Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel By Hafsat Bature
Reading file: Abban Sojojin Takun Karshe.txt
Chapter 11 of 46
Bayan hafsat ta katse kiran,ta Kifa kanta asaman pillow ɗinta,tare da fashewa da wani irin matsanancin kuka,dama ance dana sani ƙeya ce,
Farkawa Aunty babba tayi da wata irin matsiyaciyar yunwa,sae faman hamma takeyi,tashi tayi daga zaune tare da kai hannu ta É—auki wayarta tana cewa"Ko hayam ta tura mun da hoton?bari na duba na gani,Allah yasa dai bata manta ba,"
 shiga cikin whatsapp ɗinta tayi tare da duba chat ɗinsu da hayaam,rai a6ace taja dogon tsoki tare da cewa"Wai dama bata turamun hoton ba!harfa ƙara nanata mata nayi akan ta tura mun hoton amma bata turo ba," ta ƙarasa maganar tare da yin wurgi da wayar saman gadon,
 Saukowa tayi daga saman gadon,fita tayi daga cikin bedroom din ta sauko ƙasa,kai tsaye ta nufi kitchen,
 Batare da 6ata lokaci ba,ta shiga harhaɗa kayan da zatayi amfani dasu,bayan ta ɗaura girkin,ta ɗebo snacks a plate ta haɗo da coke mai sanyi ta dawo falo,ta zauna,tana ci tana kallo a plasma hankalinta kwance,
jin motsin mutun a gefenta yasa tayi firgit tare da juyawa don taga wanene,ashe hafsat ce atsaye yanayinta kamar na wadda tayi amai da zawo,fuskar nan tayi gwanin ban tausayi,idanunta sun ƙankance saboda kukan da tasha,
 "Hafsat!lafiya naga fuskarki tayi jawur?kinyi kuka ne"?
 Girgiza kai hafsat tayi tare da cewa"Babu komai mommy,wani film nake kallo acikin wayata,shine ya sanya ni kuka,"
 Tsoki Aunty babba taja"shirmen banza,kawai daga kallon film saiki kama kuka kamar wata sakarya,"
 murmushin takaici hafsat tayi tare da samun wuri daga gefen aunty babba ta zauna,batare da tace komai ba,
  Aunty babba taci gaba da cewa"gaskiya kowane film ne wannan ya ciri tuta tunda har ya iya sanyaki zubar da hawayenki,yadda kike da shegen taurin kai,
   "Mommy ba zaki gane bane,"
"Taya za'ae in gane?tunda bakiyi mun bayanin meya faru ,acikin film É—in ba,ki É—an bani labari mana,"
 Gyara zama hafsat tayi kafin ta soma bata labarin kamar haka"wata matace fa,mijinta ya kawo mata wasu marayun yara donta rainesu a wurinta,tun ranar da mijin ya kawosu gidan shi kuma yayi tafiya,ae kuwa matar nan,ta shiga gana masu azaba,ta hanasu abinci yunwa kamar zata kashesu,har bugunsu takeyi,sannan kuma ta dinga sanyasu aikin wahala,har saida suka kusa rasa rayuwarsu,mommy kinsan meya faru"?
 Dakatawa Aunty babba tayi daga shan lemun hannunta da takeyi tace"a'a saikin faɗa,"
 "Hmmm,Mommy ƙarshe fa matar nan,tasa aka kwashe yaran nan,aka 6atar dasu saboda kawai kar asirinta ya tonu a wurin mijinta...'
 "Hakan da tayi yayi mun dai dai,"Acewar aunty babba,
Murmushi hafsa tayi kamin tace"Ae ban ƙarasa maki labarin film ɗin ba,bayan tasa an zubar da yaran nan,ita duk a tunaninta sun mutu ma,Ashe can wurin gararin rayuwar da sukeyi a daji Allah ya haɗasu da kanin mijinta har ya taimakesu ya kaisu gidansu mijin,da akayi bincike aka gano cewar yaran ƴa'ƴan kawunsu ne wato ƙanin mahaifinsu,"
 Aunty babba tace"tashin hankali!ita ko wannan ya zatayi da kanta?
 Dariya hafsat tayi tare da cewa"Nima abunda nake tunani kenan!amma Mommy idan kece ya zakiyi,"
 shiru Aunty babba tayi tana tunani kafin daga bisani tace"Ae kawai tunkan asirina ya tonu zan gudu ne,a neme ni arasa,amma nikam hafsat wai ya sunan Film ɗin nan ne?tayi tambayar tare da kallon hafsat ɗin wadda itama kallonta takeyi,mikewa hafsat tayi tsaye tare da cewa"An fara kiran sallar magriba,bari naje nayi salla,"
 "Amma baki faɗamun sunan film ɗin ba!"Aunty babba ce ta sake nanata mata tambayar da tayi mata,
   *AN YANKA TA TASHI* shine sunan film ɗin mommy,yanzu na kalleshi a tashar youtube,tana kai ƙarshen maganarta,ta juya da sauri ta wuce bedroom ɗinta,
 Zugudum Aunty babba tayi tana maimaita sunan film ɗin da hafsat ta faɗa mata,wato An yanka ta tashi,
 Aranta tace"gaskiya ya kamata in kalli film ɗin nan,Inaso inga yadda matar nan zata ƙare,ko ya mijinta zaiyi da ita?tabɗijancan,akwai badaƙala,"tayi maganar tare da mikewa ta wuce kitchen domin ta duba girkin da ta ɗaura,
Bayan ta kuma fitowa daga kitchen ɗin,upstairs ta wuce bedroom ɗinta,gefen gadon ta zauna tare da miƙa hannunta ajikin drawer chest ta janyo gidan farko,sabon sim ne ta ɗauko tare da daukar wayarta dake ajiye saman gadon,zura sim card ɗin tayi aciki,sannan ta lalubo lambar wayar Ammi wadda tayi copying kan phone,danna mata kira tayi,nan take kiran ya shiga,kusan sau uku kiran na katsewa batare da anyi picking ɗinsa ba,tana kira a karo na hutu Ammi ta ɗaga kiran 😳
ɗan zaro ido Aunty babba tayi kafin ta gyara natsuwarta tare da zabga sallama"Assalamu Alaikum Ammi barka da warhaka,"ta maƙe muryarta yadda ammi bazata iya gane muryar wacece ba,
 on the other hand Ammi ta amsa mata da cewa"Wa'alaikumus salam,barkanki dai,zan iya sanin dawa nake magana"a dake take magana,
Aunty babba tace"Nasan bakisan dawa kike magana ba,saboda baki sanni ba,Ni matar abokin Abusufyan ce,wadda ke zaune a ƙasar turkey,"
 Shiru ammi tayi tana sauraran me magana,
 Aunty babba taci gaba da cewa"akwai wani mummunan abu da abusufyan ya aikata a 6oye baison kowa ya sani,shiyasa na kira don in sanar dake,don banason abunda zai ta6a mutuncin family ɗinku,wannan abun kunya ne,muddin ya fita waje mutane sukaji to fa,zaku rasa duk wata ƙima da martaba da kuke da ita....'
 tana cikin magana Ammi ta dakatar da ita"Ya isa haka!banason wata kwanana,ki faɗamun abunda kikeson sanar dani!me Abusufyan ya aikata?wani laifi ne wannan da har kike ikirarin zai ta6a ƙimar family ɗinmu a idon jama'a,"?
 Wani irin wahalallen yawu aunty babba ta haɗiye kafin daƙyar ta soma kora mata jawabi kamar haka
  "Shekarun baya da dadewa,Abusufyan yayi ma wata fyaɗe,harta samu ciki....."
 Wata irin tsawa da Ammi ta daka mata har sae da takusa sakin fitsari a wando,a tsiwace tace"Dakata!ki iya bakinki!kinaso ki shiga tsakanina da ɗana ne!wacece ke,kada kiyi tunanin kin kirani da 6oyayyiyar number,zan iya sa agano munke duk inda kike,"
 Muryar Aunty babba na kerma tashiga faɗin"wlh dagaske nake ammi ba ƙarya nake ba,gobe idan kinzo abuja wurin walima,zaki ga yaran,ae suna nan gidan Abba,Sun jima suna 6oye maki gaskiya,saboda tsoron hukuncin da zaki yanke ma Abusufyan,yanzu haka maganar da nake maki,sun gama shirya yi maki ƙaryar cewar yaran ba shaggu bane ta hanyar aure aka haife su bayan ba haka bane,suna nan yaran ƴan uku ne mata,sun girma sosai,' tana kai ƙarshen maganar Ammi tace"Kin gama"?
 Shiru Aunty babba tayi tana faman mazurai aranta tace"Wannan tsohuwa badae taurin kai ba,bansan ya zanyi na fahimtar da ita ba,ta cika jaraba,"
 tana cikin wannan zancen zucin Ammi ta katse kiran,
 Wurgi Aunty babba tayi da wayarta,tare da mikewa tana cewa"Ae shikenan,nasan cewa gobe tana ganin yaran zata tuna da kalamai na,daga nan saita ɗauki hukuncin daya dace,"
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.