Maradams Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: MAR ADAMS BOOK 3 COMPLETE BY AYSHA BAGUDU.txt
Chapter 5 of 29
Page 65
Numfashi ya sauke ya koma ya samu guri ya zauna a kan kujera yana jujjuya jikinsa gabansa na wani irin bugawa da karfin gaske haka nan yake jin zuciyarsa na matukar jin tsoron abinda zai faru yayinda a hankali maganganunta na jiya da sukai waya da some ya dinga dawo masa daki daki " na tsaya naji nayi miki me ?me ma kuka d'aukeni shasha wacce bata san ciwon kanta ba ?"kunsan zaku bukaceni me yasa kuka wulakan tani?"ya runtse idanunshi gam yana jin matsamanancin tashin hankali "wannan yarinyar fa da gani rigimammeya ce ."ya furta a fili qirjinsa na lugud'en bugu alokacin da maganarta ta sake yi masa kuwa acikin kunnuwansa da zuciyarsa ".sorry for what?, wallahi ko duk duniya za'a bani a wannan kamfanin babu ni babu wannan kamfanin har abada "shi wannan mutumin a wajenki yake da mahimanci amman a wurin maryama zero ne ,dan haka tun wuri ku nemi wata amman ni har abada bazan sake dawowa AGC company ba ".
Wani irin zufa ne ya shiga tsatsafo masa akan hancinsa da ilahirin jikinsa ,ahankali ya kai hannu ya lalubo wayarsa ya soma binciken unguwar da take domin dai yana bukatar yaga yanayin tsarin unguwarsu "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ya furta a fili yana mai sake tsurawa wayarsa do tagumi yayi da hannu d'aya yana tunani irin rayuwar da mutun zai yi a irin wannan bazar unguwar numfashi ya janyo da kyar ya sauke sannan ya soma neman layin mb yana d'agawa yace "kazo yanzu yanzu ina AGC yana gama fad'ar haka yayi discounting din kiran ya kira salim da ammar."yayi baya da kujerar da yake zaune yana ciza lip's dinsa da qarfi babu abinda yake gani acikin kwayar idanunshi sai kyakkyawar fuskarta mai mugun kyaun gaske da yanayin jikinta tana rayuwa acikin unguwarsu imagenation dinta kawai yake tun daga qarancin shekarunta har zuwa sanda ya fara daura kwayar idanunshi akanta ,yanayin tsayinta da dogon hancinta shine yafi komai fito da ainihin sahihin kyawunta da Allah yayi mata ya numfasa yana sake lumshe tsumammun idanunshi "hakika maryama iyayenki sun iya haihuwa tunda suka haifa muradin zuciyar Adam .”yana cikin wannan halin sai gasu ammar sun bayyana a gabansa ."
SALIM ,AMMAR ,M.B duk suka zuba masa idanu suna kallonsa fuskarsa a sukwane kuma d'aure take kamar ko wani lokaci sai dai kallo d'aya sukai masa suka fahimci akwai abinda ke damunsa duk suka samu gurin suka zauna sukai shiru suna jiran suji abinda zai fad'a masu."ahankali ATA ya lumshe tsumammun idanunshi tare da sanya hannunsa d'aya adaidai saitin qirjinsa yana murza daidai inda zuciyarsa take beating very fast bayan kamar second goma ya ware tsumammun idanunshi sosai akansu yana kokawa da lamarin princess dinsa saka makon matsayinta daya fahimta domin duk a tunaninsa bai d'auka zata fito daga irin area daaka fad'a masa ba ,ya d'auka zai ganta acikin royal family ne ko wani babban attajirin ne mahaifinta sai a yanzu ne ma ya fahimci bayan mugun abinda take rufe fuskarta dashi har da ma unguwar da take rayuwa aciki ya janyo rashin had'uwarsu .wani abu ya had'iye mai d'aci daya tsaya masa a mak'oshinsa kafin ahankali ya mike tsaye ya tsaya ajikin bangon office din tare da tura hannuwansa duka cikin ajihun wondonsa ya tokare qafarsa d'aya da bango yana cigaba da dubansu kamar zai yi kuka cikin kasa da murya ammar yace "Adam ya'akayi ne ?ka taso mu daga kan ayyuka masu mahimanci meke faruwa ?meye dalilin taramu dakayi ?ammar yayi masa tamvayoyin a jere duk da jikinsa ya bashi akan maryama ne dan idan akan kasuwancinsu ne bai zai nemi har da mb ba dan meye had'in soja da kasuwanci ."
"kasani ammar! "ata ya fad'a yana kokawa acikin ranshi "kasan dalili kiranku ammar amman kafin nan nasa some ta kira yarinyar nan jiya amman gabad'aya kalamanta sun nuna bazatayi aiki dani ba, amman ni ba wannan bane damwta ." meye damuwarka ata ?"mb ya tambayesa cike da kulawa "sai da ata ya sauke wani naunayen ajiyar zuciya sannan ya motsa lip's dinsa "wai princess dinace tayi rayuwa a irin wannan banzar unguwar ."yayi maganar cike da tsananin fushi yana zare hannuwansa daga cikin aljihunsa yayi taku d'aya biyu sannan ya tsaya cak atsakiyar office din tare da juya masu baya "gyaran murya salim yayi kana ya fara magana cike da sanyin murya "to meye aciki Adam kowani bawa ai da irin tasa kalar qaddarar "a ina take zaune ne ammar ?"inji cewar mb yayi tmbyr yana duban fuskar ammar ". "tana zaune ne a unguwar gwagulori "ina ne haka kuma ?""wata geto area ce acikin agege local government "cewar ammar "kunji abinda naji kuwa acikin zuciyata kamar ni Adam tariq Abdallah ace matar da nake haukar so ce tayi rayuwa a irin wannan banzar unguwa wani irin rayuwa ma tayi ?"gidansu ne ko haya suke yi ? Ata yayi masa tamvayar yana dungule hannunsa ya kaiwa bango naushi .da mamaki gabad'ayansu suka mike tsaye cikin tsananin tashin hankali suka qaraso inda yake suka rikesa suna kiran sunansa "what's wrong with you Adam ?" gabad'aya suka had'a baki wajen fad'ar haka."ka natsu mana ."
Shiru yayi kawai yana fesar da numfashi da iska mai zafi daga bakinsa gbdy yanayinsa ya canza zuwa na tsananin damuwa, fixge hannunsa yayi yana shafa daidai qashin hannunsa daya bugu yana watsa ma ammar wani mugun kallo .da sauri ammar ya d'auke idonsa saboda mugun tsoro daya kamasa ya koma ya zauna ."mb ya kallesa cike da tausayawa domin dai ya fahimci tausayi ne mai tattare da tsananin son da yake mata yasa shi shiga damuwa janyosa yayi ya zaunar dashi yana cewa "ka kwantar da hankalinka Adam haka rayuwa take kai a tunaninka zata zamanto diyar wani kamar yadda ka kasance to shi Allah ba haka yake son ganinta ba sannan ba hk tsarinsa yake ba ,ganin damarsa ne ya hada masoya masu wadata waje d'aya haka ganin damarsa ne ya hada talaka da mai arziki ." nasan kasan dukkanin rayuwa rubutaccen lamari ne daga rabbi yadda yaso haka zai yi ,saboda haka kasan duk wannan mai sauki ne a wajen Allah fatan mu yarinyar ta amince da soyayyarka tun da ka rigada ka gano Inda take .”
shiru ata yayi ya fad'a kogin tunani sosai hankalinsa ya bar duniyar da yake ya lula dashi can duniyar maryama inda zuciyarsa ta shiga hasko masa ita tare da wani tana rayuwar aure daahi . wani dogon tsaki yaja yana sake taune gefen bakinsa da qarfi saboda zafin kishin da yake ji hakika idan yace yaji dadin kasancewarta a bazawara yayi wa kanshi karya yaso ace shine mutun na farko da zai fara muamula ta aure daita bawani katon bazan can ba "Adam ka daina zurfafa tunani da yawa akanta tunda already kasan ta ta'ba aure ,tunda ta ta'ba aure kasan dole wani abu zai shiga tsakaninta da wanda ta aura ita kad'anta kake so kuma ko a wani hali take zaka kasance daita ." "jin an dafa kafad'ansa yasanyashi sauke kwayar idanunshi akansu "ba shiga damuwa ko dogon tunanin zaka tsaya ba abinda ya kamata kayi yanzu ka gaugauta aurenta domin ka inganta rayuwata kayi ma iyayenta duk abinda kasan ya dace ."inji cewar mb "Allah kad'ai yasan irin rayuwar datayi acikin wannan banzar unguwar mb ku duba map kuga yanayin tsarin unguwar datai rayuwa aciki inna ilaihi "ya sake furtawa yana yarfe hannu alamun abun na masa ciwo ".kai yanzu meye damuwarka da unguwarsu ? unguwarsu kake so ko ita ?"salim ya tambayesa wani kallo yayi masa yana fesar da huci yana sauke ajiyar zuciya da sauri da sauri." rabu dashi salim dan ma bai shiga lungun unguwarsu bane yasa yake fad'ar haka ."wani sabon zufa ne ya karyowa ata yayinda salim ya barke da wata irin dariya yana cewa "ai daidai kenan kamuwa da soyayyar yar talakawa zai sa wasu abubuwa su..."wani mugun kallo ata ya watsa masa wanda yasa salim yayi shiru yana kunshe sauran dariyarsa "ba hararar mutane ya kamata kayi ba kayi maza kayi abinda ya dace ku fahimci juna da yarinya ka aureta kafin wani yazo yayi maka shigar sauri "wannan duk ba matsala bane zan yi duk yadda zanyi ta dawo karkashin ikona . "fatan nasara abokina sun dan jima suna tautau nawa kafin daga baya kowannensu yayi masa sallama ya wuce suna fita yasa a kira masa baba gali "
*******
Cikin sauri sauri maryama ta fito daga bangarensu tana wa Aunty sallama kai tsaye part din umma ta shiga domin tayi mata sallama ta saka mata albarka tana rungumeta ajikinta "fatan alkhairi diyata "na gode umman ,maryama tai murmushi ta qarasa gurin hjy granny " Kiyi min addua kakata "allah ya tsareki maryama allah yasa zaki fara wannan aikin a saa sosai sukai mata addua ta soma kokarin barin parlour'n suna tsaye suna kallon bayanta suna rakata da addaua ."tana daf da kaiwa bakin kofa sai ga sallamar baba gali da aunty hassana tana ganinsu tai saurin durkusawa har kasa ta gaishesu"baba ina kwana aunty hassana ina kwana ? bata gama rufe bakinta ba sai ga mahaifiyarta itama ta shigo adaidai lokacin da yake amsa mata da "lafiya! Atakaice yana qare mata kallonta tare da cewa ina zuwa haka ?zani aiki ne ta bashi amsa jiki a sanyaye."what !? ya furta da karfi ai kuwa gara dana daka sammako ai wannna aikin baza kiyishi ba saboda ke na shigo bangaren nan .a matukar tsorace maryama tabishi da kallo kafin daga baya kalmar "inna ilaihi wa inna ilaihi rajiun ya dinga fitowa daga cikin bakinta tana maimaitawa nan take jikinta yayi sanyi." "ungu nan ki karanta, emvelop ya mika mata tasa hannu ta karba jikinta na cigaba da rawa a firgice ta dinga bin rubutun sako ne daga AGC compaing wani sabon tashin hankali ta sake shiga mai tsanani tana dafe goshinta ."
"ki karanta a fili so that kowa da kowa yaji babu yadda ta iya ta soma karanta sakon a fili jikinta na wani rawa gabadayansu shiru sukai suna sauraronta zufa ne ya karyo mata sakamakon anyi cancelling sabon aikin data samu sakamakon AGC compaing na bukatarta sai kuma kamfanin gidan burodi wanda yake mallakin umma shima zai tashi domin zaa hana duk wani kamfani dake sarrafa flour bashi kaya jikinta ya cigaba da rawa kafafunta suka kasa daukarta ta sauke takadar tana furta "umma ki rikeni "! da sauri duk suka yi kanta banda mutun biyu baba gali da Aunty hasana "kasancewarki a AGC compaing shi zai sa kasuwancinmu ya cigaba da tafiya akasin haka kuwa kema kinsani sai dai a rufe kanfani mu zauna haka ya qarasa mgnr yana karbar takarda da ya bata ya kalli umma ya kamata kiyi wa wannna yarinyar magana idan ba haka ba zamu rasa komai ."
"Ai wannna galaliyar zataso haka ni ban ta'ba ganin mai kashin tsiya ba irin maryama daga wannan bala'i sai wannnan Ke dai ina ganin babu kashin arziki ajinin jikinki ni wallahi da ma aikin kika rasa gabadaya muka tsira da kafaninmu da zai fi min dadi yar bantar uba mai kashin tsiya ta daga hannu zata kai mata duka.."dakata hasana karki fara cak ta tsaya ."wai bana ce miki karki kara sa bakinki acikin maganr maryama ba muddin dai ba alkhairi zaki fad'a ba cewar granny , duk wani abu da zaa samu kasuwancinmu mutuncin zamu duba wannna kamfanin da suka mata wulakanci ko bashi bane duk suka gyada mata kai "to bazatai aiki dashi ba gara ta sake fita neman wani aiki sanyayye ajiyar zuciya ta sauke ta rarafo ta rike kafafuwan granny tana zubar da hawaye aunty ma kuka take dan baba gali ne ya kirata banci haka da bazata zo taga bacin rai ba "na gode granny dan allah ki taimakeni bana qaunar wannnna kamfanin ."hajiya wai me kke fad'a ne haka da babu dadin ji kin kuwa san adadin amfanin da wannna kamfanin yake mana ?gabdaya idan aka rufeshi to zamu dawo bara ne a bakin titi tayi aiki da AGC compaing mu kuma mu cigaba da kasuwancinmu ".
"Gali kayi hakuri da hukunci hjy ai rayuwar kunci ko da wannna kafanin ko babu idan allah ya ga dama sai yajefa rayuwarka ciki ,amman maryama bata sake komawa wannna kamfanin daaka wulakantata ba ,"maryama ta tsurawa umma idanunta daga ganin yadda take magana kawai dauriya ce da sadaukar da farincikta saboda nata farinciki zamu iya cigaba da rayuwa haka amman wulakanci bazamu dauka ba maryama maza tashi ki koma daki bama zakije koina ba ,"karki damu kinji " baba gali ya bita da kallo."maza taso diyata ta d'agata da kyar tana goge mata hawaye "kama hanya ki koma daki kina zaune wani aiki zaizo ai ke mai saa ce in sha allahu zaki samu wani ."Ahankali ta dinga daga kafafunta ta nufi kofar dakin d umma sai dai ta tsaya jiki a matukar sanyaye ta kasa cigaba da tafiya tana tunanin abinda yake faruwa daita daki daki komai yake dawo mata qirjinta ya buga lokacin data tuna maganr grany da umma hawaye masu zafi suka zubo mata "ni yanzu me ya ka mata nayi hakika idan nayiwa umma haka ban kyuata mata ba na zama silar rabata da abinda ta dogara dashi da kuwa na tabbata mai kashin tsiya idan ma akwai abinda yafishi zaa iya kiranta dashi dan dole nasan abun amman bazai yuwu nayi silar rugujewar kamfanin umma ba ko babu komai umma ta wuce haka a wurina."can kuma maganrsu sectry dinsa ce ta shiga yawo acikin brain dinta ta sake runtse idanunta babu abinda bata tuna ba amman karshe taji bazata iyawa umma haka ba ko ranta tace tana so zata bata bare yin aiki da AGC compaing babu abinda ya kamata tayi daya wuce tai joing din AGC compaing.
Dawowa tayi ta durkusa gaban umma "kiyi hakuri umma ki amince min zanyi aiki da AGC " wani sanyayyar ajiyar zuciya aunty ta sauke tana hamdala acikin ranta "ko kefa maryama sai yau nasan kinsan meye hallici kuma tabbas ke yar halace,karki bari mu rasa kamfaninmu da mukai tsawon shekaru muna amfana dashi "to baba na amince ka fad'a masu zanyi aiki dasu "a'a maryama bafa zan yarda a dinga tozarta min Ke ba dan haka kiyi zamanki da rayuwa da mutuwa duk na Allah ne ko da kamfani ko babu zamu rayu "dan allah umma wallahi zan jure koma menene ni dai kawai Kiyi min addua umma tayi shiru ta rarrafa ta koma gaban grany "dan allah kiyiwa umma magana ta amince min tunda su suka nemi ne nasan bazasu tozartani ba kai ni akan martabar gidanmu babu abinda bazanyi ba idan yau mr ata rayuwata yake bukata zan iya bashi akan mu rasa kamfaninmu tana gama fad'ar haka ta sake dawowa gaban umma tana kuka tana rokonta amman umma tayi shiru tare da had'e rai "dan allah aunty kisa baki umma ta amince da kyar granny da aunty sukasa umma ta amince tare da mata fatan alkhairi."
Ahankali ata yake tafiya cikin shiga ta black suit hannusa daya cikin wondonsa yayinda James Ke biye dashi abaya rike da bakar jaka james yayi saurin shan gabansa ya bude masa glass door alokacin marayama na tsaye a office tare da sectary some suna magana akan yadda tautaunawarsu ta kasance akan waya a wancan rabar tare da neman afuwarta yana shigowa sectary tayi saurin gaishesa tana cewa "ga maryama hussein nan sir ."ya tsya cak tare da dan waigowa ya kalleta wani sanyi dadi yaji ya ziyarci jijiya da gangar jikinsa a natse ya juyo gabadayansa ya tsura mata ido itama a natse ta dago fararen idanunta ta tsura masa babu wani alamun tsoronsa atattare daita sai dai take taji qirjinta yayi wani irin bugawa da matsanancin karfi kallon juna suke ido cikin ido tana tuna haduwarsu ta farko duk da lokacin idanunta a rufe suke cikin nikaf shima rayuwar da sukayi a mafarki ne ya shiga dawo masa daki daki ,wanka da yake mata lokacin tana yarinya, wasa daita har zuwa girmanta da komai ya gama bayyana ajikjta da yanayin da yake ta'ba komai na jikinta tare da amincewarta yadda take sarrafa shi duk wani abinda Ke faruwa a tsakninsa daita acikin mafarkinsa babu wanda bai zo masa ba alokacin ."
a natse komai ya cigaba dawo masa boyayyayen ajiyar zuciya ya sauke sam ya manta james da sectary da suke tsaye sun kasa dauke idanu daga kallon juna ko kifta idanu basayi yaji kamar ya janyota jikinsa ya rungumeta yaji dumin jikinta na zahiri amman isa da jin kai bazai barsa ya aikata hakan ba ita kallon mamaki take masa mai ma yasa ya nace lallai sai tayi aiki à karkashinsa byn shine da kansa yasa aka koreta ? "shi kuwa kallon so yake mata yarinyar daya dade yana mutuwar so yarinyar daya dade yana marmarin haduwa daita ,yarinyar da yake muradin ta zamo mallakinsa itace tsaye agabansa a zahiri yana kallonta ba a mafarki ba ."
Bai ce dasu komai ba yana nufi glass door na biyu wanda Ke tsakninsa da sectary dinsa .yana shiga office dinsa ya kasa zama ya daura duka hannayensa akan kujera yana jiran shigowarsu da sauri sectry tayi gaba maryama tabiyota abaya cike da sanyi jiki some tace "kiyi knowking kafin ki shiga batai mata mutsu ba dan gabadaya ta sadaukar da rayuwarta gara kawai tai hakuri tayi aiki karta zauna haka babu aiki sannan kuma babu aure dan bata ga mai qararren kwanan da zai aureta ba bugu da gari kamfanin su."
a hankali tai knowking tana cewa "ko zan iya shigowa ?"Yes ! ya fad'a idanunshi na kan kofar shigowa tun daga kasa ya dauki kallon halittar dayafi qauna akan komai "mamanki ta iya haihuwa maryama ya fad'a acikin ransa tsayawa tayi ta rungume hannuwanta abaya tana hura masa hanci dan kallon da yake mata ya fara damunta sauke hannuwansa yayi ya zuba cikin aljihunsa yana cigaba da tsareta da tsumammun idanubshi masu bugar da zuciya da gangar jiki .Ita kuwa hade rai tayi sosai dan ranta ya soma baci tare da aiyanata wani sabon salon wulakanci zai mata shi kuwa fuskarsa wani annurin murmushi ne kwance amman idan ba mugun kallon kayi masa ba bazaka fahimta ba ya hade rai sosai yana cewa "me kikyi anan ? tayi matukar mamakin jin tambayarsa sai data maimaita kalmar sannan tace "mr ATA ne ya bukacini"ta fad'a har lokacin fuskata a hade ."
Sai data hura masa hancinta sannan ta cigaba da magana "sunana maryama hussein bagoro wannan sabuwar ma'aikaciyar da kuka d'auaka na rana daya sannna kukayi out daita, yanzu kuma kuka sake dawo daita ku kace tazo tayi aiki daku bayan kunsa anyi cancelling aikin data samu tare da barazanar zaa dakatar da kamfaninmu ."ta qarasa maganr tana sake hura masa hanci kamar yadda take masa a mafarkinsa."gabadaya ya mamayeta da tsumammun idanushi yana kallon kyakkyawan lip's dinta da siririn dogon hancinta komai na jikinta daidai ya dan lumshe mata idanunshi saboda dadin muryarta kamr ya fashe da dariya dan ya fahimci ya mugun bata haushi korar da yayi mata amman da yake shin din asalin miskili ne wuceta yayi da sauri ya zauan Kan kujera yasa hannunsa daya yana shafa sajen fuskarsa, can ya dauki wani file yana dubawa batare daya ce mata komai ba har tsawon mintuna shabiyar sannan ya ce "zaki iya tafiya yanzu nayi busy ."ta sake Shaka matuka mutumin nan fa mugun dan rainin hankali ne amman wallahi babu inda zata sai ta amayar da duk abinda Ke ranta ta sake gyara tsayuwa "nasan saboda kwarewata yasa kuka sake nemana domin dai bazaku ta'ba samu wacce zata baku abinda kuke buqa....."shhii karki wani cika wa mutane baki anan dan har yanzu baki da wannan matakin kwarewar , idan kika ga na wasu zaki sha mamaki da kanki zaki kira kanki da miss zero ".
"oh !
"gaskiya ne kam shiysa naga kun bukaci na dawo nayi aiki anan ? ya rufe file din hannusa da sauri yana kallon qaramin bakinta da magan Ke fitowa ta ciki ,kwata kwata babu wani alamar tsoro ko fargaba irin wanda yake hangowa a fuskar mutane dake aiki akarkashinsa idan suna tare dashi ."ni wallahi da an sani an barni alico insurance dina nayi aikina dan ma yafi kwanta min arai ."tayi mgnr tana rausayar masa da kwayar idanunta ."tsaki yaja yana motsa lip's dinsa "kisani duk inda zakije da sunan Kiyi aiki bazai ta'ba kai nan ba saboda aiki a AGC compaing ba qaramin abun alfahari bane ..."kayi kuskuren fad'ar hk sir ." ya ware tsumammun idanunshi sosai yana dubanta da mamaki kwamce a fuskarsa "eh haka na fad'a kayi kuskure sir kawai da dai da kun barni acan kawai batare da kun nuna karfin iko ba bare kace me ?mema kace ? "aiki a AGC compaing ba qaramin abun alfahari bane ."?"to a wurin wasu kenan yake abun alfahari amman ni dai abinda nayi imani dashi ko wani kamfanin na samu aiki zanji dadinsa sannna zanyi alfahari dashi kuma zanyi masu aiki mai kyau ." kun tursasa mutun yazo yayi aiki daku yanzu kuma kazo kace kayi busy dawa kenan kayi busy kai kai waye ma kai tukun ?ta fad'a a fusace .."
Mmn sudais
[8/31, 11:24 AM] Safwan Libiya 2: 💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
BOOK 3
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 6
sai da gabansa yayi wani mummunar fad'uwa, zuciyarsa ke qoqarin motsawa amman ya dinga kwantar daita dan idan ya bari maganganunta sukai tasiri zai yi daya sani dan haka yayi shiru kawai ya cigaba da kallonta ba dan ya rasa abun yi ba she's the most beautiful girl I have ever seen in my life ya fad'a acikin zuciyarsa yayinda fuskar maryama ke cikin wani yanayi na fushi sai dai kuma kwayar idanunta na kanshi ta tsura masa idanunta kamar yadda yayi mata muryarta a sanyaye ta cigaba da motsa lip's dinta "kana tunanin dan zanyi aiki daku zan d'auki wannan wulakanci ne ?no I can't take it any more ta fad'a tare da zaro masa fararen idanunta ,da wani irin sauri ya tashi daga kan kujerarsa yana cewa" yana da matukar mahimanci kisan wani abu , yana da kyau kisan cewa kinyi mistake arayuwarki ba wai wulakanci bane kmr yadda kika d'auka, har sau biyu kina samu aiki damu kina rejecting wacece ke da zakiyi rejecting din aiki alokacin da kika só sannan ki so aiki alokacin da
kika so "yayi mgnr yana kallon cikin kwayar idanunta ."
Ahankali ta kawar da kanta zuwa gefe tana hura hanci tace "to kuma saboda banyi joining aiki daku ba alokacin da kuka so sai ya zama matsala ? wani irin kallo yayi mata mai tattare da gargadi sannna yasa hannusa d'aya cikin aljihunsa yana kallonta yana jin wani azababben qaunarta na bin jinin jikinsa ahankali ya dinga sauke numfashi kamar wanda yayi gudun tsare sannan yaja tsaki ya kai hannu sumar kanshi ya shiga ya mutsawa yana ciza gefen lips dinsa da d'an karfi "ya Allah karka sa yarinyar nan ta bani matsala "yayi mgnr a kasan ransa still yana cigaba da kallonta ." kusan mintuna goma ya d'auka yana kallonta sannna ya koma ya zauna yana sauke numfashi ya sake d'aukar wani file ya cigaba dubawa sakamakon rashin abunyi "kawai kuce kun nemi na dawo ne saboda kunsan ina da baiwar fikira da zaku amfana dashi well shikenan kawai sai ku rubuta ku ajiye ya zama tarihi ga AGC compaing ,sun ga maryam hussein na da baiwar fikira sun dawo daita aiki byn sun koreta a ranar farko ."yana jinta amman yayi mata banza yayi tamkar bai ji abinda ta fad'a ba haka kuma bai d'ago ya kalleta ba ya cigaba da abinda yake yana satar kallonta ta kasan ido yana danne bugun zuciyarsa dan wani irin sabon yanayi ya dinga jin yana shigarsa."
yayinda maryama tayita fad'ar maganganu son ranta wannan karon kam a matukar zuciye ya ajiye file din da yake rike dashi ya sake tashi ya tsaya cak a gabanta yana sauke numfashi har suna iya shakar numfashi juna da jin bugun zuciyoyinsu "Keep your mouth shut ki kama kanki kisan irin maganar da zakiyi anan dan ba'a kawo min raini , ba'a sakani kuma ba'a hanani and no body question me okay ."ya fad'a a matukar tsawace yana sanya kwayar idanunshi cikin nata, shi aiki da mahimanci ake d'aukarsa kamar yadda shi mai kasuwanci yake d'aukar kasuwancinsa ,ban dawo dake dan kizo kina min haukan banza anan ba, na koreki ne saboda na nuna miki kuskurenki, sannna na dawo dake ne saboda tausayawa domin na fahimci kin shiga tashin hankali mai tsanani a wancan ranar dana koreki idan zaki iya aiki damu kiyi idan kuma bazaki ba "leave!ya nuna mata hanyar waje da d'an yatsansa yana fesar da huci mai zafi daga bakinsa yayinda zuciyarsa ke cike da matsanancin fargaba dan yasan kad'an da aikinta zata iya juyawa ta kama gabanta ."
adduar ya shiga yi domin neman taimakon Allah" ya Allah kada kasa zantuttukana suyi tasiri a zuciyarta Allah kasani ina matukar son yarinyar nan da d'aukacin rayuwata ta shiga zuciyata dayawa ta sace zuciyata,ya Allah kasa na shiga cikin rayuwarta kamar yadda ka shigo daita cikin rayuwata domin ta zamo abokiyar rayuwata ta har abada ina matukar qaunar wannan halitta taka ya Allah ka jarabeta da soyayyata tun kafin na kai ga furta mata soyayyarta dake raina domin na azabtu akanta ,na sha wahala akanta ,ya Allah ka tausaya min ."Ita kuwa maryama shiru tayi na second goma tana dubansa batare da tace masa komai ba har ya gama maganarsa sai dai maganarsa tasa zuciyarta tayi sanyi daga zafin datayi tare da tunani ,duk da ya jefeta da kalmar hauka amman kuma ta wani bangaren sai taji kamar ya fita gsky domin kuwa a wannan zamani aiki wahala yake, idan ba kana da hanyar samunsa ba ko wata baiwa ba sai dai ka mutu haka babu aiki amman da kwalinka da karatunka sai su zama banza bazasu maka amfani ba ."dan haka Ke maryama kiyi maza maza ki shiga taitayinki ki dawo cikin hankalinki karki yarda Kiyi kuskuren da zaki sake rasa aikin nan dan haka muryarta a sanyaye tace "shikenan zanyi aiki da amana da gasky kuma in sha allahu kamfaninku zatai alfahari da ... "da kyau go back to work ." yayi sauri katseta ta hanyar fad'ar hk batare daya kalleta ba duk da kallon nata yake da bukata dan baya gajiya da kallonta amman ya kasa sai ma boyayyayen ajiyar zuciya ya sauke dan maganrta ba qaramin dadi sukai masa ba ."
"Yanzu ko zan iya sanin da me zan fara ?meet sectary "ya fad'a a dake ,ta juya jikin a sanyaye har ta kama handle zata bud'e kofa ya tsaidaita ta hanyar cewa "ke .." ta tsaya cak batare data juyo ba sai dai qirjinta na wani irin bugawa da sauri sauri "idan zaki zo aiki gobe karki kuskure kizo min da wannan package din, kizo cikin tsari shigar aiki Kmr kowani ma'aikaci ."da sauri ta juyo tana masa kallon tsana zuciyarta cike da mamaki to mai ya samu kayanta ?ta jefawa kanta tambaya tana dubansa bai kalleta ba sai dai ta kasan idanunshi yake d'aukar kallonta tana kallonsa ya janyo system gabansa ya cigaba da aiki ta bud'e kofa ta mayar da karfi ji kake kiiiiii har sai daya d'ago yana duban kofar kai kawai ya girgiza tare da furta cray girl kawai ."maryama ta fice tana jan tsaki ranta duk babu dadi "a hankali ta dinga tunanin maganga nunsa gabadaya maganarsa babu dadi sai bugar da zuciya da saka mutun cikin tashin hankali ta sake jan tsaki tana maimaita kalmarsa ta karshe "idan zaki zo aiki gobe karki kuskure kizo min da wannan package din, kizo cikin tsari Kmr kowani ma'aikaci har ta shiga babban office din daaka tanada masu a ranar farko maganarsa bata bar zuciyarta da gangar jikknta sun huta ba ."
anan taga yusura tana ganinta ta qaraso da sauri ta rungume maryama tana cewa "kai naji dadi kawata da kika sake dawowa amman fa Kiyi hattara da mr ATA da mr sultan dan ba kai garesu ba kowa anan tsoronsu yake ji ,suna cikin mgn sultana ta shigo tana cewa "maryam hussein sannu da dawowa compaing mu " wani kallo mryma tayi mata na mamaki fuskarta da alamun tmby "yes ! Ok fa a she bakisani ba ko, to bari na fadi miki wannan kamfanin had'in gwiwar iyayenmu ne ni cousing sister din Mr ATA ce nan maryama ta fahimceta sai dai bata ce mata uhmm bare uhmm uhm .""Kinyi sa'a da kika dawo wannan kamfanin amman kuma Kisani nice nan sanadin dawowarki domin nice na nunawa ya Adam zanenki da kikayi wanda tashin hankali an koreki yasa kika tafi kika barshi "shiru maryama tayi kafin a hankali tace "na gode excuse"ta fad'a sannan ta ra'ba ta gefenta ta wuce ."
Gabdaya suka samu guri suka zauna akan makeken table din dake zagaye da office din ."maryama ta bud'e jakar kayan aikinta ta d'auko abun aikinta hanakalinta kwance ta fara gudanar da aikinta "wannna duk wahalar banza kikeyi domin duk kwarewarki bashi zai sa ki burge ya adam ba tana gama fadar haka fita daga office din maryama tabi bayanta da kallon mamaki ."
Aunty hasana ta qaraso ta mikawa hjy granny kofin shayi ta amsa tare da cewa "na gode ta kai cup bakinta sai dai da sauri ta kirata tana cewa " hasana bai kamata ina shan sugar haka ba amman kalli yadda kika zabga min sugar cikin tea ai ko baa fad'a miki ba Kinsan bai dace mai shekaruna haka ta sha sugar ba duk maganar da hjy granny take Aunty hasana bata jinta saboda hankalinta na kan kallon tv "ke hasana bada ke nake magana bane ta juyo a dan firgice tana cewa "na'am hjy kina magana ne ?ya zaki saka min sugar haka acikn shayi ?abun kunya kawai ace kamarki ace shayi ma sai anci gyaranki ba kya ganin yadda maryama take komai nata tana kokarin kula dani fiyye dake sam bata kuskure wajen abinda take min amman ke babu abinda kika iya sai aikin zagin ya'yan mutane da saka ido bazaki tsaya Kiyi koyi da mutanen kirki ba." zaginta tayi sosai ai kuwa haushi ya kamata "hjy ai daman ni na dade dasanin kin tsaneni bakya qaunata komai zaki fad'a ki fad'a ba damuwata bace" idan dai zaki canza ki canza umma ta shigo tana tmbyr lafiya hjy nake jin fad'anki "ina fa Lfy wannan yarinya ce anyi mgn zata fadawa mutane babu dadi me kike son nayi miki hjy ?" bansan me nayi mata ba komai nayi mata sai ta kushe to ki daina sakani aikin ki dinga saka wadan da kike so aranki ta fad'a hawaye na cika idanunta."
umma ta dafata tana cewa "haba hassana ki daina fadawa mahaifiyata magana haka sam bazan ji dadi ba bugu da qari Ke ma uwa ce idan yaranki suka miki bazaki ji dadi ba "to ni yanzu me nayi dag suga yayi yawa a tea sai ta hau min fad'a karbi tea ki sha kiji wallahi ba wani suga na saka ba "ki barta kawai itama ai ta haifa yaya idan ma bata haifa ba akwai na kasa daita zasu mata duk abinda tai min sam bata son gsky tunda take min rashin tarbiya kinji na ta'ba magana akai idan ba yau ba ?dan allah kiyi hakuri hajiya bazata sake ba suna cikin haka maryama ta shigo cike da murna ta tsaya kusa da umma tana cewa "umma ki tayani murna na fara aiki ." umma
tai murmushi cike da farinciki Allah yasa kin fara kenan "Ameen ya allah na gode sosai babu wata matsala dai ko ?babu matsalar komai umma duk da dai mr ata ya dan so yayi min hauka amman nayi hakuri .zanyi aiki dashi ne kawai saboda bazan iya bari wani abu ya samu komai naki ba faduwar ki faduwar gabadayanmu ne ."shiru umma tayi kafin tasa hannunta ta kamo maryama karki ce komai umma duk abinda nasan zakiyi farinciki zanyi shi koda kuwa raina ne zan iya mallaka miki shi umma ta lumshe mata ido tana cewa " na gode sosai maryam allah yasa albarka hatta hjy ma taji dadi suka saka a tsakiyarsu suna saka mata albarka ."
*******
Baba qarami yana zaune a cikin wani qaramin office dake cikin falon hjy zulai an tanadi office din ne saboda marigayi alhaji tariq alokacin da yake raye nan ne wurin zamansa ATA ya sauko daga samansa sanye cikin wasu hadaddun kananan kaya marasa nauyi kallo daya yayi masa ya d'auke kansa zai nufi kofar fita yaji sautin muryarsa "Adam zo nan ya tsaya Jim da kamar bazai je din ba sai kuma ya yi wani tunani ya juyo a hankali ya shiga har inda yake zaune fuskarsa a hade kamar ko yaushe "ka zauna saboda me kenan zan zauna? ya tamvayesa atakaice yana hura hanci baba qarami yayi shiru yana dubansa "kana da magana ne ?zan kiraka ne idan bani da abinda zance ? ya fad'a a zafafe shiru ata yayi ."Ka natsu ka shiga hankalinka ba wai ana jin tsoronka bane me ake ciki akan maganar danayi maka akan sultana idan kaki auren hindu ka turata magarkama sultana fa uwarta na bukatar jin raayinka?babu wani abinda ake ciki dan bazan yi abinda Zanzo daga baya ina danasani ba sultuna is not my test ina da raayina haka ma hindu "da alamun zaka dawo da zabin mahaifiyarka ya zama shine raayinka .? a fusace yace "yes !"yana kallonsa
"ka koyi respect Adam sam baka da respect bakasan yadda ake magana da babba ba zaka iya fad'awa mahaifinka haka ? Ko da yake wannan uwar..."
"enough baba qarami ."! ya fada a tsawace karka sako sweetheart cikin maganarka aure ne ni nake da ikon aure and sultana she's not my tast abawa wani kawai "bari na fad'a maka wani abu komai zakayi wannan karon sai dai kayi amman sai ka auri wata daga cikin family's din nan bare kuma tunda sultana tace tana sonka an gama maga.." kafin ya qarasa mgnrsa tunin ata ya juya ya barshi "kai dawo nan !"ata ya sake dawowa hannuwansa duka cikin aljihu" "wai meye haka ne baba ?nifa nasan abinda zai yi daidai da rayuwata dan allah ka barni na huta bana bukatar wani auren zumunci arayuwata a yanzu shin lallai ne sai ni zaku bawa ya'yanku ."?
Mmn sudais[8/31, 11:24 AM] Safwan Libiya 2: 💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
BOOK 3
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.