Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Rawanin_Zalinci_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 2 of 24
Cigaba da murkusoso tayi a wajen tana damke ganyayyakin dake kusa da ita, ta ciza laɓɓa gam da kyawawan fararen hakwaranta tas kamar audiga, tamkar zata fasa laɓɓan nata da hakwaran, idan cikin nata ya murɗa sai ta kara ciza laɓɓanta da karfi, Baiwar Allah, kamar laɓɓan ne suke yi mata laifi.
Haka ta yi ta fama na tsawon mintocin da a kallah zai kai arba'in zuwa hamsin, duk ta galabaita ta fita a hayyacinta, duk wasu sauran albarkatun karfi da suka rage mata sun kare, harta ciyayin da take rikewa ma yanzu ta kasa rikewa, saboda babu wani karfi da ya rage a tattare da ita, sunan Allah ma yanzu a iya zuciya kawai take iya furtawa, bakinta banda kerma tamkar wanda ciwon sanyi ya kama babu abin da yake yi, ruwan sama na cigaba da gangarowa izuwa cikin ramin, a yanzu haka yanda take zaune ruwan ya kai mata har zuwa kugunta daga zaunen.
Nakuda gadan gadan take yi, da kyar ta samu ta iya cire kayan jikinta, bata rage komai a jikin nata ba, duk ta kwaɓe komai saboda azabar wahala, Baiwar Allah sai take ganin kamar kayan ne suke kara mata zafin da wahala, duk wasu gwala-gwalai tayi wurgi da su gefe guda, ta yi ƙoƙarin ta yaga rigarta ko alkyabbar ta dan ta ɗaure cikin nata in da suka harbeta da kifiyar da kyau, amma ina ta kasa, bata da karfin iya yaga komai, haka ta daure ta hakura tare da dafe wajen kawai.
Ganin cewa kamar lokacin mutuwar tane ya yi saboda azaba yasa ta daure cikin wani irin mawuyacin hali ta fara faÉ—in.
"Ya Ubangiji na, kai kaɗai zaka taimaka mun a cikin wannan bakin azabar da nake a ciki, ya Allah dan karfin ikonka ka kawo mun ɗauki cikin gaggawa, ka saukakamun wannan nakuda cikin gaggawa, ya Allah kada ka bari na mutu ba tare da na kalli abin da zan haifa ba, ya Allah ko bayan raina kasa abin da na haifa ya zamana shi ne sanadiyar rugujewar RAWANIN ZALINCI ya tayar da RAWANIN ADALCI da aka kwantar, ya Ubangiji ko na mutu ko ban mutu ba na baka amanar abin da zan haifa, Allah ka kula mun da shi, ka raya mun shi, ya Allah ka bashi basira da kaifin kwakwalwa da tunanin da zai iya tunkarar waɗan nan azzaluman da suka zaɓi ɗaura RAWANIN ZALINCI a kansu, ya Allah ka bashi iko cika mun burina, ya Allah ka sanya mashi tsoronka da kuma aiki da abin da kace, kasa ya zamana Zaki a cikin zakuna mai ruguje ZALINCI ya kafa ADALCI tamkar jinin ABDUL MUTALLAF na hakika, ya Allah kada ka bar mahaifinsa........."
Bata kai karshen addu'ar tata ba wani irin azababben nishi ya kwace mata wanda ya sanyata dakatawa daga addu'ar nan take.
Babu wani sauran karfi da ya rage mata, dan haka nishin ma bata iya yin shi sosai ba, amma a haka take ta ƙoƙari tana fama, abin gwanin ban tausayi. Sai dai kuma abin mamaki a nan shi ne yadda take faman tana son ganin ta haihu tamkar wadda ta taɓa haihuwa, kamar ta san komai dangane da haihuwa, ga dukkan alamu wannan ba shi ne haihuwarta ta farko ba, idan ma shi ne to tabbas tana da sani sosai a wannan ɓangare, ko kuma likita ce ma.
Jim kaÉ—an ta saki wani nishi wanda ya zo mata da karfinsa, nan take baby ya faÉ—o cikin wannan ruwa, ya kuma faÉ—o duniya da kukansa na nuna alamar lafiyayyene.
Cikin sauri ta sanya hannu ta É—auke shi, dan saboda kada ruwan ya kashe mata shi. A saman kirjinta ta manna shi sai kuka yake yi, ita ma sai a lokacin ta sami damar yin kuka sosai.
Jim kaɗan bayan faɗowar baby kamar da minti ɗaya wani sabon nakuda ya taso mata gadan gadan, kankame babyn nata ta yi a saman kirjinta tana salati a cikin zuciyarta tare da ciza laɓɓa, murkusoso ta fara yi, tana wani irin numfashi mai matuƙar ban tausayi.
(Kai ko ni Princess Teema ina son sanin labarin wannan mata, kuma ina yi mata fatar Allah ya amsa mata addu'arta ta samu mai kwata mata Æ´anci kamar yadda ta buÆ™ata😠irin wannan azabar zalunci haka?ðŸ˜)
Duk kuma wannan wahala da take ciki taki sakin babyn da yake hannunta, haka ta kankame abinta gam. UWA KENAN BA WANDA ZAI IYA YIN HAKAN SAI ITA!.
A nakuda na biyu bata wani wahala sosai ba, ba ta É—auki lokaci ba shi ma sai ga nishi ya zo mata da karfi, nan take baby na biyu ma ya sake faÉ—owa, ga na farkon sai kuka yake yi mata, da faÉ—uwar baby kamar da minti É—aya sai ga mahaifa ya biyo baya.
Mahaifa na faÉ—owa kuma ta nemi duk wani ciwon kaf ta rasa, Allah ya sawwaka mata.
A hanzarce ta ɗauko ɗayan babynma ta haɗe su a saman kirjinta, sai dai baby na biyun sam bai yi kuka ba, bai kuma yi motsi ba, tamkar babu rai a jikinsa, bata damu ba, kuma bata ma lura da babayn bai yi kuka ba, saboda kukan na farkon ya toshe mata kunne kuma ya ɗaga mata hankali, dan tana tsoron kada ace waƴan nan dakarun yaki da suka biyota ɗin suna kusa su jiyo kukan jariri su zo su hallakata su karɓe mata baby's su rabasu, saukin abin ma ɗaya da akwai karan zubar ruwan sama na tashi kuma suna cikin rami, so kukan baya tashi zuwa waje sosai.
Kasancewar har lokacin ruwan gudu nan na gangarowa cikin ramin ne yasa ruwan ya kai mata har izuwa saman cikinta a yanzu. Ganin hakan ne yasa ta yi yunkurin miƙewa tare da baby's ɗin suna manne a kirjinta.
Amma ina sam ta kasa tashi, wani irin kuka ne ta ji ya zo mata, yanzu idan wannan ruwa ya cika ramin ya zasu yi? Ƴaƴanta mutuwa fa zasu yi, abin ku da jarirai mutuwarsu ba zai yi wahala ba.
Tuna cewa idan ruwan nan ya cika ramin nan baby's ɗinta mutuwa zasu yi ne yasa ta sake yin yunkurin tashi, amma ina ta kasa, kara ƙanƙame ƴaƴan nata tayi tana ambaton sunan Allah da ya kawo mata ɗauki, ruwa kuma yana ta kara cika rami, ga ruwan sama sai kara karfin zuba yake yi, walkiya da kuma tsawa ya yawaita a sararin samaniya, duniyar ta yi duhu sosai tamkar dare ne.
TO KO TA YA YA WANNAN MATA ZATA FITA DA ƳAƳAN NAN NATAâ‰ï¸
A hankali ta dawo da kallonta a kan wannan baby daketa zuba kuka tamkar makoshinsa zai ɓalle. Wasu zafafan hawayene ta ji sun fara zubo mata a saman kuncinta gwanin ban tausayi, yanzu shikenan tana ji tana gani baby's nata zasu mutu a hannunta? Ita sam bata damu da kanta ba, burinta kawai ƴaƴanta su rayu, koda kuwa ita zata mutu, dan tana da yakini da kuma sa ran Allah zai amsa mata addu'arta.
Ga baby's ɗin kuwa, jajir da su, haskensu ma irin hasken Koreans ne, dukkanninsu idanunsu a rufe gam, kyawawan gaske ne na wuce misali, dogon hancin nan sak irin na mahaifiyar tasu, wannan mai ihun ɗan bakinsa ɗan karamin, bata duba me ta haifa ba, mata ne ko maza or mace da namiji, sai hankali a kwance ake wannan, ita dai ta rungume kayanta, amma fa ba karya kyawawa gaske ne baby's ɗin, bare ma wannan mai tsallah ihun, ɗan bakinsa jajir sosai, da yake yanayin fatarsu kalar madara kalar Koreans, sai jan lips ɗin ta kara bayyana over. Ɗayan baby dai shiru har yanzu bai motsa ba, da alama dai kamar babu rai a jikinsa, shi kuma lips nasa dark purple ne mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali.
Wannan baby da bai motsa ba gashin kansa launi ne mafi tsada a duniya, wato launin white color, ba irin normal white da kuka sani ba ne, a'a na babyn ya yi wani irin gold white ne a kwance yana ɗaukar idanu, mai azababben kyau da shi, ba kasafai aka cika samun masu irin gashin a duniya ba, sai ɗaiɗaiku, ɗaiɗaikun ma sai ta can ƙasashen AREWACIN DUNIYA, ta yanki Asia ta Arewa kenan, kuma a bincike ya nuna mafiya yawan masu gold white hair nan, ba karamar baiwa da basira ke garesu ba, amma sai dai kash baby baya motsi, yaki ya motsa, babu rai a jikinsa.
ÆŠayan baby dake ta tsallah kukan kuwa, gashin kansa bakinkirin ne mai bala'in tsantsin gaske, ya yi tamkar an kifa mishi hula ne a kan nasa, tsabar bakin gashin nasa har ya yi tamkar dark blue, yana wani irin kyalli na daban, ga gashin nasu yar'yar sai tsawo ba cika, kana iya ganin farin fatar kansu, saboda rashin cikar gashin, tsawo kuma ya sauko musu har gaban goshinsu, ya kusa rufe masu idanu. A takaice dai dukkansu biyu suna da tsananin kyau na wuce misali.
A hankali hankali fa ruwan nan sai haurowa sama yake yi, yanzu ya fara taɓa mata baby's ɗin nata.
Kara haurar da su saman wajen shoulders ɗinta ta yi, tana mai cigaba da kuka tare da ambato sunan Allah da ya kawo mata ɗauki. Bata gaji ba, haka take ta kokarin miƙewa dan ta ceci ƴaƴanta, amma duk wasu gaɓoɓi na jikinta sunki yarda su bata haɗin kai wajen ta iya miƙewa, kada ku manta tana da ciwo a cikinta na kifiya da aka harbeta, ga kuma haihuwa, ai ta auna babban arziki ma da har yanzu take cikin hayyacinta, har yanzu tana karkashin kariyar Ubangiji dan shi kawai take ambata a baki da zucinta, idan kuma ka riki Allah to wlh wani abin idan Ubangiji ya hukunta a kanka, sai mutane su rinƙa kallon kamar tsafi ko asiri, saboda irin baiwar da kuma iko na mahaliccinmu, babu abin da ya fi karfin Allah a duniyar nan.
WANNAN ABIN DA SANYA MUTUN CIKIN TASHIN HANKALI YAKE...
*Masu buƙatar littafin TRIPLETS daga farko harshen su yi mun magana ta wannan number tawa, 08161390581.*
ðŸ¤PRINCESS TEEMA taku ta amana🔥
Share fisabilillahi ðŸ‘
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥ðŸ¤
ðŸ¤ðŸ”¥ð—¥ð—”ð—ªð—”ð—¡ð—œð—¡ 👑 ð—ð—”ð—Ÿð—œð—¡ð—–ð—œðŸ”¥ðŸ¤
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
🔥💔𑨠ð’•ð’ð’–ð’„ð’‰ð’Šð’ð’ˆ ð’‰ð’†ð’‚ð’“ð’•ð’” ð’ð’ð’—ð’† ð’”ð’•ð’ð’“ð’š, ð’…ð’†ð’”ð’•ð’Šð’ð’š ð’ð’ƒð’”ð’•ð’‚ð’„ð’ð’†, ð’‚ð’ð’… ð’“ð’ð’Žð’‚ð’ð’„ð’†ðŸ’”🔥
ð— ð—”ð—Ÿð—Ÿð—”ð—žð—œð—¡
â¤ï¸â€ðŸ”¥FATEEMA ZAHRA MUSA â¤ï¸â€ðŸ”¥
(â¤ï¸ð‘·ð‘¹ð‘°ð‘µð‘ªð‘¬ð‘ºð‘º ð‘»ð‘¬ð‘¬ð‘´ð‘¨ðŸ”¥)
🔥ðŸ¤T🔥ðŸ¤T🔥ðŸ¤W🔥ðŸ¤......💻
â¤ï¸ð‘«ð‘¨ð‘»ð‘¬ 30/6/2024.....âœï¸ðŸ“šðŸŒ¹
ðŸ¤ð‘ºð‘»ð‘¬ð‘· 1......âœï¸ðŸ“šðŸ”¥
اللَّهÙمَّ صَلّ٠عَلَى Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯Ù ÙˆÙŽØ¹ÙŽÙ„ÙŽÙ‰ Ø¢Ù„Ù Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯ÙØŒ كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ وَعَلَى Ø¢Ù„Ù Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ، Ø¥Ùنَّكَ ØÙŽÙ…Ùيدٌ مَجÙيدٌ، اللَّهÙمَّ بَارÙكْ عَلَى Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯Ù ÙˆÙŽØ¹ÙŽÙ„ÙŽÙ‰ Ø¢Ù„Ù Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯ÙØŒ كَمَا بَارَكْتَ عَلَى Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ وَعَلَى Ø¢Ù„Ù Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ، Ø¥Ùنَّكَ ØÙŽÙ…Ùيدٌ مَجÙيدٌâ¤ï¸
*Ga waɗan da basu sani ba, ni ina da tsayayyen lokaci na yin posting nawa, 5:30 dai'dai nake yin posting na littafina, duk wanda yake a grp nawa lokacin TRIPLETS ya sani, sai dai idan matsalar network aka samu, amma 5:30 na yamma dai'dai nake update 💘*
E____________3🔥
Tana a cikin wannan hali Allah ya aiko mata wani bawan Allah, da alama maharbine, matashin saurayi ne mai jini a jika, yana da tsawo sosai, ga faffaÉ—ar kirjinsa kamar wani zaki, jajir da shi kamar tsada, a shekaru ba zai wuce 15 years ba, dakakken namiji ne, dan daga ganin irin yanayin tsayuwar da ya yi a bakin ramin, alamu sun nuna ba rago bane, namiji ne sosai, ko da yake dama rago ba zai iya kasancewa a cikin irin wannan daji ba, duk wanda ka gani a cikinta to jarumta ta ratsa jinin jikinsa sosai!.
Yana sanye da irin takalmar nan na maharba mai kama da waterproof shoe a kafafunsa, irin kayan nan da ake saƙawa da zare da audiga ne a jikinsa, wandoce mai matuƙar kyau da aka saƙata da audiga, sakar hannu ce mai kyau, ta saƙu sosai, wandon launin brown color ce, ta sama riga ce mai karamar hannu launin white color, ita ma ta sakar ce, yana sanye da hular sanyi ta saka a kansa, hular ta kasance brown color kalar wandonsa, daga kugunsa ya ɗaura wata kyakkyawar belt launin white color kalar rigarsa, ita ma ta sakar ce.
Kayan sun yi matuƙar yi mashi kyau sosai da sosai, ga su tsab tsab, babu datti ko kaɗan, tamkar yanzu ya sakosu, kamar ba maharbi bane ba, da alama yana da matuƙar tsabta sosai, dan babu alamar kazanta, datti a jikinsa.
Kyakyawan gaske ne wannan matashi, kamar ba mutun ba kuma, jajir da shi, kalar fatarsa tamkar madara, tamkar bai taɓa fita rana ba, skin nasa har wani kyalli take yi, tamkar wadda ya girma a cikin A.c da kuma rayuwa a manya manyan jiga jigan gidajen manyan muryoyi a duniya, sam bai yi kalar wannan dajin ba ko miskala zarratin.
Yana da doguwar hanci mai matuƙar kyau, hancin nasa bata yi irin doguwa zud ɗin nan ba, ɗan dai'dai mai matuƙar ɗaukar hankali, kasancewarsa fari kal da shi, sai yasa pink lips nasa suka kara bayyana sosai, tamkar lips ɗin mace, har wani kyalli suke yi, saboda ruwan sama da ya jiƙasu, bakin nasa ɗan karami, yana da dara daran idanu farare kal kal kamar audiga, bakin cikin kwayar idanun nasa kuwa, ya yi bakin kirin da shi, irin bakin nan da zaku ga har wani kyalli yake yi, saboda ya yi baki siɗif, sexy eyes ke gare shi, yana da gashin gera mai yawa sosai, a cike suke, sai dai suna kwance luf, saboda tsantsi, ga wani bakinkirin ɗin saje ɗan dai'dai a face ɗin nasa kamar babban mutun, face ɗinsa ya kasance kamar egg face, wato fuska mai ɗan tsawo ba cancan ba, face ɗin nasa kuma tana da cika, ba'a rame yake ba, alamar ya ci ya ƙoshi, sam babu alamar yunwa a tattare da shi, daga yanayin zubin halittarsa ma sam bai yi kala da wannan dajin ba, yafi kama ne da ƴaƴan manya manyan mutane waɗan da maƙudan dukiya suke yi masu mubaya'a, hakika wannan matashin kyakkyawan gaske ne, kuma babu tsoro ko miskala zarratin a cikin waɗan nan dara daran idanuwan nasa, dan a bushe suke, zara zaran eyeslashes nasa nan a tsai tsaye suke, alamar babu tsoron da yake ji.
Yana rike da wata iriyar lema wadda babu irinta a yankin nan, ƙasashen Arewacin duniya ne suke amfani da irinta, lema ce wadda aka kerata da itace, abin gwanin ban mamaki sosai, komai na jikinsa ba irin na yau da kullum bane, sabbin kere kere ne a zamanin nan.
Yana wucewa ne yaji kukan jariri a wajen wannan ramin, shi ne ya ƙariso wajen dan ya duba, yana leƙa ramin ya gansu.
A hanzarce ya kara waro dara daran idanuwansa yana kallonta, kamar mai tsoron juyawa ya juyo a hankali yana kallon gabas da yamma gudu da arewa, abin ya bashi mamaki ne, mace da yara a cikin wannan daji kuma cikin ramin nan haka, dole ya yi waige waige ko zai ga wani abin, fuskarsa a cike fal da mamakin ganinsu.
Ko da ya jujjuya bai ga alamar mutun ko wani abin mai rai a wajen ba, hakan yasa ya dawo da kallonsa a kanta.
Duƙawa a saman gwiwowinsa ya yi tare da miƙa mata hannunsa a kan ta miƙo mashi baby's ɗin, ga ruwan sama na zuba mashi a kansa sosai, dan ganinsu yasa ya saki lemar hannun nasa ya faɗi kasa ba tare da ya lura bama, sun bashi tausayi ne ainun ga mamaki da al'ajabin abin.
Da farko taki yarda ta miƙa mashi baby's ɗin, sai da ta kalli da gaske ruwa zai cika ramin, dan izuwa yanzu ruwan ya hauro mata har izuwa kirjinta ta sama, sam ba'a iya ganin breast nata, ruwa ya rufe, hakan ne yasa ta yi hanzarin miƙa mashi wannan mai tsallara ihun.
Karɓa ya yi tare da ɗan ɗago jikinsa daga kan ramin kaɗan. Sam bai iya rike jariri ba, ga kuma cibiya a jikin babyn ba'a yanke ba. Haka ya ɗan kwantar da shi a gefe, sannan ya cire rigar jikinsa ya nannaɗo babyn a ciki, duk da rigar tasa ita ma a jike take, amma tafi babu gaskiya.
Kwantar da babyn a gefe ya yi tare da komawa ya kifa jikinsa a bakin ramin, dan ya karɓi ɗayan babyn.
Yana miƙa mata hannu ta yi maza ta miƙa mashi babyn, karɓa ya yi tare da ɗago da jikinsa, ya haɗe baby's ɗin duk ya kudundunesu a cikin rigar tasa, sannan ya mike da su tsaye daga wajen, ya rungumosu sosai a jikinsa.
Ƙasan wata katuwar bishiyar mangoro ya je ya kwantar da baby's ɗin, Allah sarki wannan baby mai tsallara ihun shi ma ya yi shiru a yanzu, da alama dama sanyin ruwan saman nan ne tasa yake wannan uban kuka haka, shi kuma ɗayan dai shiru bai motsa ba har wa yau.
Ganyen bishiyar manya manyan ya karyo tare da shunfuɗawa a ƙasa kamar katifa, sannan ya ɗaura baby's ɗin a kai, ya kuma karyo wasu ganye ya rufa masu a saman kayan nasa da ya kudundunesu.
Da sauri ya juya ya koma wajen ramin, a lokacin ita kuma matar ta yi iya ka bakin ƙoƙarinta ta maida kayanta jikinta da ta cire, ta duka tamkar mai yin ruku'e daga zaune tana ƙoƙarin laluɓar sarkokinta da sauran abubuwanta a cikin ruwan, da alama abubuwan suna da matuƙar muhimmanci sosai kasancewarsu a tattare da ita, shiyasa take ta ƙoƙarin laluɓarsu a cikin ruwan.
Yana zuwa ya yi mata magana a kan ta kawo hannunta bari ya fito da ita, ya yi maganar ce da wata harshe na daban, hakan yana nufin yana da yare a bakinsa kenan.
Ɗagowa ta yi daga sunkuyen da take, sam bata san me ya faɗa ba, saboda bata jin yarensa, kura mashi idanu kawai ta yi tana kallonsa, sai da ta ga ya miƙo mata hannunsa ne yasa ta gane abin da yake nufi kenan.
Kin miƙa mashi hannunta ta yi, saboda wani dalili nata da bata bayyana ba. Sake yi mata magana ya yi a kan ta kawo hannunta ruwan nan yana karuwa ne. Nan ma bin shi da idanu kawai ta yi, dan bata gane ko kalma ɗaya da ya faɗa ba.
Da yaga hakan, sai ya miƙe ya nufi wajen manyan itatuwa dake wajen, zabgegiyar itaciya ɗanya shakaf ya karyo, sannan ya dawo bakin ramin.
Zura mata itaciyar ya yi a cikin ramin. Ba musu ta kama itaciyar shi kuma ya ja, da kyar ya iya fitar da ita, alamu sun nuna hannunta ne bata son ya taɓa, kome dalili? Mu je dai zuwa, koma menene zamu ji.
A bakin ramin ta zauna tare da dafe cikinta tana numfashi da kyar da kyar kamar zata mutu. Tsugunnawa a kusa da ita ta gabanta ya yi yana tambayarta meyake damunta?.
Sam bata jin yaren da yake yi mata, bata gane komai ba.
Ganin bata bashi amsa bane yasa ya fahimci bata jin yarensa ne, dan haka sai ya ce mata "Are you hearing English?". Ya yi maganar a hankali, yana da sayayyar murya sosai.
Da sauri ta gyaɗa mashi kai alamar tana ji, tana ciza laɓɓanta saboda azabar da take ji.
"Okey what i said here is what's wrong with you? Is there any problem?". Ya yi maganar cikin sanyin murya sosai, kuma daga yanayinsa ya nuna shi mutun ne da sam sam bai da yawan magana, so silent yake, face nasa ta nuna ba mutun ne mai son hayaniya ba.
Da hannu ta nuna mashi cikinta dake ta faman zubar da jini.
Kai kallonsa wajen da take nuna mashi É—in ya yi. A dubu ya zaro waÉ—an nan dara daran fararen idanuwan nasa yana kallon yadda kifiyar ta soketa, sam bai lura ba time da ya jawota ta fito daga cikin ramin.
Hannu ya kai zai taɓa wajen, cikin sauri ta ɗan ja baya, hakan yasa ya ce mata to ta lallaɓa su je wajen da ya kwantar mata da yaranta, bari ya ciro ganye ya yi mata rumfa da shi, sannan sai ya kawo mata maganin kifiya.
Kasa tashi ta yi, duk wasu gaɓɓai a jikinta sunki bata haɗin kai wajen ta ɗan miƙe, duk sun galabaita, hakan yasa ta fara ja a kasan kawai. Da kyar da suɗin goshi suka isa wajen.
Tana zuwa wajen ta kwanta tare da sake dukkanin ilahirin jikinta ta bi lafiyar kasa tana mai da numfashi.
Kamar yanda ya faÉ—a, ganyayyaki dayawa haÉ—e da itacuwa ya karyo, ya zo ya yi masu rumfa kamar É—akin bukka, da alama ya jima a wannan dajin, dan ga dukkan alamu yasan duk wasu dabaru na zaman daji ta yadda wata dabba bazata cutar da mazaunan wajen ba.
Yana ƙoƙarin yi mata magana kamar saukar aradu wata zazzaƙar murya mai sautin amo mai matuƙar daɗi ta karaɗe kewayen wajen da faɗin "KAMRAN! KAMRAN where are you". Muryar ta kasance muryar mace ce mai zaƙi.
Da sauri ya wuce yana mai buÉ—e muryarsa shi ma da karfi yana faÉ—in "Here I am, one minute am coming".
Daga haka ba'a sake yin magana ba, shi ma bai sake yin magana ba ya yi maza ya kutsa ta cikin wasu dogayen bishiyoyin ɓaure dake fuskantar gabas.
Ita kuwa wannan mata tun da ta kwanta ta lumshe idanu, bata sake motsawa ba, suma baby's É—in nata basu sake motsawa ba, shi ma mai tsallara kuka É—azun ya yi shiru, da alama ya yi barci ne, ko kuma dai wani abin, amma fa É—ayan babyn nan sam bai motsa ba, da alama dai babu rai É—in ne da gaske a tattare da shi.
Haka har ruwan saman nan ya É—auke, gari ta washe, ta yi shar shar, amma har yanzu daga baby's har maman baby's babu wanda ya sake motsawa a cikinsu, shi kuma wadda ya taimaka masu, wato wadda aka kira da KAMRAN, har yanzu bai sake dawowa wajen ba, tun da ya tafi shiru kake ji.
After some hours. A hankali maman baby's É—in ta fara motsawa, gabaÉ—aya jikinta ya yi mata wani irin muguwar nauyi, da kyar ta iya waro idanuwanta da suke kunbure sun yi luhu luhu, saboda azaba da ta sha.
Tana waro idanuwanta kai tsaye sai a saman ganyayyakin da KAMRAN ya yi masu rumfa kamar bukka, a lokacin ruwan sama ta É—auke cak, gari har ta É—an fara yin haske.
A hankali tamkar mai jin tsoron wani abin ta kai hannunta É—aya a saman cikinta in da kifiyar nan ta caketa, ga mamakinta sai ta ji wajen a É—aure, tamkar an sanya abune an É—aure mata, kara waro idanuwanta sosai waje ta yi, dan ta tabbatar wa da kanta ba mafarki take yi ba.
Tabbas ba mafarki bane, magani aka sanya mata a wajen, sannan aka ɗaure mata wajen da wata farar kyakkyawar kyalle mai matukar kyan gaske, shi ma kyallen ta sakar audiga ce, kuma sakar hannu ce, kamar dai kayan jikin KAMRAN. Da yake akwai sauran jini dake fitowa kaɗan kaɗan a wajen, sai ta ɓata wannan farar kyalle da aka sanya mata, kyallen ta yi ja ta ɓaci da jinin.
Yunƙurawa ta yi domin ta mike, sai dai ina, ko motsawa ba zata iya yi ba, gabaɗaya gaɓɓan jikinta sun yi la'asar over, sun yi laushi, ga wani irin azababben ciwo da take ji a ko'ina a jikinta, mararta ma ciwo yake yi mata.
Ganin ba zata iya miƙewa bane yasa ta hakura ta kwanta shiru tare da ɗan juyo da kanta gefen da yaranta suke kwance, dan ta kalli shin a ina suke ne?.
Sun kasance ne a cikin wani ɗaki kamar bukka wanda aka saƙa shi da ganye and itace, kamar dai bukkar rugar Fulani, sai dai wannan ya sha banban da bukkar ruga, domin sakar ma ba iri ɗaya bace, wannan daban take, kwararrun masu fikira ne suka saƙa shi.
Ga wasu kwarya masu kyau da ɗaukar hankali a kusa da ita, anyiwa kwaryar zanen kwalliya mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali, baby's nata suna kudundune a cikin wani kyakkyawan towels farare kal kal da aka saƙa da audiga, ga kuma wani katon kasko irin na taɓo da ake yin nan, an cika kaskon da garwashin wuta a cikinsa, wutar ta yi jajir, hakan yasa gabaɗaya wajen ya ɗauki ɗimi, kamar ba yanzu aka gama sharara ruwan sama mai uban sanyi ba, da alama suma baby's ɗin wannan ɗimin yasa suka yi shiru suna barci, dama shi ɗayan baby already kunsan bai motsa ba tun da aka haifesu.
Daga gefen baby's ɗin kuma wasu kyawawan towels na sakar ce guda biyu da aka ajiye masu bacin wanda aka lulluɓesu da shi, sannan da alama an yi wa baby's ɗin wanka ko kuma dai an goge masu jiki, kuma an yanke masu cibiya.
To fa waye kuma ya yi masu dukka wannan hidimar?.
Da kyar ta iya motsa hannunta ta ɗan buɗe baby guda ɗaya. Kara waro idanuwanta waje sosai ta yi, mamaki ne ya lulluɓeta na ganin anyankewa babyn cibiya, ga jikinsu babu datti ko kaɗan, duk da cewa dama already ruwan sama ya taɓasu.
Zuba masu idanu ta yi da mamaki fal a cike a cikin ranta, da alama ba ita kaÉ—ai aka yi wa magani ba, har da baby's É—in aka yi wa magani, dan kuwa ga jikinsu nan duk an murje masu ganye, sun yi kore shar, ganyen magani kuma irin na cikin wannan kwarya da yake a kusa da ita É—in ne.
Jin yanda wajen yake da ɗimi duk da ruwan saman da aka yi ne yasa ta fara jujjuya idanuwanta tana bin ko'ina da kallo daga kwance, ta yi mamakin jin wannan daddaɗar ɗimin a wajen, sai dai bata iya hango kaskon wutar, saboda yana ta wajajen kafafunta ta kofar bukkar ne, kallonta ba zai iya kaiwa can ba daga kwance, sai ta miƙe.
A hankali ta lumshe idanuwanta tana mai tsananta godiyarta ga Allah a cikin zuciyarta, yau Allah ya ceceta ita da baby's É—inta, koma waye ya yi mata wannan hidima ta sanya wa ranta cewa bawan Allah ne from nowhere Allah ya aiko masu.
To bari mu kutsa cikin dajin, dan muga menene a cikinta, wata kila kafin mu dawo Maman Æ´an biyu ta kara samun sauki.
Kamar dai yadda kuka sani ne, daji ne mai matuƙar girman gaske wanda kallon iyakarsa ma ba abu bane mai yiwu wa sam sam, sannan akwai haɗari sosai a cikinsa, sai dai haɗarin ta wasu ɓangarori daga cikin dajin ne yake, ba dukka ko'ina bane, muggan namun dawan ba'a ko'ina suke zama ba, suna da ɓangarorin da suke zama a cikin dajin, already kunsa kowani dabba da irin wajen da yake yin rayuwa, ko a daji ba'a ko'ina suke zama ba, sai wajen da ya yi dai'dai da rayuwarsu.
Saman wani katafaren tsauni, a hankali wani hayaki yake tashi daga wajen, da alama akwai mutane a wajen, saboda su dai namun dawa basu shiri da wuta bare hayaki, sam basu so, basu zama ma a wajen da aka kunna wuta, sai dai idan É—auresu a wajen aka yi babu yadda zasu yi, amma basu son wuta ko ya take.
Sannu a hankali wannan yanaki yake fitowa, kuma bashi da yawa, sannan hayaki ne mai haske ba irin bakin hayakin nan ba, wannan tsauni yana nesa daga in da maman waÉ—an nan Æ´an biyun take, sai dai idan ka tsaya a samanta ka yi magana da karfi, to duk wanda yake kewayen wannan yanki zai jika, saboda dajin tana amsakuwa.
Dai'dai tsakiyar saman wannan tsauni ta gabas ta sakiya, wani jibgegen dutse ne a wajen, yana da girma da kuma faɗi, sannan yana nan tamkar kogo, dan yana da zurfi da faɗi cikinsa, daga ta cikinsa wannan hayaki yake fitowa, kofar shiga cikinsa kuwa, ɗan ƙaramin ne wanda babban abu ba zai iya shiga ba, idan ɗan Adam ya cika ƙiba sosai, to ba zai iya wucewa ta kofar ba, dan bata da girma, sannan akwai wata ƙaramar dutse mai kauri da ake rufe ɗan bakin kogon da shi, alama dai ya nuna wannan ƙaramin dutsen shi ne kofar kogon.
Tamkar gida haka cikin wannan kogon yake, an yi ciki da parlour da wani ɗaki na daban, duk kuma jinin anyisu ne da taɓo, ma'ana an gine cikin kogon, kasancewar yana da girma sosai cikin kogon, sai ya bada abin da ake so, ginin nasu kuma ya fita sosai, duk da cewa da taɓo suka yi shi, ga kuma itatuwan bambu da suka yi amfani da su wajen kawata kujerun zama na saka, tamkar gado haka suka yi kujerun zamar, ma'ana babu Head na kujerun, iya wajen zama ne kawai, haka zalika beds dake a cikin bedrooms guda biyun, dukka da itacen bambu da kuma ganyen ciyawa mai kyau aka yi su, shi ainahin gadon anyi shi da itacen, katifa kuma da ciyawan harawa, sai dai ya saƙu da kyau da kyau ba karya, ya yi matuƙar kyau kuma, an shinfiɗe bed's ɗin da bedsheet na sakar audiga ta hannu, kunsan sakar hannu da masifar kyau, ga shi bedsheet ɗin an yi mai two color, sai abin ya kawata idanuwar mai kallo sosai, ga ɗaukar hankali, wasu kyawawan smalls pillows ne jere a saman beds ɗin dukka ɗakuna biyun, suma pillows ɗin suna sanye ne a cikin rigarsu irin kalar bedsheet ɗin, sun kara kawata beds ɗin sosai.
Komai da yake a cikin wannan kogo da itacen bambu da kuma taɓo aka kyara su, tukunyaye da kaskon wuta duk na taɓo ne, da alama makyarin waɗan nan abubuwa mutun ne mai kaifin basira da ƙwaƙwalwa sosai, dan harda kwanon cin abinci da aka yi da itace, ga su cups, tamkar kowani gida dai, haka suke, harda yi wa kwanikan nasu design kala kala da wani jar kala, sun kuma yi bala'in kyau ba kaɗan ba.
Ƙasar wannan kogon kuwa ya kasance itacen bambu ne suka yi shi kamar tiles, ya kawata wajen sosai, abin da zai kara burgeku da wannan gida nasu shi ne, yadda ya kasance kowane kofar ɗaki da labulen da aka saka da audiga, very talented people's ne suke zaune a wannan waje, dan komai dake wajen basira ce ziryan ta yi aiki a kansa ba kaɗan ba, da akwai ramuka da suka ɗan huhhuda, saboda samun haske da kuma iska a cikin ƙogan, ramukan suna da yawa, amma basu da girma, kanana aka hudasu, kuma haske da iska suna shiga sosai, dan kunsan shi iska baya rena hanyar wucewa, abin kara ɗaukar hankali ma cikin wannan gida shi ne, harda dining table suke da shi a parlourn nasu, dining ɗin shi ma da itacen bambu suka yi shi, ya saku sosai, ya yi matuƙar kawata wajen sosai da sosai.
Ko'ina tsab yake tamkar babu kowa da yake amfani da wajen, sai kamshin kayan itatuwa da yake tashi a wajen.
Kwance a saman ƴar kyakkyawar bed nasa KAMRAN yake, a nasa bedroom ɗin kenan, hannunsa na rike da wani littafi mai matuƙar kyau yana karantawa, da alama littafin tarihi ne, sam ba kayan ɗazun bane a jikinsa, ya canza izuwa wasu masu kyau, suma dukka na tsakar audigan ne, still da akwai hular sanyi a kansa, kyakyawar fuskar nan tasa sai glowing take yi, tamkar ya shafa baby oil, sai ya kara wani irin kyau abinsa.
A zahiri idan ka kalle shi karatun littafin yake yi, amma kuma baÉ—ininsa ba ita yake yi ba, ya rike littafin ne kawai, hankalinsa yana can wani wajen.
"Kamran the food is ready, am waiting for you".
Wannan zazzaƙar murya ta ɗazun da ta kira shi ne time da yake wajen maman ƴan biyu, ita ce ta sake yin wannan magana a yanzu.
"Mamma am okey, I can't eat anything today". Ya faÉ—a yana É—aure fuska, tamkar Mamman tasa tana a gabansa.
A hanzarce aka yaye labulen dake kofar bedroom É—in nasa aka shigo. Kyakkyawar mace ce kyakkyawar gaske, doguwa sosai, gata Æ´ar caras cas, fara kal da ita kamar madara, launin fatarta ya banbanta da tasa sosai, saboda ta fishi haske nesa ba kusa ba, ga hanci har baka, da gani ba tambaya kasan mahaifiyarsa ce, saboda tsananin kamanceceniya da take a saman fuskokinsu, itama idanuwanta dara dara farare kal da su, sai dai ita kwayar idanuwanta ba baki irin nasa bane ba, ya É—an yi brown mai haske, sai ya yi kamar foreign tiger eyes, tana da tsananin kyau da abin da ake cewa farin jini, da ganinta ba tambaya kasan jarumace sosai, dan kuwa waÉ—an nan idanuwan nata babu alamar tsoro ko miskala zarratin a tattare da ita, macece mai kamar maza, jarumar gaske, da alama a wajenta ya gaji jarumta.
Ita ma tana sanye da doguwar riga ta saka launin white color mai matuƙar kyau.
"Kamran what are you saying? You can't eat anything today? why?".
Ta faÉ—a a ruÉ—e, tana magana dimple nata suna lotsawa, ga dimple É—in nata gwanin ban sha'awa, dan bai yi irin zurfin nan sosai ba, É—an daidai mai É—aukar hankali. Tana da sayayyar murya irin tasa, da ga ji maganarta kasan a wajenta ya gado cool voice.
"Mamma yes i can't eat anything today until you tell me the reason why you don't like people? Why you don't want me to go out? Everyday you're try to hidden our life, ni gaskiya am tied, kuma ni ina son in taimaki mutane, meyasa ke baki so? Haka last time wancan mutumin da Tiger can ta cinye, kika ki yarda mu taimaka mashi, muna ji muna gani wannan bakar damusa ta hallaka shi har lahira, why?".
Ya kai karshen maganar tare da miƙewa zaune yana mai rufe littafin da yake a hannunsa, ya ajiye a saman waɗan nan kananan pillows ɗin.
Ƙarisowa cikin ɗakin ta yi, jiki a sanyaye ta zauna a saman bed ɗin, hannu ta kai ta fara shafa lallausan kumatunsa da yake kamar ta jarirai saboda laushi.
A nutse ta fara magana. "Kamran you know that i can't do something to hot you or na takurawa rayuwarka ko? Duk abin da zan yi i can do it because of your happiness ne my son, mutane ba abin yarda bane, don't trust anyone in your life, just trust yourself only".
"Amma kuma Mamma wasu mutanen ai ba mugaye bane ba, wannan mata da na gaya maki fa wlh she's...........".
Katse mashi maganar tasa ta yi ta hanyar É—aga mashi hannu.
"Kamran! Kowani mutun da kake gani a rayuwar nan to wlh ba abin yarda bane, suffar tausayi ita ce suffa mafi haɗari a duniya, wanda kuma ni ba zan taɓa yarda da ita ba, duk wanda zai zo mun da fuskar tausayi dan na tausaya mashi, ba zan taɓa yarda da hakan ba".
"Mamma koda kuwa da gaske yake yi yana da bukatar taimakon ki?".
Ɗaure fuska sosai ta yi kafin ta ce. "Yes Kamran, ina son ka sani shi fa mugu bashi da kama, mugu yana yin galaba a kan mutun ne ta hanyar suffar tausayi, tabbas akwai masu bukatar a tausaya masu ɗin, amma kuma wake ɗaya yake ɓata gari, tabbas na tsani na ga mutun ya zo mun da suffar ban tausayi, dan haka na yanke hukunci, mu ba zamu taɓa taimakon kowa ba a rayuwarmu, mu kaɗai zamu zauna, ko da kuwa me zai faru!!".
Ta kai karshen maganar tare da miƙewa da nufin ta fice daga cikin ɗakin, da alama ranta ya ɓaci sosai, dan kuwa gabaɗaya yanayin face nata ya sauya.
Dakatar da ita ya yi ta hanyar cewa. "Mamma but why? Ki gaya mun dalilinki na ji, if the reason is so......".
Katse shi ta yi ta hanyar cewa. "Kamran ni ce nan na haifeka ba kai ka haifeni ba, babu wani dalili, bani da wata dalilin da zan ce maka ga shi da yasa bana son kowa ya raɓemu, kada ka sake jefo mun wata tambayar kuma!!".
Tana kai karshen maganar ta fice daga cikin É—akin da sauri.
Idan ransa ya yi dubu, to ya ɓaci, meyasa Mammansa take yin hakan ne? Furzar da iska mai zafi daga bakinsa ya yi yana wani huci.
Wani irin dunƙule hannunsa ya yi tare da kaiwa jikin bangon kogon dutsen wani irin naushi. Nan take hannun nasa ta fashe sosai, saboda dutsen yana da masifar karfi.
Sake kaiwa dutsen naushi a karo na biyu ya yi, kuma dukka da wannan hannu da ta fashe a karon farko, ga jini har ya fara malala, jajir jinin nasa, tamkar ba jikinsa bane ba, tamkar baya jin zafi haka ya sake kaiwa dutsen naushi a karo na uku, yana yi yana huci kamar wani kububuwa.
Da gudu Mamma ta dawo cikin É—akin, a ruÉ—e take faÉ—in. "Kamran ka fara halin nan naka ko? Ka bari mana".
Sake dunƙule hannun nasa ya yi a karo na ukun zai kai naushi wa bangon.
A dubu É—ari ta rike hannun nasa tana faÉ—in. "Ya isa haka mana".
Ƙoƙarin kwace hannun nasa ya fara yi, sai dai ina ya kasa kwacewa. Da hannu ɗaya ta rike shi, amma ya kasa kwacewa, dan Mamma fa jarumar macece ba raguwa ba, akwaita da karfi sosai.
Ganin ba zai iya kwace hannun nasa bane yasa ya yi ƙoƙarin miƙewa ya fice mata daga cikin ɗakin.
Riƙo shi ta yi da kyau tana faɗin. "Haba my son, what's all this meaning for?".
Ta yi maganar cikin sanyin murya.
Sai huci yake yi yaki ya yi magana, ga hannunsa dake ta famar malalar da jini, yatsarsa ta tsakiyar nan ma kamar ta karye ne ko dai ta samu targaÉ—e, domin kuwa gata ta kumbura suntum.
Rungumarsa Mamman ta yi tana É—an bubbuga bayansa alamar rarrashi, kamar zata yi kuka take faÉ—in.
"Kamran wai sai yaushe zaka dai'na wannan halin naka ne? Meyasa kake son ganina a cikin ɓacin rai ne? Meyasa kake damuwa da al'umma? Meyasa kullum akan jama'a muke samun saɓani da kai? Baka taɓa ɓata mun ba, baka taɓa kin bin maganata ba, baka yi mun musu, baka ce mun a'a, komai nace to kawai kake cewa, but why a wannan karon ma a kan jama'a ba zaka ce mun to ba? Why?".
Har wa lokacin bai iya ce mata ko uppan ba, bayan wannan huci da yake yi babu wani abin kuma da yake fitowa daga garesa, ya dai kwantar da kansa shiru a saman shoulder ɗinta, ya lumshe idanuwansa kamar mai jin barci, zuciyarsa ce take tafasa mashi tamkar an ɗaura dalma a wuta, hakan ce ma ta hana shi iya buɗe baki ya yi magana, wannan abin yana mugun damunsa, yana kuma taɓa mashi zuciya, meyasa Mammarsa bata son ya yi taimako? Ga shi dai tana da kyakkyawar zuciya a gare shi, amma kuma ko mutuwa a gabanta wani bare yake yi ba zata taimaka mashi ba, kuma ba zata taɓa bari shi ya taimaka mashi ba, to meyasa? Ga shi shi kuma Allah ya yi shi mutun ne mai bala'in son taimako, baya burin yaga wani bawa a cikin damuwa bai taimaka mashi ba, amma Mamma sam bata son hakan, ko zai yi taimako sai dai y yi a ɓoye kada ta sani, idan ta sani sai sun samu saɓani sosai.
Nasan zaku so jin wanenen KAMRAN, to ku kasa kunne kuji É—an kaÉ—an daga cikin labarin wanene shi.
Su dai mazauna wannan dajin ne na tsawon shekaru, kusan ma za'a ce a nan aka haifi Kamran ɗin, su biyu kawai suke yin rayuwarsu, daga shi sai Mamma, suna rayuwa ne cike da so da kaunar juna, Mamma tana bala'in kaunar ɗan nata, Mamma mace ce jaruma mai tafasasshiyar jini, bata da tsoro ko kaɗan, a shekarun baya lokacin da Kamran yake ƙarami har faɗa da damusa ta taɓa yi, Allah ya bata nasara kuma ta kashe damusar, sam bata san menene tsoro ba, bugu da kari mace ce mai magana guda ɗaya, tana da tsayawa a kan maganarta kuma, duk wuya duk daɗi baya sa Mamma ta juya baya a kan abin da ta yi niyya, abin ban mamaki tare da ban sha'awa a rayuwar tasu kuma shi ne, Mamma mace ce mai bala'in ilimi ga tarin baiwa da Allah ya yi mata, duk wasu abubuwan da yake a cikin gidan ita ta kera kayanta, a matakin karatu ko mai degree ba zai nuna mata komai ba, tana karanta da Kamran sosai, a yanzu yana matakin Ss 2 a makarantar tata da dake karantar da shi, yana da ilimi na wuce misali, ga baiwa da ya gada daga wajen Mammar tasa, sai dai kuma yafi Mamma zuciya, duk da take mace jaruma mai zuciya, to wlh ya ninkata, dan idan ransa ya ɓaci kamar yadda kuka ga ya yi yanzu, ya rinƙa buga hannunsa da jikin dutse har ya ji ciwo, to haka yake yi idan ransa ya ɓaci. Dole ce tasa yake yin hakan, domin ba yadda zai yi da Mamma, mahaifiyarsa ce, ko murya bai isa ya ɗaga mata ba, so dole idan ransa ya ɓaci ya nemi mafita, kada ya je ya haɗiyi zuciya ya mutu a banza, ga shi shi mutun ne da bai iya danne zuciyarsa ba, hakan tasa yake yin irin wannan abin na buga hannunsa da dutse ya jiwa kansa ciwo dan ya samu zuciyarsa ta yi sanyi.
(Ba wani a kusa bare ya sauke ɓacin ran a kansa😅 Mamma dai ita kaɗai ce😅 dole nan gani nan bari😅 ba yadda zai yi da ita)
A kowace safiya Mamma da Kamran suna gabatar da training na motsa jiki, a tare suke yin komai, ita ce malamarsa mai koya mashi faɗa, duk wasu dabarun yaki da salon faɗa ta koya mashi, ga shi daman kakkarfar mutun ne shi, sabon jini mai tafasa, hakan yasa Mamma take matuƙar Alfahari da shi.
Wannan shi ne kaÉ—an daga cikin tarihin Mamma da kuma Kamran. Nasan kuna da tambayoyi da dama a kansu, ni kai'na ina da waÉ—an nan tambayoyin, dan dole ne rayuwarsu akwai tambayoyi! Amma koma me, lokaci ne zai nuna mana!.
Ta jima a rungume da shi tana jiran zuciyar tasa ta ɗan yi sanyi. Ba ita ta sake shi ba har sai da ta ji ya dai'na wannan hucin, sannan ta sake shi tare da miƙewa ta nufi waje.
Jingina bayansa da jikin ƙogon dutsen ya yi yana sauke numfashi a hankali hankali.
Jim kaɗan Mamma ta dawo hannunta a ɗauke da wani kwando irin na itacen ayaba da ake sakawar nan, kwando ne mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali, ƙasashen Arewacin duniya sun fi yawan amfani da ita wajen zuba kayan miya ko kuma fruits.
A in da ta tashi ta koma ta zauna tare da riƙo hannun nasa. Wani farin audiga mai ɗan girma ta fitar daga cikin kwandon, fari tas da shi. Jinin hannun nasa ta fara goge mashi tana yi mashi sannu.
Lumshe idanuwansa ya yi kamar bai ji me ta ce ba.
Bayan ta goge jinin ne ta ɗauko wani purple abu a cikin wani ɗan ƙaramin mazubi wanda ta kyara kayanta da itace, ta yi kamar kwanon sha da marfin, gwanin birgewa, da alama Mamma likita ce.
Wani audiga ta gutsuro tare da É—an dangwalo wannan purple abin, sannan ta fara goga mashi a wajajen da hannun nasa ta farfashe. Sai sannu take ce mashi, saboda tasan abin akwai bala'in zafi sosai, amma shi kuwa yadda yake zaune tun farko, ko motsawa bai yi ba, kuma bai nuna wata alama da zata nuna cewa ya ji zafin abin ba, ya dai É—aure fuska tamau kamar hadari.
Bayan ta gama saka mashi wannan abin ne ta mayar da abin cikin kwandon, sannan ta ɗauko wani ɗan ƙaramin audiga tare da wani ganye da ta kwaɓa da wani magani, shima yana cikin wani ɗan mazubi ne wadda ta kyara kayanta.
A gefe guda kusa da ita ta ajiyesu kafin ta riko yatsar nasa da ta kunburar. Duba yatsar ta fara yi dan ta gani karayace ko gocewar ƙashi.
Ta ɗan ɗauki lokaci da a kallah zai kai 5 mins tana ɗan jujjuya yatsar kafin ta saki hannun nasa, sannan ta miƙe ta nufi waje.
Duk abin da take yi mashi yana ji har cikin ransa, amma saboda dakiya da jarumta sam bai nuna alamar kamar yasan tana taɓa shi bama.
Hannunta É—auke da wani kyakkyawan mazubin ruwa da ta kyara da itace ta dawo cikin É—akin. Ruwa mai zafi ta É—ebo a cikin wannan mazubin, sai tashin tiririn hayaki ruwan yake yi.
A kusa da shi ta zo ta ajiye ruwan kafin ta wuce wajen ajiye kayansa. Wani É—an karamin towel na sakar zare ta É—auko, fari kal towel É—in.
A in da ta tashi ta koma ta zauna tare da sake riƙo hannun nasa, sai kara kumbura hannun nasa yake yi sosai da sosai, ba karya ya bugu kam.
Ɗan dai'dai tsakiyar yatsar ta riƙo ta fara ɗan jujjuyata daga kasa kafin ta ja da karfi.
Har lokacin bai nuna wani alama ta yana jin abin da take yi ba, saboda tsabar jarumta da juriya, ya dake tamkar bai san ta rike hannun ba.
Bayan ta ja sai ta ɗauki wannan ɗan ƙaramin towel ɗin ta saka shi a cikin ruwan zafi, sai da ya ɗauki zafi sosai, ta sa hannu babu ko tsoro ta ciro towel ɗin, da zafinsa yana tiririn hayaki ta matse ruwan jikin, ko kaɗan ita ma babu alamar tsoro ko jin wani yanayi mara kyau a tattare da ita.
A saman hannun nasa ta kai towel É—in ta fara É—abba mashi wajen. Haka ta cigaba da yi har sai da wannan ruwan zafin ya yi sanyi.
Abinku da fararen fata jikin madara, nan take daga ita mai rike towel É—in da hannunta har shi da ake É—abbawa hannu dukkansu hannayensu ya yi jajir tamkar ya tara jini ne a wajen, sai dai duk da haka babu alamar kamar sun ji zafi ko wani raÉ—aÉ—i a saman face nasu.
Wani irin mai mai sanyaya ciwo ta shafa mashi. Har cikin ransa ya ji sanyi sosai, bandeji ta É—auko ta É—aure mashi hannun nasa.
Har lokacin kuma bai buɗe idanuwansa ba, yana dai ji ta gama mashi komai tsab, sannan ta miƙe tare da ɗaukar kayayyakin da ta shigo dasu dukka ta fitar da su.
Tana fita ya gyara ya kwanta a saman bed ɗin nasa tare da ɗaura hannunsa guda a saman face nasa yana tunanin maman twins ɗin nan, shi dai har ga Allah matar ta shiga ransa, kuma ya kuduri niyar koda Mamma bata so sai ya rinƙa taimakawa matar a ɓoye, dan shi yana da tausayi sosai, yana da zafin zuciya da kuma faɗa sosai kamar Mamma ɗin tasa, sai dai kuma akwai shi da tausayi da son taimakawa jama'a.
*Masu buƙatar littafin TRIPLETS daga farko harshen su yi mun magana ta wannan number tawa, 08161390581.*
ðŸ¤PRINCESS TEEMA taku ta amana🔥
Share fisabilillahi ðŸ‘
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥ðŸ¤
ðŸ¤ðŸ”¥ð—¥ð—”ð—ªð—”ð—¡ð—œð—¡ 👑 ð—ð—”ð—Ÿð—œð—¡ð—–ð—œðŸ”¥ðŸ¤
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
🔥💔𑨠ð’•ð’ð’–ð’„ð’‰ð’Šð’ð’ˆ ð’‰ð’†ð’‚ð’“ð’•ð’” ð’ð’ð’—ð’† ð’”ð’•ð’ð’“ð’š, ð’…ð’†ð’”ð’•ð’Šð’ð’š ð’ð’ƒð’”ð’•ð’‚ð’„ð’ð’†, ð’‚ð’ð’… ð’“ð’ð’Žð’‚ð’ð’„ð’†ðŸ’”🔥
ð— ð—”ð—Ÿð—Ÿð—”ð—žð—œð—¡
â¤ï¸â€ðŸ”¥FATEEMA ZAHRA MUSA â¤ï¸â€ðŸ”¥
(â¤ï¸ð‘·ð‘¹ð‘°ð‘µð‘ªð‘¬ð‘ºð‘º ð‘»ð‘¬ð‘¬ð‘´ð‘¨ðŸ”¥)
🔥ðŸ¤T🔥ðŸ¤T🔥ðŸ¤W🔥ðŸ¤......💻
â¤ï¸ð‘«ð‘¨ð‘»ð‘¬ 1/7/2024.....âœï¸ðŸ“šðŸŒ¹
ðŸ¤ð‘ºð‘»ð‘¬ð‘· 1......âœï¸ðŸ“šðŸ”¥
اللَّهÙمَّ صَلّ٠عَلَى Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯Ù ÙˆÙŽØ¹ÙŽÙ„ÙŽÙ‰ Ø¢Ù„Ù Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯ÙØŒ كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ وَعَلَى Ø¢Ù„Ù Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ، Ø¥Ùنَّكَ ØÙŽÙ…Ùيدٌ مَجÙيدٌ، اللَّهÙمَّ بَارÙكْ عَلَى Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯Ù ÙˆÙŽØ¹ÙŽÙ„ÙŽÙ‰ Ø¢Ù„Ù Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯ÙØŒ كَمَا بَارَكْتَ عَلَى Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ وَعَلَى Ø¢Ù„Ù Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ، Ø¥Ùنَّكَ ØÙŽÙ…Ùيدٌ مَجÙيدٌâ¤ï¸
E____________4🔥
*DOMIN NEMAN KARIN BAYANI KU NEMENI TA WANNAN NUMBER 08161390581*
Jim kaɗan Mamma ta dawo cikin ɗakin hannunta ɗauke da wani kyakkywar mazubi da suke zuba abinci, tamkar plastic plat haka ta kera kayanta, Mamma ba dai basira ba, daga kanta an rufe kofa, jajirtattiyar mace ce, hazika mai kaifin basira da ƙwaƙwalwa, ga tafasasshen jini na jarumta tamkar wata ƴar commander mayaka.
Sai tashin tiriri abincin nata yake yi, ya sha kayan kamshi na ganyayyaki masu inganci da karawa jiki lafiya, komai nasu fresh ne, dan komai na cikin wannan daji babu busasshen, ɗanyu ne, su corry leaf, carrots, green beans, peas, eggplant, spinach, cabbage, cucumber, tamator da dai sauransu, komai nasu fresh ne, hakan yasa abincinsu yana da matuƙar kyan gani a idanu ga kuma ɗanɗano mai daɗi a baki, akwai wani ɓangare daga cikin dajin in da Kamran ɗin yake ɗebo masu gishiri, basu da maggi, saboda kowa yasan a wannan dajin dai babu in da zasu samo maggi, amma kuma a cikin gayyayyakin da suke amfani dasu da akwai waɗan da suka fi maggi ɗanɗano mai daɗi, hakan yasa abincinsu yake da ɗanɗano na musamman, sannan dama already su basu san menene maggi ba, dan kunga a wannan daji suka taso, so ɗanɗanon da suka saba da shi tun farko, basu da wani sama da shi.
A saman katakon ta É—aura plate na abincin, da akwai wani kyakkyawar cup mai É—auke da wani irin red tea, shayi ne da ya ji gayyayyaki masu kara lafiya da inganci, ganyen shayin nasu ne yake red color tamkar ganyen shayin da jama'ar Arewacin duniya suke amfani da su. Ga wani gasasshen nama da yake ta tashin tiriri da kamshi, namar nan ta gasu sosai, dan sai da ta sanya yawuna ya tsinke.
Suna da wadatatcen nama sosai a gidan nasu, domin Kamran jarumin namiji ne sadauki kuma mafarauci, shi yake farauto masu nama duk bayan kwana biyu, sai mamma ta dafa ta kuma soya da man namar, idan tana so kuma tana iya ajiye ɗanyen ta hanyar saƙala shi a jikin wasu itatuwa wadda ta dasasu a cikin madafinta, wato in da take girki kenan, kasancewar a koda yaushe tana cikin yin girki yasa wannan nama da take ajiyewa baya yin komai, sai dai baya wuce kwana ɗaya suke yin amfani da shi, dan in ya wuce haka zai lalace.
Haƙiƙa rayuwarsu gwanin birgewa ne, musamman yadda suke da kayayyakin ci na morewa, ga fresh fruits ɗin nan kala kala, wata fruit ɗin ma sai dai ka ganta amma baka san suna ba, saboda ba a ko'ina aka cika samunta ba, mafita yawancin abubuwan da suke cikin wannan dajin, abubuwa ne da yafi yawaita ta ɓangaren Arewacin duniya, so ba'a ko'ina ake samunsu ba. Wannan cima mai kyau da suke samu ne yasa jikinsu yake da bala'in kyau, sai ka gansu kamar waɗan da suke rayuwa a wani hamshakin Daula mai cike da kayan more rayuwa, ka gansu wasu luwai luwai da su gwanin ban sha'awa.
A kusa da shi ta zo ta ajiye wannan kayan abinci da ta É—ebo kafin ta zauna a gefensa.
Cikin wannan sanyayyar muryar tasu ta fara ambatar sunansa a hankali hankali.
Kasa kasa kamar mai ciwon baki ya amsa mata ba tare da ya buÉ—e idanuwansa ko kuma ya É—ago kai ba.
"Stand up and eat your food".
Ta faɗa tana ƙoƙarin cire mashi kyakkyawar hular sakar da yake a kansa, dan ta kallah yana haɗa zufa, da alama hannun nasa ne ta fara jiƙa yasa yake wannan uban zufar, kowa dai yasan yadda gocewar ƙashi take, koba ki taɓa yi ba nasan kin taɓa jin labari, zafin bala'i ke gare shi, kawai dauriyar bala'i da taurin zuciya ce gare shi yasa bai nuna alamar kamar yana jin wani abu da ya danganci zafi ko ciwo ba.
"Mamma i can't eat anything now, i want to sleep, because am feeling sleeping".
Ya bata amsa can kasan maƙoshinsa.
Nisawa ta yi tare da miƙewa ta fice daga cikin ɗakin ba tare da ta ɗauki kayan abincin ba, ta bar mashi su a wajen, da alama kuma ranta ya ɓaci.
Fita daga cikin kogon mai gabaÉ—aya ta yi, a saman tsaunin ta zauna saman wata dutse tare da buga uban tagumi tamkar mai tunanin wani abin.
Daga yanayinta alamu sun nuna tana a cikin damuwa, dan face nata gabaɗaya ya canza, jikinta ya yi sanyi, tamkar ba ita ba, da alamu Kamran ya taɓo mata wani part da bata da buƙata ne a rayuwarta.
Ta yi nisa cikin duniyar tunanin data lula, tamkar daga sama ta ji an kwanto a saman bayanta, ya kuma zuro kyawawan fararen hannayen nan nasa ta saman wuyarta yana sauke numfashi a hankali hankali.
Shiru ta yi bata motsa ba kuma bata ce mashi ko uppan ba.
"Am so so sorry Mamma". Ya faÉ—a in a low voice.
"Sorry for what Kamran?".
Ta yi maganar tare da kai hannunta tana shafa hannayen nasa da ya zuro mata ta saman wuyar tata.
"I knew kin ji babu daÉ—i, kiyi hakuri my Mamma".
Juyowa ta yi ta rungumesa tana faÉ—in.
"Is okey my son, ni ban ji babu daÉ—i ba, kuma bana fatan wata rana ta zo wanda zaka sa naji babu daÉ—i, kai É—in É—an albarka ne, a ko'ina kake kana tare da albarkata, yanzu je ka É—auko abinci kazo mu ci".
Manna mata sumbata a lallausan kumatunta ya yi kafin ya miƙe ya nufi cikin gidan nasu, dan gidansu za'a ce tun da a nan suke rayuwarsu, kuma rayuwa ce kamar kowa suke yinta, sun fi wasu masu rayuwa a cikin gari ma jin daɗi da ƴanci, dan su babu ruwansu da hayaniya da matsalolin rayuwa na yau da kullum, kullum a cikin farinciki suke, su bama su san da akwai wasu mutane da suke rayuwa a wajen dajin ba, bare har su san da wasu matsalolin.
Ajiyar zuciya Mamma ta sauke tare da yin hamdala ga Allah subhanahu wata'ala da ya bata yaro mai biyayya irin Kamran, yana da bala'in zuciya na wuce misali, ga saurin fushi, sai dai kuma duk fushin da yake a ciki da zarar yaga Mamma a cikin ɓacin rai shi zai danne nasa fushi ya kwantar da kai da murya dan ya ganta a cikin farinciki, shi ɗin mutun ne mai tsananin son mahaifiyar tasa, bashi da burin da ya wuce ya ganta a cikin farinciki, ita ce komai nasa, ita ce duniyarsa, ta sha ɗawainiya da shi, ta sha fama da shi, ta wahala wajen renonsa, ta tsaya sayin daka tare da jajircewa wajen ganin ya samu komai na rayuwa kamar kowani yaro, ta mai da shi jarumin sadaukin, ta gina mashi rayuwarsa a kan jarumta da rashin tsoro, bai san wani abu wai shi tsoro ba kamar dai ita ma Mamma, rayuwarsu gwanin ban sha'awa abin koyi ga al'umma.
Fitowa ya sake yi hannunsa É—aya mai lafiyar na rike da kayan abinci.
A kusa da ita ya zo ya zauna tare da ajiye mata abincin a gabanta yana kallon fuskarta, while ita ma shi take kallo, kamar nace zan rabasu.
Wani irin gurnanin Tiger ne ya fara tashi daga bayan kogon nasu. Ko a jikinsu tamkar basu san da cewa Damusa ce take kuka ba, abincin kawai Mamma ta fara bawa Kamran ɗin a baki kamar wani ƙaramin yaro.
A wani irin mahaukacin gudu wani shirgegen damusa ya hauro saman dutsen, yana da girma sosai ga cikar razanarwa a tattare da shi, ƙosasshe ne mai lafiya, ganinsa kawai ya isa ya sanya bawa haɗiyar zuciya ya mutu, dan ba ƙaramin Tiger bane ba, sai wani girgiza yake yi yana jijjiga jikinsa, tamkar wanda ya taso daga barci, kunsan haka Tigers suke yi idan suka taso daga barci ko kuma suka ci suka ƙoshi, to haka suke yi.
Kai tsaye wajen Kamran É—in ya nufa, yana zuwa ya kwanta a kusa da shi yana wani zuro da harshe waje, da alamu sun saba sosai.
Hannunsa guda É—aya Kamran É—in ya É—aura a saman Tiger yana faÉ—in.
"Mamma kin ga Rocky tun jiya da ya yi fushi da ni sai yau ya dawo ko?".
Tana É—ebo mashi wani abincin ta bashi amsa da cewa.
"Kai ne baka kyautawa Rocky, shiyasa yake yawan yin fushi da kai".
BuÉ—e baki ya yi ta zuba mashi abincin da ta É—ebo É—in, a hankali ya cigaba da tauna yana faÉ—in.
"Amma kuma Mamma ai ba zai iya fushi dani mai gabaÉ—aya ya tafi ya barni ba, dole idan ya yi fushin ma sai ya sake dawowa, yanzu ma ba ga shi nan ya dawo ba, ni ai bani na je na nemosa ba, idan ya isa ya tafi mai gabaÉ—aya ya barni mana".
Girgiza kai kawai ta yi, dan tasan komai wuya komai daɗi Rocky ba zai taɓa rabuwa ba Kamran ba, saboda wani lokaci dabbobi sun fi mutane amana, yau tsawon shekaru goma shabiyar kenan tun ranar da aka haifi Kamran ɗin suke tare da Rocky, a tare suka yi wasa a wannan dajin, so tasan kome Kamran ɗin zai yi mashi ba zai taɓa rabuwa da su ba, sai dai wani ikon Allah, idan Kamran ya yi mashi ba dai'dai ba, sai ya yi fushi ya tafi, amma anjuma kaɗan zai sake dawowa abinsa, kullum suna a tare.
Kun san Damusa da Zaki daban daban suke, ita Damusa tana iya haura sama da shekaru ashirin tana rayuwa a duniya, ita kuma Zaki bata kaiwa sai wani ikon Allah, wannan zafin zuciyar nasu da wannan kukan da suke yi shi ne yake yawan kashe Zakunar, so su basu rayuwa mai tsawo sosai kamar Damusa, kun san sunfi kowace dabba zafin zuciya, to shi ne yake hallakasu basu jimawa a duniya, fatan kun gane?.
Abincin ta cigaba da bashi yana ci yana shafa jikin Rocky É—in, shi ma yana tsananin kaunar Damusan, dan yana da amana ga kuma taimakonsu da yake yi, baya barin sauran muggan namun dawa su cutar da su.
Bayan ya kammala cin abincin ya ƙoshi ne ya miƙe tsaye yana faɗin.
"Mamma am coming, I want to go to somewhere, is very close".
One thing about KAMRAN yaruka biyu kawai yake ji a rayuwarsa, daga yaren da ya yi wa maman Æ´an biyun nan magana da farko, sai kuma English, yarika biyun nan kawai ya iya.
"Kamran kada ka yi nisa fa, sannan ka dawo da wuri, dan anjuma kaÉ—an kai da Rocky zaku je ku farauto mana nama, bamu da É—anyar mama, kuma ina son gasa mana da daddare".
Jinjina mata kai kawai ya yi tare da sa kai ya wuce.
Da ɗan gudu Rocky ya rufa mashi baya. Da kallo Mamma ta bisu, tana tsananin kaunar ɗan nata, shi ne duniyarta, abin da yasa bata hana shi fita ba shi ne, tasan cewa kullum suna zuwa yawace yawacensu shi da Rocky, sai dai basu taɓa yin nisa da ita, da ta kwala mashi kira zai amsa, kun dai ga ɗazun da yake wajen Maman twins ta kira kuma ya amsa, to haka suke, baya taɓa yin nisa da ita, dan yasan bata son hakan, bata son yin nisa da shi.
Ta ɗan jima a wajen tana zaune kafin ta miƙe ta nufi cikin ƙogon nasu, dan ta je ta cigaba da yin ƴan aikace aikacenta.
Shi kuwa Kamran, kai tsaye wajen mum twins ya nufa abinsa, dan matar ta tsaya mashi a ransa, yana son ya koma ya sake dubata ita da Æ´aÆ´an nata.
Sai binsa da takun ƙatsaita Rocky yake yi, yana wani irin jijjiga jiki, irin shi ne shugaban nan.
Turus Kamran ya ja birki a lokacin da suka isa wajen da mum twins É—in take. Zallar madarar mamakice ziryar ta bayyana mashi a saman face nata, É—an zaro idanuwansa waje ya yi yana kallon wajen da kyau, gani yake kamar ba wajen bane ba.
Mamaki ya lulluɓe shi ya ƙasa gaba ya ƙasa baya, while shi kuma Rocky ya yi gaba abinsa yana son wucewa ya je ya shiga cikin bukkar.
Ganin Rockyn zai shiga ciki ne yasa shi ya É—an farfaÉ—o daga sumar mamakin da ya afka.
Da sauri ya ƙarisa ciki dan ya kara tabbatarwa da kansa abin da yake gani. Tabbas ba gizo bane, kamar yadda mum twins ta sha madarar mamakin ganin an taimaka masu an gyara masu komai, haka shi ma ya sha wannan madarar mamakin.
Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke lokacin da idanuwansa suka sauka a kan mum twins da babynta, da farko ya É—auka basu nan ne, ganin suna nan yasa ya ji wani sanyi ta ratsa shi.
Da sauri ya ƙarisa kusa da mum twins ɗin yana mai gayawa Rocky kada ya ce zai shigo cikin ɗakin nan ya ɓallah masu abubuwa, dan kofar shiga ma ta yi mashi kaɗan, idan ya ce zai shiga kaf zai karya itatuwan da aka kafa a bakin kofar, dan haka ya tsaya a waje.
Wani irin gurnani ya yi alamar bai ji daÉ—i ba, Kamran ya hana shi shigowa yaga ne a ciki.
(Ga ji mun Rocky da gulma😒 wato suma sun san gulma fa😅)
Jin motsin mutun a kanta ne yasa ta yi saurin waro fararen idanuwanta waje, dan taga wanene.
Duk da cewa É—azun da ya taimaka mata ita da baby's nata suka fita daga cikin ramin nan bata a cikin hayyacinta, amma hakan bai sa ta ji tsoron ganinsa ko makamancin haka ba, sam bata iya gane face nasa a É—azun ba, tana cikin wani hali, bata san wanene a kanta ba lokacin.
Ganin shi cikin nutsuwa da kamala sosai a tattare da shi ne yasa ta kura mashi idanu tana mai binsa da kallo.
Tsugunnawa a gabanta ya yi, cikin sanyin murya ya tambayeta wanene ya yi mata dukka wannan abin? Ko dai ita da kanta ne ta yi?.
Girgiza mashi kai ta yi alamar a'a ba ita ce ta yi ba, amma bata iya buÉ—e baki ta yi mashi magana ba.
Sake shiga cikin kogin madarar mamaki ya yi, amma sai ya daure ya kawar da mamakin nasa tare da ce mata.
"Zaki iya tashi zaune?".
Nan ma girgiza mashi kai ta yi alamar.
"In É—aga ki?".
Da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a bata buƙatar ya ɗaga ta.
Zai sake yin magana É—aya daga cikin baby's É—in nan ya fara motsi haÉ—e da kuka kaÉ—an kaÉ—an.
Kusan a tare ita da shi É—in suka kai kallonsu a kan yaran.
Wannan mai black cuiry hairn ne dai yake motsi tare da kukan.
Da sauri Kamran ɗin ya kai hannunsa ya ɗan ja towel da aka lulluɓesu zuwa kasa kaɗan, ɗan girgiza babyn ya fara yi.
Ai kuwa yana taɓa babyn kamar ya ce ya kara ihu, wage baki ya yi ya fara zunduma ihun da gasken gaske, dama already kun ga da kuka ya zo, sarki ne wajen zuba kuka, dan haka kuwa sai ya cika masu kunne da ihu.
Runtse idanuwanta gam maman nasu ta yi, har can cikin ranta take jin wannan kukan nasa, wani irin zafi zuciyarta take yi mata.
Hannu biyu Kamran yasa zai É—auki babyn, ai kuwa bai kai ga É—auka ba É—ayan baby mai golden white hair ya fara ihu shi ma.
Kasancewar daga Kamran har maman tasu basu san cewa tun da aka haife shi bai yi kuka ba, sai kukan nasa bai basu mamaki ba, sai ma rikita Kamran É—in da suka yi, ya rasa me zai yi masu, ya kuma rasa wanne zai É—auka daga cikinsu.
Allah sarki uwa da ƴaƴan, jin kukansu su dukkansu biyu yasa ta ji ba zata iya jurewa ba, ciza laɓɓanta da karfi ta yi tare da yunƙurawa dan ta miƙe zaune.
Da sauri Kamran ya juyo da kallonsa a kanta.
Wani irin wahalallen kara ta saki tare da dafa kasa da iya karfinta tana son tashi, nan take har wani irin zufar wahala ya fara tsastsafo mata, daga gani kasan tana jin azaba ba kaÉ—an ba, dama kuma ai dole ta ji azaba, suka da kifiya a ciki ai ba wasa ba, dan ma ta auna arziki ne ba kaÉ—an ba, ba dan haka ba ai da ta jima da mutuwa, kuma kunga wanda ya harbeta da kifiyar bai harbeta a in da zata cutu sosai ba, ya mata da sauki.
Kamran sarkin tausayi, duk zafin zuciyarsa akwai tausayi sosai, har cikinsa yake jin wani irin matuƙar tausayinta ya lulluɓe shi, ji yake yi kamar yasa hannu ya ɗagata, amma sam bata son ya taɓata, sanin tana gudun ya taɓata ne yasa ya hakura ya jure yana ganinta cikin wannan hali bai yi yunƙurin taimaka mata ba, ya bita da kallon cike da tausayawa fal a face nasa.
Bai kuma hanata miƙewa ɗin ba, duk da yasan tana da ciwo a cikinta, kasancewar yaga anyi mata aiki sosai a kan ciwon ne yasa sai bai hanata ba, amma kuma duk da wannan magani sosai da aka zuba mata, yana da kyau ta sami kamar kwana uku bata motsawa sosai, dan wajen ya ciko da wuri, sai dai ina, hakan sam ba zai yiwu ba, saboda yaran nan nata, da alama rigimammune number ɗaya, dan sarakan kuka ne, ita kuma ba zata iya jure jin kukan nasu ba, hakan yasa zata miƙe zaune dan ta san ta yadda za'ayi ta basu nono.
To ya Ubangiji ka sakawa iyayenmu da gidan Aljanna, ya Allah kamar yadda suke sadaukar da abubuwansu da dama masu matuƙar mahimmanci wani lokaci ma har da rayukansu a kanmu, ya Allah kasa su zamana daga cikin al'ummar da annabi zai fara ceta a ranar gobe kiyama, ka bamu ikon yi masu biyayya sau da kafa a kan dai'dai.
Da kyar da suɗin goshi ta iya tashi zaune, ta jingina bayanta da jikin itatuwan da aka haɗa masu ɗakin, tsabar azaba har wani irin jajir idanuwanta suka yi, tamkar wadda ta sha kuka na tsawon lokaci ta ƙoshi, zufa cigaba da tsastsafo mata yake yi a gefe da gefen face nata, fuskar nan tata tamkar wadda aka watsawa ruwa.
Ta datse lausasan laɓɓan bakinta gam da hakwaranta, ta kuma datse idanuwanta gam tana girgiza kai alamar azaba take ji sosai.
A hankali take sauke numfashin da yake fito mata tamkar wadda ta sha uban gudu ta ƙoshi, sai a lokacin kuma ta ji nauyin kayan jikinta ya ragu, alamar an rage mata kayan jikin nata. Tana son buɗe idanuwanta ta bi jikin nata da kallo, amma ta kasa iya buɗesu, saboda azaba, ji take yi kamar idan ta buɗe kara karuwa raɗaɗin ciwon zai yi mata.
Sosai Kamran ya yi matuƙar jinjina mata, dan kuwa ta yi namijin ƙoƙarin na wuce misali, ba kowa ne irin abu haka zai faru da shi kuma ya iya miƙe zaune a yau ba, sai wanda yake da matuƙar jarumta, da alama jaruma ce sosai ita ma, dama idan baku manta ba a baya na gaya maku da alama jarumace, da alama an sha fama da ita sosai kafin a iya kaita ƙasa.
Duk jarumta irin na Mammansa yau dai Kamran ya jinjinawa maman twins ma, bai taɓa tunanin aduniya za'a sami jaruma mai tafasasshen jini irin Mammansa ba, sai ga shi yau ya ganta duk da bata kai Mamma ba, dan ita Mamma karshe ce, jarumtarta tamkar wani sadaukin yaki haka take, macen da zata yi faɗa da Damusa ai kunga ba ta wasa bace ba!.
Su dai baby's da yake basu san halin da ake ciki ba, sai tsallara ihu suke yi abinsu, ko a jikinsu, duk sun sa Kamran ya shiga É—imuwa, ya rasa waye za rarrasa, sun rikita bawan Allah, duk da dama can ba iya rarrashin ya yi ba, yana dai kwatantawa ne, kunga shi kaÉ—ai ne a wajen Mamma, bai da kani ko kanwa bare ace yana ganin yadda Mamma take renonsu shi ma ya koya.
Da hannunta É—aya ta dafe wajen ciwon nata, É—ayar hannun nata kuma idanuwanta a datse gam ta fara yi wa Kamran É—in nuni da ya bata baby's É—in, ba halin yin magana, baki na datse gam.
A hanzarce ya ɗauko wannan mai bakin curly hair ya miƙa mata, dan yafi tsala ihu, babyn nan tamkar maƙoshinsa zai fashe, saboda iya kuka.
A karkace Kamran ya É—auko shi ya É—aura mata a saman cinyarta. Jin babyn a jikinta yasa ta sauke wani irin wahalallen nauyayyar ajiyar zuciya, alamar ta ji sanyi ya ratsa cikin zuciyarta.
Da kyar ta iya tallabo babyn ta fara kiciniyar bashi nono duk da bata da tabbacin tsabtar jikinta, ita dai burinta kawai ta shayar da su su daina wannan ihu, dan a tunaninta yunwa suke ji sosai ne yasa suke irin wannan uban ihu haka.
Shi dai Kamran yana son taimaka mata, sai dai babu hali, dan kuwa bazata taɓa yarda ya taɓa jikinta ba, sanin hakan yasa ya kawar da kansa daga kallonta ya cigaba da girgiza ɗayan babyn dan su sami saukin wannan ihun da yaran suke rera masu.
Shi kuwa Rocky ya yi kwanciyarsa a bakin kofar shigowa, sam ba haka ya so ba, ba yadda ya iya ne kawai, yana jin maganar Kamran sosai.
(Hmmm Damusa dai ki sabo ne! Duk da akwai masu amana kamar yanda yake a ko'ina akwai masu amana dana banza, Allah dai ya tsare mana su Kamran, kada wata rana Rocky ya rasa abinci ya yi ram da su😅.)
Da kyar ta iya fitar da nonon ta sakawa babyn abaki. Ai kuwa kamar jira yake yi ya fara sha babu kakkautawa, Allah sarki ashe da gaskiyarta, ashe tasan me suke yi wa kuka, uwa kenan! Babu biyunta a duniya!.
Mamaki ne ya kama Kamran sosai na ganin yadda wannan babyn ya yi shiru yana shan nono, sai a lokacin ya lura da babu wannan alkyabba ta jikin Maman twins É—in wanda kuma yasan dai ya fitar da ita daga cikin ramin nan da wannan alkyabbar a jikinta, to ko waye ya cire mata shi?.
Ya tambayi kansa da kansa. Ƴar waige waige ya fara yi ko zai ga ta in da aka ajiye mata alkyabbar tata, sai dai ina, bata babu labarinta.
Shiru ya nutsa cikin tunaninsa yana tunano a ina alkyabbar to? Waye kuma ya É—auketa?. Sai a lokacin ya tuna da cewa ba iya alkyabbar bace kawai, akwai sarka, abin hannu, da kuma É—ankunnenta na zallar madarar gold, suma ina suke? Dukka babu ko zobbe a wajen, bayan kuma shi yasan da hannunsa ya kwaso mata su daga bakin ramin ya biyota da su zuwa wannan wajen time É—in da take ja a kasa da zasu zo wajen.
Da hannunsa ya ajiye mata su a kusa da ita a lokacin yana yi mata sannu, to ina suke yanzu kuma? Abin da ban mamaki sosai gaskiya, kuma ga dukkan alamu ba wai satarsu aka yi ba, babu ma ɓarawo a wannan daji, tsawon shekaru 15 ɗin nan daga shi sai Mammansa ya sani suke rayuwa a cikin wannan dajin, sai baƙin maharba idan sun zo wucewa, sai kuma idan hanya ta kubcewa mutun ya faɗo cikin dajin, ko su maharba ba kasafai suka cika shigowa cikin wannan dajin ba, dan akwai manyan namun dawa a cikinta, idan suka yi wasa su da suka zo farauta to za'a faraucesu kamar kuda da bujumin sa, hakan yasa sam basu gigin zuwa dajin farauta, sai time to time.
Wannan dalilin yasa abin ya É—aurewa Kamran kai ya kuma bashi mamaki, to wani É—an albarkan ne kuma ya kwashi kayan maman twins? Allah masanin gaibu.
Sai da ta ji alamar barcin babyn dake a hannunta ne ta kara sauke nauyayyar ajiyar zuciya, ya sha ya ƙoshi sai barci.
A hankali ta waro idanuwanta waje, sun yi jajir da su kamar wuta, baiwar Allah fuskarta duk a kumbure kamar ba ita ba.
Zubawa babyn idanu ta yi tana mai karewa ɗan kyakkyawar face nasa kallo, ga dukkan alamu wannan baby mai golden white hair yana da matuƙar hakuri sosai, domin kuwa wannan jijjiga shi da Kamran yake yi yana ɗan bubbuga shi a hankali hankali yasa ya hakura ya yi shiru kamar babu shi a wajen, saɓanin mai black hair nan, ai shi ko jijjigawar ma baya jin ana yi, ihu kawai abinsa, da alama acici ne, sarkin cin abinci ne ba wasa!.
Hannu ta kai ta É—an buÉ—e towel É—in jikin babyn da kyar da makyarkyata, domin ta duba shin wai me ta haifa ne?.
Wani irin daddaÉ—ar ajiyar zuciya ta sauke a lokacin da ta kalli cewa macece wannan babyn dake a hannunta, wani irin daÉ—i da sanyi ta ji yana ratsata, wanda ita kaÉ—ai ta san dalilin.
Ni kuma dai na saka mata ayar tambaya? domin kuwa dole akwai wata a kasa da yasa zata ji daÉ—i tare da murnar haifar mace da ta yi, ita da take son su É—auka mata fansa? Mata dai ba iya É—aukar fansa zasu yi ba, to ko me dalilinta na murnar samu É—iya mace? Ina da tambaya, amma lokaci ne zai amsa mana waÉ—an nan tambayoyin.
Ganin tana murna da samun É—iya macece yasa shi ma Kamran É—in ya ce bari ya duba babyn dake a wajensa ya gani.
Yana dubawa sai yaga ita É—in ma macen ce, ajiyar zuciya ya sauke tare da dawo da kallonsa a kan mamar tasu yana mamakin irin uban annuri da farinciki da ya bayyana a saman fuskartar daga ganin ta haifi mace ko ace mata, duk sai kansa ta kulle bawa Allah.
A dai'dai wannan gaɓar ni PRINCESS TEEMA nasan na jijjige teburin dayawa daga cikin makaranta wannan littafin mai albarka, some that are sayin this twin's it's all boy's how far?. And also some that are saying it's boy and girl greeting from this side..........🥳😅🥱
Dawo da kallonta a kan Kamran ɗin ta yi, tana son ta ce mashi ya ɗauke mata wannan babyn tun da ta yi barci ya bata ɗayar ta shayar da ita, amma ta kasa iya yi mashi magana, domin juriya ce kawai irin tata yasa ta iya miƙewa ma.
Ganin tana ta kallon shi babu ko kyafta idanu ne yasa ya fahimci lallai da akwai abin da take son gaya mashi, kada ku manta yana da kaifin ƙwaƙwalwa kamar Mammansa.
Ɗan zuba mata idanu shi ma ya yi, a nan ne ya fahimci ga abin da take da buƙata wadda ta kasa gaya mashi ya yi mata. Hakan yasa ya kai hannu cikin nutsuwa ya ɗauki babyn yana bin fuskar yarinyar da kallo, kyakkyawar gaske ce kamar ita ta yi kanta.
A in da ya ɗaukota da farko ya mayar da ita ya kwantar kafin ya ɗauko baiwar Allah sarkin hakurin nan ya ɗaurawa maman ita a saman cinyarta, sai kallon fuskar yaran yake yi, dukkansu idanuwansu a rufe, ita ma mai black hair har ta gama zuba ihunta bata buɗe idanu ba, suna a rufe take wannan zunduma ihun, har ta sha nono ta ƙoshi ta yi barci da haka.
Bawan Allah Kamran, shi ma sai zogi hannunsa da ya ji ciwon nan yake yi mashi, amma haka ya daure ya jure.
Ita ma wannan baby ana bata nonon ta yi maza ta capke ta fara sha kamar ba gobe, bayin Allah yunwa ce ta yi masu yawa.
ÆŠago kai maman twins É—in ta yi tare da dawo da kallonta a kan Kamran É—in, tana son ta tambaye shi waye shi? Me yakawo shi nan?, amma ba halin iya buÉ—e baki ta yi magana, dan wani irin azababben nauyi ma harshenta ya yi mata, ko motsa shi bata iya yi bare ta yi magana.
Shi ma Kamran É—in a nasa bangaren yana son ya tambayeta wacece ita? Me kuma ya kawota wannan bakin daji mai haÉ—arin? Amma ina, shima sai ya ji harshensa ta yi mashi nauyin da ya kasa iya tambayarta, sai dai ya bisu da kallo kawai.
Kukan da Rocky ya yi mai É—an sauti ne yasa dukkansu suka mayar da kallonsu izuwa bakin kofar shigowa.
A takaice Kamran ya ce da Rocky ka gama kukanka dai ba zanzo ba, yau ba wani yawon da zamu je, muna tashi daga nan gida zan koma.
Ya yi maganar ne da wannan yaren nasa, da alama yafi yawan magana da wannan yaren, domin tafi zama sosai a bakinsa.
Sam Maman twins bata ji me ya faÉ—awa Damusar ba, dan bata jin wannan yaren, sai dai jin ya yi magana da wannan yaren ne yasa tunanin abin da ya faru É—azun a baya ya faÉ—o mata.
Shiru ta yi tana tunanin tabbas ta ji irin wannan yaren É—azun ya daki dodan kunnenta, amma bata iya tuna wanenen ya yi magana da yaren kuma a ina aka yi maganar ba, ta dai san ta ji wannan yaren É—azun.
Ganin yadda ta lula duniyar tunani ne yasa Kamran ya fara bubbuÉ—e kwaryayyakin da suke a rufe a gefenta, dan yaga menene a ciki, da farko duk a zatonsa abinci ne a ciki, sai da ya buÉ—e yaga ashe magungunar gargajiya ne a cike a ciki.
Mamaki ne ya kama shi, wanene ya kawo waɗan nan magunguna? Ya dai san wannan ba na Mammansa bace, domin haɗin maganin Mammansa ba irin wannan bane, kuma yasan ita Mamma wlh ba zata zo nan ba, ita fa a gaban idanunta bakar Damusa ta hallaka wani bawan Allah da hanya ta kwace mashi ya shigo cikin dajin, Kamran ɗin yana kuka yana su taimaki mutumin, amma Mamma taki yarda su taimaka mashi, a gaban idanunta ya mutu ko a jikinta, so ita ba zata taɓa yin taimako ba a cewarta, sam ba ita ta kawo waɗan nan abubuwa ba, bama su yi kama da nata ba, to waye ya kawosu?.
Dole Kamran ya tambayi kansa dan dai yasan su kaÉ—ai ne a cikin wannan daji.
Ni ma dai dole na shiga ruÉ—ani kuma na tambayi kai'na, waye ya yi wannan aikin dukkan?. To koma wani É—an albarka ne ko wace Æ´ar albarka ce lokaci zai nuna mana ita ko shi.
Ganin lodin magunguna ne a ciki yasa Kamran ɗin ya miƙe tsaye dan ya je ya samowa maman twins ɗin abin da zata ci, saboda ko ba'a gaya mashi ba yasan tana jin yunwa sosai.
*Masu buƙatar littafin TRIPLETS daga farko harshen su yi mun magana ta wannan number tawa, 08161390581.*
ðŸ¤PRINCESS TEEMA taku ta amana🔥
Share fisabilillahi ðŸ‘
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥ðŸ¤
ðŸ¤ðŸ”¥ð—¥ð—”ð—ªð—”ð—¡ð—œð—¡ 👑 ð—ð—”ð—Ÿð—œð—¡ð—–ð—œðŸ”¥ðŸ¤
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
ð— ð—”ð—Ÿð—Ÿð—”ð—žð—œð—¡
â¤ï¸â€ðŸ”¥FATEEMA ZAHRA MUSA â¤ï¸â€ðŸ”¥
(â¤ï¸ð‘·ð‘¹ð‘°ð‘µð‘ªð‘¬ð‘ºð‘º ð‘»ð‘¬ð‘¬ð‘´ð‘¨ðŸ”¥)
🔥ðŸ¤T🔥ðŸ¤T🔥ðŸ¤W🔥ðŸ¤......💻
â¤ï¸ð‘«ð‘¨ð‘»ð‘¬ 2/7/2024.....âœï¸ðŸ“šðŸŒ¹
ðŸ¤ð‘ºð‘»ð‘¬ð‘· 1......âœï¸ðŸ“šðŸ”¥
اللَّهÙمَّ صَلّ٠عَلَى Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯Ù ÙˆÙŽØ¹ÙŽÙ„ÙŽÙ‰ Ø¢Ù„Ù Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯ÙØŒ كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ وَعَلَى Ø¢Ù„Ù Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ، Ø¥Ùنَّكَ ØÙŽÙ…Ùيدٌ مَجÙيدٌ، اللَّهÙمَّ بَارÙكْ عَلَى Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯Ù ÙˆÙŽØ¹ÙŽÙ„ÙŽÙ‰ Ø¢Ù„Ù Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯ÙØŒ كَمَا بَارَكْتَ عَلَى Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ وَعَلَى Ø¢Ù„Ù Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ، Ø¥Ùنَّكَ ØÙŽÙ…Ùيدٌ مَجÙيدٌâ¤ï¸
*Labarin RAWANIN ZALINCI labari ne a kan sarauta dake tafe da Zalinci, cin amana, tauye hakki, walaƙanci, zanba cikin aminci, ku dama daga jin sunan RAWANIN ZALINCI kun san batu ake a kan sarauta mai tsuma zuciya da gabaɗaya ilahirin gangan jiki, soyayya mai cike da bahagon kuma makauniyar kalubale tattare da kaddarori, fata na dai kada ku yi sauri, ku daure ku bi komai sannu a hankali har mu kai in da kuke da buƙata, duk wanda yake da wata tambaya ko wata magana dangane da littafina RAWANIN ZALINCI, to kai tsaye ya mun magana, 08161390581 my contact, ni ce mai littafi, a wajena zaku sami duk wasu amsoshinku da kuke da buƙata. And lastly duk wanda labarin RAWANIN ZALINCI ta taɓo yarensu, al'adarsu, da sauransu, to ya mun afuwa, akasi ne*
E____________5🔥
Ganin lodin magunguna ne a ciki yasa Kamran ɗin ya miƙe tsaye dan ya je ya samowa maman twins ɗin abin da zata ci, saboda ko ba'a gaya mashi ba yasan tana jin yunwa sosai.
Waje ya nufa. Da kallo ta bishi, tana son ta yi mashi magana, amma ba hali, dan bata da bakin iya yin magana, sai kawai ta bishi da idanu har ya kurewa ganinta.
Ajiyar zuciya ta sauke kafin nan ta dawo da kallonta a kan baby's ɗin nata, har cikin ranta take jin tsananin kaunar yaran nan, tana kuma godewa Allah dayasa ƴaƴa mata ta haifa, da alama ta fi buƙatar mata sosai.
Shi kuwa Kamran, yana fita gida ya koma, ya yi sa'a Mamma tana wanka, a hankali ya lallaɓa ya shiga cikin wajen da take girki, shi kuma Rocky yana tsaye a waje yana jiransa, dan ba zai iya shiga cikin ƙogon ba, kofar ta yi mashi kaɗan, idan baku manta ba dama na gaya maku kofar karama ce sosai, bazaku haɗa jikin mutun da Damusa ba, shi Kamran zai iya shiga, amma Rocky ba zai iya ba.
Kayan cima da mamma ta girma lodi ya É—ebo a cikin kwaninan cin abincin nasu, ya haÉ—a duk abin da yake ganin ya dace mashi, cikin sauri ya É—auka ya nufi waje.
Kai tsaye wajen maman twins ya koma. Mamma kuwa, tana fitowa daga wanka ta fahimci ya shigo cikin ƙogon, sahun kafarsa ta gani, kada ku manta gari ne na damina.
Shiru ta yi tana mamakin yadda aka yi yau Kamran ya shigo cikin sanÉ—a ya kuma sake fita, abin ya bata mamaki, tunani take yi a kan anya kuwa ba zata bi bayansa dan taga me yake yi ba?.
Tunawa da abin da ya faru a tsakaninsu ɗazun na ya ce mata ta taimaki wata mata ta ce ahir ba zata taimaka ba, tuna hakan yasa ta girgiza kai tana mai ciza laɓɓanta, alamar abin bai yi mata daɗi ba. Hakiƙa Mamma tana da wata ɓoyayyiyar baiwa, domin rashin tsoron nan nata da wannan uban jarumtar tata dole akwai ayar tambaya, tabbas ana samun mata marasa tsoro, amma kamar Mamma haka dole a dasa mata ayar tambaya, ita ɗin ba mace bace kamar sauran mata, akwai dai wata a ƙasa, lokaci shi ne alkalin komai.
Cikin É—akin maman twins ya sake komawa, a kusa da ita ya zauna tare da ajiye mata kayan abincin. BuÉ—e kwano É—aya ya yi, wani irin gasasshen nama ne mai matukar kyau a ido, ga kamshi da yake tashi, namar shaniyar daji ce, da alama Mamma bata jima da gama kasawa ba, dan akwai É—umi a jikinta sosai, ta sha kayan kamshi irinsu curry leaf da sauransu, duk wanda ya ga namar nan sai yawunsa ta tsinke.
Ita kanta maman twins sai da ta ji yawunta ya tsinke da ganin namar, sai dai bata jin kamar zata iya cin wani abin, bakin ta babu É—anÉ—ano ko kaÉ—an.
Cikin harshen turanci ya sanar da ita cewa ga abinci ya kawo mata ta ci mana.
Da kallo kawai ta bishi shi da abincin nasa ba tare da ta motsa koda laɓɓan bakinta ba.
Ganin sai kallonsa take yi taki ta yi magana ne yasa ya miƙe tsaye yana gaya mata zai tafi, amma zai dawo anjuma da yamma can.
Kai kawai ta gyaÉ—a mashi alamar to ta ji.
Daga haka bai sake yin magana ba yasa kai ya fice abinsa.
Yana fita Rocky ya rufa mashi baya, gida suka nufa, dan ya san in dai Mamma ta fito daga wanka sai ta fahimci ya shigo cikin wannan ƙogon, zata gane sarai, hakan yasa ya yi saurin komawa, saboda kada ta biyo bayansa, ƙarami ne daga cikin aikinta ta biyo shi ta ce bari ta je taga me yake yi, ba yau bane farau wajen biyo bayansa da take yi idan ya fita, in kuma ta zo ta tarar da ga abin da yake yi na taimako, to wlh suna ina samun gagarumin matsala a tsakaninsu, kamar yadda ta tsani ranar mutuwarta, haka ta tsani ta ga Kamran ya raɓi wasu, ko kuma wasu sun raɓesu, shiyasa bata son ya fita, bata kauna ko kaɗan, ita ko maharban da suke wucewa time to time ma sam bata son Kamran ɗin ya ce masu ko sannu. To fah, Mamman akwai matsala babba in kuwa haka ne, da alama dai akwai wani gagarumin al'amari dan gane dake a ƙasa.
Ni kam ina da tambaya sosai a kan Mamma gaskiya, lamarinta akwai ban mamaki, nasan kuma my people kuna da tambayoyi a kanta dayawa, to ku adana tambayoyinku, lokaci zai bamu amsoshinmu.
Yana komawa ya wuce cikin É—akinsa ya kwanta, zuciyarsa cike fal da tunani iri iri a kan maman twins, yana son sanin wacece ita? Me ya kawota wannan waje?. Da wannan tunani a ran nasa barci ya yi awon gaba da shi.
Mamma ta jima a tsaya tana kare mashi kallo ba tare da ya sani ba, tun shigowarsa cikin É—akin ta biyo bayansa, sai dai bata shigo ciki sosai ba, ta tsaya ta bakin kofa ne tare da zuba mashi idanu babu ko kyaftawa, da alamar tarin tambayoyi da take son yi mashi sosai a saman fuskarta, amma ko da sunan wasa bata furta ko kalma É—aya ko ta yi wani motsi da zai sa ya ga tana kallon shi ba, tana gani har ya yi barci.
Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke tare da ƙarisowa cikin ɗakin. A gaban ƴar bed ɗin nasa ta tsaya, sosai ta kura mashi idanu babu ko kyaftawa, sai kallon face nasa take yi kamar wadda taga bako daga wani duniya mai wata halitta na daban ba irin na mutane ba, da alama dai akwai wata a ƙasa, wannan kallo bana banza ba, gata da sexy eyes da idan idanun mutun biyu ta tsare shi da kallo to sai ya shiga ruɗu.
Ta É—auki a kallah good 30 mins tana kallonsa from head to toe kafin ta sa kai ta fice daga cikin É—akin bayan ta sauke nauyayyar ajiyar zuciya kenan.
Nata É—akin ta koma ta zauna a saman bakin bed tare da buga uban tagumi ta afka cikin kogin tunani, sai Allah kaÉ—ai yasan tunanin me take yi.
Shi kuwa Rocky yana kwance a wajen ta bakin ƙogon dutsen abinsa, dama kullum haka suke yi, kamar wani shi ne mai gadinsu, Allah sarki ya yi girman da baya iya shiga cikin ƙogon, hakan tasa sai ya yi zamansa a bakin kofar yana ta kalle kalle, wani lokaci har barci ta ɗauke shi.
To mu dai bari mu kutsa cikin labarin mu duba wani part dan mu ga me ake ciki, wata kila kafin mu dawo wasu abubuwa sun ɗan daidaita ko sun bayyana mana a wannan dajin, dan gaskiya muna da buƙatar bayyanar abubuwa dayawa.
Wasu kyawawan ƴan matasan ƴan'mata ne su biyu suke tafiya, jikinsu na sanye da uniform na islamiyya launin sky blue, wando ce doguwa da riga zuwa gwiwa, sai farar hijabi har ƙasa.
Babbar ba zata wuce 7 years ba, karamar kuma 5 years, kamanninsu kusan É—aya, sai dai karamar fara ce sosai, babbar kuma ta É—an yi duhu, ma'ana wankar tarwaÉ—a, amma da kallo É—aya zaka yi masu ka fahimci iyayensu guda ne, dan fa ga kamar jinin karara a saman fuskokinsu.
Daga islamiya suke, suna tafiya cikin nutsuwa sosai saɓanin sauran yaran da zaka gansu idan an taso daga islamiya ko makarantar boko suna tafiya a kan hanya suna wasa, wasu ma ka gansu suna guje guje a kan hanya. Su waɗan nan a nutse sosai suke tafiya, bare ma ƴar babban cikin nasu, tana da nutsuwa sosai, da alama sun fito ne daga gidan tarbiya.
Suna rike da wata ƴar ƙaramar jaka na zuba litattafai, jaka ce dai ta ƴaƴan dai'dai mai rufin asiri, uniform ɗin jikinsu ya sha guga sosai, har wani kyalli yake yi, ga karin gugur nan ta zauna sosai a jikin uniform ɗin, da alama mahaifiyarsu jajirtatciya ce wajen iya wanki da guga wa yaran nata, da alama suna samun kulawa sosai, dan daga jikin yara ake gane tsabtar uwa, to gaskiya ita dai wannan uwar ba karya, akwai tsabtar.
Karamar ce ta rike masu jakar, da alama jakar babban ce, karamar ta yi karama da abata Alqur'ani mai girma da sauran litattafan addini, bata da wayo sosai.
Ita kuma babbar hannunta na rike da wata bakar leda, da alama aika ne a ciki. Sai magana ƴan yaran cikin unguwar suke yi wa karamar, amma bata kula kowa ba, ko ɗaga idanu bata yi ta kalli in da suke ba, kasancewar yanzu aka taso daga islamiyar, yaran dayawa ne suke shawagi a sararin unguwar, kowa yana ƙoƙarin nufar gidansu, saboda mangariba ta kawo kai.
Wani É—an madaidaicin gida waÉ—an nan matasan Æ´an'mata suka shiga, gida ne dai'dai na masu rufin asiri, daga kan kofar gidan har izuwa fentin gidan dukka sun nuna alamun mai gidan mutun ne mai zuciyar yi, kun san ba neman kuÉ—in ba, zuciyar yi ita ce, akwai masu kuÉ—in da kuÉ—insu bata ciwuwa, akwai kuma wadda zaku gani talaka ne, amma mai zuciyar yi, baya samu sosai kamar sauran mutane, amma da yake akwai zuciyar yi É—in, sai ku ga Æ´aÆ´ansa da gidansa duk kusan dai'dai da na wani mai kuÉ—in, komai mai kyau zaku ga ya sayawa Æ´aÆ´ansa da matarsa gwanin birgewa.
Ko'ina na cikin wannan gida siminti ne, babu kasa, an wanke ko'ina fes babu alamar datti ko kaÉ—an, kana sako kafarka a cikin gidan ma wani daddaÉ—ar kamshin turaren wuta ne zai daki kofofin hancinka, gwanin burgewa gidan.
Babbar parlour ce a tsakiya mai É—auke da É—akuna uku a cikinta, kowace É—aki da toilet a cikinta, sai wata É—aki irin ta matasan nan ta wajen tsakar gidan, filin tsakar gidan tana da girma ba laifi, akwai kitchen a tsakar harabar gidan sai toilet É—aya da ake yi a ta karshen ginin É—akuna haka.
Wannan mai gida yana da ƙoƙari sosai, har da bohol suke da shi a cikin gidan nasu, suna da ruwa available, ruwa abokin aiki kenan.
Parlourn nasu tamkar sauran kowani parlourn na masu rufin asiri ne, kujeru ne set É—aya manya manya masu laushi, launin ash da baki, sai Æ´ar madaidaiciyar TV plasmarsu 32 inches, akwai Æ´ar karamar freezer a ciki ta kusa da TV, sai wasu kyawawan jeren flowers da aka kawata parlourn da su, fanka ke garesu ba A.c ba, haka zalika ceiling garesu ba P.O.P ba, sai dai kasan parlourn nasu fa tiles ne mai kyau da zanen flowers a jikinsa, launin sky blue, ya sha mopping sosai, sam babu alamar datti, ga karamar welcome carpet a bakin kofa, abin dai gwanin birgewa da ban sha'awa, sai tashin kamshi wannan parlourn yake yi, ko'ina tsab kamar ba'a amfani da abubuwan ciki.
Tsabta akwai daÉ—i, kai da kanka idan ka tsabtace waje sai kaga ya yi wani irin masifar kyan gani, komai talaucin mutun idan yana da tsabta yana da sha'awar kallo a ido wlh.
Bakinsu É—auke da cikakkiyar sallama irin ta addinin Musulunci waÉ—an nan yara suka shigo cikin gidan nasu.
Dayawan mutane ba kowa ne yake yin cikakkiyar sallama ko ya amsa sallamar a cikenta ba, dayawa mutane suna yanketa wanda hakan kuma ba dai'dai bane, domin kamar yadda kuka yanketa haka ma'anarta ta yanke.
Dayawan mutane zaka ji suna cewa Salamu alaikum, masu amsata kuma suna cewa Alaikumussalam, wanda hakan sam ba dai'dai bane, nasan dayawanku baku san kuskure kuke yi ba, to tabbas kuskure ne yanke sallama da kuke yi, kuna yanke ma'anarta.
Masu shigowa zasu ce Assalamu alaikum, Mala'ikun Rahma suna amsata da Amin wa'alailumussalam, idan ku dayawa ne kuka shi go kenan, idan kai É—aya ne, Amin wa'alaikassalam, shi ne cikakkiyar sallama ta addinin musulunci, Allah ka yafe mana kura kuranmu.
Masu cewa in rinƙa rubuta addu'a ko wata tunatarwa kamar dai sallama dana gyara maku yanzu, masu cewa na rinƙa rubutawa da hausa ba da larabci ba, dan basu iya karantawa ba, zan yi ƙoƙarin yin hakan In Sha Allah, amma wani lokaci dole ne na rubuta da larabcin kun gane ai?.
Daga cikin ɗaki aka amsa masu cikakkiyar sallamar tasu tare da cewa. "Ƴan mata na an dawo?".
Babban cikinsu ne ta amsa da. "E mama mun dawo".
Tana magana tana cire hijabin jikinta, sannan ta ajiye wannan ledar dake a hannun nata a tsakar gidan, kafin ta wuce izuwa cikin parlourn.
Ita kam karamar dama tun shigowarsu ta sanya kai izuwa cikin parlourn da sauri abinta tana faÉ—in. "Mama baba ya aiko mun da lemun?.......".
Turus ta ja birki a tsakiyar parlourn lokacin da idanuwanta suka sauka a kan maman nata tare da wata bakuwar mata suna zaune a saman sofa suna hira. Mama ta sha kwalliya cikin wani haÉ—aÉ—É—en lace mai tsada da ya sha É—inkin doguwar riga, ta yi kyau sosai, launin black color ne lace É—in da ratsin milk, hakan ya kara mata kyau sosai kasancewarta farar fata, ta sha É—aurin É—an'kwalinta É—as da shi. Ita kuma wannan bakuwa tana sanye da abaya launin ash color, ta yafa mayafin abayar a kanta.
Nan take yarinyar ta É—aure fuska sosai kamar ba ita ba, duk da cewa dama can fuskar tata ba wani murmushi ne a samansa ba, daga ita har babban yayar tata babu alamar murmushi a saman fuskarsu, da alama basu da yawan fara'a, shi ne ma yasa da suna dawowa daga islamiya sai magana yara sa'anninsu suke yi masu, amma sun ki kula kowa.
"Zinarun babanta ya kika tsaya haka? Ki ƙariso ciki mana". Cewar matar dake hira da mamar tasu.
Kara É—aure fuska sosai Zainab ta yi, da alama bata kaunar matar ko kaÉ—an. Daidai lokacin ita ma babbar ta shigo cikin parlourn tana faÉ—in.
"Mama ga can kayan miyar nan na kawo maki, amma mama wai fa babu attarugun É—ari biyu, shi ne na saya maki ta É—ari biyar kawai, shi ma baki gansa ba É—an kaÉ—an da shi........"
Bata kai karshen maganar ba ita ma idanuwanta suka sauka a kan wannan matar, É—aure fuska sosai ita ma ta yi tare da wucewa zata nufi É—aya daga cikin É—akunan dake a cikin parlourn.
"Khadija baku ga Auntynku bane? Aunty Hauwa ce fa, ba zaku gaisheta bane". Cewar maman tasu.
Wucewa Zainab ma ta yi ta rufawa Khadijah É—in baya, dan su shiga cikin É—akinsu.
"Sannunki da zuwa Aunty Hauwa". Cewar Khadijah, ta yi maganar tana wani irin kunbura kumatu, alamar sam bata ji daÉ—in sakata gaisheta da aka yi ba.
Washe baki Aunty Hauwar ta yi tana faÉ—in. "Hadiza bage maganin maza, wai ni kam duk masu suna Khadijah haka suke ko? Haka kanwata ma take sam bata son baki".
Wata uwar harara Zainab ta wurga mata ba tare da sun lura ba, cikin É—aki ta wuce abinta, har ga Allah ta tsani wannan Aunty Hauwa É—in, ko me dalili?.
Turɓune fuska Khadijah ɗin ma ta yi kamar wadda aka aikowa da sakon mutuwa, yara kanana da su sun san kin abu, kome dalilinsu oho.
Uniform É—in jikinsu suka cire, suka sanya kayan gida, wasu dogayen riguna bakake, iri É—aya kayan, sai dai na Khadijah mai kwalliyar flowers ja ne, na Zainab kuma mai kwalliya pink color, shi ne kawai banbancin kayan nasu.
Fitowa suka yi suka sake wuce maman tasu da Aunty Hauwa, waje suka nufa, a lokacin sai kiraye kirayen sallar mangariba ake yi.
Famfo tsakar gidan suka je suka kunnna, Khadijah ce ta fara gabatar da alwala kafin ta bawa Zainab waje ita ma ta É—auro nata alwalar, da alama mamansu ta saba masu da yin komai cikin tsari, dan daga yanayin yanda suka shigo suka je suna cire uniform suka fito suka É—auro alwalar nan, alama ya nuna cewa tabbas an sabar masu da hakan ne.
Ciki suka koma, dai'dai lokacin aka kawo wutar nepa, sallah suka je cikin bedroom nasu da yake tsab tsab suka gabatar, ita kuma mamar tasu tana zaune ta biyewa Aunty Hauwa sai zuba hira suke yi har yaran suka idar da sallarsu.
Abin mamaki cikin nutsuwa suke gabatar da sallar nan tasu tamkar wasu manya.
Bayan sun idar ne suka fito parlourn, a yadda suka bar mamarsu haka suka fito suka sameta.
Khadijah ce ta ce. "Mama yau kin manta baki yi sallah da wuri ba".
"Ban manta ba Khadijah, ai ba'a mantuwa da ibada, yanzu nake son tashi na yi".
Da gudu Zainab ta nufi kofar fita daga parlourn jin an taɓa kofar gida, faɗi take yi oyoyo baba oyoyo Yah Haidar. Da sauri Khadijah ma ta rufa mata baya, tamkar basu ne masu ɗaure fuska yanzun nan ba, a take suka fara zuba murmushi na ganin mahaifin nasu da kuma yayansu, ashe dai suna dariya, amma da alama ƴan gidansu kawai suke yi wa dariyar.
Yah Haidar É—in nasu yana rike da kaji na hausa guda biyu a hannunsa, zakara da kuma mace, sai kuma wani katuwar bakar leda a É—ayar hannun nasa, shi kuma baban nasu yana rike da wata leda irin mai zane a jikin tan nan, kayan fruit ne a cike a cikin ledar.
Khadijah tana zuwa ta fara kiciniyar karɓawa baban nasu ledar hannun nasa, ita kam Zainab tuni ta yi tsalle ta ɗale jikinsa tana dariya har da kyakyatawa, kamar ba ita ce yanzun nan ta gama hararar Aunty Hauwa tare da turɓune fuska ba, dama fa masu suna Zainab da Khadijah wlh sai a hakankali, kusan kaso tamanin cikin ɗarinsu haka suke, akwai shegen tsare gida, sai dai suna yi wa wanda suka ga dama fara'a, kamar dai yadda kuke ganin waɗan nan yaran baban nasu.
"Zeezeena kun yi sallah?".
Shi ne tambaya ta farko da wannan uban na garin ya fara yi masu, ya yi maganar kuma yana sakewa Khadijah ledar fruit dake a hannunsa, yaran kirki, yana da kyau duk wata uwa ta koyawa ƴarta karɓar abin da mahaifinsu ya shigo da shi, hakan shi ne tarbiya.
Khadijah ce ta bashi amsa da. "Mun yi baba, amma mama bata yi ba, tana can suna hira da wannan Aunty Hauwar ta gidansu Khadijan nan na islamiyyarmu".
Dariya kaɗan Haidar ya yi yana faɗin. "Ke yanzu Khadijah waye ya tambayeki mama ta yi sallah ko bata yi ba? Ba dai ke kin yi ba? To Allah ya karɓa, ni bana hanaku faɗi ba'a tambayekun nan bane wai?".
Ɗaure fuska Khadijah ɗin ta yi tare da wucewa ta nufi cikin parlourn tana turo baki, ita a dole Yah Haidar ya shiga maganarta ba da shi take yi ba, ranta ya ɓaci.
Wucewa wajen É—an madaidaicin kitchen É—in nasu Haidar É—in ya yi, a ciki ya ajiye kajin tare da ledar cefenen da yake a hannunsa, sannan ya fito ya nufi wannan É—akin samarin da yake a harabar gidan.
Ita kuwa Zainab baba ya É—agata sama suka nufi cikin parlourn.
Bakinsa É—auke da cikakkiyar sallama ya shigo cikin parlourn.
A tare Aunty Hauwa da maman nasu suka amsa mashi sallamar. Ƙarisowa ciki ya yi tare da wucewa ya nufi ɗaya daga cikin ɗakunan dake a cikin parlourn, har cikin ransa yake jin daɗin shakar wannan daddaɗar kamshin turaren wutar da yake tashi a cikin parlourn, bai ce da Aunty Hauwa ko sannu ba, da alama irin mazan nan ne da idan bakin matansu sun zo gida ba su kulasu, in dai ba su ne suka ɗaga masu gaisuwa ba, to ko sannu ba zasu ce masu ba, ko kallon in da suke ma ba zasu yi ba, dan haka shi ma dai ko kallon Aunty Hauwa ɗin bai yi ba, ya sa kai zai wuce abinsa, yana ɗauke da Zainab a saman kafaɗarsa.
Cikin sauri Aunty Hauwa É—in ta É—aga mashi gaisuwa tana wani kara faÉ—aÉ—a murmushin da yake a saman fuskarta.
A takaice ya amsa mata da amsa É—aya wato lafiya, ya amsa kuma ba tare da ya kalli in da take ba, daga haka kuma yasa kai sai cikin bedroom nasa abinsa.
Ajiye ladar da ta karɓo daga hannun baban nata Khadijah ta yi a tsakiyar parlourn, sannan ta yi sauri ta bi bayansa izuwa cikin ɗakin nasa.
Miƙewa Aunty Hauwa ta yi tana faɗin. "Babansu Zainab ya dawo, bari na je gobe zan dawo mu karisa maganarmu".
Da sauri maman tasu ta ce. "A'a tsaya ki sha fruits mana".
Ba kunya ta ce to a bata, ita kuma maman cike da zumuÉ—i ta buÉ—e ledar ta fara haÉ—o mata komai É—aÉ—É—aya kamar ita ta kawo ta ajiye.
Kuskure ne idan mijinki ya sayo abu ki ɗauka ki yi kyauta da shi ba tare da saninsa ba, ansan cewa duk abin da zai sayo ku ya sayowa, amma kuskure ne ki kyautar baki tambaye shi ba, koda ƴan uwanki zaki bawa, yin hakan wlh sam bai dace ba, kina zubar da kima da kuma darajarki ne a gabansa, kuma hakan yanasawa namiji ya ji ya daina sha'awar saya maku abu idan ya fita, dan zai ga kamar baku ɗauki abin da mutunci da daraja ba, tabbas idan kin tambaye shi zaki yi kyauta da shi zai yi wuya ya hanaki, wannan tambayarsa da zaki yi ɗin zai kara maki kima da daraja, zai kuma sa mijin naki ya ji cewa yana da kima a idanunki da har zaki tambaye shi kafin ki yi kyauta da abin da ya saya maku, koda bai nuna maki ya ji daɗin tambayarsa da kika yi ɗin ba, wlh ina mai tabbatar maki ba ƙaramin daɗi suke ji ba, dan haka koma me ya kawo koda kannenki zaki bawa, ki tambaye shi cewa zaki bawa su wane kaza abu kaza, musamman ma idan a lokacin ya kawo abin, yasan adadin yawansa da in kin kyautar zai gane, wasu mazan in kin tambayesu zasu ce maki to ki bayar mana ba ke suka kawowa ba? Kada ki damu wlh suna jin daɗin tambayar, kuma kada amsarsu yasa gobe ki fasa tambayarsu, ki tambaya ɗin zai fi.
Ai kuwa ita dai maman su Zainab duk ta haÉ—awa Aunty Hauwa fruits É—in nan komai É—aÉ—É—aya, ta É—auko wani leda daga cikin kitchen ta sanya mata a ciki, sannan ta rakota har kofar gida, sai zuba godiya Aunty Hauwa ake yi kamar me.
Naira dubu ɗaya mamansu Zainab ɗin ta bata a kan ta hau abin hawa zuwa gida. Sai murmushi take yi tasa hannu ta karɓa, tana ta zuba godiya ta tafi.
Ita kuma Maman Zainab ta juya ta dawo cikin gida.
A parlourn ta isko su Zainab suna zaune, bata ce da su ko sannu ba ta yi saurin wucewa cikin É—akin baban nasu, dan ko ba'a gaya mata ba tasan ya fito daga wanka ne ya ce su Zainab su je parlourn bari ya sanya kaya, dama haka yake yi da su.
A hanzarce ta faɗa cikin ɗakin baki ɗauke da sallama, daidai lokacin yana ƙoƙarin zura jallabiya a jikinsa.
Ƙarisowa kusa da shi ta yi tana faɗin. "Ka yi hakuri baban Zainab, yau Hauwace ta tsayar da ni ban zo na fitar maka da kayan sakawa ba".
Fuskarsa a ɗauke da ƙayatattcen murmushi ya bata amsa da. "Kada ki damu, ai kullum kina fitar mun, dan yau kawai baki yi ba ai ba komai, muje bari maje masallaci lokacin sallar issha ta gabato".
Dayawan maza suna bawa mata irin wannan masa da baban Zainab ya bata a yanzu, wanda kuma magana ta gaskiya wlh ba har cikin zuciyarsu wannan amsa take ba, suna dai faɗa ne kawai, dan haka mata sai ku kiyaye, kada ki bari ya maimaita maki irin wannan amsa sau biyu zuwa uku, daga haka za'a fara samun matsala, wani ma idan ya cigaba da maimaita maki sai ki ji ya bushe idanu wata rana yana ce maki ai bama ki taɓa fitar mashi da kayan sawa ko makamancin hakan ba, duk kuma ke kika fara jawowa kanki, kada ki bari dan kin yi bakuwa tasa ki fasa yi wa mijinki abin da kika saba yi mashi, idan bakuwar ba zata jiraki ki yi attending nasa na ɗan lokaci ba, to gara maki ta tafi zai fi, dan haka sai a kula sosai.
Murmushi ta yi ita ma tana mai kara bashi hakuri, cigaba da gaya mata babu komai ya yi kafin ya É—auko perfume nasa mai daÉ—in kamshi da nufin ya feshe jikinsa da shi.
Hannu ta kai ta karɓi perfume ɗin ta fara fesa mashi tana mai yabawa kyan da ya yi. Ba karya fa babansu Zainab kyakkyawa ne sosai, sai dai chocolate color ne, ya fi mamar tasu kyau sosai, ita kuma ta fishi hasken fata, farace sosai, su Zainab duk shi suka ɗauko a kyau, sai dai ita Zainab ta ɗauko hasken mamanta, kyan babanta, ita kuma Khadija komai na baban ne harta launin fata.
Bayan ta gama fesa mashi perfume ɗin ne ta ɗauko mashi wayarsa babba da karamar da suke a saman shinfiɗaɗiyar bed nasu 6/7, gadon ya sha gyara kam, ba karya maman Zainab akwai ƙoƙari wajen sake jiki ta yi aikin gidanta da kyau da kyau, yanzu haka wannan jallabiya na jikin baban Zainab ita ce nan ta wanke ta zuba mata guga, sai kyalli take yi, ta sha iron, ita fa maman Zainab da alama gugan kaya baya yi mata wahala, dan harta bedsheet dake a shunfuɗe a saman bed ɗin nan ya sha guga sosai, da yake ma sun saba shan guga sai ka gansu da karin gugan ya fito ɓaro ɓaro, ya riga ya kama kayan, to abu ne da ake yi ba jiya ba ba shekaran jiya ba, an jima, dole kunga su kama karin guga.
Parlourn suka fito, a nan ya isko sanyin idaniyarsa wato Æ´aÆ´an nasa, Zainab tana kallon Tv, ita kuma Khadija tana rike da wayar mamanta tana buga game.
"Zeezeena zan je masallaci amin addu'a".
Ya faÉ—a yana nufar kofar fita daga cikin parlourn. Har suna rige rige ita da Khadijah wajen zuba mashi addu'ar adawo lafiya Allah ya tsare ya kiyaye hanya.
Da amin ya amsa masu kafin ya fice. Har harabar gidan maman nasu ta rako shi kafin ta dawo wajen famfo dake harabar gidan ta É—auro alwala, a lokacin aka fara kiraye kirayen sallar issha.
Fitowa daga nasa É—akin Haidar ya yi, cikin sauri ya kariso wajen famfon dan shi ma ya É—auro alwala. Sannu ya yi wa maman Zainab É—in tare da tsayawa a gefe guda yana jiranta ta gama.
Amsa mashi sannun nasa ta yi tare da tambayarsa ya kasuwa.
Alhdulillah ya amsa mata da shi, sannan ya É—aura mata da cewa. "Sadiq dai yaki dawowa yau É—in ko?".
ÆŠagowa ta yi daga wajen fanfom tare da kasheta tana faÉ—in. "Ba yadda ban yi da shi ba a kan ya dawo, ya ce mun sam shi bai kalli mama sosai ba, wai sai jibi zai dawo".
Ta kai karshen maganar tare da wucewa ta nufi hanyar komawa cikin parlourn.
"Gaskiya Sadiq bai kyauta mun ba, sam goben nan ban so fita kasuwa ba, dan ina da wanki da É—an aikace aikace da zan yi a É—akinmu, amma shi ne yaki dawowa, next time ba zan barshi ya yi tafiyar nan ba".
Murmushi kaÉ—an ta yi tana faÉ—in. "Ai kun fi kusa". Daga haka ta wuce ciki abinta.
A parlourn ta isko su Zainab É—in a saman dadduma, sallah suke yi, wucewa nata bedroom É—in ta yi, dan ta biya sallar mangariba kafin ta É—aura da issha.
Bayan sun idar da sallar, zama suka yi a saman dadduma Khadija tana karawa Zainab karatun malumat da Nahhu, a haka babansu ya dawo daga masallaci ya samesu, a lokacin kuma mamansu ta idar da nata sallar har ta zo ta ɗauki fruit ɗin da ya kawo ta wankesu tsab, ta zuba masu su a cikin plate tare da sanya masu wuƙa a saman plate ɗin wanda zasu yanka fruit ɗin, ta ajiye a tsakiyar parlourn haɗe da abincin darensu, akwaita da ƙoƙarin aiki kam, bata da son jiki, bayan ta yi dukka wannan ma kitchen ta wuce ta hau shirya kayan cefanen da Haidar ya shigar dasu ciki, su curry ne dasu maggi, kayan kamshi da dai sauran kayan girki, su tattasai da attarugu ne kawai babu a ciki, baban Zainab akwai shi da iya sayan kayan kamshin girki, ya iya cefene sosai kamar wata mace, idan ya yi cefenensa ma yafi wata macen.
Bayan ta shiryasu cikin robobin kayan miyarta ne ta dawo ta É—auki kayan miyar da Khadijah ta ajiye mata a tsakar harabar gidan, tomatoes ne da su attarugu, dama su babansu bai cika sayo irinsu a cikin cefenensa ba, da yake cefenen sati sati yake yi, su kuÉ—i yake bawa maman nasu ta saya.
Kitchen ta kai kayan miyar ta shiryasu yadda ya dace, dan na miyar gobe da safe ne, dama haka suke yi kullum, tun da yamma a hanyar islamiya Khadijah take yo masu cefanen su tomatoes na miyan washegari, dan su ajiye komai ready, saboda kada su Khadijah su yi lattin zuwa makarantar boko a dalilin jiran girki ya nuna.
A parlourn ta isko baban nasu tare da Haidar sun dawo daga masallaci, a kusa da baban ta zauna tare da fara ƙoƙarin zuba masu abinci, dan duk zaman cin abinci suka yi, da alama da yunwa suka dawo daga kasuwar nan.
Jawo plate na kayan fruits ɗin nan baban nasu ya yi, fuskarsa ɗauke da ƙayatattcen murmushi ya fara faɗin. "Zeezeena zo ki sha lemun da kika yi ta tuna mun a waya na saya, sarkin son lemu".
Khadijah ce ta ce. "Baba ni kuma ina inabi na?".
"Mamana na sayo maki kema ai, ban manta ba, duk kuzo ku sha".
Ya yi maganar yana yankawa Zainab lemun zakin da ya É—auko. Yana yanka lemun yana kallon cikin plate na fruits É—in, idanuwansa kamar suna yi mashi gizo ne, dan bai ga inabin Khadijah a ciki ba, kuma itace É—aya ya sayo inabin dama, wa ita kaÉ—ai, ita kaÉ—ai ya sayawa, dan ita kaÉ—ai take shan inabi a gidan, Zainab lemu take so, ita kuma mamansu Apple, kowa da abin da ya fi so, shiyasa idan ya tashi saya yake sayowa kowa nasa, baya manta na kowa, shi kuma kankana yake sha shi da Haidar, sun fi sonta.
"Maman Zainab kin rage wasu fruits kin saka a cikin fridge ne?". Ya yi maganar yana miƙawa Zainab lemu.
Tana kan zuba masu white rice and beans É—in a cikin plate ta bashi amsa da.
"A'a ban rage komai ba, dukka fruits É—in ne kenan".
Dawo da kallonsa a kan Haidar ya yi kafin ya ce. "Haidar malam Sani bai saka mana inabin Khadijah da kuma abarba ba".
"Any kuwa? Kamar fa ya saka a ciki, naga lokacin da ya É—auko ya saka". Haidar ya bashi amsa.
"To amma ya babu a ciki?". Baban ya sake jefa masu tambaya fuskarsa da alamar damuwa, dan shi mutun ne da baya son ko da sunan wasa Æ´aÆ´ansa su ji cewa kamar yana yi masu banbanci a tsakaninsu, da yasan babu inabi da ba zai bawa Zainab lemun nan ba har sai ya sake fita ya sayowa Khadijah nata, sai ya dawo ya basu a tare, dan komai a tare yake yi masu, yana nuna masu cewa dukkansu É—aya.
Shiru maman Zainab É—in ta É—an yi na Æ´an sakani kafin ta ce "E akwai inabi fa, dan na É—auki itace É—aya ma na haÉ—awa Hauwa a cikin fruit dana É—eba mata".
Da sauri ya É—ago kai tare da watsa mata wani irin kallo mai nuni dacewa meyasa zata yi hakan?, domin kuwa inabi guda É—aya ya sayawa Khadijah ita kaÉ—ai. Amma duba da yaran suna nan sai bai yi magana ba, ya yi shiru, har cikin ransa sam bai ji daÉ—im hakan ba, sai ma ya ji duk abincin ta fita mashi a ransa, ya ji babu daÉ—i sosai, ya sayowa Æ´aÆ´ansa abu ta wani É—auka ta kyautar kamar ya aiketa, in da ma kankanarsa ta kyautar ba zai damu ba, amma na Khadija takwarar mamansa guda, gaskiya bata kyauta mashi ba.
"Kiyi hakuri mamana, bari Yah Haidar ya je ya sayo maki wani yanzu nan, jeki É—aki ki É—auko kuÉ—i a wajen drawer ta ki kawo mun". Ya faÉ—a cikin sanyin murya, daga jin yanayin maganarsa kasan sam bai ji daÉ—in abin da maman nasu ta yi ba, ita ma kuma ta lura da bai ji daÉ—in ba, duk sai ta ji babu daÉ—i ita É—in ma.
"A'a ta bar kuÉ—in da akwai kuÉ—i a jikina bari na sayo mata da shi". Cewar Haidar.
Taɓe baki maman Zainab ɗin ta yi tana mamaki, yau Haidar da kyauta, sam baya taɓa masu kyautar ko Naira biyar ɗunsa, idan kaga ya bawa su Khadijah kyautar wani abin ci ma ba kuɗi ba to wlh sai idan babansu yana nan, eyes service gare shi, in babansu baya nan ko tsinkensa basu ci. Allah mai iko, kaga dayawa idan kana raye.
Miƙewa ya yi ya fice daga parlourn, sai hakuri baban nasu yake ta bawa Khadijah, ta dai ce mashi to, amma ji take kamar zata fashe dan haushi, sai ta ji ta kara tsanar wannan Aunty Hauwar.
(Masu suna Khadijah idan suka tsaneka ka shiga uku😅 kome zaka musu ba zasu ga farinka ba😅 in sun riga sun saneka fa to sai dai ka yi hakuri ka rungumi sorry ka kyalesu😅 ina ga dalilin cinye masu abubuwa da Aunty Hauwa take yi yasa suka tsaneta😅)
Abincin suka fara ci cikin nutsuwa, maman Zainab ba dai iya girki ba, ta kware sosai, idan kana cin girkinta idan ka yi wasa sai ka fara zuba santi ba tare da ka sani ba, saboda daÉ—i da iya tsara girkin.
A wannan hali Haidar ya dawo ya samesu, bai samu inabi ba, masu fruits na unguwar tasu duk basu kawo inabi, kun san yana da tsada, ba kowa yake sayansa ba, hakan yasa ba kowani mai sai da fruits yake kawo shi ba, sai manya masu sayarwa.
Jin cewa ba'a sami inabin ba yasa Khadijah ta fashe da kuka tare da miƙewa ta bar abincin nata, fuuu ta nufi cikin ɗaki.
Kallon maman baban nasu ya yi, irin kallon nan na ke kika jamun, ita ma shi take kallo, irin kallon nan na kayi hakuri.
Bai ce da ita ko uppan ba ya miƙe ya bi bayan ƴar tasa dan ya rarrasheta, ga shi kuma dare ne, idan ya ce zai je neman inabi a yanzu sai ya hau mashi ya fita cikin gari ta wajajen kasuwar tasu, zuwa wajen kawai ma 500 naira ne kuɗin mashi, dawowa ma haka, bare kuma daren nan kunsan kara kuɗin mashi suke yi, gaskiya maman Zainab dai bata kyauta mashi ba, kuma idan bai nemo wannan inabi ba Khadijah dai ƙaramin aikinta ne ta yi mafarki, shi ma dai ba zai iya yin barci cikin daɗin rai ba, dan yasan waye Khadijah bagensa, sarkin zuciya da rigima, dole dai anemo inabi, kuma tsautsayi ne tasa yau ya sayi inabin guda ɗaya, sau da dama biyu ko ukku yake saya, zaka gansu a jikin itacensu ba'a cire ba an sako mashi guda uku, to yau sai malam Sani ya saka masu guda ɗaya tak, Mama ta bawa Aunty Hauwa, aiki babba kenan, akwai rigima.
Nikuma dole na dakata da rubutu a nan, Maman Zainab baki kyauta mana ba, shiyasa ake son a rinƙa tambayar mutun abu idan ya kawo, ba wai ayi gaban kai ba.....….😌😒
*Masu buƙatar littafin TRIPLETS daga farko harshen su yi mun magana ta wannan number tawa, 08161390581.*
ðŸ¤PRINCESS TEEMA taku ta amana🔥
Share fisabilillahi ðŸ‘
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥ðŸ¤
ðŸ¤ðŸ”¥ð—¥ð—”ð—ªð—”ð—¡ð—œð—¡ 👑 ð—ð—”ð—Ÿð—œð—¡ð—–ð—œðŸ”¥ðŸ¤
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
ð— ð—”ð—Ÿð—Ÿð—”ð—žð—œð—¡
â¤ï¸â€ðŸ”¥FATEEMA ZAHRA MUSA â¤ï¸â€ðŸ”¥
(â¤ï¸ð‘·ð‘¹ð‘°ð‘µð‘ªð‘¬ð‘ºð‘º ð‘»ð‘¬ð‘¬ð‘´ð‘¨ðŸ”¥)
🔥ðŸ¤T🔥ðŸ¤T🔥ðŸ¤W🔥ðŸ¤......💻
â¤ï¸ð‘«ð‘¨ð‘»ð‘¬ 3/7/2024.....âœï¸ðŸ“šðŸŒ¹
ðŸ¤ð‘ºð‘»ð‘¬ð‘· 1......âœï¸ðŸ“šðŸ”¥
اللَّهÙمَّ صَلّ٠عَلَى Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯Ù ÙˆÙŽØ¹ÙŽÙ„ÙŽÙ‰ Ø¢Ù„Ù Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯ÙØŒ كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ وَعَلَى Ø¢Ù„Ù Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ، Ø¥Ùنَّكَ ØÙŽÙ…Ùيدٌ مَجÙيدٌ، اللَّهÙمَّ بَارÙكْ عَلَى Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯Ù ÙˆÙŽØ¹ÙŽÙ„ÙŽÙ‰ Ø¢Ù„Ù Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯ÙØŒ كَمَا بَارَكْتَ عَلَى Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ وَعَلَى Ø¢Ù„Ù Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ، Ø¥Ùنَّكَ ØÙŽÙ…Ùيدٌ مَجÙيدٌâ¤ï¸
E____________6🔥
Kwance ya isko Khadijah kadina kadin Allah a saman Æ´ar madaidaiciyar bed nasu 6 by 6. Gadon a shunfuÉ—e yake da zanin gado mai kyau lunin pink color da ratsin baki, tsab da shi, sai kamshi É—akin nasu ma yake yi, ga drawer kayansu mai É—an girma a gefe guda, sai drawer bed É—in da suke jera kayan kwalliyarsu da kuma mayukan shafawarsu.
Sai wani irin kuka take yi, irin kukan nan da idan mutun zuciyarsa ta hasala sosai, sai ka ji yana wani irin kuka kamar mai sifirin..........😅
To haka Khadijah take wanan kuka. A bakin bed É—in ya zauna tare da sanya hannu ya É—agota yana mai bata hakuri.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.