadijah sai dai muce Masha Allah, komai ya ciko, abinku da jahili mara ilimi, tula tulanta da shape nata ne kawai suke ɗauke mashi hankali, sune a gabansa, dan ko wayarsa ka karɓa banda hotunan mata masu tula tulanta breast manya manya babu abin da zaka gani, yana sha'awar hakan sosai, ita kuma Khadijah akwaisu sosai, shi ne yasa ya nace dole sai ita yake so, kayan takaici! Dama ace son Allah da annabi yake yi mata ne, da sai ace to da sauki, amma saboda surar jikinta yake sonta kuwa kunga akwai babbar matsala, yana iya mayar da ita karamar bazawara, dan ba hankali ke gare shi ba, mutumin da ko karatun sallah bai gana iyawa ba, sai dai ba bi jam'i a masallaci, ai kunga babu abin da ba zai iya aikatawa ba, dama kuma ba ganin Mahaifiyarta da mutunci yake yi ba, abin dai sai dai mu saka Khadijah a addu'a.
â¥â¥â¥â¥â¥â¥â¥â¥â¥â¥â¥â¥â¥â¥â¥â¥â¥â¥â¥â¥â¥â¥â¥â¥
Zaune suke a parlourn, Maman Zainab kamar kullum ta gama shirya masu abincin darensu a tsakiyar parlourn, sun yi sallar issha suna zaune suna jiran Baban Zainab. Yanzu an kara gyara parlourn sosai, arziki ya ci uban na da, dan baban Zainab mutun ne mai taimako, hakan tasa arzikinsa yake kara bunƙasa sosai.
Zainab tana kallon labarai a kan KINGDOM OF POWER a news, a duniya yarinyar nan tana son wannan masarautar sosai, musamman idan ana magana a kan KING ZUHAIR ABDUL MALIK da ƴaƴansa, abin yana ƙayatar da ita.
Ita kuma Khadijah ta buga uban tagumi tana tunanin maganar da suka yi da Haidar ɗazun a kan cewa wai yanzu yakamata ta rinƙa kai mashi abinci ɗaki ne, bai kamata ya rinƙa zuwa da kansa yana ɗauka ba, dan saura ƴan watannin da basu fi 8 ba su rubuta waec and neco, suna rubutawa kuma sai aurensu, irin shi ya fara jin kansa a angon nan.
To kawai ta amsa mashi da shi, domin idan ta tsaya yin dogon magana da shi ma ko kuma ta ce zata yi mashi gardama, ƙaramin aikinsa ne ya mareta, Mamansu kuma bata da bakin magana, idan ta yi magana to ta jira isowar maman Haidar ɗin da tawagarsu gidan, tsabar bakin ciki wani lokaci ma ji Maman Zainab ɗin take yi kamar ta haɗa kayanta kawai ta bar gidan, amma idan ta tuna cewa idan ta bar gidan dole zata bar su Khadijah ɗin a gidan, ta gudu kenan bata tsira ba, ai gara mata ma ta zauna da su, dan kada ta tafi wani abin ya haɗo Haidar da Khadijah ya zo ya yi masu ba dai'dai ba, dan ba hankali ke gare shi ba.
Wannan dalilin kawai yasa take hakuri ta cigaba da zama cikin takurar wannan balaƴaƴƴar wato Maman Haidar, shi ma baban Zainab sam baya jin daɗin abin, amma yana can yana ta faman neman mafita ta yadda zai lallaɓa mahaifiyarsa ta hakura da zancen auren, su bar Khadija ta kawo mijinta wanda take so, kullum suna cikin zuba addu'a sosai.
Sallamar Aunty Hauwa ce ta katse masu abin da suke yi a in da dukkansu suka kai kallonsu kofar shigowa, amma ban da Khadija da kanta yake kallon ƙasa ta buga uban tagumi, da alama ma bata ji sallamar Aunty Hauwa ɗin ba.
Hannunta É—auke da manya manyan ledoji ta shigo cikin parlourn. Da murna Maman Zainab ta tarbeta tana faÉ—in
"Daga ina kuma Hauwa da wannan uban kayan?".
Da yake yanzu Aunty Hauwa fa ta zama dillaliya, saye da sayarwa take yi, har gida mata suke kawo mata kaya irin kamar mace ta yi suna an tara mata atamfofi tana son ta sayar, sai ta kaiwa Aunty Hauwa ta saya da sauki ta bata kuÉ—in, sannan ta fitar ita kuma ta sayar a sabo, ba abin da bata saya ta kuma sayar, har da su gadaje second hand, su kujeru dukka.
A tsakiyar parlourn ta shirge niki nikin kayan tare da zama a saman sofa tana mayar da numfashi, tamkar ba matar aure ba ta wani yafo É—an mayafin da ko kafaÉ—unta basu gama rufewa ba.
"Wlh daga gidan wata dillaliya nake, na je ne nan na kwaso wasu manya manyan zannuwar gado, shi ne na ce bari na kawo maki ko zaki saya". Cewar Aunty Hauwar kenan.
"Kai Hauwa akwai ki da neman magana, ai kin san ni komai baban Zainab ne yake saya mun, kin taɓa ganin na sayi wani abin da kuɗi na ne?".
Girgiza mata kai Aunty Hauwar ta yi alamar a'a bata taɓa gani ba.
"To kin gani, shi ne nan mai sayan komai, zannuwar gado duk bayan wata biyu yana zuwa mana da sabbi daga kasuwa".
Ɗan taɓe baki Aunty Hauwar ta yi kafin ta furta kun ji daɗinku ai.
Murmushi maman Zainab ta yi tare da faÉ—in. "Gaskiya kam mun ji daÉ—i, kema ai kina jin daÉ—i, sai kasuwancinki kike yi kina tare kuÉ—aÉ—e".
"Hmmm kasuwanci ko wahala? Yanzu duba fa sai da na fita na je na kwaso kayan nan da kai'na, ke kuma fa? Kina zaune a gida babu in da kike zuwa, baki shan wahalar nema, baki shan rana, sai dai duk abin da kike so ayi maki, ai kinga ni dake akwai banbanci, ku ne masu jin daÉ—i, Allah dai yasa mu adanshinku".
Kara faÉ—aÉ—a murmushinta Maman Zainab ta yi. "Zainab ba zaku gaishe da Aunty Hauwa ba ne? Ki kawo mata ruwan sanyi ta sha".
Ɗan turo baki gaba Zainab ɗin ta yi tare da miƙewa ta nufi wajen fridge, tana yi wa Aunty Hauwar sannu da zuwa. Ruwa mai sanyi roba ɗaya ta ɗauko mata tare da wani kyakkyawar plastic cup. A gabanta ta zo ta ajiye mata, sannan ta juya ta nufi cikin ɗakinsu.
Miƙewa ita ma Khadijah ta yi, ba tare da ta kalli in da Aunty Hauwa ɗin take ba ta yi mata sannu da zuwa kafin ta sa kai ta wuce ɗakinsu.
"Maman Zainab wai menene yake damun Khadijah ne? Yau na ganta wata iriya da ita, sam bata da walwala". Cewar Aunty Hauwar, ta yi maganar kuma tana zuba ruwan da Zainab ta kawo mata a cikin cup dan ta sha.
"Hauwa kenan ke da kin san komai, maganar nan ne dai na aurenta da Haidar, wai ina kika baro su Khalid ne Hauwa?".
Sai da ta sha ruwan da ta zuba a cup ɗin, sannan ta amsa mata da cewa. "Su Khalid suna gidan kakarsu, amma kema maman Zainab wlh da laifinki, yaushe zaki tsaya suna yi maki irin wannan cin kashin? Sai na yi maki magana sai ki ce ai yayyunsa ne ba kannensa ba, to su yayyun nasa idan suka yi ba dai'dai ba ba'a gyara masu zama ne? A ina kika taɓa jin irin wannan? Ki zauna ki yi shiru kina ji kina gani za'a lalata maki rayuwar yarinya, kefa haka kike, tun muna makaranta ma ni nake tare maki faɗa, sai ki yi shiru ki bari kowani kare da doki yana takaki son ransa, ni wlh ba zan ɗauki wannan iskanci ba, shiyasa ma nake kara godewa Allah da ya bani yara dukka maza babu mace a ciki, dan na huta da waɗan na rigingimun". Ta kai karshen maganar alamar ranta ya ɓaci.
"Hauwa ke ba zaki gane bane, wlh ni ba zan iya fito na fito da mahaifiyarsa ba, saboda kinga babban Zainab bai cancanci na yi koda musu ne da mahaifiyarsa ba, shi zaki duba, yana yi mana komai dan ya sanya mu cikin farinciki, a gaskiya ko ba dan ma haka ba ni ba zan iya tsayawa ina fito na fito da mahaifiyarsa ba ko na yi mata rashin kunya, ba zan iya ba, dan uwa uwace ko mai lalacewarta".
Girgiza kai Aunty Hauwar ta yi. "Ai nima ban ce ki yi fito na fito da mahaifiyarsa ba, ita wannan Maman Haidar ɗin zaki gyarawa zama, ita zaki takawa birki, cin kashi ya yi yawa, suna zaginki a kan kin tara masu ƴaƴa mata a goda, ga shi har Yanzu shiru baki sake haihuwa ba sai dai ki ci ki kwanta sai kiɓa kike yi, sannan kuma saboda basu da kunya sai su dawo suna neman auren ƴar taki da kika tara masu a gida wa ɗansu? Kuma duk da suna neman auren ƴar taki ma basu dai'na ci maki mutunci ba? A haka kuma kike tunanin zaki zuba masu ido? Ai wlh basu isa ba, bari zaki yi rana ɗaya idan Maman Haidar ɗin ta zo ta nemi kawo maki rai'nin wayo, a nan ne zaki taka mata birki, ki karta mata jar warning mai zaman kanta, hakan zai sanya ki ɗan huta, haba abin ya yi yawa mana".
Tana magana tana wani kara ɓata rai.
"Hauwa ba zaki gane bane, misali yanzu idan na yi wa maman Haidar magana cikin ɗaga murya ma, wlh to ki jirayi zuwan kakansu, dan sai ta je ta kwashi karya da gaskiya ta gayawa mahaifiyar tasu, ita kuma zata sako hijabi ta zo nan ta ci mutunci na fes, kullum sai ta ce zata sanya baban Zainab ya sake ni, ni kuma a yadda su Zainab suka taso yanzu suke ƙoƙarin zama ƴan'matan nan zamana dasu shi ne mafi a'ala a gareni, a yanzu nisa da su babbar haɗari ne a gareni, kinga yanzu suke tashen girma, yanzu ne suke buƙatar kulawata sosai, dan haka gara na jure na cigaba da hakuri na zauna da babansu har izuwa lokacin da zan kaisu ɗakin mazajensu lafiya, daga nan sai na san abin yi".
Ta kai karshen maganar tamkar zata yi kuka, idanuwanta sun ciko tab da kwallah, abin gwanin ban tausayi, takura sam bashi da daÉ—i a rayuwar nan.
Aunty Hauwa na ƙoƙarin yin magana suka tsinkayo sallamar baban Zainab ɗin a bakin kofar shigowa parlourn, sun dawo ne daga masallacin sallar issha.
Jin sallamarsa yasa Aunty Hauwar ta miƙe tsaye tana faɗin.
"Zamu karisa maganar idan kin zo gida ko kuma idan na sake zuwa, yanzu dai bari na wuce dare ya yi, kuma kinga unguwar nan taku sai a hankali, kada wani ya bugeni ya kwashe mun kaya".
Tana magana tana tattare kayan nata, haka ta jidesu ta nufi waje. Dai'dai lokacin kuma Baban Zainab ya shigo cikin parlourn.
Kamar yadda kuka sani ne, ko sannu bai ce wa Aunty Hauwar ba, yasa kai zai wuce, dan haka yake.
Cikin sauri ta É—aga mashi gaisuwa, ya sha dakakkiyar shaddarsa É—inkin mutunci, yanzu kuÉ—i sun fara zama mashi zamzam, wani katafaren gini ma yake ta faman gina masu, hawa É—aya ce gidan, idan ya kammala zasu koma can abinsu, sai dai kash dangi sun sako shi a gaba a kan ya kara aure tun da Maman Zainab taki ta sake haihuwa, Maman Haidar har da wani cewa sun gaji suna son sake ganin yara Æ´an dogwai dogwai a gidan. ÆŠan adam kenan, ba'a iya mashi.
A takaice ya amsa mata gaisuwar tata tare da sanya kai ya wuce ciki abinsa.
Har bakin kofar gida Maman Zainab É—in ta rako Aunty Hauwar, yau ma kamar kullum sai da ta bata dubu É—aya wai ta hau mashi.
Karɓa ta yi tare da zuba mata godiya. Daga haka suka yi sallama, Maman Zainab ta wuce ciki, ita kuma Aunty Hauwar ta nufi waje.
Tana fita Sadiq bawan Allah ya fito daga cikin É—akinsu ya zo ya rufe kofar gidan tare da kalewa da sakata, sannan ya koma cikin É—akin nasu.
Haidar sai faman sanya kaya yake yi shi a dole zai fito tsakar gida su yi hira da Khadijah, ita kuma sam bata son yin hira da shi da daddare, dan kullum sai ya rinƙa ƙoƙarin taɓa jikinta, tsabar jahilci sai ya ce ai ita ƙanwarsa ce kuma aurensu ya kusa.
A kule take ce mashi ya bari sai anyi auren tukun nan, haka dai take fama da shi, baiwar Allah, ga shi ta kasa iya gayawa babanta abin da yake yi mata su É—auki mataki, ta rasa ina zata saka kanta, mamanta ta yi so silent over. Shiyasa wani lokaci shiru shiru ma bashi da daÉ—i sam.
Masu buƙatar littafin TRIPLETS daga farko harshen su yi mun magana ta wannan number tawa, 08161390581.*
ðŸ¤PRINCESS TEEMA taku ta amana🔥
Share fisabilillahi ðŸ‘
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥ðŸ¤
ðŸ¤ðŸ”¥ð—¥ð—”ð—ªð—”ð—¡ð—œð—¡ 👑 ð—ð—”ð—Ÿð—œð—¡ð—–ð—œðŸ”¥ðŸ¤
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
ð— ð—”ð—Ÿð—Ÿð—”ð—žð—œð—¡
â¤ï¸â€ðŸ”¥FATEEMA ZAHRA MUSA â¤ï¸â€ðŸ”¥
(â¤ï¸A-K-A ð‘·ð‘¹ð‘°ð‘µð‘ªð‘¬ð‘ºð‘º ð‘»ð‘¬ð‘¬ð‘´ð‘¨ðŸ”¥)
Writer of DUK KARFIN IZZATA, TRIPLETS, and now RAWANIN ZALINCI.
🔥ðŸ¤T🔥ðŸ¤T🔥ðŸ¤W🔥ðŸ¤......💻
â¤ï¸ð‘«ð‘¨ð‘»ð‘¬ 8/7/2024.....âœï¸ðŸ“šðŸŒ¹
ðŸ¤ð‘ºð‘»ð‘¬ð‘· 1......âœï¸ðŸ“šðŸ”¥
اللَّهÙمَّ صَلّ٠عَلَى Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯Ù ÙˆÙŽØ¹ÙŽÙ„ÙŽÙ‰ Ø¢Ù„Ù Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯ÙØŒ كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ وَعَلَى Ø¢Ù„Ù Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ، Ø¥Ùنَّكَ ØÙŽÙ…Ùيدٌ مَجÙيدٌ، اللَّهÙمَّ بَارÙكْ عَلَى Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯Ù ÙˆÙŽØ¹ÙŽÙ„ÙŽÙ‰ Ø¢Ù„Ù Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯ÙØŒ كَمَا بَارَكْتَ عَلَى Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ وَعَلَى Ø¢Ù„Ù Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ، Ø¥Ùنَّكَ ØÙŽÙ…Ùيدٌ مَجÙيدٌâ¤ï¸
E____________9🔥
A saman sofa baban Zainab ya zauna yana jiran shigowar maman daga rakiyar Aunty Hauwa da ta yi. Bawan Allah tunaninsa duk yana wajen yadda zai yi da mahaifiyarsa, ga jikin tsufa, idan ka fara yi mata magana duk sai ta bi ta rikice ta ce wai an zageta, haka take yi, ta tsufa sosai, dan a Æ´aÆ´anta Baban Zainab shi ne wajen na shidda, and dukka mata ne Æ´aÆ´an nata shi ne kawai namiji, uku daga ciki sun rasu sun bar mata jikoki tana tare da su, wani lokaci Æ´aÆ´an suna wajen kakarsu ta wajen ubansu kenan, wani lokaci kuma suna wajenta, yanzu daga maman Haidar, sai wata mai bin Maman Haidar É—in takwarar Zainab, sai babansu Zainab, sune manyan da suka rage, sai kanana mata guda biyu da duk suma sun yi aure suna É—akin mazajensu, so a takaice dai tsohuwa ce sosai kakar tasu, shi ne yasa take a birkice sosai.
Baki a É—auke da sallama Maman Zainab ta dawo cikin É—akin, kusa da shi ta zo ta zauna tana yi mashi sannu da dawowa daga masallaci.
Ƙaƙalo murmushin dole ya yi kafin ya ce. "Ina su Khadijah? And ina kayan da na dawo da shi daga kasuwa?".
"Suna ciki, kayan ma na kai É—aki".
Ta bashi amsa tana miƙewa tsaye, ɗakinsu Khadijah ɗin ta nufa domin ta kirasu su zo su ci abincin dare.
Da fitowarsu kallo É—aya baban ya yi wa Khadijah É—in ya kawar da kallonsa, har Æ´ar rama ta yi.
A in da suka saba zama a nan suka zauna.
"Khadijah ɗauki abincin su kawu Sadiq ki kai masu". Cewar mamanta, da yake bata san abin da yake faruwa ba, bata san cewa Haidar ɗin yana son keɓewa da Khadijar dan ya rinƙa taɓa mata jiki ba.
Cikin sanyin murya a takaice ta ce. "Zainab ta kai masu pls Mama".
Babansu ne ya amsa da cewa. "Yeah nima abin da zance kenan, Khadija ba zata sake kai masu abinci ba, ita ma Zainab ɗin daga yau idan ta kai masu shikenan, su zo su rinƙa ɗauka da kansu!".
Ya yi maganar ne cikin umarni, babu wasa a tattare da shi, hakan yasa Maman Zainab É—in ta amsa mashi da to In Sha Allah hakan za'ayi.
Turo baki Zainab ta yi kamar zata sa ihu, dan ita fa a duniya ta tsani zuwa koda kofar ɗakinsu ne, bare ma idan kawu Sadiq baya nan, sai ta ji kamar ta yi ta zunduma ihu idan aka aiketa koda ɗaukar abu ne a cikin ɗakin, bata son ganin Haidar, amma ya zata yi? Dole ta miƙe ta zuro hijabi kafin ta ɗauki ƙatuwar kular abincin tare da plates ta nufi waje da shi.
A bakin kofar ta tsaya ta kaiwa kofar É—akin kauri da kafa kamar shi ne ya yi mata laifi, yadda kuka san kofar ne ya sakata dole ta kawo abinci.
Daga ta cikin ɗaki Sadiq bawan Allah ya ce. "Zainab ba? Ai nasan sai ke ce zaki buga mana kofa irin haka, to sannu da ƙoƙari ƴar neman rigima......"
Bai gama rufe baki ba Haidar da yake tsaye wajen mirror ya karɓi zancen cikin faɗa da cewa.
"Ai wlh Zainab sai na koya maki hankali a gidan nan, ba ke baki da hankali ba? Yanzu mu sa'anninki ne da zaki zo ba sallama ki hau dukan mana kofa? Bari na same ki a waje sai na sharara maki Marika". On a serious note ya yi maganar.
MurguÉ—a mashi baki ta yi dan tasan baya ganinta, sannan ta ce. "Kawu Sadiq ga abincinku nan in ji mama".
Har suna haɗa baki shi da Haidar wajen magana, shi Sadiq ya ce ta ajiye a waje bari ya zo ya ɗauka, shi kuma Haidar ya ce to uban waye take so ya zo ya karɓa? Waye sa'anta? Ta kawo ciki ta ajiye.
Banza ta yi da Haidar ɗin kamar bata ji me ya ce ba, dan dama ita Zainab haka take, yadda kuka san me za'a ce ne, ta iya mannin hauka ta mayar da mutane ƴan iska, idan ka yi mata maganar da bai yi mata daɗi ba kuma kana da matsayin da ba zata iya ramawa ba kamar dai yayan nasu, sai ta mayar da kai ɗan iska, ta yi kamar ma bata ji me ka ce ba, kamar ma bata san kana yi ba, idan kuma tasan tana da halin ramawa, to wlh bata barin kota kwana, tsab zata solleka soso da sabulu. Yanzu ma abin da ta yi kenan, ta ajiye abincin a kofar ɗakin tare da murguɗa baki kamar Haidar ɗin yana ganinta, sannan ta watsa masu daƙuwa da yatsunta biyar yadda kuka san suna ganinta, kofar ɗakin ma fa a rufe yake, amma haka ta tsaya tana huce haushinta a waje, abin gwanin ban dariya.
Bayan ta watsa masu dakuwar ma bai yi mata ba, sai da ta dunƙule hannu ta yi alamar zata kai haushi tana wani watso harara da waɗan nan fararen idanuwan nata kamar na mage.
Muryar Haidar ne ya katseta da cewa. "Ke ba zaki kawo mana abincin bane kina tsaye a waje?".
Kara murguÉ—a baki ta yi kasa kasa ta ce.
"Mahaukacin banza ba za'a kawo É—in ba".
Ta yi maganar ta yadda ita kanta bata wani ji sautin muryarta ta fita sosai ba, sannan tsabar faÉ—a irin nata da rigimar tsiya har da murguÉ—a mazaunanta kafin ta sa kai ta wuce parlournsu ba tare da ta sake kula Haidar É—in ko ta ce masu ga abincin a kofar É—aki ba, ta mayar da Haidar É—an iska, ta barshi yana ta zuba masifa a kan ta kawo abinci cikin É—aki, irin shi yaya babban nan, Zainab kam dai'dai take da shi yarinyar nan, ita ce nan tasan maganinsa, idan yana mata magana ma wata sain wlh sai ta toshe kunne, ko kuma ta kara gaba ta bar shi a gantale.
Shiru shiru Haidar ya ji Zainab dai bata amsa ba kuma bata shigo da abincin ba, a kule ya nufo kofar É—akin da nufin yana buÉ—ewa sai ya zabga mata mari.
Sai dai kash, yana buɗewa bai ga ko mai kama da ita ba, tuni ta ajiye masu abincin a bakin kofa ta yi gaba abinta. Ransa idan ya yi dubu ya ƙara ɓaci sosai, amma ba yadda zai yi, dan babansu yana nan, bai isa ya je ya kamata ya daka ba, hakan tasa ya hakura ya koma cikin ɗakin kawai, tsabar shegen son girma sai bai ɗauki kular abincin ba, ya koma cikin ɗakin ya ce Sadiq ya je ya shigo da abinci.
Sadiq kuwa bawan Allah ɗan ba ruwana, miƙewa ya yi ya ɗauko abincin ya shigo masu da shi ciki, sai wani cika Haidar yake yi yana batsewa, shi a dole an ɓata mashi rai.
A can cikin parlourn kuwa, Khadija cikin hanzari ta ci abincin darenta, a daddafe ma ta tura abincin, ba wani É—anÉ—ano da take ji, ci kawai take yi.
Suna kammalawa ta miƙe sauri sauri ta wuce cikin bedroom nasu, da kallo iyayen nata suka bita da shi, dukkansu ba karamin tausaya mata suke yi ba, babanta ya so ya tsayar da ita dan taga kayayyakin da ya sayo masu daga kasuwa, ya so su buɗe kayan a daren nan ya bawa kowa nasa, amma ganin bata cikin nutsuwa da kwanciyar hankali yasa ya kyaleta zuwa da safe.
Ita kuwa Zainab sai da ta ɗan jima a parlourn tana hira da babanta bayan sun gama cin abincin kenan, sai ƙarfe 9 dai'dai ta miƙe tare da yi masu sallama ta wuce ciki.
Kwance ta isko Khadijah a saman bed, sai dai da alama bata yi barci ba. Wanka Zainab É—in ta yi tare da fitowa ta yi shirin kwanciya, sannan ta haye saman bed É—in tana kallon Æ´ar uwar tata.
"Baki kashe wutar É—akin ba ai Malama". Cewar Khadijah.
"Aunty khadina ki bar wutar a kunne mana tun da dukka labulayenmu a sake".
Shiru Khadija É—in ta yi mata, bata sake yin magana ba. Zainab bata shiri da duhu ne, bata barci cikin duhu, idan kunga sun kashe wutar É—akin nan nasu to sai dai idan Zainab ta yi barci ne, sai Khadijan ta kashe, wani lokaci dukkansu suna yin barci su barshi a kunne, sai iyayensu sun shigo yi masu addu'a, sannan ne suke kashe masu wutar É—akin.
Kwanciya Zainab É—in ta yi tana tunani rayuwar yayar tata.
A hankali Khadijar ta ambaci sunanta Zainab.
Juyawa gareta Zainab É—in ta yi suna fuskantar juna.
"Lafiya Aunty Khadina?".
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce. "Babu komai, amma anjuma idan kin tashi yin sallar dare ki sakani a cikin addu'a sosai, dan ni yanzu na shiga lokacin rashin sallah tun bayan sallar issha da na yi, dan haka kada ki tasheni yau".
Shiru ta É—an yi kafin ta bata amsa da cewa. "Aunty khadina ai kinsan kullum ina yi maki addu'a, da izinin Allah ba zaki auri Yah Haidar É—in nan ba, Allah ni kakan nan ma wani lokaci idan tana masifar nan tata kamar na kifeta da mari nake ji".
Harara Khadija É—in ta wurga mata kafin ta ce. "Ki mareta ta mutu ki shiga uku, wannan tsohuwa baki mareta ba ma tana rangaji ita kaÉ—ai a saman iska, ai kina yin kuskure ko kaÉ—an ne kika bugeta wlh ranga ranga za'a kwasheta, kin ga daga nan ke kuma sai koma".
Guntun tsaki Zee ɗin ta ja tare da juyawa ta bawa Khadijahr baya tana wani ƙara haɗe rai. Da alama fa da Zainab aka ce za'ayi wa wannan aure to ba shakka zata yi fito na fito da su, sam lamarinta babu sauki, da wuya su Maman Haidar su sha a hannunta, dan da alama zasu gasu sosai, yanzu ma dan mamanta na taka mata birki ne, ba dan haka ba, da ba abin da zai hanata yi wa Maman Haidar ɗin tas idan ta zo gidan tana zuba masifa, amma Mamansu da yake macece mai tarbiya tana tsawatar masu sosai, tana gaya masu maman Haidar dai ɗaya take da babansu, so idan har Zainab zata yi mata rashin kunya, to kenan zata iya yi wa babanta, dan haka babu ruwansu, idan ma sun ga Maman Haidar ɗin ta zo maza su wuce cikin ɗaki, kada ma su kawo kunnuwansu a kan abubuwan da zata yi ta faɗa, su kyaleta watarana sai labari.
A can parlourn kuwa, Haidar ya zo da nufin su yi hira da Khadijah, babanta ya ce mashi ta yi barci, tsabar bashi da kunya wai a tasan mashi ita akwai abin da zai gaya mata ne.
Da farko Maman Zainab zata je ta tasheta, sai baban ya ce a'a a barta ta yi barci sai da safe ko idan sun dawo daga makaranta sai ya gaya mata koma me zai gaya mata, yanzu dai tun da ta rigada ta yi barci ya kyaleta.
Da farko kamar ba zai tafi ba, dan ba hakan ya so ba, ransa ta ɓaci, ya so ne su yi hira da ita, amma da yake kawun nasa ne ya yi magana dole ya hakura, da ace Maman Zainab ita kaɗai ce a gidan da ba abin da zai hana shi shiga cikin ɗakinsu ya tasheta ta fito ayi hiran dole, dan ba kunya ne ke gare shi ba, ga rashin hankali cikakke, kuma kun san ba ganin mutuncin Mamansu yake yi ba, tsab zai iya cewa zai shiga ya tasota da ace baban baya nan.
Amma fa duk rashin kunyar Haidar yana tsoron kawun nasa, dan fa baban Zainab shi ma mutun ne mai zafi sosai, kawai sai anyi mashi ba dai'dai ba É—ayar halin nasa ta zafin rai take bayyana, Haidar É—in ya ci duka a hannunsa lokacin da yake kin zuwa makaranta, ya sha punishment, sai da kakansu wato maman baban Zainab É—in ta ce bata so kada ya sake dukan Haidar, ya kyale shi mana tun da ba za'a ci karatu ba, har da cewa wai shi ma baban Zainab É—in da ya yi karatun ai ga shi nan result É—in bata amfane shi ba, ya ajiyeta a cikin akwati kawai yana kallo, to dan haka ya rabu da Haidar É—in, kun san kaka dama yawanci haka suke, sai su hana a ladabtar da jikokinsu.
Haidar dai kamar zai yi kuka ya wuce ya koma cikin ɗakinsu, a lokacin shi kuma Sadiq yana zaune ya zuba abinci a cikin plate dan ya ci abinsa, shi ko zancen auren ma baya yi, yanzu haka master nasa yake haɗawa a ɓangaren computer engineering, ya gama degree nasa bawan Allah, akwai shi da ƙoƙari sosai, so baya batun aure ma, mata ma yanzu ba su ne a gabansa ba, ilimi da kuɗi kawai yake nema, mamansa ta ce ya nemi kuɗi da ilimi mata zasu biyo shi har in da yake ba sai ya wahalar da kansa ba wajen bin matan ba, ya bi kuɗi da ilimi a guje su kuma mata zasu biyo shi a guje, uwa ta gari kenan, saɓanin uwar Haidar da take cewa ilimi bashi da wata amfani.
Washegari da safe kamar yadda suka saba, tun karfe biyar na asuba bayan sun yi sallar asuba Maman Zainab ta wuce cikin kitchen, abinci mai rai da lafiya ta girka masu a matsayin breakfast, a tare da Khadijah suka yi aikin komai, ita kuma Zainab ta gyare masu gidan ko'ina tsab, ta zuba turaren wuta mai rai da lafiya kamar dai yadda suka saba, yanzu Maman Zainab ƴan'matanta sun girma, aiki ya ragun mata sosai, idan Khadija tana kitchen, ita kuma Zainab zata hau gyaran gida, komai a tare suke yi su ukun kamar wasu kawaye, haihuwan ƴaƴa mata akwai daɗi kuma akwai falala da rahama sosai, ƴa macece kawai Allah ya ce a ranar gobe kiyama zata kai iyayenta aljanna, manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce duk iyaye da suka haifi ƴaƴa mata guda uku, suka tarbiyantaddasu har suka aurar da su ba tare da waɗan nan ƴaƴa sun taɓa yin zina ba, to ba shakka sanadiyar haka Allah ya bawa waɗan nan iyaye aljanna, ƴan macece kawai take da wannan falala, amma a duniyarmu ta yau dayawan iyaye maza basu son a haifa masu ƴaƴa mata, ɗa namiji baya kai iyayensa aljanna kai tsaye, mace kawai Allah ya bawa wannan falala, ai ko dan kwaɗayin aljanna dole muso ƴa ƴa mata, idan ka duba sahabban Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, irin shekarun da suka shafe suna aikata aikin Allah ba dare ba rana kafin su sami aljanna, wasu daga cikinsu ma kashesu aka yi, wasu daga cikinsu kafurai sun azabtar dasu azaba mafi muni, idan ka dube su ka dubi ɗan aikin da kake yi, sai ka ji aljanna fa ba abar wasa bace, ba'a samunta a sauki, Allah dai ya bamu ita ba dan halayenmu ba, sai dai mu roki cin albarkacin fiyayyen halitta.
Karfe 6 dai'dai suka kammala girki, ita kuma Zainab ta kammala gyaran gida har ta yi wanka ta shiryo cikin white uniform ɗinta, kal kal da shi, ya sha guga malam, ta fito fes, Zainab sarkin farin jini, kowa ya ganta sai ya ce yana sonta, sai dai akwai ta da mugun hali in ji matasa da suke biyota bata kulasu, suka ce mugun hali ke gareta......... Ni kuwa PRINCESS TEEMA na ce tsare mutunci da tsare kai dai, ba wani mugun hali munafukai, dan basu sami abin da suke so ba, bata kula kowa, ga shegen kyau jajir da ita, nan gani nan bari munafukai kawai.........😂😅
A parlourn suka zauna dan yin breakfast kamar yadda suka saba, Khadija ta wuce cikin bedroom nasu dan ta yi wanka ta shirya cikin uniform nata, ita kuma Maman Zainab ta wuce nasu bedroom É—in dan ta taso baban Zainab ya yi wanka ya zo su yi breakfast, sai ya É—auki su Zainab a kan mashin nasa zuwa makaranta, dama shi yake kaisu, lokacin tashi kuma sai ya bawa Sadiq key É—in mashin É—in daga kasuwa ya zo ya É—auko su ya mayar da su gida sai ya dawo, islamiya kuma a kusa da gidansu yake, ba nisa sosai, so da kafa suke zuwa.
After some minutes
GabaÉ—ayansu sun haÉ—u a parlourn, baban Zainab ma ya yi wanka ya yi shirin zuwa kasuwa.
"Zainab É—auki abincin su Sadiq ki kai masu". Cewar mamansu.
Babansu ne ya ce. "Ba na ce su zo su rinƙa ɗauka da kansu ba?".
"Yi hakuri na manta ne ban sanar da su su zo su rinƙa ɗauka ba, amma idan sun fito zan gaya masu, yanzu dai ta ɗauka ta kai masu".
Shiru ya yi bai sake magana ba.
Ita kuwa Zainab tamkar zata zunduma ihu dan bakin ciki, ga shi jiya ta yi wa Haidar rashin kunya ta gudu, yanzu in ta je idan ta yi knocking na kofar, in dai Haidar ɗin ne ya fito tasan confirm sai ya rankwasheta a kai ko kuma ya mareta, da dai Sadiq ne ya fito lafiya lou zai karɓi abincin ya koma ciki.
Rai a matuƙar ɓace tana hura hanci ta ɗauki kular abincin tare da plates ɗin ta fito.
Ta kuwa yi sa'a tana fitowa ta ci karo da Sadiq wanda ya fito a lokacin shi ma, ya fito zai fitarwa da babansu mashin nasa ne, yana shirye cikin white shaddarsa mai shegen kyau, É—inki half jompa, ya sha hularsa, sai ya fito a babban mutun mai kima da mutunci, yanzu yana da 28 years, sai ya fito a cikakken matashi mai cike da nutsuwa da kamala.
"Kawu Sadiq ina zaka je?". Cewar Zainab É—in.
"Babu gaisuwa sai tambayar ina zan je ko?".
Ƴar murmushi kaɗan ta yi, Zainab baka taɓa ganin fara'arta sai idan da Sadiq ko iyayenta or Khadijah suke tare, nan ne zaka ga tana murmushi.
"Ai mantawa na yi, naga kayi kyau sosai ne yau shiyasa na manta da gaisuwar, to ina kwana".
Ta kai karshen maganar tare da ƙarisowa gabansa.
Hannu yasa ya karɓi kayan abincin yana amsa mata gaisuwar kafin ya ce mata. "Ina da class 7:30 dai'dai ne, yau ba kasuwa zan wuce kai tsaye ba, shiyasa na yi kyau haka, ko baki son na yi kyau ne?".
Girgiza mashi kai ta yi tana faÉ—in. "Kawu Sadiq ai dama kai kana da kyau, ranar ba na gaya maka kafi mamanmu kyau ba? Baba ya ce mama dan ita fara ce kawai, da ita baka ce mummuna ce, wai ka fita kyau baba ma ya ce, so ko baka yi kwalliya ba dama kana da kyau sosai, yau É—in ne naga kyanka ya karu sosai".
Cool murmushi ya sakar mata kafin ya ce. "Bari maman ta jiki kin ce na fita kyau, idan ta rikeki ba mai karɓarki a gidan nan, kin san ko lokacin da muke gida kafin ta yi aure bata taɓa yarda ace na fita kyau, Allah ki bari ta jiki zaki yi bayani ne ba ruwana, yadda take jin ita kyakkyawa ce ɗin nan".
Dariya sosai ta yi har sai da wishiryar dake tsakanin fararen hakwarantan ya bayyana.
"Allah kawu Sadiq ka fi mama kyau sosai, amma na san mama da Oumma take kama shiyasa, kai kuma da Abba kake kama"
Abba shi ne mahaifinsu Sadiq É—in, kakansu namiji kenan, Abba suke ce mashi, kakansu mace kuma Oumma.
"Kai, kai, kai, lallai Zainab yanzu kam ni ne zan zaneki, Oummar tamu ce kenan mummuna ko? Shiyasa da mamarki ta yi kama da ita ita ma ta yi muni ko? To baki isa ba wannan kuma, Allah duka zaki sha, ni Oummarta kyakkyawar gaske ce da babu biyunta a duniya, mamarki dai sai Allah kaÉ—ai yasan da waye take kama".
Ya kai karshen maganar yana fitar da wallet nasa daga aljihunsa.
Sai dariya take yi tana kara gaya mashi Allah kakarsu mace mummuna ce, shiyasa mamarsu bata da kyau sosai sai hasken fata.
KuÉ—i 1k ya ciro ya bata, sannan ya juya ya nufi cikin É—akinsu yana faÉ—a mata su yi breakfast da 1k É—in idan sun je makaranta, dan yasan Æ´an makaranta ba'a rabasu da saye saye na kwalama.
Sosai ta yi mashi godiya sannan ta wuce izuwa cikin parlourn ita ma.
A gaggauce suka karya, dan lokaci karfe 7 ta yi, kuma 7:30 dai'dai suke shiga cikin school kullum, babansu baya yarda su yi latti, yana kula da karatun nan nasu fiye da tunaninku.
Bayan sun kammala sai suka fito harabar gidan da nufin tafiya, su Zainab kowacce ta goyo jakarta a baya, Mamansu ta rakosu harabar gida kamar yadda suka saba.
Jin fitowarsu harabar gidan yasa Sadiq ya fito domin ya fitarwa da Baban Zainab É—in mashin É—insa daga cikin kitchen ya kai mashi waje, haka suke yi kullum, shi kuma Haidar sarkin son girma yana ciki. Kun san jahilci tana tare da girman kai, girman kai kuma yana tare da shegen son girma kamar me, mutun mai ilimi wanda yasan abin da yake yi ba zai yi girman kai ba wlh, wannan sai jahili, to dai haka Haidar yake da bala'in son girma kamar menene, ga shegen girman kai rawanin tsiya.
Ya fito da mashin É—in harabar gidan kenan da nufin ya fitar waje, shi kuma Haidar yana ciki yana aikin zuba barci, dan shi kasuwar ma sai sanda ya tashi barcinsa yake zuwa, wani lokaci sai 11 na rana yake zuwa, shegen barcin safe ke gare shi.
Murmushi ne a saman fuskar kowannensu, musamman baban Zainab, sai tsokanar Sadiq yake yi a kan ya yi kyau sosai yau dan ba Kasuwa zai je ba, wato zai je school akwai Æ´an'mata a can shi ne ya tsara kwalliya ko?.
Sai murmushi Sadiq É—in ma yake yi yana cewa da ai shi babu ruwansa da mata. Maman Zainab kuwa ta ce ba wani nan idan ba dan Æ´an'mata ba ai ba zai yi irin wannan shiga a kullum idan zai tafi makarantar ba, meyasa baya yi irin shigar idan zai je kasuwa? Sai dai ya É—auki wasu tsofaffin kaya ya sa ya tafi kasuwar, makaranta kuma a tsantsara kwalliya.
Zainab sai dariya take yi mashi tana faÉ—in Allah ya kama kawu Sadiq, yau asirinsa ya tonu.
Khadija kam fuska kamar ko yaushe, sam bata a cikin walwala baiwar Allah.
Sadiq bai kai ga fitar da mashin É—in ba suka ga an banko kofar gidan an faÉ—o masu cikin gida.
Zainab sarkin tsoro har ta juya zata zunduma cikin É—aki da gudu, ita kuma Khadija da yake dama hankalinta baya a tattare da ita, sai bata wani tsorata sosai ba, Maman Zainab ma saura kaÉ—an ta zunduma da gudu izuwa cikin parlourn. Baban Zainab da Sadiq ne kawai basu tsorata ba, suna tsaye a yadda suke.
Tun daga kofar gida ake surfa uban masifa, ba kowa bace face Maman Haidar, kakansu da kuma É—ayar Æ´ar babansu Zainab É—in mai suna Zainab. Tun daga bakin kofar gida suke surfa uban masifa tamkar zasu tashi garin.
Da sauri Mamansu Zainab ta juya da nufin ta wuce cikin parlourn abinta, dan ba zata iya masu ba.
Sirikar tata ce ta daka mata tsawa a kan ta zo nan munafuka, ai wajenta suka zo, zata wani sa kai kamar wata tsohuwar munafuka zata wuce.
Cikin girmamawa ta É—agawa surukar tata gaisuwa da "Ina kwana".
Cikin faÉ—a surukar tata ta ce. "Da ban kwana ba zaki ganni ne? Wato dama baki so na kwana a duniya ko? To na kwana na tashi, kuma ni dai nan gani nan bari, baku isa ku mallakeni ba, nafi karfinku".
Shiru Khadija ta yi tana sauraron kakar tata, idan kakan nan nasu tana magana sai ka rasa ina ma ta dosa, sam maganarta babu kan gado, idan ba rashin kan gado ba yanzu me ya kawo wani zancen mallaka da kuma zancen wai Mamansu bata son kakar tasu ta kwana a duniya, daga cewa ina kwana? Abin ma abin dariya, ko me haÉ—in ina kwana da kuma ba'a son mutun ya kwana a duniya? Kawai jaraba ce da dole sai anyi faÉ—a.
"Mama wai me yake faruw ne?". Cewar baban Zainab É—in, ya yi maganar a nutse.
"Rufe mun baki hai, ai yau wlh kome wannan matar taka ta yi maka ta mallakeka sai ta karya shi".
"Sadiq ku je ka kai su Khadija makaranta daga nan ka ajiye mun mashin É—in a kasuwa zan hau mashin É—in kasuwa na je kasuwar". Cewar baban Zainab É—in.
A hanzarce Sadiq ya amsa tare da jan mashin É—in ya fitar da ita waje, su Zainab suka rufa mashi baya da sauri. Ran Zainab kamar bakar leda saboda bakin ciki, zuciyarta sai tafasa take yi, kamar ta tsinke kakan nata da mari take ji, mata ce sai jarabar bala'i, sai ka rasa me matar nan take so a duniyar nan, kamar wadda ake sakawa battery, idan ta fara zuba bala'i ita da kanta bata sanin me take faÉ—a.
"Mama mu je cikin parlourn koma menene sai mu tattauna a cikin nutsuwa ko?". Cewar baban Zainab É—in dai. Ita dai maman Zainab bata da bakin magana.
Cikin faÉ—a mamar tasa ta ce. "Kai har kana da É—akin da zan shiga in zauna ne? Babu in da zan shiga sai wannan bakar munafukar matar taka ta gaya mun uban me ta yi maka ka lalace ka dawo mata soko sai abin da ta ce kake yi".
Shi dai baban Zainab har yanzu bai gane a kan me mamar tasa take surfa wannan bala'in ba.
"Maman Haidar wai me yake faruwa ne? Waye ya taɓo mama yau kuma?". Cewar baban Zainab, ya yi maganar kuma yana kallon Maman Haidar dake tsaye tana wani cika tana batsewa.
"Ba gaka ga mamar ba, ai ita zaka tambaya, ni ka rai'na zaka tambaya ko?". Maman Haidar É—in ta bashi amsa tana wani watsa mashi harara.
Nisawa ya yi kafin ya mai do da kallonsa a kan É—ayar yayar tasa dake tsaye shiru tana binsu da ido. "Maman Hanif ke ki gaya mun wai meyake faruwa ne? Me aka yi wa mama? Ko me aka ce nayi?".
Nisawa ita ma ta yi tare da fara magana a nutse.
"Wata ce nan ta je ta gaya masu cewa wai jiya ka sayawa matarka tsadaddun lace da shaddoji da sauran kaya namu na mata, ta dai ce makwabciyarku ce ita, wai maman Zainab ta mayar da kai wani soko, kai ne kake yin sharar gida da komai da komai, maganganu dai dayawa ta gayawa mama, ni ina waje sama sama najiyosu suna tattaunawa da mama......".
Katseta mamar tasu ta yi da cewa. "To karya aka yi mashi ne? Ai idan da baya yi makotansu ma ba zasu sani ba, abin da kika ga har makota sun sani ai kinsan ba karamar abu bace ba, abin ya yi yawa kenan".
Dafe kansa ya yi, dan shi yasan ba wata matar da ta gaya masu, karya ne, Haidar ne ya kai masu wannan magana, dan shi ne mai kwasan duk abin da yake faruwa a cikin gidan yana gaya masu, kuma duk abin da Haidar yake yi mamarsa ta koya mashi, dan ita ce tun yana ƙaramin yaro idan ya je wajenta sai ta rinƙa tambayarsa me aka yi a gidansu Zainab ɗin, me yake faruwa a gidan, shiyasa babban kuskure ne idan yaronka ya je waje ya dawo ka rinƙa tambayarsa me aka yi a wannan gidan, ko me suka dafa da ya je, hakan ba ƙaramin mummunar dabi'a bace kake koyawa yaro.
Ni kuma PRINCESS TEEMA shawarar da zan bawa mata a nan shi ne, kuskure ne ki bari wani daga cikin familyn mijinki da kike rikonsa ya rinƙa sanin halin da kuke ciki ke da mijinki, ke ko ɗan miji kike riko, kada ki yarda ki bari su rinƙa sanin me yake faruwa a gidan, ko kuma ya tukunyarki take, ace komai mijinki zai saya maki sai sun sani, ko cefenen gida sai sun san komai da yadda aka yi. Kun dai san abin da yake faruwa a gidansu Zainab ɗin nan kaf abu ne da yake faruwa sosai a cikin al'umma, amma dayawa daga cikin mata basu san daga ina matsalar take samo asali ba, na tabbata mata dayawan zasu gyara wasu abubuwa nasu a dalilin karanta labarin gidansu Zainab, dan labari ne mai cike da darusa sosai, ko ya kike da mutu kada ki bari ya san abin da mijinki yake yi maki na kyautatawa, kome zai saya maki ya zama sirrin ke da shi, kada ki nunawa kowa sai iyayenki da kannenki idan kina da su, domin duniyar yanzu wlh ta wuce tunaninki, ke zaki gayawa mutun abin alkhari da mijin yake yi maki dan ya tayaki murna da farinciki kin yi dace, baki san shi haushin ki yake ji kin sami abin da shi bai samu ba, hakan zai sa ya yi duk yadda zai yi ya shirya maki mugunta, dan tsabar bakin ciki da hasada, dan haka mata sai ku kula, maman Zainab tun farko ita ta yi kuskure, ita ta yi ganganci da ta sakewa Haidar fuska, ta kyale shi yana shigo masu har cikin ɗaki, duk abin da Baban Zainab zai yi ma matarsa da ƴaƴansa sai ya sani, kome suke ciki yana sane, a lokacin maman Zainab tana ɗaukarsa yaro, a duniyar yau wlh yara sunfi manya iya gulma da munafurci, ta yi sake ga shi yanzu abin ya kwaɓe mata ba yadda ta iya, abu ya fi karfinta, Allah dai ya kyauta ya kawo mata mafita.
"Maman Hanif zaki iya gane fuskar matar?". Cewar baban Zainab É—in, duk da zuciyarsa tana gaya mashi Haidar ne ya je ya kai masu rahoton ko ya kirasu a waya ya gaya masu cewa babansu Zainab É—in ya dawo dasu laces and atamfofi a leda, sai dai bai isa ya nuna cewa yasan Haidar É—in bane, dan idan ya ce shi ne to ba makawa wata ruwan bala'in ce zata sauko mashi, dan yanzu Maman Haidar É—in zata yi tsalle ta dire ta ce ai ya zagan mata yaro, ita ma kakan ta hau kai ta zauna.
Amsa maman Hanif ta bashi da cewa. "Matar sanye take da nikaf a fuskarta, ban ga face nata ba".
Shiru ya sake yi yana tunanin irin wannan rayuwa, tabbas bai yarda da zancen Maman Hanif É—in bama, ba wani bata gane wacece bace, gaya mashi gaskiyar cewa Haidar ne ya yi hakan ne ba zata yi ba, domin Haidar É—in ne ya san cewa ya É—auko atamfofi daga kasuwa, shi ne kuma yasan cewa ya sayo masu abubuwa na mata daga kasuwa, so dole shi ne ya kai rahoto.
Kakar tasu ce ta katse mashi tunanin da yake yi cikin faÉ—a da cewa wlh dukka kayan nan da ya kawo ya yi maza ya kwasosu ya kawo mata dukka.
Da yake zaman lafiya yake nema, sai ya ce da maman Zainab ta je ta É—auko masu kayan, ya kudurci niyar zai kawo masu wani ba tare da sanin kowa ba, ko Sadiq ba zai bari ya sani ba bare Haidar.
Da sauri Maman Zainab ta wuce cikin parlourn, sai kuka take yi hawaye bibbiyu, wannan jarabar bala'i dame ta yi kama?
Kamar yadda ya kawo masu kayan a leda haka ta É—auko ta fito masu da shi, dama can bata wani cire kayan daga ledojinsu ba, dama sun bari sai da safe ne su buÉ—e suga irin kayan da ya kawo masu.
Tana zuwa ta duka ƙasa ta miƙawa sirikar tata.
Cikin faɗa tasa hannu ta karɓa tare da cewa su Maman Haidar su wuce su tafi, sannan ta dubi baban Zainab ɗin cikin fushi ta ce maza ya sameta a gida, daga haka suka wuce fuuuu kamar wasu kumfaye suka nufi waje.
Suna fita Maman Zainab ta saki wani marayar kuka tare da juyawa da sauri ta koma cikin parlourn.
Bayanta baban Zainab ɗin ya bi, hakuri ya je ya rinƙa bata tare da yi mata alkawarin anjuma da rana zai kawo mata wasu kayan waɗan da suka fi wannan kyau.
Cikin kuka ta ce ita ba kayan ne ya dameta ba, meyasa zasu rinƙa zaginta haka? Su zageta su zage iyayenta, laifin me ta yi masu?.
Hakuri dai ya cigaba da bata, ba shi ya tafi kasuwa ba har sai da ya san ya sanyata murmushi ta cire damuwar a ranta, sannan ya fito ya nufi kasuwa, shi kuma Haidar sai zuba barci yake kamar wani gawa, duk wannan rigima da aka yi a cikin gidan sam bai sani ba, nauyin barci ke gare shi, idan ya yi barci kamar wanda ya mutu.
Baban Zainab na tafiya ta rufe kofar parlourn da key ta wuce cikin bedroom nata ta haye gado domin ta É—an yi barci, dama haka take yi, zata tashi tun asuba ta yi aiki, idan ta sallamesu suka fita sai ta kwanta ta yi barci zuwa 11, sannan ta tashi ta hau aikin girkin rana, dan karfe 2 dai'dai Sadiq zai zo ya É—aukawa baban Zainab abinci rana zuwa kasuwa, su Khadijah kuma karfe 3 suke tashi makaranta.
To bari mu waiwaya bangaren su KAMRAN, wato daji kuma muga me ake ciki tun da Maman Zainab ta yi barci.
ðŸžï¸FORESTðŸžï¸
Tafiya Kamran yake yi cikin wannan shiga tasa dai da kuka sani, ya ratayo kwari da baka a bayansa, da alama farautar nama zai je yi, yanzu ya zama matashi, kyau da cikar haiba tare da kamala sun kara bayyana a tattare da shi, yanzu yana da 25 years, dan rabonsa da su twins yanzu shekaru 10 kenan, kirarsa na jaruman maza ya kara bayyana, Mamma ta iya reno sosai kam, cikakken jarumi ne mara tsoro, haka yake kutsa cikin wannan ƙungurmin dajin babu ko ɗar ɗar a tattare da shi.
Sai tafiya yake yi Rocky yana gefensa, yanzu Rocky ma ya tsufa, ya zama wani bujumi da shi, ya kara girma sosai.............
Masu buƙatar littafin TRIPLETS daga farko harshen su yi mun magana ta wannan number tawa, 08161390581.*
ðŸ¤PRINCESS TEEMA taku ta amana🔥
Share fisabilillahi ðŸ‘
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥ðŸ¤
ðŸ¤ðŸ”¥ð—¥ð—”ð—ªð—”ð—¡ð—œð—¡ 👑 ð—ð—”ð—Ÿð—œð—¡ð—–ð—œðŸ”¥ðŸ¤
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
ð— ð—”ð—Ÿð—Ÿð—”ð—žð—œð—¡
â¤ï¸â€ðŸ”¥FATEEMA ZAHRA MUSA â¤ï¸â€ðŸ”¥
(â¤ï¸A-K-A ð‘·ð‘¹ð‘°ð‘µð‘ªð‘¬ð‘ºð‘º ð‘»ð‘¬ð‘¬ð‘´ð‘¨ðŸ”¥)
Writer of DUK KARFIN IZZATA, TRIPLETS, and now RAWANIN ZALINCI.
🔥ðŸ¤T🔥ðŸ¤T🔥ðŸ¤W🔥ðŸ¤......💻
â¤ï¸ð‘«ð‘¨ð‘»ð‘¬ 9/7/2024.....âœï¸ðŸ“šðŸŒ¹
ðŸ¤ð‘ºð‘»ð‘¬ð‘· 1......âœï¸ðŸ“šðŸ”¥
اللَّهÙمَّ صَلّ٠عَلَى Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯Ù ÙˆÙŽØ¹ÙŽÙ„ÙŽÙ‰ Ø¢Ù„Ù Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯ÙØŒ كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ وَعَلَى Ø¢Ù„Ù Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ، Ø¥Ùنَّكَ ØÙŽÙ…Ùيدٌ مَجÙيدٌ، اللَّهÙمَّ بَارÙكْ عَلَى Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯Ù ÙˆÙŽØ¹ÙŽÙ„ÙŽÙ‰ Ø¢Ù„Ù Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯ÙØŒ كَمَا بَارَكْتَ عَلَى Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ وَعَلَى Ø¢Ù„Ù Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ، Ø¥Ùنَّكَ ØÙŽÙ…Ùيدٌ مَجÙيدٌâ¤ï¸
E____________10🔥
Sai tafiya yake yi Rocky yana gefensa, yanzu Rocky ma ya tsufa, ya zama wani bujumi da shi, ya kara girma sosai.
Sai kutsawa cikin dajin sosai suke yi, da yake basu saba zuwa wannan yankin ba a cikin dajin, sai Rocky ya fara yi mashi alamar sun wuce dai'dai in da suke tsayawa fa, sun fara shiga wani yanki na daban, sai alama yake yi mashi ta hanyar tsayawa yaki tafiya.
Sarai Kamran É—in yasan me Rockyn yake nufi da shi, amma sai yaki kula shi, domin yau yana da burin ya tsalleke yankinsu ya shiga wani, dan shi ma dai ya kalli wannan dajin da kyau da kyau.
Da dai Rocky yaga da gangan Kamran É—in yaki kula shi, sai ya sha gabansa tare da É—aga kai sama zai zuba wannan kukan nasu mai rikita dabbobin dake yankin.
Hannu Kamran É—in ya É—aura mashi a saman kansa, still da wannan yare nasa dai ya yi mashi magana a kan cewa ya bari suje wasu yankuna koda guda biyu ne a cikin dajin dan suga abubuwa, wata kila akwai abin da akwai a sauran yankunan babu a nasu part É—in, sai su É—ebo su kawowa Mamma.
Girgiza jiki Rocky ya yi kafin ya wuce gaba, da sauri Kamran É—in ya ce lallai ya dawo baya ko kuma ya dawo su jera a tare kamar yadda suka saba tafiya.
Kin dawowa ya yi, sai ma cigaba da tafiya da ya yi.
Shi kuwa Kamran kamar ya kifa mashi mari dan haushi, sai dai koya mare shi ma shi ne zai ji zafin hannunsa, Rocky kam babu abin da zai ji.
Kamran yana matuƙar jin haushi idan suna tafiya Rocky ya wuce gaba, abin yana baƙanta mashi rai sosai, ya fi son shi ya yi gaba, a cewarsa idan Rocky ya yi gaba kenan tsaro Rockyn yake yi, shi kuma wai baya son ace ga wani yana bashi tsaro, yana ji da jarumta sosai, ya fiso ace shi ne a gaba shi ne jarumi.
Cak suka tsaya a wani wani mai cike da dogayen itatuwa masu yelwar cikar ganyayyaki korayen shar, kasancewar itatuwar suna da tsawo sosai, sai cikar ganyayyakin jikinsu bai sa wajen ta yi duhu ba, sai ma hasken rana da ya bayyana ta tsakiyarsu, abin ya kawatar da mai kallo matuka, kasan wajen ya kasance farin yashi ne tamkar yashin bakin manya manyan tekuna na ruwa.
Bin wajen da kallo Kamran ya fara yi, hakiƙa wajen ya yi matuƙar burgesa sosai, ga yanayin weather wajen is very very so nice, akwai yelwar ɗumi a wajen, tamkar ba a cikin dajin wajen yake ba, da yake dama dajin Allah mai girma haka ai sai abin da ka gani kawai, Allah ya yi ikonsa kala kala a ciki, duk abin da ka gani kawai ka gara jinjinawa iko da kudura ta Ubangiji.
Shi kansa Rocky da yake yawace yawacensa son ransa, babu inda baya shi ga, tabbas wannan waje ta bashi mamaki kuma ta yi matuƙar burgesa. Shi dai Kamran yana zuwa bakin teku ya ɗebi wasu abubuwa daga cikin albarkatun cikin ruwa, amma bai taɓa ganin farin yashi (ƙasa) tas irin na wannan waje ba, dan wannan ya fi ƙasar bakin teku haske sosai, idan hasken rana ta haska yashin ma har wani kyalli sosai yake yi. Gabaɗaya ma yanayin tsarin wajen idan ka gani sai ka ji imaninka ya karu, domin babu ɗan adam da ya isa ya yi wannan halitta, yadda kasan a manyan wajajen buɗe idanu na duniya suke, tamkar ba'a cikin dajin ba.
Duk da cewa Kamran bai san Allah ba, bai ma taɓa jin sunan Allah ba, bai san a akwai Allah ba, bai san akwai wanda yake halittar abubuwa ba, amma da ya zo wannan waje ya ji a jikinsa yana son sanin wadda yake halittar waɗan nan itatuwa da sauransu, saboda itatuwa ne irin masu bala'in tsawon nan, bai taɓa ganin irinsu a cikin wannan dajin ba, dan suna da tsawo sosai gaskiya, shi ne yasa ya ji cewa gaskiya yana son yaga waye ne yake gyara itatuwar nan haka? Waye mamallakin wannan dajin? Ya kuma kudurci niyar idan ya koma gida sai ya tambayi mamarsa, sai ya tambayeta ta gaya mashi wanene mamallakin wannan dajin? Dan a ilimin da yake da shi dai yasan abu bata kyara kanta, dole duk abin da ka gani akwai makerinta, musamman idan ya waiwaya ya dubi yadda Mammansa take kyara tukanen dafa abinci da taɓon da yake ɗebo mata, sannan ta kyara kwanikan cin abinci da katakon itatuwa da yake saro mata, hakan ce ta kara tabbatar mashi da cewa lallai komai da ka gani akwai wanda ya yi shi......... Toh fa, Kamran ya ɗauko babbar magana, kuma ya fara tunanin ta gaskiya, domin komai da ka gani a duniyar nan baya taɓa kyara kansa, masu cewa babu Allah kowaye ya halicce su?🤔 A barka da iya dutse ma kawai ka gaya mana waye ya yi ta?🤔 Ko kuma ka kawo wani ya yi ta mu gani, an dai ba zata kyara kanta ba kam, idan ka kai dubanka izuwa kan motoci da abubuwan hawa, dukkansu akwai waɗan da suka kyarasu, to sai halittun Ubangiji ne za'a ce babu wanda ya haliccesu dan kin gaskiya da son dole sai an shiga wutar jahannama?.🤔 To Allah ya kyauta ya kuma yafe mana zunubanmu ya kara ɗauramu bisa tafarkin koyarwan fiyayyen halitta.
A hankali hankali kunnuwansa suka fara tsinkayo mashi sautin zubar ruwa sha tamkar ruwan sama.
Dawo da kallonsa ya yi daga kallon wajen izuwa kan Rocky. Kasa kunne shiru suka yi dan su ji menene yake wannan shahhhh kamar zubar ruwan?.
Karar tana É—an nesa daga in da suke, hakan yasa Kamran É—in ya kara gaba domin ya ga menene? Kai tsaye babu tsoro ko shakka ya nufi ta hanyar da yake jiyo wannan kara.
Da sauri Rocky ya rufa mashi baya, haka suka cigaba da tafiya, sai dai a wannan karon tafiyarsu ta sauya daga ta jarumta izuwa ta mutumin daji, wato tafiyar sanÉ—o kenan, tamkar wadda yaga wata nama zai farauceta, saboda basu san me yake wannan kara ba, gada ya zamana sun dimfari abin gadan gadan kuma ya fi karfinsu, gara koma menene su yi mashi tafiyar mage mai kwanciyar É—aukar rai, idan yaso in sun ga menene, sai su san abin yi.
Kara matsowarsu ta in da wannan kara yake tashi ne ya bawa Kamran ɗin damar fahimtar cewa lallai ruwa ne yake zuwa daga ƙoramar dutse, duk da cewa babu irin wannan ƙoramar dutse dake zubar da ruwa a yankinsu, amma Kamran ɗin yasan da akwaita a cikin wannan dajin sosai, dan idan ya tsaya a saman ɗaya daga cikin tsaunikan dake ta kusa da su yana iya hango koraman dake kusa da yankinsu, waɗan da suke zubar da ruwa, sai dai kanana ne waɗan da suke kusa da su, ba katafare tamkar wannan da yake karan bane, su waɗan can ma ba zaka ji karar ruwan sosai ba, amma shi wannan karar ruwan tun daga nesa kunga suka fara jiyo shi, alamu sun nuna katafaren ƙorama ne sosai.
Jin cewa sautin zubar ruwan korama ne yasa Kamran ɗin nufar wajen cikin takun jarumta tare da isa da ƙasaita, akwai dogayen ciyayi a gabansu waɗanda suka kare masu hangen ƙoramar daga nesa, kai tsaye ya nufi wajen ciyayin. Shi kuma Rocky wata hanya daban ya bi, dan yana jin wata iriyar kamshi a wajen wadda sam bai yarda da ita ba, kunsan su dabbobi da kamshi ko wari suke iya tantance abu yana waje ko akasin haka, musamman ma ɗan adam, da kamshin mutun suke iya fahimtar lallai akwai ɗan adam a wannan waje, so shi Rocky ya ji kamshi ne ya tafi duba menene?
ROCKY BA DAI GULMA BA, WAI YA JE DUBA MENENE KAI JAMA'A 😅
Shi kuwa Kamran yana zuwa ya sa hannu ya ya ye waɗan nan dogayen ciyayi dake a wajen, nan take katafaren ƙoramar ta bayyana a idanuwnsa.
Zaro dara daran idanuwan nan nasa ya yi yana mai kallon ƙoramar, katuwa ce sosai, ruwan da yake taruwa a ƙasarta ma teku ne guda, ruwan yana ganganrawa ne har izuwa cikin tapkeken tekun dake gaba da ƙoramar, sam Kamran duk yawonsa a cikin wannan daji bai taɓa sanin cewa akwai wannan tapkeken tekun ba, haka zalika bai taɓa sanin da akwai wannan tapkeken ƙoramar ba.
A zahirin gaskiya kowa ya kalli Kamran a wannan hali da yake ciki da kuma irin wannan tsayuwa da ya yi zai ce wannan ƙoramar yake kallah, amma kuma sam ba ita yake kallah ba, shi kwata kwata idanuwansa ma basu sauka a kan ƙoramar ba, yana yaye ciyayyin idanuwansa suka yi wani irin kyakkyawar gani wanda bai taɓa yin irinsa ba, hakan tasa bai ma bi ta kan ƙoramar ba, kawai ya tsaya cak yana ta kare mata kallo.
Macece Æ´ar yarinyar da bata wuce shekaru goma ba a duniya, kyakkyawar gaske ce sosai, a kallon farko ma idan ka kalleta sai ka rantse da Allah aljanace ta rikiÉ—e izuwa siffa mafi kyau a duniya, sanye take da kaya masu bala'in kyau sosai, ba irin kayan dajin bane, hakan yasa ta sake yin kama da aljana, domin kuwa kayan jikin nata ba kaya ne kamar sauran kayayyakin da kuka saba gani yau da kullum ba.
Wata iriyar skit ce wadda daga kugunta zuwa mazaunanta ya yi mata daidai cif cif, daga dai'dai matsayar hips nata zuwa ƙasa ya yi wani irin bala'in buɗewa sosai, sai ƴar farar vest ta sama wadda ta tsaya mata a iya cibiyarta, launin skit ɗin pink color ne, yana da kyalliya sosai a jikinsa wanda kwalliyar ta mamaye ko'ina a jikin kayan, baka iya tantance ainahin yadin da aka yi amfani da shi wajen yin wannan sket ɗin, saboda yawan kwalliyar jikinta, ga kuma duwatsu masu haske da aka kawata ta da shi.
Zaune take a saman wani dutse mai ɗan girma da yake a kusa da ƙoramar, ta zura kyawawan fararen kafafunta a cikin ruwan dake a gaban ƙaramar, ruwan da yake gudu izuwa cikin tekun nan kenan, ta sunkuyar da kanta ƙasa, tana da wani irin bakin gashi, ya yi baki sosai har ya yi kamar dark navy blue, sai wani irin sheki yake yi, an ɗaure mata gashin kan nata ɗauri biyu, gefe da gefe, jelar gashin nata ya sauko mata har bayanta, kasancewar kanta na sunkuye sai jekar gashin ya sauko mata ta gabanta har izuwa saman kirjinta, hannunta na rike da wani sanda ɗan ƙarami tana kaɗawa, ta yi shiru kamar mai tunanin wani abin, duk da bata ɗago kanta ba, a iya fatar jikinta zaka tabbatar da kyakkyawar gaske ce, fara tas da ita, ga jikin nata mai bala'in kyau, da alama girman kayan marmari ce, kun san kayan fruits da balai'n gyarawa ɗan adam fatar jikinsa yake, daga gaban koshinta wasu kyawawan sidif ɗin kashi ne dake kwance a wajen, tana da gashi ɗan dai'dai a gefe da gefen fuskarta, gashin yana kwance luf, farar fata ga bakin gashi kwance a wajen, ya kuke ganin kyan zai kasance? Abin ba'a magana. Ga ta ƴar caras cas, babu ƙiba, jikinta mai kyau ne sosai, ƴar ɓul ɓul da ita, alamar ta ci ta ƙoshi dai amma ba ƙiba.
Kamran dai ya zaro idanu yana kallon wannan kyakkyawar halittar, ya ƙasa motsawa daga in da yake, da alama ya afka wata duniyar ne, bai taɓa kallon kyakkyawar halitta irin wannan ba, Mammansa kyakkyawar mace ce sosai, amma gaskiya bata kai rabin wannan yarinyar a kyau ba, shi kansa Kamran ɗin kyakkyawa ne sosai, amma ina, wannan yarinyar kyanta na daban ne, hasken fatarta har ma ta fi Mamman Kamran ɗin haske, kun san dama Mamma ta fi Kamran haske sosai, to wannan yarinyar dai ta fi Mamman ma haske, in dai mutun ba jarumi ba, kai ko jarumi ne idan ba ya dake sosai ba idan ya yi ido biyu da wannan kyakkyawar halitta a kallon farko sai ya tsorata, bare ma ace yasan babu mutane a dajin, wlh tsab kyanta zai tsorata shi ya ce aljana ce.
Amma shi Kamran ya dake sosai, dan shi fa tun da ya taso bai san menene ma tsoro ba a rayuwarsa, kuma kunsan mutun ya girma a irin wannan dajin ai dole ba zai san menene tsoro ba, this Forest no be small thing ooooo.
Ya yi nisa a kallonta da yake yi bai ankara ba sai ganin Rocky ya yi a bayanta, dama idan baku manta ba shi Rocky ya yi wata hanya daban, dan ya ji kamshi É—an adam a wajen, shi ne ya je dubawa, to yanzu ya ganta.
Da gudu ya hauro saman dutsen, kuma ya hauro ne da nufin ya far mata, saboda shi Rocky idan ba Mamma da Kamran ba to baya ragawa kowa, wlh ko maharbi ya gani idan yana jin yunwa cinyewa yake yi fes abinsa, kuma dai kunsan damusa ki sabo ce, da alama zamansa da su Mamma ma ba haka kawai bane ba, amma koma dai me lokaci ne zai nuna mana.
Jin diran abu a kusa da ita yasa ta É—ago kai a tsananin raza ne, É—ago kai da zata yi kuma kai tsaye kallonta sai cikin idanuwan Kamran da yake tsaye ya tsareta da idanu, dan suna saiti da juna ne.
Wannan ɗagowa da ta yi yasa ta kara jefa mana Kamran namu cikin wata iriyar ruɗu tare da afkawa wani irin kogon yanayin da baki ba zai iya fassarawa ba, dan yadda kasan ita ta halicci kanta, face nata ɗan dai'dai, hancinta dai'dai da face nata, bai yi irin mummunar tsawon nan ba, ɗan dai'dai, sai olive dara daran eyes nata, farin idanun nata kuwa, fari ne tas, sai ka rantse da Allah tasa kwalli a ido, saboda yadda idanun nata suka kara fitowa sosai kamar tasa kwalli, olive green eyes ɗin nata ya fito sosai da sosai, lips nata jajir da shi, ga bakin nata ɗan karami da shi, kumatunta ɓul ɓul.
Har cikin ido take kallon Kamran, ta kasa iya juyawa ta kalli damusar dake kusa da ita, da alama mayyar tsoro ce sosai yarinyar, dan daga jin numfashi Rocky dake futa da wani irin gurnani yasa har jikinta ya fara kerma sosai, nan take wani irin tsoro na wuce misali ya bayyana a saman wannan kyakkyawar fuskar tata, tsuke ɗan bakin nan nata ta yi tana mai cigaba da kallon Kamran ɗin, sai dai da alama kallon Mamaki take yi wa Kamran ɗin, da alama bata taɓa yin tunanin zata yi tozali da wata halitta ta ɗan adam irin tata a cikin wannan dajin ba, shiyasa take yi mashi kallon mamaki har haka.
Wani irin numfashi mai karfi da Rocky ya saki ne yasa bata san lokacin da ta kara tsuke fuska ba, balai'n tsoron juyawa take yi su yi ido biyu da Damusa.
(Amma na ce ba My people's idan kune a cikin irin wannan hali anya zaku iya juyawa ku yi ido huɗu da Rocky kuwa?😅 Ni dai zan iya amma idan na furta kalmar shahada na gama😅 dan ko ya haɗiyeni ma burina ya cika na karisawa da kalmar shahada 😅)
Shi kuwa Kamran ya zubawa waÉ—an nan olive eyes É—in nata idanu kawai yana ta kallo, da yake shi ya saba da Rocky, sai sam abin bai dame shi ba, a tunaninsa Rockyn ba zai yi mata komai ba, shiyasa ya kyaleta da shi, shi kuwa Rocky har ga Allah cinyeta ya yi niyar yi, dan dama yana É—an jin yunwa.
Kafin Damusa ta ci mutun, kai ba ma mutun ba, Damusa tana da wata dabi'a guda ɗaya, kafin ta ci abu sai ta waje baki tare da ɗaga kai sama, wani lokaci idan suka daga kan nasu suna yin wani irin kuka, wani lokaci kuma basu yi, amma confirm ainahin Damusa baya cin abu sai ya yi wannan abin, ɗabi'ar su ce, so shi ma Rocky hakan ya yi, ya wani wage bakin nasa gari guda, dai'dai lokacin kuma yarinyar ta yi namijin ƙoƙari wajen iya juyowa a hankali hakwaranta na garuwa da juna, saboda tsananin tsoro.
Tana juyowa kuma ta yi ido biyu da garma garman hakwaran Rocky da ya buÉ—e baki, ga hakwaran waÉ—an nan biyu na sama da biyu na kasan kamar wasu kifiyoyi, suna da tsini sosai, su Damusa take kafawa a jikin wuyar dabba ko mutun, idan ta cakasu suka shi cikin namar mutun, sai su tsinka mashi jijiyar wuya da ita, haka ma idan dabba zasu kashe, shiyasa idan suna farauta zaku gansu wuya kawai suke kamawa, saboda su tsinka agarar wuyar, kunga kuwa suna tsinke agarar wuyar shikenan abu ya zama gawa.
Wani irin ihu ta saki mai razana ƙwaƙwalwa, kan kace me tuni ta yanke jiki ta faɗa cikin wannan uban ruwan.
Shi kuma Kamran ganin Rockyn ya buɗe bakin yasa bai san lokacin da ya nufesu da sauri yana ƙoƙarin yiwa Rockyn magana ba, sai dai bai kai ga yin magana bane yarinyar ta juya taga hakwaran Damusan, daga haka kuma sai suma.
Kunsan ita fa Damusa wlh ko bata buÉ—e baki ba ka ganta sai zuciyarka ta tsinke, idan kana da zuciya a kusa ma sai suma ko mutuwa, saboda tsananin kwarjininsu, dole ake jin tsoronsu ko ba'a so.
And one thing about Damusa, basu shiga cikin ruwa, akwai waÉ—an da suke shiga cikin ruwan, sai dai masu shiga cikin ruwan basu da yawa, normal Tiger daji kamar sauran dajuka basu shiga cikin ruwa, bawai ba zasu iya shiga bane, no zasu iya, kawai basu shiga ne, dan idan ruwa ta yi yawa tana tafiya dasu.
A dubu ɗari Kamran ya ƙariso wajen, da gudu Rocky ya nufesa, wani irin harara ya wurgawa Rockyn kafin ya yi tsalle ya faɗa cikin ruwan shima, Rocky ya bashi haushi ba kaɗan ba.
Tsayuwa a wajen Rockyn ya yi yana wani girgiza, shi a dole ransa ya ɓaci bai ci nama ba, sam bai damu da harararsa da Kamran ɗin ya yi ba, shi dai nama kawai yake tunani........😅
Da kyar da suɗin goshi Kamran ya iya ceto yarinyar nan daga cikin ruwan, amma ta sha ruwa sosai kam, Allah ma yasa bata ƙarisa faɗawa cikin ainahin tekun ba ya kamata, da ta faɗa sai wani labarin ba dai nata ba, kasancewar ruwar tana ganganrawa ne yasa Kamran ya sha bakar wahala wajen iya fitowa daga wajen, da ace ruwan yana tsaye ne to da sauki, amma tana gudu kuma ganganra, kuma kunsan ba dan ya saba da shiga cikin ruwa ya kuma iya ruwa sosai ba, ai da daga shi har ita sai sun faɗa cikin tekun nan, kuma suna faɗawa shikenan, sai dai Mamma ta rungumi sorry ta kurɓi ruwan ganye shayi, dan Kamran kam da ya tafi kenan, dan ma Allah yasa duwatsu ne a wajen sosai, ya yi ƙoƙari wajen kakkamasu har ya samu ya hauro sama daga gangarar ruwan, kuma ya yi sa'a yarinyar karama ce, bata da wani nauyi, hakan tasa ya ɗauketa a saman shoulder ɗinsa kamar ƴar baby.
A bakin ƙoramar ya kwantar da ita, da gudu Rocky ya ƙariso wajen yana wani numfashi mara daɗin ji, alamar huci yake fitarwa na ransa ya ɓaci.
Shinshinar yarinyar ya fara yi kamar wani tsohon maye, cikin wannan yaren nasu Kamran É—in ya ce mashi. "Rocky ka kyaleta mana, ka sa ta faÉ—a cikin ruwa ma bai isheka ba sai ka zo kana wani shinshinata ko? To cinyeta zaka yi ne?".
Yana magana yana ƙoƙarin haɗa hannayensa dukka biyu waje guda, dan ya danna mata cikinta ta amayar da ruwan da ta sha.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.