Complete Hausa Novels

Abrah Complete Hausa Novel

Reading file: Abrah_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 10 of 21

kashii 🤦🏻‍♀ gaskiya na gaji typing... ✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻bye mee ammyn kairat
golden girl

*♠ABRAH*♠

*NA*

*AMMYN KHAIRAT*
(GOLDEN GIRL)

*Dedicated to Teemarh cute*

(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
Wannan Page sadaukarwa gamasoyana masoyan
ABRAH novel

*page 30*

*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*

*(ADU'AR*Roqon RUWA*)
*Allahumma ASKINA GAISAN. MUGISAN.MARI'AN. MARI'AN NAFI'AN GAIRAA DHARRIN. AJILAN. GAIRAAJILIN.*
*Allah kasa mudace Ameen*

Sweetheart tace son ka kwantar da hankalinka insha Allahu kasameta Abban shi yace fada mashi dai kan macce zaka zauna kana kuka sai kace ba namiji bah share hawayenka karka bada maza mana Dr. Shureem ya share hawayen shi tare da fadin Abbah bazaka gane ba irin son da nake mata injin kamar in narasata narasa rayuwata gashi ta tsaneni ya qarasa maganar da kuka ban ta6a sani haka so yake ba? Saida cutarshi ta kamani Ashe haka sauran matanda suke sona sukaji ya yin danace banasansu?

Abban shi yanisa Abinfa na Dr. Shureem ya girmi tunanusu aman insha Allahu yayi Alqawarin nemamashi Auranta ko yar wacce gidace dan ganin farin cikin gudan tilon dan nashi "

Kafadarshi ya dafa my boy son dago kanka ka kalle ni indai ina raye to ba kai ba kuka duniya wannan hawayen su zama na qarshe da zan sake gani a wajanka hawaye indai bana farin ciki bane to ban son ganinsu a fuskar ka kaji

Dr. Shueem yace insha Allahu Abbah na dai na to ko kaifa inji Abbanshi

To tashi muyi magana kaida har yanzu baka san ka girma ba ji yanda ka hayeman jikin mata sai kace zata mai daka ciki gimbiya tace qyale shi Alhaji aini har kulum yaro ne wajena inba naga ya ajeman jika Ashirin ba jika Ashiin yafad'a tare da zaro ido haba Sweetheart sai kace sai kace me? Ta tari nufashin shi to shikenan Sweetheart Allah ya kawo masu Albarka Ameen shalele haka zakace"

Abban shi ya qyara murya dacewa son yau yaka mata kaje Abuja cinda weekend ne basamun time kake ba kaje ka duba yanayin tsarin ginin gidan da kuma yanda ma aikatan ke tsara hospital din dan so nake kana Aure mutare can gaba daya garinnan ya isheni zama waje daya tsotsai hakane Abbah bari na watsa ruwa na tafi dan ban so inyi dare yau nake son dawowa okay to shikenan Allah ya mai doka lafiya Ammen mya Abbah

Ya tashi yai ma Sweetheart dinshi kiss sannan ya haura zuwa upster wanka ya yi ya shirya cikin wani danyan boyel mai shegen kyau sai qyalli yake yana daukar ido farine sol ya yi kyau Abinshi sai wanda ya gani tamkar wani sabon ango "

Ya gyara sumar kanshi yau bawani styl yai mata ba kwantar da ita yayi ta kwanta luf gwani kyau sai sheqi take farar hullace yasa da fararan shoue sai silver Agogon hannun shi kai A gaskiya ban ta6a ganin wanda shigar manyan kaya tai ma kyau ba irinshi shigar ta Amshe shi ta fito da kyanshi da haibar shi

Haka ya fito yanata zuba qamshi gimbiya ta kalle shi tai tabzihi ga Allah da yabata Shureem murmushi ya yi ganin irin kallon da take mashi itama ta murmusa ya tako wajanta ya rugumeta yace Sweetheart ko na canza maki tace ka can zaman so sai my so kaga yanda shi garnan ta mai daka babban mutum ta fito da kamalarka wannan idan sirikar tawa ta ganka ai sai ta rude ranshi ya fari an ambaci abar sanshi baki yaqi rufuwa yace nizan wuce kar nai dare yau zan dawo tai mashi fatan Alkairi ko ya yafita harabar gidan dreven shi na jiran shi

Dan haka shiga ka wai yayi suka dau hanyar Abuja yayinda tunani Abrah ya Addabi zuciyar shi

Sunje Abuja lafiya komai ya yi kyau tsarin gini Abin birgwa dan daga qasar waje aka dauko photo gidan dana hospital din Akan hanyar su ta dawowa sukayi hadari inda suka buge wata mahaukaciya da ta hau titi ba dubawa kafin drever ya yi qoqarin kauce mata har ya bugeta cikin sauri suka fito ko motsin ba tai suka kamata sukasa cikin mota

Kasancewar shi likita ko kafin su isa yabata tai makon da yakamata ya bata ko gida ba su isaba hospital yace su nufa da ita bayan Anmata duk Abinda ya kamata harda Allurar barci a kai mata domin sai zabure zabure take

Gida yanufa agajiye
*♠ABRAH♠*

*Na*

*Ammny khairat*
(golden girl)

*Dedicated to Teemarh cute*

(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09

*Assalamu Alaikum masoyana masoyan Abrah ina mai matuqar baku haquri saka makon jina shuru da kukayi kuyi hawuri dan Allah Na gode;*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.