Trending Hausa Novels

Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel By Hafsat Bature

Reading file: Abban Sojojin Takun Karshe.txt

Chapter 32 of 46

  *Boss Bature*

    🤍❤🤍
Washe Gari,

Kwance take asaman katifarsu,ta saki baki tana ta sharar baccinta,sae faman jan minshari takeyi kamar Ragon layya ga miyan bacci dake gangarowa ta cikin bakinta da ta bari a buɗe,tana cikin baccin nan taji Ringing ɗin wayarta da ƙarfin gaske har cikin dodon kunnanta,hannu tasa tare da toshe kunnanta tana faman buga tsoki,alamar an takura mata,bata ɗaga kiran ba,har ya katse kuma sai ga wani kiran ya ƙara shigowa,a hargitse Abra ta miƙe ranta a matuƙar 6ace,tasa hannu ta dauki wayar dake ajiye gefenta,picking call ɗin tayi tare da kara wayar a kunnanta Cike da masifa tace"Wai Uban wanene ke kirana tunda sanyin safiya"?
  Kafin ta rufe bakinta taji ance"Ubanki ne!" har sai da gaban abrah ya faɗi rasss,cikin sauri ta janye wayar daga kunnanta tare da kallon screen ɗin wayar don ta shaida mai kiran nata,Sunan Aunty babba ta gani,yatsina fuska tayi kafin ta mayar da wayar a kunnanta,"ina kwana aunty,an tashi lafiya"
  Rai a6ace Aunty babba tace"Ruƙe gaisuwarki,sakarya daƙiƙiya zaman uban mi kike ke da Mammy da har kuka bari AMAL ta gudo daga mai duguri tazo Abuja wurin Amani?!" jin wannan maganar yasa abrah ta zabura,don har sai da ta daki ƙirjinta da hannunta,Hankali atashe tace"Aunty laila dagaske Amal tana abuja wurin Amani!"
  "Ƙarya zan maki ne?Kuna nan sake da baki har yarinya ƙarama tayi maku wayau ta gudu,Yanzu baki ga yadda Amal ta koma ba,Yarinya ta zama ƴar hutu kamar wadda ta taso a gidan naira,Tamkar bata ta6a shan wahala ba,Irin rayuwar dana so ace ke kika same ta,sae gashi ƴar kishiyar da muka tsana ita ta samu wannan damar,ina nan dake in har mu kayi sake AMAL sai ta auri ɗaya daga cikin ƴa'ƴan Alexandra,"
  Saboda tsabar takaici Hannu ɗaya abra ta aza asaman kanta tana faɗin"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'Un!
Aunty babba tace"kaÉ—an ma kika gani!duk laifinku ne!da alama su Amani sunfi mu Jinin Nasara,shiyasa suke ta cin galaba akan mu,"
  Muryar abra tamkar zatayi kuka tace"Wlh aunty laila har shawara sai da naba mammy tun kafin amal ta gudu nace mata mu 6alle ƙafarta guda ɗaya,don ta zama gurguwa kinga in mukayi hakan ba yadda za'ae ta gudu,Amma saboda shegen son kuɗi irin na mammy tace Wai mu barta da ƙafafunta,saboda tana so Amal ta auri mai kuɗi don ta rinƙa tatso mana kuɗi a wurinta,Yanzu gashi nan Mammy taja mana"
  Shiru suka ɗanyi na wani lokaci kafin Aunty babba tace"Abra inaso kiyi gaggawar tattara kayanki kibar gidan nan!kema ki dawo Abuja gidan surukanmu da zama!wannan kaɗae ce hanyar da zamu iya cin nasara akansu,"
  "Aunty in dawo nan fa kika ce?Aunty hayaam fa?zata dawo gida ne"?
"Bazata dawo ba,zama ma yanzu ta fara shi har sai an shafa fatihar aurenta da Babban yayansu,kawai abunda nakeso dake,ki tattara kayanki ki dawo gidan da zama,saboda ni bani da tabbacin cewar zama na zaiyiyu acikinsa,atakure nake,"
  Jinjina kai Abra tayi tamkar tana agabanta tace"Shikenan Aunty laila,da yaushe kikeso inzo nan ne?kuma ya zamuyi da mammy?kinsan fa bata da lafiya tana can kwance,"
  Dogon tsoki Aunty babba taja tare da cewa"Wake ta wani mammy?ae kawai ki tattara kayanki yanzun nan ki biyo motar Abuja ta kawoki,Ita kuma mammy Allah ya bata lafiya shine kawai,"
  Fuskar Abra ɗauke da murmushi tace"aikuwa yanzun nan zan shirya,zan ma iya sa ɗaya daga cikin samari na,ya kawoni gidan don duk suna da Mota,"
  Aunty babba tace"Yawwa cikin sauƙi ma,ki kira ɗaya daga cikinsu,ya kawoki,"
  "In sha Allah Auntyna," abra ta amsa mata kafin sukayi sallama,

Duk wannan wayar da Aunty babba keyi kaf a kunnan Hafsat da hayaam dake kwance saman gado,ita kuma tana zaune asaman Stool dake agaban mirror,
   "Mommy wannan abun kunyar har ina?taya zaki ce abra tadawo gidan nan da zama?bayan ga hayaam kuma!Nan fa gidan surukanku ne ba gidan ƙanin mahaifinku ba...." a fusace Aunty babba ta jefa ma hafsat wayar hannunta cikin sa'a tasamu gefen goshinta,dafe wurin hafsat tayi saboda zafin da taji,
  Rai a6ace tace"Hafsat ki fita daga idona in rufe!kina yimun shisshigi acikin lamurrana,Ina ruwanki da zaman su Abra acikin gidan nan?ke zaki ciyar dasu ne?ko saman kanki zasu zauna ne"?
  Shiru hafsat tayi batare da ta tanka mata ba,hayaam dae bata sanya masu baki ba,saboda gudun rashin kunyar hafsat don bata raga ma kowa acikinsu,

Wuraren ƙarfe tara,Azmee da Saude suka kammala girke girken breakfast na gidan,yanzu ta samu sauƙi wurin yin aiki don Saude ba ƙaramin taimaka mata takeyi ba,dayake itama kwararriyace wurin iya girki tana son yin girki,bayan sun kammala,Azmee ta shiga jera mata Warmers acikin tray tana kaiwa saman dining table,cikin lokaci ƙanƙani suka kammala jera abincin,

É—aya bayan É—aya matasan gidan suka shiga fitowa daga bedroom É—insu,su Kanal yousouf,Irfan jabeer khaleed twins,fawan,sune waÉ—anda suka fara hallara daga baya,Abbansu tare da Mommynsu junaid suka fito,kafin wani lokaci kowa ya fito,hadasu Dr haris su Captain adam,najeeb talal da kuma junaid,da sauransu duka dai,Mutun É—aya ne bai fito ba,bakowa bane fa ce Surgeon general Rafayet,

Bayan matasan sun hallara Azmee taje É—akinsu Sehrish ta taso su daga bacci,atare suka fito bayan sunyi brush su uku kowacce sanye da hijabi ajikinta,tun ta sallar asuba ce da suka sanya ajikinsu basu cireta ba,bacci yayi awon gaba dasu,
  Gaishe dasu Abba suka fara yi,fuskar kowannansu ɗauke da murmushi haka suka shiga amsa masu gaisuwar,daga bisani suka shiga gaisar da yayyensu,kowa da irin yadda yake amsa masu gaisuwar cike da zolaya,don wasu ma hada kwaikwayon Muryarsu,hakan ba ƙaramin nishaɗi ya sanyasu ba,

Komawa su kayi tare da samun wuri suka zauna a dining chairs É—in da Abusufyan ke zaune,atare suka haÉ—a baki wurin cewa"Daddy ina kwana?ka tashi lafiya,"
É—agowa yayi tare da kallon fuskokinsu É—aya bayan É—aya kafin yace"Lafiyalou Alhamdulillah!"

Natsuwa kowa yayi,yayin da Azmee da saude suka shiga zuzzuba masu abincin,kowa na faÉ—in abunda yake so yaci,
  Gyaran murya Abba yayi tare da kallon azmee yace"An kai ma Ammi nata breakfast ɗin"!?
  azmee tace"Eh nakai masu,a ɗakin gwaggo don acan tace mun zatayi kalacinta,ita da ƴar uwarta,"
  Murmushi ya ɗan yi don ba ƙaramin daɗi yaji ba,
  "Azeema fa"? Ya kuma tambayarta,
"Itama tana atare dasu,can É—akin gwaggon,"
Jinjina kai abba yayi kafin ya kuma cewa"Aunty saratu fa?da Æ´anmatan ta suma ankai masu nasu"?
  Saude ce ta kar6e da cewa"Ni nakai masu a ɗakinsu,"
  Abba yace"Aikin ku yayi kyau,"ya ƙarasa maganar tare da kai hannu ya ɗauki plate ɗin dake hannunsa yaci gaba da cin abincinsa da azmee ta zuba mashi,
  Abbas yace"Azmee banga su Amal ba?ko ankai masu nasu ne"?yayi maganar ayayin da yake ƙoƙarin ajiye spoon ɗin dake hannunshi,?
      "Na kai masu a bedroom ɗinsu," ta bashi amsa,
  Ganin Abbas ya tambayi iyalinsa ne yasa Ishaq yin gyaran murya yace"Azmee wai ni ina ƴata hafsat ne?ko an manta dasu ne?naga ban gansu ba!?
  "Ni kaina inata so in tambayesu,tun shekaran jiya rabon da in Sanya su a cikin idona,tamkar basa a cikin gidan nan"!Acewar Abbansu,
  "Bari na kirasu,"Azmee ta faɗi hakan tare da juyawa ta nufi ɗakinsu laila,
  abinci take ci,amma hankalinta ba akwance yake ba,Yau tunda ta tashi daga bacci gabanta ke ta faɗuwa rasss!rasss!mafi yawancin lokutta in taji gabanta na yawan faɗuwa to tabbas wani abune zai faru da ita!mai kyau ko mara kyau,sam takasa cin abincinta,sae faman jujjuya cokalin hannunta takeyi acikin plate ɗin dake agabanta,
   A hankali ta ɗago da idanunta tare da azasu akan Hosana dake ta faman cunkusa Burger acikin bakinta,yadda kasan zata 6ara bakin ko gajiya da Ci ba tayi,Allah sarki rayuwa kenan,Allah mai yadda yaso,kamar basu bane waɗannan yaran ba,masu yawo babu takalmi a ƙafafunsu,kawunansu babu ɗan kwali,Kayan jikinsu duk a yayyage,babu mai son su,rayuwarsu a wulaƙance kowa gudunsu yakeyi,Amma yanzu komai ya canza!Yanzu gasu acikin danginsu,kowa sonsu yakeyi,suci mai kyau su sha mai kyau,su kwana a mai kyau,suturar sawa ma sai sun za6i wadda suke so su sanya ajikinsu,duk mai yajawo wannan, haƙuri!sun rungumi ƙaddararsu sun cinye jarabawar da Allah yayi masu,basuyi gajan haƙuri ba,kullum cikin kai kukan su wurin Allah suke,saboda sun san cewa shi kaɗai ne zai iya share masu hawayensu,duk irin ƙuncin rayuwar dasu Sehrish suka shiga,basu ta6a ƙasƙantar da kansu ba don suyi bara,ko su siyar da mutuncinsu don su samu kuɗi,kamar yadda wasu mutanen keyi,

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.