Maradams Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: MAR ADAMS BOOK 3 COMPLETE BY AYSHA BAGUDU.txt
Chapter 20 of 29
Page 34
Zaune hajiya rahma take a gefen katifarta hannunta rike da hotuna wanda a 'yan shekarun nan a duk sanda zata ke'bance kanta to wad'an nan hototunan sune abun kallo agareta, wani lokaci yasata zubar da hawaye ,wani lokacin kuma tayi murmushi tare da nadamar zartar da hukuncinta akanta ,tayi shiru cikin tsananin tunanin wacce ke cikin hotunan kamar yadda ta saba ,ta dade zaune tana kallon hotunan tana sake zurfafa tunaninta da nadamar abinda ta aikata kafin ahankali ta fara zance a fili "Allah sarki bilkisu baiwar Allah mai tsananin hakuri da son mutane, mai tsananin kawaici ,Allah sarki diyata duk inda akaje sai anyi jimamin rashinki bilkisu mai tsananin son yan'u wanta har da ma wad'an da ba yan’uwanta ba ,bilkisu mai tausayi da amana ,nayi rashinki diyata Allah ka juyo min da hankalinta zuwa gareni.."nan kuka mai qarfi yaci karfinta "ai ko ta soma kuka sosai tana duban hotunanta "yau tsawon shekaru nawa kenan tana fama da abu d'aya?"kusan shekaru ashirin da wani abu kenan ,lokacin da abun yana sabo sabo bai dameta ba amman sai daga baya ta fahimci kusku renta,a kullum idan ta tuna sai ta tuna maganar hajiya safiyya aminiyarta,ta kance kiyi hakuri rahma ki rungumi qaddarar diyarki wata rana komai zai wuce .haka kullum take fad'a mata ,kuma baa wata shida bata kirata ba,tai ta rarrashinta tana bata baki amman duk tasa qafa ta shure maganarta .ta tuna shekaru goma da suka wuce mijinta alhaji rafi'u giwa tun yana jin zai iya hakura da lamarin bilkisu har yazo ya kasa yazo yana nuna a zahiri bazai iya rashin bilkisu ba ,har ma yace zai je ya nemi inda take amman tace masa a'a yayi hakuri ya d'aure yayi zamansa kar yaje zata dawo da qafafuwanta domin matsawar sukaje gareta tayi nasara akansu kuma taci bulus akan kuskurenta gara a barta idan ta sha wahala da kanta zata dawo ."
alokacin sai Allah yazo ya dora ma alhaji rafi'u giwa wani irin hakuri akan bilkisu ya cigaba tsabgoginsa da harkar kasuwancinsa da muamula da sauran ya'yansa ."sai gashi ita daga baya ta kasa hakuri tayi ta zuba ido yaushe ne bilkisunta zata zo ?"yaushe ne zata dawo garesu a tun shekarun goman nan gashi har an haura shekara ashirin bilkisu shiru tun tana ganin abun kamar film har sai da'aka d'auki wannan shekarun babu ita babu labarinta tasan cewar lallai bilkisu tayi fushi mai tsanani dasu kuma babu tabbas din zata dawo domin duk inda take a yanzu ta tsaya bisa qafafuwanta kuka take sosai," wannan ciwon na rashin bilkisu ciwo ne da kullum yake cin zuciyarta wanda take jin bazai ta'ba warkewa ba har qarshen rayuwarta ,tunda zuciyarta tayi nisa daita ta rasa wani bangaren na rayuwarta ."tana zaune tana kuka yaya mahmud ya shigo d'akin bakinsa d'auke da sallama ,ganin halin da take ciki ya bita da wani irin kallo kafin ahankali ya qaraso gareta jikinsa na d'aukar rawa ya durkusa agabanta ya kamo hannun ta cikin nashi babu abinda ya tsana kamar ganin hawayen iyayensa balle mahaifiyarsa da bai da kamarta a duniya kukanta har cikin zuciyarsa yake ji "mum kiyi hakuri ki daina kuka nan ki fad'a min damuwarki kafin tace wani abu tuni hotunan bilkisu guda uku dake rike a hannunta suka zubo."
yabi hotunan da kallon mamaki yana jin wani iri acikin zuciyarsa dama gangar jikinsa nan take jikinsa yayi mugun sanyi domin kuwa ko bata fad'a masa damuwarta ba yasan kukan rashinta take yi nan take yaji da akwai yadda za'ayi ya dawo mata da bilkisunta da zai yi amman sun rigada sun ma kansu alqawari muddin ba itace ta dawo da qafafuwanta babu wanda zai taka zuwa gareta ,ya matso sosai kusa daita yasa kanshi akan cinyarta yana jin yadda zuciyarsa take ta fasa yana jin kamar sune silar kukan mahaifiyarsu ,yana jin duk laifinsu ne da suka taru suka had'a kai akan kin auren bilkisu ina ma sun sani sun amince a tun farko sun inganta rayuwar yaron da yanzu suna cikin walwala da farinciki ." nan take shima hawaye suka fara gudu akan kuncin soja aka rasa mai rarrashin wani acikinsu ."yaya mahmud yayi amfani da qarfin zuciya irin tasu ta sojoji ya cigaba da bata hakuri da rarrashinta "kiyi hakuri nasan bamu yi miki adalci da muka biyewa son zuciyarmu akan rayuwar bilkisu ba ,munyi nadamar abinda muka aikata agareta , kuma a yanzu a shirye muke da muje gareta, zamu dawo da yaruwarmu cikinmu mu cigaba da rayuwa ,mu had'u gabad'aya mu dinga faranta miki ."
wani sanyin dadi ne ya ziyarci zuciyar hajiya rahma dan ta dade tana mafarkin zuwan wannan ranar ta dade tana rokon allah yasa ya'yanta su fahimceta sosai yaya mahmud ya gyara kanshi akan cinyarta "ina mai sake baki hakuri ki yafe mana ko zamu samu sausauci abinda muka aikata, bai kamata mu biye miki alokacin da kika d'auki zafi akan bilkisu ba ,kamata yayi mu zamanto masu rarrashinki da baki hakuri tare da nasiha ki rungume qaddarar bilkisu amman sai muka zama mune gaba gaba gurin nuna isa da iko tare da jayayya da hukuncin ubangiji ,yau gashi bilkisu ta kar'bi qaddarata ta manta damu ta cigaba da rayuwarta cikin kaskanci batare data nemi mu ba bare ta nemi taimakonmu wanda mu abinda muka kudurta kenan aranmu tasha wahalar rayuwa ta wulakanta ta tozarta tasan amfaninmu sannan ta dawo garemu mu kuma mu samu damar nuna mata kuskurenta na za'bar wani ta barmu sai gashi tayi hakuri kuma ta jure duk wani tsanani ta cigaba da rayuwarta ta bar zukatan mu da tarin kewarta ."
ahankali hajiya rahma ta kai hannu tana shafa kanshi tace "kukan ya isa haka mahmud ni baku min laifin komai ba hassalima hukuncin da kuka zartar da yardata da kuma amincewata ne na yafe maku duniya da lahira ,ni dai ka nemi sauran yanuwanka kuyi magana a tsakaninku ina son ganin bilkisu kafin mutuwata, wallahi mahmud nayi nadamar abinda nayi ma bilkisu ku kawo min ita kafin mutuwata duk da nasan mijin data aura bai cancanta daita ba amman na hakura tunda qaddararta kenan ya d'ago kanshi yana kallonta kafin ya saka kafin ahankali yasa hannunshi ya rike kunnuwansa "I promise you mum in sha allahu very soon zamu kawo miki bilkisu har cikin d'akin nan ya qarasa maganar yana sakar mata murmushi itama murmu shi tayi tana jin wani dadi sanyi at the same time tana tunani aranta daman tasan addua bata faduwa kasa banza Allah mai amsa addua, ta godewa Allah da yasa mahmud ne ya fara fahimtarta domin shine yafi kowa zafin zuciya da d'aukar zafi tunda har ya sauko tasan saukowar sauran ma bazai yi wahala ba ."
Alhaji rafi'u yayi sallama ya shigo d'akin yana
kare musu kallo, yana ganin farin cikin a kwance a fuskar kowanensu wanda ya jima bai gani ba haka nan shima with a smile yana godewa Allah daya
bashi family d'inshi da kuma ya had'a masa kansu guri d'aya. yace. "ahhh ana mommy and son time ne haka ?" nima bari nazo ayi dani, shikenan sai ya zama daddy mommy and son time." dukansu suka kwashe masa da dariya cikin farincikin da kwanciyan hankali hajiya rahma ta kasa hakurin rike maganar
bakinta ,ta tashi taje ta rike hannun alhaji rafi'u tana murmushin jin dadi “dadynnmu albishirinka "dake wani lokacin haka take ce masa tamkar yadda yoroba kan kira mazajen aurensu " murmushi ya sake yi sannan yace "mumynmu goro "!ta kallesa tace kuma dole sai an bani tuk'uici" tana magana tana dariya yace momynsu "an gama amaryata ran gidana ,dadybmu mahmud yace very soon zai dawo mana da bilkisu cikin gidan nan very soon zamu ga bilkisu da yan jikokinmu " yadda take murna kamar karaman yarinya, shima alhji rafi'u ya biye mata sunata dariya suna magana tare da murna yaya mahmud kuwa kamar kasa ta bud'e ya nutse a cikinta haka yakeji dan haka ya yunkura ya tashi da sauri ya bar musu dakin yayinda alhji rafi'u da hajiya rahma suka cigaba da tautaunawa kuma duk akan bilkisu ."
*****
Bayan kwanaki bakwai din da mr ata yasa aka turawa nadiya sakon an dauketa aiki tazo domin interview ranar da kwanakin ya cika ya dauki maryama zuwa kamfaninsa na ATA dake cikin ikeja wani office dabam ya kai maryama yace ta zauna shi kuma ya shiga office dinsa ya zauna kusan awa uku da zuwansu inda ake ta faman yiwa sabbabin ma'aikata interview amman nadiya shiru babu ita babu alamunta nan hankalinsa ya fara tashi ya mike tsaye ya fara zariya yana kai kawo daga office dinsa zuwa office din da maryama take amman ita sam bata ma lura dashi ba ita kanta hankalinta naga babbar kofar shigowa ne yayinda pencil ne a bakinta tana cizawa tana tunanin nadiya akaro na karshe ne yana shigowa zuwa inda take ya fixge pencil din bakinta ta waigo a natse ta kallesa wanda shi daman kwayar idanunshi na kanta shiru sukayi suna kallon juna kafin ahankali ta motsa lip's dinta "so.."karki ce min wani sorry !”yayi saurin katseta ta hanyar cewa haka yana furza mata hucin numfashin bakinsa kafin ahankali yaja qaramin tsaki ya cigaba da magana"me yasa zaki dinga over thinking haka ?".
Maryama ta sauke numfashi cikin tsananin damuwa sannan ta mike tsaye ta tsaya kusa dashi "har yanzu ina mamakin nadiya da karfin halinta ne sannan ina mamakin abinda yasa ta bawa wani numberta ya kira akan nazo aiki da wuri anya kuwa babu cutarwa acikin lamarinta "wannan kuma ya rage naki da hankalinki da tunaninki baki ta'ba ganin mutun ba koda a hira shi wancan mataccen bai ta'ba baki labarinta ba amman ki bari ta shigo muku gida kuma har ki kaita d'akinsa yanzu idan ya zamo ta ajiye wani mugun abu acikin d'akin fa ?ko kuma akwai abinda ta shirya maki akan hanyar ki ta zuwa aiki yasa tasa aka kiraki kizo aiki da wuri ?duk hakan zai yuwu, ku duk wanda yazo maku da maganar masoyi sai kuyi saurin yarda dashi saboda gaku yan gani kashenin soyayya ."ya fad'a yana fesar da iska”.
"bare ni akan ya sadam kam idanuna sun rufe kuma ina saurin yarda da duk wanda yazo gareni da sunansa ko maganarsa ." tsaki yaja tare da yin shiru yana kallonta yana jin wani zafi aransa, ta kalli agogon hannunta "sir did you realize one thing ?" yana jinta kuma stil tsumammum idanunshi na kanta amman yayi mata banza "wallahi idan banga nadiya ba yau bazan ta'ba samun kwanciyar hankali ba har qarahen rayuwata duk rayuwar da zan gudanar acikin kunci zanyita "numfashi ya sauke kana ya lumshe tsumammun idanunshi yace "ina tabbatar miki sai kinsan gskyar da take boye miki dan rashin kwanciyar hankalinki zai iya shafar aikina ."na gode sosai sir !” ta fad'a adaidai lokacin da wani ma'aikaci ya shigo ya mika masa cup cike da girmamawa ya amsa ya kai cup din coffee bakinsa ".ya fara kurba ahankali ahankali.
Maryama ta dubesa a tsanake yana shan coffee yana lumlumshe idanunshi "bansa yadda zan misata maka farincikina ayau ba ina jin kamar ka bani komai dake cikin duniyar nan ne ,na gode na gode sosai sir "maryama waya fad'a miki ina yin duk wannna abun saboda ke ne ?ta kallesa a matukar tsorace gabanta na wani irin fad'uwa "yes ki daina kallona haka ni duk abinda nayi ina yi ne dan company dina ne kamar yadda na fad'a miki yanzu banason wani abu ya samu aikina idan ban yi abinda zuciyarki zata damu natsuwa ba kasuwancina zaiyi rauni sakamakon ina son na had'a miki aiki biyu a qarqashina .”ya qarasa maganar yana sake lumshe mata ido .tsaki taja a kasan ranta "wannna anyi mugun miskilin mutun mai shegen girman kan tsiya mai fuska biyu kawai sai ya nuna kmr ya damu da mutun sai kuma ya dawo ya bullo da wani salo ta fad'a a kasan ranta tana hura masa hanci ".
"me ki kace ?no..no..sir nothing “ki dawo da hankalinki jikinki wannan iskancin da kike babu abinda zai haddasa miki sai madness kizo ki rasa mai aurenki ,saboda sosai na fahimceki kina yawon magana da kanki , wallahi muddin baki daina ba zaki haukace irin haukan da ko ankai ki hospital kinfi karfinsu kinga kuwa bazasu amsheki ba ." yayi maganr tamkar bashi yayi ba yana cigaba da kurban coffee yana lumshe mata tsumammun idanusnhi ."
"me yasa zaka min irin wannan fatan sir ?ba fatan haka nake miki ba amman idan baki daina tunanin abinda ya faru baya ba , sannan baki daina magana da kanki ba zaki tsinci kanki cikin yanayin dana fad'a whatever you want to say ,say it out loud". ya fad'a a matukar tsawace ."
Ranta a 'bace ta juya masa baya tana magana da kanta "aikin banza kawai ko ina ruwan mutun dani ko.."again ? taji sautin muryarsa a bayanta "no sir zanyi magana a fili fili ."ya girgiza mata kai kawai ya koma ya zauna akan kujera yana juyi yana tunanin "taya zai aureta ma da wannan dottin tunanin damuwarta ?”ai dole ya wanke mata kwakwaluwarta fes kafin komai."maryama ta cigaba da tunani tana cigaba da duba kofar shigowa ko zata hango bullowar nadiya amman shiru lokaci nata tafiya har karfe uku ta wuce amman shiru babu ita babu alamunta ya taso daga kan kujerar da yake ya tsaya kusa daita ya tura hannuwansa cikin aljihun wondonsa batare daya ce mata komai ba "ina tunanin nadiya bazata zo yau ba "why do you said that ?"Ka duba lokaci ka gani sir , har karfe uku ta wuce wani mutun ne zai zo by this time akan aikinsa ?"kina ganin abu mai sauki ne mutun ya samu aiki a ATA company yaki zuwa?ni zuciyata ta tabbatar min da zata zo kuma nasan zata zo" allah yasa maryama ta fad'a muryarta a raunane ."
cikin haka wayarta ta d'auki ringing ta duba shima ya dan mika wuyansa yana duba screen din wayar sunan umma ya gani dan haka ya sauke numfashi ya juya ya koma cikin office dinsa "hello umma eh har yanzu ina office tukun akwai abinda muke yi ,aa karki damu in sha allahu zan dawo gida akan lokaci Eh komai yana tafiya daidai babu wata matsala sai na dawo tana gama wayar ta juya zuwa cikin office dinsa "sir !ya bar abinda yake ya tattara hankalinsa akanta tun kafin tace wani abu ya soma motsa lip's dinsa "is almost four :30 pm now har yanzu bata zo ba abinda zaa yi kije office din hisham ki jirani ."tayi shiru tana tunanin wani office kenan "office din karshe kafin muzo nan "okay sir har ta juya ta sake juyowa ta fuskancesa "kana ganin nadiya zatazo yau kuwa gashi ina ganin lokaci na Kure min banason naje gida bakwai ta wuce sir na gode sosai ni ban ta'ba tunanin zaka bata lokacinka akaina haka ba dan naji zuciyata ta yarda cewar dan i kayi haka ba dan wani kasuwancinka ba ,a halin yanzu babu wanda nake jin ya sake samun yarda da amincewa aciki zuciyata kamarka dan allah ka bari na cigaba da jin haka acikin zuciyata saboda naji dadin kulawarka sosai dan kana da kirki matuka , na gode maka sosai Allah ya jikan iyaye aransa yace “ameen! yayinda a zahiri "uhm!" ya fad'a yana tsareta da tsumammun idanunshi yana jin tamkar ya fixgota zuwa garesa .
Maryama ta sauke naunayen ajiyar zuciya sannan ta juya ta fita daga cikin office din zuwa wanda yace ta shiga ta jirasa ,tafiyarta dake rikitashi yabi da kallo tare da yin tagumi yana bin every step of her nan take yaji jijiyarsa ta harba ."
Mmn sudais
[8/31, 11:25 AM] Safwan Libiya 2: 💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
BOOK 3
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 35
Ahankali mr ata ya kai hannunsa kan jijiyarsa dake harbawa still yana sake tsurawa tafiyar maryma ido har sai daya ga alamun ta tura kofar office din hisham ta shiga sannan ya runtse tsumammun idanunshi ,gabad'aya yanayinsa ya sauya ,wani irin ajiyar zuciya mr ata ya dinga saukewa da qarfi kana ya bud'e idanunshi yana jin wani irin yanayi a sansar jikina. yayinda gabad'aya tsigar jikinsa suka mike ."ji yayi kamar ya tashi yabi bayanta ya janyota tare da sanyata ajikinsa ya rungumeta tsam ya d'an tsotsi bakinta ko ya d'an samu sausauci abinda yake ji akanta."akaro na biyu ya sake kai hannunsa yana shafa jijiyarsa da take mike sambal ,yana shafawa yana lumshe tsumammun idanunshi at the same time yana sauke numfashi "wayyo allah ina cutar da kaina over akan yarinyar nan ahalin nasan irin matsanancin qaunar da nake mata "I love you so much maryama ,sonki da qaunarki sun mamayeni ina matukar shan wahala akanki yayi maganar fili ."wani wahalallen numfashi ya sake saukewa tare da gyara zamansa yana tura gabad'aya lip's dinsa na qasa cikin bakinsa tare da rikesu da hakorinsa."
Ahankali mr ata ya soma qoqarin kawar da abinda yake ji akan maryama dan yayi imani idan bai yi haka ba komai zai iya faruwa a tsakaninsu ya janyo laptop gabansa ya soma duba sakonin da'akayita turo masa ."
maryama kuwa tana gama shiga office din hisham tabi office din da kallon tsanake komai tsaf tsaf gwanin burgewa ga wani qamshin turare mai sanyin dadi dake tashi acikin office din ,sosai office din ya had'u sai dai bai kai wanda mr ata yake zaune ciki ba .ta sauke numfashi da qarfi kana ta qarasa gaban makeken table din ta tsaya tare da rungume hannuwanta duka a qirjinta kafin ahankali ta maida shayayyun idanunta zuwa gefen makeken tabel din inda nan kwayar idanunta suka sauka akan wani qaramin madaidaicin fream mai azababben kyau tayi taku biyu tare da kai hannunta ta d'auki fream din tana dubawa, mace da nmj ne cikin shiga ta alfarma da wani kyakkywan baby, inda gabad'aya hannuwansu ke jikin baby sun bashi kyakkywan runguma ,sunyi kyau sosai kowannensu fuskarsa d'auke da murmushi wanda babu tantama na farin ciki ne .acikin kallon kurullar da takewa hoton ne ta gano irin tsananin kamar da matar dake cikin fream din tayi da mr ata ."tayi shiru kawai tana kallonsu gabanta na fad'uwa kafin ahankali ta ajiye fream din a inda ta dauka ta cigaba da tsayuwa tare da zance zuci"ya Allah kasa nadiya tazo"dan muddin ban yi mata tarin tambayoyin dake cunkushe da zuciyata ba bazan samu salama ba ,matsawar ban ganta ba kuwa zuciyarta zata qare ne acikin wasi wasi ."
mr ata cigaba da duba sakonin mutane ,bayan kamar mintuna talatin da barin maryamah office dinsa ya gama duba sakonin mutane tare da kashe laptop din gabansa ya rufe ya yunkura zai mike tsaye domin dai shima zuwa yanzu zuciyarsa ta aminta da nadia bazata zoba ,sai dai bai kai ga qarasa mikewa ba yaji ana knowking din kofa glass din office dinsa tare da neman izinin shigowa." a natse ya kai kallonsa ga kofar sannan ya koma a hankali ya zauna Inda tsumammun idanunshi na kallon glass din kofar shigowa ,nan take ya fahimce nadiya ce kuma daman yayi wannan tunanin duk da bashi da tabbaci kasancewarsa tare da maryama ne ya hanata zuwa ,sai dai ko wani dalili ne na dabam ."cike da jin isa ya motsa lip's dinsa ahankali yana cewa "coming!tare da yin juyi akan kujerar da yake zaune ta turo kofar ahankali ta shigo tare da maida kofar ta rufe ahankali ta tsaya batare data qaraso gabansa ba ."daga inda take tsaye ta soma magana cike da matsanancin fargaba "ammm so..."am so sorry sir nayi lattin zuwa sakamakon wani dalili na samu sakonku ta hanyar e-mail daga office dinku that's why I came "coming !"ya fad'a yana hade hannuwansa duka ya dafe ha'barsa yana qare mata kallon tsab ."
Jikinta a matukar sanyaye ta qaraso taja kujerar dake fuskantarsa baya kad'an ta zauna a hankali ,a natse ya d'auki d'aya daga cikin wayoyinsa dake ajiye akan table ,fuskarsa da zuciyarsa a dake ya soma neman number maryama yana manna wayar a kunnensa,ringin d'aya ta d'aga.yayi magana a can kasan makoshi sannan yayi disconnecting din kiran ya ajiye yace "ko kinzo da takardunki?yes sir! ta fad'a tana sauke numfashi "let me see!" ta mika masa wata jaka baka wanda takardunta ke ciki ,sai daya furzar da numfashi kana ya miko zafafan yatsun hannunsa farare sol ya kar'ba ya bude a natse ya fara duba takardunta yana cewa "kin tabbatar da komai na ciki ? yes sir komai na ciki ta fad'a tana faman kyalle kyalle acikin office din yayinda shi kuma ya cigaba da duba takardunta daya byn daya yana satar kallonta ,gabadaya ba'a natse take ba dan kallo daya mai hankali zai mata ya fahimci bata da gaskiya "sir zuwa yaushe ne zan fara aiki ?"very soon zai iya kasancewa ma next week "ya fad'a yana mika mata takardun tasa hannunta ta kar'ba shi kuwa sai faman kallon kofar shigowa yake yana mamakin yadda maryama ta 'bata lokaci gurin shigowa ."
"Sir na dade rabona da aiki da ATA company ko zan iya samun takardun tsaretsaren ayyukanku na yanzu?"me zai hana zaki samu mana ya fad'a adaidai lokacin da maryaamah ta turo kofar ,ahankali ta shigo ta maida kofar ta rufe ta had'e hannuwanta duka a qirjinta ta rungume fuskarta babu alamun wasa ko tsoro atattare daita ,jin motsin shigowa yasa nadiya ta d'an juya bayanta sai ganin maryamah tayi tsaye tana kallonta, kallo mai tattare da tunhu ma, da sauri nadiya ta mike tsaye jikinta na karkar wa tana kallon maryamah, ido cikin ido suke kallon juna dan sam bata yi expecting zata ganta ba duba da ba'a wannan company take aiki ba , maryama ta soma taku ahankali har ta qaraso kusa daita ta tsaya still kwayar idanun nadiya na cikin nata babu abinda maryamah ke gani alokacin sai tunanin ganinta na farko da taí lokacin da tazo gidansu amatsayin abokiyar aikin sadam yadda komai ke zuwa maryamah haka yake zuwa ma nadiya tunanin maganarta da sadam ne ya shiga dawo mata daki daki alokacin da take bashi labari samun aikinta a ATA company ."
"My heart na samu aiki a ATA company gsky naji dadin samun wannan aikin "ba dadi ya kamata kiji ba ,abun ki tsaya kiyi tunani ne ," me yasa suka kiraki adaidai wannan lokacin cewarsa "idan zaka tuna ai na ta'ba aiki dasu lokacin baya kafin naje kasar Índia kuma naji dadin aiki dasu haka zalika suma sun ji dadin aiki dani ,daman kuma ni bani da wani babban burin da wuce nayi aiki da ATA company yanzu ga dama ta samu sai yanzu nasan na samu aiki mai kyau "babu wani aiki mai kyau da kika samu dan baza kiyi aiki da wannan campany ba". ya fad'a tare da mikewa tsaye ya juya mata baya ,ta kallesa a matukar firgice tana cewa "me kake nufi da bazan yi aiki da wannan kamfanin ba ?ta tambayesa tana dawowa gabansa ta tsaya tana kallonsa ranta a bace "saboda maryama na aiki a d'aya daga cikin kamfanin su " to sai me idan maryaamah na aiki a AGC ? maryama na aiki a AGC ni kuma zanyi aiki a ATA ta ina zan hadu daita ."?
" kaga my heart banason wani rigima yanzu ."
kai yanzu ba kamata yayi kayi murna ba zan samu aiki da zamu ji dadin rayuwarmu kafin ka samu naka aikin ba ?"ya matsota sosai tamkar zai shige jikinta dan har masoyan suna iya shakar numfashin juna sannan ya kai hannuwansa duka ya riko kafad'unta tare da kwantar da murya "ina son ki samu aiki mana amman me yasa bazaki fahimceni ba idan ya kasance plan aka had'a miki fa taya zaki kubutar da kanki ?lokacin data kawo nan qirjinta ya dinga bugawa fiyye da kaida ."kafafuwanta suka kama rawa "tabbas zargin sadam ya tabbata plan akan shirya mata gashi kuma tana tsakiyarsa tsundum .
ta sake tuna maganar sadam ta karshe " ban amince kije ba amman idan kince lallai sai kinje duk abinda ya biyo baya babu ruwana kuma bazan saka kaina cikin rigimar ba sannan zaki nemini ki rasa rashi na har abada ".duk wannan sharad'in daya gindaya mata da zata fito sai da yayi qoqarin hanata hasalima shine dalilin da yasa bata zo akan lokaci ba dan rigima sukai sosai da kyar ta samu ta fito ."
"I hope that you recognize my face ?" maryamah ta tambayeta tana tsareta da kwayar idanunta masu matukar haske ." muryar nadiya na rawa da zuciyar ta tace "uhmm .." eh na gane ki sosai amman ban yi tunanin zanganki anan ba ." eh dole kiyi mamaki ganina tunda Kinsan abinda kikayi ,amman ni duk wannan bai dameni ba ,akwai tamabayoyin da nake son zan miki a halin yanzu,tambaya ta farko "me yasa kikazo gidanmu amatsayin abokiyar aikin sadam ? nan take gaban nadiya yayi wani irin mummunar fad'uwar kafin daga bisani ya shiga dukan tara tara, zuciyarta banda tsinkewa babu abinda take wani irin tsoro da matsanancin firgice suka mamayeta alakaci d'aya ta nemi dukkanin wata natsuwarta ta rasa kallo d'aya zaka mata kasan bata cikin kwanciyar hankali da natsuwarta ."
"sai tambaya ta gaba me yasa kika bawa wani number wayata ya kirani a tsakar dare nazo aiki da wuri ?"nan ma gabanta ya ba da dammm hantar cikinta ta kad'a "bayan kin rasa wayarki na samu wayarki a hannun wani bayan haka kika kirani domin kiji wayar tana hannun waye da kika ji muryata kikayi discounting din kira me kike nema atare dani ?duk me yasa kika min wad'an abubuwan da kika min ?nadiya tayi shiru ta kasa kwakwaran motsi yayinda jikinta ya cigaba da rawa "ta rasa wace amsa zata bata domin gamsar daita yadda nadiya ke kallon maryama cikin rashin sanin me za tace mata haka mr ata yake binsu da kallo yana mamakin qarfin halin maryama ,yar yarinya daita amman akwai kwarewa da qarfin hali da rashin jin tsoron fuskantar duk wanda zatai magana dashi sai a yanzu ya sake gasgata qarfin halinta ba iya akanshi kad'ai take yi ba ,kuma yayi imani bashi ba duk wanda yayi mata ba daidai ba sai ta saisaitashi tare da yi masa karan tsaye arayuwarsa kamar yadda take qoqarin yiwa nadiya a yanzu "
gabad'aya nadiya ta rasa abun yi domin tana cikin wani irin gigita da tashin hankali wanda bata ta'ba shiga irinsa ba ,ahankali mr ata ya maida kwayar idanunshi sosai ya zubawa maryama kamar yadda nadiya tayi kafin ya juye fuskarsa ya sake had'eta tamau kamar yadda ya saba zuwa yanayi na kamewa da rashin d'aukar raini sannan ya kalli inda nadiya take tsaye cikin tsananin gigita ya bud'e baki ya fara magana "ke... ya kikayi shiru ki bud'e baki ki bata amsar tambayoyinta, dan matsawar baki ba bata amsar tambayoyinta ba lallai bazaki bar office din nan ba idan kuma ya zama lallai sai kin barsa to ki tabbatar a hannun hukuma zaki kasance ."ya qarasa maganar yana kallonta à kaskance "ta waigo da sauri inda yake tana kallonsa a matukar tsorace "yes me yasa kike bibiyar rayuwarta tare da caza mata kwakwaluwa?.bana bibiyar rayuwarta amman a wasu lukuta yana da kyau mu bar wasu abu saboda sirrin dake ciki dan ..."sai kuma tayi shiru ta kasa qarasa maganarta "ko babu komai bazata fad'a masu abinda zai yi sanadiyyar rasa sadam arayuwarta ba domin shi din muradin ranta ne da soyayyarsa aka halicci zuciyarta kuma tayi imani sadam na matsanancin sonta ."
"me kike kokarin kice nadiya ?kinga karya bata da wani mahimanci arayuwar d'an adam bana bukatar kiyi min karya dan girman allah idan Kinsan wani abu akan yaya sadam ki fad'a min bare ma ni jikina yana bani kina tare dashi "what !"yes abinda kika ji shine abinda na fad'a "sadam fa kika ce ?"!nadiya ta furta sunansa tana duban maryama ?shifa fa ?"inji cewar maryamah "idan har sadam yana tare dani ai da tun tuni na kawo muku shi koda kuwa acikin halin hauka yake ko wani abu makanmanci haka idan kuma akan muryar da kika ji ne a waya kisani wannan muryar ba muryar sadam bane muryar sabon saurayina ne da zan aura ne ta fad'a tana saisaita natsuwarta tare da hura mata hanci amman dai zan fad'a miki wani abu domin nasan sadam bazai ta'ba fad'a miki tsakaninmu dashi ba ."nida sadam mun kasance masoyan juna ne mun had'u dashi a shekarun baya a makaranta ."
"abubuwa dayawa sun shiga tsakanina dashi tare da alqawarin aure byn nayi tafiya zuwa kasar india na samu labarin aurensa da mutuwarsa nayi matukar gigita da jin aurensa kuma naso da zarar na dawo kasar na maka shi a kotu .nan take maryam ta shiga wani sabon tashin hankali mai tsanani ta koma ta jingina jikinta da glas wanda shine madadin bango acikin office din tana cigaba da kallon nadiya cike da tsananin tashin hankali "."Ina ta qoqarin shirya yadda zan maka shi a kotu domin kwatarwa kaina hakina kwatsam sai kuma naji labarin mutuwarsa tsayawa fad'a miki irin tashin hankalin dana shiga maryama bata lokacin ne saboda ina mutuwar son sadam son da bazan iya bar ma wata halitta ba"
"actually akwai wasu hotunan da mukayi dashi kafin na bar kasar nan ,idanun maryamah ya cika da ruwan hawaye shi kuwa mr ATA jira yake nadiya ta gama maganarta ."nayi imani wadan nan hotunan suna cikin dakinsa kuma duk da baya raye zaa iya ganosu cikin sauki shine ma dalilin da yasa na dawo saboda banason kuga munin hotunan da mukayi dashi dan ya sha bani labarin yadda kuka yarda dashi kuka aminta dashi muddin kuka ga hotunan mu tare cikin wani yanayi kwarin gwiwarku akanshi zatai sanyi."hawaye masu zafi suka zubo akan kuncin maryama lokaci data ta tuna ranar data kamasa yana amsa wayar mace "banyi niyyar fad'a miki ba saboda nasan zakiji ciwo sosai acikin ranki amman wallahi wannan shine dalilin zuwana gidanku har na bukaci nabiki dakinsa sai dai a ranar ban samu naga hotunanmu ba shiyasa nayi tunanin sake dawo da daddare . lura da nayi idanunki biyu kina aiki yasa na kiraki tare da canza murya ni kaina lokacin zuciyata a tsorace take saboda banason kiga private pictures dinmu shiyasa nayi duk abinda nayi na kwashesu dan allah kiyi kokarin ki fahimceni amman fa kisani mijinki sadam ya yaudareni matukar yaudara ."
"maryamah sadam yaci amanata na yarda dashi na mika masa ragamar rayuwata amman ya watsar da yardar da nayi masa saboda bai fad'a min cewar zai yi aure ya barni ba ."na tafi kasar india da zumar idan na dawo zamuyi aure dashi amman sai labarin aurensa kawai naji yayi aure intakaice miki ana gobe zaa daura aurenku munyi waya dashi daace zaa ga wayarsa to da kin tabbatar da duk abinda na fad'a miki wata killa da zuciyarki ta buga sakamakon abinda zaki gani domin abubuwan dake tsakanina dashi ko Ke da kike matsayin matarsa bana tunanin kunyi irinsa dashi ."Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun maryama ta dinga furtawa acikin ranta hawaye na zuba akan kuncinta masu radadi da ciwo."
Yayinda zuciyarta ta dinga mamakin maganganun nadiya akan halittar data yi imani bazai ta'ba aikata hakan ba domin itama ta yarda dashi "maryama ki daina mamakin ,bazan ta'ba daina mamaki ba nadiya har sai naga sheida akan hakan yanzu ga wayarki a hannunki nayi imani idan har zaa samu hotunanku a wayarsa ko katin hotunanku to lallai zaa iya samu a wayarki tunda kuna tsananin son juna bai zama lallai ku iya rabuwa da hotunan juna ba "wannan haka ne maryama nadiya ta fad'a tana goge nata hawayen sannan tana qoqarin bude wayarta domin tabbatar mata da gaskiyar data bukata hotuna guda biyar ta nuna mata kuma duk suna tare da sadam babu kayan kirki ajikinsu cikin yanayi na tsananin soyayya "kadan ne wannan maryama ,kinga bazai yuwu na bar wayata a hannunki ba duk da nasan ganin wadan hotuna zasu miki wuya allah dai ya jikan sadam kawai ni zan wuce ta d'auki jakarta ta rataya ta fice daga office din ."
wani yanayi mai tsarkakkiya da wuyar misaltuwa maryamah ta tsinci kanta ciki rawar da jikinta yake yasa ta kasa tsayuwa sosai tasa duka hannuwanta ta dafe hannun kujera dan karta kai ga fad'uwa kasa da sauri mr ATA ya kamota ya zaunar daita akan kujera domin ya fahimci zata iya zubewa kasa, ya rike yatsun hannunta gam yana kallonta yana jin wani irin yanayi mara misaltuwa na shigarsa duk da yaso yayi ma nadiya nashi tambayar amman ganin tashin hankali da maryama ta shiga ya bar nashi amman lallai sai ya cigaba da bibiyi rayuwar nadiya domin akwai wata gaskiyar da yake tunanin ta boye wa maryama ".ahankali mrs ata ya sakar mata yatsun hannunta dake cikin nashi tare da mikewa tsaye yayinda maryama tai shiru dafe da kanta cikin tsananin tashin hankali mara misaltuwa."
"sosai tayi zurfi cikin tunanin rayuwa "a she haka yaya sadam yake cin amanar yardar da sukai masa ?"a she daman baya sonta ya amince da aurenta?"a she daman yana cin amanarta ne ?"hawaye ne kawai yake turereniyar zuba daga cikin kwarnin idanunta yayinda tsumammun kwayar idanun mr ata yake kanta yana kallonta tare da nazarinta kafin ahankali ya cire yar saman suit dinsa yana cigaba da kallonta tare da tura hannuwansa duka cikin aljihun wondon sa still idanunshi na kanta gabad'aya sai yaji damuwarta ta mamaye kowace gaba dake jikinsa."cikin takun nan nasa ya qarasa ya bud'e qaramin frdge ya d'auki goran ruwa ya rufe ya dawo inda take zaune tana kuka sai dai kukan nata ba mai sauti bane domin kuka take da zuciyarta ."
A natse ya bud'e murfin goran tare da mika mata "take some water "batare data kallesa ba haka zalika bata kar'ba goran ruwan ba tace "no ..!thank you." ta fad'a cikin wata irin sanyayyar murya mai tattare da tarin damu wa da tashin hankali "Ala hakikanin gaskiya ta dade bata shiga gigitaccen yanayi irin na wannan lokacin ba, ko zata kwatan tashi da wani abu sai dai ta kwatantashi da irin radadin da taji alokacin da taji tarihin rayuwar da iyayenta sukai kafin aure ,zuciyarta tayi matukar gigitata " iya tashin hankali ta shiga a zaunen da take "hakika yaya sadam ya cutar da umma ,sannan yaci amanar yardar da tai masa kuma yaci amanar tarbiyar datai masa da umma zata ga hotun sadam dinta cikin wannan yanayi da'aka kirasa da soyayya tabbas da take zuciyarta zata buga "why yaya sadam me yasa ka zabi irin wannan rayuwar ?"mai yasa kayi mana haka ?"duk wad'an story din da yarinyar nan ta bayar yanzu shi sadam din ya ta'ba fad'a miki ?."
yanayin da take ciki bazata iya bashi amsar tambayarsa zai fi ya barta taji da tashin hankali daya tsinci kanta ciki ,numfashi kawai take janyowa da kyar tana fitarwa "wannan shine matsalarki ana magana kiyiwa shiru ,okay but now this is your problem tunda kinsan komai akan mutumin da kika yarda dashi ,daman kuma matsalarku kenan mata kuna da saurin yarda da mutun kalli irin abinda ya saka miki dashi, yasan bai sonki mai yasa zai amshi aurenki har yayi nasarar dasa soyayyarsa acikin zuciyarki ?"is better to forget him in your life ki manta ko kuma nace ki goge wannan yarda da kika masa coz you trust him so many "
"bani kad'ai ba gabad'ayanmu ne ,mun yarda dashi mun aminta dashi shi din jigo ne acikin rayuwar ahlinmu kamar yadda mahaifinsa ya kasance alokacin da yake raye "sai dai mun yarda da yaya sadam dayawa batare da tunanin zai ta'ba mana haka ba ,we trusted him blind ,idan wani yace min yaya sadam zai aikata haka agare mu bazan ta'ba yarda ba duk da na ta'ba kamashi yana waya da mace amman siffa ta nagarta da kamala yaya sadam ya had'asu bazakace zai iya rungume wata mace da ba muharamrsa ba bare har ya kasance cikin irin wannan yanayin dana gansu tare da nadiya ba "I trusted yaya sadam without thinking ."ta qarasa maganar tana zubar da hawaye" I trusted him without thinking because I don't believe that yarda dashi din zai zame min qalubali arayuwata ."shiru ne ya ziyarci office din kafin ahankali ta cigaba da magana cikin muryar kuka "shikenan yanzu babu wanda zaka iya yarda dashi ?" ta fad'a wasu hawayen masu zafi da ciwo suka zubo mata "
Mmn sudais[8/31, 11:25 AM] Safwan Libiya 2: 💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
BOOK 3
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.