Abrah Complete Hausa Novel
Reading file: Abrah_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 11 of 21
*page 31*
Dr shureem A gajiye ya shiga gida Bayan yayi sallah isha i bisa kushin ya fad'a jagwaba tare da dafe kanshi da yaimashi zafi idanun shi rufe ;
Sweetheart ce tafito daga d'aki ganin shi dafe da kai ta nufo wajanshi dan batasan maya shigoba subahanalla my son lafiya?"
Da qyal ya bude eyes na shi da sukayi mashi ja yace my sweetheart im very tired na gaji sosai ga hungry inaji yunwa sosai sannu my son kasha hanya duk tadamu sai kace wanda yace bai lafiya ta kalmimshi takecire mashi bayan ta cire mashi tace" to bari na kawo maka Abinci nan kaci bai ce komai ba ta tashi ta hado mashi Abinci ta kawo mashi kan kafet ta Ajemashi itama ta zauna tana zuba mashi sannan tace sauko qasa zakafi jin dadinci
Da kanta take bashi Abinci A baki yanaci dan tasan koda yake fadin yunwa bawani na kirki zaiciba becouse bai son cin Abinci"
Tana bashi yana bata labarin zuwanshi Abuja inda yake sheda mata gini yayi kyau harda na hospital din yafi birgeshi sannan kuma yace" sweetheart hanyata ta dawowa mukai hatsari ai bata san sadda ta saki cop din hannutaba da ta dauko zata bashi ruwa a rude tace" hatsari son ba kadeji ciwoba yace" ah ah Allah dai ya tsare wata mahaukaciya ce ta kawo mana karo kuma da ita na tafe saboda mun bugeta da mota taji ciwo yanzu haka tana hospital kuma Abinda keban mamaki data farlka sai ta riqeni wai danta gimbya tace" karka damu duk cikin haukane yace" hakane sweetheart Aman inajin tau santa dan haka kafin nazo na kira malma Abdulrahaman na sheda mashi da safe zan kawo mashi tah ai mata Adu,a ko Allah yada Adace"
Gimbya tace" to Ameen my son shiyasa nake qara sonka saboda tai mako kayo halin mahaifinka"
Kacigaba da tai makama Al uma"
Ina Alfahari da kai Allah kuma ya baka mata ta gari"
Ameen yace" cikin da muwa domin Ta famamashi cinda ke mashi ciwo ita kanta ta ga hakan dan haka tace"
Gobe ne Alhji zaije gidansu sirikar tawa murmushi ya yi yace" Allah shi kai mu
Tace" Ameen
Sweetheart bari naje na watsa ruwa nadan huta nagaji tace" bazaka koma hospital din bane?"
Nagaji so sai sweetheart sai dai in Allah ya kaimu duk wad'an da ya kamata na duba na duba to shikenan Aje Ahuta aman bandafa tunani yace" to bye
Ya haura sama zuwa room din shi toilet ya nufa ya watsa ruwa bayan ya fito ya goge jikinshi ya shafa lotion da turare sannan ya d'auko kayan sleeping dinshi yasa masu laushin gaske
Computer shi ya dauko ya koma bisa bed ya zauna yan kunna ya jima yana yan ta6e ta6en shi daga bisani ya maidata wajanta ya koma kan yan rubuce rubuce bai tashi ba sai wajan Qarfe goma da rabi sannan ya kwanta"
Tare da jawo wayar shi ya kunna number ta ya tsurama ido gabanshi na faduwa;
Yana sonjin muryarta sosai Aman yasan ko ya kirata bazata d'aga ba?
Miya yai mata haka shi kanshi yasan Abinda yai mata jiya bai kyauta ba ai ban son ita be yanzu gashi naja taqara tsana ta
Haka dai yayi ta maza ya danna kiranta Abrah na barci taji wayar ta na ringin tsaki tayi tace" sirinah kin matsaman wallahi na gaya maki barci nakeji "
A tunaninta kawarta ce sirinah ta kirata dan basu dade da gama waya da itaba tana mata qorafin dr ta kirashi bai d'aga ba ta mashi message ba repyl"
Koda ta duba number sai taga ba quwar no to no din wacece wakeda wannan number ?
Har kiran ya katse tana nazarin mai number Acan kuma dr. Yaga kira ya dawo bata d'aga ba daman yasan Arin wai Ansaci zanan mahaukaciya🤣
Ko dai tayi barci yake tambayar kan shi bari dai nasake kira naji dan haka ba6ata time yasake dannan kiranta
Yanzukam ta dauka Assalamu Alaikum tace"
Cikin muryatta mai dankaran dadi kamar zuma saida gaban shi ya fadi dayaji zazzaqar muryata harda lumshe idanu hello hello helloooo shine Abinda Abra kefad'a
Please wake magana dan Allah wanne irin wulaqancine Akira mutum ayi shuru metssss taja tsaki ta kashe kiran
Jinshi yake cikin gajimare ko bakomai zaiyi kwanan farin ciki cinda yaji miryata"
aman yayi mamaki da take tambayar wanene shi saboda da kanshi yasa mata number sho kuma yasa suna kenan gogeta ta yi murmushi ya yi yace" jolley na kenan "
kinyi dai dai dakika goge dabaki gogeta ba da bazaki dauki kirana ba da banji muryarki ba yasake gyara kwanci tare da rugumar fillo yanaji wano felling na shigar shi dan haka yace bari nayi Amfani da wannan damar na cima wani burinawa"
Wajan message ya shiga dan rubuta mata saqo kamar haka
Please jolley am sorry na kiraki ban jinki network ne kiyi haquri wani masoyinki ne mai matuqar sonki da qaunar zan iya haukacewa dominki i love you ina sonki ina qaunar ki "
Zuciyar shi sai halbawa take shin ya turamata kokar ya tura mata tura mata shine shwarar zuciyar shi dan haka hannu narawa ya turama tayuya kwanci kenan taji qara saqo yashigo wayar ta jawo wayar yayi ta duba numbr da akakirata yanzuce ta karanta yafi so ukku to waye wannan
Ko dai malam billa ne amanshi kuma ai inada numbr shi
Dan Allah waye kai shine Abinda tatura ya kwance yana tajiran tsammani dan ya yi tunani bazata mai domashi ba saigashi ta maido wani bawan Allah ne mai qaunar ki ya maida mata humm bawan Allah bai da suna yana dashi mana kina son jin sunana?
Eh shiyasa ma na tambaya
To shikenan
Muhammad ne
Muhammad babban suna kowama indai namijine ai muhammad yake
Hakane aman ni shine sunan muhammad
Oky muhammad to na gode wanne gari kake?tatura mashi
Katsina
Katsina garummu daya kenan ina kasamu numbr ta?
Humm Abinda rai keso ai ko inane zakabi hanyar da kasame sho manta da butun numbr ni dai Abinda kawai zan ce maki shine inasonki
Bayan Allah da manzon shi da kuma mahaifana to babu wancce nake matuqar so sama dake dan Allah kisoni
Bayan ya karanta tace to shikenan muhammad na gode da irin son da kake man kuma ka bani time zanyi tunani Akai
Oky yace bayan ya duba badmuwa jolley kamar zuwa yaushe ya tura mata
zuwa rana ita yau
Wuuuo harsati daya ai zakisa zuciya ta ta buga ina laifin kice zuwa Asuba
Dariya tayi zuwa Asuba ai banyi tunani komai ba to shikenan zuwa gobe zakajini sai da safe dare ya yi barci nakeji
Bayan ya duba sai ya kalli agogo lallai dare ya yi sosao sha daya da rabi
Sai ya tura mata da oky thank you so much jolley good blessing you mutashi lafiya kiman waje inan zuwa maki cikin mafalki
Gaskya muhammad dan soyayya ne humm wannan irir zafafan kalame oky thank you good neght ta tura mashi ta kashe wayar ta
Bayan ya duba harda eehun dad'i goge number shi da tayi ya tai makamashi matakenan yace ya yi Adu.a ya kwanta
Asubar fari ya tashi sakamakon mafalkinta da yayi wanda ya zaman mashi jiki kulum ne sai ya yi mafaljinta sai dai in bai kwanta barci ba Abin mamaki ko dara nane indai zaiyi barci to sai ya yi mafalkinta kuma sai yayi wanka"
yanzu wankan yashiga bayan ya fito yai shirin masallaci ya nifa sun hadu da Abban shi bayan sunyi sallahr Asubah sai wajan bakwai da rabi suka fito
Abban shi yace" shureem kamar yanda mukayi magana da kai yau zanje gidan Alhaji ibirahim akan magana ka da yarinyar nan
To shikenan Abbah Allah ya tabbatar da Alkairi Ameen
bayan sun shiga gida sun gaisa da sweetheart din shi black tea ya sha ya fita zuwa hospital"
kamar yanda ya,saba duba marasala fiyar shi d'aki d'aki har ya zuwa wajan matar da ya bige tana ganin shi ta rungume shi tana fad'in dana yace" na am mama
Taso muje office din shi yajata ya zaunar da ita tea ya hado mata ta sha bayan ya magama Abinda da zaiyi tana zaune tana ta shir manta na mahaukata
tamashi barna so sai da ya magama ya jata suka fita cikin mota ya suka nufi gidan malam Abdulraham
sun gaisa da malam yace" to madalla insha Allahu komai zai dai dai ta"
Yace" to shikenan nan yabarta yatafi da qyal aka rabasu dan ta ruqeshi tana fadin danta "
qarfe hudu dai dai Aljha muhammad mai Naira ya shirya zuwa gidan su Abrah
kafin wannan time din daman muhammad mai naira ya kira baban Abrah ya fad'a mashi zai zo kuma ga abinda zai kawo shi"
hudu dai dai Aljahi muhammad mai Naira ya yi parking qofar gidan su Abrah
wayar shi ya kira Alhji ibirahim
yace mashi gashi waje
da kanshi yaje ya yai mashi iso
zuwa cikin gida
Parlour baqi ya sauke shi sun gaisa Amutum ce suna cikin gaisawa Abrah da hanif su kai salama
hannuwan su dauke da kayan motsa baki
cikin na tsuwa suka aje komai suka duqa har qasa suka gaishe da Alhji muhammad
shima ya Amsa masu cikin jindadi ya yo farin cikin gani yara da kuma irin tarbiyar su Adu,a shi Allah yasa su samu wannan irin
dady su Abrah yace Allhaji ga yarannan namu su kaidene gare ah ah masha Allahu Allah shirya
yace Ameen gasunan da fatima da kuma mai sunan babana
masha Allah ita dai Abrah kanta na qasa tana wasa da hijab dinta
bayan sun fita Alhaji muhammad ya gyara murya ce da farko dai Abinda ya kawoni shine dana yaga yar wajanka yana so to shine nace bara nazo naji inba ai mata mijiba to mungani muna so kan hauswa nacewa da zafizafi akan bigi qarfe
dady Abrah yace kai msha Allah ai mu garemu Abin farin cikine muhada zuri,a daku Alhji kuma na jidadin zan canka Abrah ai yar kace kaga shikenan tuwo na mai ma
ban mata mijiba sai dai wani hanzari ba guduba Abrah na da gurun yi karatun low kuma na mata Alqawarin cika mata burin ta indai zaku iya jira har wannan time din to dan yanzu tana shekara qarshe na secondry
muhammad mai Naira yace wannan ba abin da muwa bane indai karatune ba matsala zatayi shi koma wane irir ne harsai tace ta gaji dashi na maka wannan Alqawarin to shikenan Alhaji najidadi Allah ya tabba tar mana Da Alkairin shi
katuro yaron su fahimci junan su in Allah yasa sun dai dai ta kansu sai a tsaida magana to bakmai insha Allahu na gode suka sake gaisawa Alhj muhammad ya tashi dan komawa gida dadyn Abrah ya yo mashi rakiya suna tafe suna tau taunawa akan kasuwaci sai ya shiga motar sannan dadyn Abrah ya koma cikin gida "
topa mai karatu koya zata kasance Abra da tsani dr ta gashi kuma ga dukan Alamu dr ya samu shiga to ya zatai da malam billa kuma dr zai cigaba dayi mata basajane koko
kuma wacece wannan mahaukaciya indai mai karatuna biya dani to zai gane kowacece mahaukaciyar nan
sai naji daga gareku taku ce mai san ganin farin cikinku
Ammny kairat
*more comments more typin*
golden girl ce
*♠ABRAH♠*
*Na*
Ammyn khairat
*(GOLDEN GIRL)*
Dediceted to Teemarh cute
(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/
TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
*BISMILLAHI-RAHMANI-RAHIM*
*PAJE* 32
Cikin mutunci da dad'tako Alhaji muhammad suka Rabu da Alhaji ibirahim"
Zaune yaki cikin office dinshi bayan ya gama duk Abinda yake sai ya dauko wayar shi ya kira malam Abdulrahman suka yi magana Akan mahaukaciyar da ya kai mashi inda malam Abdulrahaman yake sanan da shi jikinta da Sauqi"
Ana ganin Alamun Nasara domun yanzu ta dai na sabbatun da take yi,
Inda dr. Yani sa yace" Allah ya qara bata lafiya malam yace" Ameen"
Byan sun gama wayar sai ya fad'a kogin tunani yanzu ko ya Abba ya yi da Abban Abra ko ya Amince ya bashi Auranta?"
Gashi ya kira waya Abban Nashi bai same shi ba yana cikin fargaba; Allah ka tabbata'man da Alkairi
Idan Abrah Alkairi ce A gareni Allah ka bani ita idan kuma ba Alkairi bace Allah ka fidda man sonta A zuciya ta Sai yaji An Amsa mashi da Ameen
Kan shi ya dago ya kalle su idanun shi sunyi ja jir kama garwa shi shi bai ma'san sunzo ba kuma Atunanin shi cikin zuciya yake fad'an komai murmushi yai masu Abokan shine Sauban da Sudais hannu ya basu saka gai'sa
Sun zura mashi ido sunata kallon shi kamar yau suka fara ganin shi tun ranar da ya hadu da Abrah yarasa Natsuwa da kwanciyar hankalli ya rame kamar ba shi ba sai idanu da suka qara fitowa soba ramar da ya yi ga hancin shi ya qara tsawo ya yi dan ziriri da shi ya yi rama ba kad'an ba duk da da man ba wani jiki ne da shi ba Aman duk wanda ya ganshi ya san ya Rame kuma yana tattare da da muwa suna mai tausa'yawa Abokin nasu domin ya fad'a tarkon so kuma sunaga kamar son maso wani ne yake ita yarinya ba son shi take ba"
Meyasa qaddara son shi tazo A haka ya jima bai'so ba Ai nahi bai son kowa mata ba su gaban shin da sun mashi maganar soyayya yanzu sun'6ata ko kuma ya tashi ya bar masu wajan in bai'jin yan rugimar sai gashi yanzu da rana tsaka ya kamu da soyayya da wada bata san yanayi ba" Ya Allah ka kawo ma Abokin mu dauke"
duban su ya yi yace" kai lafiya kunzo kun sani gaba kamar kun samu kayan kallo na chan'za maku ne? Nisawa suka yi tare kuma da had'in baki suka ce yes ka chanza mana so sai ka chanza mana"
Ashemu ba bakin komai muke Awajan kaba Ashe har'Akwai Abinda zaka iya b'oye mana shi Ashe mu bamuda wayo da muke fad'a maka sirin mu" ko ko mu bamuda siri ne da in wani Abu ya same mu har'jikin mu ke rawa muzo mu sanar da kai to bakomai mun gode"
((((((((((((((((((((((((((((((((((((((
Ka kyauta Sudais ya dubi Sauban yace" Abokina ta shi mu'tai cinda ba muda wani Amfani wajan shi suka ta shi zasu tafi yai sauri ya sha gaban su Yace" haba Aminne na bai kama kuyi man haka ba ban so insaku cikin da muwa ne shi yasa na taushe da muwa ta ban f'ada maku ba Aman cinda haka ne na yi laifi to Afuwan Am so sorry 👏🏻 ya had'e hannuwan shi waje guda duk maganar da yake fad'a masu muryar shi rawa take duk dauriya irin ta shi gaba yake da yin kuka saboda da man zuciyar shi cike take da tarin da muwa yana ne man wanda zai fad'a ma da muwar shi ko yasa mu sassaucin Abinda yakegi cikin zuciyar;
Hummm suka ce bakomai bama sai kafad'a mana ba cinda Abin siri ne mu ba mu kai matsayin mujiba to ba sai munji ba ruqe sirin ka zamu dai tayaka da Adu,a
Dan Allah kuyi Haquri haba Sauban Haba Sudais na gaya maku ban so ne nasaku cikin damu cinda kuma hakane Na baku haquri yaka'mata ku haqura kuyi'man uzuri da qarfi yake masu magana kanshi ne yaji ya sara mashi domin shi bai'iya hayaniya ba kuma bai' son yaji hayaniya dan ko doguwar magana bai cika yi ba sai ta kamashi dolle komawa ya yi ya zauna
Hawaye na bin fuskar shi ganin haka hankalin su ya yi mugun ta shi yau dr.Shireem ne ke'kua lallai Abu ya 6ace sai suce rabon da suga kukan shi har sun manta mutum ne shi mai dauriya da juriya Aman tunda ya kamu da cutar so ya koma mai rauni zuciya;
Dafa kafad'ar shi sukayi suna bubugawa Alamun haquri suka haba maza Na mazaje jarumi uban jarume haba karka bada muna"
Fad'amana mine matsalar menene da muwarka kasan mu masu shema ka hawanyen kane; fad'a mana waya ta6a mana kai"
Dago kanshi ya yi ya kalle su na d'an wani sakanni yace" meya sa so yai mani haka meya sa ita bata so na Ina da wani Aibu ne? Ko ban kai Namijin bane?" bain kai Asoni" bane?"
Banida haline mai kyau?" ko ko banda Nagarta ne"?
Banda ilimine"?
Koban girmama mutane?"
Ko ban da kyau ne ban jiki mai kyua ban da tsayine?
Banda fuska mai kyau koban da le6o mai kyau ku gayaman yafad'a da qarfi ban da komai ne da baza.a so'ni ba" ya fashe masi da kuka gaba'd'ayan su suka rungume shi suma kukan su lallai so da ban ne dan gashi harya zautar da Abokin su;
cikin kuka sukace zata soka so sai kanda komai kana duk Abinda kowace macce keso gana miji ka matan ta yanda yan mata ke rububinka"? Ba dan komai ba sai dan saboda Nagartar ka da kirkin ka da girmma muta ne da sanin ya kama ta ga tai makon Al,uma kana da mahaukatan kud'i Aman basu da meka ba burinka ka kyauta tama Alumma
Duk Abinda Ake bud'a gana miji kana da shi uwa uba ilimin na Addini ne da Na boko 6an garan Addine kai Ustaz ne koku ma muce ya shakk malam shireem shi kan shi sai da yad'an yi dariya domin sun ba shi dariya😄
Sukaci gaba da cewa ga kuma kyau wanda inaga baka duba madubi ka'ta6a jin Na miji yace" ma dan uwan shi Na miji yana da kyau to yau zan fad'a maka kai kyakyawa ne kyau so sai wanda ko Namiji ya ganka sai ya sake kallon ka ba dai Ai maka kallo guda A dauke kai ba sannan gaka da Le6o mai kyau wanda yan mata ke so wato peank lipes ga kuma uwa uba blue eyes ka had'a komai Abokina
Na tabba ta ita ma zata soka so so sai wanda har yafi wanda kake mata da bakin ta zata fad'a maka cewa duk duniya babu wanda take so sai kai ka kwantar da hankalin ka kuma kai ta Adu,a muma zamu tayaka Aman Abrah taka ce kai Na tane ban ta6a ganin masoyan da suka dace da juna ba irin ku"
Haka dai su kai ta kwantar mashi da hankali suna ta gaya mashi maganganu masu dad'a da sanyaya zuciya"
Shi kan shi ya jidad'an hakan domin kuwa Nauyin dake ga zuciyar shi ya ragu.
Na gode Abokane na shiya sa Ako da yaushe nake Alfahari daku domin banda kamar ku kuci'gaba da tayani da Adu,a idan Alkairi ce ita Agareni Allah yabani ita Allah ya karkato'man da hankalin ta da zuciyarta waje na taji bawanda take so sama dani in'kuma ba Alkairi bace Allah ya fidda man son ta Arayuwa ta yai'man za6i mafin Alkairi suka'ce"Ameen" gaba dayan su sukace"in'sha Allahu Abra Alkairi ce gareka Zaka Aureta in'Sha Allahu zata haifa'maka kyawawan ya,ya masu Nagarta wad'a zayi Alfahari da" masu Amfani ga Al,uma masoya manzon Allah (S.W.)
Sun sa shi farin ciki mara misaltuwa sai murna yake suma ganin yana murna suma sai sukai ta murna Abotar su ta yi dan haka suke kan si had'e yake idan dayan su na cikin damuwa to suma zasu kasance cikin damuwa sannan zasu hadu su tattauna kan da muwar har'sai sun samo mafita kuma suyi iya kar qoqarinsu nagani d'an uwansu yafita daga cikin da muwa Abotarsu Na birge mutane so sai dan mafi yawa mutane suna masu laqani da yan ukku ko kuma kai Ana jiran su da S.S. sabo dukkan'su sunan su yafara da s. Ne"
Zaunawa sukayi to yanzu gaya mana ya kuka yi da ita suke tambayar dr sai ya nisa yace" nifa har'yanzu ban fad'a mata da bakina ina sonta ba domin bata bani damar hakan ba kan ta rawa yake so sai tana da d'anyan kai kuma Abinda na fuskanta kamar bata so na,
Qarin 6awar danayi kuma itace mun hadu Dad'an kowa da ita taje wajan motasa jiki sai ban son miya kai ta har saman d'akina Ba niban son ita bace ina cikin motsaji Naji motsin shigowa Abin ya bani mamaki miya kawo macce har'nan saman UpStar in'da nake to ta juya Bayan tane ban samu ganin fuskar taba to Nikuma rai na ya riga da ya6e da ganin macce d'akin in'ba iskanci ba mezai'kawota wajan sai shedan yai tai ma hudubar banza na in mata Abinda bazata manta da shi cinda shiya kawo ta haka Nabi shawara zuciya ta koko in'ce huduba shedan dan haka na isa wajanta da wannani niya Abinda ban ta6a yiba shi na Aikata A gareta"
Ai ido suka zaro 😳😱 tare da tagumi sukace innalillahi mi kai mata injin dai... Sai sukayi shuru ba su ida ba injin dai me? Ku ida mana yace masu Ah Ah fad'a mana dai muna jinka me kai mata miya faru?
nisawa ya yi yace mi kuke tunani zan'mata kuna tunani zan'iya yi'mata wani Abu koda ma wata ce ba ita ba"
Kawai dai Abinda Nai mata ne sai ya yi shuru shine me sukace kaga gaya mana domin mu samo'mafita
bawani Abu nai mata ba illa Na d'an ma'mma tseta🙈
Na shanun ka wai Na ta6a sai bakin da Na tsotsa Amanfa duk Abinda ya faru idona Arufe🙈 suke sai da na gama Na bude ido na wuuo 😳 Nai mugun gani gani wadda banyi tunani ita bace" kuma Atake ta zageni ta kuma gaya man cewa ta tsaneni yanzu,tana man kallon dan iska;😭
Sudais da yake dan duniya ne yana da ta6a harakar mata yace kai na yi tunani ko Rage zafi kaye da ka yi fata fata da ita Ai da karege fama da ciwon mara dan wannan d'an Abu sai duk kabi ka tada Hankalinka"
kai fa dan iska ne wannan ne Abin batada hankali ba kako san istigifari konawa na yi har yan'zu cikin tuba Ga Allah nake"
Sauban yace" insha Allahu ka kwantar da hankalinka komai zai dai dai ta ita soyayya ba Ai mata nuqunuqu ka tun kare ta kai tsaye kace mata kana Sonta Ayi ta taqarel
yarinyar nan fa bazata saurare niba ko kiranta nayi bata d'agawa qarshe ma ta goge number ta dan jiya da Na kirata na yi mamakin da ta d'aga sai cewa ta yi wanene ni kuma jin haka yasa nai mata basaja muka sha hirar mu ta massege yan'zu haka yau tace zata fad'a man in na samu shiga bayan nan Abba ya tai ne maman Auran ta to ban san yanda su yi ba "
to kai kace Abu ma yazo gidan sauqi sai dai kace Akwai chakwakiya nan gaba in ta gano kai ne ke mata basaja ni'ina ga kawai ka Aje maganar basaja ka tukare ta gadan gadan komi kace" ni inaga zan cigaba da yi mata basaja lokacin da zata gane ni ne soyayyata ta mata illa yanda Bazata iya rabuwa dani ba to shikenan suka Allah ya tai maka yakuma shige mana gaba sukace"Ameen "
yanzu dai sai ka koma gida muji yanda kukayi da Abban sannan sai musake tattaunawa muga yanda zamu 6uloma Al,amarin.
haka dai suka ci gaba da tattaunawa har Akayi kiran sallar magariba suka ta shi suyo masalacin dake cikin hospital din dan gabatar da sallah bayan sunyi sallah su Sauban da sudais suka fito suka bar dr can dan shi sai ya yi isha,i da shafa,i da wutiri ko zai fito haka yake kulum
Bayan Anyi isha,i ya fito kai tsaye kamar yanda yake kulum d'akin pertion ko hakane ban'fa iya English ba 😫
wato wajan mara sa lafiya ya nufa domin basu magungunan dare dan yanzu da kan shi yake ba su magunguna dana safe da na rana da da'dare haka yakebi ko wanne room yana basu cikin tausa'yawa da girma'mawa yayin da hakan Na masu d'adi gashi dai babban likita Aman bai dau duniya da zafi ba did d'akin da ya shiga sai kaga suna sa mashi Albarka yara ko k'ana na har'zallo suke suna so ya dauke su haka cikin wasa da murmushi zai dauke su yai masu wasa cikin hikima da dubara zai basu magani su sha ba tare da sun san sun sha ba sai ya raba masu sweet da melik wasu yaran har kuka suke idan zai bar d'akin su uwayan d'iya na jin'dad'in wannan tabi'a ta shi suna yi mashi Adu,a da fatan gamawa lafiya"
wannan hali na shi yasa hospital din shi yaqara suna da dauka ka ko ina Ansan da shi garuruwa da da ma sai kaga Ana tururuwa zuwa Asibitin kulum cike yake da jama,a gashi kyauta ne ko sisinka baka biya su kan su ma,ai katan hospital din na jin dad'in zama da shi ba ruwan shi da kowa bai shiga harakar kowa suna girma mashi suna bashi girmani shi gashi dukk wata yake biyan su Albashi su"
qarfe goma dai dai yake ta shi daga hospital ya koma gida sai kuma bakwai na safe yanzu haka shirin tafiya gida yake"
*more commets mo typing*
takuce mai son gani farin cikinku da nusha dinku
*wato Ammyn'khairat*
golden girl❤🥰👏🏻
*♠ABRAH*♠
*Na*
*AMMYN KAIRAT*
(GoLDEN GIRL)
*Dedicated to Teemarh cute*
(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/
TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.