Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel By Hafsat Bature
Reading file: Abban Sojojin Takun Karshe.txt
Chapter 18 of 46
Gaba ɗaya duk sun kashe ma ishaq baki yama rasa abun cewa,tsananin baƙin ciki da takaici ya hanashi cewa uffan,jikinshi sae faman tsuma yake yi,burinshi kawai yaji abunda suka aikata ma yaran,da har suka tsorata da ganinsu,tabbas sai sunci Ubansu,muddin yaji wani da ba dai dai ba,don bazai yarda suja mashi tozarta ba a idon ƴan uwanshi,
Aunty Azmee ce ta taimaka wurin ɗebo ruwa suka yayyafa ma Aunty babba a fuskarta,ae tana farfaɗowa kamar wata zautacciya tayi zumbur ta miƙe,ko waiwayonsu ba tayi ba,ta watsa aguje,tayi cikin gidan,Allah kaɗae yasan inda ta kutsa kanta,
A fusace General ishaq zai bi bayanta,Abbansu junaid yayi saurin ruƙo hannunshi tare da cewa"kada ka bita,yakamata mubi komai a sannu,yanzu bamu kaɗai bane a wurin nan ba,akwai ƙannenka kuma akwai bare a wurin nan,"
 Jinjina kanshi kawai yayi ba don ya haƙuri ba,
 Batare da sanin kowa ba,hafsat ta zame jiki daga wurin,saboda wani irin mugun kallo da taga Daddynta nayi mata,bashi kaɗae ba hatta Marshal kallon tuhuma yake yi mata,hakan ne yasata ta sulale tabar wurin,sauƙinta ma basu ambaci sunanta ba,amma tasan dole sunanta ya fito aciki,kuma daddynta in ya tashi yanke hukunci hada ita zai haɗa ya yanke mawa,tabbas tayi dana sanin biye ma mahaifiyarta wurin cutar dasu hosana,gayanan sunja ma kansu,
 Ruƙo hannun hosana yayi tare da janyota,ta dawo ta gabanshi,fuskarnan tayi jawur,sae faman kuka takeyi tana faɗin"ya Omar a koreta tabar gidan nan,bana son ganinta,bata da Imani,itace ta rufe mu acikin store tayi mana horon yunwa,ta dinga bugunmu da bulala,kuma ta dinga samu aiki,har gadon asibiti sai da aka kwantar dani.......'
Cikin sauri Omar ya sanya tafin hannunshi ya toshe mata baki,cikin lallashi yace"its ok hosana,na fahimce ki,zansa sojoji su koreta daga gidan nan hakan yayi maki,"
 ɗaga mashi kai tayi alamar eh,sannan yace"kada na sake jin kukan ki to,ya isa haka,kalli fa ki gani duk kin 6ata kwalliyarki da hawaye,"
 Curo handkerchief Abusufyan yayi daga gaban aljihunsa,ya ruƙo hosana,tare da sanyashi a fuskarta yana goge mata hawayenta,"Daddy matar can bata da Imani ko kaɗan,taso ta kashe ni,dan Allah ku sakar mata karnuka su rakata bakin gate,tabar gidan nan,"
 Muryar abusufyan tamkar zaiyi kuka yace"Kiyi haƙuri kinji hosanata,zansa a koreta kamar yadda kikeso,amma yanzu kiyi shiru da bakinki,ki daina magana,banason ganin hawayenki,"
 "Daddy bakasan yadda nakeji bane,zuciyata tafarfasa takeyi,raɗaɗi takeyi mun kamar ana rura garwashin wuta acikinta,wlh daddy waccen matar bazata ga Manzon Allah ba,sai ta shiga wuta,'
Hankali atashe Marshal ya daka mata tsawa har saida ta dawo cikin hayyacinta,fuskarshi a daure yace"kar na sake jin kince uffan a wurin nan,surutun ya isa haka!banace za'a kore ta ba,"
 Saboda tsoratar da tayi da tsawar da yayi mata ne yasa ta faɗa jikin daddyn nasu ta ƙankameshi,tana faman sauke ajiyar zuciya,'
 jikin kowa yayi sanyi,musamman Ishaq,bawan Allah duk yabi ya takure kansa,idanunshi sunyi jawur saboda tsabar 6acin rai,
  Abba ne yayi ƙoƙari wurin dawo dasu daidai daga yanayin da suka shiga,daƙyar aka samu hosana ta zauna itama amma duk da haka tana yawan firgita wannan ya ƙara tabbatar masu da cewa ba ƙaramin Abu Aunty laila ta aikata masu ba,wuri kowa ya samu ya zauna agaban table ɗin dake a wurin wanda ke shaqe da abinci kala kala,nan fa kowa ya shiga bama cikinsa abinci,jikin Sehrish ba ƙaramin sanyi yayi ba,saboda ta gane dalilin dayasa su jahad suka tsorata da ganin matar,wato itace matar da Omar ya kaisu gidanta,wadda ta azabtar da rayuwarsu,kamar yadda jahad ta bata labarinta,kowa ya lura da yanayin yaran,sun kasa sakewa suci abinci sosai,ƙarshe sai dae Abusufyan ya dinga binsu one by one yana sanya masu abinci abakinsu suna ci,a haka har ya samu suka ci sosai,bayan sun kammala cin abincin,Junaid ya ɗaukko Camera ɗinsa,nan fa aka shiga ɗaukar hotuna,abun gwanin burgewa,Happy family,kowa sai da ya fito Hajiya azeema,su gwaggon katsina Saude,Dr harris,hatta ƴan matan da hajiya sarah tazo dasu,sae da suka fito akayi masu hotuna,mutun uku ne kawai babu a wurin Ammi wadda kowa ke fargabar fitowarta,bayan ita sae Haroon wanda ke ƙumshe acikin ɗakinsa,Sgr kuwa baya cikin gidan,tun wuraren ƙarfe uku yabar gidan,
 Anyi masu hoto tare da mahaifinsu sun sanyashi atsakiya,sae wanda akayi masu tare da Abbansu junaid tare dashi kanshi junaid ɗin,kowa saida yayi hoto tare dasu,hatta Su twins da fawan dasu irfan,kowannansu sae da yayi hoto dasu,sun sha hotuna ba ƙadan ba,
Basu suka kammala ba sae wuraren sallar magrib,sannan kowa ya shige ciki domin yin alwala,
Kamar jira jahad takeyi su shiga É—aki ta rufe hosana da faÉ—a,tamkar zata bugeta,"Sai yanzu na tabbatar da cewar ke cikakkar zararriyace baki da hankali,meyasa ba zakiyi shiru da bakin ki ba?don me zaki tona mata asiri agaban mutane"?
Fashewa da kuka hosana tayi tana faɗin"kada ki ƙara cemun zararriya,kuma naje na tona mata asirin,Ni bazan ta6a yafe mata ba wlh,kamar yadda ta cutar da rayuwarmu itama sai ta fuskanci sakamakon abunda ta aikata mana,'
"Hosana,karna sake jin kin tada wannan maganar,idan ba so kike ranki ya 6aci ba,"
 "Wlh saina faɗima Daddy da Abba,kuma saina faɗa ma yaya Omar,sai dai duk abunda zai faru ya faru,'
 rai a6ace tayi maganar,cakumar rigarta jahad tayi,tare da yin wurgi da ita,ta faɗa saman gadon tana kuka,fitowa Sehrish tayi daga cikin toilet,ganin jahad na ƙoƙarin bugun hosana yasa tayi saurin zuwa tare da ruƙo hannunta"karki kuskura kice zaki hukunta hosana!abunda tayi dai dai ne,koda ace ita bata faɗa masu ba,to ni saina faɗa masu abunda waccan matar ta aikata maku,saboda bata da Imani,muguwace ita,muddin akace za'a cigaba da yafe ma mutane irinta to tabbas bazasu ta6a canza halinsu ba!Suna buƙatar a ladabtar dasu,a hukuntasu,idan suka aikata ba dai dai ba,Ni hakan da hosana tayi ta burgeni,!"
 Shiru jahad tayi,ta wani 6angaren zancen sehrish gaskiya ne,muddin ba'a ɗauki mataki ba akanta taga an ƙyaleta to tabbas bazata ta6a canzawa ba,amma yanzu idan suka hukunta ta dole nan gaba taji shakkar ƙara yin irin kuskuren da tayi abaya,
Â
"Kin faÉ—i gaskiya sehrish,ni banyi tunanin hakan ba,kuma koda nake yi ma hosana faÉ—a,saboda 6arin zancen da tayi ne agaban mutane,bai kamata ta yi magana akan idon kowa ba,in ma faÉ—in ne Ya Omar yakamata ta sanar mawa,sae su yanke mata hukuncin da suka ga ya dace da ita,"
Ta ƙarasa maganar tare da ɗauke idonta daga kan sehrish ta mayar dasu kan hosana dake baje saman gadon tana kuka,nan take taji bata kyauta mata ba,hawa saman gadon tayi tare da janyota jikinta,tana lallashinta,daƙyar ta samu tayi shiru,daga bisani suka tashi domin yin sallar magrib,
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.