Abu turaab Complete Hausa Novel
Reading file: Abu-turaab_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 17 of 18
32.....Alh.chanji cikin kwana ukku ,da yaga yana son rasa nainah ,ya samar masu visar fita waje dashi da nainah da kuma mami ,nainah ta zabi su zauna a kasar England na Dan wani lokaci .
Dan kawae ta manta da Rayuwar Abutturab duk da tasan zay yi wuya ta fiddasa aranta ,sageer kuma tun daga Ranar bata kara nemanasa ba ,zay kirata wya sau ashirin bata daga ba .kullum cikin turo mata text din ban hkuri yake.
Humy kuma ta koma garin su ,bayan sunyi kaca-kaca da Alh .chanji akan ya yaudareta yaki aurenta haka ya bata mata Rayuwarta,
Yajira Dan gaba kadan abunda zay biyo baya.Dan bazata taba kyalesa ba,
da yake Dan dunia ne ko dar"bai ji aransa ba illah yace su zuba sugani shege ka fasa,
Muddin taci gaba dabin Rayuwarsa zaysa a batar daita ,da duka ahalinta.
*
Few months letter.
Abutturab yasamu aiki awani babban company dake Lego's ta hnyar baban mamdud ,
Wanda a duk bayan sati biyu yake zuwa kano ,yana ganin noor da Aunty Wanda itama karatun ta ya Riga da ya miqa................yanzu tana ss 3 ta kara wayewa da gogewa haka ta kara zama cikakkar macce jikinta yyi wani irin bul"bul alamr ya fara samun Hutu.
Har yau har gobe, Abutturab bai taba fadawa Aunty sanadiyar barin aikinsa Aiki karkashin nainan chanji ba."
Watarana ne Alh.sule da yazo zance wajenta yake fada mata ,Wanda tasha mmki bbu laifi tana sakewa da Alh.Sule a yanzu.
2 years leaf......................
gama makarantar noor da auren Aunty duka ya faru acikin shekara biyu ,
Harda haihuwar Danta Na miji mai suna Yusuf Wanda suke kira Abba,
Ba karamin Ji dashi Abutturab keyi ba,
Muddin zay zo kano da tsarabar Abban sa Yusuf yake zuwa koda baiyiwa kowa tsaraba ba.
Noor ta koma Lego's Wanda ,Abutturab ya siya masu gida achan sai dae sukan ziyarci Aunty yawancin lokutta.
Itama noor har yanzu haihuwarta shuru wannan shekara sae da ya biya masu Hajji shida Aunty da kuma noor ,
Yyi rokon Allah yabasa haihuwa Wanda Rashin haihuwar ya fara damunsa ba kadan ba.
"Yana samu hop a wurin auntysa tana masa misali da kanta ,tana ne kawae take samun kwanciyar hnkalinsa.
" Ranar Jummu'a yazo kano wannan karon shikadai yake banda noor.
Wanda Aunty tasha mmki ,
Tana serving dinsa tana tambayarsa meyasa ya taho yabar noor .
"Aunty kibar noor kawae da Rigima university takeso ta wuche ,nikuma na fada mata bana da Ra'ayi ta fadi duk abunda takeso a Rayuwa muddin baifi karfina ba zanyi mata ,amma banda zancen shiga university.
Har mota nasa akawo mata a kwatano "Amma taki karba a kwanakkin nan cikin Rigima muke.
Ya langabar da kai yana fadin" Aunty bakiga na Rame ba Dan Allah?"ya qarasa mganar tamkar wani karamin yaro.
Hararar sa tayi ta zauna akan kujerar dinning tana dannawa noor kira awaya.
Tamkar jira akey aka daga wyr.
Cikin sanyi murya noor ke fadin "Aunty ina wuni" mun wuni lfy noor ,
Ya kk?"
Ina lfy Aunty."ina my boy?"
Boy yna lfy sai Rigima ,kae Aunty bayada wata Rigima."daria aunty tayi ,
Ta daura da fadin shine kika ki biyo yayanki ko noor?"tana Juyo dariarta A hnkali tana fadin"bana son tafia a mota Aunty daga Lego's zuwa kano akwae wahala ,shikuma Yaya yana son tafiar mota.
Haka kuma ina da matsalar ciwon baya shiyasa kawae.
Ae yace kwana biyu kawae zaiyi.
"Hira sosae sukayi da Auntyn nata Wanda ta debe mata bacin ran yayan nata,
duk yarda Aunty taso noor ta fada mata ko akwae abunda Aliyu ke yimata taki bata damar hkan .
shikam Aliyu Ko a wannan stage din yana alfahari da noor na kasancewarta mahadin Rayuwarsa,
duk yarda suke da Aunty bata taba gayamata matsalar Aurensu itada Abutturab......
💝ABUTTURAB💝
~By Written by Asmy b Aliyu~
Haske writer's Association.
33......
"Tare dukan su suka kalli doctor noor da Aliyu.
Dan murmushi Dr.khaleel ya saki yana wasa da pen din hnnunsa ,yake fadin ba wani abun tashin hnkali bane Mr.bamalli Spem dinka kawae muke bukata,
zamu sakasa ajikin matar ka .insha allahu wannan karon za'a dace.
Kwana biyu kawae nabaka kayi tunani ,bayan sun fito daga clinic din noor cikin mota kuka ta fasa masa ,
" kagani ni bana son haihuwar nan maybe ma mutuwa zanyi Dan Allah mu hkura."!kuka takeyi tsakaninta da Allah tana yarfe hnnunta,
Pkn yyi gefen titi ya jawota ajikinsa yana famar lallashinta ,
bbu abunda zai faru habibaty lafia zaki haihu ,ki daina daga hnkalin ki kinji"..wannan satin idan anyi aiki an samu nasara wani watan Kano zan kai kiyi Hutu a jirgin sama zamu tafi kinji ko babyna"...tana kwance ajikinsa amma ita kam tsoro takeji.
*
Nainah chanji tayi crossing legs dinta a katafaren offishin Dr.khalel bakori,Tana Juya car key din hnnunta,
Cikin taushin murya take fadin "Tun daga kan 1 million zuwa 10 zan iya baka in har ka yarda zaka saka sperm din Aliyu bamalli acikin mahaifata ,
Tsa tsonsa nake so yafito acikin jikina ,koda bai aureni ba zanyi alfahari da hkan.
*
Dr.khaleel yyiwa nainah umurni akan ta kwanta wani Dan qaramin bed Wanda marar lfy ke kwantawa yyinda likita ya bukaci hakan.
Cikin sauri yake komae sai hada gumi yakeyi ,
Ya saka glove's a hnnun sa,
Sa'annan ya shiga hada wasu irin abubuwa ,
Umurni yyiwa nainah chanji akan ta cire pant dinta bbu musu ta cire
Sae da aka sage kafafunta akan wani qarfe sa'annan ya ta fara aikinta cikin kwarewa .
nainah taji zafi sosae haka ta daure har aka gama.
Bed rest aka bata na awa ukku.
Koda Aliyu ya kawo noor a hospital barinta yyi ya tafi Dan suna da meeting ,
Haka noor ta shiga a tsorace ,
Allurar barci kurum Dr.Khaleel yyi mata .
Some hours latter.
Nainah tabiya Dr.Khaleel 5million ,sauran 5 million sae aiki yyi kyau.
Misalin qarfe biyr noor ta farka ,da wata irin mutuwar Jiki ganin Aliyu tayi zaune akanta ya zuba mata ido,
Shiya taimaka mata ta tashi zaune ,
Gaba daya batajin ddin Jikinta ,cikin kankanin lokaci ya kira Dr.Tamkar gaske ya shiga Auna noor yana fadawa Aliyu"anyi aiki cikin nasara zasu iya dawowa nan da wata Biyu.
godia sosae Aliyu yyi masa,
daukar noor yyi chak!zuwa mota,
Dr.khaleel yana mmkin wannan wane irinso ne Abutturab keyiwa matarsa...........
Wasa gaske har kusan wata ukku su Aliyu shuru suke Ji ,sun koma ga Dr.khaleel yafi sau biyr ya fadawa Aliyu sae idan matarsa che batada Rabon ta haihu har sa,insa sukayi a tsakaninsu a fusace Aliyu yabar hospital din.
*
England....
Wannan wane irin Amai ne kk yi haka nainah?"na shiga ukku ni zulfa'u yau mezan gani haka?"nan take ta kira daddy awaya Wanda baya kasar Yana kasar Japan, nan yyi umurnin akaita hospital zay shigo zuwa gobe bbu musu Hajia zulfa ta shirya Itada nainah Wanda tayi fayau ,tayi wata irin Rama ta zabge tafita hnkalinta lokaci daya bata cin komae sae bakin shayi ,
Koshi da ta gama take amayesa hnkalin mami yyi masifar tashi addu'a takeyi Aranta Allah yasa nainah ba abun Kunya ta yomasu ba.
Hawaye na zuba a idonta suka isa asibiti.......
💝ABUTTURAB💝
~Writeen by Asmy b Aliyu~
Haske writer's Association.
34.....
"Gwajin farko likita ya tabbatar masu nainah Nada cikin wata biyu harda sati biyu" lumshe ido nainah tayi tana murmushi a hnkali ,
Zubewa akan coach mami tayi tana zubar hawaye,
Afusace ta fisgo nainah tagawayen mari tabata har kwara biyu."shakota tayi tana fadin"don ubanki kafin ki kasheni ni zan kasheki nainah ,ko ajikin nainah .Wanda likitan yasha mamaki"cikin bacin rae take fadin cool down"mami bafa cikin shege bane ?"wannan da ubansa ,bata hnyar zina aka samesa ba!"mami ta kurawa nainah ido ,
Batace komae ba ta Juya tabar office din ,haka ta koma gida tana sharbar hawaye .bayan fitar Mami.cikin harshen turancin,baturen likita ke fadin"kina ganin yarda mahaifiyarki ke zubar hawaye akan kinyi cikin shege shine ko ajikinsa,
Wani irin irritating look nainah keyi masa ,Afusace ta Juya tabar masa office din duk da jirin dake dibarta bai hanata yiwa Dan taxi kwatance wurin da suka sauka ba.
Koda ta koma bata ga mami afalo ba,
Bata damuba dakinta ta wuche wani irin zazzabi ya rufeta lokaci daya .
Haka ta kwana tanayin sa.
qarfe goma na safe taji muryar dadynta na buga mata ko'fa cikin wani irin tashin hnkali tamkar zay karyata .
Jiri na dibarta tazo ta bude masa ko'far anan ta zube kasa a sume................"kusan awarta ukku batasan inda take ba ,
Bude idon da zatayi sukayi ido biyu da mami .
Wanda kallo daya tayi mata tasan tasha kuka ,
ganin ta tashi mami taje ta kira dr.sae gasu sun shigo tareda Daddy"ido ta zubawa daddynta Wanda bbu alamr fara'a akan fuskarsa ,nan take jikin nainah ya dau Rawa .
Dr.bama bukatar wani abu kawae ka bamu takardar sallama Jirgin karfe biyu zamu bi zuwa Nigeria.
*
Wannan magana ta arziki bai shiga tsakanin nainah da daddyn ta ba,sae saqon harara.
uncle saleem ne yazo ya daukesu a air port ,umurni daddy yyiwa saleem akan ya kaisu gidan Alh.sule dake maska Road ,
Dan yasamu lbrn Abutturab yana kano .ayita ta qare Dan hukuma che zata Rabasa dashi."
*
Noor na zaune a falo tana yiwa Little Yusuf wasa cike da sha'awa Abutturab na zaune akan Rug yana lunch ,Aunty kuma ta shiga wnka......sallamar maigadi sukaji abakin kofar shiga falo tsam Abutturab ya miqe ya nufi kofar ,
Nan baba maigadi ya tabbatar masa da Suna da baki ,
Jeka shigo dasu da sauri ya kalli noor Wanda tayi Rolling kanta da veil din bakar abaya ,
Tana cikin shigar Arabian gown da alamr dai fita zasuyi da turab take Jiransa,
"Jin baki yasa ta hade ranta ,
Nidai wlhi yau bazan yarda ba bbu Ruwana da wasu bakin Aunty na Riga da nafito kitchen ,gidan su bikra zani.
dai dai lokacin da Aunty ta fito tana murmushi take fadin" ae ko dole kishiga kitchen munada baki shaye da toka take fadin "Akwae snack's da drink's ae ya ishesu daria Sosae Aliyu keyi ,ya tsagaita dariar ne sakamakon ganin waya'ndda ke shigowa a falon haka lokaci daya yaji wani irin faduwar gaba..." Arikice ya miqe yana kallonsu ,
Aunty che ta tarbesu da fara'a tana fadin su zauna.
Alh.chanji banda mugun kallo bbu abunda yake aekawa Abutturab dashi ,
Kallon sa ya maida kan nainah yanayinta yake kallo tamkar ba itaba cikin idanunta yake kallo,
Wanda bbu wadatar barci acikinsu.
bata damu da mutanen dake kallonta ba da gudu tazo ta shige Jikin Abutturab lokaci daya ta saki kuka."
"Ya Rabbi.......Nainah"! Minene?"ya dago fuskarta gaba daya bayajin zuciyarsa dai -dai!"
Kowa daskarewa yyi afalon yana kallonsu idanun noor kar"akansu ,
Juyawa tayi zatabar wurin.
Aunty tayi saurin riqota.
"da wannan zaka saka mana Aliyu?" Bamu taba tunanin haka daga gareka ba!"ya tsinkayi muryar mami akansa,
Arikice ya saki nainah ya Juya kan mami yana mata kallon tuhuma?"
ban fahimceki ba mami wai meke faruwa?kun sani a rudani?"bakashiga Rudani bama tukuna sai na daureka ka zauna a gidan yari!"ya tsinakyi muryar Alh.Chanji akansa.
Kansa ya riqe yana jin maganganun su na samun wurin zama azuciyar sa duk da ba fahimtar hakan yakeyi ba.
"Cikin ka gareni wata biyu Aliyu"... Ya tsinkayi muryar nainah akansa!
Ido ya zuba mata kamar da wani yare take mgana ,baya ma fahimtar abunda take fada,
" nooooo!"yake fada yana toshe duka kunnuwansa biyu, Agigice ya isa ga Auntynsa Wanda ta gama sandarewa a wurin ,
"Aunty kice mafarki nakeyi Dan Allah." Yyi mganar jikinsa na mugun kadawa,
Aunty tana iya rantsewa tana Jin bugun zuciyar Abutturab."gumi fito masa yakeyi ta koina duk Acn.da ke aiki a falon tamkar Yana cikin Rana ,
Aunty ta damqe hnnunsa tana fadin"ka natsu plss Aliyu bbu abunda zai faru ina tare dakai!"
da kyar ta samu ya zauna kan cushion har lokacin Jikinsa karkawa yakeyi.
A hnkali noor ta sulale a kasa hawaye na ambaliya a fuskarta ,
Aunty ta zube gwiwonta akasa tana rokon nainah akan ta taimaketa ta fada mata ,
gaskiyya.
Dan murmushi nainah ta saki ta zauna ,daya bayan daya take kallon kowa a falon.
Sunkuyar da kanta tayi akasa ,
Ta soma basu lbrn yarda aka samu cikin bakaramin kaduwa kowa yyi ba,
Cikin minti biyar Dr.khaleel bakori ya hallara a wurin Dan nainah ta masa alkawarin bbu Wanda zai kamasa ,
ya fadi gaskiyya yyi tafiar sa,
cikin inda inda Dr.bakori yyi bayanin komae,
Kowa sae da ya girgiza a wurin afusace Aliyu yyo Ku kan kura akansa ,
Punch yake basa ta koina ,
da kyar aka kwaci Dr.bakori a hnnun Abutturab .
Nan take Uncle saleem yyi waya ,bbu jimawa sai ga Polisawa aka tafi da Dr.bakori.
Nan take Aliyu ya yanke jiki ya fadi "...bayan ya farfado sae surattai yakeyi ,Noor na tallabe da kansa tana kuka itama.
Alh.chanji yyi Rantsuwa Nainah bazata koma gidansa da Abun kunya ba,sae dai ta zauna a wajen Aliyu idan ta haife masa dansa ta koma daga baya.
*
Bbu Wanda yabi takan nainah ,
Aunty mace mai sanyi zuciya ita ta baiwa nainah daki tayi wnka taci abinci.
da tamatsa akai ta wurin Aliyu ,lallashinta ta somayi akan tayi hkuri tunda batada lfy.
ta fada mata haka ,sabida Aliyu baya ko son ganin ta .
Washe gari ............Aliyu ya koma Lego's shida noor yabar nainah a hnnun Aunty acewarsa ya tsaneta bayason ganin ta ,
Kudi masu yawa Ya zubewa Aunty akan ta kula da nainah da abunda ke cikinta.
*
Kwance take a dakin ta ,tana jin shigowarsa da kwantawar da yyi abayanta ,kala batace masa ba.
" ya kira sunan ta yafi sau biyar bata amsa saba.
"Yaya ka fita a dakin nan I want to be a lone Dan Allah ka fita ,idan baka fita ba nizan fita."tayi mganar a sanyayye yanayinta da muryarta na qara hurting dinsa,
Tsayawa yyi yana kallonta so yakeyi ta kalli idanunsa da yanayinsa ,Taga shima bazai iya yafe ma kansa ba Hurting dinta da yyi duk da yasan ba laifinsa bane ,Kaddara che !"zuciyata na tareda ke ,
Nasani amma ajiarka na acikin wata .
Kaddara che hakan kinfi kowa sani?"
Tana girgiza kai take fadin."ni ban sani ba,kadaina yiwa qaddara sharri!"ke kuma ki daina yiwa kaddara musu,
Hnnu ta saka a tafukkan hnnunta tana rufe idanunta take fadin kafita "Abutturab Dan Allah "... Karo na farko acikin Rayuwarsu da ta fadi sunansa,
Fita yyi daga dakin cikin sassarfa ,gamida Jamata kofar.
Kwanciya tayi agado ta cigaba da kukanta Wanda ya haifar mata da wani irin ciwon kai.
Kusan wata biyu noor ta kwashe suna Rigima da Aliyu ta daina basa hakkinsa ta daina ,yimasa girki sae dai yayo take away a waje dukansu su biyu sunyi wata irin Rama." Ranar wata laraba ya shigo gidan fuskarsa bbu walwala yake fadin"ki shirya zamu tafi kano."shaye da toka take fadin"bbu inda zani!
Bai ko kalleta ba ya Juya yabar dakin shirinsa ya cigaba da yi yana gama hada Jakarsa ta kayansa ya hada nata, tana zaune tana kallon irin Ramar da yyi.
da Isar su nainah kawae suka sama agida Aunty tana gidan baffan mijinta da Allah yayiwa ya'rsa Rasuwa.
Sunyi mmkin irin chanjawar da nainah tayi ,
Cikinta ya fito sosae da fara'arta ta tarbesu ,
noor che mai karfin halin gasheta cike da tausayi take mata yaya Jikinta?"karo na farko da noor taji tausayin Nainah aranta,
da Dan murmushi nainah ke fadin "jiki da sauqi noor" yaya Lego's ,
Murya a sake take fadin"lfy qlau,
Bari na kawo maku Ruwa ,
Ta miqe da kyar noor tayi saurin dakatr daita tana fadin "kiyi zamanki Dan Allah karki Ji chiwo." Tayi mganar cikin muryar tausayi.
Tabe baki turab yyi yabar falon ,
Kwana biyu kacal noor ta sake da nainah sosae .
tausayinta takeji ,A bangaren Aliyu ko kallon arziki baya yiwa nainah."
Ya tsaneta tsanar da baisan qarshenta ba.
da dare suna zaune a falo ,
Suna kallo banda nainah dake zaune a dakin ta ,
bata iya jure kallon tsanar da take gani a idon Abutturab. "Aunty kingan sa yadaina harara Aunty nainah ,bayasonta ko kadan cikin nan yana bata wahala.
" noor ta karasa maganar kuka nazo mata ,
Aunty tayi daria tana kallon Aliyu take fadin."to kai kaji ka daina ,
Baice komae ba ya dauke kai .yana son Dan cikin nainah itache baya so.
Satin su daya bbu laifi Turab na amsa gaisuwar nainah har yana tambayarta batajin komae ?"tana amsa masa da bbu wata matsala..
Satinsu daya sukayi shirin komawa ,
Anan noor ta murje ido tache ita bazata koma ba,
Awurin Aunty nainah zata zauna harta Haifa masu baby."Rigima sosae sukayi har yyi fushi yyi tafiar sa ,
Sae da ya kwashe wata ukku cur."baizo ba waishi ala dole yyi fushi ,
Ko ajikin noor akai akai tana kiransa a waya kuma tana hadasa da nainah ,haka yake daurewa su gaisa.
Cikin nainah ya nainah shiga wata Tara."
*
Ranar wata lahadi da safe sae ga humy ta sauka garin kano ,dauke da Dan Alh.chanji har acikin gidansa,shima lokacin chiwon zucia ke damunsa.
"Ya girgiza da yaga humy ta taho masa da yaro mai kama dashi sak!harta yatsun kafarsu iri daya Anan ta dire masa shi ,tana fadin." Aure na nan da sati biyu Alh.wani Dan uwana nasamu zay aureni ya Rufamin asiri ga danka nan ,sunan Ku daya ana kiransa khaleel sae wata rana."da haka ta Juya ko waiwaye ,mami tayi kuka tamkar Ranta zai fita hakama Alh.chanji ciwonsa ya tsananta ,musamman ganin wannan abun kunyar da yyi ,
da kyar ya lallashi hajia zulfa macce mai kawaeci da daukar kaddara !"ta shirya masu fita Dan yaje ya nemi gafarar ya'rsa Dan shi yasan tashi ta qare.....
Mami ta qarayiwa Khaleel wanka ,yaro mai kyau komae na mijinta bai baro ba tanajin kaunar yaron aranta.
Jin wannan mummunan Labarin da mahaifinta yabata nan take nakuda ta kamata Aliyu ma yana Lego's aka kwasheta sae hospital cikin dare ta riqa nakuda har safe ,
Noor tamkar itake nakudar sae kuka take Risga tana hngo Abutturab na tahowa ta Ruga ta kankamesa.fadin take."tana labor Room Dan Allah karta mutu yaya ."do something I love her a lot.....tamkar Aliyu ake Jira sae gashi ta haifo santaleliyar yarta mai kama daita sak!"
Aka nadota a towel aka miqawa Aunty,cikin tashin hnkali Abutturab ke fadin"Yaya jikin uwar.?"am sorry to say Aliyu maihaifiyar ta rasu ,
ga sako tache abaka ,likita ya miqawa turab envelop jiki na kyarma ya amsa.
Wasu irin hawaye ke zuba a idonsa."
"Ta mutu ta Rasu yaya."
"Innalillahi wainnah ilaihir Raji'un.....kawae yake fada ,
Nan take noor ta suma.
Kuka yakeyi sosae yana fadin nainah ta tashi ya yafe mata yana sonta ta tashi suyi Aure haka ya koma wani irin zautattace acikin hospital din,
Jin yakeyi tamkar ya cire zuciyarsa ya ajey gefe ,Yaji mutuwar nainah chanji fiye da tunanin mai karatu ,sae dai muce Allah ya jikanta ya kuma Raya.(miss fatyma Aliyu bamalli)" Rayuwa ta musulunci.....
💝ABUTTURAB💝
~Written by Asmy b Aliyu~
Haske writer's Association.
Thursday, 6 September 2018.
END.....
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.