Maradams Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: MAR ADAMS BOOK 3 COMPLETE BY AYSHA BAGUDU.txt
Chapter 15 of 29
Page 22
Mr ata ya tasa maryama gaba da kallo tamkar wani tsohon maye ido cikin ido yake kallonta dan sosai ya sanya kwayar idanunshi cikin nata ai ko tana lumshe idonta sai hawaye sharrr ..”suka shiga gangarowa akan kuncinta,bai san sanda ya mike tsaye ba ya soma taku ahankali har ya qarasa inda take tsaye Ya tsaya yana qoqarin kamo laulausar tafin hannunta cikin nashi tayi saurin zame hannunta cike da jin haushinsa amamn sai da yayi nasara riko yatsun hannunta yana murzawa a hankali tare da hura mata iskan bakinshi a saman fuskarta.”
sun kai minti goma a haka tana hawaye shi bai rarrashinta ba ,shi bai sakar mata hannu ba har sai data gaji dan kanta tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya a jere murmushi yayi aciki yana cewa “kin d’auaka d’an wannnan hawayen zai sa na tausaya miki ,”?” “yarinya baki san adadin hawayen dana zubar akanki ba ,baki san kalar wahalar dana sha akan zafin soayyarki ba ,baki san tashin hankalin da dana shiga akanki ba, nayi kuka nayi hauka duk akanki a qarshe har aka so a d’aukeni mahaukaci alokacin da nake jin cewar kina cikin duniyar nan amamn aka nuna min ke din iya mafarki ce ,wannan wahalar kad’an ce daga cikin wahalar dana sha akanki maryama dan kukan dadi kike yi a yanzu tunda kina dani .”
Office din ya d’auki shiru bakajin motsin komai sai na saukar numfashinsu wanda ke sake haddasawa zuciyar maryama shiga tashin hankali yayinda shi kuma zuciyarsa ke narkewa akanta gabad’aya marayama a matukar rikice take dan bata qaunar kusancinsu haka, dan ma Allah ya taiamketa har zuwa lokacin sauran abonkan aikinta basu qaraso ba
batayi tsammanin zai yi magana dan a tunaninta a haka zasu tabbata sai kawai ta jiyo muryarsa a kasalance “menene dalilinki na barin office jiya ?”kamar tace masa takurawarsa ce tayi yawa sai ta share tace “am very sorry sir jiya kaina ke ciwo “tana fad’ar hk ya sakar mata hannu yana cewa” I hate lies “ya fad’a yana jan tsaki .”nan take ta diririce “shi kuma wayarki me yasa kika kashe ?“saboda matsalar wuta ne “ta bashi amsa da haka bakinsa ya ta’be “daman yaushe zaa samu natsuwa a wannan banzar unguwar taku, kiyi qoqari kiyi aure ki bar wannan banzar unguwar “kamar tace masa unguwarsu ba banza bace dan duk lalacewarta tayi wa rayuwarta amafani ,kuma ta rufawa ahlinta asiri na tsawon shekaru amamn saboda alqawarin data d’aukarwa kanta na bazata sake yin abinda zai hassalashi ba saboda abincinta dake qarqaahinsa yasa ta sauke nunfashi kawai tana jin quna aranta dan taji zafin mgnrsa amman bata da zabin daya wuce tayi shiru .”
"new design dinki sunyi ready "?new desing kuma ?ta tambayesa zuciyarta na rawa dan ta manta da wani batunsa Kallon da ya dauketa dashi ne yasa tayi saurin cewa "yes ready ready sir” good kije ki kawo min yanzu na gani yana gama fadar haka ya juya ya wuceta ya fita daga office din ta juya a natse tana kallon bayansa tana sauke wani naunayen ajiyar zuciya tare da lumshe idanunta “kai wannan mutumin zai iya kashe mutun da ransa .”
ahankali ahankali take d’aga qafafunta tana kallon tafiyarsa, tafiyarsa ma abun burgewa ne har sanda ya shiga wani office dinsa yana shiga ya d’auki wani file green ya fito ya sake shiga office din daya baro ya zauna ya d’aura kafarsa d’aya akan d’aya .”
tana fito da desing’s din tana mita “wannan mutumin mugun dan rainin wayo ne cewa yayi babu ruwansa da wani new designs din da zaayi yanzu kuma yazo yana tmby dana yagasu dana shiga uku ko kuma da nice nayi masa magana da yanzu yau ni da maseefa, takardu ta rike ta fito zuwa office dinsa ta nemi izinin shiga ya bata izini ta shiga ta qarasa daf dashi ta tsaya tana dubansa yana duba file .”can ya ajiye sakamakon kiran wayar office dinsa da akayi ya amsa kiran.”
ta cigaba da tsayuwa can ta duba agogon hannunta byn ya gama ya ajiye wayar yana dan waigo inda take fuskarta ahade da alamun jin haushi muryarta a dake tace” Mr ATA sir !” ya sake tsura mata idanu alamun yana saurarenta”a sanina baka zuwa office da wuri amman me yasa jiya da yau kazo da wuri ?a d’an tsorace yace “why are you asking me foolish question?ya qarasa fad’a tsawace yana mika mata hannunsa alamun ta bashi desing din ya gani zuciyarta a dake ta mika masa a hankali ya kar’ba ya fara budewa yana kallo zanen mace ce sanye da doguwar riga da abun hannu da sarkar wuya yayinda take tsaye a gefensa tana ciza harshenta ya dan waigo kadan ya kalleta ya dauke idanunshi ya sake maidawa kan desing din hannunsa.” byn second goma ya ajiye ya dauki dayan takardar zane zane ne masu matukar kyau da daukar hankali ta zana ta sake kai dubanta ga agogon hannun
“wannan dabia nata na mugun bashi haushi ita da bata bawa lokaci mahimanci sai yaransa uwar me take dubawa a agogo ,yaja tsaki yana shafa sajen fuskarsa sannan ya dauki pencil ya daura akan takardar zanen tana ganin hk tayi saurin cewa"sir what are you doing?
kallon da yayi mata yasa tayi kasa da muryarta sosai "sir idan akwai abinda bai yi maka ba kamata yayi kabari na gyara da kaina ba sai ka wahalar da kanka ba ,ta fad'a tana kokarin kwace takardar ya hana akwai abinda bai min ba a desing din kuma zan gyara any problem?"No sir !ta fad'a ba dan ranta yaso ba can tace “amman shekaranjiya da mukayi magana akan plan dinmu kin amincewa kayi amman kuma me yasa yau kayi mgn akanshi "bana son yin mgn akan abinda ya wuce yanzu zamuyi aiki ne ko kuwa tmby zaki kasheni daahi ?numfashi ta sauke tace “ muyi aiki “ta fad'a am tana d’auke kanta .”
"your design are very nice but there's something mistake kina bukatar taimakon irinmu kafin ki zama expect, nan take ya shiga mata bayanin abinda zatai tasa hannunta acikin bakinta ta dan ciza tana lumshe idanuwa wanda kadan ya rage mr ATA bai sume ba gabadaya yanayinsa ya sauya hatta tsigar jikinsa sun tashi, allah dai ya tamaikesa sanye yake da suit da babu abinda zai hana bata gani ba ."
Yadda yake mata bayani itama batayi sanya agwiwa ba ta shiga yi masa bayani tana juya hannuta da kwayar idanunta ta a qarshe ta saka yatsan hannunta cikin bakinta duk sanda tayi haka sai yaji wani iri yerrr ajikinsa kuma ya lura dabiar ce haka ya mike tsaye daga mazauninsa ya qarasa inda wasu manya takardun zane suke ,ya dauki guda daya ya bude yana dubawa har ya taho gareta ya tsaya kusa daita yana nuna mata kokuwa tashiga yi da numfashinta dan kamshin turarensa mai tsuma zuciya da gangar jiki ne irin turaren da nmj yayi amfani dashi yazo gareka babu tantama zaka iya sakar masa ragamar rayuwarka ,ta dan kallesa tana yatsina fuska bayan wani lokaci ya rufe ya ajiye ya amshi takardar hannunta ya bude yna nuna mata bayanin abinda zatai wanda zai sake sakawa ta dauki hankalin client yana gamawa ya nuna mata kofar fita da hannusa sannan ya koma mazauninsa.”
ta fara tafiya a hankali tana cigaba da kallon takardar hannunta yayinda aranta tana sake mamakinsa wani irin juyayyen hali garesa idan mutun bai da tsananin hakuri bazai ta’ba jin dadin zama dashi “Ko me ta tuna sai ta juya ahankali nan take kwayar idanunsu ya tsarke cikin juna dan shima bayanta yake kallo dayar takadarta dake kan table dinsa ta nuna masa ,ya dauka ya mika mata ta sake juyawa shi kuma ya gyara zama yana cigaba da kallon yadda take bada step ."bayan kmr minti goma ta sake shigowa "sir dan allah ko zaka taimaka min ina son nayi aiki amman kayan aikin duk suna cikin wancan durowa din nayi nayi na bude na kasa ko zaka taimaka min dan Allah ?shiru yayi yaki cewa komai "please sir !"okay ya mike yayi gaba ta biyo bayansa har zuwa office dinsu ta nuna masa durowan da hannunta ya qarasa cike da kwarin gwiwa yaja sai dai ya kasa budewa.”
ya waigo ya kalleta ta hade fuska tamau tmkr wacce bata ta’ba dariya ba tana ciza harshenta dan daman tana sane ta bashi aiki ,shi kullum bashi da aiki sai zama Kan kujera yana amsa waya da zarar kayi mistake ya kiraka da nonsense,stupid ,ko sai gama shan wahala kayi aiki yace bai masa ba .”ya sake ja still the same ya saka iya karfinsa ai ko yana já durowar ya bude shi kum yayi baya zai fado kanta itama tayi baya luuuuu yasa duka hannuwansa yayi mata riko mai kyau batare daya sani ba hannuta ya sauka akan daidai saitin zuciyarsa dake bugawa da mahaukacin qarfi shima hannunsa daya ya rike tsintsiyar hannunta dake rike da zane dayan hannunsa kuma ya zagaye kungunta dashi .”
ido cikin ido suke kallon juna yana kallonta cike da tsananin soyayya yayinda ita kuma abun ya zame mata bakon alamari dan tunda take hakan bai ta faruwa daita ba, hasalima kullum cikin hijab da nikaf take shine silar canza mata rayuwa sun dade tsaye suna kallon juna yana kwakume daita jin saukar tafin hannunsa a gefen fuskarta yasa ta dawo haiyacinta da sauri ta zare jikinta tana juya masa baya tare da rungume takardar aqirjinta tana jin wani irin kasala ajikinta numfashi ya sauke yana kallon bayanta kafin ahankali ya tura hannunwansa duka cikin aljihunsa muryarta a matukar sanyaye ta furta "am sorry sir ?babu abinda yaji hakan ma dadi yayi masa .”
ta juyo ta sake bude bakinta zata sake furta masa am sorry "ki zauna Kiyi aiki dake gabanki “ ya fad'a yana juyawa ta lumshe idanunta, ta zauna masa dariyar mugunta ai taso ya kasa ne ,tana cikin aiki ya sake shigowa hannunsa rike da cup biyu ya ajiye mata a gabanta ta dago ta kallesa a natse da shayayyun idanunta "coffe !
"Thanks “. kawai ta fad’a atakaice taso tace masa bata sha sai dai tayi shiru zuciyarta cike da mamakinsa yau din kamar bashi ba ta cigaba da aikinta a natse ya dinga tafiya acikin office din yana kurban coffe yana lumshe idanun har zai wuce yaga bata da alamun shan coffe "me yasa bazaki sha coffe ba ? ya fad’a domin a tunaninsa tunda tazo da sanyin safiyar nan ba lallai ta karya ba sai data yatsina fuska tace “ bani da raayin shan abu a waje bare abun hannun nmj ba kuma dan rashin yarda bane raayi ne kuma ma I don't like drinking coffee ai kamar na fad’a maka last time .”
shiru yayi yana kallon qaramin bakinta komai nata dabam ne da sauran mata ya koma bakin kofa ya tsaya yana rike da kugunsa yana kallonta ta maseefar burgesa "maryama !ya kira sunanta cikin wata irin murya mai kashe jiki” yes sir !” ta amsa ko zan iya sakaki wani aiki ?why not sir “ta fad'a ya ajiye cup din hannuna yace biyoni ya fita zuwa office dinsa ta biyosa ya mika mata wani jaka mai shegen kyau "ta karba ta bude taga kaya ta tsaya tana dubansa da jakar hannunta "ki bude ki gani?”
batai mutsu ba ta bude ta fito da kayan ciki doguwar riga ce wacce akayiwa aiki da stone tun daga sama har kasa "ko zaki gwada naga yadda zai yi ajikinki ?da sauri ta tsura masa ido tana kallonsa da mamaki"
Muryarta cike da tashin hankali tace “but sir !"Kar dakikiyar kwalkwaluwarki ta kawo miki wani abu matata na siyawa "sir tunda matarka ka siyawa ai kamata yayi ka kai ma.."Ke nake son ki gwada ajikinki na gani so kije kiyi abinda na sakaki ga daki can ki shaga karki bata min lokaci jiki sanyaye ta wuce tana yatsina face ta murda handle ta shiga .
"shi kuma ya dauki cup din coffee dinsa ya shiga sha yana kai kawo .”
Byn wasu mintuna ta bude kofar ta tsaya batare data fito sosai ba ta hade hannunwanta waje daya tana jin faduwar gaba kafin daga baya ta soma taku a hankali ya ajiye cup din hannunsa tun daga sama ya dauki kallonta har kasanta ahankali ya zuba hannuwansa cikin aljihunsa yana cigaba da kallonta kafin a natse ya qaraso ya tsaya abayanta yana sauke numfashi sannan ya cire hannunsa daya acikin aljihunsa ya ta'ba kayan a hannunsa yana dubawa can taga ya dauki takarda yana rubuce rubuce yana mata bayani ina bukatar zanen mace da irin wannan kayan har komai da komai exactly ta tsura masa ido tana masa wani irin kallo "ko bazakiyi ba ?.
Jikinta a sanyaye tace “zanyi!” só sai kije ki fara ya gbdy ta kasa magana kai kawai take gyada masa dan yanayin da take ji ajikinta babu sauki yanayin da bata ta’ba jin irinsa bane ,ya sake yin taku biyu yayi kusa daita sosai ya kai kansa daidai saitin wuyanta yana sauke mata numfashinsa a wuya ya motsa bakinsa a hankali "mar ..."sautin muryar sultana ta katse masa hanzari ..."cak ta tsaya mamaki qarara kwance akan fuskarta tana dubansu , jikin maryam yayi sanyi sakamakon matsananciyar kunyar data rufeta, ta dan saci kallon sultana ta kasan idanunta taga irin kallon tsanar da take mata mai cike da tsantsar kishi ."
mr ATA bai kalli inda sultana take tsaye tana kallonsu da mamaki ba ya bawa maryam umarnin kije ki cire kayan "good morning sir “! amman me Ke faruwa haka ?ya lumshe mata tsumammun idsnunshi yana sauke numfashi sai maryama ce tayi mata bayani dan shi bashi da lokacinta "you could have called me ya Adam I can do more than this for you ,ita nayi raayi ta min any problem?amman me yasa sai ita bayan gani dana kasance jininka ?ya ma akayi kuka kasance tare adaidai wannan lokacin ko tare kuka zo ne? gaban maryama ta rikice ta dinga jin wani irin mummunar fad'uwa gaba yayinda jikinta ya dauki rawa ta kasa motsi bare taje ta cire kayan jikinta shi kuwa wani irin mugun kallo yayi ma sultana sannan ya wuceta zuwa mazauninsa batare daya ce mata komai ba dan bata isa ba.”
da sauri maryama ta shiga ta cire kayan ta fito zuwa office dinsa wanda zuwa lokacin mutane sun fara zuwa "good morning!!!ta furta tana zama sannan ta kallesu daya byn daya mr ATA fa ya amince da new desings din mu "me Kike qoqarin kice ya amince maryama cewar surayya maryama ta gyada masu kyau tana lumshe idanunta suna cikin haka sectray ta shigo "maryama !yes ma !gabadaya desings dinku sun kammala dan zaa fara shirin aiki akansa ?eh !ni dai nawa ya kammala har na shiga sabon aiki na sauran ne dai sauran kadan su qarasa madam some ta juya maryama tace “excuse me ma!” ta tsaya dan Allah idan zaa dinka kayan ayi kamar yadda na zana "okay ta fad'a tare da juyawa ta fita gabadaya kowa ya fuskanci aikinsa ."
******
Suna zaune mr ata ya shigo yana magana da some yayinda gabadayansu suna tsaye cike da girmamawa yana cikin magana wayar sultana ta dauki qara ya juyo ahankali yana mata kallon banza irin kallon da yake mata yasa taji jikinta ya dauki rawa qoqarin kashe wayar ta fara dan a dokarsa baa kiran mutun idan yana magana sannan mutun bai isa ya amsa kira ba ,ta dan saci kallonsa kamar yadda maryama tayi ,sultana ta aikata laifin amman gabadayansu zuciyarsu rawa take kallo daya zaka masu ka fahimci haka muryarta a hankali tace sorry sir "lumshe lumtsatsun idanunshi yayi ya cigaba da magana zamuyi qoqarin mu gabatar da new desings din nan in sha allahu idan kunci saa zaa da.. .."wani kiran ya sake shigowa ya katse masa mgn wannan karon qarara ake iya hango bacin ransa yaji kamar ya kifa mata mari ita kuwa idanunta ta kai ga kallon screen din wayar sunan Aunty abida tagani yana yawo numfashi ta sauke "ko me zan mata adaidai wannan lokacin "me Ke damun tunaninki ne sultana “?me zai hana kisa wayar a silet me yasa bakya yin abinda dan Adam yake ?”kalli maryama kwararriya ce a gurin iya zane amman kin ta'ba ganin wayarta na qara . koda yaushe wayarta na silet nan take maryama ta sha jinin jikinta ta fara zazzare idanuwa” to be your last warning nonsense girl kawai da batasan komai ba sai zallar shirme “yana gama fadar haka Ya juya ya koma office dinsa yana fita maryama ta dubi surayya da sauran matan tace “kuyi ku qarasa aikinku kafin ya sake shigowa ."
Sultana na fita ta kira Aunty abida tana dauka ta hau magana cikin zafin rai "me yasa kika daukar wayata ? taya zan dauka ina tare da ya Adam sister idan kinga abinda yayi min a gaban abokan aikina sai kin tausaya min” what akan me kenan “?nan ta shiga koro mata duk abinda ake ciki da new desings din da'a zaa gabatar batare da sanin kamfani ba na fad’awa sultan amman ban san me ye shirinsa ba dan har yanzu bai zo office ba bare naji yadda sukai da baba qarami .kice wannan yarinyar ta samu dama haka lallai akwai sabon aiki agabanmu shiyasa banason ayi aikin ba kuma wai dan banason cigaba yaya adam bane idan akayi nasara maryama ce nasara saboda ita ta kawo tsarin kinga dole zai Bata mahimanci arayuwarsa .”
“naji bari na kira Ibarahim naji ko yasan abinda Ke tafiya suna gama wayar ta kira yaya Ibrahim byn ya dauka tace "ka natsu da kyau akwai abinda zan fad'a maka very important sultana ta fad'a min tun last week a office anyi shirin gabatar da new desings batare da sanin kamfani ba” what”! ya furta da karfi yana mikewa tsaye cike da bacin rai me kike qoqarin fad'a min?” abinda muke gabatarwa duk qarshen wata me yasa zai shirya haka byn shine ya karfafa wannan dokar” wannan ba shirinsa bane shirin wannan tsinanniyar sabuwar maaikaciyar ce maryam ne sunanta ko maryama shiyasa nace nayi sauri na fad'a maka kayi duk yadda zakayi hakan bai tabbata ba ai wannan maganar dole sai baba yaji amman bari na bincika na gano gaskiya mgn yay discounting din kira.”
Mmn Sudais
[8/31, 11:25 AM] Safwan Libiya 2: 💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
BOOK 3
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 25
daidai kugunta mr ata ya rike yayinda ita kuma hannuwanta duka suka sauka akan kafad'ansa saurin d'auke numfashi tayi cike da tashin hankali ta tsura masa shayayyun idanunta tana kallon cikin kwayar idanunsa, azababen kamshin turarensa ne mai sanyin dadi da bugar da zuciyar duk wanda ya shaka ya ziyarci hancinta, nan take zuciyarta da kwakwaluwarta suka soma amsar wani babban sako na musam man ,ajiyar zuciya kawai maryama ta dinga saukewa da sauri da sauri yayinda kwayar idanunta ke cikin nashi cike da matsanancin tsoro."shi din ma kallonta yake sai dai shi hankalinsa a kwance yake kallonta babu wata alamar tsoro ko firgice a tattare dashi, a inda tsoro da matsanancin firgicin ya bayyana akan fuskar maryama ,zuciyarta kuwa banda bugawa da karfi babu abinda take a sakamakon yanayin data tsinci kanta ciki mai wuyar misaltuwa, dan zuwa yanzu numfashinta ya soma barazanar d'aukewa sakamakon kamshin turarensa dake kai kawo a hancinta ."sun d'auki kusan minti goma suna tsaye suna kallon juna cike da jin wani yanayi na dabam a gabad'aya sansar jikinsu mai kama da shocking wanda shi daman ba sabon abu bane agurinsa itace dai ya zamewa sabon al'amari dan ba sai an fad'a maka ba ,kana kallonta kasan sabuwar shiga ce shiyasa azahiri yake iya hango tashin hankalinta ."
"Nana hauwa'u da mami ne tsaye suna kallon abun mamaki fitowarsu kenan daga parlour'n mami nã biyu domin kallon presentation wanda ita mami din da biyu ta fito tana son ganin sabuwar maaikaciyar adamcy'nta a natse ta cigaba da kallon adamcy'nta cikin wani irin yanayi wanda kwata kwata bata ta'ba ganinsa ciki ba sai yau ,sosai ta tsura masu matsakai tan idanunta ,yadda mami da nana hauwa'u ke kallonsu haka sauran ma'aikatan dake tsaye a parlour'n ke kallonsu cike da fargaba da tashin hankalin abinda zai biyo baya ,da'akace a office ne bazasu damu ba saboda norma normal suna ganin hakan na faruwa a tsakaninsu. yawon kallonsa gareta amman irin haka ma basu ta'ba gani ba wannna shine karo na farko da suka gani kuma ko haka zai faru sai a gidansu qarin tashin hankalinsu ma ganin yadda mami da nana ke kallonsu a firgice".
ahankali nana hauwa'u ta gyara tsayuwarta tana sake dafe bayan ashraf dake rungume a kafad'anta ta waiga inda mami ke tsaye jikinta na d'an kirma tace "mami ko kinga abinda na gani kuwa ?"ta tambayeta tana sake maida kwayar idanunta kansu mr ata qirjinta na bugawa ."
mami ma kallon diyarta tayi tace "auta na gani "wacece wannan yarinyar?"meye matsayinta a wajen yaya ?"nayi imani duk duniya babu macen da yaya zai yiwa haka cike da kulawa mami lallai akwai wani abu a kasa". numfasawa mami tayi tana sake maida kallonta garesu adaidai lokacin da suka had'a ido da maryama dake fuskarta na kallon kofar shigowa ne shi kuma fuskarsa na kallon step ne ".
da sauri maryama ta dawo haiyacinta tare da cire hannuwanta duka ajikinsa ta tsya tana wasa da yatsunta ."duk da batasan ko su waye tsaye ba amman zuciyarta ta gigita da ganinsu."sanyayyen numfashi ya sauke muryarsa a kasalance yace be careful I wil not always be there for you".ya fad'a yana lumshe mata lumtsatsun idanunshi ."shiru ne ya biyo baya kafin ahan kali ta gyad'a masa kai alamun taji sannan ta sake juyawa ta cigaba da tafiya cike da sanye jiki ,shi kuma ya juyo da niyyar ya dawo wajen client dinsa kawai yaga mami tsaye a bayansa tana kallonsa ."
Ahankali mami ta soma tahowa zuwa inda yake tsaye suna kallon juna inda sauran ma’aikatan suka bi bayan maryama zuwa sauya kayan jikinsu muryar mami a raunane ta soma magana "halan wannna yarinyar itace maryama ?"yayi shiru yana dubanta batare da yace komai ba dan bai san me zai fad'a mata ba ".adamcy ban ta'ba ganinka cikin irin wannan yanayi ba sau yau ,yayi taku d’aya yana gyara tsayuwarsa tare da tura hannuwansa duka cikin aljihun suit dinsa yana cewa “itace amman abinda ke tunani ba haka bane yana gama fad’ar haka ya soma taku cikin isa da kasaita don barin wajen kafin ta sake wata tambayar sai dai cikin sanyi murya mami ta kira sunanshi “adamcy …” ya tsaya cak tare da juyowa suna fuskarta juna da maminsa idanunta ta zuba mishi kawai tana kallonsa tare nazarinsa ganin yadda gabadaya yanayinsa ya sake sauyawa cikin d’an kankanin lokaci .
Suna tsaye mami bata bata kai ga sake magana ba su maryama suka sauko d’aya bayan d’aya suna gama saukowa kawai sai shigowarsu baba qarami suka gani mr ATA bai lura da shigowarsu ba madam some ce ta hankaltar dashi ya juyo a hankali yana dubansu tare da sultan ."a natse client din ya qarasa ya samu baba qarami "barka da dare mr Edris!” ya mika masa hannu fuskar baba qarami a hade ya mika masa hannu "yanzu nake maganarka araina gsky naji dadin yadda akayi representation din yau.”
gaban baba qarami yayi mummunar faduwar “inda cliet dinsu ya cigaba da magana “ shiyasa ma zanyi order kaya masu yawa a hannun mr ATA gsky wannan yaron naka yasan Kan kasuwanci "baba ni ..."baba qarami yayi saurin daga ma sultan hannu inda client ya cigaba da magana "gsky wannan yaron shine hasken kamfaninku duk ranar da'aka babu shi gsky kamfaninku zai samu matsala .”
Nan take zuciyayoyinsu ya dinga bugawa "he has figueira and effort , bealiant “. ya sake fad'a yana kallon mr ATA daya fuskanci baba qarami fuskarsa a had’e tamkar wani zaki kafin ahankali ya motsa lip’s dinsa "banason mutune na shigowa inda nake batare da neman izinina ba ,baba qarami ya sake kallonsa cikin matsanancin ‘bacin rai zuciyarsa kamar ta buga tsabar bakinciki “mr lawyer's I will like to show you my design “inji cewar sultan mr lawyers ya girgiza masa kai yana cewa "no time for now til next time saboda yanzu gbdy mun gama zabar wanda yayi mana a gurin dan’uwanka dan haka mu yanzu ma zamu wuce ya fad’a yana kallon mr ATA “dan allah ka tabbatar zuwa sabon wata komai yayi ready ,bazan samu damar zuwa ba kawai ka tura a sauke min kaya "an gama” na gode sosai mr ATA ya fad'a yana mika masa hannu sukai sallama sannan ya juyo yana kallon yammata d’aya bayan d’aya tare da cewa su biyosa a lokacin maryam na amsa kiran umma ".
Muryarta can kasan makoshinta take magana dan idan ba kusa kayi daita sosai ba bazakaji muryarta ba ta ra’ba ta gefen mami inda mami ta d’auketa da wani kallo tun daga samanta har qasa tare da yi mata kallon sani bata kai ga qare mata kallo ba maryama ta wuceta tana cewa “umma kinga yadda aikinmu ya samu kar’buwa wallahi nayi mamaki ban d’auka new design dinmu zai samu nasara haka ba kinga yadda mai order kayan ya dinga murna yana jin dadi "na godewa allah da sanyi idaniyana ta samu nasara a aikinta kinsa ina kallon fuskarki d’auke da murmushi, Kiyi maza ki dawo gida da wuri kinga banana banason kina dadewa a waje “in sha allahu amman umma dan allah ki dawo gida gobe mana dan gidan baya min dadi idan bakya nan .”“karki damu bari da zarar na gama abinda nake zan dawo ina miki fatan alkhairi da samun nasara arayuwarki, farincikinki shine farincikina maryama allah ya dangwamar dake cikin farinciki “Ameen umma na gode ina jin dadin yadda kike bani kulawa sannan kike supporting dina akan komai nawa shiyasa matsayinki ya zarta na kowa acikin zuciyata ,"ni dai ki kasance cikin farinciki sannan ki rike mutuncin kanki da aikinki da kyau domin ki samu nasarar da tafi wannan "in sha Allahu umma amman kinsa wannan nasara har da mr ATA aciki domin shima ya bada gudunmuwa sosai “ kingani ba shiyasa nake yawon cewa ki kwantar da hankalinki Kiyi hakuri da halinsa da sannu zaku saba ki fara jin dadin aiki dashi “see you umma sai kin dawo “take care of yourself my maryama ."
Shiru mr ata yayi yana kallonta har sanda tai sallama da umma ganin yadda take cikin farinciki shima sai ya tsinci kanshi cikin farinciki ya dinga kallonta yana jin kamar kar ya bari ta wuce gida ,a yanzu tunanin wannan uguwar tasu yake, runtse idanunshi yayi yana mai tsananin tausaya mata, ko yace ya bata kyautar mato a yanzu ba lallai ta amsa ba amman zai had’asu gabad’aya yayi masu kyautar mota bisa qoqarinsu yasan bazata fahimci komai ba dan bazai juri ganinta cikin tirmitsitsin mutane a motar haya ba .idan ka bata mota a ina zata ajiyeta ?”kwakwa luwarsa tai masa tambayar ya kai hannu ya shafa goshinsa zuwa karan hancinsa “abinda yafi kawai ka hanzarta aureta shine mafuta agareka gabadayansu mr ata yasa aka d’aukesu acikin hadaddun motocin sa tare da bada umarnin a sauke kowaccce a gidansu, sannna ahankali ya dawo zuwa parlour’n mami .”
Inda zuwa wannan lokacin parlour’n ya cika da mutane tsaye mami , yaya Ibrahim ,aunty abida uncle jay da dai sauran yan’uwansa yana gama shigowa uncle jay ya hausa da fad’a "me yasa kayi abinda kayi adamcy ?kafin uncle jay ya cigaba da magana baba qarami yayi tsigil yace “me ka d’auki kanka? ka fad'a min ina jinka ,mr ata yayi shiru kawai yana kallonsa “ka bani amsa ina sauraranka ka bani amsa”. baba qarami ya sake mgn a matukar fusace uncle jay ya matso kusa dashi ya dafa shi yana cewa “yaya kayi hakuri abinda zai faru ya rigada ya faru amman bai kyauta ba .”muryar baba qarami ta cigaba da fitowa a zafafe “kowa yasan wannan zalinci ne dan bama kasuwancinmu haka kuma bazan ta'ba yarda da hakan ba Adam ya had’u da client privet bayan nayi masa gargadi mai qarfi har uwarsa tana bani kwarin gwiwa bazai yi ba kawai sai naga ya aikata kenan duk abinda zanyi nayi ?kuma nasan yayi haka ne da had’in bakin uwarsa .”
Mr ata zai yi magana mami tai masa gargadi da idanunta tana qarasowa zuwa inda yake dan haka ya furzar da hucin numfashi yana kamo lip’s dinsa na kasa parlour'n ya dauki shiru har mr ATA bai ce komai ba sakamakon qafarsa da mami ta take tana masa gargadin kada ya furta komai "dan allah kayi hakuri tabbas yayi kuskure kuma ina tabbatar maka bazai sake ba ka ga dare yayi yanzu kaje ka kwanta gobe sai ayi magana "bazan ji wani hakuri ba ko naje na kwanta har zuwa wani gobe yanzu nake bukatar amsa daga bakinsa”. mr ATA ya kallesa idanunshi cike da’ bacin rai "baba ai Adam bazai iya cewa komai akan tambayar daka masa saboda shi kansa ba ra’ayin kansa bane wannan fa duk ba plan dinsa ba plan din wata maryama ce ."da sauri mr ATA ya maida idanunshi kan aunty abida yana mata wani mugun kallo mai razanarwa .”
"Maryam !?
“Wacece maryama” menene had’inta da kamfanin mu?wannan shegiyar yarinyar data fita yanzu tana waya tana wulwulaga idanuwa kamar mayya itace maryama kuma itace yarinyar da yake wulakata yar uwarsa sultana akanta "wannan ai wulakanci ne akwai dokoki akan kamfanin dan me yasa wata staff can zata canza mana tsarinmu ?”to na rantse da Allah kayi na farko kayi na karshe da zaka sake had’uwa da client private karka manta wannan ba kamfanunka bane kai kadai kamar yadda kasani hadin gwiwa ne ,bazai yiwu ka dinga yin mana abinda kaga dama ba, idan iko da takama kake son yi ka tattara ka koma compines dinka kaje can kayi abinda kaga dama, amman anan baka isa kayi abinda kaga dama ba “.
“wallahi baba duk ya canza tsarin komai shi da yar iskar yarinyar nan "bazan duba wata dangantaka ba idan kika sake kiranta da yar iska sai na wulakantaki
ya fad’a yana nuna aunty abida da yatsan hannunsa sannan ya kalli yaya Ibrahim “warn your wife kana ya sauke zazzafan numfashi ya cigaba da magana “wannan ba plan din maryama bane tsarina ne ni ne naga dama yi kuma nayi abinda raina yake so ya fad'a tare da juya masu baya” wannan new desings din yanzu aka fara kuma zaa cigaba da gabatar dashi a duk lokacin dana so kuma babu wanda ya isa ya hana hakan faruwa ko acikin kamfanin ko kuma a wajen kamfani "amman kasan wannan cin amana ne , ya kake son muyi damu kasuwanci ?abinda baka son a fad'a ne kuma sai an fad'a wannan maryama itace ta tsara komai kuma wallahi bazamu ta'ba d’aukar hakan ba cewar baba qarami zan tabbatar dana dauki mataki akan wannan tsarin naka idan ba haka ba komai zai iya faruwa .”
“Enough please!” kada wanda ya sake sako sunna maryama cikin matsalar nan dan bata da hannu ciki mami ta sauke numfashi kawai tana dubansa wato har laifinta baya so lallai akwai wata a qasan zuciyarsa ? "babu ruwanta amman me yasa kake side din yarinyar ?cewar baba qarami sabod nasan bata da hannu ciki idan zakuga laifin kowa kuga laifina domin nine na shirya komai kuma nine na kawosu gidan nan sannaan akan kamfani naji komai zaku ce amman anemi a wulakanta maryama wannnan ne kuma bazan dauka ba”gabad’ayansu idanun suka zuma masa sultan yafi kowa shiga tashin hankali domin qarara yake hangon soyayyarta atattare dashi "babu ruwan maryama aciki wannnan plan din ni nan na tsara komai ku fita harkar ta kar wanda yayi qoqarin shiga rayuwarta “yana gama fadar hk ta wuce ya barsu Adam !!! Har sau uku baba qarami ya kirasa amman bai tsaya ba ya haye samansa da sauri .”
Mmn Sudais
[8/31, 11:25 AM] Safwan Libiya 2: 💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
BOOK 3
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.