Complete Hausa Novels

Abrah Complete Hausa Novel

Reading file: Abrah_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 12 of 21

PAGE 28

*Bismillahi rahmanir rahim*

Mun tsaya inda ta yanke shawara; ba kawarta Number din Dr.

Yau ta kama Asabar mom ta gama komai na kari kowa ya halarta falo amman banda Abra"

Abra a d'akin ta sai shiri take"

Kayane tasa riga da wando wando da kad'an ya wuce gwuwa" da riga da wandon Duk iri daya ne penk colour"

Wuyan ta sanye da qaramar sarqa mai barima"

Sai qafar ta sanye da ta kalme masu kalar na yan kwallo suma penk colour"

Duk wannan shiri tana yin shi ne dan zuwa gidan motsa jiki;

Wani zuqeqen hijab ta sanyi tsayin shi har qasa"

Hijab d'in mai dogon hannu ne shima kalar kayan ta"

Turare ta fesa bayan tasa hijab d'in

Kasa ta sauko da sauri zuwa parlour su Mom na zaune harda dad saboda asabar ce ba karatu ba aiki"

Durgusawa ta yi gaban su Mom ina kwana dad ina kwana"

Lafia lau suka ce" tunda ta sauko suke kallon ta mom tace sai ina kuma Tun dazun muna jiranki akarya Aman kin fito da shirin fita"

Mom kin manta yau Asabar wallahi gidan motsa jiki zani

Mom tace" hummm wato daga ta shinki Abrah Wallahi mom jiki duk ya yi tsame;

Sauri nake inje ko indawo ko dad Eh to sai kin dawo aman da kin karya

Ah ah dad sai na dawo to
Hanif a dawo lafia ameen bro

Key din mashin dinta ta dauka ta fita mom ta yi Ajiyar zuciya wallahi dad duk ka bata yarinya nan

Ban son zuwa motsa jikinnan amman bayan da na iya

dad to my kiyi haquri an riga an saba mata yanzu kuma hanata wani 6acen rai ne;

to Allah shi kyauta Ameen sukafi gaba da karin su

itako Abra da ta fita harda sa hullar kwano tasa A kanta

Tafiya take A hankali dan zuwa da d'in kowa"

Kuma da nisa da gidan su zuwa can

kar kumanta lokacin sanyi ne dan haka Anayi shi sosai irin mai buji dinnan

Kan titi take amman buji ya hana ko ga banta bata gani sosai

Sai tsoki take da tasan garin haka yake da bata fito bah ta haqura"

Dolle tasa take kanna fitilar mashin dinta wadda bata san ta samu matsala ba

Dan ba abin haske sosai yanda ya kama ta

Cikin mota yake shikade shike tuqin

Cikin uzuri yake da kaga yanda yake tuqin kasan cikin sauri yake

Tun daka naisa ya hango ta kan mashin sai yawo take da mashin kan titi sakamakon hazon dake ga fitilar tata ba haske

Shikan shi yana da nasani fitowa yau

gab da ita ya kawo yanata yi mata hon wanda ya rudar da ita

Saboda bata san da mota ga banta ba"

Wajan qoqarin kau cewa ta kawo mashi karo ji kake garam

Sunyi karo ta fadi qasa shikuma mai motar na ciki ko fito wa bai yi ba"

ta tashi ta kakka6e jikinta bataji ciwo bah saukin ta da hullar kwano akan ta

tsaye tayi tana jiran taga ko ya fito suba junan su haquri sai taga yaja motar shi ya yi rubas baya ya yi gaba ya barta sake da baki🤔

Cikin ranta sai Allah ya isa take mashi da yafito da yagane shayi ruwa ne

Itama mashin dinta taja tai gaba zuwa inda zata"

Dad'in kowa yau cike yake da dumbun jama, a yan mata da samari sunci ado na kece raini

sai yauqi suke kai da kaga mafi ya wansu kason ba motsa jiki ya kawo suba

Duk da daman wajene na sha qatawa ba Abinda babu

Bayan ta yi parking din mashin dinta sai taje ta sai risit inda aka bata katin tai gaba ita Abinda ke bata mamaki yan mata sai wani yauqi suke sai taji wasu na cewa wallahi mai kamfanine ya dawo

Ya kusan satima biyu da dawo wa kai kawata kin san gayan ya hadu kibari kawai ni dan shi nazo

Ke kibari duk wadda ta same shi ai ta more ance yazo yana ciki bene na sama

Aini inanan har sai sadda ya ta shi

Ita dai Abra gaba ta yi tana mamakin yanda matan yanzu ke zubawar kan su aji "

Wajan da aka tanada dan motsa jiki ta nufa yau ma ba kowa saboda mata basu cika motsa jiki ba nice dai nafi kowa nacewa

Da taje ta cire hijab dinta ta cigaba da Abinda ya kai ta

Sai zufar take bayan ta gama taje wajanda aka tanada dan hutawa

Bayan ta huta ta goge gumi sai ta ta shi Tunda take zowa wajan bene sama rufe yake sa6anin yau da ta ganshi bude "

Dan haka zuciyar ta tarinqa raya mata taje taga ya wajan yake

Da gana a kwai qofar da zata kai ka bene sama da man hanya biyu ce dan haka dayar qofar tabi

ba tare da wani ya ganka ba ta fiya take tana yaba tsarin wajan

Tun daga matattaqalar bene zakasan komai yaji koda ta isa qofa da yace kuma ya bude take dan haka shiga kawai ta yi ba tare da tsoron komai ba
tunani wanda zata shiga dan gani kwam

qofar gabas ta shiga Abubuwan dake ciki sun girgiza ta; dan kaya ne na motsa jiki kala kala masu matuqar tsada da kyau;

Sai tabe tabe take cikin farin ciki jitake dama ace nata ne ai da ta more irin su take so dad dinta ya sai mata ko aure ta yi ta tai da Abinta"

Sai da tagama ta6a komai sannan ta zauna kan dan qarimin bed dake d'akin gefen shi kuma wani dan qaramin firjin ne ta bude marfin firjin din lemukane kala kala masu dadi da tsada dan haka ba tsoro ko shakka kamar tana dakin ta ta dauki wanda take so ta fasa tasha harda lumshe ido dan ya mata dadi"

Da lemun ruqe ahannu ta futo zuwa dan dakin sai nushadinta take ita kade

Shima dai kayan motsa jikine cikin shi amman kala ya sha Bannan da na dayan d'akin su na musamman ne dan sai nace ban ta6a gani irin su ba"

Suma ta qare idon ta dan basu haqqinsu tunda ta shigo yaji motsi da kuma mamaki mi ya kawo macce d'akin shi dan ba shakka maccace dan yaji qamshin turaran mata;

Abin ya daure mashi kai wacce yar kasada ce da har take iya hawa har sama bene shi har.ma ta shigo dakin shi;

Dan haka sai ya dakata da Abinda yake wato motsa jiki

Ita ko Abra bata masan da shiba harakar gabanta take"

Inta juya nan ta juyanan dan su ba ta6a su take ba dan nata ta6a ganin irinsu ba"sai dai ta kalla"

Da baya da baya take tafiya ya yinda shikuma yake tsaye koda ta kusan Kawawa wajan shi sai yai tsaya tana duba Wani Abin da ya dauke mata hankali Shikuma yana tsaye yana kallon bayan ta sanyi take da zuqeqen hijab harqa to wacece wannan yake Tambayar kanshi"

A hankali A hankali yake takawa zuwa wajanta saboda ba TAKALMI qafar shi itama bataji qara yafiyar shi ba shiko tunani yake irin hukuncin da yaka mata yai mata na ganganci shigowa wajan shi"

Zuciyar shi na raya mashi yai mata abinda bai Ta6a yi ma wata shi ba wanda zai zama izina gareta da kuma sauran yan matan zamani masu hali irin nata"

Dan shi yana mamaki yan mata zamani da suka Ari Al, Adun Nasaru suka dauke su Abin koyi agaresu da sunan wayewa "

Shi baiga abin wayewa ga rashin kunya ba saboda wannan rashin kunya ne tsan tsa ga ya yan hausawa da akasani da kunya da kawai ci aman yanzu duk sun watsar saboda hauka "

Da gudun shidan da kuma duniya da suka sa gaba da yahudanci

da wannan tunani ya Isa gareta tare da kwarin guwar yi mata rashin mutunci "

Da isar shi wajan ta bai yi wata wata bah yasa hannuwan shi duka biyu saitin nonuwana ta ya rungumota ga badaya zuwa jikin shi ita dai batasan hawaba balle sauka taji anmata haka aiko qara tasaki tare da fadin innalillahi Auzubillahi

Tana kiciniyarw kwatar kanta shiko Duk datana cikin hijab bai hana shi murza na shanunta yanda yakamata"

Kuma da biyu yake mata matasar su yake yanda zataji zafi cikin ranshi kuma fadi yake kaji munafuka wai harda wani korar shaidan akwai babbar shaidaniya irinki;

Sai kuka take tana qoqarin kwacewa amman yamata ruqo bana wasaba kuma duk Abinnan da yake mata idanun shi a rufe suke dan bai ta6a yi ba sai yau ;

Kuma ya rufe idanun shine dan bai san ganinta kokadan gurin shi da yagama wulaqantata ta yi gaba batare da ya ganta ba "

Itama Abra danta rufe suke cike da hawaye da tarin nadama da da nasani wadda hausawa kecewa qeyace fadi take yau wacce irin qaddara ce kebinta ya Allah katsareni ka fitar dani Adu, a take tayi a cikin ranta

Juyowa ya yi da ita gaban shi ya yin da dukansu idanun su rufe itako sai kai mashi yakusa take da cizo ta ko ina;
Ahakan ya lalubi bakin ta ya kama yai ta tsutsa ta mugunta dan da zafi zafi yake mata sai dai ya yi mamakin jin taushi irin na lipe dinta ga kuma qamshi wanda ya kai gasawa muguntar ta sauya salo dan ba kadan bakin nata yai mashi dadi ba ga laushi ga daddadan qamshi ko da yake bai yi mamaki ba gogaggun yan mata Ai ba sun tsaya hakan ba"

dolle su gyara kansu Abrah taji salon ya canza daga mugunta ya zuwa wata duniya da ban da kuma na shanunta da ya sassauta murza suma yakoma yin Mai dadi jitake zirzirzir cikin jikin ta kamar ana mata ya fiyar tsusa dan haka itama ta daina yaginshi da cizon shi Duk da tasan tagama jimashi ciwo da zaratan A kaihunta sakamakon jikin shi ba riga

duka su kamar ance subude idanun su suga junansu ido cikin ido sukayi da juna take duka su suka sake juna tare da zaro idanu suna nuna junansu da yatsa

to jama, a ko wanene Abrah gani to sai naji daga gareku FNS

wallahi rashin gani comments dinku yanda ya kamata Shike sa ban typing da wuri dan ganinake wahalar banza ce nake nai maku ba

inason unga ruwan comments dan Allah
*♠ABRAH♠*

*Na*

*AMMYN KHAIRAT*
(GOLDEN GIRL)

*Dedicated to Teemarh cute*

(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.