Complete Hausa Novels

Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Rawanin_Zalinci_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 14 of 24

Cigaba da lallaɓata matar ta yi tana kwantar mata da hankali har sai da taga ta samu nutsuwa, sannan ne ta riƙo hannunta suka miƙe ta raka cikin toilet, da kanta ta haɗa mata ruwan wanka saboda makirci, duk cikin taku ne.

Bayan ta haÉ—a mata ta nuna mata yadda zata yi komai ne ta nufo waje ta barta a cikin toilet É—in. Sai da Leesharh ta É—auki almost 30 mins a tsaye a cikin toilet É—in tana tunane tunane kafin ta fara wanka.

Sosai ta wanke jikinta tsab da tsadaddun shower gels É—in da suke a cikin toilet É—in, har wani É—an haske ta kara yi, dattin gidan AAJ ya fita. Daga yanayin yadda take amfani da abubuwan cikin toilet É—in zaka fahimci ba yau ta fara ganin ire-irensu ba, da alama ta saba gani, so bata wani nuna kauyanci ba, towel ma ta É—auro ta nufo waje bayan ta kammala, sai tashin kamshin take yi.

Lokacin da ta fito sai ta tarar da an kawo mata abinci kala kala na larabawa masu shegen tashin kamshi, an geresu a saman rug da yake a cikin room ɗin. Da ido ta fara bin abincin da kallo, wajen kala huɗu ne abinci, duk kuma ita kaɗai aka kawowa, kara jinjinawa wannan al'amari ta yi kafin ta wuce ta ɗauki kayan da yake a saman bed ɗin wanda wannan mata ta ajiye mata. Ba tare da ɓata lokaci ba ta sanya kayan a jikinta. Sun yi mata kyau sosai, sun kuma zauna a jikinra kamar sun san size ɗinta, har jikinta ya fara sanin cewa ta fara samun canji.

Zama ta yi a gaban abinci, ta zaɓi wanda zata iya ci, ta zuba a plate, hannu baka hannu kwarya ta fara kai abincin nan bakinta, dan a yunwace take baiwar Allah, hakan yasa ta ci sosai da sosai. Wani irin ƙoshi da ta yi ma har sai da ta ji numfashinta yana yin sama sama, da kyar ta iya tattare wajen ta haɗa kayan abin waje guda. Kaɗan ta sha ruwa dan gudun kada ta yi amai, sannan ta ɗan sha lemu kaɗan.

Bayan ta kammala ne ta tashi ta fara gabatar da sallolin da suke a kanta a wajen saman rug É—in, dan ta É—auro alwala tun daga cikin toilet da ta gama wanka.

Tana idar da sallar a wajen ta ɓige da barci, anci an ƙoshi me ya rage? Ai sai barci, dama ga wahala da gajiyar gidan AAJ a jikinta.

Ba ita ta farka ba sai da yamma, nan ma wannan matar ce ta zo ta tasheta a kan ta tashi ga mai koya mata aiki ta zo. Da kyar ta iya buɗe idanunta, yau ta kwanta a waje mai laushi ga sanyin Ac haɗe da daddaɗar kamshin perfume, sannan ta ci abinci mai rai da lafiya ta ƙoshi, barci ya yi daɗi har da munshari, duk jikinta sai ta ji ya yi mata nauyi, sam barcin bai isheta ba. Idanuta sun ɗan kumbura sun kuma yi jajir, alama ce ta barci bai isheta ba.

Ba ƙaramin madarar mamaki ta shaba lokacin da ta kalli mai koya mata aikin, ita ma matar tana sanye da nikaf, wannan batu na nikaf ɗin ya fara ɗaurewa Leesharh kai sosai, kowa ka gani a gidan da nikaf? Ita a yanzu bata san face ɗin ko mutun ɗaya daga cikin ƴan gidan ba, su kansu securitys ɗin gidan sanye suke da face mask a fuskokinsu, abin da alamar tambaya sosai, duk da yarinta irin na Leesharh yanzu ta fara tunanin anya akwai gaskiya a wannan gida kuwa?.

Fita wannan matashiyar matar ta yi ta basu waje, ya rage daga Leesharh sai mai koya mata aiki, ita ma matashiyar macece wadda ba zata wuce 30 years a duniya ba, tana tare da wani haɗaɗɗen echolac ɗinta ɗan ma dai'dai ci, hakan ya nuna cewa tare zasu rinƙa kwana da Leesharh a wannan ɗakin kenan.

Sannu da zuwa Leesharh ta yi mata tana ƙoƙarin miƙewa tsaye, ga mamakinta sai taga duk an kwashe kayan abincin da ta ci ta bari, babu komai a room ɗin.

Sam matar bata amsa mata ba, yadda kuka san wasu abokan gaba, sai wucewa da ta yi ta sanya echolac É—inta a cikin katafaren wardrobe da yake a cikin É—akin, sannan ta nufi toilet.

Cike da mamaki sosai Leesharh ta bita da kallo, ta sha madarar mamakin ganin yadda matar bata amsa sannunta ba, tunani ta fara yi to ko dai matar bata jin larabci ne? Ga dukkan alamu kuma balarabiya ce, duk da cewa baka iya ganin komai na jikinta sai ido, saboda kayan da ta sanya ta rufe ko'ina nata, amma da alama ba bakar fata bace ba, ko meyasa ta ki amsa mata? Allah masani.

Cike da tunani Leesharh ta wuce wajen katafaren windown da yake fiskantar harabar gidan dan ta leƙa taga ko zata iya samun damar ganin fuskar ɗaya daga cikin ƴan gidan.

Ta kai 10 mins a tsaye a wajen, amma shiru bata ga giftawar wani ɗan adam a harabar gidan ba, jin motsin alamar wancan mata tana ƙoƙarin fitowa daga cikin toilet ɗin ne yasa ta yi saurin barin jikin window ta koma bakin bed ta zauna.

Fitowa matar ta yi a in da ta zo ta ciro dadduma daga cikin echolac ɗinta ta shunfuɗa a kasa saman tiles ɗin ɗakin tare da tada sallah. Sai ƙure mata kallo Leesharh take yi, dama ita fa ba baya ba wajen iya yi wa abu kallon ƙurilla, ba kallon wasa take yi wa abu ba, ƙure mashi kallo take yi ta haddace komai.

Tana ta ƙurewa wannan mata kallo har ta idar da sallarta cikin nutsuwa tare da dai'daito kamar yadda addini ya faɗa, daga ganin yadda wannan mata take sallah tabbas addini ya ratsata sosai, to amma meyasa duk da tana da sani take yi wa waɗan nan unknown mutane aiki? Wannan amsa sai alƙalamina ne kawai zai warware maku, ku dai kasance a tare da ni dan mu warware komai a tare, nasan kuna da tarin tambayoyi sosai a kan rayuwan kowani part na cikin wannan littafi, to kada ku ji komai, sannu a hankali zan nemo bakin zaren kowace part in warware maku dukkan wasu amsoshinku my people.

Bayan wannan mata ta idar da sallah ne ta miƙe ta nufi wajen bed in da Leesharh take a zaune kenan, cikin harshen larabci ta umarceta da ta tashi su nufi cikin gidan, domin ta je ta fara nunnuna mata abubuwa, shi ne abu na farkon da zata fara koya mata, zasu koya mata hakan ne kuma saboda kada Leesharh ɗin ta je ta yi masu kauyanci, dan duk ba ƴan kauye bane suke yi wa familyn Abu Abdussalam bin Badeen aiki, sai mai kwalin maratu suke ɗauka aiki, dan basu son shirme da shiririta, dan haka duk sai an wayarwa da Leesharh kai sosai da sosai, ta zama kamar cikakkiyar ƴan boko, an kara buɗe mata idanu, kada a samu matsala.

Gaba matar ta yi ba tare da ta jira ta ji me Leesharh zata ce ba. Jiki ba kwari ta tashi ta bi bayanta tana mamakin hali irin na wannan mata, ita kuma haka rayuwarta yake kenan? A haka kuma zasu zauna har tsawon sati É—aya zuwa biyu? Tab akwai matsala kuwa.

To nima dai bari na motsa na leƙa wani bangare kafin mu dawo watakila Leesharh ta iya aikin da suke son ta iya.

🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

GIDANSU KHADIJAH💔😥

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

Share fisabilillahi 👏

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍

🔥CROWN OF INJUSTICE🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)

🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 8/8/2024.....✍️📚🌹

For information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E____________31🔥

🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

GIDANSU KHADIJAH💔😥

Sai can rana wuraren karfe 2 su Maman Zainab suka dawo daga wajen malamin nasu, gidanta Aunty Hauwa ta wuce, ita kuma Maman Zainab ta nufo nata gidan. Tun da ta kamo hanyar gida take jin gabanta yana faÉ—uwa, amma bata kawo komai a ranta ba, a duk lokacin da ta tuna alkawarin da wannan malami ko ace bokan ya yi mata na cewa tana komawa gida zata ga result É—in aikinta, sai ta ji wani sanyi ya ratsa zuciyarta.

Kuɗi raina na dukan naira har naira 200k ta kwasa ta bawa wannan bokan, Aunty Hauwa ce nan ta yi ta zugata a kan ta bada kada ta wani damu tun da buƙatarsu zai biya, da yake tana da kuɗi issassu, da ni da ku duk mun san da cewa baban Zainab dai bai rageta da komai ba, tana samun kuɗi a hannunsa sosai, wani lokaci haka kawai zai dunƙule dubu ɗari ya bata ya ce ko zata yi wani buƙata, to tara kuɗin take yi, dan kunga bata sayan komai a gidan, ko ashana shi yake sayowa dayawa ya ajiye, hakan yasa take da isassun kuɗaɗe a cikin account ɗinta, shiyasa bata nemi ko sisi daga hannunsa ba da zasu je wajen malamin, sai dai single ɗinsa da ta ɗauka da kuma hularsa, dan Aunty Hauwa ta ce mata ta ɗauki wasu daga cikin abubuwan da yake amfani da su, domin bokan nasu zai buƙaci hakan, ita ma haka wai aka yi mata na mijinta, to shi ne yasa ta ɗauki wannan ma.

Ko da ta iso gida cike da murna, ga mamakinta sai ta ga kofar gidan a buÉ—e sabanin fitarta, ta dai san ta rufe gidan kafin ta fita, kuma lokacin dawowar su Khadija daga school bai yi ba bare ace kawunsu Sadiq ne da ya dawo da su ya buÉ—e masu gidan, kowa na gidan daga kan Baban Zainab, Haidar, Sadiq duk suna da key É—in kofar gidan.

Ciro wayarta ta yi ta fara duba time, nan take kirjinta ya fara dukan uku uku na ganin cewa lokacin dawowar su Khadija bai yi ba, to kenan waye ya buÉ—e gidan? Ta tambayi kanta tambayar da bata da amsarta.

Fargabarta É—aya kada ace Baban Zainab ne ya yi masu dawowar rana irin na kwanaki biyu da suka wuce, idan kuwa shi ne to fa akwai cakwakiya, dan kuwa zata sha faÉ—a ba kaÉ—an ba na fita bada izininsa ba, ya fita kishi sosai, kawai dai kawar da kai wani lokaci yake yi dan a samu zaman lafiya, amma ita nata kishin nafila ne a kan nasa.

Cike da fargabar abin da zata tarar a cikin gidan ta turo kofar ta shigo. Tsoro da mamaki ne suka kara kamata lokacin da ta turo kofar ta ji ko jam lock ba'a sanyawa kofar ta ciki ba. Ta san da cewa tabbas suna sanya jam lock ta ciki, saboda matasan marasa tarbiyar da suka yi yawa a unguwar, ga shaye shaye, kana zaune baka san hawa ba baka san sauƙa ba zasu faɗo maka cikin gida, sun sha sun bugu ba hankali a tattare da su, basu san ma sun faɗo gidan ba, hakan yasa suke rufe kofar duk wanda ya zo sai ya yi knocking azo a buɗe mashi. Amma yau sai ta ji kofar a buɗe, hakan yasa ta kara fargaba da shiga tsoro, sai yanzu ta fara danasanin fita bata tambaye shi ba da ta yi.

Sai kuma yanzu ne abubuwan da suka faru É—azun É—in suka fara dawo mata cikin kanta, gabaÉ—aya sai ta ji jikinta ya saki, duk sai ta ji ta yi nadama kuma ta ji babu daÉ—i. Kutsawa cikin gidan ta yi tana tafiya kamar wadda kwai ya fashewa a ciki, ita kaÉ—ai tasan me take tunani.

Ƙasa ƙasa ta yi sallama a bakin kofar shiga parlourn. Shiru babu wanda ya amsa mata, cike da fargaba ta sanya hannu ya yaye curtain ɗin kofar.

Kwance yake a saman doguwar sofa mai zaman mutun uku, ya ɗaura hannunsa ɗaya a saman fuskarsa, ɗayan hannun nasa kuma yana riƙe da remote na Tv, ga Tvn yana magana ƙasa ƙasa, sanye yake da brown ɗin jallabiya wadda ta sha guga sosai, har wani kyalli take yi saboda an saba gogeta sosai, ga karin gugan nan a jikinta ya fito ɓaro ɓari, sam ba barci yake yi ba, yana jin sallamar tata, a cikin zuciya ya amsa, magana ne baya son yi mata.

Wani irin dum dum ta ji gabanta ya faɗi, tunani ta fara yi a kan tun yaushe ya dawo? Idan bai jima da dawowa ba in ya tambayeta ina ta je sai ta yi mashi karyar maƙota nan ta shiga, tasan cewa ko gidan Aunty Hauwa bai yarda ta je ba, idan tana son zuwa shi yake kaita da mashin ɗinsa, idan ya kaita kuma zai gaya mata ga time ɗin da zai dawo ya ɗauketa, lokaci na cika kuma ɗan halak zaku ga ya zo ya ɗauketa sun dawo, bata zuwa ko'ina ita kaɗai ko da kanta, saboda yadda ya ɗaukota daga garinsu ya kawota nan garin da bata da kowa sai ƴan uwansa da basu sonta sai kuma Aunty Hauwa, hakan yasa yake kula da ita sosai, saboda ya sauke hakkinta da yake a kansa, akwai shi da ilimin addini sosai, kuma yana aiki da ita, duk wani hakkin mace ya sani, kuma yana ƙoƙari wajen saukewa iya iyawarsa.

Cikin parlourn ta shigo jiki ba kwari, sai faɗuwa gabanta yake yi, tun da ta shigo take binsa da kallo, ko gezau bai yi ba, bai yi kamar ma yasan da mutun ya shigo ba, hakan yasa ta fara jin fargaba da faɗuwar gaba. Room ɗinta ta wuce da sauri dan ta je ta ɓoye abubuwan da bokan ya bata da ta sanya a cikin jakarta.

Tana ajiyewa ta yi maza ta dawo parlourn, da yake bata da gaskiya ko da ta je ajiye jakar sai taga kamar baban Zainab ɗin ya biyo bayanta yana leƙarta, hakan yasa ta yi saurin ajiyewa ta fito, abin ku da bata saba ba, duk sai ta bi ta tsargu tana neman tonawa kanta asiri, ta rasa a ina zata sanya ranta.

Saman sofa mai zaman mutun É—aya ta zo ta zauna tare da ce mashi sannu da dawowa, tsoro da fargaba yasa ta manta da cewa faÉ—a suke yi, ta manta da cewa tana fushi da shi bata yi mashi magana.

Yana jinta amma bai amsa ba, ya yi kamar bashi a parlourn, dan iya ɓacin rai ta ɓata mashi rai, tun karfe 11 ya dawo gidan domin ya ɗebe mata kewa, ya dawo ya cigaba da rarrashinta tare da bata hakuri kamar yadda ya saba, amma sai ya zo ya ga bata nan, kuma bata sanar da shi ga in da zata je ba, ya kira numberta a lokacin suna kan dutse babu network, ya gwada numberta ya fi sau hamshin, amma bata shiga, ya kira number Aunty Hauwa ma bata shiga, ya je gidan Aunty Hauwar Khadija kanwar mijin Aunty Hauwar ta ce mashi Aunty Hauwa bata nan tana wajen business ɗinta na yawon bin gidan dillalai, ita kuma maman Zainab bata zo gidan ba, bawan Allah ya shiga damuwa sosai a kan to ina ta je tun da bata je gidan Aunty Hauwa ba? Ya dai san bata san kowa ba, bata kuma zuwa gidansu Haidar, gara ma gidan hajiyarsa wani lokacin yana kaita su kuma dawo a tare, baya yarda ya barta a can, dan yasan hajiyarsa zata takura mata, a tare suke zuwa su gaisheta su kuma dawo a tare.

Bawan Allah nan ya yi tunani sun fi kala ɗari a kan ina taje? Wani zuciya ya rinƙa raya mashi cewa kila ta yi fushi ne ta shiga mota ta koma gidansu, ya kira mamanta cikin hikima ta yadda ba zata yi zargin komai ba ya tambayeta ko ta yi magana da maman Zainab da safe ne? Da maman ta tambayesa lafiya? Sai ya ce lafiya lou kawai dama maman Zainab ɗin ce ta tambayesa a kan zata je gida shi kuma ya hana, shi ne ta ce sai ta gayawa mama, to shi ne ya kira ya ji idan ta kawo kararsa ya bada hakuri. Bawan Allah.

Murmushi kawai mahaifiyar tata ta yi tare da gaya mashi bata kira ta kawo kararsa ba ya kwantar da hankalinsa, rabon ma da su yi waya tun shekaran jiya, hakan yasa ya fahimci lallai ba garinsu ta tafi ba, dan da garinsu ta nufa dole zata sanar da mamarta, ya kira Sadiq da ya baro a kasuwa ya tambayesa ko ta gaya mashi zata je wani waje?.

Mamaki ne sosai ya kama Sadiq ɗin, domin kuwa bai taɓa jin maman Zainab ta fita har baban Zainab ɗin ya nemeta ba, abin ya ɗaure mashi kai, haka dai ya bawa baban Zainab ɗin amsa da a'a ai shi ta kwana biyu ma bata yi mashi magana tun lokacin da suka yi wannan faɗar.

Da okey kawai baban Zainab É—in ya amsa mashi tare da katse kiran. Yana katse kiran Sadiq É—in ya hau kiran numberta dan ya ji a ina take? Amma ina number bata shiga, babu network.

Tunani baban Zainab ya fara yi a kan to kodai dama haka take yi kullum ne? Abin ku da shaiÉ—ai ko ya ya samu kofa sai ya cusa maka wani mummunar tunanin, sai ya fara raya mashi cewa ai dama kullum idan ya fita ita ma fita take yi ta tafi yawonta, sai yau ne Allah ya nufa dubunta ya cika ya kamata, wannan tunani shi ne yafi tsaya mashi a ransa sosai, kawai burinsa yanzu ya ji ina take zuwa to?

Kamar zai yi hauka haka ya rinƙa nemanta har wajen karfe 1 na rana, sannan ne ya hakura ya dawo gida ya kwanta, sallar azahar ma yau a gida ya yi, damuwa tasa ya kasa iya zuwa masallaci ya bi jam'i, ya rasa ina zai sanya ransa bawan Allah nan, ta ko'ina ba sauki, ga hajiyarsa a gefe ga kuma maman Haidar, yanzu kuma maman Zainab ta kawo mashi sabuwar bala'i, kunga kuwa ai bai yi laifi ba da ya shareta da ta dawo! Yana ma da ƙoƙarin da kuma hakuri tare da juriya, idan wani namijin ne wlh kina yin sallama zai fara sauke maki buhu buhun masifa a kan gidan uban waye kika je ba tare da izininsa ba? Amma shi sai ya yi shiru yana mai cigaba da haɗiyar bakin cikinsa a ransa, ya yi kamar bai ganta ba, da alama kuma ya yi hakan ne dan baya son ya yi magana da ita cikin fushi da ɓacin rai, yana da ilimi, yasan cewa idan mutun yana cikin fushi ya buɗe bakinsa to tabbas sai ya yi danasani, hakan yasa bai kulata ba, sai ya huce tukun nan.

Ta kai almost 20 mins a zaune a wajen bai ko É—ago idanun ya kalleta ba, idanunsa na a kan Tv kamar mai yin kallo da gaske, alhalin ba wani kallon da yake yi, duniyar tunani ma ya afka, yo bakinciki ma ina zata barshi ya iya yin wani kallo? Ai babu wannan zance kuma.

Da dai taga bashi da niyar kallon in da take ma bare ya yi mata magana sai ta miƙe ta nufi kitchen domin ta girkawa ƴaƴanta abinci sun kusa dawowa daga school. Farar shinkafa ta dafa masu, already tana da miyar steew ɗin da ta yi da safe, so sai ta ɗauko shi ta sake ɗumamawa, ta zubesu a kulolinta kamar yadda ta saba ta kwasa izuwa cikin parlourn.

Tana kokarin shirya abincin su Khadija suka shigo, sun dawo daga school, lemun kankana da abarba ta haɗawa baban Zainab na daban kamar yadda ta saba haɗa mashi, sai dai a yau ta zuba mashi maganin da boka ya bata, tana zuba maganin jikinta na kerma, hannunta na ɓari har ta ɗan zuzzubar da maganin a wajen, abinku da bata saba ba, tana yi tana leƙo wajen kitchen ɗin, dan sai taga kamar baban Zainab ɗin yana yi mata laɓe ne, sai taga kamar ya ganta, duk ta ruɗe zata tonawa kanta da kanta asiri, shi kuwa baban Zainab bawan Allah yana can cikin parlourn suna zuba hira da su Khadija, sai dai daga jin yadda yake magana zaka fahimci kawai ƙaƙalo maganar dan dole yake yi, dan kawai yaga ya kwantarwa da ƴaƴan nasa hankali kuma matsalar da yake a tsakaninsa da mamarsu bata shafesu ba, yana ƙoƙarin yaga bai ɗauko matsalar mamarsu ya shafa masu ba, yasa su rasa farincikinsu da kulawar da suke samu daga garesa a kullum ba.

Bayan ta kammala haɗa mashi lemun ta shirya a saman try ɗin jug ɗin tare da cup's ta ɗauka sai cikin parlourn, sam bata ji tsoron kada su Khadijah su sha ya zamar masu matsala ba, ita dai bukatar ta ya biya taga abubuwa sun dai'dai ta mata kamar da....... Ni kuwa PRINCESS TEEMA na ce ki kauce hanyar Allah kuma ki yi tunanin abubuwa zasu dai'dai tun maki? Lallai kin tabba babban kuskure kuwa, domin wane mutun, babu wanda ya isa ya ga dai'dai idan ya sauƙa daga kan haryar Allah, ai yama kullah da rashin daidai kenan har sai ya tuba, idan kuma bai tuba ba haka zai mutu cikin ƙunci da baƙinciki, ya je lahira kuma ya girbi abin da ya shuka, Allah ka kiyashemu sauƙa daga kan hanyarka, Allah ka tsaremu kaucewa faɗar ma'aiki, ka kare mu daga sauka daga turbar da ma'aikinka ya ɗauramu, duk wuya duk daɗi ya Allah ka tausaya mana ka barmu da imaninmu, ya Allah cikin jarabarwa da zaka yi mana kada ka haɗa mana da raunin imani tare da tawakkali.

Kamar yadda ya saba shan lemun ya kuma ci abincin haka yau ma ya ci ya sha, sai dai fa yau É—in ya ci ne kawai saboda su Khadija, ba dan haka ba bai da niyar cin girkinta yau, bama yau ba bai da niyar sake cin girkinta har sai ta gaya mashi in da take zuwa, idan ta gaya mashi kuma sai ya bincika yaga da gaske ne ko karya, dan haka kawai ya ji hankalinsa sam yaki ya kwanta.

Bayan sun kammala cin abincin, har da su Khadijah duk sun sha lemun baban nasu, miƙewa ya yi tare da nufar room ɗinsa, ita kuma maman Zainab jiki ba kwari ta zo ta tattare wajen, ta shiga damuwa sosai na ganin yaki ya kulata, har ta yi tunanin ta bisa ɗaki ta bashi hakuri, sai kuma ta sake cewa bari ta barshi tun da ya sha maganin nan, wata kila zai sauko ya zo ya fara yi mata biyayya................ Babbar magana, akwai case kuwa ba karama ba, ga su Khadija ma dai sun sha magani, ko me zai faru? Mu dai je zuwa zamu ga komai dallah dallah, kun san ni dama da iya yi maku komai dallah dallah ta yadda zaku fahimta da kyau da kyau, to mu dai je zuwa, na yi gaba sai kunzo!.

Shirin komawa kasuwa ya je ya yi tare da fitowa, bai yi mata sallama ba ya sa kai ya fice izuwa harabar gidan. Da sauri Zee and Khadijah suka bi bayansa.1k ha ciro daga cikin aljihunsa ya basu a kan su sai wani abin idan sun je islamiya, ya san ba'a rabasu da kayan kwalama.

Sai zuba mashi godiya tare da adduar a dawo lafiya suka rinƙa yi, ita kuwa maman Zainab ta maƙale a windown parlourn tana leƙansu, ji take yi kamar ta je ta bashi hakuri, amma kuma idan ta tuna ya sha magani sai ta ce ina babu wani hakurin da zata bashi, da kansa zai kawo kansa gabanta yana mai ƙasƙantar da kansa a ƙasa, a nan ne zata zuba mulkinta ita kuma. Babbar magana.

Tana ji tana gani ya fice ya tafi kasuwa, su Khadijah kuma suka dawo cikin parlourn, room É—insu suka nufa domin su yi wanka tare da É—auro alwala su yi shirin zuwa Islamiya, dan lokacin sallar la'asar ta kusa, saura kaÉ—an, suna yin sallah kuma zasu wuce Islamiya.

Ita ma mamar tasu nata room ɗin ta shiga ta kwanta, dan ta huta, duk a gajiye take, dutsen nan da suka hau ya ja mata ciwon kafafu................ Ni kuwa nace har da uban ciwon kafafu ma zai ja maki ai, ai kafafu ma kaɗan ne ba dai saɓon Allah ba?.

Sai da suka kammala shiri cikin uniform ɗin islamiyarsu, sannan suka yi sallar la'asar, dan a lokacin an kira, bayan sun idar da sallar lafiya lou suka zo suka yi mata sallama a kan sun tafi islamiya, kuɗin kayan miya kamar yadda suka saba ta basu su sayo mata a hanya idan suna dawowa, daga haka bata sake yi masu magana ba, suma karɓa kawai suka yi suka wuce abinsu, dan sun san kwana biyun nan fa gidan nasu sai addu'a kawai. Yara masu hankalin manya kenan, kullum cikin yiwa iyayen nasu addu'a suke yi bayin Allan!.

Tamkar Khadija zata dawo ta ce mata an kira sallar la'asar, sai kuma ta fasa saboda kada ta yi mata faÉ—a ta ce ai ita ba kurma bace tana ji. Haka suka wuce Islamiyarsu, gwanin birgewa idan suna tafiya islamiya, cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, kai daga ganinsu kasan tarbiya ta ratsasu sosai.

Maman Zainab kuwa barcinta ta hau yi ba tare da ta yi sallah ba, dan ta ci mugun wuyar hawa dutsen, duk gaɓɓan jikinta ciwo yake yi mata, hakan yasa da ta kwanta ta ƙasa iya tashi, sai kawai ta hau barci ƴar kaniya.

Ɗan tsokaci, saɓon Allah komai ƙankantarsa yana mugu mugun nesanta bawa da Ubangiji tare da raba shi da imani, barema saɓon Allah mafi girma wato shirka, haɗa Allah da wani kenan, kun dai san maman Zainab tana da ƙoƙari wajen yin ibada, amma da yake ta saɓawa Allah kunga har abin ya fara shafar ibadarta, ko a jikinta ta kwanta tana barci lokacin sallah, to haka saɓawa Allah yake, kishiyoyi ne da rabaka da Ubangiji, daga nan kuma zaka ga komai yana taɓarɓare maka, please ƴan uwana mata, zan yi amfani da wannan dama na ja hankulanku sosai, duniya dai ba matabbata bane, kwana nawa ya rage? Lahira ita ce madauwamiya, kada ki je garin neman duniya ki ɓata lahirarki wadda kuma ita ce madauwamiya, duniya tamkar kasuwa muka zo ci mu koma gidan gaskiya, duk daɗi duk wuya kada ki taɓa yarda ki rasa lahira, gara maki ki rayu cikin ƙunci na tsawon rayuwarki da ki lalata lahirarki, Allah ka karemu da kariyarka, ka shiga cikin lamuranmu, ka dafawa musulmi da musulunci, ka kara ɗaukaka musulunci da musulmai bakiɗaya, ya Allah ka jikanmu, ka tausaya mana, kai mana rahmarka, dama kai arrahman ne kuma arrahim, ka gafarta mana, dama kai algaffar ne, mai gafartawa bayinsa a duk lokacin da suka ƙasƙantar da kai suka nemi afuwa, ya Allah ka kawo mana zaman lafiya a duk in da muke. Ku ce amin a cikin zuciya!.

Bari mu leƙa wani wajen, wata kila kafin mu dawo baban Zainab ya dawo mu ga result ɗin maganin bokan ya ake ciki?!.

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

🏞️FOREST🏞️🌼

After some days. A cikin ƴan kwanakin nan da suka suɗe, Kamran sun yi muguwar sabo da su Pretty, kullum yana zuwa kamar yadda ya saba, har yau kuma ya kasa iya tambayar mammarsa menene aure, tun da ya tambayeta menene Alhdulillah ta ɓata rai sosai kamar zata maresa, ta kuma tsare shi a kan dole sai ya gaya mata a ina ya jiyo wannan kalmar ta Alhdulillah? Da kyar ya iya shawo kanta ya gaya mata cewa wasu maharba ne suna wucewa ya ji suna faɗin Alhdulillah, shi ne yake son sanin ma'anarta, warning ta yi mashi sosai a kan babu ruwansa da jin abubuwan da mutane masu wucewa zasu faɗa, a wannan rana dai sam bai je wajen su Pretty ba, saboda mamma ta yi mugun ɗaukar zafi na jin kalmar Alhdulillah ta fito daga bakinsa, hakan yasa ni PRINCESS TEEMA na kara sakawa mamma ayar tambaya a kai, duk yadda aka yi tana da sani a kan addinai ba iya musulunci kawai ba, tana da sani sosai a kan har sauran addinan, dole akwai wani abin da yasa ta ce ita bata yarda da addini bama kwata kwata, ita bata da addini, yadda ta ɗauki zafi daga jin kalmar Alhdulillah ya nuna tasan ma'anar kalmar.

Shi kuwa Kamran a bakin su Pretty yake yawan jin wannan kalma ta Alhdulillah, sai ya yi gangancin tambayar mamarsa bai tambayi su Pretty ɗin ba, tun da yaga ta ɗauki zafi sosai haka sai ya ji tsoron yi mata tambaya a kan menene aure, dan gudun kada ya zamana shi ma auren wata magana ce babba da zai ja mashi a rabashi da su Pretty, duk abin da zai sanya a rabasu baya kaunar ko jin makamancinsa, dan sun zama wani ɓari na rayuwarsa, wani abu guda ɗaya da ya lura da shi shi ne, duk wani abin da zai fito daga wajensu Pretty yana cin karo da ra'ayin mammarsa, ma'ana zaka tarar da Mammarsa ta tsani jin makamancin wannan abin, abin har ya fara bashi mamaki yana kuma ɗaure mashi kai sosai, hakan yasa ya fara zargin lallai Mammarsa tana da sani a kan irin wannan addini nasu su Pretty, sai dai ya barwa zuciyarsa wannan tunani, saboda baya son ya ɓallo ruwan da zai rabashi da sanyin idaniyarsa wato su Pretty, ga shi mum ɗinsu ta bashi amanarsu, ai kunga nauyi ya karun masa a ka, dole ya zage dantse wajen kula da su.

A ƴan kwanakin nan da suka shuɗe sun yi muguwar sabo da shi na ƙin karawa, har ta kai ta kawo yanzu sai ya zo suke cin abinci a tare, suna fita waje filin ƙoramar nan su yi ta wasa, a yanzu yana koyawa Pretty harbi da kifiya, sakamakon ya rage jin feeling da yake yi, hakan kuma ya samo asaline saboda maganin da mammarsa take basa ba tare da saninsa ba, so yanzu idan ya taɓa Pretty baya jin abin sosai.

Yanzu ya koya mata busar wannan sarewar tasa da yake kyarawa da abin ayaba, ya koyawa Sweetie ma, idan suka zauna a wajen ƙoramar nan yana koyawa Pretty harbi da kifiya ita kuma Sweetie tana yi masu busa mai daɗi, abin gwanin birgewa, wani lokaci ya goyi Pretty su hau saman bishiya su ciro mangoro, Sweetie tana ƙasa tana yi masu busa, sai dai su ciro su zo su wanke mata su bata ta sha.

Sai dai fa har yau har gobe Pretty dai taki yarda da Rocky, taki yarda su zama abokai, ta ce babu wannan magana, kowa ya tsaya a matsayinsa, Kamran dai bashi da zaɓin da ya wuce ya yi masu iyaka idan yana son zaman lafiya, baya yarda ya bar Rocky ya taɓata, dan yana taɓata zata haukace masu ne a wajen.

Taƙa tsantsan sosai Kamran yake yi wajen zuwa wajen nasu, dan kada Mamma ta gane shi. A yanzu warriors ɗin nan sun ɗan rage shigowa cikin wannan dajin, yau tsawon kwanaki biyar kenan Kamran bai haɗu da ko mai kama da su ba. Gawarwakin warriors ɗin da wannan jarumin sadaukin mutumin ya kashe su ma duk Kamran ɗin ya jefasu cikin ruwan dake gudu har izuwa wajen babban teku ruwan ya tafi da su.

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

Gari ya yi sanyi, rana ta yi yamma ta kusa faɗuwa, inuwa ta sauko a dajin, ƴelwar ni'imar iska tana kaɗawa a ko'ina, iska ce mai matuƙar daɗi da ratsa jiki, dogayen bishiyoyin sai kaɗawa suke yi, ba iska bace ta ruwan sama, ba kuma iska bace ta hunturu, iskace ta bishiyoyi suke kaɗawa, yanayin gari ya yi matuƙar daɗi musamman ace ga masoya, dajin ta yi shiru sai sautin kukan tsuntsaye ne yake tashi da kuma sautin zubar ruwan koramu, gari babu hadari.

Rocky yana kwance a kasar wata jibgegiyar bishiyar ɗorawa da take a kusa da ƙoramar wajen su Pretty, da alama ma barci yake yi. Sweetie tana zaune a kusa da shi, kasancewar bata gani baiwar Allah bata san a kusa da ita Rocky yake kwance ba, kayan marmari ne a gabanta take sha cikin nutsuwa.

Su kuma sarakan suna saman dutse, Kamran yana zaune ya miƙe kafafu ruwan koramar tana sauƙa a saman kafafun nasa, ita kuma Pretty tana zaune a ta gabansa, sai dai ta bashi baya ta ɗan kwanto a jikinsa, ita ma ta miƙe waƴan nan ƴan guntayen kafafun nata, ko wajen ƙoramar kafafun basu iya kaiwa ba saɓanin nasa da yake cikin ruwa tsulumdum, sai takura mashi take yi a kan su matso baki bakin dutsen dan ita ma kafarta ya shiga cikin ruwan. Shi kuwa ya ce ai ita gajera ce ko sun matso kafafun nata ba zasu iya taɓa ruwan ba, ta bari sai ta zama babba kamar shi.

Mai hali dai baya fasawa shi ne ta sa mashi kuka tare da miƙewa tsaye wai zata faɗa cikin ruwan mai gabaɗaya.

Jawota ya yi ta zauna, dukkansu biyu hannunsu na rike da abin busar suna busawa ne dama, sun yi harbi da kifiya har sun gaji ne suka koma yin busa.

"Kai our Pretty kin iya rigima fa". Ya faÉ—a yana jan hancinta.

"Ba wani rigima, ni ka matso nima kafata ta rinƙa taɓa ruwa".

"Sai ki yi mun busar da ta fi ta jiya daÉ—i zan matso". Ya yi maganar yana tattare mata gashin kanta da iska ke kaÉ—ata tana rufe mashi fuska.

"Idan na yi maka zaka goyani mu hau kan Giwa?".

Ƙulle mata gashin nata ya yi yana faɗin. "E amma ai ba yau bako? Dan yau ba zamu je wajen giwayen can ba, kinga lokacin komawata gida ta kusa".

Turo baki ta yi kafin ta ce. "To ba kai ne ka je ka jima wajen cirowa Sweetie fruit ba? Ni Allah ba zan yarda ba sai mun sake zuwa wajen, akwai daÉ—i hawa bayan giwa......"

Tarar numfashinta ya yi da cewa. "Akwai daɗi kuma kike yi mana ihu? Jiya duk kin yagushe mun wuya da waɗan nan faratunan hannun naki, duk saboda tsoron giwa, kin wani ƙanƙameni kamar idan zasu cinyeki ba zasu haɗa da ni ɗin dukka su cinye ba, kin sa na koma mamma tana tambayata me ya jimun ciwo, sai da na ce mata mage ne ta yakusheni". Ƙasa ƙasa sosai ya yi maganar kamar mai raɗa.

Sweetie dake shan fruits ɗinta ne ta amsa zancen da cewa. "Ai ba zaka kara kaita ba Kamran, jiya da daddare muna barci sai ta yi ta kurma ihu cikin tsakiyar dare wai ga giwa ya buɗe baki zai cinyeta na ceceta, sai da na rinƙa tofa mata addu'oi sosai kafin na samu ta yi barci".

A hanzarce Prettyn ta ce. "To waye ya ce ki gaya mashi? Ya tambayeki ne? Ni ba wani ihun da na yi, sharri ne kawai dan baki son a kaini, kuma sai ya kaini É—in".

Shi dai dariya suke bashi idan suka fara wannan diramar tasu, ita Pretty bata son ace ta gaza a kan wani abin, ta fi son ace ta iya komai, ita kuma Sweetie sai iya faɗar gaskiya bata rufawa Prettyn asiri......... 😅

"Nikam Kamran ka kammala karanta littafin da mum ta baka É—in ne?". Sweetie ta tambaya, dan a cewarta ba zata biyewa Pretty ba, haka dama take yi kullum, bata biyewa Prettyn.

"No na dai fara karantawa, amma ban samun ishasshen lokaci sosai ba, ni kai'na ina son na kammala karantawa, a ƙage nake da na karanta, dan naga duk wani abin da ta bar mun a cikin saƙo kama daga waɗan nan ring ɗin da komai da komai akwai labarinsu a cikin littafin, shiyasa nake son karantawa na ji me zan yi mata da su, amma da na fara marantawa ne sai Mammata ta zo, bana son kuma taga littafin da kuma kayan, shiyasa sai na ɓoye, bana samun lokaci a gida na karanta, a waje kuma ina tare da ku, da daddare kuma ban isa in kunna wuta a ɗaki na ce zan yi karatu ba, mamma zata ce me nake yi ban yi barci ba, amma soon zan karanta". Yana magana yana ta murɗawa Pretty kyakkyawar dark black curly hairnta. Ita kuma ta wani kwanta mashi a jiki sarkin son jiki.

Sweetie tana ƙoƙarin yin magana Prettyn ta rigata da cewa. "Ni Kamran ka matso bakin dutsen nan please, ina son kafata ta taɓa ruwa, kuma gobe zaka kaini wajen Giwa, Allah Sweetie babu ruwanki, tun da ke kin ce ba zaki je ba ai sai ki barni ya yi ta kaini yawo nikam".

Dogon hancinta ya É—an ja tare da faÉ—in. "Ki yi ta wahalar da ni ina goyaki ko? Saboda tsoro sai ki ce ba zaki tafi da kafafunki ba, kisa na goyaki duk na gaji".

Sweetie ce ta ce. "Katuwa da ita zata yi ta karya maka baya ko ta saka ka ciwon kwankwaso ba?".

"Allah Sweetie bana so, babu ruwanki da ni, ni ƴar karama da ni ɗin ne zaki ce zan karya mashi baya? To ni yaushe ma nake da ƙiba? Baki fini girma bane? Kin fini ai, kuma a haka shekaran jiya ya goyaki muka tsallake duwatsun can, ke baki ɓalla mashi baya ba sai ni? Kamran kada ka kulata sharri take yi mun ko? Ina bani da nauyi?".

Yadda ta yi maganar gwanin ban dariya, irin ita ma wai zata yi mashi wayon nan ta saka mashi magana a baki.

Shiru ya yi bai amsa masu ba, dan yanzu idan ya amsa da cewa tana da nauyi Sweetie zata ji daɗi, ita kuma Pretty ba sai na faɗa ba kunsan kuka zata yi mashi ance tana da nauyi, idan kuma ya amsa bata da nauyi, to Prettyn zata yi dariya har ma ta yi wa Sweetie gwalo, ita kuma Sweetie bara ta ji daɗi ba ga watsa mata ƙasa a ido, dan haka sai ya yi shiru ya kyalesu, haka suke yi mashi wani lokaci, sai su saka shi a tsakiya ya rasa bayan waye zai bi bawan Allah. Idan ya bi bayan wannan, sai wannan ta yi fushi, idan ya bi na wannan, wannan ta yi kuka, shirun dai shi ne mafita a gare shi!.

Rayuwarsu gwanin birgewa sosai da sosai, sai sun baka sha'awa idan ka gansu, sun ɗauki Kamran tamkar ɗan uwansu na jini, shi ma duk da yana jin son Pretty a ransa sosai da sosai baya taɓa yarda ya nuna masu banbanci, ya fi nunawa Sweetie ma kulawa, saboda akwai ranar da ta ce mashi Kamran saboda bani da ido bana gani ne yasa baka hira da ni sai Pretty kawai ko? Wannan maganar tata ta taɓa mashi zuciya sosai da sosai, hakan yasa ya ɗaura ɗamarar koyan zama dasu su dukka ba tare da nuna masu wani babanci ba, sai ma ya fi bawa Sweetie kulawa dan kada ta ji babu daɗi ta ji kamar cewa ita ba mutun bace dan bata da ido, yana janta a jiki sosai yanzu.

Ita kuwa Pretty ta daban ce a cikin zuciyarsa, yana bala'in kaunarta, kome ta yi kyau take yi mashi, amma kuma abin da bai sani ba shi ne Sweetie ce take son shi ba Pretty ba, ita Pretty da kauɗi ya yi mata yawa a kai ina ma take wani bi ta kansa sosai, ta dai shaƙu da shi fiye da Sweetien, tana kuma kaunarsa a matsayin ɗan uwa da suka ɗaukesa, bayan haka babu wani abin, amma watakila a gaba zata iya fahimtar tana son shi. Akwai cakwakiya sosai kam, domin ita Sweetie da iya gaskiyarta take son shi, bata san ya kamaninsa yake ba, amma zuciyarta ta kamu da kaunarsa, wannan ita ce ma kauna ta gaskiya duk da ita ma bata san me kaunar ba a yanzu, saboda ƙananun shekarunsu.

Hmmm akwai case ba kaɗan ba, mum ɗinsu ma auren Pretty ta bashi bana Sweetie ba, Allah sarki baiwar Allah ga cutar makanta gana soyayya, to Allah ya baki ikon cin jarabawarki. Bari mu leƙa DUBAI mu dawo.

🌼DUBAI🌼

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

Share fisabilillahi 👏

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍

🔥CROWN OF INJUSTICE🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)

🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 9/8/2024.....✍️📚🌹

For information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E____________32🔥

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

🌼DUBAI🌼

After some days.🕊️

LEESHARH🌼

Kwance take a saman bed ɗin nata, idan ka kalleta zaka yi zaton ba ita bace, ta goge ta yi wani kyau da ita, dattin gidan AAJ duk ya fita, ta ɗan yi dumurmur da ita, alamar ta samu huta da kula, ba karya suna kula da ita sosai, dan a halin yanzu ita ce kawai hope ɗinsu, ita ce zata biya masu buƙatarsu da suke ƴinwace wajen nema, kula da ita sosai suke yi tamkar kwai a saman bajajjen plate.

Mayuka da sabulan gyaran jiki kala kala masu kyau da tsada suka saya mata take amfani da su, wannan mata dai ta zage sai koya mata aikin take yi kamar yadda suka gaya mata.

Sai dai kuma har yau bata iya samun damar ganin ko face ɗin mutun ɗaya daga cikin gidan ba, ta yi iya ka baƙin ƙoƙarinta wajen ta samu ta ga face ɗinsu, amma abin ya ci tura. Daga harshe dai sai ta hakura ta fawwalawa Allah komai... Hmmm ga shi ita da kanta bata san a wani location wannan gida yake ba, an dai keto da ita cikin unguwa, ga gidajen da yake a unguwar duk ginin iri guda ne, in fact bama ta san wace unguwar bace ba, bata san komai dan gane da su ba.

Duk nacinta da yadda ta so ta iya sanin wani abin a dangane da su to fa hakura ta yi, domin ance duk wanda ya rigaka kwana to zai rigaka tashi, wannan haka yake, sun ko fita wayo, idan juranta sammako to su a tafe suka kwana, sun ki yarda su bata wani dama, a shirye suka tsab kafin su fara duk abin da za su yi.

Ta kwanta shiru tana tunanin duniya, mahaifinta ne kawai a cikin ranta, ta ƙurawa sama idanu kamar wata mai kallon wani abin, dama kun san akwai ta da ido kam, tafi kowa manyan idanu a gidan AAJ.

Wani irin jiniya ne ya karaɗe gabaɗaya unguwar ta su, jiga jigan motoci ne suka saki jiniya tun daga nesa da wannan gida, ya karaɗe ko'ina, tun da Leesharh ta zo wannan gida bata taɓa jin jiniya makamancin hakan ba, wani lokaci jefi jefi tana jin karar jiniyar motar ƴan'sanda ya wuce, da yake unguwa ce ta manya, akwai irinsu ƴan majalisu, ciyamomi da sauransu, hakan yasa wani lokaci motocin ƴan'sanda da sojoji suke giftawa tare da motar wani ɗan majalisa, to amma na yau jiniyar ta daban ce, domin ta karaɗe ko'ina a faɗin unguwar, daga ji kasan wasu manyan shegu ne suka dimfari arear.

Kamar wadda aka tsira ta miƙe zaune a tsakiyar bed ɗin, tunani ta fara yi akan wannan jiniya kuma na menene? Waye ne kuma ya zo?.

Bata ankara ba sai jin jiniyar ta yi har tsakar kanta kamar zasu tashi gidan nasu, alama ce ta motocin cikin wanna gida suka shigo.

Ai a dubu É—ari ta diro kasa daga saman bed É—in, da gudu ta nufi wajen window dan taga wanene? Sai addu'a take yi Ubangiji Allah yasa su basu rufe face É—insu ba, ta samu dai taga koda mutun É—aya ne, dan tasan ya kamanin Æ´an gidan yake.

Jikinta na kerma ta ɓalle labulen window, har tana ƙoƙarin faɗuwa saboda sauri. Kurawa parking space ɗin gidan idanu ta yi kamar idanun nata zasu faɗi ƙasa. Danƙara danƙarar motoci masu numfashi har guda goma ne suka keto cikin wannan gida, kai daga ganin motocin kasan na manyan shaggu ne, sun haɗu iya haɗuwa, ga motar polices biyu a baya ɗaya a gaban jerin gwanon motocin nasu.

Gabaɗaya bodyguards ne a cikin motocin da suka kasance launinsu bakake, mota ɗaya ce ta kasance launinta fari a cikinsu, mamallakin wannan mota kuma bai fito ba, bodyguards ne kawai suka firfito tare da tsaitsayawa a gefe da gefen motocin, ƴan'sanda kuma suka diro ƙasa daga saman bayan motocinsu hannayensu a riƙe da wasu shegun bindigu waɗan da basa saɓa saiti.

Daga bodyguards ɗin har ƴan'sanda dukka akwai face mask a face ɗinsu, su bodyguards ɗin ma sun kara da black glass a idanunsu, jiga jigai ne bodyguards ɗin, suna ji da ƙoshi da lafiya.

Ƙara kura masu idanu sosai Leesharh ta yi tana jiran taga wanenen mamallakin wannan luxurious white car ɗin, ga shi bodyguards sun buɗe mashi kofar motar amma shiru bai fito ba, yana zaune a ciki.

Ji Leesharh take yi tamkar ta fita ta je ta janyoshi ya fito daga cikin motar koma wanene ta gansa. Amma ina ba hali, dole ta yi jira sai lokacin da aka ga damar fitowa.

An ɗauki a kallah tsawon good 10 mins kafin nan ya sako kyawawan kafafunsa waje, wadda yake sanye cikin wani haɗaɗɗen black booth mai matuƙar kyau da tsada, kai daga ganin wannan shoe ɗin kasan bana ƙananan kai bane.

Ko da ya sanya kafafun nasa waje ma sai da ya É—an É—auki 2 mins kafin ya fito waje mai gabaÉ—aya, nan take bodyguards É—in suka fara sara mashi.

Matashei ne mai ji da lafiya, cikakken namiji ne wanda a kallah zai iya kai 27 years a duniya, sanye yake da ƙananan kaya, wandon jeans dark ash and white polo shirts, arab hairnsa yana kwance har wajajen bayan wuyansa, ya gyara gashin nasa sosai da sosai, farin balarabe ne tas da shi, kyakkyawa ne ajin farko, duk da kansa a sunkuye yana kallon ƙasa hakan ba zai iya hana ka gane kyakkyawan gaske bane.

Hannunsa ɗaya na ɗaure da wani dankareran diamond watch, ɗayan hannunsa kuma babu komai yana riƙe da wayarsa, arab skin ɗinsa sai sheki yake yi, ya ji hutu har ya gaji. Daga yanayinsa zaka fahimci jininsa a tafashe yake.

Cikin tafasar jini ya taku ya nufi cikin gidan kai tsaye, Leesharh bata samu damar ganin face É—insa da kyau sosai ba, amma dai tabbas ta gansa, saboda bai rufe face É—insa da komai ba, da alama ba É—an gidan bane, duba da rashin amfani da face mask da ya yi kamar yadda su suke yi.

Wani irin ajiyar zuciya ta sauke tare da ƙara mannewa da jikin windown tana tunanin to wanenen kuma wannan haɗaɗɗen guy ɗin?

Kamar saukar aradu daga bayanta ta ji an ce. "What are you doing there?".

A razane ta juyo da kallonta kirjinta na dukan uku uku. Wannan mata ce mai koya mata aiki, ita ce ta jefo mata wannan tambaya.

Ƴan kame kame ta fara yi na rashin gaskiya tana zaro waɗan nan idanun nata kamar ball ɗin mota, cikin rawar murya ta amsa da nothing tare da sakin labulen window ta bar wajen. Da kallo ta cikin nikaf matar ta bita da shi har ta isa saman bed ɗinta, sumui sumui kamar munafuka da asirinta ya tonu aka kamata tana munafurci haka ta haye saman bed ɗinta ta takure waje guda.

Wucewa wannan matar ta yi ta nufi cikin toilet ba tare da ta sake yi mata magana ba. Shiru Leesharh ta yi tana binta da kallo, ita ta kasa iya gane halin wannan mata, yau ka ganta kamar mutuniyar kirki, gobe kuma sai kaga wlh ta ma fi shaiɗan iya shaiɗanci, ga bakin hali, mugunta da rashin son magana, idan ka yi mata magana ko ka tambayeta wani abin, sai dai ta nuna maka da hannu ko ta ɗaga maka kai, amma ba zaka ji tana magana ba, sai ayi magana goma bata amsa ɗaya da muryarta ba, sai dai da hannu ko kai kamar ƙadangaruwa, yadda kuka san mai ciwon baki.

Jim kaÉ—an ta fito daga cikin toilet É—in ta nufi kofar fita. Ko sanu bata sake cewa Leesharh ba, dama ita kuma Leesharh ba magana take yi mata ba, a haka suke rayuwa a cikin wannan É—aki, sai dai fa ba'a nan matar take kwana ba, da dare ya yi zata bar É—akin, ba zaka sake ganinta ba sai gobe da safe, tun abin yana bawa Leesharh mamaki har ya dai'na, yanzu ita ta riga ta saba da ahalin wannan gida.

Matar na fita ba'afi da minti biyu ba sai ga wannan matashiyar matar ta shigo cikin room ɗin bakinta a ɗauke da sallama. Amsa mata sallamar Leesharh ta yi tare da ɗan sakin fuskarta kaɗan, domin sun saba da wannan mata, ita kaɗai ce Leesharh take ganin ta Allah a gidan, ita kaɗai ce mai yi mata magana mai daɗi, ƙananun shekarunta yasa ta kasa iya banbanci kalaman soyayya da kuma kalman yaudara, ita dai a ganinta wannan matashiyar matar tana sonta tsakani da Allah..... Hmm yaro yaro ne bai san wuta ba sai ya taka. Wannan hali na matar shi ake kira da makirci kuma kisan karkashin ƙasa or mummuƙe! Leesharh dai bata gane ba, bata san suwa ye ake cewa makiran mutane ba.

A bakin bed ɗin wannan mata ta zauna, cikin nutsuwa ta ce. "Leesharh gobe za'a kaiki gidan Abu Abdussalam bin Badeen, ki tsaya sosai ki jajirce ki yi aikinki, ki mai da hankali ki yi abu da wuri dan ki samu ki je wajen babanki ku koma ƙasarku, kada ki yi wasa, kin dai ɗauki duk abin da aka koya maki ba?".

Kai ta gyaɗa mata kamar kan ƙadangaruwa alamar e ta ɗauki komai.

"Good girl, to kada ki yi wasa kin ji? Ga wannan wayar idan kin je ki tabbatar kin ɓoyeta kada kowa ya gani, zan kara jan kunnenki Leesharh, ban yarda ki yi hira da ma'aikatan gidan ba bare har ki je kiyi suɓutar baki ki saki layi ki sanar da su abin da ya kaiki, nasan ma'aikatan gidan ba kakanun masu ilimi bane, wasu ma zasu yi maki dabara su bugi ruwan cikinki, kin dai ji abin da mai koya maki aikin nan ta ce ko? Kada ki yarda ki saki baki kiyi hira da wata, idan ya wuce gaisuwa ina wuni shikenan kada ki kara kada ki rage, sannan bayan Ramish ban aminta da ki kula kowa a cikin gidan ba, shi kaɗai zaki sakawa ido, kibi a hankali".
Ta kai karshen maganar tana kallon Leesharh har cikin ido.

"Aunty zan yi duk abin da kika ce da kuma abin da kuka koya mun In Sha Allah, amma Aunty ya za'ayi na gane wanene Ramish É—in? Sannan kuma a wajensa zan yi aiki ne?". Ta yi tambayar cike da fargaba, tsoro take yi kada Aunty tata ta ce mata ta cika tambaya sosai.

Shiru matar ta ɗan yi kafin ta ce. "Ramish! Ramish! Ramish, kina ganinsa a jikinki zaki ji cewa shi ne, domin shi ɗin ganinsa ba kowace zuciya take iya ɗauka ba, amma dai zan turo maki hotonsa ki gani a cikin wayar, ki kula sosai, and yana da wasu kanne da ba zasu wuce mate ɗinki a shekaru ba, i think ba zasu wuce 13 years ba, kin ma fisu shekaru, they're twins, (Obaid and Omaid) and they're very very stubborn, basu cika zuwa gidan ba, amma na tabbata duk ranar da suka je idan kika yi wargi kaɗan zasu iya gano cewa ke ƴar leƙen asiri ce ko kuma akwai abin da ya kawoki gidan, because they're very very talented and suna da sharp brain fiye da tunaninki, kamar aljanu haka suke, ki kula sosai, idan sun zo gidan kada ki yarda ki yi wani kwakkwaran motsi, idan da dama ma kada ki bari ku haɗu da su kin ji?".

"To Aunty amma ta yaya zan gane sune har na guji haÉ—uwa da su ni da ban sansu ba?".

"Ai waÉ—an nan twins É—in idan suka je gidan dole ma kisan sun je, saboda kamar yadda na gaya maki yadda kika san aljanu haka suke, kuma kowa a gidan sonsu yake yi, har shi kansa mai girma Abu Abdussalam bin Badeen kaunarsu yake yi, idan suka ce zasu je gidan ma har wani shagalin murna Æ´aÆ´an Abu Abdussalam suke haÉ—awa, dan suna kaunarsu, ai zaki gani idan kika je, yawanci weekend ne suke zuwa gidan su É—an yi hutu, kwana biyu kawai suke yi a gidan Saturday and Sunday, amma wlh sai ki rantse da Allah wani shugaban ne yaje gidan, saboda kauna da ake nuna masu, ke dai ki kula dasu, dan sun fi bala'i iya bala'i, makirai ne na karshe!".

(Yo ai dole ayi mata kashedi a kan Obaid and Omaid 😅 hmmm yaranda kamar ba mutane ba, anya Momma lafiya aka bar maki ƴaƴan nan naki kuwa?🤔 Na fara tantanma, dan sun fita zakka a cikin ƴan uwansu, ai kuwa Leesharh tana yin wani wargi zasu kamata waɗan nan yara, da kuwa sunanta sorry wlh baiwar Allah)

Da okey ta amsa mata, saboda a yanzu an koya mata dabaru kala kala. Ji take yi kamar ta tambayi Auntyn nata wanene wanda ya zo yanzun nan? Sai kuma ta basar da maganar gudun kada ta jama kanta wani abin.

Miƙa mata dalleliyar wayar hannunta matar ta yi, waya ce mai tsada ga kyau, sannan ta miƙe ta nufi waje tana gaya mata cewa mai koya mata aiki ta tafi, aikinta ya kare yau.

Haka kawai Leesharh ta tsinci kanta da jin faÉ—uwar gaba a lokacin da ta ji zancen mai aikin..... Ni kaina na ji wannan faÉ—uwar gabar, fatana dai shi ne Allah yasa ba kashe mai aikin zasu yi ba, dan sun ce babu mai jin sirrinsu kuma ya rayu, kunga kuma ita mai aikin ai ta ji sirrinsu, dan sai da suka gaya mata abin da zata koyar da Leesharh É—in, to Allah dai ya nuna mana lokaci ya kai mu mu ji komai a tare.

Zubawa wayar idanu sosai Leesharh ta yi tana kallonsa, a cikin wannan sati biyu da suka yi an koya mata yin amfani da waya, sai dai abin da bata sani ba shi ne an saka mata abubuwa biyu zuwa uku a cikin waya. Na farko an saka mata na'urar bi diddigi a cikin wayar, na biyu ansaka mata abin sauraren magana, matuƙar wayar tana kunne ta yi magana a kusa da wayar to waɗan da suka bata wayar suna sauraren duk abin da zata faɗa, abu na uku kuma shi ne anyi setting na wayar ta yadda duk wanda ta ki zasu sani. Hmmm wlh akwai cakwakiya ba kaɗan ba a wannan part ɗin. Duk Leesharh bata san da waɗan nan abubuwa da suka sanya mata ba fa tab! Waya sani ma kila akwai wasu abubuwan da basu bari muma mun sani ba.

Yanzu ita Leesharh duk bama wannan bace a gabanta, face ɗin wannan mutumi da ya shigo a yanzu take son ta sake gani, tana son sanin wanenen shi? Ko ba komai yau karo na farko ta ɗan ga face ɗin wani a cikin gidan, duk da tasan tabbas ba ɗan gidan bane, dan a yanayin yadda ya shigo ya nuna cewa koma wanenen ya fi ƴan gidan nan kuɗi da ji da isa, saboda idan ka lura da irin kallon da yake yi wa gidan, kallo ne na raini da kuma ƙasƙanci, kuma fuskarsa ta nuna kamar dole aka yi mashi zuwa wannan gida ba da son ransa ba, sannan idan ka kalli yanayin motocin da suka rako shi da masu tsaronsa, haɗe da motocin ƴan'sanda har guda uku zai nuna maka ba ƙaramin mutun bane, ya fisu komai da komai, kuma yana bala'in ji da kansa sosai, duba da yadda ya shanya waɗan nan shirga shirgan bodyguards ɗin suna a tsaye suna jiransa tsawon lokaci yana cikin mota, sai lokacin da ya ga dama ya fito, ko mutun ɗaya daga cikin waɗan nan ƴan'sanda da bodyguards ɗin babu wanda ya nuna alamar ya ji wani abin, alamu sun nuna cewa lallai ba yau bane farau, halinsa ne shanya mutane suna jiransa, sai dai a jirasa amma shi baya jira.

Sosai Leesharh tasa ƙwaƙwalwarta a cikin tunanin tana ƙoƙarin haɗa abin da tasan sam ba zai yi wu ba, dan wannan matashi shi ne kawai ta kalli face ɗinsa a cikinsu, shi ma ba sosai ba, ba lallai ma idan ta sake ganinsa a wani waje ta ganesa ba, amma ta dage tana ta ƙoƙarin haɗa idanun ƴan gidan, ita a yanzu da idanu da kuma murya take son ta gwada iya gane su wanene su, shiyasa take ta ƙoƙarin haɗa idanun wannan guy da bata gani da kyau ba da kuma idanun wannan matashiyar mata tare da mamarta, dan ta gane shin wannan matashi yana da alaƙa ta jini da su ko kuma bashi da shi? Leesharh kenan, akwai ƙwaƙwalwa, wani lokaci kuma akwai iya shirme da shiririta, ga yarinta da yake ratsowa ta cikin ƙwaƙwalwar tata.

Ta jima tana kallon wayar da aka bata ba tare da ta shiga cikin wayar ba, bata ma sha'awar shiga cikin wayar, saboda tasan babu komai a ciki.

Sai hidima take ji ana ta famar yi a cikin gidan, amma ita babu halin ta fita taga me ake yi, dan idan bada izinin wannan hajiya ba ko kofar ɗakin bata leƙawa baiwar Allah. Tana ƙunshe a ciki kamar daddawa!.

Tana dai ji anata kai komo tsakanin hawan kasa da sama, elevator sai zarya yake yi, amma haka ta cigaba da kwanciya shiru.

Wunin ranar dai haka ta wuni a takure, ta takure kanta da burin son fita ta leƙa me ake yi a cikin gidan, amma babu hali, haka ta wuni babu wanda ya leƙo in da take har can yamma. Kamar daga sama ta ji motsin jama'a a harabar gidan. Ai a dubu ɗari ta diro ƙasa daga saman bed ɗinta ta nufi wajen window dan taga menene?.

Wannan matashin saurayin ne zai tafi, ga mamakinta sai taga mata wajen huÉ—u ne suka rako shi wajen motarsa, ita dai tasan mata biyu kawai ta sani a cikin gidan, sai mai koya mata aiki wadda kuma tun da rana ta koma, to su kuma saura mata biyun nan daga ina? Ta tambayi kanta.

Ga wannan Hajiya da kuma ƴarta waɗan da already Leesharh ta rike kamaninsu ta yanayin idanunsu duk da suna cikin nikaf, kuma wata basira irin tata ko basu yi magana ba tana iya gane da waye take a tare ta hanyar idanunsu. Sam basu kawowa ransu cewa Leesharh zata iya yi masu wannan sani ta haka ba, a tunaninsu ai ba zata taɓa iya ganesu ba.

Kamar dai ɗazun, yana sunkuye da kansa yana kallon ƙasa ya nufi motarsa, sosai Leesharh ta baza idanu tana son kallon face ɗinsa da kyau da kyau, amma sam hakan bai samu ba, saboda yana ƙasa ita kuma tana sama, ya kuma sunkuyar da kansa ƙasa, ba halin ta gansa sosai!.

Tana ji tana gani suka bar wannan gida, sam ranta baiso haka ba, ta so dai taga wannan haÉ—aÉ—É—en guy É—in mai cike da shegen isa da izza.

Sai da ta ga tafiyar motocin nasu ne ta juyo ta koma wajen bed É—inta cike da haushi, sai kuma ta fara tambayar kanta a kan cewa kenan ko da wannan matashi ya zo basu cire nikaf É—in da yake face É—insu ba? Ko dai sun cire a cikin gida da zasu rakoshi waje ne suka sake sanyawa? WaÉ—an nan tambayoyi shi take ta jerawa kanta wadda kuma har lokacin sallar mangariba ta yi bata samu amsarsu ba.

Jiki ba kwari ta tashi ta yi sallah ta dawo ta cigaba da kwanciya tana tunanin irin rayuwar da suke son jefata a ciki, ga shi sun yi mata kashedi da kada ta yi kusa da kowa a wannan gidan aiki da zata je, sannan kuma sun ce kada ta yarda ta rinƙa sanya hijab irin nasu na Africa, a kayan da zasu saya mata ma ba za'a sayi irinsa ba, sai dai arab hijab zata sanya wanda iyakansa kirjinta ya tsaya, abin ya ɗan ɗaure mata kai da har ta fara tunanin kenan tallar jikinta zata yi wa Ramish ne ko yaya? Ta ƙasa gane komai, waɗan nan mata akwai shegu, duk sun birkita mata ƙwaƙwalwa ta yadda ta kasa iya kamo zaren bakin abu guda ɗaya a cikin waɗan nan matsaloli ta warware ta gani, anya kuwa waɗan nan mata su suke shirya wannan plan ɗin kuwa? Saboda abin ne ya wuce tunani, dole akwai sama da su, to waye? Wannan tunani Leesharh ta fara yi a cikin ranta.

Kamar a mafarki muryar babanta ya fara yi mata yawo a cikin kunnuwanta in da yake ce mata. "A'isha duk abin da zaki yi a rayuwar nan ki riƙe gaskiya da amana, in dai kika rike waɗan nan abu biyun to Allah ba zai taɓa bari ki taɓe ba, Allah zai ji ƙanki, ki tabbata baki cutar da kowa ba a rayuwarki, hakan zai sa Allah ya sanya bargon ni'imarsa ya lulluɓeki daga kowani irin cuta da ɗan adam zai yi maki, kada ki bari mutuncinki ya zube ta hanyar cutar da wani, gara maki ace mutuncinki ya zube wajen ƙoƙarin tsayar da gaskiya".

Sai gizo kalaman babanta suke yi mata a cikin kunnuwanta, gabaɗaya ta rasa madafa, hankalinta ya yi mummunar tashi gobe za'a kaita gidan aiki, ji take yi kamar ba zata iya ba, duk da wannan mata ta ce mata ba cutar da kowa zata yi ba, amma ita a jikinta tana jin cewa kamar cutar Ramish ake son yi, to amma koma cutar ce a wannan gaɓa dai bata da zaɓin da ya wuce dole ta yi wannan aiki, idan ba haka ba ita kuma zata rasa babanta wanda shi kaɗai ya rage mata a duniya. Tashin hankali, duniya ta ɗau mata zafi fa.

Cikin ƙoƙarin neman mafita da tunanin ina zata sanya ranta ne Jasrah ta ratso mata ta cikin tunaninta, daɗaɗan kalam Jasrah ta fara tunawa a in da take ce mata. "Leesharh a duk lokacin da kika rasa mafita, kika shiga damuwa, kina ganin kamar baki da mafita, kina ganin kamar komai ya lalace maki, a dai'dai wannan lokaci ki fara furta Hasbunallahu wani'imal wakil, domin babu wanda zai iya kawo maki ɗauki sai Allah, kada ki tunkari kowa da ya ya ye maki damuwarki, ki tunkari mahaliccinmu kawai ta hanyar ɗauro alwala ki yi nafila raka'a biyu tare da karanta Alqur'ani mai girma koda shafi biyu ne, zaki ji sauki sosai a ranki, domin Allah shi ne kawai mai kowa kuma mai komai, shi ne kawai zai iya fitar dake daga zafi izuwa sanyi, duk tsananin da zaki shiga kada yasa ki manta Allah".

Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, zamanta da Jasrah babban alkhari ce a gareta, ta koyar da ita abubuwa da dama. Tunano da kalamar ƴar uwar tata ne yasa ta yunƙura zata tashi ta ɗauro alwala kenan wannan matashiyar matar ta shigo cikin room ɗin bakinta a ɗauke da sallama. Tare suke da wani babban likita da yake biye da ita a baya, yana sanye cikin ƙananan kaya ya ɗaura rigarsa na likitoci a saman kayan, hannunsa na ɗauke da A box, babban mutun ne da zai iya haura shekaru 45 a duniya, farin balarabe ne tas da shi.

Leesharh matar ta nuna mashi da hannu tare da zama a saman bedside drawer tana faÉ—in. "Doctor Suhail this is the patient".

ÆŠan zaro idanu Leesharh ta yi tana tunanin ita a yaushe ta ce bata da lafiya to? Ita dai tasan lafiyarta ras, to me za'ayi mata kenan?.

"Zaki iya bamu waje". Dr Suhail ya yi maganar cikin harshen larabci.

"No Dr, ka yi aikinka kada ka damu da ni, ina son bata kulawa ne sosai". Ta faÉ—a cike da nuna mashi cewa tana kaunar Leesharh É—in sosai.

Sai kallon face ɗin Dr da yake sanye da farar face mask na likitoci a face ɗinsa Leesharh take yi. Ko kaɗan alamu basu nuna cewa waɗan nan mata suna da wata alaƙa ta jini da wannan Dr ba, saboda shi yanayin idanunsa daban da nasu, amma fa a tunanin Leesharh ne hakan.

Jinjina kai Dr ya yi tare da cewa Leesharh ta gyara kwanciyarta bari ya dubata ya kuma duba maƙogoronta me yasa maganarta baya fita sosai?......... NI KAM NA CE ANYA BA WANI ABIN ZA SU SANYA MATA BA KUWA?🤔 BAFA A YARDA DA IRIN WAƊAN NAN MUTAEN!.

Ba musu ta gyara ta kwanta, dan ma dai bata da wata zaɓin da ta wuci hakan. Alluran barci Dr ya ciro daga cikin A box ɗin ya fara haɗawa, amma kafin ya yi mata sai da ya tambayeta ya akayi maganarta bata fita sosai? Shin haka aka haifeta ne ko dai daga baya ne ta samu wannan cuta?.

Kallon wannan matar ta yi alamar tana jiran ta ji me zata ce. Cikin sanyin murya matar ta ce. "Ki saki jikinki ki bawa Dr duk wani amsar tambayar da zai yi maki, ta hakance kawai zai sa a iya yi maki magani cikin sauki, ba sai an shawahalar wani dogon bincike ba". Cikin harshen larabci ta yi maganar.

Bayani Leesharh ta fara ƙoƙarin yi masu, sai dai ga dukka alamu a tsananin razane take da maganar da ta fara yi ɗin, alamu sun nuna bata son yin maganar, in fact bala'in jin tsoron yin maganar take yi, hakan zai tabbatar maka da cewa akwai babban abu dangane da ita da take tsoron faɗarsa ga duniya, dole akwai abin da ya faru da ita a rayuwarta ta baya, baiwar daga tambayar meyasamu voice ɗinta duk ta ruɗe, ta shiga tashin hankali kamar ba ita ba.

Kasa iya yi masu bayanin ma ta yi, daga fara wa sai ta fara kuka da hawaye bibbiyu. Ganin hakan yasa wannan mata ta matso kusa da ita tare da É—an rungumota ta fara rarrashinta a kan ta yi hakuri.

Cikin kuka take faɗin. "Ni dan Allah kada ku tambayeni meya samu voice ɗina, kawai dai abin da nasani shi ne ba'a haka aka haifeni ba, last year ne ma abin ya faru da ni, kuma garwashin wuta ne silar komai, garwashin wuta ne ya shiga bakina har maƙogorona ya kona mun baki da yasa muryara bata fita, please kada ku tambayeni wani abin kuma".

(Garwashin wuta zai shiga bakin mutun da kafafunsa ne?🤔)

Ganin yadda ta ruɗe ta fita a hanyacinta daga cewa ta bada labarin abin da yafaru da muryarta ta dai'na fita yasa Dr Suhail ya fahimci lallai yarinyar nan gabaɗayanta tana under barazanar mutane ne, dole dole akwai gagarumin abin da ya faru da ita a rayuwarta ta baya wanda kuma take a ƙarƙashin barazanar kada ta yarda ta tona wannan abin da ya farun, hakan yasa da suka tambayeta ta yi wannan ruɗewa har haka, da alama kuma wannan dalili yasa ta ƙasa iya buɗe baki ta yi magana a kan mutuwar mahaifiyarta da ake ta cewa ita ta kasheta, dole wani abin ya saɓa, rayuwarta akwai abin dubawa sosai, amma kada ku ji komai, ni PRINCESS TEEMA ba zan gaji ba sai na je na leƙo masu asiri na binciko maku tarihin rayuwarta koma ta halin yaya ne, ai ba za'a barmu a baya ba, daga jin wannan abin kasan tarihin rayuwarta akwai darasi da abubuwan karuwa, dan haka dole na binciko mana dan muji komai mu kuma ƙaru..........😎

"Dr Suhail ina ganin kada ka sake yi mata wani tambayar kuma, tun da ta ce ba'a haka aka haifeta ba, kuma ta ce last year ne abin ya faru da ita sannan garwashin wuta ne ya shiga bakinta yasa voice É—in nata baya fita, ina ganin ka bata magani kawai ba sai ka sake yi mata wasu tambayoyi ba". Cewar wannan mata da take aikin gogewa Leesharh É—in hawaye.

"Tayaya zaki ce mun kada na tambayeta? Idan na bata maganin da bai yi dai'dai da ciwon nata bafa? In fact ma kin taɓa ganin garwashin wuta yana da kafa ne da zai tashi ya shiga bakin mutun haka kawai? Ke baki ga yadda ta ruɗe daga tambayarta ba, dole akwai abin da ya faru a rayuwar wannan yarinya na shekara ɗaya da ya wuce, yana da kyau mu san menene". Dr ya bata amsa.

"Dr Suhail bana son jin dogon magana, kawai kayi aikinka kada ka sake tambayarta, idan kuma ba zaka yi aikin bane sai na kira Dr Bakir na sanar da shi ya turo mun wani likitan". Ta yi maganar a gasale. Da alama ranta ya É—an sosu da jin kalaman Dr na neman son jin tarihin Leesharh, ta ga alama kamar ya ji tausayin yarinyar kuma yana son janta a jiki ya taimaka mata, shi ne ta yi saurin taka mashi birki!.

"Am sorry, bari na dubata na yi mata abin da ya dace". Ya bata amsa tare da fara gyara alluran barcin.

Da kyar Leesharh ta tsaya aka yi mata alluran. A takaice dai Dr Suhail ya dubata ya kuma yi mata abin da ya dace, sannan ya basu magunguna da zata rinƙa sha, a hankali hankali voice ɗinta zai koma normal, daga haka ya yi masu sallama ya tafi.

Ita kuma wannan matashiyar mata miƙewa tsaye ta yi tare da zubawa Leesharh dake ta faman barci idanu tana kallonta, kamar mai tunanin wani abin, kamar kuma tana ɗan jin tausayinta. Ta ɗauki a kallah 5 mins a haka kafin ta sa kai ta nufi waje.

Leesharh kuwa, babu sallar mangariba bare issha, sai barci take yi sakamakon wannan allura da aka yi mata, ba ita ta farka daga wannan barcin ba sai wuraren asuba.

A hankali ta waro idanunta da suke jajir dasu saboda barci, jikinta duk ya yi mata nauyi, da kyar ta iya miƙewa zaune, har wani irin jiri ta fara ji, kanta na sara mata, cikin matsananciyar kasala ta miƙe ta nufi cikin toilet.

Alwala ta É—auro ta zo ta yi sallar mangariba, dan a tunaninta yanzu mangariba ce, saboda taga É—an haske haske, sai take ganin kamar yammace irin an fara kiraye kirayen sallar mangaribar nan.

Baki a É—auke da sallama Auntyn tata ta shigo cikin room É—in, hannunta na a rike da akwati mai bala'in kyau da kuma wata envelope mai É—an girma. Leesharh dake zaune a saman dadduma ce ta fara binta da kallon mamaki.

A bakin bed matar ta zauna tare da faÉ—in. "A'isha idan kin idar da sallar ki zo".

Miƙewa ta yi daga kan daddumar tare da naɗeta ta mayar cikin wardrobe ɗin, sannan ta zo gaban matar ta tsugunna tana faɗin gata nan, duk jikinta ciwo yake yi mata tana son ta je ta yi wanka, dama bata yi wanka bane wai dan kada lokacin sallar mangariba ta wuce ta, kun san shi gajeran lokaci ne da shi, to a tunaninta yanzu mangariba ne ta yi sauri ta ɗauro alwala kawai da nufin idan ta yi sallah sai ta yi wanka tare da ƙara ɗauro wani alwala ta yi sallar isha.

"Tashi ki zauna a saman bed É—in". Matar ta faÉ—a.

Ba musu ta miƙe ta haye saman bed ɗin abinta.

"To A'isha, wannan akwatin kayan sakawarki da zaki yi amfani da su ne a gidan Abu Abdussalam idan kin je, akwai komai a ciki, na tabbata ba zaki buƙaci komai ba, wannan envelope ɗin kuma takardun makaranta ne a ciki, dama na gaya maki mai girma Abu Abdussalam baya ɗaukar jahilai aiki, daga irin masu diploma ne suke mashi aiki, kema ba karamar wahala muka sha ba kafin mu samu su amince su karɓeki aiki da kwalin secondary school, dan ma dai muna da hanyar da ba za'a iya kin bukatarmu bane yasa Abu Abdussalam ya yarda, dan haka ki mayar da hankali, ga takardun makaranta nasa an buga maki, nasan kin yi karatu from primary two Jss two, babanki ya gaya mana, so yanzu dai waɗan nan takardu har da result na waec ne a ciki, na primary da komai da komai yana ciki, kuma da first class kika fito, already takardunki sun kaiga mai girma Abu Abdussalam, ya gani kuma ya yarda ya shaida, yanzu zan damkamaki su a hannunki ne kawai dan wata kila watarana za'a buƙacesu a gidan, so ki ajiyesu da kyau a wajenki, sannan ki yi ƙoƙari wajen aiki cikin nuna wayewa da ilimi, kinga result ɗinki sun nuna ke first class ce mai ƙoƙari sosai, so kada ki je ki yi masu kauyanci da shirme".

Jinjina mata kai Leesharh ta yi tare da yi mata alkawarin In Sha Allah zata kula sosai. Shafa kanta matar ta yi tare da sanya mata albarka. A takaice dai haka ta kara gaya mata komai da komai tare da gaya mata wasu dabarun, sannan ta bata takardun tare da ce mata ta yi wanka ta shirya yanzu za a kaita gidan wadda zata kaita gidan Abu Abdussalam ɗin.......Tirƙashi! Wadda zata kaita gidan ma gidanta daban?.🤔

Miƙewa matar ta yi ta nufi waje, ita kuwa Leesharh toilet ta nufa, a gurguje ta yi wanka ta zo ta hau shiri, a nata tunanin fa lokacin sallar isha bata yi ba, saboda tana cikin room, bata ganin rana.

ÆŠaya daga cikin tsofaffin kayan da ta saba sakawa ta sanya, abaya ce black color mai kyau, ta gyara gashin kanta da ya sha wanki da gyara a wajen wannan mata mai koya mata aiki, ta feshe jikinta da perfume mai daÉ—in kamshi, ita da kanta tasan ta yi kyau sosai, amma sai fargaba da faÉ—uwar gaba take ta ji a ranta.

Bayan ta kammala shirinta fes ne ta nufi wajen window dan ta leƙa wajen harabar gidan. Tana yaye labule ta buɗe window me zata gani? Sai ganin rana ta yi ɓaro ɓaro, a lokacin ma karfe bakwai ta kusa. Zaro idanu waje ta yi tana mamaki, ita da take jiran lokacin sallar isha ta yi? Ashe bata san tuni asuba ma ta wuce ba.

A hanzarce ta dawo cikin room É—in tare da shinfiÉ—a dadduma ta tada sallah. Isha ta fara biya kafin ta yi asuba, tana idarwa bata kai ga yin addu'a bama sai ga wannan mata ta shigo, ta zo É—aukarta ne su tafi.

A hanzarce ta yi addu'a ta shafa tare da naɗe daddumar matar ta riƙo hannunta suka nufi waje bayan ta ɗauka mata wayarta da yake a saman bed in da ta ajiye tun daren jiya bata sake bi ta kai ba. Wasu mata guda biyu ne suka zo suka ɗauka mata akwatin kayanta izuwa harabar gidan. Sai kallonsu da mamaki take yi, ta gane masu aikin gidan ne, dan a aikin kitchen da aka koya mata tana ganinsu a kitchen ɗin suna nasu aikin suma, yanzu ita damuwarta ɗaya shi ne taga ina waɗan can hajiyoyi guda biyu da suka rako wannan matashin jiya? Tasan dai su ba ƴan aiki bane, duba da yanayin kayan jikinsu, hamshaƙai ne a gidan, to ina suke?!.

Suna tafiya wajen parking space na gida wannan mata tana yi mata bayanin aikin da aka É—auketa zata yi a gidan, ba komai bane face yin mopping na babbar parlourn gidan in da family suke haÉ—uwa su ci abinci, daga nan sai gyaran bedroom na yaran gidan, shikenan aikinta, banda wankin toilet, akwai masu wankin toilet, iya gyaran room É—in ne kawai.

Sosai ta kasa kunnuwa tana sauraron matar har suka isa wajen motar da zai É—auketa izuwa gidan wadda zata kaita gidan aikin.

Rungumarta matar ta yi tare da yi mata fatan nasara kafin ta kara karfafa mata gwiwa, sannan ta bata wayarta da ta kashe mata shi already, daga haka suka yi sallama ta shige cikin motar, wancan hajiyar mahaifiyar wannan bata ko leƙo in da suke ba. Har motarsu ya bar gidan bata kalli wannan hajiya ba, yau kwana uku kenan ma bata haɗu da wannan hajiya face to face ba, ko ina take zuwa oho mata.

A takaice dai wani dakareran gida aka sake kai Leesharh, a nan ne wani mota ya ɗauketa tare da wata hamshaƙiyar hajiya dake sanye cikin abaya tare da nikaf ita ma suka nufi gidan ABU ABDUSSALAM BIN BADEEN tare da wasu bodyguards guda biyu da suka yi masu rakiya.........

Kai tsaye unguwar.............

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

Share fisabilillahi 👏

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍

🔥CROWN OF INJUSTICE🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)

🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 12/8/2024.....✍️📚🌹

For information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E____________33🔥

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼

Kai tsaye unguwar.............EMIRATES HILLS motarsu Leesharh ta nufa........ Ku daga jin sunan arear kun san bana ƙananan kai bace ba, area ce wadda take da gamayyar kera keran haɗaɗɗun high rise building da manyan ƙasashen duniya take ji da su, duk wata ƙasa da ta amsa sunanta ƙasa to tana takama da ire iren waɗan na high rise building ɗin, gini ne wadda zaku gansa kamar da glass zallah aka yi sa, luxurious area ne dake ta farko a cikin faɗin DUBAI, babu ƙananan gine gine ko guda ɗaya a gabaɗaya arear, dukka luxurious gine gine ne na manyan shegu a ƙasar, ta ko'ina shinfiɗaɗiyar titi ne mai ji da lafiya har kofar gidaje, ga hasken lantarki ta ko'ina, tsayawa zayyana maku haɗuwar wannan area ma sam ba zai yi wu ba, domin baki ma ya yi kaɗan ya faɗesa, ga wasu mahaukatan cameras ta ko'ina dake ɗauko duk wata abu da zata gifta a wannan area, gabas da yamma kudu da arewa Cameras ne.

Wasu irin jiga jigan zaratan lafiyayyun securitys dake tsaron arear tun daga farkonta har karshenta kawai ma ya isa ya sanya hantar cikin bawa ya kaɗa, kowani security ka gani fuskar nan tasa kamar ta saniya, a tuɓune, a fusace, kamar waɗan da aka aikowa da saƙon bakar takarda ta albishir da shiga cikin wutar jahannama, sam babu annuri ko miskala zarratin a tattare da su, ga wasu shegun bindigu a hannunsu. Sai dai securitys ɗin kala kala ne, ciki akwai ƴan'sanda ma, abin ku da Defence minister, duk wata kaki a kasarsa take, dole ai kuga kaki kala kala a gidansa. Sai kai komo suke yi wasu daga cikinsu, da alama komai ƙanƙantar motsi suka ji sai sun duba.

(Ni kam nace dole waɗan can ƴan leƙen asiri na matan can su kasa iya basu information a kan gidan Abu Abdussalam bin Badeen, irin wannan tsaro dake a arear ma kawai?🤔 Ina ga gidan kuma?🤔)

Ganin waɗan nan securitys kawai sai da ya sanya hantar cikin Leesharh ya yi wani irin kaɗawa, duk da tana cikin mota amma ta tsare hanya da kallo, da alama tana son sanin tsakanin gidan da aka ɗaukota da wannan gidan ya tazararsu take, Leesharh ba dai wayo ba. Sai dai ganin waɗan nan securitys ɗin yasa ta mance duk wasu abubuwan da ta gani a hanyar zuwa dan riƙesu a matsayin yadda zata gane hanya ko watarana, ta manta komai tsabar shiga tashin hankali, sai ma da ta ji cikinta ya yi wani irin murɗawa mai bala'i zafi, nan take ta nemi nutsuwarta ta rasa, tunani ta fara yi asirinta ya tonu gata can a hannun waɗan nan dodannin securitys ɗin suna cin namar jikinta ɗanye. Ai bata san lokacin da ta kurma ihu a cikin motar ba, ta ɗauka da gaske ne ake yagar namar jikin nata.

Sai da matar ta taɓa ne ta farga ashe dai tunani ne. Wani irin wahalallen yawu ta haɗiye tare da fara yin danasani mafi muni na karɓar wannan aiki da ta yi tun daga yanzu, tun ma bata kai ga shiga cikin gidan ba ta fara yin nadamar zuwanta duniya, tunani take yi kawai ta shiga uku ta lalace! Shikenan karshenta ne ya zo, idan asirinta ya tonu a irin wannan gida ace gata an kamata a matsayinta na ƴar leƙen asiri ai shikenan ko gata namar jikinta ba zai samu na agasa shi ba, a ɗanye zasu cinyeta, yau ta shiga uku ta lalace!! Ashe su Jasrah sun yi gaskiya, sune ainahin masoyanta da suka hanata karɓar wannan aiki!.

Duk da sanyin Ac dake a cikin wannan danƙareriyar mota ita fa Leesharh zufa ce ta fara tsastsafo mata a gabaɗaya face ɗinta, kukan mutuwa a cikin zuciyarta kawai take yi, ta yi tsuru tsuru idanu sun rena fata, har buƙatar shiga toilet ta fara ji ya kamata saboda yadda cikinta yake murɗa mata ga kuma dukan uku uku da kirjinta yake yi, kunsan mara gaskiya fa shi tsoratarsa daban take da kowa!.

Sosai wannan mata ta lura da halin da Leesharh ta shiga, amma sam bata kula taba, domin kuwa tasan duk wanda zai shiga gidan Abu Abdussalam bin Badeen to fa sai ya razana makamancin haka, bare kuma ita da tazo da zallar rashin gaskiya? Ai tama yi ƙoƙari da bata saki fitsari a wando ba, leƙen asiri ta zo yi wa masu farautar ran ɗan gidan fa aka turota ta yi, tab ai kunga idan akwai abin da ya fi fitsari a wando ma yi zata yi.

Bata ma kara tsananin tsorata ba sai da ta ga sun dimfari wani katafaren luxurious High rise building wanda ya fita daban da sauran gine ginen dake arear, kuma jiga jigan securitys sun fi yawa sosai a wajen, design na ginin ma kawai abin kallo ne, ba wai gini ne da aka yi shi dogon bene kamar na yau da kullum ba, a'a shi wannan idan ka gansa sak design ɗin world, wato duniya yake, ya yi matuƙar ƙawatuwa kuma ginin ya zauna ya zanu da kyau, ya fita iya fita.

Duk ba shi bane ya ƙara ɗagawa Leesharh hankali, masu tsaron titin da zata sadaka da cikin wannan hamshakin ginin ne suka ƙara ɗaga mata hankali da har suke ƙoƙarin sanya zuciyarta ta buga. Wasu irin jiga jigan bodyguards ne waɗan da kallonsu a wajen Leesharh da sauran marasa gaskiya kai har ma da masu gaskiya waɗan da suke da karamar zuciya dai'dai yake da kallon mutuwa, fusatattun fuskokinsu kawai ya isa ya sanya mutun tsumar tsaye. Sanye suke cikin baƙaƙen kaya sidif, wasu irin shegun securitys shoes ne a kafafunsu, shi ma baki, irin waɗan nan takalmar ne da idan sun takeka da shi sai mutuwa, ga wasu uban black glass da suka zuba a ido kamar ka kurma ihu idan ka gansu, fararen larabawa ne tas waɗan da babu ɗigon baki ko kaɗan a fatarsu, dayawansu suna da dogayen gemu bakin kirin, sannan gasu da tsawo tare da cikar halitta ta jarumai.

Tun daga ɗan nesa da katafaren gate na gidan wani shirgegen bodyguard ya ɗagawa motarsu Leesharh jan wuta, alama su dakata daga in da suke kada su ƙariso, aikin wannan bodyguard ɗin kenan, idan sun san da zuwanka to wannan bodyguard zai ɗaga maka wata farar wuta dake a hannunsa jikin wata kyakkywar na'ura mai bala'in haske, to idan kaga ya ɗaga wannan farar wutar alama ce ta sun sami labarin zuwar wannan mota mai kira kaza da numberta kaza, shi ne zai ɗaga maka wutar alamar ka ƙariso bakin gate su cajeka, ba wai zaka wuce ciki bane, no, wannan farin wutar iso ake maka izuwa bakin gate, sannan wasu bodyguards ɗin su caje motarka tsab ta hanyar amfani da na'urori da komai ƙanƙantar abin zargi bata ɓoyewa, idan suka gama caje motarka tsab, sannan su baka damar wuce gate na farko izuwa na biyu, a nan ma sai ka sake tsayuwa amsa wasu tambayoyi tare kuma da a kara dubaka da kyau, sai sun tabbatar lafiya lou sannan su baka hanya ka wuce ciki izuwa katafaren parking space na gidan.

Idan kuma suka ɗaga maka jan wutar nan, to alama ce ta basu san da zuwan wannan mota ba, ba a gaya masu mota kaza mai number kaza zata zo ba, so dan haka tun kana dimfaro gate ɗin gidan zasu ɗaga maka jan wuta, idan kaki dakatawa a wajen to fa zasu sanya bindiga su harbi tayar motarka ne babu ruwansu, so is better for you da ka dakata tun wuri, in kaƙi jiki magayi.

Da yake ita wannan mata tasan da dokar gidan sanka sanka, sai ta sanya driver ya dakatar da motar. Wani irin kukan kura cikin Leesharh ya kara yi na tsoro, dan a tunaninta ko asirinta ne ya tonu, tun bata ma fara aikin ba har ta fara tunanin asirinta ya tuno, kai a gaskiya rashin gaskiya sam bai yi ba a rayuwar nan, idan baka da gaskiya a waje dai kana cikin tsaka mai wuya, fargaba da faɗuwar gaba ba zasu barka ka zauna lafiya ba, kullum kana cikin tunanin asirinka zai tonu, Allah ka rufa mana aisiri kasa mu kasance cikakkun masu gaskiya a duk in da muke, ko dan mu samu zaman lafiya da zuƙatanmu.

Wayarta matar ta ciro daga cikin jakarta mai shegen kyau da tsada. Massage ta shiga kan wani contact da aka rubuta Hajiya Babba. Gajeran rubutu ta rubuta mata tare da tura mata, sannan ta koma ta jingina da jikin kujerar motar.

Ita dai Leesharh sai haɗiyar wahalallen yawu take yi dan bushewa da wuyarta ya yi saboda tsoro, fargaba da razana yasa maƙoshinta ya bushe ta fara jin ƙishi, ga tsoro yasa bata iya haɗiyar yawun nata ma, bama ya fitowa ta nemesa ta rasa.

Almost 10 mins da tura saƙon da wannan mata ta yi sannan ne wannan bodyguard ɗin ya ɗaga masu farin wuta alamar su ƙariso ya samu saƙon zuwansu. A hanzarce wannan mata ta ce da driver ya tada mota su ƙarisa. Leesharh ƙwaƙwalwarta ya daina iya gane komai, kwata kwata ma bata san wani doka ce ta dakatar da su na tsawon mintuna goman nan ba, bata san se da izini ake nufar gidan ba, ita dai ta yi wiki wiki da ita kamar an tare ɓera a tarko.

Gaban bodyguards dake a bakin gate ta waje ma tukun nan suka paka motar nasu. Wasu ƙosassun zaratan bodyguards su biyun ne suka zo suka fara bincikar motar da wata haɗaɗɗiyar na'ura da take a hannunsu.

Kada kuso ku ji yadda kirjin Leesharh yake dukan uku uku baiwar Allah, ta sanya hannu ta dafe kirjin nata ko zata ji wani sassauci, ga fitsari da take ji kamar zai zubo mata a wando, ta rasa ina zata cusa ranta, ta datse idanunta gam wai dan kada ta kalli waɗan nan bodyguards ɗin, suna matuƙar razana ta, baiwar Allah da alama fargaba da faɗuwar gaba ne zai kasheta!.

Tsab waÉ—an nan bodyguards É—in suka gama caje motar, babu komai na barazana a cikinta.

(Ni kuwa nace basu san mutanen da suke a cikin motar sune barazanar ba, rashin sani ya fi dare duhu.)

Umarni suka basu a kan su wuce ciki. Kunna motar driver ya yi tare da nufar gate ɗin. Yana ƙarisawa dab da gate ɗin sai gata ta wangale kanta da kanta, da na'ura take aiki, babu wanda yake control ɗinta wajen buɗewa da rufewa, da zarar bodyguards sun baka izinin shiga ciki gate ɗin kuma zata buɗe maka kanta, haka aka yi setting ɗin na'urar ta.................. (Wayyo Allah ka yi mana arziki mai albarka mai amfani, har na ji na fara kamuwa da tausayin Abu Abdussalam bin Badeen🥱 tausayi fa na ce😅)

Kutsa motarsu cikin gidan suka yi, a nan Leesharh taga duniya, zantukan su Jasrah ce kawai suke yi mata yawo a kunne yadda suke bata labarin gidan Abu Abdussalam bin Badeen, ashe duk basu faÉ—a dai'dai bama, gani da ta yi a yanzu yasa ta ji su Jasrah basu san komai a dangane da gidan ba, dan makurar haÉ—uwa ne wannan gini.

Parking space na wannan gida kawai ya ci plot 5 girma, amma kuma duk girman nan nasa cike yake maƙil da luxurious cars kala kala masu zafi, kowani mota ka gani sai ka zaci sabo ne, saboda wani irin ɗaukar idanu da suke yi dan tsabta.

A can gefe driversu Leesharh ya samu ya saƙala motarsa ya yi parking ɗinta,. Da farko Leesharh tana ganin motar nasu kamar wani abi ne, sai da ta shigo parking space na Abu Abdussalam sai ta ga ashe motarsu kam banza ne ma, babu ma irinsa a cikin kerarrun motocin da suke parking space ɗin, saboda ƙarami ne.

"A'isha mu je ko?". Cewar wannan mata, ta yi maganar tare da sanya kai ta fito waje daga cikin motar, already driver ya buɗe mata mota. Gabaɗaya gidan tiles ne har harabar gidan, tiles mai mugun kyau launin sararin samaniya wato sky blue, hakan yasa ya haɗe da haske ya kara ƙawata gidan sosai da sosai. Ga haɗaɗɗun flowers masu bala'in ƙamshi da kamshinsu ya karaɗe ko'ina a harabar gidan, kamshin nasu irin mai daɗin shaƙar nan.

Duk Leesharh sai ta ji ta rai'na class ɗin matan ma gabaɗayansu, har mamaki ne ya ɗan kamata na ganin driver ya buɗewa wannan mata kofar motar, a ranta ta ce ashe ma gidan talakawa aka kai ni da farko, ina cewa ba dan dukiya zasu farauci rayuwar Ramish ba dan suna da ɗinbin dukiya, ashe ni mahaukaciya ce ban san komai ba, ashe ma talakawa ne na ƙarshe a gaban familyn Abu Abdussalam, lallai na yarda son kuɗi zai iya sawa su farauci rayuwar Ramish, wannan shi ne gaba ma da gabanta wai aljani ya taka wuta.

(Ku kuwa daga ganin irin wannan gida yakamata ku gane cewa dole Mommar Gimbiya Zunaira ta fita daban a cikin sauran matan King, nan fa gidan yayanta ne uwa É—aya uba É—aya, kuma ita ce kaÉ—ai mace a cikinsu, kunga kuwa dole su kaunace ta over, dole komai nata ya fita na daban a cikin KINGDOM OF POWER.)

Tana can tana tunane tunane sai ji ta yi an janyo hannunta tare da fito da ita daga cikin motar suka nufi ciki. Gidan bashi da wata hayaniya, ma'ana ba part part bane, a cure yake waje guda gwanin birgewa. Kai tsaye elevator suka nufa wadda zai kaisu izuwa katafaren ginin da family suke.

Leesharh an saki baki, ido hanci, kunnuwa da komai da komai ana bin ko'ina da kallo, bata wahalar da kanta wajen ɓoye kauyancinta ba, ta fito da shi fili tana morewa idanunta kallo abinta, ta ki bari kanta ya yi marfi ato, har ta manta da cewa wancan mata ta ce kada ta yarda ta nuna kauyanci, kome zata gani ta dake irin ita ƴar birnin nan, tab aiko dai ga shi nan ta saki baki tana baza kauyancinta son ranta.

Ai bata ma karasa sakin bakin nata mai gabaɗaya ba sai da suka shiga katafaren parlourn gidan, a nan ne ta fito da tsantsar kauyancinta tana ganin royal furniture dake a ciki, ta buɗe kofofin hancinta dukka tana shaƙar wani ni'imantaccen haɗaɗɗen arab air freshener dake kwantar da hankalin mai shaƙa wadda ya karaɗe gabaɗaya parlourn da kamshi, ga tsabta da sanyin Ac.

Wata hamshaƙiyar hajiya kyakkyawa fara tas ne take zaune a saman sofa mai zaman mutun biyu, babbar macece ba yarinya ba, tana sanye cikin arab jallabiya, fara tas da ita, ta yi rolling veil a kanta, yatsun hannunta na sanye da wasu shegun ring na diamond masu bala'in tsada har guda uku, ta haɗu iya haɗuwa, ta ji hutu har ta ƙoshi, da alama itace matar gidan, ga wata kyakkyawar matashiyar yarinya da take kwance a kusa da ita ta tada kai da laps ɗinta, a shekaru yarinyar ba zata wuce mate na Leesharh ɗin ba, kyakkyawa ce sosai ita ma, tana da ɗan yanayi da wannan hajiya, da alama mahaifiyarta ce, da alama ita ce ƴar Abu Abdussalam da aka ce yana da ƴaƴa maza biyu da mace ɗaya, yarinyar ma arab jallabiya launin white ne a jikinta, kanta babu ɗan'kwali, wannan kyakkyawan arab hair ɗin nata an ɗaure mata shi gida biyu kamar yadda Gimbiya Zunaira da kuma Chuchu suke yawan ɗaure nasu gashin, haka ita ma aka yi mata.

Fuska ba yabo ba fallasa ta tarbi wannan mata da ta zo da Leesharh. Saman sofa matar ta zauna, ita kuma Leesharh ta zauna a ƙasa saman wani haɗaɗɗen Turkey carpet mai bala'in laushi, har wani lumewa zaka ji kafafunka sun yi idan ka taka carpet ɗin.

Cikin girmamawa wannan mata ta ɗagawa hajiya babba gaisuwa. Cikin mutunta zuna hajiya ta amsa, da alama tana da kamala da dattaku, babu alamar walaƙanta mutane a tattare da ita duba da yadda ta karɓi su Leesharh cikin mutunci duk da tasan cewa tabbas Leesharh ƴar aiki ce, domin tun kafin Leesharh ɗin ta zo gidan tasan da hakan, kada ku manta kafin ma su zo sai an san da zuwansu an kuma san su waye su, so tasan aiki Leesharh ta zo yi, amma bata nuna irin kyama ko kyara ba, ta tarbesu da mutunci.

Sosai Leesharh ta ji jikinta ya yi sanyi na ganin yadda matar ta mutuntasu, ko ba'a gaya mata ba ta san cewa wannan mata itace hajiyar wannan aljannar duniyar bakiÉ—aya, amma ji yadda ta tarbesu kamar wasu Æ´an uwanta, duk sai ta ji jikinta ya yi la'asar da ta fara tunanin to meyasa ake son cutar da su tun da dai alamu sun nuna su É—in mutanen kirki ne?. Yarinta bai bari ta iya gane cewa yanzu ai masu kirki ake cutarwa ba, da zarar kana da kirki neman ganin bayanka ake yi, musamman idan ta haÉ—o da kana cikin siyasa, sarauta, da dai sauransu, idan ka ce zaka yi adalci ko ka yi wa al'umma hidima ai kana tsaka mai wuya a hannun abokan gaba sai dai Allah ya tsare!.

A fili ta furta Allah masani wadda sam bata san maganar ma ya fito ba, sai da ta ga hajiyar tana kallonta ne ta fahimci ashe ta yi magana.

Cike da tsoro ta yi ƙasa da kanta. Ita kuma hajiyar sai ta ce. "Turai yanaga kamar ƴar aikin namu bata da lafiya ko kuma wani abin yana damunta?".

Wani irin dum dum Leesharh ta ji gabanta ya bada bugu.

Matar da suka zo a tare É—in ne wadda Hajiya Babba ta kira da Turai ta ce. "Hajiya Babba ai dole ki ganta a birkice haka, kema kinsan duk wanda zai shigo wannan gida sai ya razana, securitys É—in nan naku masu fusatattun fuska da babu amnurin nan ba dole su birkita mutum komai jarumtarsa ba!".

Ƴar murmushi Hajiya Babba ta yi kafin ta dubi ƴar matashiyar yarinyar da ta tada kai da laps ɗinta ta ce. "Sharifat jeki ki kira mun Radia ta zo ta wuce da wannan yarinyar izuwa part na ma'aikata dan ta je ta huta, da alama akwai gajiya da firgici a tattare da ita".

Miƙewa zaune yarinyar ta yi, ɗan waro idanu waje ta yi irin mamakin nan lokacin da ta kalli Leesharh, da ƴar siririyar zazzaƙar voice ɗinta ta dubi Hajiya Babba. "Ummie she's so beautiful, Allah kyakkyawace sosai, harta kalar fatarta ya yi mun kyau".

Ƙasa da idanu Leesharh ta yi tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya, yanzu ta kara tabbatarwa da kanta waɗan nan mutane mutanen kirki ne, ji yadda yarinyar gidan ma ta karɓeta kamar ba ƴar aikinsu ce ita ba. Allah wadarar mummunar aikin da ta zo aikatawa a kansu ta fara yi, sai dai kuma bata fa da wani zaɓin da ya wuce dole ta yi wannan aiki ko zata mutu kuwa, dan mahaifinta shi ne duniyarta. Babbar magana, wlh akwai cakwakiya da tashin hankali ba kaɗan ba a wannan part ɗin!.

Sharifat kyakkyawar yarinya ce sosai, amma a rayuwarta tana kaunar kyawawan mutane, idan taga mace kyakkyawa sai ta ce su ƙullah abota, haka take yi, shiyasa take kaunar yayanta Omar, yayan gimbiya Zunaira kenan, saboda fa kyakkywa ne sosai kamar Zunaira ɗin shi ma, idan kuka gansa kamar shi ya yi kansa, ga idanun nan nasa ba'a magana, so suna mugun shiri da Sharifat sosai! Shi ma a gidan nan yake, ba'a gidan kakarsa yake zama ba, ya fi jin daɗin zama a gidan nan saboda Sharifat ɗin babbar kawarsa kenan.

"Sharifat kenan, ai haka Aisha take da kyau, sai ma ta yi make up". Cewar Turai.

Murmushi Sharifat ta saki tana faÉ—in. "Kai bari Yah Omar ya zo zan gaya mashi ankawo Æ´ar aiki kyakkyawa wadda ta fishi kyau".

Girgiza kai Hajiya Babba ta yi kafin ta ce. "Da kuwa kinci bugu a hannunsa, GUYSON É—in namu ne zaki ce wata ta fishi kyau? Kin manta me ya gaya maki na cewa babu wanda ya kaisa kyau a duniya ko? FaÉ—a mashi wata ta fisa kyau ina ga yau ko Abbunki ba zai iya kwatarki a hannunsa ba".

Ɗan turo baki ta yi tare da miƙewa ta nufi wani haɗaɗɗen curtain, yaye shi ta yi ta shige ta kofar da yake a wajen, tana tafiya tana ɗan juyowa ta kalli Leesharh, ita dai har ga Allah Leesharh ta yi mata kyau ba kaɗan ba, ga shi a tsawo ma tsawonsu zai iya zuwa ɗaya, shekaru ma haka, sai take jin dama ace Leesharh ƴar uwarta ce ta jini, kasancewar ita kaɗai ce mace a gidan, hakan baya yi mata daɗi, ƴan uwa maza kawai take da su, ita sam bata damu da kalar African skin ɗin Leesharh ɗin ba, ita dai kawai ta burgeta tunda kyakkyawa ce. (Ni kuwa na ce a'a Sharifatu baiwar Allah, ki nesanta zuciyarki da Leesharh, dan ita ɗin kyan ɗan macijine a gareku keda ƴan uwanki, cutarku tazo yi, duk da cewa ba laifinta bane, amma dai ku yi nesa da ita, kada ma ku jata a jiki, idan kuka jata a jiki ne ma zata samu damar cutar da kuɗin yadda yakamata, amma dai nayi shiru......🥱)

Shiru parlourn ya yi na tsawon lokaci, har Sharifat ta dawo daga wajen kiran Radia. A tare suka dawo da Radia É—in, tana gaba tana binta a baya. Saman sofar da ta tashi ta koma ta kwanta tare da tada kai da laps É—in Ummie É—in nata.

Ita kuma Radia a gabansu ta zo ta tsugunna, balarabiya ce ita É—in ma. Cikin girmamawa ta ce. "Ummie gani nan".

Nuna mata Leesharh da hannu Ummie ta yi tare da faÉ—in. "Ki wuce da ita part É—inku, already É—akinta is ready tun da Abbu ya gaya mun za'a kawo wata Æ´ar aiki nasa su Fadila suka gyara mata room É—inta, dan haka ki ce Fadila ta nuna maki room da suka gyara mata ki kaita can". Ta kai karshen maganar tare da dawo da kallonta a kan Leesharh.

"A'isha ko?". Ta tambayeta.

Da sauri ta gyaɗa mata kai alamar e kanta na'a ƙasa kamar wata sahabiya.

"Okey tashi kuje ta kaiki room É—inki, ki yi wanka ki kwanta ki huta, su Fadila zasu baki abinci, yau ki huta gobe sai ki fara aiki ko?". Cikin sanyin murya Ummie ta yi maganar, tana da cool voice sosai kamar yadda yanayinta ya nuna ita É—in so silent ce.

Duk maganar da suke yi cikin harshen larabci suke yinsa.

Da okey Leesharh ta amsa mata tare da yi mata godiya, sannan ta miƙe tsaye, Radia ma ta miƙe ta yi gaba Leesharh ɗin ta rufa mata baya, sai kallonsu Sharifat yarinyar kirki take yi, taga Leesharh kyakkyawa jinin Africa tamu ta gida!.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.