Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel By Hafsat Bature
Reading file: Abban Sojojin Takun Karshe.txt
Chapter 28 of 46
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة ØØ¨ رومانسية بين Ø³ØØ±ÙŠØ´ ÙˆØ§Ù„Ø¬Ø±Ø§Ø Ø§Ù„Ø¹Ø§Ù… Ø±ÙØ§ÙŠØªðŸ’‹ðŸ’˜â¤ðŸ¤â¤ðŸ’•💖*
*Father of soldiers*
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*
â¤ðŸ¤â¤
Daƙyar suka samu ƙopar ta buɗe nan suka same ta a kwance rai hannun Allah,wani irin ruwan kumfa kumfa ne ke fitowa daga bakinta,gaggawar ɗaukarta su kayi,su biyu suka cuccu6eta sai cikin motar Mommyn,da kanta tayi driving ɗin motar,yatsun hannunta nata kerma tana yi tana dan bugun steering,Su zeenatu kuwa dake a back seat na motar,sae kuka sukeyi suna jijjigata don karta mutu basu isa asibitin ba,
Suna ƙarasawa asibitin,da sauri suka cuccu6eta suka shiga da ita mommyn na fadin"Emergency pls doc,nurse....!"reception Nurses ne suka kar6eta da sauri da sauri suka shiga da ita ɗaki,anan aka kwantar da ita,doctors suka taru a kanta.
Zama sofia da Zeenatu su kayi asaman waiting seat,yayin da Mommyn Amrish ke ta faman zarya a corridor din,jikinta sai faman kerma yake yi,sam bata ta6a tunanin cewa Amrish zata iya yunkurin kashe kanta ba sai yau da ta tabbatar mata,tasha faÉ—in cewa zata kashe kanta in bata faÉ—a mata wanene mahaifinta ba,bata ta6a É—aukar abun serious ba,sae yau,ta tsorata da irin hukuncin da Amrish ta yanke wa kanta,
 "Mommy wai meya faru ne?Nasan cewa Amrish bazata ta6a yunƙurin kashe kanta ba,batare da anyi mata wani abu daya 6ata mata rai ba!"
Zeenat ce tayi maganar,yayin da idanunta ke fitar da hawaye,
 "Ni banyi mata laifin komai ba,kan dai maganar nan ce da take yawan faɗamun na cewar ta tsane ni bata sona,in faɗa mata su wanene iyayenta ko ta kashe kanta,ta 6ata mun raine yau saboda tayi mun tsawa shiyasa na kwashe ta da mari sannan nace taje kafin gobe in samu gawarta,shine fa ta fusata har ta aikata hakan,"
  Cikin shessheƙar kuka zeenat tace"meyasa ba zaki iya lallashinta ba?saboda me zaki sa hannu ki mare ta?kuma kika furta mata cewar taje ta kashe kanta bayan kinsan cewa ita yarinyace ba wayau tacika ba,yanzu gashinan kinja zamu rasa ta gaba ɗaya"cike da takaici Zeenatu ta ƙarasa maganar tare da komawa saman waiting seat ɗin ta zauna tare da kifa kanta saman laps ɗinta tana cigaba da matsar kwalla,hannu sofia tasa tana ɗan bubbuga bayanta,ɗagowa tayi da idanunta waɗanda suka rune jawur dasu,daƙyar ta iya buɗe baki tace"Mommy yakamata ki sanar da yayanta halin da ake ciki,tun kafin rai yayi halinsa,"
  A tsananin tsorace Mommyn tace"bazan sanar da kowa ba,idan ma ta mutu bazan bari wani ya sani ba,guduwa kawai zanyi in yaso daga baya sunji labari,don wlh bazasu ƙyaleni ba,"
 "Saboda me kika ce haka mommy"?
"Zeenat mubar zancen kawai,ni kaÉ—ai nasan halin da nake ciki,"tayi maganar tare da kifa kanta jikin bangon da take tsaye,
 Jikinsu ba ƙaramin sanyi yayi ba,
"Amma mommy meyasa kike 6oye mana abubuwa da dama game da Amrish?har yau bamu ta6a ganin mahaifinta ba,bayan wannan bamu ta6a ganin wani acikin dangin ku ba,sae mutun É—aya kawai,yayanta dake zuwa wurinta ...."
 Kasa ƙarasa maganar tayi saboda ganin irin juyowar da mommyn Amrish tayi a ruɗe,la66anta har rawa sukeyi wurin cewa"Kar na kuskura na ƙara jin kinyi mun wannan maganar!baida amfani sanin wanene mahaifin Amrish!Ni ɗin nan ni ce Mahaifinta kuma ni ce mahaifiyarta!!
 Shiru sofia tayi,batare da ta ƙara cewa Komai ba,,,,,,,,
Ranar dae A asibiti suka yini har dare ya ritsa dasu,
*Boss Bature*
â¤ðŸ¤â¤
Fitowarsa kenan daga cikin toilet jikinshi na sanye da bathrobe,hannunsa kuma na ruƙe da short towel yana ɗan matse sumar kanshi,wani irin daddaɗan ƙamshi ne ke fitowa daga jikinshi,tamkar wanda aka tsamo daga ruwan turare,saboda ƙamshi,gaban dresssing mirror ya tsaya yana ƙarasa tsane sumar kan tashi,ɗan dakatawa yayi tare da wurga eye balls ɗinsa ta cikin mirror yana kallon Shimfiɗeɗen gadonsa,bedsheet ɗin duk yayi squeezing,ga blanket ɗinsa dake a cukurkuɗe saman gadon,komai ya hargitse ba don komai ba sai don rashin mai gyara,2 days kenan ba'a gyara mashi part ɗinsa ba,a ƙa'ida duk rana sai an canza mashi bedsheet da Blanket amma yau har 2 days ba'a musanyasu ba,mutun ne shi mai tsaftar gaske,ga ƙyanƙyami,gashi ko kaɗan baijin zai iya ɗaga yatsanshi da sunan zai gyara bed ɗin nasa,ba don komai ba,sae don saboda kasancewar shi mutun mai matuƙar Ji da kanshi,a wurinshi wannan tamkar ƙasƙanci ne da matsayinshi ya zuƙunna da sunan zai gyara bedroom ɗinsa,tamkar ƙaskanci ne namiji yayi aikin da mace ya dace tayi shi,ko ba don wannan ba shi tun yana yaro ko tsinke wannan acikin gida kawar masa shi akeyi,sam bai iya aikin gida ba,wanka ne kawai yakeyi ma kanshi,amma da zarar ya fito daga toilet akwai masu taimaka mashi wurin yin dressing na Outfits ɗin da zaisa,
Yana cikin tsayuwar nan,Yaji sallamar Azmee daga cikin palour ɗinsa,bai amsa mata sallamar ba,hannu yasa tare da ɗaure igiyar Bathrobe ɗinsa sosai,sannan ya juya tare da nufar ƙopar fita daga bedroom ɗin,adai dai bakin ƙopar ya tsaya tare da goya hannayenshi asaman wide chest ɗinsa,
Azmee kuwa tunda taga ya fito gabanta ya shiga faÉ—uwa,dama zuwa tayi don ta gyara mashi part É—insa,
 "Where's she"? Ya tambaya batare da ya aza eyes ɗinsa akantaa ba,
 Tunda ya ambaci hakan ta gane cewa akan sehrish yake magana,don haka tace"Tana a bedroom ɗinsu,"
 "Okey,call her right now,"
Yayi maganar cike da bada Umarni sannan ya juya tare da shigewa cikin bedroom É—insa,.Â
 Juyawa Azmee tayi da sauri ta fuce daga part ɗin nasa,downstairs ta saukko kai tsaye ta nufi ɗakinsu Sehrish,hannu tasa tare da knocing ƙopar,a lokacin duk sunyi nisa acikin baccinsu,can cikin bacci Sehrish taji bugun ƙopar ɗakin nasu,buɗe idanunta tayi a hankali sunyi mata nauyi saboda wani irin bacci da take ji,jikinta a kasalance ta yunƙura daƙyar ta sauko daga saman gadon ta buɗe ƙopar tana tambayar wanene,
Tunda taga Azmee taji gabanta ya faÉ—i rass,duk da batasan meya kawota ba,
"Aunty azmee lafiya?tayi tambayar tana yin hamma,
Azmee tace"ina fa lafiya,Sgr ne ke son ganin ki,yace in kira mashi ke yanzun nan"
Daram taƙara jin gabanta ya faɗi,"nashiga uku ni yau,"ta faɗi hakan tana yarfa hannu,
  "Yakamata kiyi sauri kije tun kafin ya hasala,don da alama yau ranshi a 6ace yake,"ta ƙarasa maganar tare da juyawa ta bar ƙopar ɗakin nasu,
 Jiki a sanyaye sehrish ta koma cikin bedroom ɗin nasu,gaban wardrobe taje,ta buɗe ta ɗauko mayafi ta yafa shi asaman kanta,kayan bacci ne ajikinta,
Fitowa tayi daga ɗakin,ƙafarta na sanye da slipper,tana tafiya cike da zullumin me zai biyo baya,ba komai take hangowa ba face tafin hannun Sgr,ya wanka mata mari,har runtse ido takeyi saboda ganin abun take kamar dagaske,tana ƙoƙarin giftawa ta babban falon ta wuce sama,kwatsam Abusufyan ya fito daga bedroom ɗinsa ya hango gifcinta,tsayawa yayi yana ƙare mata kallo daga inda yake,jinjina kanshi yayi tare da lalla6awa yabi bayanta,cikin sanɗa batare da ta sani ba,
 Hayewa tayi saman stairs ɗin,sannan ta wuce part ɗinsa,bakinta ɗauke da sallama ta shiga ciki,babu kowa a falon nasa,tsayawa tayi a tsakiyar Sofas ɗin,don bazatayi gangancin shiga bedroom ɗinsa ba,ƙwara daganan idan taga ya harzuƙa ta watsa da gudu,amma in can ciki ne zai iya kama ta,
 Tana cikin tsayuwar nan zuciyarta na ɗar ɗar,taji motsinshi da sauri takai idanunta kan ƙopar bedroom ɗinsa,gabanta ne ya faɗi rass ganin shi a tsaye,hannunshi ɗaya ruƙe da waist ɗinshi,yayin da yake sanye cikin sleeping dress white color ba ƙaramin kyau su kayi mashi ba,Amma fuskar nan fa babu annuri ko misƙala zarratin,
 Da hannu yayi mata alamar tazo,hakan yasa ta nufi wurinshi ɗan nesa dashi ta tsaya sannan tace"Gani,"
Hakan da tayi ba ƙaramin 6ata mashi rai yayi ba,maimakon tazo kusa dashi saita tsaya nesa dashi,
  "Ni kike so in ƙaraso inda kike"!?
Girgiza kai tayi alamar a'a,jinjina kanshi yayi tare da matsa mata hanya yace"shiga ki gyara mun bedroom É—ina,"
 kasa motsawa tayi saboda alƙawarin da ta ɗaukarwa kanta na cewar bazata ƙara zuwa part ɗinsa ba,da sunan yin aiki,saboda umarnin mahaifinta,
 Ja da baya ta ɗanyi tare da girgiza mashi kai gabanta na faɗuwa ga tsoro amma ahaka ta daure ta cije tace"daddy ya hanani,"
Wani irin kallo da yayi mata ita kanta saida ta girgiza,tausasan la66ansa har kerma sukayi wurin furta"Ni kike faÉ—ama cewa Daddy ya hanaki"?
..shiru tayi tana faman zare ido,hakan ya ƙara fusata shi,gadan gadan ya tunkarota,ƙoƙarin juyawa tayi amma ina kafin tayi wani yunƙuri tuni ya ruƙo mayafinta nan take ya zame ƙasa,kwakkwaran damƙa yayi ma gashin kanta,hakan yasa tayi screaming saboda Zafin da taji,
 Jijjiga kan nata yayi,tamkar wata Ƴar babyn roba haka ya ɗaga ta gaba ɗayanta da hannu guda,kuma ta hanyar gashin kanta daya damƙa,wutsil wutsil tashiga yi da ƙafafunta,hawayen azaba na gangarowa akan fuskarta,fashe mashi da kuka tayi muryarta na rawa ta shiga faɗin"Wayyo Allah na!Babban yaya dan Allah kayi haƙuri ka sauke ni ƙasa,wlh bazan ƙara ba,zan gyara maka ɗakin,'
 Zuba mata ido yayi yana kallonta tun daga ƙasa har sama,wata ƴar ƙarama da ita,mamakinsa a ina ta samu ƙwarin guiwar gaya masa magana batare da jin shakkarshi ba,
 "Babban yaya dan Allah ka sauke ni!Wayyo Allah da.. daddy,nashiga uku,zai kashe ni,gashin kaina zafi,zai cire mun gashina,"saboda tsabar kuka hada majina,fuskarta tayi jaga jaga da hawaye,sai da ta galabaita sosai sannan ya saki gashin kan nata,gaba daya ta zube saman guiwowinta saboda jikinta da ba ƙwari,
    Zura hannayenshi yayi acikin aljihun dogon wandon dake ajikinsa,sannan yace"Tashi ki shiga ciki,ki gyaramun bedroom ɗina"
 Jikinta na kerma ta miƙe da sauri da sauri ta tunkari ɗakin nashi tana faman shessheƙar kuka,tana ɗaga ƙafarta zata shiga ɗakin taji an dakatar da ita,
 "Karki kuskura ki shiga ɗakin nan"!!!! Rass taji gabanta ya faɗi jin Muryar daddynsu,a firgice ta juyo don ta shaidawa idanunta,
 Shigowarshi kenan cikin palourn yayi maganar,a wani sukwane Sgr ya wurga eye balls ɗinsa akanshi,takawa yayi har zuwa gabanshi ya tsaya suna Facing ɗin juna,sannan yace"meyasa kake son takura rayuwarta ne?yarinyar nan ba ƴar aiki bace,ƴata ce!kuma ni ne na bata Umarnin cewa ta daina aiki acikin gidan nan!akan me kakeso ta fifita Umarninka akan na mahaifinta?matsayinmu ɗaya ne a wurinta ne"?
Wannan maganar ta Abusufyan ba ƙaramin Fusata shi tayi ba,Yadda kasan zaki haka ya shiga fitar da huci ta hancinsa,ya ma rasa amsar da zai ba Uncle ɗin,saboda zuciyarshi da ta hasala,don har bugu zai iya kai mashi,muryarshi na kerma yace"Un...cle!Are u telling me dat matsayinmu ba ɗaya ba a wurinta!"jinjina kanshi ya shiga yi yana fama ciccije la66ansa,ran manya ya 6aci,yaci gaba da cewa
 "Of course our position is not the same,but she's my younger sis,ina da right ɗin da zan sanyata aiki tayi mun,why kake so kajamin raini a wurinta"! daƙyar voice ɗinshi ke fita saboda tsabar 6acin rai zuciyarshi har wani tafarfasa takeyi,
 "Ba raini nakeso naja maka ba a wurinta!tabbas ƙanwarka ce ita halak malak,kuma kana da ikon da zaka sanyata abu tayi maka,wannan gaskiya ne,amma Ni mahaifinta na hana haka!ban amince ba,tayi aiki a ƙarƙashin kowa ba,Azmee itace mai aikin gidan nan!ita yakamata ace tana yin duk wani aikin daya dace,idan ma Aikin azmeen ke baka so,Zan iya sawa a ƙaro wasu masu aikin da zasu rika yi maka,amma ba ƴa taba,saboda ita ba ƴar aiki bace......"tunkan ya ƙarasa maganar Sgr ya daka mashi wata irin gigitacciyar tsawa,a tsiwace yasa hannu tare da toshe ears dinsa yana faɗin"ENOUGH!Enough!banason ji,banaso,she must execute my Command,that's may final say" ya karasa maganar yayin da idanunshi ke aruntse ruff ya rufesu
 Abusufyan yayi ma tsawar,amma gigitar da sehrish tayi,tamkar zata zauce,ƙanƙame jikinta tayi,cike da fargaba,
  Zuba mashi ido abusufyan yayi yana kallonshi,a hankali ya zame tafin hannayensa daga toshe kunnuwansa da yayi,a hankali ya ɗan ware blue eyes ɗinsa,tare da juyawa ya kalli wurin da Sehrish ke tsaye a ƙopar ɗakinsa yace"Wuce ciki ki gyaramun bedroom ɗina"!babu wasa a fuskarshi yayi maganar,wannan ƙarfin halin na Sgr ba ƙaramin mamaki yaba Abusufyan ba,a tsananin tsorace ta wurga idanunta kan daddynsu don taji me zaice,
  "Karki kuskura ki sanya ƙafarki a ɗakin nan!idan har na isa dake"!!wannan shi ake kira da tashin hankali,zazzare idonta tayi tana kallonsu,ta rasa Umarnin wa zata bi,A zarihi dae tafi tsoran Sgr,a baɗini kuwa tafi son tabi umarnin mahaifinta saboda sanin matsayin da yake dashi a wurinta,sa6a mashi zai iya haifar mata da gagarumar matsala a rayuwarta,haka zalika sa6ama sgr ba ƙaramar matsala zaija ma kanta ba,ta rasa inda zata tsayar da kwayar idonta,idan ta kalli Sgr sai ta kalli abusufyan,kowannansu ita yake kallo,daga ganin fuskar Abusufyan zaka san cewar hankalinsa ba a kwance yake ba,babban abunda yake fargaba shine Sehrish taƙi bin Umarninsa,duba da yadda ta gaza motsa jikinta,tabbas zai kunyata sosai kuma darajar da yake da ita ta mahaifinta zai zube ne a idon sgr,zai cigaba da ganin kanshi ne amatsayin Sarki,wanda ke bada Umarni kuma dole abi,
 Wata irin tsawa sgr ya daka mata,wadda har sai da jikinta ya girgiza sosai tabi ta rikice,a fusace yace"won't u go in!"
 Yana rufe bakinsa,Abusufyan yace"idan har kika kuskura kika shiga ciki,zan yafe ki ne acikin ƴa'ƴana,babu ni babu ke!"
 Jin wannan maganar yasa ta fashe da matsanancin kuka,baiwar Allah tana a cikin tsaka mai wuya,yarfa hannunta tashiga yi tana faɗin"innalillahi wa'inna ilaihirraji'Un Ya Allah ka kawomun ɗauki!daddy!!babban yaya!!bansan ya kukeso inyi da kaina ba!!dan Allah ku ƙyale ni!kubarni in ba haka ba zuciyata zata iya bugawa in mutu,"
 Tuni jikin Abusufyan yayi wani irin sanyi,idanunshi suka cika tab da hawaye,tsananin tausayinta ne ya kamashi,kamar yaje ya rungumota ajikinshi ya lallasheta,Amma yaci alwashin cewa bazai ta6a bari Sgr yaci nasara akanshi ba,
 A 6angaren Sgr kuwa,ya gama hasala tunda yake a rayuwarshi bai ta6a bada umarni aka tsaya yi mashi jayayya ba sai yau,sau ɗaya yake bada command kuma dole abi batare da anyi mashi musu ba,runtse idanunshi yayi tare da tura yatsun hannayenshi cikin sumar kanshi yana cakuɗata,yayin da yake ɗan cizon lips ɗinsa,wani irin huci ke fita daga hancinsa,wannan ɗabi'arsa ce aduk lokacin da ranshi ya 6aci sosai,steps uku ne matakin hauhawarshi,idan yakai step na ƙarshen the most dangerous kenan don tamkar aljani yake komawa kuma kowaye gabanshi bai gani tamkar makaho yake komawa,a wannan step ɗin idan ya damƙi mutun a hannunshi yana bugunshi sae yaga gawarshi,kuma babu mai iya control ɗinsa har sai lokacin da Allah yasa zai dawo hayyacinsa,amma zaiyi wuya yakai wannan step ɗin sai in ya damƙi mai laifi zai hukunta shi,iya step na biyu yake tsayawa,mataki na farko shine zaka ga yana huci yana zagaye wuri,na biyu kuma Shine yake cizon la66ansa sosai,ya runtse idonshi ya kuma cusa yatsun hannunshi acikin sumar kanshi yana faman sakin huci tamkar mayunwacin zaki,
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.