Complete Hausa Novels

Abrah Complete Hausa Novel

Reading file: Abrah_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 21 of 21

*page42&43*

🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚

__________📖jirgin su ya sauka ingila lafiya da man Ansan da.zuwansu sarauniya ta aiko daukar su masarautar ingala Aka nufa dasu
Sun samu tarba mai Kyau so sai Aka karrama su

Wani makeken part guda Aka basu mai dauke hudu koya ya Shiga da matar shi Sarauniya taji dadin zuwansu sosai sai murna take

Laila taga ba fuska ga Dr ta Dan haka bata tusa kantaba itama tasamu miji aure zatai sai Jan Abra take Ajiki musamman ma cikin da kegareta komai ta kawo Abra take nufa dashi ita Abra ta sake da ita

Sun zaga wajajan shaqatawa so sai daga cikiko harda fadar sugaban qasar na ingila wato kaka ga Dr Ambasadar ma'aruf kanada

Garin ingila yayi so sai ga Abubun tarahi Dana bude ido satin su biyu suka daga madina domin yin ibada da kuma Adu'o'i
Nan ma sati biyu sukayi daganan suka wuce Jordon sakayi sati guda sun zaga qasashe dadama duk sunyi siyayyar kayan bby

Suma su sirina da khairat matar Sauban duk sun qunshi nasu cikin tafiya yayi Albarka sun dawo gida lpy

Lokacin cikin Abra wata takwass da ya shiga watan haihuwa suka tattara suka dawo katsina A Cewar Dr ta haihu gaban iyayanta gidan su na katsina suka yada zango da man kaka Nana yanzu nan ta dawo da zama wajan Dan haka ita ta dawo da zama wajan Abra tana bata yan jiqejiqen magungunar na masu cikin

Cikin ikon Allah cikinta na shiga watan haihuwa ta haifo yaranta yan biyu macce da na miji duk masu kama da ubansu

Murna ga wannan family Abin ba'a magana ko da yaushe gidan tamtsan da jama'a sai Alkairi suke samu mai tarin yawa inda mai Naira shima

Yai ta sadaka ga yan UWA da Abokan Arziqi murnan samun jikoki da yayi

Haka Abban Abra shima ya taka tashi rawar gani balle mai gayya mai aiki harda kujerar makka ya rarrabama jama'a

Ta kowanne bangare dangi sunzo ranar suna Anti gagarumen biki na gani da fada yara sunci sunan kakannin su na mujin Akasama sunan Abban Abra maccen kuma sunan Gimbiya taci suncemata Gimbiya qarama

Taro ya tashi lpy Baki suntafi da gagarumar tsaraba a gidajen su Maijego da yaranta sunyi shar da su

Bayan tayi Alba'in tazaga dangi har jibya saida Abra taje wajan dangin ubanta daganan ta wuce zamfara wajan dangin uwar ta bayan ta dawo ta huta Dr yazo ya dauke suka koma Abuja

Dr Arziqi ya qara bunqasa Dan yanzu harda kasuwanci yake tabawa kuma Allah yasama Abin Albarka

Yaran su sun murmuge suna samun kulawa da gata

Abra ta qara zama babbar macce ta qara Kyau Dan inka ganta ba ka Gane ta

Yanzu ta wuce karatunta na low

Sirina ta haihu ita khairat suma duk sun wuce karatu

Sirina na karantar business khairat na karantar nursing

Laurat ta haihu Amma Dr kanwa inda taci sunan yarta ta baya wadda tarassa wato Amal Dr na matuqar qaunar Amal so sai
Kwanci tashi ba wuya Abra ta zama cikakkiyar barrister

Yaune ta fara zuwa kotu domin yin wata shari'a kuma Alhmdll ta samu nasara domin itace shari'a farko da ta fara kuma ta samu nasara

Dr ya sake Gina masu wani qaton gida sun koma Sabin gidan su Anan Abra ta sake haihu da na miji soyayyar su da Dr sai Abinda yayi gaba suna qaunar junan so sai sukeba junansu kulawa Dan yanda suke kula da junan su Abin sai ya birgeka yan biyu sun girma
So sai suna matakin secondary

Haka rayuwa taci gaba da tafiya cikin nasara

Da Annashuwa

Afannin kasuwanci Abra ta kudance tana tai makon yan uwanta da kuma mabuqata

Ko INA sai San barka Ake mata da fatan Alkairi

*Alhamdulillah Anan na kawo qarshen wannan labari nawa mai taken Abra kurakuran dake ciki Allah ka yafe man 👏🏻*

Ammyn khairat

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.