Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel By Hafsat Bature
Reading file: Abban Sojojin Takun Karshe.txt
Chapter 4 of 46
Kamar yadda Abba yayi alƙawarin shirya gagarumar walima na bayyanar ƴa'ƴan ƙaninsa Abusufyan,Da kanshi ya fidda date ɗin da za'a gabatar da ita,Kuma tun aranar ya fara kiran Ƴan uwa da abokanan arziƙi yana sanar dasu game da ƴa'ƴan abusufyan da suka bayyana,Babu wanda bai bari ba,kowa kira yake tun daga kan danginsu na Zaria,na damaturu dana sauran states ɗin da kuma waɗanda ke zaune Ƙasashen waje,kowa saidaya sanar mawa,Bayan Abbas ya koma gidane da safe Amani ke tambayarshi meya faru ne jiya ya hanasu zuwa gidansu,Anan ya kwashe duka abunda ya faru game da su Sehrish ya sanar mata,wani irin farin ciki ne ya cika ta,Ba don komai ba sai don sanin cewa plan ɗin Aunty babba ya gama Tarwatsewa,ae tunda taji cewar ƴan mata ne kuma sun kai shekara goma sha bakwai zuwa sha takwas kyawawan gaske,Nan fa ta kwashe da dariyar mugunta aranta tana cewa Naga yadda za'ae Aunty laila ta cimma burinta,Gida bai ƙoshi ba taya za'a ba na waje,Ae tuwona maina za'ayi,Haba ae xance ya ƙare,
ita kanta Amani ta ƙosa ranar walimar tazo saboda suje gidan,saboda taji cewar Aranar Aunty babba da hafsat zasu zo Abuja,babban burinta taga tashin hankalin da aunty babba zata fuskanta inta gansu,
Ranar walimar kuma yayi dai dai da ranar da Ammi zata zo,tare da wasu daga cikin danginsu,haka zalika captain Najeeb da kuma Talal suma duk a ranar zasu dawo gida,ba don komai ba sai don su sanya ƴa'ƴan uncle ɗinsu abusufyan acikin idanunsu,Kowa ɗokin ganinsu yake yi kamar kamar me,musamman da sukaji irin rayuwar da yaran sukayi a wulaƙance sai suji wani irin tausayinsu da kuma ƙaunarsu ya shiga cikin ransu,kuma duk aranar MG Osman da kuma Captain Adam suma zasu dawo gida,wanda tun dawowarsu daga U.s suka tafi sada zumunci,Gaskiya wannan Babbar rana ce,Hakan yasa ma Zamuyi shiri na musamman ni da makaranta littafina don mu halarci gidan amatsayin gayyar soɗi tunda ba'a gayyace mu ba,Sa kaine kawai,
Cikin Æ´an kwanakin nan wata irin rayuwar farin ciki suke gudanarwa tare da Daddynsu,kullum yana manne dasu,Da kanshi ya zauna yayi masu kitson kalaba guda bibbiyu akansu kamar yadda ya ta6a yi masu suna yara,koda yazo kan Sehrish,Cike da mamaki yace"Ya akai naga gashin kanki guntu?ko kinyi wani ciwo ne dayasa aka datse maki gashin,"girgixa kai tayi tare da cewa"a'a Laifi nayi ma Babba yaya shine ya yanke mun gashin da almakashi,"
da buÉ—ar bakin Abusufyan sai cewa yayi"Yayiwa kanshi ai," murmushi sehrish tayi duk da batasan me daddyn nasu yake nufi da hakan ba,duk a wannan kwanakin basu je school ba,Abusufyan da kanshi yace kada su damu shi da kanshi zai kaisu makarantar don karma a tuhume su,
A 6angaren Sir Commander haroon kuwa,tamkar munafuki haka ya koma acikin gidan,ba kowa ma ke sanin lokacin da yake shigowa gidan ba,da kuma lokacin da yake fita,Da alama dae akwai wani abu da yake shiryawa a 6oye,
*AMRISH*
Zaune take acikin class ɗin gaba daya ta shiga damuwar rashin ganin Sehrish kwana biyu ko layinta ta kira bata samu,hatta wayar junaid ta jaraba kira shima ba'a ɗagawa,hakan ba ƙaramin tayar mata da hankali yayi ba,tagumi tayi idonta cike tab da hawaye saboda damuwar da take ciki,taso ace sehrish na nan atlease zata ɗebe mata kewa,tana cikin wannan tunanin har malam ya shigo cikin class ɗin nasu bata sani ba,bayan ya kammala amsar gaisuwa daga wurin student din,kai tsaye ya ƙarasa seat ɗin da Amrish take,hannun shi yakai wanda ke ruƙe da maker ya ɗan bubbugi desk ɗinta,a firgice takai idanunta akanshi,Yunƙurawa tayi tare da miƙewa ganin Ya mu'allim,wanda tun ranar daya ba sehrish Ruwan addu'ar nan bai ƙara zuwa makarantar ba,duk da sun samu labarin cewar Ya tafi Umra ne,shiyasa aka musanya masu shi,
Murmushi ya É—an saki afuskarshi yana kallonta yace"tunanin me kike yi ne?har na shigo cikin class É—in baki sani ba?
Muryarta na rawa tace"Ayimun afwa ya mu'allim,Bana jin daÉ—i ne bansan ka shigo ba,
Jinjina kanshi yayi tare da É—an kai idanunshi kan Seat É—in sehrish yace"Ina yarinyar nan take?Æ´ar family É—in Salahuddeeen hussein naga kamar bata a class É—in"?
fuskarta É—auke da damuwa tace"Batazo ba,yau kusan kwana huÉ—u kenan bata zo school ba,kuma nayi trying kiran layinta amma bana samu,har brother É—inta na kira,shima layinsa ba'a samu,'
Jin hakan yasa shi fargabar to kodai wani abu ya faru da yarinyar?Yaso yaji ya tayi da ruwan addu'ar daya bata,shin tasha ko bata sha ba?
Jinjina kanshi yayi tare da juyawa yace"Allah yasa dae lafiya,in har batazo ba,zuwa sati mai zuwa zan je gidansu don na binciki dalilin rashin zuwan nata,'
Jiki asanyaye Amrish ta koma ta zauna,saman seat É—in nata,jikinta har ya fara kerma saboda tsoran kar ace wani abune ya faru da Sehrish,
A ƙarshe dae ta yanke shawarar neman gidansu don taje ta ganta da kanta.
*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃
*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*
*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*
*LOCATION KANO*
08062073990
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining.
Snack
Awarah
Farah
Zobo
Samosa
Cup cake etc
Contact me 09063302182or 09012179727.
Â
Â
Â
  Â
 *💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.