Trending Hausa Novels

Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel By Hafsat Bature

Reading file: Abban Sojojin Takun Karshe.txt

Chapter 33 of 46

Janye idanunta tayi daga kan hosana ta mayar dasu kan jahad,wadda ke ruƙe da bread a hannunta,tana goga mashi butter,abun ya ɗaure mata kai kowa sai cin abinci yake yi hankali kwance,amma ita takasa Cin nata,to ko dai bata da lafiya ne? ta ƙarasa zancen zucin tare da juyawa,karaf idanunta suka sauka akan Fuskar Abusufyan wanda ke kallonta,har sai da ta ɗan razana kaɗan,sunanshi ta ambata abakinta a hankali"daddy,"
..murmushi ya ɗan sakar mata tare da cewa"Daughter,tun ɗazu ina kallonki,kin ƙi cin abincinki,kin tasa ƴan uwanki gaba kinata kallonsu ɗaya bayan ɗaya,faɗamun meke damunki ne'?
  "Daddy am not feeling well,gabana sai faɗuwa yakeyi,bansan meyasa ba,shiyasa ma nagaza cin abincin"muryarta akasalance tayi maganar,
  Jahad tace"Daddy,jiya ma batayi wani isasshen bacci ba,"
  "Saboda me"?yayi tambayar yana kallonta,
  "Nikaina bansan meyasa ba,kawai bana jin daɗi ne,"
  Jinjina kai yayi tare da cewa"Kada ki damu in sha Allah wannan faɗuwar gaban da kikeji Alkhairi ne zai faru dake,"
  "Allah yasa haka ne daddy" ta ƙarasa maganar tare da kai hannu ta ɗauki cup of tea ɗin dake agabanta,ta shiga kur6arsa a hankali,ba don tana jin daɗinsa ba,

Suna cikin cin abincin nan,sae ga Azmee tare da hafsat,sun shigo dining area É—in,Aunty babba na a bayansu ta sanya Niqab a fuskarta,hayaam dai bata fito ba,saboda gudun karsu haÉ—u da Sgr a wurin,da hannu Azmee tayi masu nuni da su zauna a inda su Jahad suke,saboda nan ke akwai empty chairs guda biyu da suka rage,da yake table É—in mai mazaunin mutun Shida ne,
  Tunda suka zo wurin,idon kowa ya koma akan Aunty babba dake sanye da niqabi,abun ba ƙaramin ɗaure masu kai yayi ba,sai da suka fara gaishe dasu Abba,sannan suka samu wuri suka zauna,hankalin Aunty babba sam ba'a kwance yake ba,bata so fitowa ba,Azmee ce ta sanar da ita cewa Ishaq yace su fito dining suci abinci,tayi mata hakan ne saboda ta rama Wulaƙancin da sukayi mata,

Daƙyar ta iya gaishe da Abusufyan,batare daya ɗago ya kalleta ba ya amsa mata,hafsat tace"Uncle ina kwana,"?
"Lafiya lou hafsat,ashe kuna acikin gidan,ae nayi tunanin kun koma Kaduna ne,"
Murmushin yaƙe tayi,sae faman zazzare ido takeyi,duk sunbi sun tsargu,ita da mommynta,ita dai Sehrish ta zuba ma sarautar Allah ido,so take taga ta yadda Aunty babba zataci abinci da niqabi a fuskarta,ba ita kaɗae ba hatta jahad abunda take jira kenan,Ishaq kuwa tuni ranshi yayi mugun 6aci,sarai yasan cewa da gangan ta zura niqabi a fuskarta bayan tasan cewar abinci zata ci,alamun rashin gaskiya duk sun bayyana atattare dasu,ita da hafsat,
Serving ɗinsu Aunty azmee tayi,ta tura masu plate ɗin abincin agabansu,hafsat dai tayi kokarin cin abincin,kaɗan kaɗan take tura chips abakinta,Aunty babba kuwa kamar gunki haka ta ƙame saman kujerar taƙi motsi,fargabarta kada hosana ta gane cewa itace,
Murmushin mugunta sehrish ta saki,tare da yin gyaran Murya tace"Aunty,ki cire niqabin mana,in ba haka ba,bazaki ji daÉ—in cin abincin ba,gashi yana ta hucewa,bazaiyi maki daÉ—in ci ba inya salafce,"
Mazurai Aunty babba tashiga yi ta cikin niqabin,ƙululun baƙin ciki kamar ta shaqo sehrish ta rufe ta da bugu,ƙin magana tayi saboda gudun kar Hosana taji Muryarta,ta kara tona mata asiri,hakan yasa Jahad cewa"Na ji tayi shiru,kodai bacci ne bai isheta ba"?tayi maganar tana faman ƙumshe dariya abakinta,sehrish tace"inaji tayi bacci ne a zaune,bari na cire mata niqabin don tasha iska kada numfashinta ya sarƙe," yunƙurawa Sehrish tayi tare da kai hannu zata zame niqabin dake a fuskar Aunty babba,ae kuwa a firgice Aunty babba ta zabura ta miƙe tsaye tana faɗin"Karki kuskura ki ta6amun niqabi na," rai a6ace tayi maganar,aikuwa Hosana najin Muryarta,ta daddage ta fasa uwar ƙara,tare da yin wurgi da kofin dake a hannunta,a gigice ta miƙe tana ƙokarin guduwa,gaba daya hankalin kowa ya dawo kanta,Omar ne ya miƙe da sauri ya ruƙo hannunta yana tambayarta lafiya,
A tsorace tashiga fadin"Banason ta!na tsane ta!wlh ya Omar muguwace matar nan,tazo nan ne don ta kashe mu,dan Allah ku koreta daga gidan nan,wayyo Allah na....."ta fashe da matsanancin kuka,tashin hankalin da ba'a samashi date!nan fa kowa ya miƙe tsaye yana bin Aunty babba da kallo,saboda tsabar ruɗu muryarta na kerma tashiga cewa"wa...wallahi Billahil azimu Ni bansanta ba!bansan laifin me na aikata mata ba,yarinyar nan fa mahaukaciya ce tana da ta6in hankali,shiyasa take wannan sambatun...."tunkan ta ƙarasa maganar Abusufyan ya daka mata tsawa tare da cewa"karki kuskura ki ƙara kiran ƴata da sunan mahaukaciya!in ba haka ba ranki zai 6aci a wurin nan ne!hosana bazata ta6a tsangwamar mutun hakanan ba batare daya aikata mata wani mugun abun ba," ya karasa maganar tare da jan dogon tsoki,
"Ya Omar dan Allah ku sakar mata karnuka su fiddata daga cikin gidan nan,wlh babu Allah aranta!so take takashe maka hosanarka,"cikin shesshekar kuka take maganar,Marshal sai ƙokarin rufe mata bakinta yakeyi don ta daina amma ina hosana taƙi rufe bakin,don har cizon hannunshi takeyi,in yayi ƙoƙarin toshe mata baki,Aunty babba kuwa sae faman zabga salati takeyi,jikinta sae kerma yakeyi,tuni zufa ta jika ta sharkaf,ƴan hanjin cikinta kuwa sae faman kaɗawa sukeyi,hankalin General ishaq ba ƙaramin tashi yayi ba,tsoranshi kada ace wani mugun abunne laila ta aikata ma yarinyar da har take tsoron ganinta,
Lalla6awa Aunty babba tayi da gudu tabar dining area É—in ta koma cikin dakinsu,tana shiga ciki ta aza hannayenta asaman kanta tana faÉ—in"Na shiga uku!Na bani!na lalace!Waccen mahaukaciyar yarinyar tana son taja mun bala'e ina zaman zaman lafiyata,"tana magana tana cizon yatsan hannunta,"Aunty laila meya faru,"hayaam ce tayi mata tambayar,
"Hayaam ta faru ta ƙare!yarinyar can ta gama dani!"muryarta tamkar zatayi kuka tayi maganar,hannu tasa tare da zame niqabin fuskarta,tayi wurgi dashi ƙasa,sannan tashiga zagaye ɗakin tana faman cizon yatsanta,

"Dan Allah kowa yayi haƙuri ya koma ya zauna,ina tunanin ciwon hosana ne ya motsa,ba wani abu ba shiyasa take ta sambatu,"Omar ne yayi maganar don ya kwantar masu da hankalinsu,
Fashewa da wani sabon kukan hosana tayi tana faɗin "Wlh ya Omar Ni da hankalina,da tunani na!nasan me nakeyi,wannan matar itace ta...."kasa ƙarasa maganar tayi saboda tsawar da Omar ya daka mata "Shut up hosana!bana son na ƙara jin maganarki a wurin nan!in ba haka ba saina sa6a maki," tafin hannunta tasa tare da toshe bakinta,tana yin kuka ƙasa kasa,
"Ka daina yi mata tsawa Omar,tabbas akwai abunda akayi ma yarinyar nan,wanda ya ƙona mata zuciya shiyasa take wannan sambatun,ya kamata mu lallasheta,muji menene matsalarta"? Acewar Abba,
Ishaq yace"hakane,In ba damuwa Inason ganinka Omar tare kuma da yaran,"
Ya ƙarasa maganar tare da shigewa gaba,Omar yabi bayansa hannunshi ruƙe dana hosana,jahad kuma na abayansu,

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.