Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel By Hafsat Bature
Reading file: Abban Sojojin Takun Karshe.txt
Chapter 7 of 46
Hannu Sgr ya sanya tare da yago tissue ya goge bakinsa,kafin ya miƙe tare da juyawa ya nufi upstairs,Miƙewa Marshal yayi da alama shima ya kammala breakfast Ɗin nasa,shima upstairs ya nufa,
Fitowar Hajiya azeema keda wuya daga cikin bedroon É—inta,ta jiyo muryar gwaggon katsina tana ta faman sambatu tana cewa"Tsiyarta kenan mutun yazo gidan Æ´an gayu,Ni bazan iya rayuwar turawan nan ba,taya za akai ma mutun salalar biredi tare da tea rabin kofi kamar wata Æ´ar iska ace in sha"?
 Tafiya take tana sambatu zaninta a hannu sai ɗan undi ajikinta,kanta kuwa ta kifa wannan ɗaurin ɗan kwalin nata mai kama da helmert,
 har zata gifta hajiya azeema tayi gyaran murya tare da ambaton sunanta"Goggo," fuska a yamutse ta juyo tana kallonta,dawowa tayi daga gefenta suna fuskantar juna tace"Yawwa azeema,wai nikam inaso in tambayeki,'
Natsuwa hajiya azeema tayi tare da cewa"ina sauraronki gwaggo,"
 "Jiya nayi wani mafarki,ƴa'ƴan abusufyan sun bayyana,wasu ƴan uku kyawawan gaske,da nayi tunanin koda gaske ne abun ya faru amma daga baya na gane ba gaskiya bane,in ba haka ba,yaushe abusufyan ya ta6a yin aure"? Tayi tambayar tana kallon hajiya azeema,wadda ta saki baki tana kallon gwaggon,
 Ganin azeema tayi sototo tana kallonta yasa tayi tunanin cewa ko abunda ta faɗa ya bata mata rai ne,
 "Nasan dole kiyi mamaki kema,Mafarkin fa kamar dagaske,ɗaya daga cikinsu har tana sharara mana labarin ƙarya waisu ƴa'ƴan wata zainabu ne,kuma ma acikin labarin hada wata hajiya Ameena,in banda shaiɗan ina abusufyan ina ƴa'ƴa"?
 Ƙiris ya rage Azeema ta fashe da dariya agaban gwaggon katsina,ganin yadda ta haƙiƙance tana kora mata bayani,kuma babu alamun wasa a fuskarta,
Ƙunshe dariyar bakinta tayi tare da basar da ita tace"Gwaggo Anya kina shan maganinki kuwa?ina Dr harris yake?gaskiya inason ganinshi,'
 Tsoki gwaggon katsina taja tare da cewa"Harrisun daya zama ɗan iska,"
Waro ido waje azeema tayi tace"gwaggo harris ne É—an iska"?
 ta6e baki tayi tare da cewa"Zan masa ƙarya ne?ba ɗan cikina bane"?nasha wahalar yima yarona tarbiya amma waccen sauden.....'kasa ƙarasa maganar tayi saboda kukan daya ciyota,zanin hannunta takai saitin idonta tana ƙoƙarin goge hawayenta,
 Zuru harris yayi wanda fitowarshi kenan kuma atare da saude suka fito,jin maganar gwaggone ma yasa yayi hanzarin cire hannunshi daga cikin na sauden,
 Hajiya azeema tace"gwaggo faɗamun me harris ɗin ya akaita,?
 Hankali tashe Saude tace"ya harris pls kada ka bari gwaggo ta faɗa mata abunda muka aikata,kasan gwaggo yadda take ɗaukaka abu,inta tashi faɗi saita ƙara ma miya gishiri,'
 Dr harris yace"just don't worry ur self,insha Allah bazata faɗa mata ba,"
FaÉ—in hakan keda wuya gwaggon Katsina tace"Azeema abun da ciwo,yanzu yunwa nake ji,shiyasa ma kika ga nafito ina sambatu,Wurin waccen matar zani,wlh ba azmee ba Allah yasa ramadan ce ita yau saina zazzaga mata rashin mutunci!Ni zata raina ma hankali tunda safe,takawo mun tea rabin kofi da salalar biredi wai in fara da wannan,don ta raina mun hankali,nayi mata kama da kusu ne?
 Rai a6ace tayi maganar,aikuwa atare haris da saude suka fashe da dariya,a hanzarce ta juyo sakamakon jin sautin dariyar tasu,nan take ta tsuke fuska ganin shi tare da saude,
 Murmushi Hajiya azeema tayi tare da cewa"haba gwaggo baki fahimce ta bane,cewa fa tayi ki fara da wannan tana nufin kafin ki tashi fitowa zuwa yin breakfast ɗin,yanzu haka yana can an shirya mana mu kawai ake jira muje muci namu kalacin,"
 Hajiya azeema ta ƙarasa maganar tare da ruƙo zanin hannun gwaggon tace"Bari na taimaka maki ki ɗaura shi,"
 Girgiza kai tayi tare da cewa"Barmin shi a hannuna,nafison inji iska na shiga ta ko'ina,"murmushi hajiya azeema tayi kafin tace"hakan ma yayi gwaggo,ae under skirt din ma bamai sharashara bane,yana da kauri,amma duk da haka dae ki ɗaura zanin yadda zaki fito da kyau tunda ga rigarshi kin sanya ajikinki,Kuma kinga Abusufyan na nan,Ga kuma ƴa'ƴansa,bazasu so suga gwaggonsu a haka ba,"
 wani irin ƙayataccen murmushi gwaggon katsina tasaki tare da cewa"Kenan dagaske ne Mafarkin da nayi jiya"?
 Jinjina kai Azeema tayi tace"Ae suna nan,duk abunda ya faru jiya dagaske ne,ba mafarki kikayi ba,agabanki akayi komai kin dai shafa'a ne,'
 Jin haka yasa tayi saurin mayar da zanin ajikinta tana ɗaure shi tana cewa"Allah sarki ƴa'ƴan abusufyan ɗina,bayin Allah,sunsha wahala a hannun wannan fasiƙin mutumin baƙin shaiɗani,Allah mutumin nan ƙaho ne kawai bai fito masa aka ba,amma ina tantama anya ba Irin shaiɗan bane"?
  "gwaggo kidaina maganarsa ma,Ni wlh ko zancen shi ma bana so anayi,Na tsani mutumin nan kamar yadda natsani mutuwa ta,"acewar hajiya azeema,tayi maganar ne a yayin da take kama hanyar Zuwa Dining area ɗin nasu,bin bayanta Gwaggon tayi tana cewa"Ae ko sai dai ki toshe kunnanki,don zancen sayyadi ya zama dole,in har ba'a kawo min kansa ba,bazan daina faɗan sunan shi ba,'
 Murmushi kawai hajiya azeema tayi,atare suka ƙarasa dining area din,
  Gaggaisawa suka fara yi da junansu,su jahad na ganin saude suka tashi atare suka nufe ta,dama Jiya basu samu damar gaisawa da ita ba,saboda yanayin da suka shiga gaba ɗayansu,haɗasu tayi ta rungume ajikinta,cike da farin ciki tace"Ina tayaku murna sosai,nayi farin ciki sosai,Ya harris ya sanar dani komai agame daku,ashe ku jininsu ne,'ta ƙarasa maganar ayayin da take raba jikinta daga nasu,kowannansu fuskarshi ɗauke da murmushi,Jahad tace"Aunty saude kinga ikon Allah ko?munsha wahala sosai,mu kanmu bamu ta6a tunanin cewa muna da dangi ba,amma sai gashi ƙaddara ta haɗamu da ya Omar,Ita kuma ƴar uwarmu Sehrish ƙaddarar aikine ya kawota gidan nan,Muna tare da ƴan uwanmu ba tare da mun sani ba,sae gashi rana ɗaya Allah ya bayyana mana komai,'
 Saude tace"Congratulations Once again,ina ƙara tayaku murna sosai da kuka fito daga tsatson wannan Family ɗin,abun alfahari ne wannan"kafin ta mayar da idanunta kan Hosana,Cike da zolaya taja kumatunta tare da cewa"Hosana Kinga yadda kika canza?kamar ba wannan Sha takwas sha taran ba,mai ɗan kai,kinyi kumatu kamar Balon balon,Ga haske gaskiya ya Omar ya Iya raino,"
Fashewa da dariya hosana tayi tana faman sunnar dakai,
"Kiyi ma sister É—inku mana,Ita bazata taso mu gaisa ba"?tayi maganar tana kallon sehrish dake zaune,tana faman kallonsu É—aya bayan É—aya,
Murmushi jahad tayi tare da juyawa tayi mata alamar ta taso da hannunta,
Miƙewa sehrish tayi tare da nufar inda suke,koda ta ƙaraso saude ta sanya hannu tare da janyota ta rungumeta,kafin ta raba jikinta dana sehrish tace"Masha Allah,gaskiya ban ta6a ganin triplet,masu kama iri ɗaya sak kamar taku ba,ina taya ki murna sosai da Allah ya haɗaki da ƴan uwanki,da kuma mahaifinku,da kuma danginku,'
Fuskar sehrish É—auke da murmushi tace"Ngde sosai,"
"Allah ya tsare mana ku,Ya Albarkaci rayuwarku ya kuma kare ku daga sharrin maƙiya,'
Atare suka amsa mata da Ameen,bama su kadae ba,hadasu Abba dake sauraron maganganun nasu,
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.