Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel By Hafsat Bature
Reading file: Abban Sojojin Takun Karshe.txt
Chapter 15 of 46
DARE YAYI GARI YA WAYE,
Tun bayan Kammala Sallar asuba,Azmee da Saude,Suka fara ɗaura girke girken da zasuyi anan cikin gida,Uban aiki ne a gabansu,saboda Abinci ne kala kala zasuyi,na kasashe daban daban,saukin su ma Naman da za'a yanka basu zasuyi aikinshi ba,An riga da an bada aikin naman already,sai dai kawai in an kammala akawo masu shi Hada snacks sukayi order wanda za'a ci,akwai kuma Naman da Azmee zatayi masu farfesu dashi,da kuma tsiren nama,don ta kware a wannan 6angaren,Sunyi nisa acikin aikin sai ga Hajiya azeema ta shigo,bayan sun gaisa da junansu,itama tace tazo ayi aikin da ita,hakan ba ƙaramin daɗi yayi masu ba,nan suka haɗu su uku,suka tasar ma girkin nan,Cikin ƙanƙanin Lokaci,Wani irin daddaɗan ƙamshi ya gauraye ko'ina na kitchen ɗin,
Hatta main palour ɗin kamshi ya karaɗe cikinsa,gwaggon katsina dake kwance,saman gado,tun bayan sallar asuba ya ɗauketa,tana cikin bacci ta dinga jin ƙamshin abinci nashiga Hancinta,ba arziƙi ta farka tana faɗin"wannan wani irin ƙamshi ne mai tashin mutun daga bacci"?tana maganar tana shinshinar kamshin,saukowa tayi daga saman gadon,jikinta sanye da kayan baccin nan nata na gado,fitowa tayi daga cikin bedroom ɗin nata tana tunkarar inda kamshin ke fitowa,
Kamar daga sama suka ji muryar gwaggo tana cewa"Ikon Allah,ƙamshi ya tashe ni daga bacci,ya kawo ni cikin kitchen,don inci daɗi,"
 Murmushi suka saki gaba ɗayansu,kafin suka shiga gaishe da ita,
 ƙarasawa tayi cikin kitchen ɗin suna haɗa ido da saude ta watsa mata harara tare da cewa"ya akai kuka bar wannan tana girki?bafa ta iya girki ba,Rannan ta zuba mana Gishirin lalle amatsayin gishiri cikin farfesun nama,gaba ɗaya girkin nan bai ciyu ba,ƙarshe saboda tsoran kar asirinta ya tonu inyi mata faɗa,ta dauki farfesun ba tare da sanin kowa ba taje ta zuba ma karnukan layinmu,kunsan kare da nama nan fa suka lashe farfesun nan tasss suka cinyi shi,aikuwa cikinsu ya kumbura sumtum,sukayi mussai,gaba ɗaya suka mace aka zubdo su,mai karnukan nan yace bazai yarda ba,sai yayi shari'a da Saude,ranar saude har gudawa saida tayi don jin za'a kaita ƙara kotu,yarinya tabi ta burkice mana,daƙyar Harrisu ya biya diyarsu,daba don haka ba,da tuni saude an jima da yanke mata hukuncin kisa....'
 Tunkan gwaggo takai karshen Labarin da take basu gaba ɗaya suka fashe da dariya,banda saude wadda ta tur6une fuska,rai a6ace tace"Kai gwaggo,"
 gwaggo tace"ƙarya nayi?ko ba haka akayi ba,ki faɗi tsakaninki da Allah in ba ayi hakan ba,ranar fa har gudawa kikayi,kika dinga kuka kina cewa gwaggo ki maishe ni rugarmu,saboda kawai na kashe karnuka shine za'a kai ƙarata kotu,wlh ko shanun baffa na kashe ba za'ayi mani wannan hukuncin ba,sai ku ƴan gayu da kuka ɗauki ran kare da mahimmanci karen da ko hisabi baza'ayi dashi ba,"
 Sake fashewa da dariya sukayi,yadda gwaggo take kwaikwayon muryar Saude,ba ƙaramin dariya ta basu ba,saboda hausar irin ta fulanin da basu kware bace,"
fuskar saude tamkar zatayi kuka,batasan meyasa gwaggo keyi mata haka ba,duk in suka shiga cikin mutane saita kunyata ta,wannan labarin da take bayarwa ya jima da faruwa,tun lokacin da Dr harris ya ɗaukota daga rugarsu ya kawota gidansu,lokacin batasan komai ba,ita arayuwarta ba abunda ta bama mahimmanci inba Kiwon shanu ba shi kadae tafi sani,gwaggo kuma bata koyar da ita komai ba,kwana uku da zuwanta gidan ne,ta shiga kitchen ta ɗaura masu girki,tana cikin girkin ta fara neman gishiri zata zuba acikin,gafa gishirin acikin farar roba an zubashi,amma saboda ta saba ganin gishiri kulle acikin leda yasa tayi zaton koba gishiri bane,hakan yasa ta fito ta wuce ɗakin gwaggo don ta sanar da ita cewa babu gishiri a gidan,tana shiga ɗakin gwaggon katsina,ta same ta tana bacci,harta juya zata fita shine taga wasu kullun kaya da aka kawoma gwaggo acikin leda,nan fa ta shiga laluban kayan,ta zaƙulo ledar gishirin lalle ta fuce dashi,duk a tunaninta gishiri ne,dayake kanta a toshe yake,kwata kwata bata lura da lallen dake acikin ledar ba,ita dae kawai gishirin lallan ta ɗauko,taje ta zuba masu acikin girkin,ba don Allah yasa gwaggo ta tashi tana neman gishirin lallanta ba,har saude taji,daba ƙaramin illa zata yi masu ba,karshe dai abun kan karnukan layinsu ya ƙare,tun daga wannan lokacin ne harris ya sanyata a makaranta,da kuma makarantar koyon girki,har ta samu ta kammala secondary,daga nan ne akasamu kanta ya waye,
 "Gwaggo me kikeso a zuba maki ne?nasan yunwa ce ta koro ku,"azmee ce tayi maganar,
 Gwaggo tace"komi ma da kuka girka,a zuba mun in ɗanɗana inji yaya ɗanɗanon girkin naku yake,don tunda kuka sanya saude acikin girkin nan naku nasan cewa dole a samu matsalar rashin gishiri kodae ta zuqa shi,ko kuma yayi kaɗan,"
murguɗa mata baki saude tayi tare da juyawa ta shige cikin store,tana faɗin"nashiga uku da wannan matar,a haka Haris yakeso in zama surukarta,bansan ya zan ƙare da ita ba,lafiya lou nake yin girkina acan gida,har santi takeyi amma yanzu tazo sai sharri takeyi mun agaban mutane,Zamu koma gida ne,nasan me zanyi mata,ae mun saba dama,"
 Saude bata fito daga cikin store ɗin ba,sai da taji fitar gwaggo daga kitchen din,bayan sun zuzzuba mata abincin da suka girka,komai sai da tasa suka zuba mata,a ƙaton tray ta fuce dashi tana cewa"idan na cinye wannan zan dawo a ƙara mun,"
 dawowa tayi cikinsu suka cigaba da aiki,azeema tace"sai kin dinga haƙuri da ita,bayin kanta bane,ku tayata da addu'a,Allah ya yaye mata wannan haukan da aka ɗaura mata,"
 Saude tace"insha Allah,zamu cigaba da tayata da addu'a,ae yaya harris ya sanar dani komai,na tausaya mata sosai,Allah dai ya tonu asirin waɗanda ke shirya masu wannan maƙarƙashiyar,Allah ya kawo ƙarshensu,"
 Azmee tace"ae bazasu kai labari ba,a sannu asannu zasu gane kurensu,"
 Suna aiki suna tattaunawa game da irin rayuwar da su sehrish sukayi a baya,
Wuraren ƙarfe 10 sun kammala Komai,an gyara kitchen ɗin tamkar ba'a ta6a girki acikinsa ba,tun da wuri Abokanan Abba suka fara zuwa,Hada wasu daga cikin abokan Abusufyan wanda ke zaune a Nigeria,tuni gida ya fara ciki,tun da su sehrish suka tashi daga bacci ko arziƙin yin wanka basu samu damar yi ba,saboda kiransu da ake tayi,duk wanda yazo saiya buƙaci a kira mashi su ya gansu,daga sunje haka za'a dinga yabon kyawunsu ana sanya masu albarka,gashi duk wanda sukaje gaidawa cikin abokanan Abba,sai Yayi masu kyautar makudan kudi,babu wanda yayi masu kyautar ƙasa da naira dubu ɗari biyar,hosana duk tabi ta susuce,sae faman lissafin kuɗaɗen da suka samu takeyi,daga sun dawo cikin ɗaki zata fara fadin Abokin abba mai farin gemu ya bamu kyautar Dubu ɗari takwas,sae wannan abokin nasa mai sanye da kaki da yazo ya bamu kyautar gonaki guda uku,kuma ya haɗa mana da dawakai,Sai kuma wannan mai ƙaton tumbin shine ya bamu kyautar miliyan Uku,Ni miliyan ɗaya,Jahad miliyan ɗaya,sae sehrish itama miliyan daya,bayan shi kuma sae wannan abokin daddyn namu ɗan fari mai kumatu,wanda ya biya mana Umrah,Ashe da rabon zanje in ta6a ka'aba ɗakin Allah,harma in roƙe shi akan ya yaye mun haukan dake damuna,don banson jin anace mun Zararriya,haka ta dinga sambatu har sai da suka fara gajiya da surutun hosana,
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.