Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel By Hafsat Bature
Reading file: Abban Sojojin Takun Karshe.txt
Chapter 21 of 46
Bada jimawa ba,Hosana ta fito hannunta ruƙe dana sehrish,ɗayan hannun kuma ruƙe da hannun Jahad,jikinsu na sanye da hijab don tunda su kayi sallar Magrib basu ciresu ba,hosana ce kawai ta cire hijabin jikinta,ta yafa mayafi akanta,
da sallama a bakunansu suka shigo cikin falon,ya salam ae tuni Abusufyan ya zauna ƙasa dirshan yana lazimi,Abba kuwa sae faman jinjina kai yakeyi,gwaggon katsina kuwa tana ganinsu jahad ta shiga zare na mazurai don tasan cewa ƙarshe abun kanta zai ƙare ita da ta sanya mashi hannu ta ɗaure mashi mazaunai wurin yin auren batare da sanin Ammi ba,kowa dai yashiga zullumin abunda zai biyo baya,
 Aunty babba kuwa suna la6e ita da hayaam sun kasa kunne suna jiran jin mai zai biyo baya,jikinsu sae faman tsuma yakeyi,
 Zuba masu ido Ammi tayi tana kallonsu,one by one,ganin yadda matar ta ƙura masu ido yasa duk suka sha jinin jikinsu,daƙyar suka iya haɗa baki wurin gaishe da ita"Ina yini,"
 Bata amsa masu gaisuwar tasu ba,sae nuni da tayi masu da sandar hannunta alamar su zauna,wuri suka samu agaban kujerar da su Omar ke zaune,suka zauna daga ƙasa tare da lankwashe ƙafafunsu,zaman cin tuwo,
  Nuna Sehrish tayi da sandar hannunta tace"Ya sunanki"
 Jiki asanyaye sehrish ta bata amsa da cewa"Sunana Sehrish,"
 Ammi ta kuma cewa"wanene mahaifinki"?
 wurga idanunta tayi akan Abusufyan ta nuna shi da hannu tare da cewa"Gashi nan,shine mahaifinmu"
 jinjina kai Ammi tayi tare da kallon abusufyan wanda keta faman zubda gumi a fuskarsa,duk sanyin A.c din dake akwai a falon,
...hmmmm janye idanunta tayi daga kan Sehrish ta mayar dasu kan Jahad tace"Kefa ya sunanki"?
"Sunana jahad,"
"Wanene mahaifinki acikinsu,"
Juyawa jahad tayi tare dakai hannu ta nuna abusufyan tace"Shine daddynmu,"
Rai amatukar 6ace Ammi ta daka masu tsawar da ta gigitasu gaba É—ayansu duk suka razana,a tsiwace tace"Kowa ya zuba mun ido yana kallona,ba zaku faÉ—amun a ina kuka samo su ba?taya akai Abusufyan ya zama ubansu!"
Abba ne yayi ƙoƙarin buɗe baki yace"Ya'yanshi ne dagaske,kamar yadda suka faɗa Ammi,"
AruÉ—e Ammi tace "Ni kake faÉ—ama cewa Æ´a'Æ´anshi ne?kada ku raina mun hankali ta gidan ubanwa Abusufyan yayi aure da har zai haifi waÉ—annan balagaggun Æ´an matan!"?
Fashewa da kuka hosana tayi,sehrish da jahad kuwa tuni hawaye sun soma wanke masu fuskarsu,jikin Marshal ba ƙaramin sanyi yayi ba,haka zalika sauran dake zaune a wurin,
"Abusufyan!ka faÉ—amun taya akai ka samu yaran nan?Na yarda cewa Æ´a'Æ´anka ne koda basu faÉ—amun da bakinsu ba,saboda ina ganinsu nasan cewa Jinina ne su,ko ba don kamanninka dake akan fuskarsu ba,So nake naji TAKUN hanyar da aka Same su!?nasan halinka tun fil azal baka rabuwa da mata,ka faÉ—amun gaskiya,ka ta6a yin mu'amala da wata Æ´a' mace ne har ta samu cikinka"?
A kiÉ—ime abusufyan ya shiga yi mata rantsuwa yana faÉ—in"Wlh Ammi tunda nake arayuwata ban ta6a kusantar zina ba,Nasan cewa zaiyi wuya ki yadda dani,amma wlh saida na auri mahaifiyarsu sannan na same su,ga gwaggonan itace shaidata,"
 Tamkar zata rufashi da duka haka tashiga balbaleshi da masifa"Bazan ta6a yadda da kalamanka ba,karka kuskura ka ƙara cewa ta hanyar aure ka same su,in ba haka ba saina ci maka mutunci a wurin nan!dama najima ina zarginka abusufyan,banta6a tunanin zakayi mun haka ba,ka cuce ni,bazan ta6a yafe maka ba,rashin jin maganarka har yakai ka kawo mun Shaggu acikin zuri'ata,bazan ta6a lamun ta ba......'
 Rai a6ace gwaggon katsina ta katse mata hanzarinta da cewa"Ya isa haka,babu laifin abusufyan acikin wannan lamarin,Nice na aura mashi yarinyar da ta haifa mashi waɗannan ƴa'ƴan,don haka kidaina ambaton sunansu da shaggu saboda baki da hujjar yin hakan,bazan ta6a yarda a tozarta ƴa'ƴan abusufyan ɗina a gabana ba ehe," kowa yayi mamakin yadda gwaggon katsina ta mayar ma Ammi martani,tamkar wata mai cikakken hankali,
 "Dan Allah Ammi ki daure ki fahimce shi,rashin sanar maki da basuyi ba,shine babban kuskuren da Abusufyan da gwaggo suka yi,Gwaggo ta aikata hakanne saboda son da takeyi ma abusufyan wannan dalilin ne yasa ta aura mashi mahaifiyarsu batare da saninki ba,saboda tasan halinki,kin tsani auren bare,gashi shi kuma abusufyan ya kwallafa rai akan yarinyar,wannan ne yasa ta aura mashi ita,saboda gudun karya faɗa halaka..... "Wani irin kallo da Ammi ta jefa mashi ne yasa shi dakatawa da yin maganar da yake,wato Abbansu junaid,
 Aunty babba dake la6e ita da hayaam suna sauraronsu,saboda tsabar farin ciki kamar su zuba ruwa a ƙasa su sha,burinsu kawai Ammi ta koresu Jahad,
 Kowa saida ranshi ya 6aci a wurin nan,saboda yadda ammi ta haƙiƙance akan cewar bazata kar6i shaggu ba acikin zuri'arta,a ƙarshe tace"na riga da na yanke hukuncin korarsu daga cikin zuri'ata,banason ganinsu,kuma duk wanda yayi yunƙurin binsu acikinku wlh saina tsine mashi yabi duniya,kuma zan yafe shine acikin ƴa'ƴa Na,
 Wani irin matsanancin kuka su jahad suka fashe dashi,haka abusufyan ma kuka yake yi tamkar ƙaramin yaro,ƙiri kiri za'a rabashi da ƴa'ƴanshi,su Abba kuwa gaba ɗaya jikinsu yayi mugun sanyi,Hankalin Omar ba ƙaramin tashi yayi ba,haka zalika sauran kowa hankalinshi yayi mugun tashi,
 Su aunty babba kuwa dake la6e,jin an kori su sehrish,yasa suka daka uban tsallen farin ciki,saboda tsabar dariyar mugunta,hada hawaye,da gudu suka koma cikin ɗaki,suna faman dariya,burinsu ya cika,
"Ku tashi ku fuce daga cikin gidan nan tunkafin insa ayi waje daku,"jiki asanyaye suka miƙe tsaye jahad ta ruƙo hannun sehrish da jahad acikin nata,tafiya sukeyi kamar wanda aka zarewa laka,yayin da hawaye ke gangarowa daga idanuwansu,yunƙurawa abusufyan yayi da sauri zaibi bayansu,aikuwa abba yayi hanzarin damƙo rigarshi ya janyoshi,ya dawo da shi saman sofa din,a haukace ya shiga kiciniyar kwace kanshi yana fadin"Ka barni yaya hossein wlh sai dai ta tsinemun amma bazan bari rayuwar ƴa'ƴana ta wulakanta ba,duk inda zasu je ƙafata kafarsu,"ganin abusufyan na ƙoƙarin zaucewa yasa su Marshal Omar dasu ishaq da abbas suka rurrukeshi,sai faman hargowa yakeyi,yana kokarin kwacewa don yabi bayansu sehrish,
bazasu iya jurar ganin halin da mahaifinsu ke ciki ba,hakan ne yasa suka fuce waje da gudu suna kuka,tamkar ransu zai fita,sae faman shessheƙar kuka sukeyi,
Suna cikin wannan yanayin Motar SGR,ta shararo da gudu cikin gidan,a tsiyace su kayi parking É—in motar,tunkan Amstrong ya buÉ—e mashi motar,ya sanya kafarshi tare da harba murfin motar,ya fito daga ciki,kai tsaye ya nufi wurinsu Sehrish dake a tsaye suna kuka,kwata kwata basu lura dashi ba,sae dai suka ji an ruko hannayensu,Jahad da hosana,a firgice suka É—ago suna kallonshi,"ku wuce mu shiga ciki,"yayi maganar tare da jan hannunsu,sehrish ma tabi bayansu suka koma cikin falon,jin sallamar Sgr yasa hankalin kowa komawa kansu,ganin ya dawo dasu sehrish yasa kowa ya shiga sauke ajiyar zuciya,Zuba mashi ido Ammi tayi tana kallon ikon Allah,
 ƙarasawa cikin falon yayi tare ce masu sehrish"Ku samu wuri ku zauna,"jiki asanyaye suka samu wuri ƙasa suka zauna,suna faman sauke ajiyar zuciya,
 Zama sgr yayi asaman sofa,tare da aza ƙafarshi ɗaya bisa ɗaya,yayin da yake fuskantar Ammi wadda ta zuba ma sarautar Allah ido,
 Sai da ya mula yasha iska sannan ya soma magana
  "dama saida raina ya bani cewa hakan zata iya faruwa,that's the reason why na tanadin hujja ɗaya kuma kwakkwara wadda zata wanke zargin da kikeyi akan abusufyan da kuma waɗannan triplet ɗin,"
 Ƙarasa maganar yayi tare da sanya hannunshi cikin aljihun wandon jeans ɗin dake ajikinshi,ya zaro wayar shi,
 Â
 *mu haɗu On monday don jin yadda zata kaya,*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.