Complete Hausa Novels

Abu turaab Complete Hausa Novel

Reading file: Abu-turaab_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 5 of 18

8..

kallon fuskarta kurum yakeyi ga macce har macce but sai kyawon Dan maciji .
"I hate you so much Mrs.nainah canJi from d bottom of my heart!" Abutturab ya qarasa maganar afusace gamida tura center table din dake tsakiyar falon.
Afusace ya Juya yabar falon ,nainah duk da bata cikin hayacinta tana ganin fitarsa .
qoqarin miqewa zaune takeyi ta kasa dafe kanta tayi da duka hannayenta biyu ,Ahnkali ta shiga lumshe idonta .cikin mintunan da basuyi biyar ba tasamu barci.
Dakyar ya samu Abun hawan da zai maidasa gida ,
dare ya farayi sosae shabiyu saura minti goma.
Koda ya koma gida basu da nepa, har ya nufi dakinsa sai kuma ya tsaya chak!
Sae lokacin ya tuno da halin da yabar Noor aciki,
Hnyar dakinta ya nufa da sauri fitilar wyarsa yyi amfani daita yana haske dakin ,
Hangota yyi kwance akan bed ta dunkule kanta wuri daya.
Haka yana jin kukan sauro a dakin tunda batashiga net ba dole sauro ya dameta ,A hnkali ya dagata atsorace ta bude ido tana shirin saka masa ihu yyi saurin rufe bakinta .
Cikin muryar Rada yake fadin nine fa!"
Jin muryarsa yasa tayi lamo Ajikinsa,
Tana sauqe ajiyar zuciya.
da haka ya nufi dakinsa daita.
adaren bai samu wani barci ba ,sae tunanin hali irin na nainah yake.
Wai tasamu gata bazaayi mata fada akan Abunda takeyi ba,gudun kar a bata Ranta.
*
Kusan qarfe goma sha daya na safe tashigo falon nasu.mamin dinta che hakimce acikin custions din dake zagaye da falon.Nana CE agefenta tana hada mata tea.
qallo Hajia zulfa tabita dashi lokaci daya kuma taji gabanta ya fadi !"badai nainah ta sake dawo ma shaye -shaye ba?"
Zama nainah tayi gefen mahaifiyar ta ,murmushi dauke afuskarta take fadin."good morning Mami!"Hajia zulfa ta hade rai lokaci daya batareda ta amsa ta ba take fadin!"badai kin dawoma halinki na shaye-shaye ba nainah?"
Kin manta irin bakar wahalar da kika sha a baya?"har sai da akayi maki dashin Hanji!"Hajia zulfa ta qarasa mganar cikin daga murya da zafin Rai!"
."Mami plss!
"Nainah." ta fada cikin qunar Rai,
Ki daina daga min murya Dan Allah!
Ae Kadan nasha Raina ne naji ya baci shiyasa kawae nasha."sai kace wadda tayi mummunan Abu zaki riqa daga min murya agaban Ya'r aiki!"this is d last tym da zakiyi min Haka mami ,Iam not taking it any more...........this is my life am not your!"Afusace nainah tabar wurin da gudu ta haye up stair's da ido Hajia zulfa tabita tana goge kwallar dake son zubo mata.
Ba laifinki bane nainah laifin duka yana ga Alhaji!"
*
Alh.Ibrahim chanji shine asalin sunan mahaifin nainah Dan Asalin Jihar danbatta ne karamar hukumar Kano.
Su ukku kacal mahaifinsu ya Haifa .yana da shekara goma sha takwas mahaifinsa ya Rasu sakamakon hadarin mota.
Mahaifinsa cikakken Dan kasuwane,
Wanda yake da babban shago acikin kasuwar Kano,mahaifinsa Attajirin gaske ne ,kannensa biyu duka mata Hafiza da saratu .hafiza a Kaduna take aure yyinda saratu ke Aure acikin garin danbatta.
Ibrahim Awaje yyi karatunsa ,
kasancewar mahaifinsa yabar masu dukia mai yawa.
Yana kammala degree dinsa a fannin Economic computer nan mahaifiyarsa tayi masa sha'awar yar uwarsa Rabi'a .akan ya aureta
Anan yabuga hnnu ga kasa yache baisan zancen ba ,shi bayasonta.
Hnkalin mahaifiyarsa ya tashi sosae Dan lokacin Ibrahim yana da shekara 34 adunia.
Anan kannensa mata suqa riqa tausarsa.nan yache zai samo wata amma bayason Rabi.
Wata daya da mganar ya Auri Zulfa'u wadda asalinta shuwa Arab ne kasuwanci ya kawo Baban ta kano ,
Biki akayi nagani na fada acikin kawayen danbatta .
Haka Ibrahim ya Gina gida acikin garin Kano ,
Haka yyiwa mahaifiyarsa part nata katon gaske gidane na gani na fada haka na zamani.
Anan mahaifiyarsa tabuga kai ga kasa tache ita Sam bazata koma tabar dangintaba.
Bbu lallashin da Ibrahim baiyi mataba amma taki .
Haka yan uwansa suka basa hkuri ,haka ya hkura yatare da amaryarsa macce mai kirki da Alkunya asalinsu shuwa Arab ne.
Wata biyu da Aurensu mahaifiyarsa ta kwanta jinya satinta biyu Allah ya Amshi Ranta,
Mutuwar ta ta girgizasu bakadan ba.har akayi kwana arbain Ibrahim baidawo cikin natsuwarsa ba.sai da taimakon matarsa zulfa ya fara walwalah.
Bayan wasu shekaru ,zulfa ta haiho ya'rta kyakkyawa sak mai kama daita ,
Murmushi dauke afuskar Alh.Ibraheem chanji yake fa'din nasamu Nana Fatima .murmushi Hajia zulfa tayi tana fa'din sunan Hajia za'a saka mata kenan?"dagemata gira daya yyi Wanda zasu riqa kiranta ("Nainah) yana qara gyara kwanciyar Jaririya
Haka akayiwa waleema gagaruma haka aka riqa sanarwa a jarida gidan redio a talabijin.
Gata sosae ake nunawa nainah haka ta taso cikin gata da sangarta haka zalika mafadaciyar gaske ce nainah ga Rigima abunda takeso shi akeyi ,
Haka zatayi laifinda zaa iya dukanta amma sai ace ko kallon banza bazaayi mata ba.
Wasa gaske nainah ta samu shekara goma sha biyar amma ko batan wata Hajia zulfa bata sakeyi ba.
Bbu asibitin da basu zaga ba ciki da wajen Nigeria mgana dayache lafynta qalau Allah ne bai kawo ba.
Tun Abun yana damunta har tazo tabar saka Abun Aranta ,
Ga Allah yabasu ya'h tagani ta fada wadda zaa iya likawa a goshi amma ko kadan nainah batada tarbiya mahaifinta ya Riga da ya sangartata .
Nainah tun tana secondary skull take zuwa party da zuwa club,
Haka maza tanadasu Friend's Wanda idan mahaifiyarta tayi mgana sai uban ya kada baki yace ,shin zulfa'u sokike kiga nainah ta kebance kanta ita daya bbu walwala?"Alh.Amma ace kamar nainah shekara goma sha biyar tana kula maza?"ran Alh.chanji abace yake fa'din to mata kikeso ta kula?"tun daga wannan Ranar Hajia zulfa ta kawo ido ta sakawa nainah ,haka bata zuwa islamiyya daga boko sai zaman gda.
Tana da shekara goma sha shidda tagama secondary skull.
Haka ta fadawa daddynta ita A London takeson yin karatunta ,a Nigeria yan tsurku sunyi yawa.Alh.Ibrahim yyi daria yana shafa kanta yake fadin karki damu my daughter duk inda kk son karatu zan kaiki ,
Karatu nainah awaje ya kara bude idonta sosae ,
Haka tasamu qofar fara iskanci .nainah bbu abunda batasha na kayan maye ,Haka bbu irin shigar da bazata iya fita daita ba.
Karewa ma gida mahaifinta ya saya mata nan ta dauko friends dinta mata su biyu ,Wanda suma yan Nigeria ne .
Afra da Humaira ,haka zasu kawo maza agidan su kwana suna tsotse-tsotse ,Abu dayane nainah bata yi shine sexxxxx!alkawari ne ta daukarwa kanta duk namijin da ya nemi yyi sexx,
Daita tabasa baya har Abada.....
Cikin shekara hudu Rayuwar nainah awaje ta lalache,
Likitoci sun tabbatarwa da Alh.Ibrahim chanji muddin nainah ta cigaba da shaye -shaye hanjinta zasu katse ,zasu iya rasata!
Hawaye na zuba a idon Hajia zulfa take fadin kagani ko Alhaji ?"komae nainah keyi da daurin gindinka!"haka duk wani zunubi da take aikatawa da saka hannunka aciki!"
"Ya isheki haka zulfa'u!"
Alh.chanji yyi maganr Cikin daka mata tsawa ,
Komae ya samu ya'ta kece silaaah tunda bakya iya fadin alkhairinta sai aibunta.
Sai inga idan Rayuwar nainah a hnnun likitoci take sai su kasheta na gani!aekin banza aikin hofi kawae kidaina aibanta min ya'h wlhi Ranki zai baci!"
Saida nainah tayi Jinyar wata 3 agadon asibiti sa'annan ta samu sauqi,
ga mahaifinta ba zama yakeyi ba,kullum yana waje bayama da tym din matarsa .
Idan tamasa mgana sae yache aeki yyi masa yawa.
Bbu fitar da Alh.chanji zay yi awaje batareda maccen banza ba!"waiya zubillah Ansha fadawa Hajia zulfa ana ganin mijinta da Matan bariki sai dai ta boye kanta adaki tayi ta kuka."tasan bbu Jin ddin da basu ganiba A rayuwarsa ,Wanda Jin dadin na banza ne Amma tana jin bakin Cikin Rayuwar da mijinta keyi da ya'rsa.
Cikin shekarar nan Alh.chanji ya budewa nainah katon company na saida motoci Wanda ake yin oder dinsu daga waje,
Haka mahaifinta ya" fada mata sai yarda tayi dashi haka duk Wanda yyi mata shi zata saka Wanda baiyi mata ba ko kallonsa kar tayi barantana Alfalmarsa."
Lokacin da lbr yasamu Hajia zulfa tasamu nainah da mganar akan tasaka kaninta saleem Wanda uncle yake ga nainah!"
Budar bakin ta tace. "Mami shi bayada bakine da zai aiko ki?" Na lura uncle saleem din nan yana Jida kansa,zan saka shi sabo dake Amma ki fada masa bana son shisshigi da saka ido!"gobe ya sameni office 8:00@m na safe batareda Hajia zulfa tache komae ba ta kada kai tabar dakin.
*
Abun mamaki a tattraeda nainah chanji duk tsawon Rayuwarta tasan tayi samari da dama, amma acewarta har yau baa halicci mijin da takeso ba!"
ga Dan governor din Kaduna dake matuqar sonta ,
Amsa daya tabasa kayi hkuri sageer gaskiyya bana yimaka soyayyar Aure nafison muyi kawanche kawae!"....
*
Abutturab"...
Next page zakuji Asalinsa.......
??ABUTTURAB??
~Written by Asmy b Aliyu~
Haske Writer's Association.
9...

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.