Abrah Complete Hausa Novel
Reading file: Abrah_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 13 of 21
Page 29
*bisimillahir rahamanir rahim*
Cikin kaduwa suka nuna junansu da ya tsu tare da zaro idanu suka hada baki wajan cewa kece yace mata itama Abrah tace kai ne?"
Da man haka halinka yake ban'yi mamaki ba cikin qaraje da daga murya tare da 6acin rai tace mashi wallahi na tsaneka na tsaneka har sau ukku ta fashe da wani ma tsane cen kuka da gudu tai waje
Yana kiranta aman ina ta riga da tafita
Kanshi ya dafe tare da fadin innalillahi komai ya kwa6e man kwana hudu kenan nake fama da jinyar zuciya ta na rashinki da tunani ta wace hanya zanbi ki soni?" dan naga kinada dan yan kai
Yanzu gashi na ganki kuma na qara 6atawa yanzu yanayi misa zuciyata ta tunzurani ta kaini yin abinda ba shi bane zuciya bakiman adalci ba
Idanun shi sunyi jajir kuma ya yi dana sani aikata haka a gareta nayi nadama to miyasa tazonan miya kawo ta
Itama ai tayi kuskure inda bani bane Allah kade yasan abinda zai faru
A haka ya tashi yafita zuwa dayan d'akin toilet ya shiga ya sakarma kanshi ruwa
Bai jimaba ya fito ko tsane jikin shi bai tsaya yi ba kayan shi ya kesawa da sauri da sauri
Yayinda sumar kanshi ke jiqe sai ruwa ke zuba ta zubo mashi harkan wuyan shi wata kuma ta zubo ta rufe mashi gashin girar shi itama sai digar da ruwa take
Da sauri da sauri yake saukowa daga upster ran shi na matuqar 6ace da abinda yai ma masoyiyarta shi gashi za tai tai mashi kallon dan iska
gaskiya bai ji dadin abinda yai mata ba kuma haka Allah ya hukunta
Yan matan da sukazo domin shin tunda ya fara saukowa kowacce ta zuba mashi na mujiya😱 tana kallon kyakyawan gaye matashin saurayi da ya hada komai na rayuwa mai jini ajika wanda ko wacce macce ke fatan samun kamar shi
Ko gaban shi bai kallo saboda tsanani 6acin rai ba manura da kallon da yan matan ke mashi ba dan basu gaban shi wajan da ya yi parking din car din shi ya nufa da zuwa ya bude ya shiga ya bata wuta da wani mahaukacin gudu ya fita yan matan dake kusa da motar ya badesu da qura
Yanda ya fita da car din kai kasan dreving ne yake ba na hankali ba
Sai da yafita sannan yan matan suka dawo haya cinsu
Inda kowacce ke hararan yar uwar ta dayi mata kallon saura kwata
Kowa da abinda ke ranta na nizan same shi gayan nawane
Niko Ammyn kyrt tace hummmm
Zamani kenan yan mata ke budar maza Allah ka shirya Ameen
Wanda kuke dan shi bai masan kunayi ba
Abra koda ta futo idanuta cike da hawaye na bakin cikin Abinda yai mata Ashe dan iskane wannan dan iskanan shine Abin so da yan mata kema dandazon zuwa wajan shi dan ya sosu halan basusan halinshiba
Ko dayake ai duk sune inba iskanci ba tayama zakaje wajan na miji kace kana san shi
Mashin dinta ta hau tai gaba yau tayi danasani fitowa motsa jiki kuma yau itace rana ta qarshe bazata qara zuwa gidan motsa jikiba ta na haqura zan sa Dad ya siyaman komai na runqayi a cikin gida
Dan yau zuwanta ya haifar mata da baqin cikin da bazata ta6an tawaba na tsane shi take ambata daqarfi yau ni Abra wani qato ya kamaman nonuwa yana ta murza san ranshi kamar ya biya sadaki
Yaman mugunta Ta sake fashewa da kuka dajin tsanar shi acikin zuciyarta
Da kuma tunani miya kawoshi wajan to kodai shikeda wajan inba shikeda wajanba taya akai ya shiga wurin in bata mantaba taji yan mata na fadin mai wurinne yazo daman shike da wajan daman dad'in kowa na shine gaskiya na shine taba kanta amsa
Inbata mantaba Asaman symbl din An rubuta da manyan bak'i kamar haka
*S M N* ma ana *s* tana nufin shureem *M* tana nufin muhammad *N* tana nufi Naira
Wato shureem muhammad mai Naira sannan daqa ganshi aka rubuta dad'in kowa ba shakka wa jan shine
Hummm zai gane ni Abra ya ta6ama mutunci da wannan baqin cikin tai gida kai tsaye d'akinta ta nufa toilet ta fada ta cire kayanta dan watsa ruwa gaban ma dubin toilet din ta nufa bayan ta fidda rigarta saboda radadin da nonanta keyi da ta duba ga ma dubi junyi jaji jini du ya kwanta sun sha matsa bata wasaba Allah ya isa tace mugu ban ya femaka ba wannan da gani harijine matarka ta shiga ukku irin kune masu kwana dare kuna aiki mata ta tashi da safe tafiya ta gagareta saboda jarabarku
A haka dai tayi wankan ta
Da mugun gudu yayi gida ko da ya isa gida wani mahaukacin hon yai ta banka ma maigadi gidansu sai da ya rude yana kwance kan dan benci yanajin dan redion shi har barci ya dan dauke shi cikin barcin yaji hon kamar cikin kunnan shi dan haka ya zabura harda fadowa daga kan benci ya tashi da sauri hulla riqe a hannu ya wangale get da gudu ya shigo ba dan da Allah yasa mai gadi ya yi tsalle ya koma gefe guda ba da ya yi gaba da shi
ya rufe get ko kafin ya juyo shi har ya fita shiga yayi ranshi bace idanu jajir gimbiya ko kuma nace maku sweetheart kamar yanda yake cemata tana zaune kan kafet ta dan shigingida
haka ya shigo wajanta ya nufa ya kwanta ya shige mata cikin jiki sai kace wani jariri sannan yasa hannu ya rungumota sai ya fashe da kuka ita daman ko dataga yamata haka tasan da walaki domin
indai har ranshi 6ace yake to haka yake mata hakan ke nuna mata yana cikin damuwa ma tsaneciya dan haka bata ce mashi komai ba ta qyale shi ya cigaba da kukan shi kamar yaro qarami ita kuma tana shafamashi kanshi tanajin kukanshi nashigarta
hummm da da mahaifikenan
tanaji damuwarshi har cikin ranta sai da ya yi mai isarshi sannan ya tashi zaune ya tan qwashe qafafun shi ya dubeta yace sweetheart
ina son ta ina matuqar sonta itace rayuwata zan iya mutuwa dominta inba ita bani zan iya haukacewa dominta ina mugun sonta sweetheart Ashe haka so yake miyasa so bai zoman ta sauqi ba
hawaye na zubo mashi da sauri da sauri ita kanta sweetheart hawayen ne ke zubo mata wacce mai sa,a ce tasace zuciyar son dinta jawoshi tayi ta rungume shi cinkin sigar lallashi tace haba son kar kabada maza man sai kace ba na miji ba kan macce kake kuka wacece ita ai ka sameta kagama sai yace sweetheart ba zaki gane bane ai nahi ita yarinyar ta tsanene bata so na nitawa qaddara haka ta zomani na dade bayi so ba ban so kowa ba ina tunanai soyayya 6ata lokacine ba yarinyar da zan iya so Ashe ba haka bane akwaita na samu aman ta tsaneni da bakin ta ta fadaman cewa tasaneni sweetheat yazanyi inna rasa ta narasa komai nawa Abban shi da tunda ya shigo shima ya fito daga d'akin shi ya yi tsaye yana jinsu yace Haba son ta sho ai wanna abin murnanae yasamu ranar da naketa jita yau gashi tazo
itadin wacece wanene mahaifin ta bar 6arnar hawaye ka dan indai ina raye to har kasame ta
ita wacece da zatace bata son ka mikarasa kanada komai ilimi isam da na boko uwa uba dukiya duk inda na miji yake ka kao tayaya zatace bata son ka
hummmmmmmmm Abban kenan ka manta bakomai ake nema asamu ba
kai na gaji wallahi
*♠ABRAH♠*
*NA*
*AMMYN KHAIRAT*
GoLDEN GIRL
*DEDICATED TO TEEMARH CUTE*
(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/
TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.