Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel By Hafsat Bature
Reading file: Abban Sojojin Takun Karshe.txt
Chapter 9 of 46
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة ØØ¨ رومانسية بين Ø³ØØ±ÙŠØ´ ÙˆØ§Ù„Ø¬Ø±Ø§Ø Ø§Ù„Ø¹Ø§Ù… Ø±ÙØ§ÙŠØªðŸ’‹ðŸ’˜â¤ðŸ¤â¤ðŸ’•💖*
â¤ðŸ¤â¤
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*
Hannu yasa tare da tallabo fuskarta yace"Hosana bada sani na nayi maki hakan ba,laifin ki ne,meyasa zaki toshe mun hancina?so kike na mutu'?
Girgiza kai tayi"a'a,banso ka mutu,ae ni wasa nayi maka ko,"tayi maganar tana satar kallon fuskarshi,
 "Faɗa mun me ya kawoki bedroom ɗina har saman gadona"?
  A ƙule tace"nifa nazo ne na tashe ka don kaje ka ci abinci,naga kowa ya fito banda kai,kuma zasu iya cinye abincin duka,"
fuskarshi É—auke da murmushi yace"Waya faÉ—a maki za'a cinye abincin,ae ko ban fita ba Azmee zata kawo mun ne har cikin part É—ina,"
   Shiru tayi tana faman sauke ajiyar zuciya,ɗagowa ta ƙara yi zata saci kallonshi suka haɗa ido,ganin yadda yake kallonta ko ƙyaftawa baiyi hakan yasa ta ɗaure fuska cikin shagwa6a tace"Ya omar wannan kallon fa,ka wani tsare ni da ido,"
 yadda tayi maganar ba ƙaramin burgeshi tayi ba,ya jima yana kallonta batare da yace wani abu ba,har sai da ta hasala rai a6ace tace"shikenan tunda ba zaka mun magana ba,bari na tashi na tafi,dama ko abincina banci ba,saboda kawai inzo in tashe ka daga bacci,amma ko farin ciki ba kayi ba,'
 Ajiyar zuciya ya sauke tare da ruƙo hannunta cikin nashi"Hosana,so nake ki faɗa mun gaskiya,kina sona da gaske?kuma zaki aure ni? Waro ido waje hosana tayi tana kyakkyaftasu kamar na ƴar tsana jin abunda yace,a ruɗe tace"Ya Omar!aure fa!"_
Jinjina mata kai yayi tare da cewa"eh,aure hosana ko baki shirya ba,"
 Turo baki ta ɗanyi tana ƙunƙuni ƙasa ƙasa,hankalinsa kam harya ɗan tashi saboda ganin yadda ta tsorata don yayi mata zancen aure,dama fargabarsa kada sai anje wurin nema mashi auranta tace bata shirya ba,don yasan ba cikakken hankali gare ta ba,
Lalla6ata ya shiga yi"pls hosana,ki faÉ—amun gaskiya,zaki aure ni"?
 daƙyar ta iya buɗe baki tace"Ni yanzu tashi zanyi in tafi,dama zuwa nayi fa don in tambayeka,wani kalar ƙunshi kake so ayimun baƙi ko ja,"
  ya lura cewa batason zancen auren shiyasa ta kawo maganar ƙunshin,cikin sanyin murya yace"Nafison jan lalle zai fi yi maki kyau,kuma ba mai yawa ba ƙunshin,ƴar flower kawai za'a zana maki mai kyau,"
 Yana kai ƙarshen maganar,hosana ta miƙe tana faman shan ƙamshi,da sauri ta juya ta bar bedroom ɗin nashi,bin bayanta yayi da kallo har ta fuce,jiki asanyaye ya miƙe tare da nufar toilet ya shige,
  Hosana na fita daga cikin bedroom ɗin nashi,a falonsa ta tsaya tana faman zabga murmushi,tsabar farin ciki kamar ta zuba ruwa a ƙasa tasha,Yau ya Omar ya nuna yana sonta harma yanayi mata zancen aure,ta rasa ma wa zata fara faɗamawa,sai faman zagaye zagaye takeyi a cikin falon,
Wuraren ƙarfe biyu da rabi na rana,Abusufyan ya ɗaukesu acikin motarshi kamar yadda yayi masu alƙwarin kaisu wurin saloon da kanshi,hosana da jahad suna a bayan motar duk sun ɗau wankan jallabiya sun laga mayafi,Sehrish na agaban motar kusa da driver seat inda Uncle abusufyan ke zaune yana driving ɗinsu anatse,Su jahad da hosana sae fira sukeyi tare dashi,amma ita ko uffan bata tanka masu ba,dama tunda ta shigo cikin motar Abusufyan ya lura da yanayinta,
gyaran murya yayi mata hakan yasa ta É—an dago da kanta ta kalle shi,
 "Meyake damunki ne Daughter?tunda kika shigo cikin motar nan baki tanka mana ba,ga ƴan uwanki suna ta fira a tsakaninsu amma ban dake".
 Muryarta asanyaye tace"Babu komai,"
 "ko don saboda na hana ki kai ma Sgr abinci ne"? Yayi maganar batare daya kalleta,
 Cikin sauri tace"a'a ba haka bane,kawai bana jin daɗin jikina ne,"
 "Ban yarda ba daughter,saboda shi ne yasa kika shiga damuwa,"_
 Shiru tayi bata ce komai ba,murmushi abusufyan yayi kafin yace"banyi hakan don na takura maki ba,face don na ɗaukaka darajarki,nasan ba zaki fahimce ni ba a yanzu amma nan gaba da kanki zakiyi mun godiya akan hakan,idan kuma hakan ya 6ata maki rai,kiyi haƙuri,'ya ƙarasa maganar adai dai lokacin da suka ƙaraso wurin Saloon ɗin,parking ɗin motar yayi jahad da hosana suka fita waje,tana ƙoƙarin buɗe motar ta fita ya ambaci sunanta"Sehrish,"juyowa tayi tare da kallon fuskar daddyn nasu tace"Na'am daddy,"
 "Murmushi kawai nakeso kiyi mun kafin ki fita,"
fashewa tayi da dariya har fararen hakoranta suka bayyana,duk a tunaninta wani abu mai muhimmanci ne yasa ya kirata,ashe kawai don ya tambayi murmushinta ne,shima dariyar yakeyi,kafin su fita daga cikin motar atare,
**************
Fitowarshi kenan daga wanka,yana cikin shirya kanshi cikin riga da wandon jeans,yaji an kwankwasa ƙopar ɗakinshi,daga muryarshi yayi tare da cewa"ƙopar a buɗe take,"yayi maganar tare da juyawa yana kallon mai shigowar,
 Cike da mamaki yace"Ya HAROON!kaine!dama kana nan,"
Shu'umin murmushin nan nashi ya saki tare da ƙarasa shiga cikin bedroom ɗin nashi yana cewa"Ina nan mana junaid,kaine ka manta dani,kowa ma ya manta dani,"
 "Ya haroon ba haka bane,wlh ni ban manta dakai ba,kana araina,"
 ta6e baki haroon yayi alokacin da yake tsayawa agaban junaid suna fuskantar juna yace"Ka ƙara kyau da haske,hankalinka kwance baka da wata damuwa,ba kamar ni ba,kullum cikin damuwa nake,zuciyata har nauyi takeyi mun saboda halin da nake ciki amma babu wanda ya damu dani,yau ko mutuwa nayi babu wanda zai damu,sae ma farin ciki da za'ayi,"
 Jin wannan maganar ta haroon yasa jikin junaid yin sanyi,wani irin tausayin shi ya kamashi,muryarshi tamkar zaiyi kuka yace"pls Ya haroon dan Allah kadaina faɗin wannan maganganun,wlh bana jin daɗi,"
 "Junaid ƙarya nayi ne?an damu dani acikin gidan nan ne?kowa yayi watsi dani,babu wanda ke damuwa dani,tamkar bare haka nakeyin rayuwata,hatta azmee da take ƴar aiki acikin gidan nan ta fi ni muhimmanci tunda ita ana damuwa da ita,ni kuwa fa?
 Hawaye ne suka cicciko a idanun junaid,dama shi akwai tausayi,gaba ɗaya tausayin haroon ya kamashi,saboda duk abunda ya faɗi gaskiya ne,ba'a damu dashi ba,ko zancen shi ma babu maiyi acikin gidan,idan zai share wata a waje babu mai tambayar ina yaje,
 "Tamkar maraya ni fa haka nake acikin gidan nan,kalli kaga yadda na koma duk na rame saboda damuwa,gaskiya ni bazan iya cigaba da rayuwa ba junaid,zan kashe kaina ne kowa ya huta," yana kai ƙarshen maganarshi ya juya da sauri zai bar ɗakin,
 Da gudun gaske junaid ya rungumoshi ta baya tare da fashewa da matsanancin kuka yana cewa"Meyasa ya Haroon!pls stop saying that,banason jin kana zancen mutuwa,ko kowa bai damu dakai ba,Ni nadamu dakai,ko don saboda ni ya haroon kada ka aikata hakan,idan ka kashe kanka,nima bazan rayuwa ba,zan bi ka mu tafi tare,"
 Wannan kalaman na junaid ba ƙaramin sanyaya mashi zuciya su kayi ba,cire hannunshi yayi daga ruƙon da yayi ma waist dinshi,sannan ya juya suna fuskantar juna yace"Junaid dagaske ne ka damu dani?kuma bakaso in mutu"?
 cikin shessheƙar kuka junaid yace"Eh ya haroon bana so pls,"
 Hannu haroon yasa yana share mashi hawayenshi,kafin daga bisani ya janyo shi ajikinshi tare da rungume shi sosai ajikinshi,kamar zai mayar dashi cikin shi,saitin kunnanshi yakai bakinshi tare da cewa"I love u so much junaid,cos you're so special,in dai zan kasance tare dakai bazan ta6a shiga wani ƙunci na rayuwa ba,kallon ka kawai zai iya sanya farin ciki a cikin zuciyata,daga yanzu inason ka zama abokina junaid,saboda ka dinga ɗebe mun kewa,muna fita yawo atare,don bani da aboki,nifa kowa gudu na yake yi,bansan meyasa ba,'ya ƙarasa maganar tare da janye junaid daga jikinshi,
 "Junaid!ka amince zaka zama abokina"?
Jinjia kai junaid yayi tare da cewa"Eh,na amince,amma dan Allah ya haroon kadaina zancen zaka kashe kanka,banjin daÉ—i banso pls,"
 "Shikenan na daina,daga yau kome kakeso ma zanyi,am sorry na sanyaka zubar da hawayenka,"
 "Ya haroon ni zanje nayi ma Abba magana akanka,nasan abba zai fahimce ni,"
 cikin sauri haroon ya ruƙo hannun shi tare da cewa"A'a junaid,just leave it,banason kowa yasan meke tsakanina dakai,kada kayi ma kowa maganata don ba lalle su fahimce ni kaman yadda kai ka fahimce ni ba,"
 "Shikenan bazan faɗa ba,"
"Yawwa junaid ɗina,Yanzu zan barka ka ƙarasa shiryawa,"
 Yana faɗin hakan ya juya tare da fucewa daga ɗakin junaid,ya koma bedroom ɗinsa,agaban dressing mirror ɗinshi ya tsaya yana ƙarewa fuskarshi kallo,
 A hankali wannan mugun murmushin nashi ya soma bayyana akan fuskarshi,fashewa yayi da dariya kafin daga bisani ya ɗaure fuskarshi,kalaman junaid ya shiga tariyowa,tuni jikinshi yayi sanyi,ta wani 6angaren ji yake tamkar bazai iya ba,amma bai da wata mafita daya wuce wannan!
 "Junaid kada ka damu zamu mutu atare,"ya faɗi hakan tare da komawa ya zauna daga gefen gadonshi,
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.