Complete Hausa Novels

Abrah Complete Hausa Novel

Reading file: Abrah_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 4 of 21

*PAGE NA RUDANII GASKIYA YYI DADI SOSAI ALLAH YA KARA BASIRA*

*ALLAH YASA KIZAMA ZAKARAN GWAJIN DAFI ACIKIN DUNIYAR MARUBUTA. NA GODE MALAMA TA* ~I LOVE YO U~

Bisimillahi rahamani rahim

Ambasada ya dubi matarsa sarauniya karima yace kina dai ji da kunnuwanki abinda yarinyannan tace

Da badan da yaron nan yariga da ya furta cewa yana sonta ba da ba musan halin da zata shiga ba

Haka Allah ke ikon shi ita soyayya baka san sadda take shiga ba to ke meki kagani akan wannan al amarin

Ke uwace kuma kinada hakki akan yar ki sarauniya kharima ta nisa tace banida ta cewa sai dai nace Allah ya zaba mata mafi Alkairi

Shi al,amarin Aure mutum baya jayayya akai did da nima da inada wani buri akan gimbiya na Aura mata dan kawata

Dan harmiye magana akai wato dan wajan waziri aman yanzu na janye maganar cinda yariya tasa mu wanda take so kuma niba zan mata doli ba

fatana dai shima yaso ta kamar yanda take haukan son shi Allah ya tabbatar da Alkairi

ameen Ambasada ma'aruf yace shikenan shi lamarin aure ba kai ma Allah shishige wannan abu sai muce haka Allah ya rubuta da macan shine mijin nata

Yace bari nakira wani Abokina dake najeria ya qara yiman bincike akan shi muhammad din

cinda ba boyayye bane kowa yasan shi ya fido wayar shi yai kira bayan sun gaisa ya ke cema Abokin nashi ko kasan muhammad mai naira

Yace kware kuwa niko na shi Abokin kasuwanci nane yanzu haka ma baya qasar nan ina jinma kamar yanan kanada

Injin dai lafiya Ambasada yace lafiya lau lallai yanan qasar kuma dalilin kiranka shi ne yaga yata yana so to hardai munyanke hukunci

Bashi ita to kasan rayuwa shine nace bari na kira ka muji koya halayan shi suke

sai yace a a indai muhammada ne bai da wata matsala mutumen kirki ne yanda halin kirki so sai kuma ina murna da jin wannan Abu
Ubangiji Allah yasa Alkairi ya kuma sa ayi damu

Ambasada yace ameen na gode su kai salama yace ma sarauniya kinji
Tace Allah ya shige mana gaba ameen

Muhammada suna tafiya suna harar Ambasada MA'ARUF gaskiya ba suyi tunani samun shi da saukin kai haka ba

Khalifa yace ai baida wata matsala daman yana da kirki so sai naji ana yaban shi akan halin shi na kwarai

Da wannan hira sukayi gidan khalifa Bayan sunci abinci sai muhammad yai masu salama ya tafi gidan shi

Ya kira gimbiya ta shi ya shaida mata ya isa gida kuma yai mata godiya abisa karmcin da tai masu

Tace ba komai itama ta gode da amsa kiran da tai mashi na yazo ya gai sa da mahaifinta yace bakomai ai shima mahaifin shi ne

Da yake dare ne kuma yanayi da dan sanyi sanyi jin su suke cikin an nashuwa

suna waya kowa naqara rumgume fulo bawasu kalame na soyayya suke ba aman suna jindadin kasan cewa ahaka

suna cikin wayane sai yaji kira na shigowa dake ba quwan nomber ce sai bai san mai kiran ba yace mata minti biyu zan kira ki tare da daukar kiran da ake mashi

Koda ya dauka sai yaji murya Ambasada ce cikin girma mawa kama yana ga banshi suka gai sa inda

Ambasada yace Akan dai magana da mukai da kai yanzu na baka dama ku fahimci juna kai da ita dan ban so Abinnan ya dau lokaci

muhammad yace to yaqara yima shi godiya saboda murna bai san ya jawo fulo ya mashi kiss bah

sake kiranta yayi harkinyi barci ina zanyi bacce kace zaka sake kirana inanan ina jiran kiran naka

to na gode dame tace mashi da matsayin da aka ban tace bakomai muhammad yace a kwai magana da zamu yanzu kibani hankalinki kuma kifa daman gaskiya

To ina jika kuma insha Allahu zan fada maka gaskiya yace masha Allah

zeeenat ya kira sunnanta yace daga haduwarmu zuwa yau nasan kin fahimci wanni abu tsakanina dake

In mabaki fahimta ba bara na fahimtad dake ni dai kin gani ba yaro bane da zan tsaya muna musayan kalame ni dake

magan ta gaskiya shi ne ina sonki kuma auranki nake sonyi shin yakaka gani na maki kin amice ban son ki kwari kan ki ina maki shikenan

sai natura maga bata na anai mamani aurenki to yaki kace murna wajan gimbiya kama ta taka kan jariri

yace ina jinki kinyi shuru kiyi tunani akai dan karki kwari kanki tace to Allah ya tabbata da Alkairi tare da kashe wayatta

ameen yace ya duba waya yana dariya wato kashe waya tayi wannan yanuna ta amince kuma kunya yasa ta kashe waya ta qara birge ni ba kadan ba

Agurguje soyayya mai qarfi ta shiga tsa kanun su suna Son junan su sosai

Yau ma yana jidan su gimbiya Awani waje da aka keybe dan shaqatawa suna zaune kan fararen kujeru

gefe guda kuma ga tsusaye sai shawagi suke sai yace mata gobe nake son koma wa gida saboda phappha yace naje na turo da magabatana dan haka gobe zan tafi insha Allahu

tace to Allah ya kai mu aman in katafi sai yau she yace ba jimawa zanyi bah kinsan duka nan gaba wai wuce wata daya bikin namu haka mukayi da

phappha shiyasa zan tai na shiryo kuma inna dawo sai bayan biki zan koma tace to Allah ya kai mu yace ameen ya naga dukkin bata fuska tace ba komai jimami ne

nake tun yanzu na rabuwa da kai yace ba komai zamu rinqa waya kafin na dawo

tun Asuba ya shiya saboda jigin qarfe 7:26 zaibi ya gama komai ya kira gimbiya ta shi sai Addu,a take mashi

Allah ya sauke shi lafiya kuma ya gai she mata da madam din shi yace ameen

ya jidadin Addu,a da tai mashi sosai saboda Abinda hjy laurat bata taba yima shi ba wato Addu,a

shi yasa yake qara gode ma Allah da yahada shi da zeenat fatan shi shi ne Allah ya nuna mashi ranar auran su nace ameen

sai da yaje airport sannan ya kira laurat yace mata gashinan zai ta so shine sai yanzu zaka ceman zaka taso to sai katafo ka dai sawoman saqona

shi ne abinda take cewa yace na sawo maki nina isa na manta da saqonki ranke dade to ai shine sai katafo

ta kashe wayar ta gaskiya ne akwai banbanci mata suna suka tara a kwai mata a kwai muna mata Allah ya shirya mashi laurat ita ko me take daukar kanta oho

Back to NAJERIA sai da ya isa airport sannan ya sake kiranta yace mata ya sauka shi yasan daman laurat baza tazo ta tsaya jiran shi har jirgin su ya sauka ba bai kai wannan matsayi ba

kuma inya kira a zo a dauke shi wani ta shin hankalin ne ya kusan minti 20 da zuwa sannan sai gata tazo anci kwaliya

ga kitson atace ansha ba laifi tayi kyau da macan da kyanta qazantace ta kasheta sai wani farr da ido ake mashi

ba sanu da zuwa ba komai sai yanzu kuka sauka kaji raini wayyo muje ko yace tama gaskiya kinyi kyau sosai

naji shi ne abinda tace sun isa gida qofa gidan shi tamtsan yake da muta ne kamar kullum dama haka suke taruwa ko yanan ko bai nan da masu dafa masu abinci

ana basu aqalla kulum sai an kusan dafe bun shikafa did wulaqancin da hajiya laurat kemasu bai da mesu ba saboda ba dan ita suke zau ne ba

da murna su su kai da fifi gaban mota suna jiran fito warshi cike da farin ciki yafito da murna da gani talakkawan na shi suma cikin farin ciki suke da ganin shi

sai sannu da zuwa suke mashi shiko sai basu hannuwa yake suna gai sawa kowa kagani farin ciki

afuska shi dan yau kakar su ta yanke saqa sunnan yau aljihunsu sai ya cika da nairori

Bakuna su dauke da Adduar fatan Alkair aga reshi laurat ta kasa ta tsare dan ita ma bata shiga cikin gidan ba

sai hararan su tak su kau ko kallo bata ishe su ba dan sun saba da halinta daga cikin su Akwai musa Addua Allah ya ba muhammad macce

tagari wadda tasan mutumcin dan Adam su isa cikin gida anta nadar mashi abincicika kala kala wadan da aka barbade da garin magani

da aka anso wajan bokaye dan ita ba boka daya take biba bokaye gefe guda kuma ga maluma Allah ka shiya ta da masu hali irin nata ameen

ruwa ya fara watsa wa sannan ya shiya ya fito zuwa falon dan falon shi kade ne yasa mu Albarkacin gyara aman bed room da tolet su basu same wanna gyran ba sai wari da qarni suke da kyar ya samu yayi wanka cikin tolet din kamar zaiyi amai

ta zuba mashi Abinci kafin yaci sai da ya fara da bisimilla ita ko Abinda ta tsana kenan

dan gani take bisimilla da yake take karemata asiri ko tayi bai ta siri wani lokaci har dauke mashi hankali take idan zaici Abici dan karda yayi aman ina sai yayi ta saboda ya riga da yasaba ko ruwa zai sha sai yayi bisimilla

Abin nabata haushi kuma yana bata mata rai dan bata da damar da zatace karyayi

nace hummm ina ko kike da wannan damar

*gaskiya ne bisimilla na magani sihiri musamman sihirin da akai ma mutum ta Abinci da zarar kayi bisimilla to ka karye du wani lago na sihiri ba zai maka ta siri ba da yarda Allahu subahanahu wata Alah dan haka mukiyaye wajan yin bisimilla yayin cin Abinci bama Abinci kade ba kome mutum zaiyi yayi bisimilla kuma mukoyar da yaran mu yinta Allah kasa mu dace ameen*

tun yana cin Abinci take ta shafar shi saboda bukace take da shi cikin ran shi cewa yake ba abida kika iya fa sai fa ai fa tausarki

bayan ya kammala yai godiya ga Allah ita ko zuwa wannan lokaci idanu sun rufe mata sun mata jajir

yau dai ko room bata bari sun shiga ba a parlour aka baje hajar sai ihu take mashi wanda shi kuma yake qara jin hau shinta saboda shi dai bai taba jin testen din ta ba da ya gaji

ya tureta ya ta shi badan ta qoshi ba dan ba taqi ya kwana yana aiki ba na ce ko harijace 🤔

dakin shi ya nufa kai tsaye tolet ya fada ya gyara shi ya wanke Abinshi cikin zuciyar shi yana Addua,r Allah yasa gimbiy macce mai tsabta ce
dan shi ya tsani qazanta

sai da ya gama sannan yayi kwanka tare da alwala ya fito sai ya gyara dakin shi ya kuna A c tare da air freshener

daki ya dau qamshi yasa kayan shi ya fita dan zuwa masallaci

Agurguje gobe ne zai koma kanada yan zukuma sun raba kaya da hajiya laurat ya fada mata zaiyi aure kuma yar kanda ce zai aura diyar Ambasada kuma jikanya ga sarkin mesira

ta tada hankalin ta so sai sai bala i take ma shi tun ranar da ya fada mata basu sake zaman lafiya ba bala,i yau da ba na gobe da ban kuma ta fada mashi did mata da ya aura itace ajalinta

kanada sun sau ka lafiya tare da manya Abokan Abban shi su ka tai domin su nai ma mashi auran gimbiya zeenat

kai tsaye gidan shi suka sauka bayan su futa suci sun sha sai ya kira gimbiya ya shaida mata sunzo lafiya karku manta ko da ya koma gida najeria

suna waya da ita kuma yau da zasu tafo sai da ya sheda mata sun taso kuma tare yake da baki

sun gama waya sai ya kira khalifa bayan su gai sa sai yace mashi ya zo gidan shi su tautau na akan magana auran shi kuma tare ya da uwayan shi

khalifa yace to ganinan zuwa bayan mintina kadan sai gashi ya iso

sun gai sa da baki su ka tau tau na akan auran ida khalifa ya kira Ambasada ya sana da shi cewa gobe sunanan tafe suda baki sai yace

Allah ya kai mu qara da zaku zo gobe daba ku iskoni ba dan zanje kasar mesira ga goben da yamma sai kuzo wajan qarfe 11

yace to su kai salama nan suka yanke shawar su tai su hado lefe

Ambasada yace ma sarauniya gobe fa muna da baki kinji kuma ina tunanin in sunzo mu tsaida magana guda

koya kika gani tace hakan shine dai dai yace haka za ai innaje mesira zanfada ma mai martaba halin da ake ciki tace to Allah shi kaimu yace ameen

bikin muhammad ko nace uwayan shi yau sunga duniya dan tun kan hanyar zuwa gidan su gimbiya

suke kallon daula basu ga komai ba sai da suka shigo cikin unguwarsu sai jinjina kai suke lallai ba qaramin gida bane muhammad ke Nai man aure ba dubada yanayin unguwa da kuma qOfar gidan da

suka tsaya cikin unguwama kade aka bar mutum ta ishe shi rayuwa muhammah ya kira gimbiya ya shida mata suna waje

tace to wani bawane yazo yai masu iso zuwa cikin gida yau gida tunda ga get na farko bati ne maza da mata

sai sannu da zuwa suke ma bakin na su tare da zubewa qasa suna kai gai suwa muhammad yace sarauta mai dadi yau suma sunci Albakaci

sai zubewa qasa ake ana gai shesu sai kace wasu sarakuna du acikin ranshi yake fada

babban parlour aka sauke su wanda yafi na ranar da su kazo komai na more rayuwa a kwai shi a cikin porlour babu Abinda ba a tana dar masu ba kan na ci da na sha sun zauna

akan manya lutsama luntsuma kujeru Ambasada ne ya shigo suka gai sa yace su ci abinci tukunan

mintuna 30 sai gasu sun sugo su ukku bayan sun gara gai sawa su su muhammad sun fita shi da khalifa zuwa dakin da akai masu iso inda gimbiya zeent ke ciki sun ba maga batan su da mar magana

bayan gai she gai she sai mahaifan muhammad wato Abokan baban shi suka gabatar da kansu a matsayin su na mahaifan muhammad kuma sun zone domin ne mama dan nasu auran yar su

nan dangi Ambasada da na Sarauniya suma suka gabatar da kansu wajansu kuma sukace sumbasu auran yar tasu suma sukace sun amsa suka yanka sadaki suka biya kuma suka shaida masu cewa tare suke da lefenta suma sunyi murna a garesu kuma tare da fatan Alkairi kuma sun sanya rana nan da sati biyu masu zuwa

sun amshi aure cikin mutumci da karamci tare kuma da halin dattako ta kowan ne bangare sai san barka da fatan kuma Allah ya kai mu ranar auran

suyi sallama da su suma suka fito su muhammad daman sun riga da sun gama gabayi ne naga suna ta sauran hugowa da a kwatina a kwati Ashirin da takwas

rana bata qarya sai dai uwar diya ta ji kunya yau ne Ake daurin Auran

*ALHAJI MUHAMMAD MAI NAIRA TARE DA AMARYA SHI GIMBIYA ZEENAT MA'ARUF KANADA DAURIN AURENE DAYASAMU HALARTA DUBUN DUBATAR MUTANE NA NAISA DA NA KUSA DAGA CIKIN SUKO HARDA MAI MARTA BA SARKI MUHAMMAD SHUREM*

an daura aure lafiya akan sadaki naira dubu dari biyu da dad dare aka kai Amarya gidanta tare da rakiyar yan uwa da Abokan arziki da ga cikin su harda mai martaba shima yace sai ya kai jikan yar shi dakin ta ankaita gidan ta dake nan kanada wanda muhammad yasiya

gida ne mai shegen kyau kowa ya yaba da kyau da tsarin gida did da banan zasu zauna ba acewar shi sai sunyi wata biyu sannan

su koma gida najeria kowa ya watse Ambar Amarya daga ita sai halinta Abokan Ango Snun rako Ango Bayan sunyi Adua ga ma aurata suma suka kama

ga bansu

Bayan sunyi komai na alada sunci sun sha Ango bai daga ma Amarya shi ba dama da ishurwa shi yake ya darji Sadakin shi da kyau da kyau kuma yanzu ne ya banbance tsakanin aya da tskuwa

sai
sa mata albarka yake daganan ya dau abishi ya kai tolet ya gyara ta sanna suka dawo suka kwanta domin suna dauke da gajiya koda yake shi ai ya huce gajiya shi ga Amarya shi sai dai ita kam bai war Allah baccen gayjiya yayi gaba da ita inda shikuma ya tsaya yana qare mata kallo yana ba idanun shi haqqinsu

da kuma godiya ga Allah daya bashi zeenat Ama tsayi

matar shi to Asuba tagari ma aura ta

*♠ABRAH♠* *PAGE 16*

*Na*

*AMMYN KHAIRAT*
(GOLDEN GIRL)

*Dedicate to Teemarh cute girl*

Wannan page.. Naki ne my shalele na gode kwarai da gaskey a madadinki ina meqa dubun gaisuwa da fatan alkairi zuwa ga masoyiya ta my Beelat Alkairin Allah ya kai maki daganan har qasarki....

*Bisimillahirahamanirahim*

Tunda asuba muhammad ya farka daga nanauyan baccen da ya dauke shi na jindadi ya kai duban shiga gimbiya ta shi yaga batanan yai zumul ya ta shi yana dube dube zuwacan yaji qara ruwa tolet

Allah sarki shi ne abinda ya fada harta ta shi cikin ranshi yana jinjina mata Abisa dauriya ta

Yana cikin tunanin ta sai ta futo daure da tawul ta kalle shi tai qasa da kanta tare da murmushi dauke a fuskar ta

Shiko mutuwa zaune yayi ganin yanda gashin kanta yayi ya jiqe sai ruwa ke diga

Abin burgewa ta nade a hannuta gaban mirorr ta nufa ta dauko Abin bisar da kai tana busar da shi

Sai kallon ta yake sai shatar kan take tana rufe idanu da gani tana jin zafin shatar

Sai sannu yake mata da dai yaga lokacin salla na qure mashi shima ya tashi ya nufi tolet yai wanka yazo su kai sallah tare

Agurguje muhammad da gimbiy zeenat suna zaman su lafiya cikin soyayya da Aminci da girmama junan su

Yayin da hajiya laurat kulum sai ta kira sho ba dare ba rana tana sauke ma shi kwandon rashin mutumci A cewata yaci amana ta

tunda yai aure haryanzu kusan wata guda bai dawo ba ai yazo zai isko ta koku ma in ta zonan baiji da dadi shi dai yace mata tayi haquri nan da wata guda sunana tafe

A kwana a tashi yau ne muhammad ya kai gimbiya zeenat gidan su domin tai ban kwana da mahaifan ta gobe ne zasu koma nijeria

Ya kai ta sun gaisa da sarauniya kharima kuma sun tarda Ambasada nana shi ne muhammad yasana da shi cewa sun zone suyi ba kwana gobe zasu ta shi zuwa qasar shi

Ambasada yace to har tafiya ta ta shi abu yayi muma da mu muka rugaku ta shi dan muma cikin satin nan zamu koma kasar mesira

domin zabe ya matso kuma mai martaba sarki shureem ya matsa mu koma dan nada sarauniya a qaragar mulki

muhammad yace to Allah ya nuna mana lokacin kuma Allah yasa alkairi suka Ameen daga nan muhammad da Ambasad su ka fita

A kabar gimbiya da mahaifiya ta sarauniya ta dubu gimbiya tai murmushi tace gobe sai ta fiya kenan tace mata Eh idanun ta suka kawo ruwa

Saraunya tace kuka kuma na me yanzufa kin riga da kin girma kinyi dakin kan ki kuma na sanki da daurya da jarumta

Gefe guda kuma kinda haquri to sune zaki qara a kai yanzu dai kinyi aure kuma zaki tai can wata qasa wanda ba dangin iya ba na baba

ba kida kowa sai Allah sai mijinki to ki zauna da kowa lafiya kima mijinki biyayya bakin gwargwado

Dan shi ne ya kai ki kiji kiqiji kigani kiqi gani ki zauna lafiya da Abokiya zamanki kinga dai munan mun maki nisa banso ki kai nisa dani ba naso koda yaushe kina kusa dani aman haka Allah ya hukun ta zanta yaki da adua Allah ya baki nasara Arayuwarki

Allah kuma ya tai makeki adu inda kike zanci gana da yimaki fatan alkairi sannan abu na gaba kuma shine kisan kanki

Kuma kinsa yanda zaki ta fiya da mujinki kina tsu ki karance shi ciki da bai miya ke so mike bai so yau she yake farin ciki yau she ya ke bakin cikin sanana a kowane hali yake kinsa yanda zaki mashi magana

abinka na da mahaifi nan ta cigaba dayi mata na siha akan yanayi zamanta kewar aure da rayuwa ta yau da kulum

gimbiy tana tsu tana dauka sai hawaye ke tai mata zuba ji take kama wasiya ce mahaifiya tata kema kamar sun rabu kenan har abada kuma sai yanzu ne take dana sani aure nai sa da tai

Niko nace da nasani qeyace baya take 🤣🤣 bake dadi soyayya ba😢 ai ga shinan zaki tai kiba kanada baki daya hajiay laurat nacan na jiran gashi☹

Sai magari ba muhammad yazo dauka ta bai dade da zuwa ba Ambasada ma,aruf shima ya shigo sun sake gaisawa
Inda shima ya gara yimata nasiha mai shiga jiki itako sai kuka take😭😭 wayyo

Kuma yace ma muhammad ga amana nan dai na qara ba ka kariqe man yata da gaskiya da amana in kuma kace amana ta to wannan kuma kai da Allah
Shima yai mashi nasiha na su zauna lafiya da aminci

Sarauniya taba ta wata laida cike da kaya yau da kanta ta rakota harwaje inda motar su ga baki daya bayin gidan yau suma suna waje dan ban kwana da uwar dakin su

Duk ma aikatan gidan yau suna waje sarauniya tai mata kyauta baiwa ta wata datijuwa mai kirki tun zamani mahifiya ta take ita ma lokacin auran ta da

Ambasada mahaifiya ta ta bata ita shi ne itama yau taba yar tata gaskiya gimbiya taji dadi da wannan kyau ta ta mahaifiya tata

koba komai zata dai be mata kewa mahaifiya ta saboda atine baiwa ce mai kirki dole ka zauna da ita sai ka qaru

kuma daman sun shuqu da gimbiya so sai shiya sa ita ma sarauniya tai tunanin bata ita Kuma gani farin ciki

akan yar tata yasa itama tai murna da kyar suka samu suka lallabata ta shiga mota tana kuka kamar zata mutu

sarauniya ta juya tai gida itama idanun ta cike da kwalla yau ce rana ta farko da taji tayi kewar rabuwa da diya ta sosai

to dama haka aure ya gada rabuwa ta zama cilas inba aure a kwai mutuwa kuma da man sabo shi akewa kuka

a haka su katafi tana kuka kowa yau zuciyar sho ba dadi musamman ma bayin gidan sun saba da ita sosai kuma tana shiga cikin su si ta hara wada da dariya

sau gashi yau gimbiy ta masu nisa wasun si harda kuka Ambasada ya shiga cikin gida jikin shi did ba dadi jin shi yake kamar marar lafiya

tausayin yar shi ya shiga zuciyar shi to ya zaiyi aure kenan mai raba diya da mahaifi sai dai ya bita da kyakyawar adua itace kade abinda zai ma gimbiya

ya shiga da muwa so sai dan sai nace yafi sarauniya da muwa couerse ya shaqu da ita so sai haka dai suka yini cikin jimamin rabuwa

acan cikin mota sai lallabe ta muhammad yake yana ta bata hakuri tare da kwan tar mata da hankali atine ma sai bata haquri suke aman ba tai shuru ba

har su ka isa gida tana kuka muhammad did ya shiga damuwa so sai zazzabe mai zafi ya rufeta saboda kukan da tasha

Asuba fari suka ta shi dan hada kayan sun sun hada kayan su atine tai masu abin kari suka karya suka dau kayan su suka zuba cikin mota mai gidan gidan yau shi zai kai su airport domin shi zai dawo da motar

jirgin qarfe 8:30 suka biye sun shiga jirgi inda gimbiy ta zauna bakin taga jirgin su ya daga tajuyo fuskar ta bakin taga tana qarema kanada

kallo yanzu ko tasan tabar kanada ita da kanada sai in tazo ziyara aman da zama dai ta barta kenan saboda mahaifan nata ma tashi za suyi zuwa wata qasa

take idanun ta suka kawo ruwa muhammad na nura da ita shi dai sai tausai take ba shi rabuwa da mahaifa da kuma qasar ka wadda kasa ba da ita ba dadi sai doli

sai ya kama hannu ta ya damqe cikin na shi yana murzawa sai tai shuru musamman ma da ta kalle shi ta ganshi shima yana cikin da muwa

Agurguje Back to *NIJERIA* *katsina state ta duko dakin kara kunya garemu ba dai tsoro ba katsinawa ba ta kenmu kenan🤣*

airport cike da masoya kuma Abokane shi Aminna shi su ya kira ya shaida masu zuwan shi dan suzo su dauke shi

dan yasan koya kira hajiya laurat yau bata zowa dau kar su dan haka bai ne maita ba yane mi mutan arziqi sai ga shi tukan jirgin su ya sauka sunma filin tamqam da jamaa

sunzo daukar su sai sannu suke mashi masu mata did sun zo da matan su sai nanan suke da gimbya itako sai kalle kalle take yau gata nijeria

wadda ko Amafalki ba tai tunani zowar taba sai ga ta yau ita ce acikin ta kuma ta zone da zama mutu karaba fatan ta da aduar ta shi ne

Allah ya sa tazo Asa,a dan shiya sama da zata fito daga jirgi da qafata ta dama ta fara saukowa da adua dauke a bikin ta tama da murna take ma matan Abokan yawwa

suko sai yaba kyan ta suke kowa sai nanan da ita yake sun shiga mota day shi da ita tawani baban Abokin shi ya zasu zuwa kata faren gidan shi dake

*goruba Raod* gidan ya sha gyra na ban mamaki inda kowa fat din shi da ban shima da na shi yayin da ko wacce ta cikin dakin ta a kwai qafar da zata sadaka da na shi dakin

sunyi fakin da motacinsu qofar gidan kamar kulum cike da jamaa sunyi dafifi sai sannu suke masu tun anan gimbiya ta san cewa mujin ta ba qaramin mutum ba ne mutumain mutanen
Matan Abokan shi sun jata zuwa cikin gida kai tsaye fat dinta suka nufa da ita

itako did inda zata sa qafar ta bakin ta dauke yake da adua masha Allah fat dinta ya hadu iya haduwa komai na jin dadi anzu ba mata shi

ba abinda ba bu a cikin shi wannan kuma did akin mahaifin tane dan shi ya kira Abokin shi ya turo da kudi yace a je dubai a hado mata komai

na marore rayuwa to shine komai yaji fadin su 6ata lokaci ne

hajiya laurat tun da taji haya jiya tayi yawa tasan ba shakka sun iso tace ma kawayen nata ga shegiyar nan ta iso kuma wallahi Abakon muhammada sai nayi magani su da su da matan su

shegu yan iska zan gyra maku zama Amina da hafsat sukace da kyau kawata haka muke so kibari sannu ahankali zaki gyara masu zama

aman yanzu karki ce komai ki dau shawar da muka baki tace hakan za aiye da yake magariba ta ga bato

kowa na harama salla suma can waje sun ga bata da ta su salla sai gaba dayan su su kayo cikin gidan dakin Amarya

Bayan gaishe gaishe suka gabatar mata da kansu Amtasyin su na Abokan muhammad kuma Abokan kasuwanci shi suka kuma gabata da mata yansu gare

su kai adua tare da bata kyaututuka musu yawan gaskey cikin mata khadeeja itace jini su yafi haduwa da gimbiya

matar usuman ita ma dai Amarya ce tawan su biyar da aure kuma bata wuce yarin gimbiya ba gata bata cika hayaniya ba kamar gimbiya

shi yasa tasu tafi zuwa daya sauran kuma gaskiya sun girme mata naisa ba kusa ba

kowa yaka ma gaban shi inda aka ba atine daki daya infa zata zauna shima harda tolet a ciki

laurat Abin duniya tun yanzu ya fara sha mata kai kawayan nata suma sun tafi sai ita kade sai zagaen falo taje ga muhammad har yanzu bai zo inda take ba lallai da sake ama mai dame daya sata

tana cikin haka sai ga shi ya shigo da sallama ko ta ansa salama ina kanta ya dau zafi

jewa janta yace uwar gida sarautar mata tare da rungume ta yace na dawo ko kije kiman sannu da zuwa aman shuru

baki da mu dani ba to ni dayake nada mu dake kuma ina son jin dumen mata ta kusa dani ai gashi na biyo ta

ke baki san nayi missing dinki ba kina jina kiyin shuru to kiyi hawuri laifi nai ko tare da juyo da fuskarta ga ban shi ya hada bakin shi da na ta yai ta tsutsa san ran shi

sai da yaga ta na shirin faduwa qasa ya qara ruwota da kyau ya zaunar da ita kan kushin yace mata ranke dade in anyi sallar isha,i kisameni falo zanyi magana daku

sannan ya juya ya fita ta bishi ida idanu ya ta doma ta da abinda ke balla mata na cikin zane😉

Bayan sallar isha,i ya gama abinda yake ya fito falo ya kira waya Abokin shi cewa ba zai samu da mar fita ba

yaje hotal ya hado mashi did abinda ya kamata laurat yau kishi ya hana ta hada masu komai
ya zauna yana ta zama jiran su ba wanda ya zo gimbiya ana can ana ta shiri zuwa part din miji in da ita kuma laurat ba abinda take tunani zuwa su hadu da Amarya ta ta take shin wacce iri ce ta fita koko dan koda kawayan ta zasu ganin Amarya hana su tayi

sai yanzu take jin haushin hana su da tayi da yanzu sun bata labari to mema zata fita ai macce take itama macce take

to me zata nuna mata sai dai kudi da mulki ta nisa did haka ta dai nuna man wani abun da tafini take taji ranta ya qara baci

dawanna tunani ta isa falo na shi bako sallama sai ware idanu take taga ina zata ga Amarya da tai shishigin auran mata miji

aman bata gan taba ta samu kujera kusa da ta shi ta zauna ta dora qafa daya kan daya tana ta karkada qafafu sai cika take tana ba tsewa hohoho uwar gida 🤣🤣🤣🤣🤣🤣

muhammad ya kalle shi dariya ma taso ta bashi yanda take cika tana bata fuska shi did yau baiji maganar taba

ba tafi mintina goma ba sai suka ji sautin ta fiya za a shigo hade da wata yar qara qamshi ko yai masu salama tun kan ta qara so

zuwa can su kaji shuru ba ai sallama ba ba kuma ashigo ba ga qamshi ya cika masu hanci kowa hankalin shi na ga ta inda za ashigo aman shuru

sai zuwa can sai suka ji sallama kamar daga sama cikin zazzaqar murya mai kama da busa sarewa

hajiya 🤣 laurat sai da gabanta yafadi sai dakan Ukku ukku yake ga badaya ta shugo qafata sai qara sauti sarqar qafa da tasa take

shiga ce ta ya,yan sarauta tayi ita ma zuwa tayi ta samu daya da ga cikin kushin ta kusa da shi ta zauna ta harde afafunta daya kan daya hannuta guda kuma saman kujera wato daga bayan kujera tasa hannu nata

zamane tayi na ainahin sarakai wanda ta ta so gidan su taga mahaifiyar ta nayi to yau irin zaman ne tayi

dukan su ba wanda yasamu da mar magana barema hajiya laurat da tun da tagan ta serves dinta ya dauke bari ma da taga ainahin yanda ake zaman sarauta na aza kafa daya kan daya bata san sadda ta dauke tata qafar ta aza qasa ba sai ta ga ita ba taiya

lalai wani abin sai dan gado wanda yai haye koyayi bai masa kyau lalai tana da aiki gaban ta wannan irin kyau sai kace aljana badan da muhammad na kusa ba in ita kade ce cewa za tai gamo tayi ko yanzu haka zaman datake yan cikin ta kadawa suke

muhammad yai gyran murya yace asalamu alaikum gimbiy ta ansa mashi sallama sanna ya fara da yi masu nasiha ta su zauna lafiya da junan su

kowa ya mutunta dan uwan shi yace ke laurat kiriqe girmanki a matsayinki na ta babba kija girmanki kema ki mutum tata dan ita ce babba gareki kowa ya tsaya a matsayin shi

inso ku had kanku ku zauna lafiya kowaccen ku ina sonta shiya sa na aure ta dan haka a zauna lafaiya abisa al,ada kwana biyu biyu ne ake dan haka da ga yau za a fara kwana biyu biyu tsakaninku inda mai magana injinta

gimbiya tai wani shumin murmushi tare da qara kashe mirya tace my niban da wata magana dokokin da aka aza zaka samen mai kiyayesu fata na dai shi ne Allah ya hada hankulamu ya kuma

bamu zama lafiya yace mata to na gode ke hajiya laurat kice komai ba gimbiya zeenat tayi na ta bayani saura ke

ai bani da ta cewa kariga da kagama bayani kuma kwana biyu aida man haka akeyi saboda haka waneje na za a fara sai ta ta shi ta qara gaba cind yau ba kwanan ta bane

a na cikin haka Abokin shi ya kira shi yace ga saqon shi nan wajan mai gadi zai kawo mashi shi ya wuce yace to ya gode sai ga mai gadi da sallama ya kawo saqon laida hudu ci cike da kayan hotal

yaba gimbiya laida biyu ya ajema su laida biyu gimbiy ta ansa tare da yima shi godiy tace sai da safe my sai hajiya lairat ban gane ka bata laida biyu ita kade mu ka barmana laida biyu rashin adalci harka fara daga yau

muhammad bawan Allah yace a, a ranke dade miya kawo nara Shin adalci suma can su biyu ne shi yasa su biyu ta fada da qarfi yace mata Eh hummm Shine abinda tace

ita dai gimbiya ko sauraran su ba taiba tai gaba da tunanin laurat a zuciyar ta yau ne rana ta farko da tafara ganinta aman tafara karanta halayan ta

to masu karatu koya zaman nasu zai kasan ce ku biyo ni kuji karku manta muna ci

kin jin wanene shureem

.........✍🏻✍🏻✍🏻

https://www.instagram.com/proficient_writers/

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.