Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel By Hafsat Bature
Reading file: Abban Sojojin Takun Karshe.txt
Chapter 36 of 46
*Aunty Babba*
Suna kwance ita da hayaam sai faman sharar bacci sukeyi suna jan minshari yadda kasan bijimayen sa,sun cika gadon su biyu kawai,babu wanda ya farka acikinsu balle suyi tunanin yin sallar asuba,can cikin bacci Hayaam ta dinga jin ana bugun ƙopar ɗakin nasu tamkar za'a balle ta,dogon tsoki taja tana faman yatsina fuska alamar an takurata,a ƙule tace"Wai dallah wanene ke buga ƙopar ɗakin nan"!?
 Muryar hafsat tajiyo daga waje cikin shessheƙar kuka tace"Ni ce,ki zo ki buɗe mun ƙopa,"
 Jiki na rawa hayaam ta saukko daga saman gadon ta ƙarasa tare da buɗe ƙopar,gabanta ba ƙaramin faduwa yayi ba ganin fuskar hafsat sharkaf da hawaye,hankali atashe tace"Meya faru ne kike kuka"?
 A tsiwace hafsat tace"Ba dole inyi kuka ba!kun jefani cikin masifa!ki bani hanya na wuce,Da Mommy nake so inyi magana,"tana faɗin hakan ta bangaje hayaam tare da wuce wa ciki,duk tabi ta ruɗe,wani irin ƙululun baƙin ciki ne ya tokare ma hafsat maƙoshinta,lokacin da tayi arba da Aunty babba,baje saman gadon tana sharar bacci,wato hankalinta kwance ita,batasan wainar da ake toyawa ba,
 Da karfi ta ambaci sunanta"Mommy!Mommyyyyyyyy!
 A firgice Aunty babba ta farka,agigice ta tashi zaune tana faɗin"Lafiya hafsat kike mun irin wannan kiran"?
 "Ina fa lafiya mommy!ashe ke kina nan kina sharar bacci,ni kin barni cikin tashin hankali,jiya ko isasshen bacci ban samu ba,saboda tunanin hukuncin da Ya Omar da daddy zasu yanke mana..."
 Jin wannan maganar yasa Aunty babba fashewa da dariya tana tafa hannu,
 Hakan ba ƙaramin fusata hafsat yayi ba,muryarta na rawa tace"Mom...my dariya ma kike yi"?
Aunty babba tace"to me kikeso inyi in banda dariya,ke bakisan meya faru ba jiya"?
 Zuba mata ido hafsat tayi tana kallonta,
 "Hayaam zo ki faɗa mata da alama batasan meya faru ba,ae mu yanzu bamu da sauran damuwa,hankalinmu a kwance yake kamar muna cikin jirgi gobara ta kama," tana magana tana faman washe baki,
 Ƙarasowa inda hafsat take a tsaye,hayaam tayi fuskarta ɗauke da murmushi ta kalli hafsat tare da cewa"ke bakisan cewa jiya Ammi ta kori su Jahad daga gidan nan ba?korar ma korar wulaƙanci,ae shiyasa kika ga mun saki baki muna bacci hankalinmu kwance,saboda bamu da sauran damuwa yanzu,"
 Wani irin kallo hafsat ta wurga mata tare da cewa"Amma dae a mafarki hakan ya faru ko"?
 Aunty babba tace"Wani mafarki,jiya agabanmu Ammi ta korasu,da gudu suka fita daga gidan nan suna kuka,"
 Tsabar takaici ya hana hafsat cewa komai,
   Hayaam tace"Ae kawai ki kwantar da hankalin ki kema,babu mai tuhumarki akansu,Yaran da yanzu ba'asan ma inda suke ba,"
  "Mommy!dama tunanin da kuke kenan?shiyasa baku damu ba,ko kaɗan"
 ""Kwarai kuwa akan me zamu damu"?
Hannu hafsat tasa tare da dafe kanta,tana faÉ—in"Ya salam!Wlh Mommy idan mafarki kike toh ki farka!domin kuwa jahad da hosana suna acikin Gidan nan!babu inda suka je!!
 Wani irin bugu zuciyar Aunty babba tayi ji kake daraam,a ruɗe tace"Kamar ya kenan"?
 "Mommy Jahad da hosana suna nan!Yanzu haka daga bedroom ɗinsu nake,naje ne domin in nemi yafiyarsu akan laifin da muka aikata masu,"
 Saboda tsabar tashin hankali har suna haɗa baki Ita da hayaam wurin cewa"Jahad da hosana suna acikin gidan nan!!!"
 Jinjina kai Hafsat tayi kafin ta ɗaura da cewar"mun shiga uku mommy,mun ja ma kanmu bala'e da masifa!Ashe Ya Omar shine ya taimake su hosana acikin gidan Gonar mutumin nan,kuma a dai dai lokacin da yake ƙoƙarin yin raping ɗin hosana!
 Hannu Aunty babba ta aza aka tana fadin"innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!"
 Hayaam kuwa sai faman zazzare ido take,
 "Mommy,bugu da ƙari,a nan wurin Ya Omar ya tarwatsa kan mutumin nan ya mutu har Lahira,"tunkan hafsat ta ƙarasa maganar Aunty babba ta saukko daga saman gadon,hannayenta asaman kanta take fadin"Nashiga ukuna,Na bani na lalace,na ru6e!hafsat dan Allah ki faɗamun gaskiya,!dagaske baba alamu ya mutu!kuma Omar ne ya kashe shi saboda su Hosana!ashe shiyasa kenan naita neman number wayansa daga baya ban samu,wannan wata irin masifa ce!,
  Zarya tashiga yi acikin ɗakin tana faman cizon yatsa,Hayaam tace"Aunty laila don Allah ki kwantar da hanlinki...."
 Hankali tashe Aunty babba tace"taya zaki ce in kwantar da hankalina?bayan ga kashi cike a wandona,ni bansan wani irin hukunci Omar zai yanke mun ba" tana magana zufa na gangarowa a fuskarta,
 Ita kanta hayaam,duk a tsorace take duk da ba ita ta aikata laifin ba,amma ta razana da jin cewar Omar ya kashe mutumin da Aunty babba tasa ya zubar mata da yaran,
 "Yanzu hafsat menene mafita"!tayi maganar muryarta tamkar zata fashe da kuka,
 Kafin hafsat tace wani abu hayaam ta rigata cewa"Ni ina ganin kawai Aunty laila,ku tattara kawai kubar gidan nan ke da hafsat,"
 Wani irin kallon rainin wayau hafsat tayi mata tare da cewa"Mu tattara mubar gidan nan fa kika ce?ke kuma fa?ko kina tunanin cewa In asirin mu ya tonu,ke bazai shafe ki bane?tun wuri kusan inda dare yayi maku ke da Mommy!saboda kune baku da alaƙa da gidan nan!Ni kuwa ba inda zanje saboda nasan cewa duk hukuncin da daddy zai yanke mun bazai ta6a korata ba a gidan nan,saboda Ni ƴarsa ce,nan kuma gidan kakana ne,"
 Zuru zuru hayaam tayi jin abunda Hafsat tace,Aunty babba kuwa batasan ma me suke magana akai ba,saboda kanta ya ɗau chargy,sae faman zagaye ɗakin takeyi,ta rasa inda zata tsoma ranta taji daɗi,
  "Wlh da nasan yaran nan suna acikin gidan nan,da tun jiya da daddare zanbi dare,in taushe masu hanci da pillow har sai sun bar duniya don ubansu,yara sun zame man bala'e!"
 Girgiza kai hafsat tayi tana kallonta,har yanzu dae babu alamun dana sani atattare da ita,
 "Tunda nake ban ta6a shiga tashin hankali ba arayuwata sai akan waɗannan yaran!komai nasa agaba sai naci nasara akanshi,amma waɗannan tsinannun yaran sun tarwatsa mun duk wani plan ɗina,Ba kowa nafi jin haushi ba,face Ubansu,duk shine silar daya auri uwarsu a 6oye harta haifo mana mugun abu,Allah danasan da zaman yaran tun suna cikin ciki zansa a markaɗe munsu,don karsu duniya,'
 "Mommy dan Allah kidaina wannan soki burutsin!kin ishemu da surutu kamar wata zautacciya,duk waye ya jefa mu cikin halin nan in ba ke ba?maimakon ma kiyi tunanin sama mana mafita,Sai wasu sambatu kike marasa kan gado,ni bazan iya jurar jin waɗannan munanen kalaman da kike jifar su jahad dashi ba,inaso ki sani su ɗin ƴan uwana ne,"
 Juyowa Aunty babba tayi tamkar zata rufe hafsat da bugu,"Don Ubanki Har ni zaki faɗama cewar ƴan uwanki ne!sun fini kusanci dake ne?Ko ciki ɗaya kuka fito tare dasu ne?
 "Wlh mommy da ace ciki ɗaya na fito dasu dana fi kowa farin ciki,tun daga kan halayansu da ɗabi'unsu zai tabbatar maka da cewar mahaifiyarsu ta basu tarbiyyar daya dace,kuma ita mai kyakkyawar zuciyace shiyasa ƴa'ƴanta ma suka kasance masu kamar yadda take,Ni ce dai nayi babbar asara,dana fito daga jikin ki!gashi nan yanzu sai danasani nake....."kasa ƙarasa maganar tayi,a hanzarce ta watsa da gudu tabar ɗakin,saboda yadda taga Aunty babba ta tunkarota azafafe,yadda ranta ya 6aci ɗinnan komai zata iya aikatawa,
ƙafafunta ne suka fara yi mata raɗaɗi ba arziƙi ta koma daga gefen gadon ta zauna,idanunta sunyi jawur saboda tsabar 6acin rai,zuciyarta sae faman tafarfasa takeyi mata,tamkar zata fasa ƙirjinta ta fito waje,zama hayaam tayi daga gefenta,kowannansu yayi zuru zuru,
 "Aunty laila!ni ina ganin kawai ki gudu batare da sanin kowa ba,in ba haka ba,inajiye maki tsoron abunda zai biyo baya,"
  Cike da takaici Aunty babba tace"Hayaam naso ace hada Amani muka aikata wannan laifin,saboda banaso taci galaba akaina,yanzu in ishaq ya sake ni,ni kaɗae zanyi zawarci na,bakowa nafi jin haushi ba face hosana!mahaukaciyar banza,ina zaman zamana lafiya na,ta nemi tozarta ni agaban kannen mijina,wlh in har ta tona mun asiri,ni kuma sai nayi silar mutuwarta!!!!!!!!!!!!!!
 "Dan Allah Aunty laila kidaina kira mana mutuwa,muji da abunda ke damun mu,duk yadda za'ae yanzu kada ki bari kuyi arba da hosana ɗin, yunwa nata cinsu,amma saboda gudun haɗuwarta da Omar ko Ishaq,yasa ta gaza ko ɗan leƙawa waje,
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.