Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Rawanin_Zalinci_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 13 of 24
Part ɗinsa kai tsaye ya nufa, sai saƙa kalaman daddyn nasa yake yi a cikin ransa. Ƙasa ƙasa ya yi sallama kamar mai ciwon baki. Babu kowa a parlourn nasa, sai tashin kamashi da ko'ina yake yi, kai tsaye cikin room ɗinsa ya nufa.
A nan ya isko Gimbiya Chuchu ta yi kneel down sai aikin sharar kwallah take yi, har idanunta sun yi jajir saboda kuka.
A kusa da ita saman katafaren bed É—insa ya zo ya zauna tare da ajiye wayoyinsa haÉ—e da nata a gefensa. Zancen daddy nasa ne kawai yake yi mashi yawo a cikin kansa. Ji kawai ya yi zuciyarsa ta aminta da ya yi abin da daddyn nasa ya faÉ—a.
Slowly ya kai hannunsa ya ɗago haɓarta daga yadda ta sunkuyar da kai ƙasa tana ruwan hawaye. Datse idanunta gam ta yi saboda tsoron su haɗa idanu da shi.
Sai da ya ji tsikar jikinsa ya wani irin tashi na ganin face nata kawai da ya yi, a haka ma ba cikin kwayar idanun nata ya gani ba, ga shi face ɗin nata ma ya yi jaga jaga da hawaye, duk ya ɓata mata kwalliyarta.
In a low voice sosai ya furta. "Open your eyes".
Bata da zaɓin da ya wuce ta buɗe idanun nata, slowly ta warosu waje, sai dai taki yarda su kalli juna ido cikin ido, sai ta kawar da kallonta gefe guda tana mai cigaba da ruwan hawayenta suna bin gefe da gefen face ɗinta kasancewar ya ɗaga mata kanta sama.
Wani irin shock ya ji tun daga tsakiyar kansa har izuwa tafin kafafunsa, yana kallon face nata sosai a duk time ɗin da suka haɗu, amma bai taɓa jin yanayi irin na yau ba, anya ba baki uncle Abbas ya yi mashi ba kuwa? Ya tambayi kansa da kansa. Luluƙawa duniyar tunani kawai ya yi, ji yake yi har cikin ransa yana sha'awar ya yi ta kallon face nata ba gajiyawa.
Kyawawan laɓɓanta ne suka fara kerma saboda yadda ya ɗaga mata wuya sama ya fara yi mata zafi, hakan yasa ta tsananta kukan nata da take yi, shi ne dalilin ja mata kermar laɓɓan nata.
Slowly ya mayar da kallonsa a saman lips ɗin nata, yadda suke kerman nan ba ƙaramin kyau suka yi mashi ba dan mugunta, har shaiɗan yana ƙoƙarin raya mashi wani abin na daban a cikin zuciyarsa. Ganin ya fara tunanin ya yi kissing na lips ɗin tata ne yasa ya yi saurin sakar haɓar tata tare da dafe kansa da hannu ɗaya.
"Tashi ki tafi Jannat". Ya faÉ—a cikin wata iriyar murya mai kama dana mai jin barci.
Da sauri ta miƙe, ba tare da ta kalli in da yake ba ta yi saurin nufar waje. Da idanu ya bita da kallo har ta fice. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke tare da miƙewa ya kwanta a saman bed ɗin, tunanuka kala kala ne a cikin ransa wanda bai bama kowa damar sani ba.
A haka barci ta yi awon gaba da shi, ba shi ya farka ba sai da ringing ɗin wayarsa ta tashesa, cikin barci ya ji wayar tana ƙara, da kyar ya iya buɗe idanuwansa da suka yi mashi bala'in nauyi, jikinsa duk a mace, wannan barci da ya yi tun daga farkonta har izuwa ya tashi mafarkin Gimbiya Chuchu kawai ya rinƙa yi, ta tsaya mashi a rai kamar uncle Abbas ya yi mashi baki.
Da kyar ya iya laluɓar wayar tasa, ɗaukota ya yi tare da bin saman screen ɗin da kallo. Ɗan zaro idanuwansa waje ya yi lokacin da idanunsa suka sauƙa a kan time. Karfe 8:30 pm, ko sallar mangariba bai yi ba ga issha ta wuce. Shafa arab hairnsa ya yi tare da yunƙurawa zai miƙe.
Ina kasa miƙewar ya yi, duk jikinsa a mace, ga barcin yamma ga kuma mafarkin Chuchu, abin ya haɗu ya yi mashi yawa, dama kuma da tunaninta ya yi barci.
Call na biyu ne ya sake shigowa wayar tasa, dan wancan ta katse kafin ya É—auki wayar. Ganin sunan my daddy ne yake yawo a saman screen É—in yasa ya yi picking call É—in tare da kara wayar a kunnensa.
"Hello daddy". Ya faɗa cikin murya ƙasa ƙasa, dan bai wastsake ba.
Daga ɗayan ɓangaren uncle Abbas ya ce. "Barci kake yi ko my son?".
"Wlh daddy barci ne ya É—aukeni sai yanzu na farka".
"Oh ka ci abinci dai ko?". Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya amsa da no bai ci ba.
"To ka tashi ka ci abinci, amma kafin nan bani amsata na Assignment dana baka a kan Jannat".
Miƙewa zaune daga kwanciyar da yake ya yi. "Daddy i didn't feel anything ni kam, na kalli cikin idanunta ban ji komai ba". Ya faɗa yana kwaɓe fuska.
Sarai uncle Abbas yasan ba gaskiya ya gaya mashi ba, dan shi yasan wlh tun Chuchu tana ƴar shekara 5 yake daƙon sonta, idan anyi magana sai ya ce kawai sistersa ce, bayan haka babu komai, wannan soyayya ba ta yau bace, ta jima, tsohuwar zuma ce.
"Okey tashi ka ci abincin zan zo next month ai". Uncle Abbas ya faɗa, shi kwata kwata ma bai san cewa ko sallah ɗan nasa bai yi ba, yana can duniyar mafarkin babynsa, ya tashi kuma tsabar bushewar ido wai shi bai ji komai ba, bayan kuma har da mafarki, kai maza duniya.........🤔
"Okey dad take care". Ya faɗa tare da katse kiran, a hankali ya zuro kafafunsa kasan bed ɗin tare da miƙewa tsaye ya nufi toilet dan ya yi wanka tare da ɗauro alwala.
Da alama uncle Abbas yana son haÉ—a Gimbiya Chuchu da Yah Jawad aure, ga shi Mammie kuma kun ji ta dakawa Yah Jawad É—in warning a kan Chuchun, ta ce bata sonta, to ko ya zasu kare? Akwai cakwakiya babba kuwa, dan kuwa Mammie idan bata son abu babu abin da ba zata iya aikawa dan ta rabu da wannan abin ba...... Hmmm akwai rikici nan gaba ba kaÉ—an ba.
🕊ï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸ðŸ•Šï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸ðŸ•Šï¸
UAE💔😥
DUBAI HILLS ESTATES💔😥
Kai tsaye cikin wani haɗaɗɗen bedroom wannan matashiyar matar ta kai Leesharh. Tun da suka sanya kafafunsu cikin room ɗin Leesharh ta saki baki tana kallon irin dukiyar da aka narkawa wannan room ɗin, kamar room na hajiyar gidan gabaɗaya, amma a haka ace ɗakin ƴar aiki? Wai me mutanen nan suke so ne a rayuwarsu? Irin wannan uban tarin dukiya dukka kuma suke neman leƙar asirin wani, wannan ya tabbatar ba kuɗin suke yi wa ba, sai dai idan wutar ɗaukar fansa ce take ruruwa a cikin zuƙatansu, kuma da alama ba waɗan nan mata ne kawai suke shirya wannan abin ba, da alama akwai shegun manyan kai daga sama, idan kuka yi duba da yadda hajiya two seater ta kawo Leesharh kuma bata shigo cikin gidan ba ta juya tare da waɗan nan motocin, dole ita ma nata team ɗin daban, sannan suma waɗan nan motoci da alama bana wannan gida bane, suma na wani team ne na daban, abin dai akwai ɗaure kai sosai.
Ƙananun shekarun Leesharh yasa ta kasa iya gane cewa ba komai ake yi dan kuɗi ba, ba kuma komai ne kuɗi yake iya saya ba.
"Leesharh this is your room, ki je ki yi wanka, zan kawo maki kayan sakawa da abinci ki ci ki ƙoshi kin ji? Sai ki kwanta ki ɗan huta zuwa anjuma mai koya maki aiki zata zo, don't mind about what my mum said kin ji? Babu abin da zai sami daddynki, zaki koma wajensa lafiya lou, babu wani abin da zamu yi mashi, yadda kika ga kina cikin wannan room ɗin cikin daula haka shi ma yake, mun ajiye shi ne kawai a ɗaya daga cikin gidanjenmu yana cin arziki shi ma, so dan haka ki kwantar da hankalinki ki nutsu ki koyi duk abin da za'a koya maki, sannan ki yi aikin ki cikin natsuwa da iya taku ta yadda ba za'a ganeki ba, idan ma kika mayar da hankalinki two months ya yi ti yawa ki kammala mana aikinmu ki koma gida kin ji ko?".
Allah sarki yarinyata, kai kawai Leesharh ta gyaÉ—a mata alamar ta gansu da maganganunta. Juyawa matar ta yi ta fita domin ta bata waje ta yi wanka.
A hankali kamar mai tsoron taka ƙasa ta ƙarisa bakin shinfiɗaɗiyar bed ɗin ta zauna, sai buɗe hanci take yi tana shakar daddaɗar kamshin perfume ɗin dake room ɗin, tunani kala kala ne a cikin ranta, sai dai zantukan babanta ya fi yi mata yawo a cikin kanta sosai, tana kaunar baban nata sosai, musamman ma da ta zauna da Jasrah yarinya mai ilimin addini, ta koyar da ita abubuwa da dama, a nan ne ta gane cewa babanta yakamata ta so sosai ba mamanta ba, domin baban nata ya fi mamarta gaskiya.
Ta kai a kallah 30 mins a zaune a wajen tana aikin tunanin zantukan babanta dana mamar tata, lokacin da tunanin Jasrah ya ratso mata ta cikin ƙwaƙwalwa tata, nan take wasu siraran hawayen ya fara bin ƙuncinta, har ga Allah bata kawowa ranta rabuwa da Jasrah ba, sam bata taɓa yin wannan tunani ba, amma rana tsaka an rabasu, rabawa mara daɗin ji, ta tabbata yanzu haka Jasrah tana can tana ruwan hawaye, ga shi bata da wata kawa a gidan AAJ, ba kowa, yanzu haka zata yi zaman kaɗaici cikin kunci?.
Kara tsananta gudu hawayen face É—in nata ya yi, a gaskiya tana kewar Jasrah over. Dafa shoulder É—inta da aka yi ne ya fargar da ita tare da dawowa cikin hayyacinta. A hanzarce ta É—ago da dara daran idanun nata da suka yi jajir saboda kuka da damuwa.
"Leesharh baki yi wankar ba kin zauna a nan kina kuka? Kukan me kuma kike yi?". Cewar wannan matashiyar matar, hannunta na rike da wasu kaya masu shegen kyau da tsada, abaya ne da mayafinta launin brown color, ya ji stones jikinsa sosai, sai kyalli yake yi.
"Aunty ina kewar Jasrah ce, and ina son ganin babana da kuma kabarin mamata".
Zama a kusa da ita matar ta yi, cikin mutawa tare da nuna fifikon ilimi da shekaru ta fara tsara mata magana kamar haka. "Leesharhi i promise you that idan kika tsaya kika fara aikin nan da kyau, kika yi one to two weeks kina aikin na ga yadda kike tafi da komai, komai ya tafi dai'dai, idan kika mayar da hankali naga kina ƙoƙari, to na yi maki alkawari zan zo na ɗauke ki daga gidan Abu Abdussalam muje na kai ki ki kalli babanki, sannan mu wuce AAJ ki kaiwa Jasrah ɗin ziyara, idan muka dawo naga kina ƙoƙari a kan aikin sosai to duk end of the week zan rinƙa kai ki wajensu kuna ganawa".
Yadda ta yi maganar kana ji kasan kalaman karya da yaudara tare da makirci ne, amma da yake ita Leesharh ba ilimi ishasshe ne ke gareta ba, ga kuma ƙarancin shekaru, sai ta yarda da zancen, kuma da alama ta yarda da wannan mata sosai.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.