Abrah Complete Hausa Novel
Reading file: Abrah_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 18 of 21
Cigaba da ainta tayi har tagama ta jima tana jiran shi Aman shiru bai fito ba dan haka ta yanke shawara Shiva ciki ta isko shi shikuma barci ne yai gaba da shi tare da mafalkin Abin kaunar shi Abra wai yana kwance kan cinyarta ita kuma yana shafa sumar kan' shi
Yanata murmushi Salami tajima tsaye tana kallon shi yanda yake barci fuskar shi dauke da murmushi
Jitai kamar tai'ma cute lipes din shi kiss Aman badama dan haka ta kai hannuta bida lallausar sumar kanshi dan itace mai saukin ta6awa gareta jin Anashafa kanshi ya dauka duk A cikin mafalkinne sai wani qara gyara kwanci yake ita kuma jin taushi sumar shi tasa hannuta ciki taji sun lume cikin sumar har wani lumshe ido take tana fadin Ashe haka sumar take da laushi sai yamutsa mashi suma take shikuma jin Abin na yawa yasa shin kamar ba,a mafalki bane ita kuma dai dai ta dugo kanta Zara sumbaci sumar shi dai ya bude idon shi Yayi to zali da bajejen hancin ta zumul Yayi ya tashi zaune ita kuma taja baya wani mugun kallo ya watsa mata Wanda yasata fita bata shirya ba tana fadin sorry sir. Da idanun shi yabita wadanda sukayi jajir saboda baccin da ya dan dauke shi sai wani motsa mazauna take rumtsai idanun shi yayi tare da gilgiza kai yace" mata mata!!
Ta shi yayi ya shiga toilet ya watsa ruwa domin yau juma,a kuma yaga lokaci na qara towa ya fito ya gyara jikin shi tare da shafa mai ya sake kayan shi farar shadda yasa da farra hulla .
Yanada komai a office din shi kamar yana gida tarare yasa sannan ya fito dan zuwa masallaci Ahanya ya gadu dasu Sauban da Sudais suma zasu masallaci sun gai'sa kowa yayi wajan motar'shi .
Shima Dr ya shiga drive ya sahi kamar d'azun sukafita zuwa masallacin q'erau shi suka nufa domin halartar sallar juma,a
Abra sai shirya shirya tarbar Malam Bilal Ake domin yau ne yace"mata zai'zo in anfito juma'a tasanar da dadyn ta cewa malamin su yace zai'zo su gai'sa dady yace"to sai ya shigo .
An gyara dakin saukar baqi harda su tararen wuta komai ta kai na motsa Baki shi kawai Ake jirah momy dai sai binta da ido take domin itafa tafi son Dr da kowa kuma tana mata Adu,ar samun shi A matsayin miji.
Bayan Anfito juma,a kamar yana yace" gidan su Abrah yayi tsinke sai da yazo bakin get sannan yace mata gashi yazo A time din. Ita kuma suna tsakar cin Abinci ta dubi mahaifin ta dan shima sun rigada sun dawo daga masallacin shida hanif
Dady shinan yazo malamin mu owk Hanif jeka shigo da shi d'akin baqi hanif yafita yana turo Baki cikin ran'shi yace"sai ya kira Dr ya fad'a mashi .
Mai gadi hanif yace ya bude get shi kuma Bilal ya shigo da motar'shi hanif ya gai'she shi cikin girma mawa domin sun samu tarbiya mai'kyau
Ba laifi kyakyawa ne cewar hanif da yaqarema Bilal kallo .
Jagora yai mashi zuwa d'akin baqi sannan yaje ya sanar dasu .
Abrah ta jima bata ta shi ba sai da dadyn ta yace kin bar baqo shi kad'e maza jeku gai'sa ki dawo inada magana sake to'Dady tace " gabanta na tsaneta faduwa
Da sallama ta shiga yana zaune yasha lallausan yadin shi mai tsadar gaske ya hullarshi mai Kyau ya Murza .
Gai'she shi tayi ya Amsa yana binta da kallon so da qauna ..
Sundan ta6a hira soyayya inda yace mata zai'tafi hajir'su naji ranshi zai kai ta wani waje sukai sallama ya fito ita kuma tai cikin gida ..tayi karo da Dadyn ta shikuma zai fito .
Da sauri saboda kiran gaggawa da akai mashi wajan kasuwancin shi
Bilal gabi Dadyn Abra na tafowa yasa shi tsayawa su gai'sa sun gai'sa Amutunce inda Dady yace mashi yanzu sauri yake Aman zaine meshi Bilal yace to yai godiya kowa ya kama gaban shi ..
k'arfe 4 dai dai. Sirina Ce taxi kwalliya Abinta sai baza Qamshi take ..
Tace mommy na tafi sai na dawo mommy tace to Sirina ki gai'she man da su hajiya tace to zasuji
Sirina tama mommyn ta k'arya A kan zataje gidan kakaninta Alhalikuma bacan zata ba Hospital zata wajan Dr shureem kamar yanda taima kanta Alqawari
Tafe take cikin motar'ta zuwa Barhim inda Hospital din yake haka dai taci gaba da driveng din ta duk kuwa da gabanta na faduwa .
Har ta iso cikin Hospital din tai parking din car din ta kai tsaye ta tambayi office din Dr shireema A ka nuna mata .
Bakin office din taja ta tsaya na yan mintina kad'an tana wasu'wasi zuwa can tayi shahada tayi nocking yes comeng shine taji zazzaqar muryar shi mai'kama da busar sarewa tace sai' tai Ajiyar zuciya sannan ta shiga da sallama dago kan'shi Yayi dan gani wanene kyakyawar yarinya ya gani ei Sirina kyakyawace
Asalinsu ba yan nan bane Buzayene na Agadas
Wurin zama yanuna mata ta zauna tare da gai'she shi UA Amsa mata yana mata kallon kamar ya ta6a ganinta
Shuru sukayi bawanda Yayi magana shi yana jiran yaji mike tafe da ita ita kuma tana tunani ta INA zata fara ..
Gyaran murya Yayi yace mike tafe dake baiwar Allah mike da munki .
Kallon shi tayi ido cikin ido
Sannan tace mashi Abinda ke damuna bakomai bane Illa ciwon so ciwon so ke damuna matsalata ta so ce ciwon so ne ke damuna ba komai ba shine nazo kabani maganin shi.
Tunda tafara magana ya zaro ido shima yana kallonta kamar yanda itama take kallon shi
Kuma Abida ya fahimta bikin gaskiyar ta take fada mashi dan yaga hakan Acikin idanun ta .
Sai yace da it'a kinada hankaliko INA kika ta6ajin haka Aini bani bada magani ciwon so sai dai Na rashin lafiya .
Shima ciwon son Ai rashin lfy ne babba
Ta ci gaba da cewa ba komai bane ciwon so na illa kai kai ka haddasa man shi kai ne Make so Ina sonka Ina sonka so sai nake mugun sonka Dr shireem .
Ba Abu qarami bane zai'sa macce tace tana son Na miji gaba da gaba
Saboda kunya ta diya macce da Aka Santa da it'a Aman ba haramun bane dan kaga Abinda kake so kace kana son shi
Annabi yace duk Wanda kakeso to kafada mashi kana son shi .
Babbar matsalar munan hausawa ba mu dauki Kalmar so da mahimmanci .
Alhali kalma Ce babba mai matuqar mahimmanci Agurin Wanda Aka fada mawa da Wanda ya fad'i
Larabawa da turawa suna mutunta wannan kalma suna darajjata domin ingancinta
Kalmar so kalma Ce mai Nauyin gaske mai matuqar mahimman ci
Dan Allah kaso ni kamar yanda nake sonka
Dan Allah ko sau daya ne kace kana so na ta qarashe fada da hawaye taf idanta
*tofa komai Dr zai'ce da Sirina shin zai Ce mata yana sonta kamar yanda ta buqata ko sau daya ne*
*Shin koya zata kasan Ce*
*To dai kubiyoni sannu A hankali dajin ya zata kaya*
*More comments more typing*
Ammyn khairat Ce golden girl 😄💔💃🏻🥰
*♠ABRAH♠*
*Na*
Ammyn khairat
*Golden girl*
*Dedicated to Teemarh cute*
(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/
TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.