Complete Hausa Novels

Abu turaab Complete Hausa Novel

Reading file: Abu-turaab_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 6 of 18

da gudu ta nufi toilet Acikin toilet ta zube tana kwarara amae ,tamkar zata hada da kayan Cikin ta duka.
Gaba daya saida ta amayar da beer din da tasha ,
da kyar ta samu tayi wanka tana dafe dakanta ta fito daga toilet Wanda ke Neman ya Rabe mata gida biyu ,
Zubewa tayi akan gado tana maida numfashi wani irin zazzabi taji ya Rufeta lokaci daya.
dakyar ta daga waya ta kira family doctor dinsu,
Tana gama waya dashi ta kira Nana akan taxo ta hada mata tea sa'annan ta wanke mata toilet.
*
Aunty tana shirin fita aiki ta leko dakinsa tana kiran sunan sa A hnkali ,
Amsa wa yyi farar jallabiya che ajikinsa kallo daya zakayi masa kasan yanzu yatashi barci.
Baki bude Aunty ta saki tana ka'llonsa bazaka fita Aiki bane yau?"Bana Jin zuwa Aiki yau Aunty ,bana son wannan aikin da Alh.sule ya samarman gaskiyya zan canja aiki!"ya qarasa mganar sounding so very serous! "Kallonsa yamaida kan Noor wadda take Cikin shigar Arabin gown tayi Rolling kanta da bakin veil ,fuskarta bbu kwaliyya Amma hakama tayi kyau.
Hade rai noor tayi ta dauke kanta,
." ita wannan ina zataje?
Yyi mganar shaye da toka ,
Tace zatabi ni ne! A Ina?"Aunty ta hareresa Ina kasan zan tafi."Cikin satin nan kayi kokari ka canja mata skull ,gashi karatun ta yatsaya ka hanata zuwa wancan makaranta.
Maganar aikin ka kuma baka isa ba Aliyu!"wai kai wani irin mutum ne?"sau nawa ana Samar maka aiki daka fara zuwa sai kace baiyi maka ba."wannan qaron bazan saurare kaba,haka kawae kasa Alh.sule yache nike zogaka,
Shige mutafi Noor ya tsayarda mu zamuyi latti.
da ido yabisu ,
Kan soofa ya koma ya xauna ."Azahirin gaskiyya bazai iya cigaba da Aiki a karkashin nainah chanji ba,
Abunda yasa kuma yau baifita ba haka kawae yaji ."he don't want to see her face ,he don't like her Any more...................
"Aliyu Yusuf bamalli!(Abutturab)"Asalinsa bamalli ne na garin giwa.
Mahaifinsa Asalinsa Dan giwa ne,haka ma mahaifiyarsu .su biyu iyayensu suka Haifa Abutturab bai bude ido yaga iyayensa ba.ya bude ido ne ya Rayu da Yayarsa Asma'u ,Wanda kafin Iyayensu su Rasu Asma'u taga gata duk da iyayenta ba karfi garesu ba,
Haka suke Rayuwarsu Cikin Rufin Asiri mahaifinsu Mln.Yusuf kiwo yakeyi ,sai kuma noma Wanda aka gada tunda ga iyaye da kakanni.
Mahaifiyarsu laraba kuma yin kirba fura shine sana'arta Asma'u idan ta dawo makarantar boko,
Kafin su tafi islamiyya tana fitarwa da mahaifiyarta dashi .
Bayan Rasuwar mahaifansu suka koma A hhnu baffan su lokacin Abutturab yana da shekara ukku a dunia.
Haka lokacin Asma'u tana da shekara sha Hudu ta gama secondary school bayan kammalawarta ne samari sukayi chaaa akanta!" Lokacin hnkalin Asma'u yyi masifar tashi ,
Baxa taiya yin Aure tabar Abutturab ba.ko gidan baffan nasu a takure suke .
Nan baffanta ya Rufeta da fada akan tafitar da miji acikin samarinta shi yagaji da ciyar daita.
Cikin watannin da basu wuce ukku ba ,Asma'u tabi ta Rame.
dakyar ta samu tafitar da wani Dan Abokin baffan ta.
Har yamata Alkawarin zai dauki nauyin karatun Abutturab ,haka zay hadasa da yayan sa dayake yana da mata daya da yaya ukku duka maza.
Ba karamin ddi Asma'u taji ba nan aka kawo kayan angani anaso,haka akasaka biki watan moleedi .
Bayan wasu shekaru................Abutturab ya fara karatu Cikin nasara gashi da kokari,
Har yagama primary school
Amma Asma'u ko batan wata bata tabayi gidan Mln Bello ba,
Abutturab yana da shekara 18 yagama secondary school kuma a lokacin mijin yayanrsa Allah yyi masa Rasuwa.
Mutuwar ta girgizasu duka,
Bayan shekara daya Abutturab zaune a gida bbu aikin ki sai yar buga bugar da bazaa Rasa ba.
Haka lokacin Ya shaku da wata yarinyar mai suna noriyyah wadda ta taso Cikin maraici kamarsa ,
Bbu uwa bbu uba haka ta taso a hnnun matar uba ,dangin mahaifinta kuma .duka matattar zuciya garesu bbu mai iya Riqata.
Kullum idan aka basu Assignment a makarantar boko Wanda kawunta Yunus shiya sakaata ,shine kanin mahaifiyarta .
Sai takaima Abutturab yyi mata,
Abutturab yana balain jin tausayin Rayuwar da Nooriyya keyi.
Haka zata saka shi agaba da surutu ,
"Tana fadin Yayana Iya Jummai bata sona idan nayi kudi bazan bata ba.
Yayana inason karatu inason nazama likita inason na riqa yiwa mutane Allura.
dafa kanta Abutturab kurum yakeyi ." Yana fadin Karki damu Noor watarana zaki zama wani Abu A rayuwarki mutanen kauyen nan zasuyi Alfahari dake.
Jin haka Noor zata saki baki tana dariar murna.
Shima Abutturab dariar kawae zaiyi,
Bayan shekara daya Auntynsa zata karayin Aure ,agidan waziri lokacin waziri zai kawae Sarki takardun Abutturab Wanda gwamnati zata dauki nauyin karatunsa Waje ,tunda yarone mai hazaka. wata biyu aka gama shirin tafiar Aliyu akasar New York!"Asma'u ba karamar murna tayi ba ,hakama Abutturab damuwarsa daya baisan a hannun waye zaibar Noor ba.yana matuqar tausayin Rayuwar da nooriyyah keyi.
Haka ya hkura yyi bankwana da mutanen kauyensu ,haka ya damka Rayuwar nooriyya A hnnun Yayarsa Asma'u.
Tafiar Abutturab nooriyya saida ta kwanta ciwo."iya Jummai saidai kawae ta Jefa mata haibaci tana fadin."Yagama Lalata ki ya gudu kasar Arna ya buda sabuwar Rayuwa ,dama wannan yaron mai kama da Ya'yan Aljannu ya maki nisa yafi qarfin ki ,ko kyawonsa Abun sone ga yayan masu hnnu da shuni..haka Nooriyya ta cigaba da Rayuwa bbu Ranar da bata zuwa gidan Aunty Asma'u tana Jin labarin yayanta!"
4years leaf.............Abutturab ya dawo a kauyensu ya iske mummunan Labarin da ya gigitasa ,
Waziri ya saki yayarsa saboda ya gaji da cinye masa abinci da takeyi tunda tazama Juya bata haihuwa."lokacin da turab yaji wannan lbrn Ransa yabaci ,zay isko Waziri Asma'u ta hanasa karkaje Abutturab Dan Allah!"meyasa bazanje ba Aunty!yyi mganar sounding so very Angry.
Rufe kansa yyi a daki yana tunanin hnyar da zai Samar masu farin ciki.
da Yamma ya shirya ya nufi turakar sarki ya gaishesa sarki yyi matuqar murna ganin Abutturab!"anan yake basa hkuri Akan Abunda waziri yayiwa yayarsa.
*
"Yayana!"... "......Ta fada tana kara shigewa ajikinsa ,
Har Abada bazay mance wannan fuskar da muryar nan ba." My Noor !"ya fada yana riqo hnnunta duka biyu sanye take cikin Riga da skirt na kanti ,masu duhu amma sun tsufa sosae haka sun yayyage."ga mamakinsa sai yaga hawaye a idonta,
Zaunar daita yyi akan dakalin gidan su.shima ya zauna gefenta yana share hawayen idonta yake tambayarta lfyr ta?"
Kuka na zomata tana Rufe baki haka tana leqen gidan su kar wani ya ganta.
Murya kasa-kasa take fa'din ."Aure iya Jummai zatayi min ,ta fada hawaye na Rolling akan fuskarta!"
"Wat!" Abutturab."
ya fada hnkali atashe ka sassauta murya yayana karta Jiyomu ,yayana yau zaa dauramin Aure!" Ta qarasa maganar tana fashewa da kuka ,karatun kifa?"yyi maganar cikin fushi!"haka nan take idanunsa suka Juye zuwa tsantsan bacin rai.
"Sun fitar dani yaya!" Meyasa?"Ina kudin da nake aiko maki dashi?"yana tambayr ne duka acikin fushi .
"Sannu Hamshaki bokan Turai!" Yaji muryar iya Jummai akansa,
Wani irin Juyi yyi yana kallonta ,yyinda Noor ta miqe tsaye jikinta na Rawa take fa'din Dan Allah iya !"saukar mari taji tasssss!"iya Jummai ta dauke nooriyya dashi ,wani irin Ihu Noor ta saki gamida zubewa akasa dafe da fuskarta.....

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.