Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel By Hafsat Bature
Reading file: Abban Sojojin Takun Karshe.txt
Chapter 12 of 46
â¤ðŸ¤â¤
*Boss Bature*
Zaune yake asaman Sofa mai mazaunin mutun uku,gaba ɗaya ya tattara hankalinshi akan Laptop ɗinshi da yake daddawana anatse,jikin shi na sanye da linen tank top,blue colour tabi shape din jikinsa,sick pack din nan nasa ya bayyana ajikin rigar,trouser ɗin jikinsa kuma white colour ne,wani irin daddaɗan ƙamshi ne ke fitowa daga kowani sashe na jikinsa,
Shigowa Azmee tayi part ɗin nasa da sallama a bakinta,yayin da hannunta ke ruke da tray,amsa mata sallamar yayi batare daya ɗago ya kalleta ba,ƙarasawa azmee tayi tare da ajiye mashi tray ɗin asaman empty table din dake a gefenshi,hannu takai tare da ciro plate ta daukko serving spoon tana ƙokarin buɗe warmer,muryarshi ta katse mata hanzarinta da cewa"ɗazu da safe meyasa kika kawomin breakfast?kuma kika gyaramun bedroom ɗina,dama kece ke gyara mun part ɗina ne"?
gabanta ne taji ya faÉ—i rass,muryarta na kerma tace"A'a bani bace,Sehrish ce,"
"Meya hanata yi mun aiki,"?yana magana yana danna laptop dinsa har time É—in bai É—ago da idonshi ba ya kalle ta,
Azmee tace"Am...um...dama..."bata ƙarasa maganar ba,ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannunshi,cikin sauri ta shiga taitayinta,
Cike da bada Umarni yace"Call her right now,"
Jiki na rawa azmee ta juya tare da fucewa daga part dinsa,downstairs ta saukko,babu kowa a falon duk suna a bedroom É—insu,wasu ma sunyi bacci,
Kai tsaye ɗakinsu Sehrish taje,tsayawa tayi abakin ƙopar ɗakin tana kwankwasawa,sai faman knocking takeyi amma ba'a buɗe mata kopar ba,da alama sun jima da yin bacci,
Har sae da ta fidda rai da za'a buÉ—e mata kopar,tana kokarin juyawa tabar wurin,taji alamun za'a buÉ—e kopar,Jahad ce ta buÉ—e É—akin tana tambayar wanene,
Ganin azmee yasa tayi saurin gaishe da ita cikin girmamawa,
Azmee da nan take ta gane ba sehrish bace tace"kiyi hakuri na tashe ki kina bacci,Sehrish nake nema,dan Allah ki sanar da ita cewa SGR yana nemanta a part É—insa,"
Jahad tace"tayi bacci,bari na tashe ta,"tayi maganar tare da juyawa cikin sauri ta shiga cikin É—akin,
Wucewa azmee tayi ta koma kitchen,cike da zullumin mai zai biyo ba idan Sehrish ta sanar ma Sgr cewa Uncle abusufyan ne ya hanata yin aiki a part É—insa,tabbas za'a kwashi Æ´an kwallo,
"Sehrish!ki tashi babban yaya yana son ganinki a part ɗinsa,dan Allah ki tashi kije,"jahad ce keta kokarin tashinta daga bacci,sehrish kuwa sai faman mutsu mutsu takeyi,daƙyar ta iya cewa"Wanene ke nema ne'?
Jahad tace"babban yaya,"
Jin sunanshi yasa Sehrish buÉ—e idanunta ta wurgasu kan jahad dake tsaye,yatsina fuska tayi tare da maimaita sunan nashi"babban yaya?shike nema na,waya faÉ—a maki"?
"Aunty azmee,yanzun nan bata jima da tafiya ba,naga kamar ma bata acikin natsuwarta,"
Jin hakan yasa gaban sehrish faɗuwa rass,yunkurawa tayi tare da mikewa zaune,ta saukko da ƙafafunta ƙasa,kafin ta miƙe tsaye,saboda tsabar saurin ta fita ko Mayafi bata ɗauka ba,gashi kanta ko kallabi babu,sumar kanta ce da tasha gyara,an mayar mata da gashin mai gazar gazar ya sauko har kafaɗarta,a hankali gashin kan nata ke toho yana fitowa,har ta launin gashin anyi mata dying dinsa ya koma 2 colour,Kayan bacci ne ajikinta riga da wando sharara suke,farare masu laushin gaske,irin waɗanda kana sanyasu ajikinka,Ko baka jin bacci nan take zai zo maka,
Tunkan ta ƙarasa shiga falon nashi take jin ɗar ɗar acikin zuciyarta,tun jiya rabon da ta sanyashi acikin idanunta,daƙyar ta iya yi mashi sallama tare da kutsa kai cikin falon nashi,bai amsa sallamarta ba,har ta ƙarasa inda yake,atsaye muryarta na rawa tace"Gani,"bai dago ba kuma bai tanka mata ba,sae ma cigaba da danna system ɗinshi da yake yi,lokaci bayan lokaci yakan kai hannunshi ya dauki Coffee ya kur6a,zuba mashi ido tayi tana kallon kyakkyawar fuskarshi,ba ƙaramin kewarshi tayi ba,sam batayi tunanin ma zai nemeta ba,
sai da ta ƙara cewa"babban yaya gani,Aunty azmee tace kana kira na,"sannan ya soma magana anatse"yau da safe,meya hanaki zuwa part ɗina"?
Shiru tayi gabanta na faÉ—uwa,batasan amsar da zata bashi ba,saboda tsoran abunda zai biyo baya,
"Kinsan bana maimaita magana,amsarki nake jira,"
Runtse idanunta tayi aranta tana fadin"nashiga uku,!Allah ka kawomin ɗauki,bansan me zan faɗa masa ba,"shirun da tayi mashi ne ya fusata shi,aikuwa a zafafe ya daka mata tsawa,har sai da ta zura da gudu saboda yarda ta tsorata,kama hanyar fita tayi saboda ruɗewar da tayi,hakan yasa ya miƙe tsaye tare da bin bayanta,ruƙo hannunta yayi tare da fusgota ta dawo saitin shi,Waro ido waje tayi tare da ja da baya da baya,har suka ƙure ma bangon,runtse idonta tayi muryarta na kerma tashiga faɗin"Am so sorry babban yaya,I can explain,zan faɗa maka,"
A hankali ya ware blue eyes ɗinshi akan fuskarta,sumar kanta yabi da kallo,yayi mamakin ganin yadda gashin yayi tsayi cikin ƙankanin lokaci har ya kamo kafaɗarta,gyaran gashin da akayi mata ya ƙara fiddo da kyawun fuskarta,mayar da idanunshi yayi akan La66anta dake ta faman kerma duk tabi ta gigice,lokaci guda ya tsinci kanshi cikin wani irin yanayi mara misaltuwa,moving ya ƙarayi gaba ɗaya yayi mata rumfa da faffaɗan ƙirjinshi,lokacin da taji tsinin hancinshi na gogar nata,nan take gabanta ya kuma bugawa daramm,jikinta ya shiga yin kerma ta ko'ina,gaba ɗaya duk tabi ta susuce har lokacin ta gaza buɗe idanunta saboda tsabar tsoro,jin saukar hannunshi asaman ƙirjinta yasa ta yin saurin ware idanunta arazane,kai tsaye suka sauka cikin nashi,face to face,Eyes to eyes,nose to nose,mouth to mouth!!,
A firgice ta janye idanunta daga kan fuskarshi ta mayar dasu akan ƙirjinta,Ashe gaban rigarta ne ta bari a buɗe ta manta bata sanya links ɗin rigar ba,Shine ya sanya hannunshi a wurin yana manne mata su,jurewa kawai takeyi amma ba ƙaramin yanayi Sgr ya jefa mata ba,musamman yadda hannunshi ke nutsewa a cikin boobs ɗinta,ba ita kaɗae ba,hatta shi kanshi daya kai hannunshi wurin saida yayi regretting,saboda wani abu daya dinga jin yana fisgarshi yadda kasan magnet,mayen karfe ba,
daƙyar ya iya zame hannunshi daga saman ƙirjin nata,bayan ya kammala sanya mata links ɗin,Sannan cikin sanyin murya yace"tell me the reason why baki zo yi mun aiki da safe ba!bakisan bana son sharing a aiki na ba!?
Magana yakeyi amma idanunshi sae ƙokarin lumshewa sukeyi tamkar mai jin bacci,wanda kuma ba kowa ne yajawo hakan ba face Sehrish,
Cikin en ena tace"Kayi haƙuri ba laifina bane,Daddy ne ya hanani zuwa"
Cike da mamaki yace"Kina nufin Uncle ne ya hanaki zuwa,"
Jinjina mashi kai tayi alamar eh,yayin da take ta faman haÉ—iyar yawu,
. "just without any reason ya hanaki aiki a ƙarƙashi na"?
daga mashi kai tayi alamar eh,
Cije pink lips ɗinsa yayi tare da tsoma hannunshi acikin sumar kanshi yana cakuɗata,ranshi a matuƙar 6ace yace"hakan bazai ta6a yiyuwa ba,dole kiyi aiki a ƙarƙashina!ban damu da matsayinshi a wurinki ba,dole ne ayimun biyayya!!!!!!!!*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.