Complete Hausa Novels

Abu turaab Complete Hausa Novel

Reading file: Abu-turaab_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 3 of 18

4..

Kai tsaye tayiwa Nana umurnin ta ha'da mata Ruwan wanka bajimawa Nana ta fito tana fadin ta hada lokacin nainah daga ita sai pant da bra Wanda tana kokarin ciresu ne agaban Nana ,
Wanda hkan yana daya daga cikin Al'adarta bbu Ruwanta ko agaban maminta zata iya cire kaya.
Cikin taushin murya take fadawa Nana a ha'da mata lunch datafito wanka zataci ,tana jin yiwa.
Nana ta amsa mata da toh."gamida ficewa a dakin.
Tsayawa tayi ajikin mirrow dressing din cikin toilet dinta ,
Ka'llon fuskarta tayi nan take fuskar turab ta bayyana yana sakar mata murmushinsa mai kyatarwa ,
Wani sashe na zuciyarta na yaba kyawonsa kota ina Kyawon Abutturab ya Rudata matuqa ranar farko da ta fara ganinsa batayi zaton Yaron da Alh.Sule ya kawo mata bane ,sae da taji abakinsa .
Tasan itadin kyakkyawar che ta qarshe haka mamanta shuwa Arab che Wanda gaba day'a maminta ta kwaso .
Amma zata iyachewa idan suka fara buga gasar kyau itada wannan Abutturab din ,to tabbas zay zo na day'a ita tazo a matsayin ta biyu.
Yana day'a daga cikin dalilin da yasa nainah taji ta fara tsanarsa ,Haka kurum taji bai dache ache yana da wannan kyawun ba kasancewar sa Dan talakkawa gaba da baya.
Tsoki ta buga haka tayi saurin daura yatsan hnnunta akan dan kyakkyawan bakinta da cwt voice nata take fa'din ,
"Shittttttt!"
Nainah !"
Karki bada kanki mana da haka tayi saurin watsar da tunanin Abutturab aranta ta cigaba da wankanta.
Agurguje ta shirya cikin Riga da skirt na English wear's long skirt black ,
da orange din T.shirt mai dogon hannu mai maballai agaban Rigar ,
Kan soofa ta ko'ma ta zauna wyarta ta Jawo kirar IPhone 8
Minti biyr da zamanta sai ga Nana nayi mata knocking.
sae da tagama Jan ajinta kafin tabata damar shigowa ,
Angama ha'da komae saida tagama hura iska kafin tabata amsar tana zuwa,
gaban mirror dreassing ta ko'ma ta dauki Ribbon tana tattara sumar kanta baka wuluk mai sheqi wadda ta sauqa har tsakkiyar bayanta.
bedshoes ta zura akafanta ta nufi main falonta ,
Wanda anan ne dinning side dinta ,
Kai tsaye zama tayi tana baiwa Nana umurnin tayi serving nata.
Still hnkalin ta na kan chart din da takeyi da friend dinta dan governor Kaduna.
*
ba ajima ba sai ga shi Nana ta shigo tareda Aliyu Wanda yaci wankan kananan kaya ,
Fuskar shanu nainah tayi tana watsawa Nana wani irin irritating look,
Cikin katseta Nana ke fa'din."hajia tache ayi mashi iso wurinki bata qara fadar komae ba ta juya tabar falon .
Ka'llo ka'llo suka tsayayi a tsakanin su ,
Lokaci day'a taji ranta yyi mugun baci ture abincin gabanta tayi sai taga ya nufo dinning side din yana kasheta da murmushi Wanda ta lura haka fuskarsa take,
qa'ra tsuke fuska tayi Jan kujera yyi gaf da tata ya zauna wani mugun haushi da tsanarsa taji sun dirar mata lokaci daya meye wannan yaron ya'ke nufi?"shin Meyasa ma Mami zata turo mata shi a turakarta batareda Neman izininta ba?"
💝ABUTTURAB💝
~Writeen By Asmy b Aliyu~
Haske Writer's Association.

5.
daukar glass cup yyi ya dauki bottle water ya tsiyaya aciki sa'annan ya ka'fa abakinsa baki wangalau ta saki tana ka'llon tsabar rainin hnkalin da yyi mataA yanzu cup din nata zai dauka yasha Ruwa!"how dare he?"
Ka'llon cikin idonta yyi Wanda yana hango ba'cin Ranta qarara ,smile ya saki kafin ya fara fa'din ."Am sorry maah Nayi laifi haka na amsa laifina hakan bazai qara faruwa ba!"ya qarasa maganar sounding so cwt.
Baki wangalau ta saki tana ka'llon kyakkyawan fuskarsa,
Shaye da to'ka take fa'din waya baka izinin shigowa part dina?"Hajia !"ya bata Amsa sounding so free.
Ya isheka haka?"
Ta daka masa tsawa ranta Abace?"
Hi !"
Don't use tongue with me young lady,"cewar Abutturab ya fada in a high tone da ya tsorata nainah.
Tana hango bacin Ransa,
Ke wacece da zan zauna ina baki hkuri ki kiyi kina cin darajar Hajia ne da nake ganin girmanta da na ajey wannan aikin."dan baayi maccen da zata zauna tana wulakantani ba.
Arziki haukane!"ya qarasa maganar a tsawace,
da yasa nainah ta tsorata haka ta tsura masa ido.
Zaki iya daina ka'llona dan ni ba Tv.bane ,sosae nainah taji kunya amma da yake kafiya gareta nan take ta sha to'ka wai kai waye boss tsakanin ni dakai?"haan? Kanme zaka tsaya akaina kana yimin fada tamkar wani ubana!"have your way out?"
Ta fada masa cikin daka tsawa tana nuna masa qo'fa ranta abace ,
Ko a kwalan rigan Abutturab ya nufi ko'fa farin cikinsa day'a ya bata mata rai hakan dama yakeso.
Zubewa tayi akan soofa tana maida numfashi fuskarsa take qa'llo yana mata tsawa da matsifa ,mai makon taji haushinsa bataji hakan ba .Amma ranta a bace yake wani gefen kuma batason Abutturab ya daina aiki akarkashinta,
Tafiso ya cigaba da zama akarkashinta yarda zata samu damar wulakanta shi.
*
Washe gari.karfe takwas nainah tayi shirin zuwa office sauri takeyi suna da meeting ,
Tana cikin shigar traditional kaya atamfar super sharaton che ajikinta dinki Riga da skirt Wanda yakamata sosae ya Riga yagama bayyana siffar Jikinta ,sae dan qaramin veil kalar dark blue ,
Da ta aza akan kafarta .
Sae talkamin qafarta shima blue amma hill ne,
Fuskarta tasha make up har tagaji sai zuba qamshi takeyi tayi kyau na fitar hnkali ,dan irinsu nainah baka yimasu kallo day'a ka dauke kai.
A babban falo suka hadu da nana.
Tana ka'llon agogon hnnunta take tambayr Nana Mami fa?"tana barci bata tashiba.
daukomin lunch box dina zuwa mota achan zanyi break fast."
Abutturab na awaje yana Jiranki yazo baki tashi ba!"Shaye da to'ka nainah ke fa'din karfe nawa yazo?"
7:00@m.
da haka ta fice daga falon,,
A harabar gidan ta hango Abutturab yana hira da Isah mai baiwa Flowers Ruwa.
Yana ganinta ya taho da sauri ,yamika mata car key na Benz dinta da ya wanke.
Ka baiwa wanchan yazo mutafi.
Ta fada cikin basa umurmi,
Shigar English wear's ne Ajikin Abutturab farar shirt.da bakin wando na Jean's,
Sumar kansa ta kwanta luf tamkar ta larabawa.
Ba karamin kyau yyi ba.
Kafin ta nufi motar Abutturab ya rigata ,gaisheta yyi fuska a ha'de ta Amsa batareda ta kallesa ba.
Back side ya bu'demata ta zauna ,
Ya amshi lunch box a hnnun nana ya saka agaban motar.
A mota zaman shuru suka zauna,
da Isar su .suna gama parking ,
Aka fara gaisheda nainah cike da isa take da'ga hnnu wasu ma a haife sun haifeta Ran Abutturab ya qara baci.
daukar lunch box yyi yabita dashi a katafaren office nata.
Office ne mai girman gaske ,mai ha'de da master bedroom.fridge California bed ,TV.soofas bbu abunda bbu aciki.
Zama tayi akan soofa ,
Yyinda shi kuma Abutturab yyi tsaye tamkar gunki."
Leg's dinta ta nuna masa,
Ciremin shoe's din kafana ,
Ta fada tana basa umurni,
Bbu musu ya durkusa agabanta ya shiga cire talkamin kafarta,
Ajey su yyi agefe sai yaga ta Ciro tissue tana goge dai dai wurin da ya taba akafanta,
dauke Kansa yyi ransa na tafasa.
Ha'damin tea ka zuba min chip's akae ,
Ta fada bata kallesa ba tana danna wya .
Hada mata yyi yaja dan qaramin center table dake tsakiyyar office din ya tura agabanta,
Yana tsaye ta fara break fast bata ko kalli inda yakeba,
Still tana danna wayarta,
"Shaye da to'ka ta dago fuskanta tana kallonsa ,I will appreciate it in xaka daina qa'llona hakan kanemi wuri ka zauna.
Ta fada ta maida hnkalinta kan wyarta..........
💝ABUTTURAB💝
~Written by Asmy b Aliyu~
Haske Writer's Association.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.