Abu turaab Complete Hausa Novel
Reading file: Abu-turaab_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 7 of 18
💝ABUTTURAB💝
~Writeen by Asmy b Aliyu~
Haske Writer's Association.
10..
Wani irin irritating look yakeyi mata Wanda yasa Iya Jummai shan Jinin jikinta ,Amma dayake dakakkar zuciya gareta sai Ta hade rai tana watsa masa wani irin Arnen ka'llo .cikin kunfar baki take fa'din."Auhh dukana zakayi ?"to dakeni mana!
"Afusace turab ya daga hnnu da nufin ya zabga mata shegen mari sai Yaji an riqe hannunsa,
Afusace ya Juya sai ganin Auntyn sa Asma'u a tsaye cike da tashin hnkali take fa'din." Mekake shirin yi ne haka Aliyu?"kasan dai this not d support way da zaka daga hnnu akanta.
Zai yi mgana Taja hannunsa Ransa abace bai koma magana ba har suka shige gida.
"Iya Jummai sai famar fada takeyi da cika baki .take fa'din ."yau da kasan wadda ka kai hannu Jikinta acikin garin Giwa Dan iska kawae aikin banza aikin wofi." Nan ta Juya ta Rufe Noor da duka da gudu Noor ta miqe tsaye ta shige cikin gida tana Ihu kamar Ranta zai fita nan ya'n taron biki sukayo kanta."Wanda mafi yawancin su dangin Iya Jummai ne sai yan qalilan dangin mahaifin noor!"kubarni na kashe shegiya na huta!ni zaa gawadama dabanci !"Ehhh wai wannan yaron mai kama da Aljannu ni zay daga hnnu yace ya daka!"
Ae wlhi da ya kuskura ya da'ga Hnnu akaina ,saina makasa A koto !
Naga ina zai samu arzikin da zai kwaci kansa.
."matsiyatan banza!matsiyatan wofi ."yan tofin Allah tsine ,nan yan uwa sukayo kan Iya Jummai suna bata baki.
*
"Yanzu ace Aunty kamar Noor itace ta isa Aure duka shekarunta nawa?" Turab ya qarasa mganar Ransa abace tagumi Asma'u tayi tana qallon kanin nata Wanda yabi ya rikice ,
Zubur Abutturab ya miqe ya zura talkami akafarsa yyi hnyar barin dakin."ina kuma zakaje Abuu ?"ni bana son Rigima fa?kasan Halin baffa.gun sarki zani Aunty bazan yarda akashewa nooriyya Rayuwa ba .da haka yyi waje batareda yaji mai Asma'u zata qara fadaba.
."kowa baki yasaki yana qallonsa mutanen dake zaune cikin fada suna kallonsa,
Sarki yyi murmushi Toni Aliyu ya kk so nayi?"banida ikon Akan wannan yarinyar ,
Cikin taushin murya Abutturab ke fa'din rankai Dade kana da ikon hanasu wannan Auren.wlhi bana son nooriyya tayi Rayuwar kunci inason kyautata Rayuwarta ne ,pls kaduba magana ta.Shuru sarki yyi Yana Juya maganar Abutturab aransa kafin ya sauqe ajiar zuciya! "
to naji da karfe nawa zaa Daura Auren?"gaban Abutturab na dokawa yake fa'din."nima ban saniba ,
Nan sarki ya Juya kan dogari ."yana fa'din Ajey a binciko wane yaro nooriyya zata aura?"haka kuma azo da wakilin yaron da uwar Yarinyar dashi kansa Yaron.
Cikin minti talatin sai gasu bayyane acikin fadar,
Ka'llo daya Yyiwa yaron da wai shine zai xama mijin Noor dinsa ya dauke kai gamida binsa da harara.
Dariya Danladi yyi yana washe baki."danladi irin mutanen ne zaune gari banza can lokacin da Yana saida Arakke abakin gidansu.
Yanzu kuma sana'ar saida Ruwa yakeyi acikin amalanke."Wanda danladi baxai yi shekara Ashirin ba a dunia Dan dai yana da Girman Jikine ,haka bbu abunda bayasha na kayan maye. "Allah ya doramasa son Noor kamar me haka kullum cikin aikamata da saqo yakeyi iya Jummai ta amshe tana godia Ruwa ma kyauta ake zuba masu aduk safiyar Allah ."Dan yache bayaso Noor na zuwa Rafi !" Nan take iya Jummai ta aminche da danladi tache ya Turo iyayensa ,murna kamar yazuba Ruwa akasa yasha."
Nan take aka tsiyar da magana ,
Da dangin mahaifin Noor sukayi magana akan bai dace ba ace Noor bata ga Wanda zata auraba sai danladi.!"
Cikin su tayo da masifa ,tana fa'din."bbu Ruwansu ae ba su suke ciyar da nooriyya ba!"haka suka zuba mata ido."Idan akwae Abun da nooriyya ta tsana a dunia bai wuche danladi ba batasonsa bata kaunar ganinsa."
*
Nan sarki ya katse shurun da fa'din kunji bukatar Abutturabl?"iya Jummai ta hade rai lokaci daya tana fa'din bangane ba yallabai?"bamufa da dangantaka da wannan yaron! "Shine ubanta da zay hana ayi mata Aure?" Shekarun ta nawa sa'aninta yanzu haka suna da ciki da goyo.
Idon danladi sun kada sunyi Ja.sai famar watsawa Abutturab harara yakeyi!"
Cikin kuka Noor ke fa'din ."Dan Allah yallabai ka taimakeni bana son danladi!"kowa tausayinta yake ji Afusace Danladi ke fa'din."bakya sona don ubanki !"kudi na da kukaci fa?"kowa kallonsa yakeyi da mamaki .
Cikin taushin murya Abutturab ke fa'din ."mind your language guy agaban sarki kake!"
Harara danladi ya watsa masa gamida dauke kansa,
Sarki yyi gyaran murya yache ."............yanzu nawane kudin naka?"bbu kunya bbu tsoron Allah danladi yache ."dubu hamsine yallabai bbu yawa.
Murmushi Abutturab yyi zan baka kudinka indai zaka barmin noor!"kai Dannladi Ashe babban Dan fashine ban saniba?"kudinka ko dubu Ashirin sunyi ?"iya Jummai ta fada tana nunasa a fusace harara ya zabga mata gamida fa'din ."to karya zan maki ne?"duk garin nan waye baisan halinki da son kudi ba!"
Duk safiyar Allah ni nake siyamaku naman sawa a miya ,Dan dai noor taji ddi tsoka nawa kk bata munafuka!"zatayi magana sarki ya daka masu tsawa!"
Kuyi min shuru."A fada kuke baa filin dambe ba!
Ayi hkuri Rankai dde amma inada mgana?"fadi ina Jinki?"
Muddin Abutturab yace ya hana Aurenta saidai shi ya Aureta!...bazan yarda da Lagudeta da yakeyi ba yaci bulus wae anan shi mai wayo ,wai bayaso tayi Aure yanzu!"lalatar da yakeyi daita ne yasata fara kirin dangin batar...............!"Just shut up!Aliyu ya fada afusace cikin daka mata tsawa!
Bbu shiri tayi shuru sarki ya girgiza kai gamida fa'din."baki kyauta ba ,ko kadan bakya kyautawa Jummai .naji Aliyu zai auri Nooriyya A yanzun nan basai gobe ba.
Ni zan zama wakilinsa waziri ya zama wakilin nooriyya Hankali Atashe turab ya buda baki yyi magana !"sarki ya katsesa.
Jin yyi duniar gaba daya tana Juya masa.............
💝ABUTTURAB💝
~Writeen by Asmy b Aliyu~
Haske Writer's Association.
11..
cikin mintunan da basuyi talatin ba aka Daura auren Noor da Aliyu ,akan sadaki mafi karanci dubu hamsin Wanda sarkine yabada sadaqin.
Lokacin da Asma'u taji labarin abakin wani makwafcinsu hankalinta yyi masifar tashi ,
duku -duka yaushe Abuturrab yyi girmn yin aure?"Dan kawae yyi karatunsa da wuri yagama shekarunsa bazasu wuche Ashirin da biyar ba.
Anan kuma iya Jummai tace ."Noor tabar gidan ta har abada!zaman me zata koma tayi agidanta tunda tana da aure a yanzu.
Ya'n biki suka cigaba da fadin Albarkacin bakinsu.
Wasu suna fadin ."Abutturab dame zay riqeta ?"wasu kuma suna taya Noor murnar samun miji Dan gayu ,Wanda yasan ciwon kansa.
Bayan an watse sarki yyiwa Abutturab nasiha ,haka yache zai bar Noor agidansa kafin ya gyara wurin da zasu zauna ."tunda auren ba wani cikin shiri akayisa ba.
Sai bayan sallah ishai ya samu shigowa gida ,anan matan baffan sa .sukayo cikinsa da Habaici kota Kansu bai biba ya shige dakin Auntynsa,
Lokacin tana zaune akan sallayah."
da alamr yanzu ta gama sallar isha ,samun wuri yyi agefen katifa ya zauna .yyi minti ashirin zaune kafin tagama azkar!"
Ganin yarda Ran Asma'u yake a hade yasa turab shan Jinin jikinsa.
Langabar dakai yyi yana qallonta cikin sanyi murya yake fadin."Aunty na mai kuma ya faru Aliyu din ki fane?"Wanda kk matuqar so fiye da komae.
girgiza kai Asma'u ta shigayi cikin Raunin murya take fadin."Wannan ba Abutturab dina bane Aliyu na ba zai Yi Abu batareda na sani ba?"meyasa kayi haka Aliyu?"idon sa rau rau yyi yazo ya Dora kansa akan cinyar Auntynsa ya dunkule wuri daya tamkar karamin yaro yake fa'din."kiyafemin Aunty bada niyyyar Auren nooriyya naje gun sarki ba............!"nan ya zayyane mata abun da yafaru ,Asma'u ta girgiza haka ta tausayawa Rayuwar Noor ,
Shafa lallausar suman kansa ta shigayi mai zubin Fulanin asali take fadin."Anya yarona Abutturab ya isa aure a irin wannan yananyin?"dago kansa yyi yana kallonta murmushi dauke afuskarsa ya miqe zaune yana fuskantarta,
Ya daqune fuska yana qallonta gamida langabar da kansa ,nima ban sani ba Aunty!"Amma ni Auren Noor bai dagamin hnkali !sabida turab yanason Noor tun ashekarun baya Aliyu yake cikin tsananin soyayyar kanwarsa nooriyya!"Asma'u zatayi mgana sukaji an turo kofar da karfi !"baffansu ne ya shigo a wulakanche yake kallonsu kafin ya maida hnkalinsa kan Aliyu"cikin kunfar baki yake fadin wato kai ka Girma?"har kai zaa daurawa aure agarin nan batareda sani naba?"yyi kyau ba laifinka bane!"amma daga yau din nan haka daga yanzun nan zaka kwashe komae naka kabarmin gidana!"ke kuma!"ya fada yana nuna Asma'u wadda ta zuba masa ido nabaki nan da sati 1 dal !"kifitar da miji kiyi aure idan bahaaka ba kema zakibi sahunsa!"Afusace yajuya yabar dakin yana banbamin fada Ran Abutturab idan yyi dubu to yabaci ganin yarda Auntynsa ke zubar da hawaye.cikin bacin rai yabar dakin ,
Cikin sati daya ya saida duka kaddarorinsu,
Batareda sanin Auntynsa.
Ranar Assabar da karfe shidda ya nufi gidan sarki akayi masa iso a turakarsa ,
Bayan sun gaisa yake fadin zasubar garin giwa.
"Shida Auntynsa a Kano zasu koma achan ya samu aiki awani company!" Yyiwa sarki karya!nan sarki yamasa murna ,gamida samashi Albarka anan ya aika akan Noor ta shirya mijinta zai tafita daita.
Murna awurin Noor tamkar meye?"kusan kwana biyar bata ga yayanta ba ,gashi mama ladi nabata kulawa uwargidar sarki!
Tana kula daita har wani fresh tayi.
Karfe bakwae Abutturab sukabar fadar sarki sukayi masa sallama Wanda sarki yabaiwa Abutturab sadakin Noor dakuma kyautar dubu goma.godia sosae hambal yyi masa,hannunsa cikin na Noor suka nufi gidan baffan sa."A hnya Noor sai surutu take zuba masa duk inda suka wuche sai an kallesu ana nunasu !"
cikin daka mata tsawa yake fadin kiyi shuru haka Noor!"...Idonta yyi rau rau kamar zatayi kuka bbu abunda Noor tafi tsana irin ayimata tsawa!"amma yau yayan ta datake so shiyake yimata tsawa kamar yarda iya Jummai keyi mata.har suka kawo gidan baffa bata qara magana ba,tana dai ganin Aunty ta saki hannun Abutturab ta Ruga da gudu ta shige Jikinta.wannan shine dalilin dawowarsu hambal acikin birnin Kano da zama ,cikin Rufin Asiri Asma'u ta hada diploma dinta haka qaramin gida ne sukaya siya acikin unguwar Jan bolo.da Rufin Asirin ne suka saka Noor a makarantar secondary wato government girl's day.har kuma lokacin Asma'u bata qarayin aure ba,
Haka Alh.sule Wanda a unguwarsu yake matansa ukku yana balain son Asma'u amma fir taki haka shiya Samar mata aikin karantar wa a wata private skull Wanda duk karshen wata Albashinta dubu talatin ne!"Asma'u tana girmama Alh.sule amma tana hango gobarar dake ci acikin gidansa.
Kawar Noor dayache Wanda a unguwarsu take duka sa'anin junane haka uwayenta masu kudine sosae!"duk da hambal baya barin Noor na fita ko makwafta haka bai hana kullum bikra zuwa gidansu Noor.
2days latter!
"Abutturab na zaune agida yadaina zuwa aiki ,da Auntynsa tafita tareda Noor zuwa skull shikenan da yake yanzu a skull dinda Asma'u ke koyarwa achan Noor take Wanda duk bayan wata ukku dubu biyar ake biya.
Kwance yake afalo ,Yana game da wayrsa kiran nainah ya shigo a wayarsa.
Agogo ya kalla kusan karfe sha daya na safe.
Sai gafda zata tsinke ya daga ,
Sallama yyi baa amsa ba!
" cikin cool voice nata take fadin ."kasameni office da kwalin karatunka ."tana maganar sounding so very command! "Zaiyi magana ta katsesa da cool voice nata take fadin." Aliyu pls!"da sauri ya cire wayar daga kunnensa ,yana son yakara tabbarwa kansa shin da nainah chanji yake magana?"Ashe tasan sunan?"Ashe zata iyayiwa mutum mgana cikin sanyi murya haka?"mezatayi da kwalin karatunsa?tambayoyin da Aliyu bamalli ya shiga jerawa kansa kenan!."
💝ABUTTURAB💝
~Written By Asmy b Aliyu~
Haske Writer's Association.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.