Trending Hausa Novels

Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel By Hafsat Bature

Reading file: Abban Sojojin Takun Karshe.txt

Chapter 23 of 46

*Boss Bature*
The genius

  ❤🤍❤

bari mu leƙa falo muga meke wakana,shin ansamu cigaba ko kuwa ana nan yadda ake?

Natsuwa su kayi gaba É—ayansu,wurin yayi tsit tamkar mutuwa ta gifta,kowa ya natsu ya nabba'a tamkar É—alibai ne agaban ya sayyadi,bafa sayyadi mijin abu ba,ina nufin malami,kar ayimun wata fahimta,

"WaÉ—annan sune Æ´an ukun Abusufyan É—in"modibbo ne yayi maganar yayin da idanunshi ke akan Su jahad dake zaune sunyi zuru zuru,'
  Har suna haɗa baki wurin cewa"Sune,"
Jinjina kai yayi tare da mayar da idanunshi kan Ammi yace"Ki kace yaran shaggu ne ko?Wata hujja gare ki na cewar bada aure ya haifesu ba?
  Fuskarta aɗaure tace"Ina da hujja,saboda nice mahaifiyarshi,kuma ni bansan an ɗaura mashi aure da kowa ba,"
  Girgiza kai modibbo yayi,sannan yace"hannunki ya taso ne?ko kuwa wurin ki kaɗae za'a iya ɗaura mashi aure ne"?
  Shiru tayi batace masa uffan ba,cigaba da magana yayi"don haka baki da wata hujja ta cewar abusufyan yayi aure ko baiyi aure ba,ya samu ƴa'ƴa,wlh Aisha kin ban mamaki!wai har yaushe ne zaki ajiye waɗannan makaman yaƙin naki ne?ke fa yanzu ba yarinya bace,kin tara ya'ya da jikoki amma har yau bazaki ajiye wannan zafin ran naki ba,sai yaushe ne ya'yanki da kuma jikokinki zasu ji daɗin zama dake ne?yanzu ni ba misali bane agareki?ko bakisan wanene modibbo ba?kinfi kowa sanina bani da wasa ko miskala zarratin,duk wani kangararre acikinku,keda ƴan uwanki nine nan nake tankwarashi,amma yanzu saboda na manyata,na tara ya'ya da jikoki,duk na ajiye waɗannan ɗabi'un,Na canza kaina ne ba don komai ba sai don saboda ya'yana da kuma jikokina suji daɗin zama dani,kuma suyi alfahari dani amatsayina na kakansu,bawai su dinga tsoro na ba,suna gudu na harma su dinga yi mun fatan mutuwa,kamar ke ɗin nan dai.....'yayi maganar yana nuna ta da sandar hannunshi,sunnar dakai Ammi tayi tana faman jinjina kai,

Canza harshe modibbo yayi izuwa harshen fulatanci,yayi hakan ne saboda kada faÉ—an da zaiyi mata ya zama tamkar tozarci ne agaban jikokinta,

  "Gaba ɗaya kin takurawa rayuwar ya'yanki,da ta jikokinki,kin hanasu sakat,ko irin wasan dake tsakanin kaka da jikan nan bakya yi masu,kullum burinki ki ƙuntata rayuwarsu,shin menene ribarki idan kinyi hakan? Ya ɗan dakata da maganar yana kallonta,kafin yaci gaba da cewa"Yanzu jibi yaran nan ƴan wurin fatima,hakanan kika ɗaura karan tsana kika ɗaura masu sai kace ba jininki ba!in ma saboda mahaifiyarsu ne,ke kin ta6a ganin inda laifin wani ke shafar wani ne?in kuwa haka ne ae da dukkanmu mun shiga uku,saboda wancan zaiyi sata ne a ɗaura maka laifin bayan bakai ne ka aikata ba,"
  Katse shi tayi cikin harshen fulatanci tace"Amma yaya modibbo ni meyasa ya'yana basu jin maganata ne?basu ɗaukeni mahaifiyarsu ba,suna yin abu gamon kansu batare da sun sanar mun ba,Hossein ya ƙetare ƙasar nan yaje yayi aure batare da sani na ba,sai dai kawai na ganshi da mata ya dawomin,matar kuma ma farar fata ba jinsun mu ba,sannan kuma Abusufyan shima yayi aure batare da sani na ba,saboda me zasuyi mun haka ne?
anzo dai dai wajen,acewar modibbo gyara zama yayi sannan yace"kin manta yadda akai kika auri salahuddeen ne?to idan kin manta bari na tuna maki,dama duk wanda ya bijire ma iyayensa ko ba daɗe ko ba jima sai shima yaga ba dai dai ba,na farko bada sa hannun iyayenmu ba,kika shiga aikin Soja,babu irin yadda ba'ayi dake ba don ana ganin bai dace dake ba,ba kaman daya kasance ke bafullatana ce,amma kika ƙeƙashe ƙasa kikace sai kinyi aikin soja,a ƙarshe da aka takura maki,shine kika tattara kayan ki kika dawo gidana da zama saboda kina tunanin cewar ni zan goya maki baya don ki samu abunda kikeso,da kika zo wurina a lokacin na nuna cewar nima bazansa hannu na ba acikin lamarin tunda har iyayenmu sun nuna basu so,a ƙarshe sai kika gudu batare da sanin kowa ba,kika shiga aikin Soja,sae dai kwatsam muka ganki da kakin Soja ajikinki,ko ba haka akayi ba"?

Wata irin zufa ce ta shiga wankowa a fuskar Ammi sam bata ta6a tsammanin cewa wannan ƙaramin kuskuren data aikata na bijirema iyayensu,zai dinga bibiyar rayuwarta bane,
"Akan wannan aikin sojan da kika shiga,babu wanda baiyi kuka dake ba,saboda kafiya,da taurin kai irin naki,ga jinkai dake gareki,iyayenmu basu isa su baki umarni kai tsaye kiyi abu ba,sai sun biyo ta wurina saboda shakkarki da suke ji,bayan wannan kuma,baki sanar ma kowa ba game da salahuddeen lokacin da kuka fara soyayya dashi ba,sai daga baya ne muka fahimci shi ya hure maki kunne har kika bijire mana kika shiga aikin sojan,hakan kuma yasa duk muka ki amincewa da farko ki aure shi,amman da yake Allah ya kaddaro aure tsakaninku ba yadda muka iya dole muka kyale ki ko don kafewar da kika yi da kuma rabon itama Ameena anan zata samu mijin, ko ba haka akayi ba"?
  Jinjina kai Ammi tashiga yi yayin da idanunta suka cicciko tab da kwalla amma bata bari sun zuba ba,
Gwaggon katsina kuwa,sae faman sakin murmushi takeyi,tana faÉ—in"kwarai kuwa,haka akayi,"Abban su junaid kuwa da hajiya azeema duk jikinsu yayi mugun sanyi,sae yanzu suka gane daga inda matsalar take,dama duk in mutun yaga rayuwarshi tana tafiya ba dai dai ba,kuma bai akaita wani zunubi,toWlh ya binciki kanshi!ya tuhumi kanshi ahankali zai gano dalili,

Su jahad dae suna nan tsugunne sun kasa kunne suna sauraronsu,sai dai subi bakin modibbo da kallo,daga bisani in Ammi na magana subi ta da kallo saboda basu iya fulatanci ba,haka Marshal Omar dasu ishaq duk basa jin fulatanci,haka zalika Sgr baya jin harshen nasu,dama shi ko hausa daƙyar ya koye ta,kuma har yau in yana magana da harshen hausa sai ka gane cewar ɗan koyo ne don sam hausarsa bata nuna ba shiyasa bai fiye yin magana da hausa zalla ba saiya haɗa da turanci ko spanish,amma kuma hausar tashi ba ƙaramin daɗi takeyi ma mutane ba,

  Murmushi Modibbo ya ɗan saki kafin yaci gaba da cewa"ina fata yanzu kin tuna komai"?
  Siraran hawayen da take 6oyewa ne suka gangaro a saman fuskarta,muryarta ƙasa ƙasa tace"Na tuna,"
  Modibbo yace"Tunda kin tuna bari na ƙara ɗaura ki akan hanya,irin abunda kika aikata ne yasa shima ɗan cikinki da kika haifa yaje yayi aure batare da saninki ba,saboda gudun kada ya fara sanar dake ki hana shi yin auren,hossein ya auri Alala..kunzandariya...."kasa ƙarasa maganar yayi saboda bai iya ambaton sunanta ba,abun yaso yaba Sgr dariya,amma ya basar da ita tare da gyara mashi sunan yace"Alexandra ne sunan,"
Modibbo yace"yawwa ɗan gari,bazan dai iya Ambaton sunan nata ba,a barshi a fatima,tunda ae ta ta6a musulunta,kuma muna sa ran zata ƙara musulunta insha Allah,"
  Suka ɗanyi dariya,kafin ya ɗaura da cewar"Hossein ya auri fatima batare da saninki ba,saboda yasan halinki sarai kin tsani jinsin da ba naki ba,gudun kar ya sanar dake kiƙi amince masa yasa shi yin hakan,sannan......"modibbo bai ƙarasa maganar ba,ammi ta kuma katse mashi hanzarinshi da cewa"Yaya modibbo amma ae ni harsu biyu sukayi mun haka!bayan ni,ni kaɗai ce na bijire ma iyayenmu haka,"
  wannan maganar ta Ammi yasa shi yin dariya,tare da girgiza kai yace"in kikayi wata maganar kina tunamin da ƙuruciyarki wlh,dama ita irin sakayyar nan tamkar ramuwar gayya haka take,kuma ita ramuwar gayya tafi ta gayyar zafi,sakamakon abunda kika shuka ne,yasa kika girbi kyakkyawan sakamakon da ya zarta nakin,kuma tunda har kika iya ƙyale hossein bayan laifin daya aikata maki na auren bare kuma farar fata ae yaci ace kin yafe ma Abusufyan tunda shi da ƙuruciyarshi ya auri yarinyar,kuma hada sa hannun gwaggonshi,kuma kinsan wacece ita a wurinki,da mahaifinmu da nata uwa daya uba daya,kuma saboda yardar da kikayi da itane yasa kika damƙa mata amanarshi,ita kuma ƙaunar da take yi maki ne ya shafi ɗanki da kika haifa,hakan yasa ba zataso wani abu ya cutar dashi ba,Yaro ya nuna yana son ƴar mai gadin gidansu,ke kuma kin tsani auren bare mara asali,gashi shi kuma yaron ya kwallafa rai akan yarinyar,don lokacin da ita Aminatu taso ta sanar dake game da yarinyar balbaleta kikayi da masifa,kina cewa karta kuskura ta bari alaƙarsu tayi nisa,ta raba tsakaninshi da yarinyar,a ranar saida Abusufyan ya suma jin za'a raba shi da abunda yakeso,wannan dalilin ne yasa hajiya ameenatu ta aura mashi yarinyar batare da ta sanarma kowa ba,sai ni ɗinnan da nake magana,"
  ɗagowa Ammi tayi tana kallonshi cike da mamaki,
  Jaddada mata maganar yayi"kwarai kuwa ta sanar dani,nasan da zancen auren,kuma aranar da aka ɗaura auren Abusufyan da zainabu abu,ina ɗaya daga cikin waɗanda suka halarci ɗaurin auren batare da sanin kowa ba,ita kanta hajiya ameenatu batasan na halarci ɗaurin auren nasu ba,a iya waya kawai ta sanar dani,sae kuma akaci sa'a ina da wani taron manyan malamai da zamu halarta anan jihar kano,wannan ne babban maƙasudin daya kaini garin harna shaida wannan ɗaurin auren....."
Ae tunkan modibbo yakai ƙarshen maganar wani irin murmushin farin ciki ya bayyana akan fuskar kowannansu,saboda yayi maganar ne cikin harshen da zasuji,wata irin nauyayyiyar ajiyar zuciya abusufyan ya shiga saukewa,nan take yaji wani irin sanyi ya ratsa zuciyarshi,duk da yayi mamakin zuwan modibbo wurin ɗaurin auran nashi saboda bai ganshi ba,amma tunawa da irin dubban al'ummar dake a masallacin kuma ya kasance ranar juma'a ne ana kammala salla aka ɗaura auren nasu,tabbas bazai iya tantance kowa dake a wurin ba,amma ko a lokacin bayan an ɗaura auren sun koma gida sai da baba buzu ya kirashi gefe guda yake sanar dashi cewa"Wani babban malami,yayi mashi alheri bayan sun fito daga masallaci,kuma yana tunanin cewar Kamar jininsu ne saboda yaga kamannin Hajiya ameena a fuskarshi,a lokacin Abusufyan bai gane wanene ba,sai yau da modibbo yayi maganar nan kwatsam ya zancen ya faɗo mashi aranshi bayan ya shiga zurfin tunani,tabbas kuwa modibbo ne,
  Murmushi modibbo yayi tare da kallon Abusufyan yace"nasan zakayi mamaki,saboda nazo ɗaurin auren ka batare da sanin kowa ba,uzuri ne ke gare ni a lokacin shiyasa ban nemeka ba,don nasan muddin ka ganni a lokacin saika nace akan in tsaya,"
  ya ƙarasa maganar tare da mayar da idanunshi kan Ammi,tun kafin ya kuma cewa wani abu,muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"Amma yaya kasan da maganar auren nashi shine ba'a sanar dani ba?saboda me?
  "Saboda halinki"! Kai tsaye ya bata amsa,
  "Tabbas naso in sanar dake ko alokacin,saboda kinsan cewa ni bana jin shakkarki,hajiya ameenace ta rokeni akan cewar karna sanar dake,saboda hakan zai iyasa ki fusata harma ki yanke ma Abusufyan hukunci mai tsanani,kuma a ƙarshe zumuncin dake tsakaninki da ita ya tarwatse,dana nace akan zan sanar dake har kuka saida tayi mun,wannan dalilin ne yasa ban sanar dake ba,kuma ana haka daga baya kwatsam naji labarin mutuwar auren Abusufyan ɗin,hada ƙarin haka yasa akabar zancen gaba ɗaya,ashe yarinya ta fita da cikinsa ta auri wani,to kinji dalilin dayasa mu kanmu bamu san da ya'yan nashi ba,har suka kai wannan girman a hannun mijin da ta aura daga baya,"
  Dakatawa yayi da maganar,falon yayi shiru na wani lokaci,kafin ya mayar da idanunshi kan Sgr dake zaune,yace mashi"ka kunna mata audio din nan daka kunna mun itama ta saurare shi,"
  "Okey,"ya amsa mashi tare da,daddana wayar hannunshi,ya shiga audio din tare da kunnashi,sannan ya miƙe tare da ƙarasawa kusa da kujerar da Ammi ke zaune ya miƙa mata wayar,yatsun hannunta na kerma tasa hannu ta kar6i wayar tashi,ta ajiye asaman hannun sofa ɗin tana sauraronshi,wannan audio din na labarin da abusufyan ya bayar ne da kuma Labarin dasu sehrish suka bayar na irin ukubar da suka sha a hannun ya sayyadi,ashe ranar da abun ya faru,Sgr ya ɗauki audio na maganganun da sukayi kaf acikin wayarshi,tabbas shi ba ƙaramin jami'in Soja bane!yana Aikinsa wani lokacin tamkar jami'in sirri,Na jinjina masa,da irin baiwar da Allah yayi mashi da kuma irin kwazon dake gare shi,ta ko ina Sgr ya haɗa,shiyasa nace maku shi ɗin komai nasa Extraodinary ne~~~

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.