Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel By Hafsat Bature
Reading file: Abban Sojojin Takun Karshe.txt
Chapter 31 of 46
Ƙura ido jahad tayi tana ƙare masu kallo,gani take tamkar idonta ba dai dai suke nuna mata ba kamar mutun biyu ne kwance a gefen hagunta,hannunta ta miƙe tare da yaye masu Sehrish bargon da suka rufa dashi,gabanta ne ya faɗi rass!ganin Sehrish ga kuma hosana baje suna ta sharar bacci,nan take hankalinta yayi mugun tashi,wani irin tsoro ne ya lullu6eta,tabbas akwai mutun ɗaya 6angaren damanta,wanda suka kwana rungume da juna a ƙanƙame,wanda yayi silar taushe numfashinta,tashin hankali! kasa juyawa tayi don taga wanene saboda tsabar tsoro,sae dai ta zura hannayenta dake ta faman kerma ta laluba don taji in da gaske wani ne kwance a wurin,Sumar kan junaid ta shafo da hannunta,a razane ta zame hannunta,la66anta na kerma ta shiga furta"La'Ila ha'illah Anta subhanaka,Inni kuntu minazzalumin,"daga bisani ta shiga faɗin"innalillahi wa'inna ilaihirraji'Un!!,
Muryarta na kerma ta shiga kwalama su sehrish kira kaÉ—an kaÉ—an don kada aljanin ya farka,"Hosana!Sehrish!!dan Allah ku tashi!Mutum mutumi acikin É—akinmu saman gadonmu!ina tunanin Aljani ne ya faÉ—o É—akinmu don ya cutar damu,Wayyo Allah na" babban tashin hankalinta aljanin na akusa da ita,in ma cutar dasu yazo yayi toh ta kanta zai fara tunda itace a kusa dashi,
Tuni zufa ta gama wanko mata a fuskarta,numfashi kanshi daƙyar take fitar dashi don kada aljanin yaji yasan cewar idonta biyu,
 "Sehrish!Sehrish!!hosana!wai ba zaku tashi ba?dan Allah ku tashi kuga abunda na gani,asaman gadon mu,"tana magana hawaye na sauka daga idonta,don ita ta riga ta sallamawa kanta cewar ajalinta ne yazo,
  Duk wannan surutan da Jahad ke yi kaf a kunnan Sehrish,wadda ke lamo tayi nisa cikin zurfin tunanin da take yi,Duk a tunaninta Jahad mafarki takeyi shiyasa take sambatu,wannan dalilin ne yasa bata motsa ba,kuma bata tanka mata ba,idanunta ne kawae ke arufe amma idonta biyu,likimo kawai tayi,
Jahad na cikin wannan yanayin taji an aza mata hannu asaman waist ɗinta,a wani irin Firgice ta fashe da wata irin gigitacciyar ƙara,wadda tayi silar tashin hosana daga bacci,hatta sehrish sai da ta razana,a tare suka tashi zaune ita da hosana suna kallon Jahad dake ta ihun neman agaji,ai koda Hosana da sehrish suka ga hannun mutum a saman qugun jahad,a gigice suka duro daga saman gadon da gudun gaske har suna tuntu6e wurin tunkarar ƙopar ɗakin don su buɗe ta su gudu,jahad kuwa sam taƙi motsawa,sai ihu take tana kuka,waɗanda take tunanin cewa zasu taimaketa sun gudu sun barta asaman gadon ita kaɗai,jikinsu sae faman kerma yakeyi burinsu su buɗe ƙopar su gudu amma taƙi buɗuwa,hakan yasa Sehrish watsawa da gudu,ta shige toilet taja ƙopar ta rufe,ganin haka yasa hosana tunkarar wardrobe ɗinsu,ta buɗe gidan ƙasa da babu kaya sosai acikinsa sae bedsheets,Ta faɗa ciki tare da jan murfin wardrobe ɗin ta rufe shi,kowa yayi ta kansa kenan,duk wannan budurin da akeyi Junaid bai sani ba,domin kuwa ba ƙaramin abune ke iya tashinshi daga bacci ba,irin mutanen nan ne masu nauyin baccin tsiya,
Jahad na cikin wannan halin na firgici,taji an aza mata ƙafa asaman jikinta,firgitar da tayi ne yasa tayi wurgi da junaid gaba ɗaya,ya tafi dama yana dab da bakin gadon,aikuwa ji kake timmmm!ya ƙundumo ƙasa kanshi ya bugu sosai saman tiles,
raÉ—aÉ—in da yaji ne yasa shi farkawa daga baccin,ya fashe da matsanancin kuka,
  Gaban jahad ne ya faɗi rass!!jin sautin kukan Junaid,rarrafowa tayi ta dawo gefen gadon tare da ɗan leƙawa don ta tabbatar ma kanta abunda kunnuwanta ke ji,Zaro ido waje tayi cike da mamaki take kallonshi,yadda kasan wani jinjiri ya 6are baki sai kuka yake yi,da ƙarfi ta ambaci sunanshi"JUNAID"dakatawa yayi daga yin kukan da yakeyi jin an ambaci sunanshi,wurga idanunshi yayi akan jahad,yayi mata wuri wuri da ido yana kallonta,
 Muryarta na rawa tace"juj..junaid!dama kai Ne?me kake yi acikin ɗakin mu?
cikin shessheƙar kuka yace"Nifa Zuwa kawai nayi don in taya ku kwana,"
...zuba mashi ido kawai tayi tana kallon fuskarshi don abun ya fi ƙarfinta,
 Daga cikin toilet ta jiyo Muryar Sehrish tana ce wa"Jahad wai dagaske junaid ne?Naji kin ambaci sunanshi"?
 A ƙule jahad tace"Bansani ba,ku fito ku gane ma idonku,kunaji ina kukan neman taimako amma duk kuka watsa a guje kuka barni,yanzu da wani mugun abunne ba junaid ba,da Allah kaɗae yasan me zai biyo baya,"
 buɗe ƙopar sehrish tayi tare da fitowa daga cikin toilet ɗin,hosana ma ta buɗe wardrobe ɗin tare da fitowa daga ciki,suka tunkari inda junaid yake kwance yana faman sauke ajiyar zuciya,sae faman lumshe ido yakeyi,saboda baccin dake a idanunshi,
 "Junaid!" sehrish ce ta kira sunanshi,ware idanunshi yayi akanta yana kallonta,
.."junaid me kake yi a ɗakin mu?waya kawo ka?anya baka fara shan ƙwaya ba"
 Harara ya wurga mata tare da murguɗa mata baki yace"bansani ba,duk kun bi kun takura rayuwata,hakanan kawai ina baccina kun tashe ni,laifi ne in na kwana aɗakinku,ni ba ɗan uwanku bane"? Sakin baki sukayi suna kallonshi,hosana tace"wlh saina faɗa ma Daddy da Ya Omar,ince ka shigo ɗakinmu ka kwanta mana asaman gadonmu,ƙato dakai,"tana kai ƙarshen maganarta,junaid yace"idan kin tashi ki faɗama Kaka ƙarewar daddyn,mai kan kurciya kawai" wannan maganar ba ƙaramin fusata hosana tayi ba,jikinta har rawa yakeyi wurin dauko pillow daga saman gadonsu,ta buga mashi asaman fuskarshi,koda ganin hakan,sehrish ma ta ɗauko pillow ta shiga taya hosana,jahad tace"wlh nima bazan ƙyale ka ba,junaid saboda ka bani tsoro,kuma babu kyau ma tsoratar da musulmi,"tasa hannu ta ɗauko pillow itama,nan fa suka tasa junaid kamar sun samu jaki,suka dingi jibgarshi da pillows,tun yana yi masu magiyar su daina har ya sake fashe masu da kuka yana bubbuga ƙafafunshi,suna cikin bugun nan nashi,suka ji tsit junaid ya daina motsi,cikin sauri Jahad ta kalli jikin pillown hannunta,Ɗigon jini ta gani,ɗagowa tayi da nufin ta nuna ma su Sehrish aikuwa karaf idonta ya sauka akan pillown dake hannun sehrish da hosana,duk ɗigon jini ne ajikin pillown hannunsu,Tashin Hankali!
 Gaba ɗayansu ba ƙaramin kiɗima suka yi ba,ƴan hanjin cikinsu suka kaɗa,zagaye shi su kayi a zuƙunne suna kallon fuskarshi,
 Fashewa hosana tayi da kuka tana faɗin"Wlh babu ruwa na!bani na kashe junaid ba!"maganar da tayi ba ƙaramin tsoratar dasu tayi ba,tuni ido ya raina fata,daga wasa!?
 Jijjigashi suka shiga yi atare suna ambaton sunanshi"Junaid!junaid!!!ka tashi!dan Allah junaid ka tashi!!Wayyo Allah munshiga ukun mu!!dan Allah baby junaid ka tashi," ko motsi wannan junaid baiyi ba,matsawa sehrish tayi tare da kanga kunnanta asaman hancinshi don taji in yana numfashi,ɗufff taji babu numfashi da sauri ta sanya tafin hannunta asaman kirjinshi saitin zuciyarshi nan ma taji zuciyar tashi tadaina bugawa,a wani irin sukwane ta ɗago da idanunta waɗanda sukayi luhu luhu cike tab da hawaye tana kallonsu Jahad da hosana,jiki a mace tace"ZUCIYAR JUNAID BATA BUGAWA HAKAN NA NUFIN MUNYI SILAR MUTUWAR JUNAID"!!!
 Girgiza kai jahad ta shiga yi tana cewa"Junaid bai mutu ba,dan Allah ki daina faɗan hakan,kada ya tabbata dagaske,"tayi maganar a yayin da take kai hannu tana tatta6a fuskarshi"junaid!junaid!ka tashi dan Allah ka tashi junaid,"
  Ganin yaƙi motsi yasa suka fidda rai da cewar junaid zai tashi,kifa kai sukayi su duka ukun suna shessheƙar kuka,ɗan ɗagowa jahad tayi tare da kai idonta kan fuskarshi,Abun mamaki sae ga murmushi ya bayyana akan fuskarshi,dimples ɗinsa guda biyu sun lotsa,Wani irin ihun farin ciki ta saki tana fadin"Bai mutu ba!junaid wasa yake yi mana,gayanan yana murmushi,'jin haka yasa su sehrish saurin ɗagowa da kawunansu suna kallonshi,sae faman wangale baki yakeyi yana dariya,abun ba ƙaramin ɗaure masu kai yayi ba,
 "Junaid"sehrish ce ta ambaci sunanshi,a hankali ya buɗe manyan idanunshi yana kallonsu one by one,sai faman 6a66aka dariya yakeyi,
 Har suna haɗa baki wurin cewa"Kai junaid!meyasa zakayi mana haka?wlh ka tsoratar damu sosai,"
 "Wanda yasa kuka bugeni,ko tausayina bakuji,kun wani taru akaina kuna jibgata kamar kunsamu jaki amale,shiyasa nima na rama da gangan na ɗauke numfashina don kuyi tsammanin kona mutu"yayi maganar yana murguɗa masu baki,Ajiyar zuciya suka shiga saukewa,
 "Junaid dan Allah kayi haƙuri,bazan ƙara bugunka ba,kada ka faɗama kowa,"acewar hosana,
 Harara ya jefa mata tare da ƙara tamke fuskarshi,
 Cikin sanyin murya jahad tace"junaid baka da lafiya ne?mun ga jini ajikin pillow lokacin da muke bugunka,kuma da alama daga hancinka muka gogo shi,"
 Shiru ya ɗan yi yana kallonta kafin yace"Lafiyata ƙalau Ni,nose bleeding ne ba wani abu ba dama ina yawan yinshi,yafi zuwa mun da daddare,shiyasa baku ta6a gani ba"
 "Amma ka faɗama Abba ko wani game da nose bleeding din"? Girgiza kai yayi alamar a'a,da alama baison maganar,don haka yace"pls nidai mubar wannan zancen,kusan yadda za kuyi dani don Allah bazan iya komawa bedroom ɗina ba,tsoro ma nakeji,"yayi maganar ashagwa6e,
 Jiki asanyaye jahad ta kalli su sehrish tace"kuje ku kwanta,bari ni na rakashi ɗakin nashi," mikewa su kayi atare da ita da hosana suka koma kan gadon suka kwanta,tare da jan bargo suka lullu6e,
   Miƙewa daga zaune junaid yayi yana cewa"Allah sai dai ki goyani,don na riga dana faɗa maki cewa ƙafafuna ciwo suke yi mun bazan iya taka stairs ba,"
 Murmushi jahad tayi tare da cewa"shikenan,zan goya ka amma ka bari sai munje wurin benen tukunna in goya ka," amsa mata yayi da toh,sannan ya mike tare da ruƙo hannunta cikin nashi yace"Tashi muje,"mikewa tayi suka fita atare,suna tafiya tana satar kallon gefen fuskarshi kamar wani zautacce sai faman sakin murmushi yake yi,hakanan ta dinga jin gabanta na faɗuwa,lamarinsa ba ƙaramin mamaki yake bata ba,kokonto ta shiga yi anya wannan ɗigon jinin da suka gani na ha6o ne? Yanayin yadda abun ya afku tamkar ba jinin ha6o bane,tabbas akwai dae wani abu dake damunshi wanda baison kowa ya sani,
Tana cikin zancen zucin nata taji yace"Mun ƙaraso wurin stairs ɗin,yanzu ki goyani,ki kaini har bedroom ɗina,kuma ki kwantar dani,"
 Amsa mashi tayi da toh,sannan ta zuƙunna,ya daddage ya haye saman bayanta,tare da kwantar da kanshi luff kamar wani jinjiri,zagayo da hannayenshi yayi ta saman stomach ɗinta,hakan ba ƙaramin yanayi ya jefa ta ba,ji tayi tamkar bazata iya miƙewa tsaye ba,saitin kunnanta taji daddaɗar muryar nan tashi mai haɗe da shagwa6a"jahad ki tashi mu tafi,bacci nake ji,"
 Daƙyar ta iya mikewa tsaye goye dashi abayanta,hannu tasa ta tallaboshi sosai,sannan ta haye saman benen,tana tafiya tana tangal tangal har ta ƙaraso ɗakin nashi,hannu tasa ta ɗan tura ƙopar sannan ta shige ciki,Talal suka samu kwance yana ta sharar bacci,ƙarasawa tayi tare da sauke junaid saman gadon,ya gyara kwanciyarshi,bargo taja ta rufe mashi body ɗinsa zuwa neck ɗinsa,tana ƙoƙarin juyawa tabar wurin,taji ya ruƙo hannunta cikin nashi,jimmm tayi tana jiran jin me zaice mata,
 "Jahad"ya ambaci sunanta da wata irin murya ta mai jin bacci,
 "Na'am,"ta amsa mashi kiran a yayin da take juyowa" murmushi ya sakar mata tare da sanya yatsan hannunshi acikin dimple ɗin fuskarshi yace"Kiss me pls," bakomai ya faɗo mata aranta ba,face abunda ya ta6a faruwa atsakaninsu,cikin motarshi,daga zuwa manna mashi kiss a side face ɗinsa,bakinta ya goce izuwa cikin bakinsa,a ranar zauce mata yayi,
 Maƙe masa kafaɗa tayi alamar bazatayi mashi kiss ɗin ba,bubbuga ƙafarshi ya shiga yi yana yi mata shagwa6a,hakan ba ƙaramin burgeta yayi ba,saboda wani irin kyau da yake bayyana akan fuskarshi aduk lokacin da yake shagwa6a,tamkar tayi hugging ɗinshi ajikinta haka ta dinga ji,
  "Baza kiyi mun ba ko"?yayi maganar.yayin da idanunshi ke ƙoƙarin lumshewa,
  "Shikenan,zanyi maka,amma ka rufe idanunka," da sauri ya rufe su yana jiran jin la66anta asaman fuskarshi,tsayawa tayi asaman kanshi,tana karanto addu'o'i tana tattofa mashi akan fuskarshi,daga ƙarshe ta haɗe yatsun hannunta guda biyu na hannun damanta,a hankali ta aza yatsun nata asaman la66ansa,sannan ta furta sautin kiss ɗin da bakinta,wani irin farinciki ne ya lullu6e junaid,duk a tunaninshi bakinta ne ta aza asaman nashi,baisan cewa wayau tayi mashi ba,tasa yatsun hannunta amatsayin la66anta,
rufe mashi fuskarshi tayi da bargon,sannan ta kama hanyar fita daga bedroom É—in,
  "I Love u so much jahad," muryar junaid ce ta katse mata hanzarinta,dakatawa tayi tare da ɗan juyawa tana kallonshi,yana acikin bargon ya furta mata wannan kalmar,
  "Kina sona jahad"?
Wani irin ƙayataccen murmushi ne ya sauka akan fuskarta,bata bashi amsar tambayarba,cikin sauri ta fuce daga ɗakin nashi,ta koma bedroom ɗinsu ta kwanta zuciyarta cike fal da farin ciki,ta ji daɗin kalmar da junaid ya furta mata,duk da bata da tabbacin cewar ko dagaske yake yi mata," da wannan tunanin bacci ya ɗauketa,
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.