Maradams Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: MAR ADAMS BOOK 3 COMPLETE BY AYSHA BAGUDU.txt
Chapter 17 of 29
Page 24
"Saurin 'bata fuska maryama tayi "dan me zai dinga dangatata da kalmar hauka alhalin ita ba mahauka ciya ba ?"kuma ta lura daga lokacin daya ganta da sultan ne ya sake shigo da wani sabon salon wula kanci ,mr ata yayi bala'in tsareta da ido duk da suna cikin duhu ne amman idanunshi suna iya karantar halin da take ciki sakamakon maganar da yayi mata a yanzu ,cike da tsananin tsoro tace"please sir ka daina dangantani da kalmar haukan nan ina jin kamar na munzanta dayawa " bai ce daita uhm ba bare uhm uhm kawai sai ji tayi ya riko tsintsiyar hannunta da qarfin ya soma tafiya daita, nan take ta turje amman yaki sakar mata hannu dole tasa tace "ka sakar min hannu nayi tafiya da kaina ."yana jinta yayi mata banza tamkar ba dashi take magana ba ."
"acikin unguwarmu muke idan wani ya ganmu haka wata fassara daban za'a mana "ta fad'a tana 'dora hanunta a saman shi a qoqarinta nason zare hannunta, shareta yayi batare da yace mata kala ba sai ma sake damke tsintsiyar hannunta yayi ya cigaba da tafiya "shi ina ruwansa da wasu , ita din tashi ce kuma kome zaa ce akanta zuciyarsa bazata d'auka ba ."
"jin yaki sakar mata hannu yasa jikinta ya fara rawa dan tasan tunda ta bari ya tunzura sai abinda yaga dama zai yi." alhankali muryarta ta fito "please sir kayi hakuri wallahi bazan sake jayayya da kai ba ka sakar min hannu"dogon tsaki yaja yace "wannan kuma problem dinki ne ".bai tsaya daita akoina ba sai daf da bakin get din gidansu sai dai yaki sakar mata hannu ,inda zuciyarta ta shiga tashin hankali mai tsanani da jin tsoron abinda zai biyo baya, dan bazata so wani acikin 'yan unguwa ya fito ya gansu haka, bare wani daga cikin 'yan gidan su. shi kuwa tsura mata ido yayi acikin duhun yana kallonta yana jin kamar ya janyota jikinsa ya rungume tsam tsam!!
maryama bata gama tunaninta ba sai ga fitowar husna diyar aunty hassana daga cikin gida tana waya tana waige waige da alamun wani ta fito nema jin sautin muryarta yasa maryama ta d'an juyo cike da tsoro ,ganin husna yasa wani bakinciki ya tokare mata kahon zuciya wanda yasa hawaye zuba daga idanunta ,da sauri ta dawo da kallonta garesa muryarta can kasa cike da shagwa'ba tace "ka gani ko ."
Shima muryarsa a kasalance yace "me nã gani ?
"cousing dina ce ta fito yanzu "so what ina ruwana da fitowarta ?ko gani tayi ina miki wani abu ? "ba zaka gane abinda nake jin tsoro ba, abinda zai je yazo nake gudu ".tayi maganar muryarta cike da matsanancin tsoro "ki ganar dani zan gane "ya fad'a cike da kulawa yana sake motsata so take taja baya saboda bata són kusancinta dashi amman tana gudun husna ta gane itace tsaye a wajen "menene damuwarki a gidan ?yayi maganar cikin wani irin salo "da sauri ta girgiza masa kai tana cewa "no karka damu kawai sakar min hannuna na wuce "ke matsalarki kenan kinsan bana son taurin kai da jayayya bare kafiya amman a dole sai kinyi min "ya qarasa maganar yana hura mata hucin bakinsa a fuskarta da wuyanta sakamakon kusancin da suka samu saurin lumshe idanunta tayi zuciyarta na wani irin tsinkewa ."yayinda husna tayi shiru tana duban inda suke tsaye sun yi mugun yin kusa da juna wanda bai fi taku d'aya zasu qara jikinsu ya had'e ba . "a fili tace "wacece wannan kamar maryama ?"
"aiko jin haka yasa hankalin maryama yayi matukar tashi tun da take arayuwarta baa ta'ba ganin tasamu kusanci irin haka da wani d'a namiji ba ."ganin husna na qoqarin tahowa inda suke tayi saurin jan hijab dinta ta rufe rabin fuskarta iya bakinta da rabin hancinta ne kawai a waje tun kafin ta qaraso ta ganta taje ta bazawa aunty hasana ita kuma tasamu abun zaginta dashi ."husna na gama qarasowa kusa dasu ta tsaya tana cewa "maryama !" ko ba maryama bace ?" maryama na jinta amman tayi mata banza a zuwan ba ita bace ,shi kam mr ata kallon d'aya yayi mata ya d'auke kanshi ya cigaba da kallon princess dinsa ." ganin da husna tayi ba'a kulata ba gashi wanda take waya dashi yana sheida mata inda zata zo ta samesa yasa ta juya tana taku tana cigaba da wayarta sai dai zuciyarta cike take da wasi wasi akan maryama ce ko kuma wata ce daban tsaye a kofar gidansu amman wani bangaren na zuciyarta yafi amince mata da maryama ce."
sai sanda mr ata yaga dama sannan ya sakar ma maryama hannu tana jinta free ta juya ta nufi cikin gidansu da sauri batare data waiwayo ba ,tana shiga bangaren umma ta nufa tana haki bata iske umma ba da alamun tana ciki tana sallah ta zauna akan kujera ta kifa kanta akan hannun kujera kawai sai hawaye ya soma gangaro mata kukan da bataso tayi akan shi shine ya kufuce mata ba dan taso ba dan hakan ne kawai zai iya sanyaya zuciyarta akan wulakancin da yake mata "yana son ya maida mata jiki banza, babu wani shamaki kawai daya so zai riketa, ita kam sam bazata d'auki wannan wulakanci ba gara tun wuri ta takawa abun burki bazata sake yarda ya dinga ta'bata anyhow ba ,jikinta mai daraja ne ,jiki ne data d'auki tsawon shekaru tana killace abunta bazai yuwu lokaci d'aya yazo ya dinga wasa dashi son ransa ba ,ya hanata saka hijab da nikaf ta yarda amman jikinta kam tana da rowarsa bana ta'bawa bane nã aure ne, tana kuka tana zancen zuci sai da tayi mai isarta sannan tayi shiru ta shige d'akinta tun kafin umma ta fito ."
Tsaye mr ata yayi a wajen gidansu maryama tamkar wanda aka dasa tsabar mamakin kansa da yake duk yadda yake son ya boye tarin soyayyarta da qaunarta acikin zuciyarsa abun ya cutura har yau gashi tsananin kishinta da son kare lafiyarta da mutuncinta ya kawo shi kofar gidansu a karo na biyu har sai daya ga shigarta cikin gidansu sannan ya samu natsuwa da kwanciyar ahankali ,yana tsananin qaunarta ita kuma tana tsnanin qaunar waninsa . "
"wasu hawaye masu zafi da ciwo ne sukayi nasarar biyo fuskarsa a lokacin daya tuna tun sanda ya fara ganinta a mafarkinsa wanda shine asalin lokacin daya fara jin zazzafar soyayyarta acikin zuciyarsa haka rayuwar take cike da tarin abin mamaki da fari ya d'auka komai da sauki ake samusa ashe abun ba haka yake ba ,abun ba kamar yadda ya taso bane da duk abinda yace yana so ya zama dole ayi masa, idan kuma babu dole sai an nemoshi a duk inda yake an bashi."
Ahankali mr ata ya d'auke kwayar idanunshi akan kwara'babben get din gidan su maryama ,ya juya cike da sanyin jiki, ya soma tafiya zuciyarsa na sake nitso cikin tafkin shaukin qauna da tunani da kyar yake iya d'aga qafafuwansa tamkar wanda bashi da laka haka yake ji a sansar jikinsa inda zuciyarsa ke wani irin bugawa da karfin gaske "wai shine yau acikin irin wannan kwarababbiyar unguwar a karo na biyu ?" a tun tasowarsa idan aka fad'a masa cewar a irin wannan unguwar zuciyarsa zata mace zai karyata wata killa ma sai anyi mugun rigima dashi."
sannan duk tsawon shekaru da yayi yana nemanta bai d'auka daga irin wannan family zata fito ba ,ya d'auka daga gidan mulki ko gidan wani shararren attijira ko d'an siyasa da duniya tasan da zamansa sai gashi zuciyarsa ta tsallake tarin mata bilaadadin masu tarin arziki mulki tattare da boko soyayya tayi wuji wuji dashi ta wullosa cikin wani ahli da ba kowa bane ,bama kowa ne ya sansu ba a iyakar agage ma yayi imani ba kowa ne yasan da zamansu ba ."
a natse ya cigaba da taku yana cigaba da zance zuci still yana jin dinga hawayensa akan kuncinsa shi ba gudun ahlinta yake ko kyamar ahlinta yake ba a'a tsantsar mamaki ne kawai cunkushe a zuciyarsa da tarin iliminsa da tarin dukiyarsa da tarin nasabarsa da tarin nuna isarsa amman Allah ya nuna masa shi din ba kowa bane face bawansa kuma wanda yake qarqashin ikonsa ,ya nuna masa wannan itace irin kalar qaddarar da zai d'aura masa kuma bai isa ya canzata ko ya gudarwa qaddarar dake biye dashi ba ko akan maryam ya kamata ace ya fahimta duk yadda ya kai ga kin yarinyar yadda ya dinga gudun aurenta babu irin qiyayyar da bai nunawa yarinyar ba amman a qarshe sai da allah ya nuna masa shi din bakowa bane ya aura masa ita ya kuma zauna daita a qarshe ga ciki "ya rabbi " ya furta a fili alokacin daya tsoma qafarsa d'aya cikin ca'balbali ai bai tsaya dubawa ba dan yasan zuciyarsa bazata d'auki kallon inda ya sanya qafarsa ba gara ya cigaba da tafiya zai fiyye masa alkhairi da kwanciyar hankali ."
" ya d'auki tsawon shekara shatakwas yana tsnanin sonta shi kad'ai yasan irin wahalar da zuciyarsa ta sha akanta ,babu dare babu rana kullum muradinsa da rokonsa ya ga ko mai kama daita ne a zahiri sai gashi allah ya amsa rokonsa ya had'asu a gaske ai duk yadda maryama take ya amsa koda kuwa zata kasance bata da kowa ,bata da komai bata da galihu kai koda kuwa acikin tsatson bayi ta fito zai 'yantata da ko nawa akace ya maidaita mallakina take wani bangarensa na zuciyarsa yace "tabbas adam kai din masoyi ne tunda kana sonta a duk yadda take "wallahi ina matukar son maryama ya bawa zuciyarsa amsa da haka .bayan mahaifiyata itace abinda nafi só a kaf duniya yana tafiya yana ciza lip's dinsa yana ganin hanya da kyar kasancewar unguwr nada mugun dubu. naunayen ajiyar zuciya ya sauke yayinda soyayyar maryama ke cigaba da kutime meniya da zuciyarsa da gangar jikinsa qaunar maryama ya dinga bin dukkanin sansar jikinsa ji yake kamar ya zarta duk mazan duniya saa da allah ya kwatota a hannun wani ya dawo masa da farinciki rayuwarsa."
" hakika Allah yana son shi domin daya had'u daita da aurenta da lallai zaayi gagarumin tashin hankali dan ko ta kashe auren ta dawo garesa ko kuma ta kasance mai maza biyu amman bazai ta'ba yarda ya barwa wani ita ba ,amamn dake Allah yana son shi da rahma kuma had'uwarsu tana cikin qaddararsa sai ya kashe masa tsohon mijinta saboda shi ya sameta ."Allah kenan yadda yaso haka zai yi inda yayi parking din motarsa ya qaraso da kyar yana kakkabe qafarsa data fad'a cikin cabalbali ".
Mr ata ya iske tarin samarin unguwar dake zaman banza a bakin titi kamar safiya haka yaga wajen kasancewar zuwa wannan lokacin an kunna street light suna ganinsa duk suka matso suna sara masa a hakan ma basu san ko waye shi ba kawai dai kyawun motar daya zo daita ne yasa sukai masa kyakkyawan zato, bud'e motar yayi ya shiga ya zauna sai daya saka seat belt sannna ya d'auko bandir din yan dubu d'aya d'aya guda uku yayi warning glass din motar kad'an ya miko masu yace su raba . nan take ihunsu ya karad'e unguwa wad'an da ya bawa kudin suka shiga bashi hanya suna korar mutane a guje ya figi motar ya hau babban titi yana tunani"yana son dauke maryama daga wannan unguwar amman yana tunanin soyayyarsa ."
"Zai so ya fito mata da zahirinsa amamn kuma jin tsoron tace bata son shi "kai kuwa adam akwai macen da zatace bata sonka ?" Wani bangaren ba zuciyarta ya tambayesa .zata iya cewa bata sona mana tunda zuciyarta da hankalinta yana kan matacce tunda gashi tna mata maganar aure amamn ita ba wannan maganar bane arainta “akwai tarin abubuwa dayawa agabana wanda aure ne zai zamo last .”kwakwaluwarsa ta tariyo masa maganrta tsaki yaja yana sake ganin aurenta a boye shine kawai mafuta agaresa idan yaso ahankali zai koyar daita yadda zata shi fiyye da wancan mataccen ."qarfe shadaya na dare da mintuna ashirin ya tako cikin babban parlour'n mami wanda babu motsin komai da kowa acikinsa sai nã makeken tv bango da ac nan dake aiki ,kai tsaye samansa ya nufa yana furzar da hucin iska daga bakinsa yana shiga ya fad'a bedroom dinsa ya fad'a kan makeken gadonsa yana sauke wani wahalallen numfashi."
Yana kwance mami ta shigo har cikin bedroom dinsa ta tsaya akanshi tana qare masa kallo tsab dottin data gani tun daga step har parlour'n kenan a takalminsa ya kwaso ?” to ina yaje ma har ya kai by this time ?shi da matukar yana gari duk tsanani takwas a gida take masa "adamcy !"mami ta kira sunansa ahankali ata ya juyo yana kallonta kafin ya dauke tsumammun idanushin daga cikin idanun maminsa ya yunkura ya tashi ya zauan yana dafe goshinsa da hannunsa daya kusan minti goma mami ta dauka tana kallonsa batare da tayi yunkurin cewa komai ba sai dai yanayinsa take karanta yanayinsa yau tamkar wani mara lafiya tana kallonsa ya gyara zamansa tare da numfasawa ya zare takalmin qafarsa da duk dottin unguwar maryama ne yayi shiru kawai yana kallonsu gabansa na fad’uwa .”
tsawon lokaci mami ta dauka tana dubansa yayinda cikin zafin rai ya kamo lips dinsa na kasa ya soma cizawa da karfi sakamakon hawayen da yaji yana kokarin son zubo masa." wani irin nauyin zuciyarsa tayi "yana ji yadda qirjinsa ke masa zafi da ciwo tamkar an daura masa dutse mai shege nauyi a sama kirjinsa yanayinsa yasa hankalin mami yayi matukar tashi duk abinda kaga ya maida adamcy haka baqaramin abu bane ."
guri mami tasamu nan kusa dashi ta zauna tare da kamo tafin hannushi cikin nata tana mai cigaba da nazarin yanayin daya yake ciki ,ka natsu ka kwantar min da hankalinka adamcy ka daina sakawa zuciyarka damuwa too much idan ba haka ba zaka Sakani a tashin hankali. fad'a min wani abu ya faru ne a AGC ?tayi masa tambayr cike da kulawa irin ta uwa hannusa ya kai goshinsa yana sauke numfashi "zuwa Ibrahim uku bai sameka ba ko akwai wata matsala ne data taso ?dago tsumammun idanushi yayi yana kallon mami dasu "ni a wajena babu wata matsala sai dai ko daga garesa "to allah yasa shima haka .ka kai dare a waje a ina ka tsaya haka”?shiru yayi gabansa na cigaba da luguden bugu “ko kuma nace ina kaje daka kwaso dotti mai muni haka .”
Takalmansa yabi da kallo yana mai runtse idanunshi “duk takalminka ya 'bata step da parlour'n ka ?shiru yayi kawai yana soso gefen kanshi "ko wajen wannan sabuwar maaikaciyar kaje ?sake kallonta yayi a d’an rikice "adamcy kana son yarinyar nan? "take yaji wani abu ya tsigar masa a gabad’aya ilahirin jikinsa yana yawo cikin ’ bargo da tsoka tsayawa yayi yana kallonta ya kasa kwakwarar motse ballanantana yace mata wani abu .”
ahankali 'mani ta numfasa sannan ta cigaba magana “wannan shine karo ba biyu dana tambayeka , irin wannan soyayyar zaka boyewa sweetheart dinka "?zan so naga yarinyar nan naga abinda tafi maryam dina dashi, nasani baza tafi maryam dina da komai ba, maryam dina yar asali ce yar dangi ce ,yar gata ce, kuma mai galihu ce ace mutun yana da dangina kamata ai abun ayi alfahari dashi ne “shiru yayi yana duban mami yana nazarin inda maganrta ta dosa "kenan dai hasashensa ya tabbata idan ya kawo maryama matsayin matar da zai aura ahlinsa bazasu amince ba, idan kuma sun amince zabasu sota ba zasu kyamaceta ?yayi wa kanshi tamabayr "ina son naganta adamcy da kyar ata ya samu ya had'iye abinda yaji ya tsaya matsa a makoshinsa sannan 'ahankali ya iya motsa lip's dinsa tare da kiran sunan mami " sweetheart ki bar maganr nan zamuyi later mami ta katse shi ta hanyar daga masa hannuta, nasan halinka adamcy bazaa qara maganar ba "ki kwantar da hankalinki yarinyar zata zo a gidan nan zaayi presentations kinga dole zaki ganta amamn fa babu komai a tsakanina daita bayan shaani na aiki ."ya fad'a yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa."
"yanzu kai haka zaka qare rayuwarka ?we will talk about it later “yana gama fadar haka ya shige bathroom."shiru mami tayi tare da bin kofar daya rufo da ido ."tarasa gane abinda ke damun tunanin d'anta shine zurfin ciki shine miskilanci shine jin kai shine rashin son magan shine rashin kunya ya rabbi ka taimakeni ni idan son yarinyar ma yake ya kawo min ita amatsayin wacce zai aura zan fi samun natsuwa dan gara yayi aure da zaman da yake haka tana bukatar ganin ya'yansa masu tarin yawa gashi ance maryam mace zata haifa tana son duk abinda ke cikinta amamn taso ace d'a namiji zata haifa masa domin kuwa haihuwar da namiji yana bawa uwa kariya daga duk abinda zai taso gaba na tashin hankali ,domin ita karon kanta misali ce tayi imani da babu adamcy acikin rayuwar ita da ya'yanta mata da tana ji kuma tana gani zata kaskanta acikin dangin ubansa amman tun yana yaro yake takawa duk wanda ya nemi ya kawo mata rainin hankali burki ."
Bangaren maryama har qarfe d'aya na dare idanuta sun kasa runtsawa ta yunkura ta tashi ta zauna sosai a tsakiyar katifarta ta janyo pillow ta rungume tsam a qirjinta tana going over maganganun mr ata tana son ta gano wata gaskiya da yake qoqarin boye mata ,wani bangaren na zuciyarta sai taji tana so ta yarda a cikin yanayinsa akwai alamun soyayya amma kuma acikin maganganunsa kwata kwata babu wata alama ,acikin kwayar idanunshi ma zaa iya tabbatar da akwai wani abu acikin zuciyarsa .”shiru tana tana tariyo irin kallon da yake mata domin son gano wani abu .”girgiza kai tayi tace “wad'an mugayen idanuwan nashi babu komai acikinsu sai tarin firgici "Idan kin san baki tashi aure ba a yanzu kar na qara ganin kin kula sultan magana ma ta fatar baki kar ya qara shiga tsakaninku dashi maganarsa kusan ta qarshe kenan to me yake nufi da hakan shi bai ce yana sonta ba sannan kuma zai ce karta kula wanda ya nuna yana sonta ."
Kwakwalwa maryama ta bude sosai duk abinda mr ata ya fada sun samu kyakkwan mazauni acikin
zuciyarta ta rufe shayayyun idanunta ta jingina bayanta da jikin gado ta sake rungume pillown dake makale a qirjinta tana jujjuya maganganunsa tana kuma yin filla filla da su tana so ta fito da komai daga rami daya shige ya fake a ciki, ta sake tariyo hirarsu da sultan a kanta ta kuma hada da maganar sa, ta so ta fahimci abubuwa da dama a kansa amma wani abu guda daya yafi komai girma, he is smart duk abinda yake yana yinsa da gogewa idan ba mugun karantarshi kayi ba bazaka ta'ba gane inda ya dosa ba , maganar sultan kuma wannan ba wani abun damuwa bane a wajenta saboda a yanzu ba soyayya bace a gabanta kamar yadda ta sheidawa mr ata bare tayi tunanin aure a nan kusa , abu daya yake tsaye a cikin zuciyarta wanda yasa kwakwalwata ya kasa samun kwanciya shine yaya sadam dinta da take jin har yau cewar yana raye ."
Washegari maryama bata samu zuwa office da wuri ba sai wajajen karfe goma da wasu mintuna dan tuni duk wani maaikacin dake aiki a qarshin AGC yana cikin kuma yana kan aiki jiki a sanyaye ta shigo office dinsu bakinta d'auke da sallama ta gaishesu ta cire jakarta sannan ta samu waje ta zauna tare da yin shiru tana kallon sauran abokan aikinta da suka dukufa suna kan aiki madam some ta shigo tace "sai yanzu maryama ?me yasa baki d'aukar aikinki da mahimanci ai shikenan daman idan kana jin mugunta bakayi wa kanka ba ai baka cika mugu ba. "maryama ta kalleta a kaikaice sannan tace "madam please me haka yake nufi ?"ina nufin duk ranar da sir ya gaji da halinki ya dakatar dake kinga ai kanki kika cuta ,"maryama ta numfasa sannan tace "duk abinda Allah ya hukunto akaina daidai ne "ai shi kenan kuma daman muslim’s din nan haka kuke da taurin kai ,ga aikinki gobe zaa kar'ba idan kuma kingama shi a yau mrs ata zai ji dadi maryama tasa hannu ta kar'ba tana cewa me zaa zana? ahankali madam some ta soma mata bayani tana gama mata bayani ta fita ."
Maryama ta mike ta dauki jakarta ta fice daga office din ta koma qasa office din da'aka maida ema.
yayi matukar mamakin ganinta amman dake bai san zuciyar mr ata bace kawai ya sakar mata murmushi yana murnar ganinta wunin ranar tana tare da ema inda mr ata bai sanyata acikin kwayar idanunshi ba amman dai ance masa tazo kuma har an bata aiki sai dai bai nemeta ba duk da kwayar idanunshi ita suke son gani amman ya danne saboda kar ya bada kofar da wasu zasu fahimci halin da yake ciki ."
karfe shida daidai maryama ta hawo sama ta ajiye aikinta a gaban madam some dake zaune tayi mata sallama tace zata wuce gida tana gama fadar hk ta juya bayanta ya hango daga inda take zaune tana rausaya kmr ba daga wacan jagwal gwalaliyar unguwar take fitowa ba komai mata tsab tsab kuma a natse . ya hard'e qafafuwansa waje d'aya yana cigaba da kallon yadda take juya sansar jikinta anya kuwa bazata koma saka asalin kamilalliyar suturarta ba ? dan irin wannan tafiyar ai sai wani yayi masa ganganci ,haka ma the next day a kasa tayi aikinta tare da ema duk yadda mr ata yaso ya ganta taki yarda su had'u aranta tace "aiki take masa ba jikinta ta kawo masa ya dinga ta'bawa ba yana yin yadda yaga dama ita ba ."
Tsawon kwanaki biyu kenan bai sanyata acikin idanunshi ba sai dai ya hangeta daga nesa ta shigo ko ta sauka hankalinta ma gabad'aya baya Kanshi tsabgar gabanta kawai take, yana zaune akan kujera sanye da riga da wondo blue sai yar cikinta light blue yayinda nick tied dinsa ya kasance brown colou hannunsa rike da wani nicktie din brown yana nadewa ahankali har ya gama ya soka cikin aljihun gaban rigarsa yana kallonta ta shigo office din some . gata ga office dinsa amman ko d'aga ido tayi ta kalli office dinsa batayi ba haka yana kallonta ta juya yaga ta nufi qasa wani zazzafan numfashi ya sauke sannan ya yunkura ya mike ya fito ya biyo bayanta tana zaune tare da ema da wasu ma'aikatan takalmansa ya shigo office din ,kamshin sanyayyen turarensa daya ziyarci hancinta da kuma bugun da zuciyata yayi ne ya tabbatar mata da shine ya shigo "good morning sir "!!! duk ma'aikatan dake cikin office din sai daya gaishesa illa ita qoqarin juyowa take ta gaishesa taji sautin muryarsa a zafafe "ke me kike yi anan ? cikin tsananin firgita, da tsinkewar zuciya da tsoro, tare da kyarman jiki, ta qarasa juyowa ta fuskanci inda yake tsaye sanye da suit yayi matukar kyau kamar wani matashi dan shekara talatin” just one second na baki ki tattara ki koma inda aka ajiyeki. tamkar gilmawar walkiya yaga ta zabura ta mike ta rungume jakarta da kayan aikinta gam-gam cikin tsuma da karkarwa ta bace .
wani irin masifeffen dariya ne ya taso masa tun daga kasan zuciyarshi har zuwa kan lips dinshi amman dole ya taune lip din shi na kasa kana ya gimtse ya murtuke fuska cikin tsare gida yace.ema "! yes sir ya fad’a cike da girmamawa “da alamun kagaji da aiki damu ko ?"no sir wallahi babu ruwana sir bance .."
“enough! ya d’aga masa hannu “to be your last warning. iya abinda ya fad’a kenan ya juya ya koma office dinsa sai lokacin hankalinsa ya dawo gangar jikinsa duk lalacewa ko wani abu bazai had'asu ba gara tana sama yana kallon duk abinda take ."ranar kusan tare ma sukai aiki akan presentation dinsu dake motsawa ,yadda bata sakar masa fuska ba haka shima wanda daman shi kusan fuskarsa a daure take .”aiko ta gane bata da wayo dan ya lafta mata aiki kamar me dan haka a matukar gajiya ta qarasa gida tayi wanka tayi magriba da isha’i saboda tsananin gajiya ma bata ci abinci ba ta kwanta.”
******
Yau ne ya kama zaa gabatar da presentation zaune mr ata yake tare da client dinsa mutun uku a gidan mami tun daga sama yasa akayi decoration har zuwa kasa surayya ce ta fara fitowa sanye cikin riga da siket na suit tayi juyi kamar yadda yan fashions desings keyi sannan ta koma gefe ta tsaya sannan yusura ma ta fito tayi Kmr yadda surayya tayi mutun na uku some ce sai wasu maikata guda biyu sai maryama wacce ta sauko cikin doguwar riga ta rike gefen rigar kad'an tana rausaya tamkr wata fure wani murmushin ne mai daukar hankali kwance akan fuskarta wanda ya bayyana wushiriyarta da dimples dinta ,tayi matukar kyau sosai mr ata ya gyara zama yana kallonta tun daga samanta har qaraso saukowa kwayar idanunshi na kanta .”
Mutane da suka zo ganin new design dinsu suaki tafi yayinda mutun daya acikinsu yace "wooo gsky naji dadin ganin representation dinku yayi min kyau sosai thank you so much mr ATA "wannan desings din ya bambamta da sauran desing daka saba kazo da wani salo dabam daman kuma ina da yakinin AGC company ne kawai zatayi min abinda zai kwanta min arai akan kowani kamfani dan haka akan wannan suprisse din zanyi double din order kaya."
" that's great mr ATA ya fada tare da mikewa tsaye yace "just a second !yasa hannuwansa a aljihun wondon suit dinsa ya qarasa inda yammatan suke tsaye "sannuku da kokari aikinku yayi kyau "thank you sir suka hada baki gurin fadar haka" sir ko zamu iya zuwa mu canza ?yes of course" ya fad'a yana kallon cikin kwayar idanun maryama tayi kyau matuka itace ta fara yin hanyar sama yabi bayanta da wani shu'uminn kallo tare da yin taku a hankali yabi bayanta da kallo ,jikinta a sanyaye ta dan juyo dan kallon bayanta ai kuwa ta zame tayi baya luuuu zata fadi kan tayis aiko da wani irin sauri mr ata yasa hannuwansa duka ya tarota bayanta ta fado jikinsa ."
Mmn sudais
[8/31, 11:25 AM] Safwan Libiya 2: 💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
BOOK 3
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 26
Cike da sanyin jiki mami tabi bayan mr ata da kallo kafin ahankali ta d'auke idanunta ta maida kan baba qarami dake tsaye zuciyarsa cunkushe da haushi da bakinciki abinda mr ata yayi masa "kinga kalar tarbiyar ki ko ?a gabanki d'anki yayi min zagi bayan ya wulakanta maganata "tukuna ma ina alqawarin da kika min na cewa bazai yi aikin nan ba "?numfashi mami ta sauke kawai wanda hakan yayi sanadiyar qara hassala baba qarami dan haka a tsawace yace" kin tsareni da idanuwa kin kasa cewa komai tunda kinsan da had'in bakinki yayi komai ."shikenan tunda ke da d'anki kunyi son ranku amman fa ki sani bashi kuka ci." mami ta sake kallon baba qarami dake surfa maseefa ta hade hannu wanta waje d'aya kasamcewar ta rasa me zata ce masa ya fahimce ta .kusan mintuna goma ta d'auka tana kallonsa batare da tayi yunkurin dakatar dashi ba ko ce masa wani abu ba har sai daya gama amayar da abinda ke ransa sannan ta gyara tsayuwarta muryarta cike da laushi ta soma magana "dan girman allah baba qarami kayi hakuri kai ma kasan halin adamcy da taurin kai "sai da ya ta'be bakinsa sannan yace "ai dole kince min nayi hakuri tunda ke da d'anki kun gama ci min mutunci mami bata damu da maganarsa ba dan tasan kad’an daga halina idan ranshi ya ‘baci kamar adamcy ne .”
sake kwantar da murya mami tayi "ni dai hakuri nake baka kuma in sha allahu..."saurin d’aga mata hannu yayi dan baya da bukatar alqawari ta "dakata ya isheni haka karki cika min kunne naji amman wallahi wallahi kinji na rantse ki ga yawa wannan d'an iskan d'an naki ya kiyayyeni kar ya sake gigin sake aikata mana haka "shikenan hakan ma bazai sake faruwa ba zai kiyayye yayinda aranta tace “bama zai cigaba da kula da kamfanin ba ,ya bar maku har abada domin dai tasan halin d'anta idan yace yes yes ne haka zalika idan yace no tô no ne tunda yayi mata alqawarin bar masu kamfanin tasan bazai ta'ba dawowa ya canza magana ba."da rarrashi da komai uncle jay da yaya Ibrahim da mami suka samu ya hakura ya fice daga parlour'n tare da sultan ."
yayinda mr ata ke zaune akan kujera a bedroom dinsa yana zukar sigari ahankali yana magana a fili "wannan mutumin so yake sai muyiwa juna rashinmutunci tukun zai fita a tsabgata,ko ina ruwansa da yadda zanyi da rayuwata? zanyi aiki a duk lokacin da nake so kuma dole ku barni koda kuwa ranku bai so “saboda son zuciya irin nashi kawai ya zauna yana biyewa ya'yansa inda ni d'ansa ne zai min haka ?"ya tambayi kanshi yana jan dogon tsaki tare da shafa sumar kanshi da hannu d’aya sannan ya mike ya fad’a kan bed dinsa yana cigaba da zugar sigari ."
Direban daya d'aukosu maryama, yusura ya fara saukewa sannan maryama, karfe goma daidai na dare maryama ta shiga gidansu part din umma ta shiga inda ta iske Aunty hassna zaune a parlour'n tana kallon tv "sannu da gida aunty ."ta fad'a muryarta a sanyaye sannan ta ra'ba zata wuce ta gefenta" ina kika tsaya har goma na dare"? maryama tayi matukar mamakin jin tambayarta ita da babu ruwanta da rayuwarta yau kuma me janyo wannan tambayar “ta tambayi zuciyarta tana duba agaogon hannunta goma ma har ta fara wucewa" .
“ki duba tun lokaci da kika bar gidan nan sannan ki kalli lokacin da kika shigo maryama kina yin abinda kike so acikin gidan nan kawai dan an baki dama ko ba haka ba ?"ta fad'a tana dubanta a kaskance bama zaki kira kowa ki fad'a dalilin da ya tsaida Ke ba karki manta wannna gidan namu gidan mutunci ne karkiyi abinda zaki 'bata mana sunan gida kamar yadda uwarki ta 'bata sunan gidansu dan nasan har abada irin guje gujen datai bazai ta'ba gogewa a zukatansu ba .”
Wani abu maryama taji ya caki kahon zuciyarta ranta yayi matukar 'baci zuciyarta ta dinga tuttukin bakinciki ,idan tace bata ji ciwon maganar aunty hasana ba wallahi tayiwa kanta karya ,amman data tuna bazasu wani sake d'aukar lokaci mai tsawo a gidan ba zasu tattara su barsu gidan su canza rayuwa sai kawai ta rarrashi kanta ta danne abinda take ji a yanzu muryarta a sanyaye tace "aunty hasana daman akwai wani aikai dazaa gabatar a office dinmu ne yau tun kwana uku daya gabata ake shirnsa umma ma tasan da zamansa to sai yau aka gabatar dashi shine dalilin da yasa nayi dare a waje amman in sha allahu bazanyi abinda zai ‘bata sunan family dinmu ba ,da safe ma naso na tsaya na fad'a miki koda na shigo d'akinki kina bacci amman Kiyi hakuri dan allah "ta fad'a tana ra'bawa ta bayanta zata shige daki "tsaya ! ta jiyo sautin muryarta."maryama taja ta tsaya tana lumshe idanunta "me kake ce a office ko me ?"
"uhm gskiya yanzu kin kware a iya tsara karya amman kisani na samu number wayar office dinku a hannun kanwar yusura kuma na kira an fad'a min lokacin da kika bar office a ina kike adaidai lokacin?eh amm gabad'ayanmu muna gidan mr ATA ne " me kika ce ?ta fada tana dubanta da mugun kallo "me naji kin fad'a yanzu "?sake maimaita min naji kawai dan iskanci sai ki kama hanya kije har gidansa anya ma kuwa ba iskanci kike yi awaje ba yasa maza ke gudu su barki ba ?"shi kuma wannan da yayi shahada ya aureki kin kashesa "muryar maryama ta na rawa tace "haba aunty hassana me kike kokarin cewa ? Karyar me zanyi idan nayi karya meye ribata ?" me zata bani” yanzu ke aunty hassana har kina tunanin ina yin iskanci a waje ."?dan allah ki cire wannan zargin aranki kawai dai akwai wani aikin sirri da zamuyi shine yace muje gidansa kuma bani kadai bace ki bincika zaki .."
“Kiyi min shiru banason jin wannna karyar naki yanzu dai rashi aure yasa zaki fara d’auko mana magana Allah yasa ba abinda yasa aunty tace nazo na zauna ba kenan idan ba haka me zai same ki dan kin zauna ke kad’ai “.?"akan me zanyi karya to ?" maryama ta fad'a a zafafe cike da jin haushi ta cigaba da mgn "dan allah ki daina min irin wannan kallon."ni bance ni ta gari bace amman ni ba yar iska bace idan na dawo aiki da wuri fine idan ban dawo ba shima daidai ne dan …”dakata ba dani kike wannan maganar ba da waccan uwar taki kike sannan ki bude kunnenki da kyau bazan mu yarda da wannna iskancin ba sannan shi mr ATA din akan wani dalili zai kaiku gidansa idan ba da wata manufa ba?” ko da yake sai dan iska ya bada dama sannan zaa kawo masa batun iskanci "Aunty hassan kin dade kina kirana da wannna kalmar amman idan allah yaso bazai jarabeni daita da zama yar iska ba dan bana aikata abinda ya danganci hakan , sannn karki danganta mr ata da wannna kalmar domin kuwa ke uwa ce ,kawai dai yau aikinmu ne yazo da wannna tsarin dan haka kisani naje gidansa ne kawai dan aiwatar da aikina ba dan wani abu ba .”
"idan ma kuma dan wani abu ne babu ruwan kowa da rayuwata dan babu mai ciyar dani zan iya yin duk yadda naso rayuwata ce ." tana gm fadar haka ta shige daki ta barta zaune tana Maimaita kalmar karshe data fda” idan ma kuma dan wani abu ne babu ruwan kowa da rayuwata zan iya yin duk yadda naso rayuwata ce ."cab din jan lallai yarinyar nan wuyanki ya isa yanka tunda an fara danna miki jijiya kinsan dadinta ai dole ki fad'a min haka amman kisani ba ni kika fad'awa magana ba wacan ganta lalliyar uwar taki da ta gama zubar da mutuncinta kafin aure kika fad'awa mgn ,ta fad'a tare da yin kwafa tana gyara zamanta tare da cigaba da mita “a lallai maryama anji dadin maza ina fad’a kina fad’a .duk maryama na jiyota amman ta daure ta cije dan kar tayi kuka amman sai da wasu hawaye masu zafi suka zubo mata tana sharewa wasu hawayen na zubowa daga idanunta a lokacin da take tuna asalin mahaifiyarta sannan ta tuna irin rayuwar kuncin da sukayi a baya, ynx ma gashi
irinta sukeyi. .”
“Duk runtsi duk wuya baza tayi irin kalar rayuwar mahaifiyarta ba ,bazata ta’ba zabar namiji ta bar ahlinta ba ,haka zalika bazata ta’ba yarda wani namiji yasanta diya mace ba muddin ba aure sukayi ba ,zata rike mutuncinta da darajarta ta diya mace duk mijin data kawo suka nuna basa so wallahi ta barshi kenan har abada bata da abinda zatai dashi koda kuwa da zinari akayisa ,ba dan komai ba sai dan siyawa kanta mutunci da daraja,shekaru sama da ashiri kenan amman har zuwa wannan lokacin rashin mutuncin dangin mahaifinta ba bar mahaifi yarta ta huta ba ,basu barta ba haka zalika suma ya’yanta basu tsallake rashin mutuncinsu ba .”
“amman duk wa janyowa kanshi ?ta tambayi wankakkiyar kwakwaluwarta tana sake share hawayenta ,inda ta samu waje ta zauna tare da rafka tagumi tana tunanin rayuwa “yanzu aunty haka zaki qarar da rayuwarki batare da kin koma ga ahlinki ba ?”why aunty?!me yasa bazaki koma garesu ba ?”
”me yasa kike jin tsoro ?“mikewa tayi tsaye ta had’e hannuwanta waje d’aya“lokaci yayi aunty ,lokaci yayi da zaki koma ga iyayenki dan dole nasan abun yi.”
A natse hjy zulai ta tura kofar d’akinsa ta shiga yana kwance flat akan gado har zuwa wannan lokacin babu abinda ya cire ajikinsa zuciyarsa banda tuttukin bakinciki babu abinda take a hankali ta soma magana cikin zafin rai "kayi kuskuren Adam kuma dole na fad'a maka haka, wannan cin fuska ne qarara kayi , aikin nan kowa yasani baa yinsa a boye shiyasa kaga naki amincewa amman ka nace ai kaga abinda ka janyo ko ? ya bude idanunshi kadan wad’an da suka dan canza kala ya tsura mata yana sake jin zafi acikin zuciyarsa ,magana yake son yi amman yasan koya bude bakinsa maganar bazata fito ba saboda ‘bacin rai sosai ta dinga masa fad'a kafin daga baya ta koma nasiha "bazan gaji da fad’a maka ba baba qarami matsayin ubanka ne ba makiyinka ba yana son yaga cigabanku ne gabadaya kaga yanayin abinda yake amman na rasa me yasa baka fahimta,me yasa baza ka fahimcesa kuma kaji maganarsa ba?” bai dace ba abinda kake yi masa yana fad'a kana fad'a kuma a gaban d’ansa bana jin dadi sai naga kamar nagaza wurin baka tarbiya ne “
“Wallahi bana jin dadi adamcy ka daina zubar min da mutunci, ka daina yin abinda zaa dinga kallon ban baka tarbiya ba ,tunda tasoma fad’anta bai ce mata uhm ba bare uhm uhm har ta gama ta fita."
*****
Washegari
Knowking akayi har sau uku ajire Aunty hasana dake zaune akan daya daga cikin dining tabke ta mike tsaye tana cewa"waye Ke buga mana kofa haka da bazaiyi a hankali ba yanzu wannan yarinyar ce aka sake buga kofar ,kai jamaa gani nan zuwa ta qarasa ta bude tsaye taga umma sai dai kallo daya tai mata ta fahimci bata cikin haiyacinta "Aunty kece da yamman nan amman ya baki fad'a min dazu da safe cewar kina Kan hanya ba ?” sannnu da zuwa nasan agajiye Kike ?umma ta shigo tare da baba gali a bayanta wanda shima duk ilahirin jikinsa a sanyaye yake " bari naje na kawo miki ruwa ta fad’a tare da juyawa da sauri ta nufi fridge yayinda umma ta samu guri ta zauna .”aunty hasaana ta dawo hannunta rike da cup din ruwa ta mika "Kinsan abinda maryama tayi jiya kuwa ?umma dai ta kar’bi cup din ruwa amman bata kai bakinta ba “yarinyar Ingaya miki bata dawo gidan nan ba sai wajen shabiyun na dare .”
umma ta kalleta tare da yin shiru sai dai kana kallonta kasan ranta a bace yake “ ba wani abu nake nufi ba kawai dai bai dace ace kamarta yarinyar mace tana kaiwa dare a waje ba “ zaka iya sheidawar wanda kake tare dashi kema kuma kinsani maryama bazata ta'ba aikata wani abu da zai zubarwa ahlinta mutunci ba dan haka ki fadi alkhairi ko Kiyi shiru domin kema uwa ce kuma duk uwa ta gari fatan alkhairi take wa yayanta dama wadan da ba nata ba .”umma ta kawo qarshen zance .”
"Allah ya kyauta to ya kika bari yanuwa acan ijesha fatan kin barosu lafiya ?Kafin ta bata amsa baba gali yace "Aunty ki fahimceni dan Allah ?fahimtar me zan maka gali tun yaushe ma abubuwa suka dawo haka bansani ba, yanzu banda naje kamfanin da kenan bazan san halin da kamfani yake ciki ba ?”
”wannan karon fa bazan fahimci komai ba kuma zan iya daukar duk matakin daya dace wai ma duk me haka yake nufi ?wannan ai cin amana ne qarara kuma komai yazo karshe domin kuwa zan tsaida duk wani zalinci da aka dade ana yi "
"aunty !
Aunty hasana ta kira sunanta tana duban baba gali dake tsaye cikin matukar tashin hankali "yaya meke faruwa ne ?”me naji aunty tana fad'a ?"kar dai kai ne duk ka aikata hakan ?muryarsa na rawa ya soma mgn "dan girman allah aunty ki yafe min nasan nayi kuskure amman dan allah ki yafe min ,me ma yasa nayi mata haka ?”ya fad'a yana juya bayansa tare da dafe goshinsa ,"duk qoqarin da take akanmu me yasa zan mata haka ? wallahi ba wai na dauki lokaci ina yin haka bane ,wannan shine karo na farko kuma in sha allahu nayi miki alkwarin bazan sake aikata makamancin haka ba, dan allah ki yafe min aunty ina neman yafi.." "zan yafe maka ne kawai idan na tsaida kai daga abinda kakeyi wanda shi zai sa ka fahimci abinda ka dade kana yi ,ka kuwa san nawa aka nema aka rasa akamfani?"gabdaya kana neman ka karyar mana da busines koma nace ka gama lalata komai ,wallahi ina mamaki ace wai kaine da kanka ka aikata haka wannna abun kunya da ne yayi kama ."?
Aunty hasana ta kallesa a matukar rude "da gaske duk abinda Aunty ta fad'a yaya ka aikata hakan?ya gyada mata mai alamun eh "to gsky koni bana bayan abinda ka aikata ka cutar da Aunty gskiya" ta fda tana kukan karya " duk abinda take mana itace komai namu fa tana kokarin kula damu amman me yasa zakayi haka? me yasa ka cutar daita ? Aunty Aunty!! ta fad'a cikin rawar murya"kar ma ki bata bakinki dan bazan janye kudirina akan ba".
" dan allah aunty ki bashi wata damar bazai sake ba nayi imani bazai sake ba yanzu idan kika tsaidashi aiki dame zai dinga kula da iyalinsa dan allah ki duba yanuwantaka ki yafe ma.."bafa zan cigaba da yafe masa yana cigaba da cin amanata ba hasana kawai dan ya kasance danuwa sai ya dinga abinda bai dace ba ,"wannan shine karo na karshe da zan sake kuskuren maidashi matsayinsa "tana gama fadar haka ta mike ta shige dakinta ."
shiru sukai gabadaya cikin tsananin tashin hankali kafin ahankali aunty hasana ta kalli bayanta"kayi hauka ne yaya ?”me yasa ka bari ta fahimci wani abu ?”yanzu me kake tunanin zai faru ?”Kiyi shiru ki barni naji da abinda nake ji na rigada nayi kuskure bani da kuma abinda zanyi kowa nayi kuskure ko ba haka ba ?yanzu yadda zan samu ta sauko kawai zanyi dan bazan ta'ba yarda da hukuncinta ba idan ba haka ba sai dai afito araba gadon sadam kowa ya kama gabansa karshenta ma na mallaki kamfani tunda ni nmj ne cike da tsoro Aunty hsssna take kallonsa har sanda ya juya ya fita daga parlour'n ."
Shiru baba qarami yayi zaune a parlour'nsa sanye da jallabiya fari sol yana tunanin abinda ya faru jiya gabadaya maganganun ATA yana sake zurfafa tunaninsa har sanda matarsa ta qaraso rike da cup din tea ta zauna kusa dashi "ba dai kana nan har yanzu kana tunanin abinda ya faru jiya ba ?ya juyo ya kalleta bazaki fahimci irin zafin da nake ji acikin zuciyata ba “wai dan damuwa na yana son ya zama tamkar ma Kiyi a wurina wannan abu na min ciwo matuka shi sam bazaa fad'a masa magana yayi aiki dashi ba ban san ina zulai ta samo wannan yaron ba idan ance ga abinda zaiyi shi kuma yace ga abinda yake so shi sam baa isa dashi ba . yaro kamar wanj sheidan gashi uwarsa bata ganin laifinsa "karka fadi haka ta mika masa cup din tea data shigo masa dashi "tabbas Adam bai kyauta ba kuma yana da taurin kai amman kuma zulai na kokari akan taga ya sauka akan wannan tsarin nasa wallahi ko jiya ba qaramin bude masa wuta tayi ba kuma bata goyi bayansa ba akan abinda yayi amman kasan wannann yaron yasan Kan business sosai “nasan haka “.
“Kasan haka amman me yasa kake jin haushinsa akan komai ?”to shi me bazai tsaya akan tsarinmu ba? abinda yake yi ba daidai bane cin amana ne "duk fa abinda kake tunani akansa ba haka bane kuna son cigaba kamfani Adam ma haka koma nace yafi ku kuma nasan komai yayi yayi dan cigaba kamfani ne matsalar dai ta sultan ce ya kamata ka fahimci haka dan ni bana bayan karya ,Eh na yarda da haka amman shi wannan business din baya bukatar mutun yayisa shi kadai tunda ba haka aka fara ba tun mahaifinsa na raye komai tare akeyi kuma yasan da haka me yasa zai dawo daga baya yayi haka dole nasan yayi haka ne da wata manufa sanin manufar ya rage mana kada yayi abinda yayanmu zasu shiga damuwa ".ya kamata kasan wani abu Adam bazai ta'ba barin wani mummunar abu ya same kamfani ba “Ke yanzu kina ganin abinda yayi daidai ne ?”
“Aa ni bance haka ba san nasan kuskure ne yayi business din cikin sirri batare da sanin kowa ba hakan ya sabawa dokar kmafani amman kai kuma kayi over react jiya sai mahaifiyarsa ta dauka saboda danka kayi haka, amman fa kasani Adam ya sadaukar da komai nashi dan yaga kamfaninan ya tsaya da kafafunsa kuma kai kasani nasani dan saboda muni ne gbdy yake yin haka ,da dan ta sauran ne da yanzu babu wannan kamfanin kawai dai ni nasan bazai yi komai ba kuma bashi da wata manufa akan haka kamata yayi ka zaunar dashi kayi masa bayani yadda kake son ya dinga tafiyar da komai ,yau ko dan daka haifa sai kabi shi a hankali bare dan da ba naka ba, amman kai duk kuskuren da yayi sai kace acikin mutane zaka masa mgn to me yasa shima bazai dinga maka kallon makiyinsa ba ?"
“Ina son ka yarda wannan kamfanin ya samu cigaba ne saboda shi idan ma baka yarda a fili ba ka yarda da hakan acikin zuciyarka kuma kowa yasan hakan yau da zai cire hannunsa ya tattara hankalinsa akan nashi kamfanin komai zai iya faruwa dan acikin yaran nan babu wanda zai iya da kamfani ka yarda ko karka yarda yana cire hannunsa kowa sai yasha wahala acikin kamfanina nan "yanzu ni me zanyi kenan yaron nan fa ya rigada ya gama rainani ?
“abinda zakayi yanzu idan yayi maka laifi ka zaunar dashi Kmr danka ka fahimtar dashi kagani idan bazai maka biyayya ba, kayi kuma tunanin abinda na fad'a, kawai ka kasa tsayawa ne ka fahimcesa saboda abinda ya faru .”ka cire son rai idirs adam yaron kirki ne dan da zaayi alfahari dashi ne fiyye da kowa acikin family .”
“kuma nagartarsa yasa kake son had’a aurensa da hindu .”da lokacin da yace bai sonta ka hakura da yanzu komai yana tafiya daidai daka tsira da mutuncinka ,sannan diyarmu tana tare damu amman ka dinga biye mata kana karfafa mata gwiwa har tayi yunkurin kashe maryama wanda hakan yasa aka samu damar daura mata laifin da ba nata ba yanzu wa gari ya waya ?”wallahi mu dinga cire son zuciya muna fadawa kanmu gasky ka duba lamarin nuzla da mahaifinta ya biye mata da yanzu an ta’ba daya goma bata gyaru ba amamn kai ka dinga biyewa hindu so hauka ne da zatai yunkurin kashe yar mutane ?”ai duk sharrin daaka bita dashi daidai ne ni na wuce amamn ka zauan kayi nazarin maganata da kyau wannna tashin hankalin babu abinda zai haifar sai qarin kiyayya wallahi sam bakayi wa mahaifin adam adalci ba dan nasa kwaya daya zaka maidashi makiyinka abinda shi bazai ta’ba yi maka ba kenan .”tana gama fadar hk ta juya ta kama gabanta baba qarami yabi bayanta da kallo ” daman ita haka zuciyarta take sam bata goyon bayan karya koda kuwa akan kanta ne kuma tabbas yasan gsky ta fad'a masa sai dai me zai yi yanzu ?” ya cigaba da zama a wajen yana tunani maganganunta."
Mmn Sudais
[8/31, 11:25 AM] Safwan Libiya 2: 💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
BOOK 3
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 27
Gabad'ayansu a tsaye suke acikin office dinsu fuskarsu d'auke da murnar samun nasarar da sukai
a jiya inda madam some ta zagayo ta tsaya kusa da maryama tare da dafa kafad'anta tace "duk wannan cigaba mun samu ne saboda ke . maryama ta saki kyakkyawan murmushi wanda yayi matuqar bayana kyawunta sannan tace " karki ce saboda ni ,nasarar gabadayanmu ce, kuma kowa acikinmu tayi kokari .
"kowance daga cikinmu ta cancacin yabo na mussa man tunda tare mukayi, wannan cigabanmu ne gbdy. ". sukai murmushin jin dadi suna sake yaba mata "amman fa duk da haka kin cancanci a miki ban girma ,kuma kinsan wani abu ?maryama ta girgiza mata kai tana cizan lip's dinta na qasa . "yanzu gbdy a kamfaninmu kece sama da kowa kuma kece wacce tafi kowa iya tsara zane mai d'aukar hankali you're the best maryama ."
"maryama ta sake yin murmushi batare da tace uffan ba ."sultana dake zaune tunda suka soma maganar bata ce komai ba sakamakon jin haushin babu ita ciki presentation din , sai dai aranta tace "in sha allahu wannan dariyar da kike yi sai tazame miki damuwa arayuwarki .
Ahankali yusura tayi taku ta nufo inda maryama take tsaye rungume da hannuwanta duka a qirji tace "ai sani ne bakuyi ba wannan nasarar ba komai bace a wajen maryama ,ai nasara a koda yaushe tana biye daita ,duk abinda tasa gaba sai tayi nasara, ba akan aiki ba kawai , ko akan karatu haka take akwaita da kwakwaluwa ko lokacin da muke karatu first class take d'auka ita din yar baiwa ce "karki manta ni din marainiya ce ta gaskiya tun da na bud'e idanuna na ganni acikin maraicin kinsani mahaifina ya rasu tun ina yarinya kakata data rungumi maraicinmu da kyau take nuna mana qauna muraran sai dai itama bamuyi tsawon rayuwa daita ba ta rasu kinga babu yadda zanyi dole na jajirce nayi karatu "duk da haka maryama ke din yar baiwa ce ,"kunga mu bar mgnr haka muyi aikin dake gabanmu kafin mr ata ya shigo ya fara rikita mana lissafi ". inji cewar maryama ."gabad'ayansu sukai dariya tare koma mazauninsu kowacce ta soma aikin dake gabanta .”
Alamun kira ne ya shigo wayar maryama adaidai lokacin da take qoqarin zama ta kai kallonta ga wayar tana duba number dake yawo a screen din wayar "number da ake yawon kiranta dashi ne wanda ta d'auka ko sultan ne sai dai daga baya ta fahimci bashi bane "dan ta nemi numbersa taga ba iri daya bace, ta d'aga kiran tare da yin shiru daga can bangaren ma shiru akayi ana sauke mata numfashi acikin kunnenta dan tana jin sautin saukarsu ahankali ta fara taku ta nufi kofar fita daga cikin office din yayinda sultana ta zuba ma bayanta ido ganin yadda take bada step tana rausaya abun burgewa yarinyar tana da shep na d'aukar hankali ,ba lallai kowani nmj ya ganta ya iya hadiye miyonsa akanta ba".maryama ta numfashi kana ta cire wayar a kunneta ta duba har lokacin mai shi yana kan layi sai dai babu alamun wannan saukar numfashi muryarta can kasan makoshi tace "hello !sai dai shiru taji babu amsa .
"hello wake magana? "ta sake yin mgn still dai shiru ne ya biyo baya kusan second biyar babu alamun zaayi magana dan haka tayi disconnecting din kiran ta nufo office tana tunanin kiranta daakayi mata kwanakin uku da suka wuce akace mata daga office ne wai tazo da wuri bayan tazo din kuma taji shiru bata ga kowa ba sai mr ata wanda tayi imani ba muryarsa bane ,to waye ya kirata ?"waye wannan da yake son dagula mata lissafi ?"ta furta a kasan ranta tare da samun guri ta zauna ta kasa aiwatar da komai tana sake zurfafa tunaninta lallai ya kamata ta nemi mai wannan number da yake kiranta taji dalilinsa na kira wayarta yana damun rayuwarta ."
Ahankali tai dealing number a qaramar wayarta ta shiga neman layin sai dai ba'a d'aga ba tana cikin wannan halin mr ATA ya shigo office din yayinda kwayar idanunshi ke kanta sai dai ganin hankalinta na kan wayarta yasa shi d'auke idanunshi akanta ya soma mgn a natse akan qokarin da sukai jiya "naji dadi sosai da qoqarinku na jiya na jinjiwa kokarinku "sir ai ina tunanin maryama ce ta cancanci haka,dan gsky ta cancanci jinjina har ma da especially thanks ".inji cewar madam some "ta fad'a tana murmushin farinciki .”
asukwane ya kalli inda take zaune inda tayi busy sosai wajen bincike layin daake damunta dashi a truecaller tana son taga da wani suna akayi registrater layin sai dai wani birkitaccen suna ta gani ."mr ata yayi shiru yana kallonta a tsanake yana nazarinta dan tunda ya shigo ya soma magana ya fahimci bata tare dashi,haka hankalinta yana wani guri dabam ya cigaba da kallonta kafin a hankali yayi taku biyu ya dawo kusa daita sosai yana kallon cikin wayar dake rike a hannunta still dai bata maida hankalinta garesa ba." abinda yafi tsana kenan daga gareta ta ganshi amman tayi kamar bata gansa ba aranshi yace ko number wa take kira hk "?amman a zahiri muryarsa a kausashe yace "some ke kinfi kowa sani ina bawa wad'an da kad'ai suka d'auki aikinsu da mahimanci ne lokacina,yayinda ita wannan macece da bata bawa aikinta mahimanci any way kizo kisame a office akwai ayyukan da zamu yi magana akansu yana gama fadar hk ya juya ya fice ."
Mr ata yana fita office dinsa ya koma ya zauna akan kujera yana juyi sai dai hankalinsa da nastuwarsa suna gareta ." yayinda ita kuma tayi busy gurin son gano ko waye yake son damun rayuwarta yana kallonta tasa wayarta ta dafe goshinta wanda daga gani ta rasa mafuta ne yasa tayi haka "to me yasa ba'a d'aga kiran ?"kuma idan ban kira ba bazan san kowaye ya kirani a akwanakin baya da km daren shekaranjiya har ma da yau din nan lallai ya kamata nasan kowaye daga cikin ma'aikatan kanfanin nan sosai mr ATA yake son yasan damuwarta." yana zaune a office dinsa amman kwayar idanunshi na kanta har sanda sultana ta shigo office din tana kiran sunansa wani irin mugun kallo ya jefa mata wanda yasa tayi saurin cewa”oh sorry sir congratulations sir duk da dai ni baa sakani ciki presentation ba wanda bansan ni laifin me nayi ba daaba sakani ba “wani irin matsefaffen haushinta yaji ya taso masa tun daga kahon zuciyarsa har zuwa kan fuskarsa sai dai bai yi magana ba ya cigaba da juyi akan kujera yana sake maida hankalinsa ga sarauniyarsa ."
ta sauke naunayen ajiyar zuciya kana ta cigaba da magana tana kallonsa "ko zan iya sanin dalili da yasa ni baa sakani ba bayan nima maaikaciyar kamfani ce kamar sauran ma'aikatan kamfani ?"irin Kallon da yake mata ne yasa gabanta ya dinga faduwa "I think kinzo office dan Kiyi aiki ne ?ta gyad'a masa kanta cike da rauni "okay pls kije kiyi aikinki ."wai dan Allah mai yasa ya Adam kake min hk Kmr ni ba jininka bace ?komai nayi sai ka nuna ni din ba kowa bace agurinka ,kasani wannan ba daidai bane this is not right ya Adam ko dan kaga na damu da kai ?"shiru yayi tare saisaita kanshi “kana yi kamar baka san me nake nufi ba alhalin kasani
“ka kuwa san irin son da nake maka ?"saboda kai na .." "actually get out ". ya fad'a a matukar fusace yana nuna mata hanyar fita da yatsan hannunsa d’aya tare da kiranta da nonsense."ranta a matukar bace ta fito da sauri tana goge hawayenta ta wuce maryama tsaye wacce kusan duk taji wasu daga cikin maganganunta ."
Cike da tausayawa maryama ta kira sunanta har sau biyu sultuna!sultana !!sai dai sultana bata tsaya ba sai ma qarasa wucewa da sauri tayi ,kai tsaye marayama ta bar abinda take ta juya ta nufi kofar office dinsa tana cewa "may I coming sir ?sai daya sauke naunayen ajiyar zuciya jin sautin muryarta mai sanyi sannan yace "coming !”dan tun safe bai ji muryarta ba sai yanzu ta shigo cikin office din a natse ta tsaya agabansa tana kallonsa a lokacin yana duba wani file dan haka bai dago ya kalleta ba ta cigaba da kallonsa a tsanake “kyau iya kyau ai dole mata su rikice akanka ganin ya shareta kuma tasan halinsa idan zata shekara tsaye matuqar bayi niyyar yin magana ba bazai mata ba .”dan haka muryarta a sanyaye tace "sir ina son nayi magana da kai ko zan iya ?”shiru yayi batare daya dago ba har ta cire da zai yi magana sannan ta jiyo sautin muryarsa acan kasan makoshi “uhm go and ahead “.
“Dan Allah sir me yasa kake yawon yiwa sultana ihu ko hantarrta fiyye da kowa acikin ma’aikatar nan alhalin ita din yaruwarka ce ta jini ?yana jinta amman yaki yin magana sai ma ajiye file din hannunsa yayi ya d’auki wani ya cigaba da dubawa "a zahirin gsky babu kyau abinda kake mata ai ko babu komai ita din jininka ce, kaga koma meye a tskaninku bai dace ka dinga disgata irin haka ba .
an ji mu idan ka mana ba wani abu bane kasancewar mu din ba komai bane a wajenka, amman ita kamata yayi ka manta komai idan ma akwai abinda tayi maka ka jata ajikinka "."ke wacece da zaki min wannan tmbyr ?" shiru tayi tsabar kunyar data mamaye ilahirin sansar jikinta Kmr ta nitse qasa haka taji ".sai daya gimtse ya murtuke fuska cikin tsare gira sannan ya sake maimaita mata tambayarsa "wacece ke tukunna ?"shiru maryama tayi ta kasa cewa komai duk da tasan zai iya aikata abinda yafi haka .”
“cikin ni dake waye ya rike past dinsa ya kasa manta komai “?ke da kika kasa manta abinda ya wuce a rayuwarki zakizo kina fadawa mutane nonsense and rubbish ".yayi mgnr yana tsareta da tsumammun idanusnhi masu matukar firgitarwa .“cikin ni da ke waye ya rike past disa fad'a min da har zakice na manta komai na jata ajikina ?"zuwa wannan lokacin ranta a matukar bace take kallonsa har ya rufe bakinsa ". "daman kana sane da past dina ne ?tai masa tamabayar zuciyarta na wani irin tsinkewa .
yay shiru yana kallonta d'an bashi da amsa da zai bata "koma dai menene zaka iya bata chance sir saboda soyayya tana bukatar kulawa kuma duk lalacewa kaso mai sonka sannan kayi amfani da damarka dan sultana na matukar sonka ." tana gama fad'ar haka ta juya har tayi taku biyu ta jiyo Amon muryarsa cikin yanayi na tashin hankali "wannna shine tunaninki "ta tsaya cak tare da juyowa tana dubansa kafin ahankali ta qara taku biyu ta yadda zai iya jinta sosai ".
“Bai wai shine tunanina ba, haka ne tana sonka kuma har ta furta hakan a yanzu wanda ni bansan sau adadi nawa tasha furta maka tana sonka ba amman dukkanin alamunta sun nuna .karka ga wai dan kana da kyau da kudi tare da nasaba kanemi ka wulakanta mutumin da ya damu da kai dan so .."are you still arguement with me?ya fad’a hk ta hanyar dakatar daita tayi shiru tana kallonsa taba jin wani irin mummunar fad'uwar gaba mai tsanani ."
Tana kallonsa cikin yanayin na jin kai ya mike ya tura kujerar da yake zaune akai baya kad'an ya fara taku zuwa inda take tsaye cikin tsananin tashin hankali taja baya da sauri jikinta na dan kyarma ya sake matsota sosai kamar zai rungumeta ajikinsa har suna iya jiyo bugun zukatansu cikin tsuma da karkarwa maryama tasa hannuta d'aya ta tokare qirjinsa dashi ji tayi kamar ta daura hannunta a saman dutse nan da nan ta soma furta kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ,hasbunallahu wani imal wakil acikin zuciyarta.”
cikin d'an d'aga murya ya soma magana "ai nasani nasan ke kadai ce zaki iya wannan karfin halin ina fad'a kina fad'a ba .?"jikinta yaji yana rawa a saman qirjinsa ,naunayen ajiyar zuciya ya sauke sannan ya soma ja da baya tare da dauke kwayar idanunshi akanta yana mata gargadi da idanunshi ya koma mazauninsa ya maida hankalinsa kan laptop dinsa muryarsa can kasan makoshi yace "ba laifinki bane nasan dalilin dayasa kike min haka "me ka fad'a sir ? I don't know kuma karki qara tamabayata ."yayi maganar yana sake gargadinta da kwayar idanunshi sannan ya sake kai idanunshi ga laptop."karkayiwa mgnr wata fassaran dabam ni dai kawai na baka shawara ne dan ka gyara ina ma mata zasu kasance irina ?"dan ni bana daga cikin matan da zasu tsaya batawa kansu lokaci akan nmj ".
“really?
ya fad’a tare da dago kanshi yana dubanta muryar a fusace "ke da kika kasa manta mutumin daya mutu arayuwarki saboda son da kike masa shine zakice bakya daga cikin matan da suke iya bata lokacinsu akan nmj"? kenan ke din ba mace bace ? ko kuma ke din makaryaciya ."ta bud'e baki zata sake magana taji sautin muryarsa yace "go ....."mutuwar tsaye tayi,ta saki baki tana dubansa har sanda ya sake cewa "I saida go back to your work." ta juya da sauri ta fara tafiya "kai mr ata mugun mutun ne ,a gaskiya sultana baki yiwa kanki adalci ba ko kuma nace zuciyarki ta cuceki irin wannan mutumin zaki so “? Kwata kwata mutun bai da fahimta Jifa daga fad'a masa gaskiya ya hau kan mutun yana qoqarin razana mutun har yasa hanjin cikina ya fara hautsenewa ta qarasa fitowa tana bugo masa kofar da karfi ."
Shi kuwa mr ata tana fita wani irin dariya ne ya taso masa tun daga kasan zuciyarsa har zuwa kan lip's dinsa na kasa a zahiri ma kana iya hango hakan a tattare dashi dan kasa rike dariyar yayi "uhm tana cikin rukunin mata jarumai ,sannan karfin halinta na matukar burgesa most especially dakiya, gata da shegen tsoro amman tana qoqarin gurin dannewa ta fad'a min mgn son ranta lallai ba a banza zuciyata ta rasa sukuni akanta ba, daman kuma an halicceta ne dani ,duk abubuwa da yake mata yana mata haka ne saboda ya auna gudun zuciyarta akanshi kuma ya gano adadin gudunsa da alamun nan kusa zuciyarta zata makance a soyayyarsa ,shi din kwararren dan kasuwa ne sannnan kuma kwararren mai gane shaukin só né a karon farko aka fad'a soyayyarsa tabbas zai gane duk da cewar tana da jarumta amman kuma akwai burbushin tsoronsa da qaunarsa acikin kwayar idanunta "marayama kenan rigima zalla ko ina ruwanta da matsalar wata ?ban da rashin sani irin nata ina ita ina bawa wata damar ta so abinda zata so daga baya ."
flaks cup din tea ya d'auka ya kai bakinsa yana kurba ahankali yana kallonta tana kai kawo "me yasa ma na shiga harkar wannan mutumin taja tsaki tana rike kanta "wallahi yau ya gama bata min rai ta fad'a a fili tana furzar da iska mai zafi tana cigaba da sake neman number "cikin saa aka dauka akace " hello daga can bangaren "he..hello maryam ta furta cikin rawar murya bai bari tayi mgn ba ya cigaba da nashi mgnr "allah yasa kece mai wayar nan ina ta kiranki kina tare da saurayinki ko mijinki ne ni dai bansani ba na fad’a miki kin yarda da wayarki amman baki tsaya ba yanzu ina zanganki na baki wayarki maryama tayi shiru tana jinsa har sanda ya dasa aya ,kawai ta tsinci kanta da ce masa kana ina yanzu?" ta fadi haka ne saboda ta gano wanda ke damunta da kira yace"Ina nan Ikeja ta wajen jara shopping mall "wai muna da d'an nesa dan ina wajen aiki amman da ace daga gidanmu bamu da wani nisa amman ko zaka iya kawo min wayar wajen aikina sai na baka kudin mota har ma da qari ?"okay babu matsala a ina awajen aikinki yake ?."nan take maryama ta fad'a masa sannan ta koma cikin office tana zance zuciya.”
Bayan awa biyu mr ata ya shigo office din a natse gabadayansu suka natsu suna sauraran bayaninsa bayani yake masu akan nan da sabon wata zasu bar wannan kamfani zuwa wani dabam su cigaba da gudanar da aikinsu amman hankalin maryam naga kofar shigowa jira kawai take taga daya daga cikin securities yazo kiranta ,muryarsa a dake ya kira sunanta "maryam! ta juyo da sauri tana dubansa tare da cewa "sorry sir! ya lumshe idanunshi ya cigaba da masu bayani still dai ta sake maida hankalinta zuwa ga bakin kofa tana wasa da yatsun hannunta can sai ga d’aya daga cikin security yace "wacece maryama hussein ? batare daya shigo ba bare yasan ko mr ATA yana gurin " nice !" ta fad'a da sauri ga wani can a waje yana neman ki ,okay na gode ta juya ta kalli mr ATA a tsanake tace "excuse me sir zan dan ga wani a kasa yanzu zan dawo "waye shi ?ya tmby ransa a matukar bace yana tsareta da kwayar idanunshi "wani ne!” ta bashi amsa atakaice "ba zaki koina ba ,ko bakiga abinda muke yi bane?na gani sir amman wannan kiran yana da matukar mahimanci “ta fad'a tare da wuce abunta .yayi shiru yana binta da wani kallo mai tattare da zallar kishi ma’aikatan dake zaune a gurin babu wanda bai girgiza da abinda maryama tayi ba ."
Ayi hakuri dashi
Mmn sudais
[8/31, 11:25 AM] Safwan Libiya 2: 💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
BOOK 3
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 28
Ahankali mr ata ya cigaba da kallon bayanta tana wata irin shegiyar tafiya mai bugar da zuciya, tafiya ce dake mantar da zuciya duk wani tarin damuwar dake tattare daita sai dai shi a bangarensa hakan bai sa ya daina jin zafi da rad’ad’in abinda tai masa a yanzu ba ,dan wani irin matsefaffen kishinta da soyayyarta ne ya had’e masa waje d’aya sannan yake bin dukkanin sansar jikinsa ”wai excuse me sir zan d’an ga wani a kasa yanzu zan dawo " maganarta ta dinga masa yawo acikin kwakwaluwarsa “waye shi din da zataje ta gani ?ya sake tmby kanshi,kamarshi za’a yiwa haka ?”tun sanda ma’aikata suka fara zama qarqashin ikon mahaifinsa har zuwa kanshi babu wani mahaluki daya ta’ba masa abinda maryama take masa a matsayinta na maaikaciya dan a ajiye batun na soyayyar da yake mata gefe tunda har yanzu bata ma san yana mutuwar sonta ba “.wani irin yanayin mai zafi ya ziyarci zuciya dama gangar jikinsa, zuciyarsa ke masa zafi sosai wanda a zahiri kallo d’aya zaka masa ka fahimci halin damuwar da yake ciki yayinda zuciyar madam some ke cike da matsanancin tsoro da firgicin abinda zai biyo baya dan yau kam maryama ta tsallake limit dinta dayawa kuma tasan mr ata farin sani bazai ta’ba mata hakurin wannan sakacin nata ba dan matukar kaga yanayinsa yayi haka akan maaikaci tabbas kora ne zai biyo baya idan kuma kayi saa bai koreka ba to ka kwana da shirin zai dakatar da kai aiki na wasu satittika .”
“a matukar rikice madam some ta kwallawa mryma kira adaidai lokacin da take qoqarin shiga lift tace "meye haka maryama maza maza ki .."saurin d'aga ma madam some hannu yayi yana furzar da numfa shi mai zafi daga bakinsa ,lallai lokacin dakatar da maryama aiki yayi a wannan ma’aikatar.” madam some ta fad’a aranta inda bangaren mr ata shi kam ba wannan ne acikin ranshi ba, zancen zuci yake inda yake ganin ya kamata ya nuna wa maryama menene so ta yadda zatai masa soyayya mai zafin da bazata cigaba da son waninsa ba bare ma ta saurari wani “lallai zai sake nunkaya daita wata duniya wadda ma'abota so da shauki ne kad’ai suka san zakinta .”ahankali madam some ta soma bashi hakuri "please sir kayi hakuri zan mata magana bazata sake aikata haka ba I don’t why maryam always play with her work ta fad’a cike da tsoro .”
wani dogon numfashi ya sake saukewa yana sake jin zafaffar qaunarta da kishinta nabin jinin jikinsa yana mutuwar son maryama kamar ranshi shi kanshi yana mamakin zazzafar soyayyar da yake ma maryama mai tafiyar da dukkanin wani motsin na bugun numfashi, a yayinda kishi da soyayya ke kutimemeniya da mr ata ita kam maryama na cikin lift tana Allah Allah ta sauka ta amshi wayar dan wannan ce hanya mafi sauki da zata gane wanene yake son yin wasa da rayuwarta .”
A bakin makeken get din ma'aikatan ta samu mutumin tsaye ,ya mika mata wata takarda mai ruwan kasa “sai dai kamar ba fuskarki na gani ba alokacin da kika yarda da wayar ba ?”eh bani bace yar’uwata ce ta fad’a haka ne dan kar ya fahimci wani abu .”kai gsky wannan yar’uwartaki bata da natsuwa inata kiranta amman sam taki tsayawa ta saurareni tana ta faman zubawa mijinta ko saurayin ta ne bansani ba bala’i tare jan hannunsa . mryma tayi shiru tana saurarensa tare da nazarin maganar sa .kuma at the same time tana danna gefen wayar .
hoton fuskar budurwar da tazo gidansu da suna taaziya wacce har ta bukaci takardun project din da sukai da yaya sadam ce taga ya bayyana a screen din wayar ,nan take gabanta ya fadi dan haka ta tsinci kanta da cewa "ya mutumin da ka gasu tare yake "uhm dogo ne sosai sai dai baki ne yana da suma akansa kad’an.”yana da dogon hanci ?maryama ta tamvayesa “no gsky banga fuskarsa ba bayansa na hango amman dai naji yarinyar ta kirasa da wani suna ban dai rike sunan ba gsky "ko sadam kaji tace ?gsky bazan iya tunawa ba ,sauri nake madam dan akwai inda zani .”
Maryama ta ciro kudin mota datai masa alkwari har ma da qari ta bashi ya wuce ita kuma ta juya zuwa ciki ,wanda zuwa lokacin tuni sun gama meting wasu daga cikin maakatan sun dukufa aiki .”ta zauna shiru tana tunani ,kira ne ya shigo wayar da mutumin ya kawo mata yanzu gabanta na fad’uwa ta d’aga batare da tayi magana ba "hello hello!! muryar namiji taji muryarta a hankali tace “hello da wa nake magana ?”daga can bangaren akayi shiru ,can kuma aka kashe wayar ."maryama tayi shiru tana tunanin muryar da taji a yanzu dan haka gbdy kusan yinin ranar mryma kasa samun natsuwar zuciya tayi bare tayi aikinta.” cike da tsinkewar zuciya ta maida wayar cikin takarda da take ta bud’e wata durowa ta ajiye takarda ta koma ta zauna tana tunanin me yasa akayi amfani da layin anifa wajen kirata kuma aka ce tazo aiki da wuri ?”wannan amsar take nema kuma lallai babu inda zata samu wannan amsar sai abakin wannan budurwar data kira kanta da anifa “ a ina zanganta?” ta ina ma zan fara nemanta ."ta jerawa kanta tambayoyin da bata da amsa sai abakin anifa ."
Madam some ce a tsaye kusa da mr ata hannunta rike da fine mr ATA yana mata bayani abinda zatai byn ya gama yace kin fahimceni tace "yes sir!”tana sake bashi hakuri akan abinda maryama tayi tare da bashi tabbacin zata daina bazata sake ba mr ata ya bar abinda yake tare da tsura mata ido kawai yana nazarinta a fahimtarsa itama tana qaunar maryama kuma bata son ta bar aiki a qarqashinsu numfashi ya furzar yace “by the way ban san abinda ke damunta ba amman ko kinsan abinda ke damun maryam yau ?”gsky bansani ba sir ko na tmbyeta ne ?no bance kiyi ba kije ki cigaba da aikinki .”ta juya ta fita cike da murna ganin har ya sauko da alamun mryma ta kuma takar sa’a a zuciyar mr ata tun gashi ma bata laifin datai masa yake ba ,damuwarta yake da bukatar sani .”shiru maryama tayi akan kujera ta had’e hannuwanta biyu guri daya ta dafe habarta dashi tai zurfi cikin tunani .”
Mr ata ya d’an waigo a hankali ya kalleta zaune shiru ya d’auke kwayar idanunshi akanta yana lumshewa yana jin duk babu dadi aransa yana nan tsaye har sanda madam some ta sake shigowa office dinsa da file biyu ta bude tana nuna masa inda zai saka hannu byn ya gama ya kira sunanta “some !”ta amsa masa da yes sir “ko kin tambayeta ?what sir?” yayi shiru yana jin fad’uwar gaba “what should I ask her ?”ta sake tambayarsa dan ita ta manta maganar da sukai dazu "maryama !"A'a ai kace kar na tambayeta “yes haka nace ba wai dan nasan damuwarta bane Aa kar damuwarta ya shafi business dina ne wad’an can kaya ki bari a had’asu da guri d’aya sannna idan kin fita kicewa maryama ta shigo tasameni yanzu “okay sir !” ta fad'a tana juyawa ."madam some ta tsaya akan maryama tare da kiran sunanta “maryama!” ta dago a firgice tana mikewa tsaye cike da girmamawa tana cewa” yes ma “.
“munyi meeting d’azu amman na lura gabadaya
hanakalin ki baya tare da sir amman bari na tura miki duk abinda muka tautauna akai “okay ma na gode"meke damunki maryama?” idan akwai wani abu da yake damunki ki fad’a min”? shiru tayi kafin ahankali tace “ babu komai ma iam completely oright ma “okay ki samu wani abu ki dan ci sannan ki maida hankalinki akan aiki "okay ma thank you so much ma ".sai abu na gaba sir yana bukatar ganinki okay ma .”madam some ta nufi kofar kasa aiwatar da komai tayi ta mike ta fita zuwa office dinsa sai data sauke numfashi sannan tace “sir may I coming ?”coming !” ta shigo yana zaune akan daya daga cikin kujerun office yana daddana laptop a hankali ta maida kofar ta rufe jiki a sanyaye ta qaraso ta tsaya kusa dashi "sir gani ."
“Wani kamfani da muka saba business dasu tun kafin ki fara aiki damu suna bukatar ganin new design dinmu ko kina da wasu akasa ?yah yah ta fad'a tana gyada masa kai alamun “eh! ,"desings masu matukar daukar hankali kamar masu yanayin irin wadan da mukai presentation tace “yes sir!”okay zamuje tare dake mu gana dasu yau amman kafin nan bari na nuna miki wasu desing’s din da wani kamfani yake bukata amman shi sai zuwa next week tace “alright sir “.magana kawai take amman kashi 50 na natsuwarta basa garesa .ya mike tsaye ya qarasa kujerar dake fuskantar wanda yake zama tare da laptop ya daura akan table ya ja kujerar ya zauna yana cewa “maryam matso kusa” ta zagayo zuciyarta na rawa dan gsky hankalinta a matukar tashe yake ta tsaya kusa dashi sosai tare da rakwafowa ta daura hannunta daya akan table desing din wondo da Riga na maza ya fara nuna mata sannan ya dauki wani takarda ya bude still yana nuna mata amman ita sam hankalinta baya gurinsa yana can waje tunani ya dauki tsawon lokaci yana mata bayani amman na banza saboda babu kalma daya daya shige cikin brain dinta “ina da tabbacin idan suka ga irin wanda muke dasu zasu so su qara .”
dukowa tayi sosai idanunta na kallon wani guri har gefen mayafinta datayi rolling din kanta dashi ya makale ajikin karfen suit din da yake sanye dashi kasancewar akwai manyan stone ajiki “maryama !”ya kira sunanta a harzuke yana rufe laptop dinsa da qarfi "yes! yes sir !! tayi maza ta dawo haiyacinta da sauri zata mike tsaye ta kasa sakamakon mayafinta daya makale ajikinsa "ta soma kokarin cirewa tana bashi hakuri “kayi hakuri sir bansan yaakayi ba sai dai rawar da jikinta yake yasa ta kasa cirewa dan haka ya soma kokarin ya cire itama tana qoqarin ta cire duk ta rude sai hakuri take bashi "maryam !”ya sake kirata a tsawace “kin dameni da ban hakuri ki bari na cire tunda kin kasa cirewa ya fad’a tare hadawa da tsintsiyar hannunta ya rike yayinda idanunsu ya tsarke cikin juna yana kallonta cike da tsantsar qaunarta ita kuwa a matukar tsorace take kallonsa .”numfashi ya sake sakamakon jin jikinta da yayi ya dauki zafi ya sake tsareta sosai da idanunshi yana son yasan damuwarta dan tunda ta fara aiki dashi bai ta'ba ganin yanayinta haka ba sai yau .”
ta kalli hannunta dake rike cikin nashi tayi sauri ta cire tana shafa tsintsiyar hannuta ta cigaba da tsayuwa tana jiran ya cire mayafinta har ta bude baki zatai magana yayi saurin daga mata dan yatsansa alamun tai masa shiru ,ahankali ya cire da karfi yana furza da iska mai zafi daga bakinsa sannan ya mike ya tsaya yana fuskartata sosai dan har yana iya jiyo saukar numfashinta "what's the matter ?”nothing sir! ta bashi amsa tana sauke numfashi da kyar saboda kusanci da suka samu sai da yayi mata kallon second goma sannan ya cire idanunshi akanta yana kawar da kanshi gefe tare da zagayowa ya tsaya abayanta yana sauke mata numfashin bakinsa "meye damuwarki ?” shiru tayi qirjinta na bugawa da sauri sauri “ko zaki iya fad'a min damuwarki ?”idan zai yiwu ina son nasani ?.ahankali ta juyo suka fuskanci juna ido cikin ido suke kallon kwayar idanun junansu muryarta a sanyaye tace “sir ai baka bada wannan damar ba ,babu wata damar daka bayar ayi maganar wani abu daya danganci matsalar wani bayan ta aiki?” bance ki tsaya fad'a min wani kaidodin aiki ba ki fad'a min abinda me damunki "?shine abinda nake bukata yanzu .”yayi maganar yana sake motsata.”
Mmn sudais
[8/31, 11:25 AM] Safwan Libiya 2: 💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
BOOK 3
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 29
Kallonta ya shiga yi tun daga foring head dinta har zuwa d'an qaramin bakinta kafin ahankali ya kai yatsan hannunsa kan pink lip's dinta ya fara shafa wa ahankali ahankali yana kallon cikin kwayar idanunta yana sake maimaita tambayar da yayi mata "maryama fad'a min abinda ke damunki "?cike da jin fad'uwar gaba tace "babu komai sir idan ma akwai karka damu da matsalata na gode sosai da kulawar ka," ta fad'a tana kawar da fuskarta gefe zuciyarta na bugawa da sauri sauri ,kamo fuskarta yayi ya had'e da tashi yana wurga mata harara mai tattare da zallar qaunarta had'e jan dogon hancinta "tell me maryama i want to know your problem's ".ya fad'a a can qasan makoshisa "babu komai sir duk yadda yaso yasan damuwarta amman taki. shiru mr ata yayi yana kallon kyakkyawar fuskarta zuciyarsa cike da tsananin tausayinta ya sani da wata acikin ma'aikatansa yayiwa wannan tamabayr cike da kulawa lallai zata fad'a masa fiyye da damuwarta amman gata ita ta kasa fad'a masa "ko wani irin zurfin ciki gareta haka ?yayi tambayar acikin ransa. "yasan akwai tarin damuwa atattare daita amman ta kasa fad'a masa abinda ke damunta “ina ma zata fad'a masa damuwarta da babu abinda zai hana bai magance mata ba, dan zuciyarsa bata son ganinta cikin damuwa."
Ahankali maryama ta zame jikinta daga nashi tana cewa "na gode sosai sir " babu bukatar ki gode min fatan kin ga desings din dana nuna miki yanzu kuma zamuje mu hadu da wani abokin business dinmu zuwa anjima “ shiru tayi na second goma kafin ahankali muryarta ta fito. "sir me yasa sai tare dani zaka bayan akwai tarin ma'aiktan dake bukatar haka ."eh na sani amman dake nayi ra'ayin zuwa any problem?no sir!"ta fad’a cike da jin haushinsa dan tasan yau ma so yake ya ‘bata mata lokaci ya d’an kalleta da gefen idanunsa yaga yadda ta mugun had’e rai nan take yaji zuciyarsa ta damu amman dai yace “ kije ki fara shiri at anytime zan nemeki “.
jikin maryama a matukar sanyaye ta juya ta fita ranta bai so fitar da zai yi daita ba ,yabi bayanta da kallo yana tunanin abinda ke damunta”. bayan maryama ta koma office ta bud’e durowar data ajiye wayar anifa ,ta dauko wayar ta zauna rike da wayar tana duba screen din wayar inda taga miss call da yawa amamn babu damar taga sunan masu missed call sakamakon wayar nada security code bata jima da zama ba kira ya shigo wayar da wata number dabam qirjinta na bugawa ta d’aga batare da tayi magana ba .”har kusan second goma wayar na manne a kunnenta jin bazaayi magana ba yasa daga can bangaren akace “hello !” a natse ta motsa lip’s dinta tace “ina ji dawa nake magana ?” still shiru akayi can sai aka katse kiran .”
acan bangare kuwa yaya sadam ne ya waiga ya kalli inda nadiya take tsaye ransa duk a ‘bace “na fad’a miki wannan murayar muryar maryama ce yaakayi ma wayarki taje hannunta .” I don’t know my heart !”ni dai nasan na rasa takardar dana saka documents dinka da wayata ,tsaki yaja yana dafe goshinsa da hannuwansa duka “nadiya ta kai hannunta ta dafa kafad’ansa tana cewa “me yasa zaka damu bayan mun san inda zamu ganta “kina nufin muje gareta kenan?”ya fad’a yana d’ago kanshi ya zuba mata idanunshi “ idan bamuje ba har ta bude taga documents dinka kaga ai ka shiga matsala inda wayata ce kad’ai wannna mai sauki ne “ko wayarki kad’ai ba abu ne mai sauki ba “ya fad’a yana sake shiga tashin hankali “wallahi nadiya kin cika care less dayawa just rike takarda ya zame miki aiki “
“Wani irin careless gareni ?nifa banga dalilin da zai sa ka damu kanka dayawa ba .maryama tana da ilimi da fahimta my heart ka fito ka mata magana a zahirinka,ya kamata tasan komai ka saketa ka nemi ta rufa maka asiri muyi rayuwarmu that’s all idan son samu ne ni ba haka bane araina ya cigaba da kallonta atsanake tana magana da d’agawa “yes ni ba haka bane araina banason boye boye arayuwata nafi son komai forwardstret ka saki maryama kawai sannna ka koma gida idan kace baka son maryama akwai wanda zai maka dole ne ?” numfashin ya sauke kawai yana dubanta “ my heart ya kamata ka furta mata saki .”
“Kinga mu bar maganr nan haka nadiya nemo mana mafuta lallai ya kamata documents dina da wayarki su dawo garemu “nadiya tayi shiru kawai tana dubansa dan ita a halin yanzu rashin sakin maryama ya zame mata qalubali ga rayuwarta zata só kafin suyi aure ya zamanto babu wata halaka atsakaninsu amman ta rasa dalili da yasa yaki sakinta bayan kullum lallabashi take akan ya saketa “.ya mike zai wuceta tayi saurin riko tafin hannunsa cikin nata cak yaja ya tsaya kafin ahankali ya juyo gbdy ya fuskanceta , cike da matsanancin sonshi ta qara taku biyu ta zube jikinsa muryarta cike da rauni tace “my heart ko ka fara son maryama “?numfashinsa ya hau sauke mata a fuska da wuyanta “ka fad’a min idan ka fara sonta ne ni na hakura na bar mata kai ?” tayi mgn a shagwabe kamar zatai kuka hannuwansa duka ya kai ya zagaye kugunta dashi ,inda nadiya ta sake shige masa sosai tana tado masa da sha’awarsa “kema kinsan ke kad’ai zuciyata take so “amman me yasa ka kasa sakin maryama ni so nake naji ka raba kanka da ….bata qarasa mgnr ba taji saukar lips dinsa akan nata alamun tayi shiru “sau nawa zan fad’a miki bata cikin rayuwata ?ba dai saki kike da bukata nayi mata ba ?”ta gyda masa kai tana mai lumshe masa ido “ki kwantar da hankalinki zanyi “.
ai nadiya bata tsaya wata wata ba ta soma sucking din lip’s dinsa ,sun dade suna shan bakin juna kafin ahankali suka tsurawa juna ido “ina sonka my heart. “baki kai ni ba .ni dai nasan nafika sonka.”
kanshi ya girgiza mata yana cewa “kowa nashi ya sani amman ina mutuwar sonki nadiya ke kinsan irin abubuwan da nayi facing kafin mu kasance tare gashi sakacinki yana neman sakamu cikin matsala “in sha allahu my heart bazamu shiga matsala ba .”
sun dade makale da juna suna tsara yadda zasu bi maryama su amshi abubuwansu a hannunta ,”shiru maryama tayi tsaye tana duba screen din wayar kafin ahankali ta sake maidashi cikin durowa ta ajiye “ko me yasa suke son damun rayuwarta haka ?”ta cigaba da zama shiru tana nazarin muryar da taji yanzu wanda shine karo na uku da taji ,yadda zuciyarta ta kasa yarda cewar yaya sadam dinta bai mutu ba yana raye haka ta kasa yarda cewar wannan muryar ba muryarsa bace zuciyarta ma tafi tsaiduwa akan muryarsa ce .ranar dai kowa ya kalli yanayin maryama yasan babu lafiya kuma sai ya tambayeta amsa d’aya take bayarwa shine babu komai yayinda acan bangaren yaya sadam da nadiya abu na farko da suka fara shine trancking din number wayar nadiya domin su san takaimaiman inda maryama take cikin sauki kuwa suka gane inda take sakama kon wayar na kunne har lokacin.”
Maryama ta numfasa daga zaunen da take tana duba agogon hannunta tsaki taja saboda lokacin tashi aiki ya kusa."ahankali ta dafe ha’barta da hannu d’aya ta kalli office din mr ata taga aikinsa kawai yake yana amsa kiran mutane wani tsaki ta sake ja tana cewa “Ko me yasa sai dani zashi ganin abokin kasuwan cinsa byn ga sauran mutane nan ? bayan kamar mituna talatin mutane suka fara watsewa ahankali tana zaune kowa ya wuce har madam some aka barta ita kad’ai zaman jiran mr ata.”
Mr ata ya d’an leko yana cewa maryama “kin shirya ? tace ”yes na shirya !”ta furta muryata a raunane jakarta ta d’auka ta rataya kana tayi hanyar shiga lift sai dai duk ranta a ‘bace yake ,bayan ta wuce ya fito cikin sauri inda ya had’u da wani matashin saurayi goye da kayan aiki na spray din gida da office ,fuskarsa rufe da face mask haka ma ilahirin jikinsa sanye da kayan aikinsu mr ata ya tsaidaishi yana cewa" who are you? "Uhm amm spray control ." "wa ya kiraka ? "wani daga cikin maaikatan office dinka ce ta kirani “suna cikin hk maryama ta d’an dawo baya kad’an tana cewa” sir lokaci na tafiya fa "okay.! ya fad'a ya wuce matashin saurayin “.
Sadam ya ciro wayarsa ya fara duba tracking number a wayrasa kafin ahankali ya shiga cikin wani office ya fara dube dube can aka kirasa a wayarsa "eh nadiya na samu na shiga office din da tracking ya nuna min nayi sa’a babu kowa aciki amman fa kisa ido sosai idan kinga dawowar maryama kiyi maza ki kirani na fito dan banason muyi face to face daita no matter how zata iya ganeni “.ya fad’a tare da katse kiran yana cigaba da bubbud’e durowas din duk wanda ya bude ya duba sai yaga bai ga abinda ya kawosa ba yayi shiru tsaye yana tunani ko ina ta ajiye wayar da document dinsa yasan dai idan bai ga documents din da wayar nadiya anan ba lallai yana cikin jakarta kenan?” Ya rabbi sadam zai sake koma zuwa gidansu kenan ?”inji cewar zuciyarsa “a’a ka sake duba tracking sosai kafin kasan matakin da zaka dauka ,"yana cikin wannan tunanin sai ga daya daga cikin securities ya qaraso yana cewa” who are you looking for?ya juyo a hankali baka ga alamun kayan aiki ajikina ba spray control ne? amman may yasa sai a wannan lokacin zaka zo? " eh ! wacce ta kirani ne tace nazo by this time saboda mutane sun watse ,"Okay shikenan ka cigaba da aikinka “ thank you “!ya fad'a yana sauke numfashi security ya juya shi kuma ya cigaba da aikinsa ,"
ahankali motar mr ATA Ke gudu akan titi shi da kansa yake tuki wanda escort dinsa da direbansa sunyi mamaki da duk inda zashi tukashi akeyi amman a wannan lokacin yace duk suyi zamansu .” ahankali ya kalleta tana zaune a gefensa ta kawar da kanta gefen titi tana kallon motocin dake wucewa
ya dauke kanshi ya maida Kan titi ya cigaba da murza stearing mota yana tunani taya zai rabata da tunanin wannan matacen mutumin ya dasa nashi tunanin a zuciyarta ,dan dai yayi imani tunaninsa take yi ,ya sake waigowa ya kalleta cikin haka wayarsa ta dauki gara mara sauti ya tsaida motar a gefen titi yana amsa kiran bayn ya gama wayar ya kira sunanta a kasalance "maryama !" "yes sir ! ta amsa batare ta kallesa ba , mutumin da zamu hadu dashi yayi cancelling din haduwarmu wani sanyay yen numfashi ta sauke najin dadi tana godiya ga allah ,zata wuce gida da wuri akan lokacin "bari mu juya zuwa office "taso ta roki alfarmar ya sauketa ko a bakin titi ne ta samu mota da zata qarasa daita gida ,amman babu hali tana magana yanzu zai maida maganar bala'i dan haka ta hakura idan ya sauketa a ma'aikatan ta kama gabanta tana jinsa ya juya ya dauki hanyar komawa office.”
ahankali yaya sadam ya cigaba da duba document din a bangare dabam dabam still bai gani ba to yanzu idan banga wayar da file din ba fa ya kenan ? to kuma idan ya zamo yana jakarta fa ko kuma ta bawa wani ajiya fa ?amman bari na cigaba da dubawa ? "madadin mr ata ya tsaya ta sauka a bakin ma'aikatan kai tsaye ya shige ciki daita a haraban kamfani yayi parking ya bude ya fito ya zagaya bangaren da take zaune yana kiran sunanta "maryam.”! alokacin tana daf da qarasa fitowa ta tsaya tare da rungume hannuwanta a qirjinta "yanzu tunda anyi cancelling aikinmu me ya kamata muyi "?me ya kamata muyi kuma ? ta maimaita abinda ya fad'a acikin ranta amman a zahiri kam tayi shiru ta rasa amsar da zata bashi ” ko zamuje office ki had’a min coffe na sha ? “coffe kuma ”! ta furta a fili tana yatsina fuska "eh ko bazakiyi ba ?"
“sorry sir am not in the mood" ta fad’a kamar zatai kuka "meke damunki ?”nayi nayi ki fad'a min abinda Ke damunki ko zaki rage jin damuwar dake damun zuciyarki kinki ,"sir ko zaka fad'a min kai ma dalilinka na “wad’an nan tambayoyin “damuwa da abinda ke damuna ? meye matsalata ?ta tambayesa a zafafe tana juya masa baya " wai ma dole ne sai ka tmbyeni abinda ke damuna da matsalata ."?ta fad’a muryarta na rawa .”
"Bana son jin damuwar kowa kema bansan dalilin da yasa nake son sanin damuwarki ba ,ya tsinci kanshi da fad’a mata haka “ya d’an lashi lips dinsa na kasa kad’an kana ya cigaba da magana “me ma kike tunani akaina dan na tmbyeki damuwarki ? " dole nayi tunanin wani abu ,dan kaine da kanka kace baka bukatar jin matsalar kowa da damuwar kowa kuma kowa yasan wannan yana daga cikin dokokin aikinka to me ysa zakayi ta tambayata akan abinda ya shafi rayuwata ?"dan allah ka barni naji da abinda ke da...."bansan me yasa na tmbyeki ba bare ki samu damar fad'a min rubbish and nonsense ya katseta ta hanyar fadar hk yana fidda numfashi sama sama "me yasa ka tmbyeni to ?”me ma yasa kamin mgn bare har na fad'a maka rubbish and nonsense“
"yadda kaima baka bukatar a shiga rayuwarka nima haka nake bana bukatar ana shiga rayuwata kawai kana son qarawa mutun damuwa akan wanda yake ciki .ta fad'a tana jan tsaki zata wuce taji ta makale ajikin mutun , tayi tayi ta motsa ta kasa sakamakon gefen rigarta daya makale da murfin mota "me kake kokarin yi sir ?me yasa ka rike min riga "what.”? ya furta a razane yana dubanta "naga alamun kana son wuce gona da iri daga ta’ba min jiki yanzu kuma ka dawo rike min riga ko ance maka ni din rin wadan nan mata ne dake banzatar da kansu a gurinka ? .
"ni kike fad’awa haka ?kenan wannan tunanin Kike yi akaina ?okay tunda tunaninki kenan zan san abun yi “ nan take jikinta yayi sanyi tsoro ya kamata yanzu idan ya fusata ya turata wani guri acikin ma'aikatan yayi reping din fa ?nan take wani tsoron ya sake mamayeta ,ta juyo ahankali idanunta ya sauka akan gefen rigarta dake makale ya hade da murfin mota an rufe yayinda mr ATA ke tsaye yana faman fitar da hucin numfashi "ganin ba rike mata riga yayi ba yasa ta shiga tashin hankali mai tsanani muryarta na rawa ta soma bashi hakuri "am very sorry sir karka yi fushi dani dan allah dan har jijiyon kansa sun tashi sunyi rudu rudu saboda bacin rai "idan zakiyi irin wannan hauka ki fara tunani ,ni ba irin wadan mazan bane nonsense kawai ya fad’a yana wuceta "am sorry sir!” me yasa na fad'a masa son raina batare da nayi tunani ba ? Sam sam bai kamata na fad'a masa haka ba tunda babu wanda ya ta'ba fadar wani mugun abu akansa kowa kaji yayi magana akansa sai dai ace shi din miskiline mai kamewa baya shiga harkar mata "dan allah sir kayi hakuri madadin ta wuce gida kamar yadda taso sai ta tsinci kanta da biyosa tana sake bashi hakuri .”
a can kuwa office sake cigaba da dube dube yaya sadam keyi har ya samu nasarar bude durowar qarshen wanda yafi kowa ne wahalar budewa ya shiga duddubawa yana daga wasu file ,duk file din daya gani sai ya bude cikin haka yaci karo da wayar nadiya ya sauke naunayen ajiyar zuciya yana cewa allah na gode maka dan zaman wayar nan a hannun
Maryama zai iya zama matsala a rayuwarsu.”nadiya wacce Ke duba masa waje tana duba masa dawowar maryama taga dawowarsu ita da maryama dan haka cikin tsananin tashin hankali tace "me ya tsaya yi ne haka idan bai ga wayar da file din ba ya fito mana mu wuce kar akama mu, bari nayi sauri na samesa idan bai gani ba mu wuce kawai ."ta shigo da sauri rufe da fuskarta alokacin sadam yana shirin fitowa "idan baka ga file din da wayar ba kazo mu wuce mana me yasa kake bata lokaci ?" Me yasa kika biyoni Ke da nace ki jirani a waje ga waya nagani tasa hannu ta amshi wayar "gsky kayi kokari ina file ?”shi nake kan nema dan shine damuwata amman duk na duba koina ban gani ba.." sautin muryar mr ATA ne ya katsesu da sauri nadiya wacce ta shigo yanzu ta tsugunna ta boye akarkashin table tana sauke numfashi ,shi km yaya sadam da ke tsaye da kayan aikin spray control ya soma kokarin fita daf da zai wuce mr ATA yaji sautin muryarsa"wait!yaya sadam tsaya cak gabansa na luguden bugu dan baya son su had’u da maryama dan kallo d’aya zata masa taganeshi mr ata ya tsaya yana dubansa "are you done?yes sir !” na gama ina sauri ne zani aiki wani guri "okay zaa tura maka kudin aikinka daga asusun kafaninmu zuwa naku “okay sir ya wuce da sauri ya bar nadiya akarkashin table ."
Ganin da nadiya tayi mr ata ya zauna ta fito da sauri ta soma tafiya tana waigen bayanta yayinda maryama Ke tafiya tana magana da zuciyarta kamar yadda tasa ba , daf da nadiya zata fita daga cikin office din ita kuma maryama na qoqarin shiga office din suka ci karo da juna cikin tsarkewar murya maryama ta furta "am sorry !nadiya batai magana ba ta sake rike mayafin data rufe fuskarta dashi gam "excuse me who are you?kina aikina a AGC company ne?”ko kuma kina bukatar wani abu ne ?Shiru nadiya tayi tana qoqarin guduwa .”shi kuwa mr ATA daga inda yake zaune acikin office dinsa ya hangosu tsaye ya tsura masu idanunshi yana kallon dawa maryama take magana ?haka jikin maryama ya bata ta bud’e fuskarta matar taga ko wacece ai kuwa maryama tayi taku biyu tasa hannu zata zame mayafin da nadiya ta rufe fuskarta dashi nan take nadiya tasa hannuwanta duka ta tura maryama da iyakar karfinta maryama ta tafi luuuuu ta fad'a Kan durowar karfe nan take hannunta ya bugu da gefen karfen nan da nan sai jini ya balle "ouch ta saki qara mai sauti sannan ta matso da sauri ta rike hannun nadiya dake rike da kofar shigowa tana qoqarin zare hannunta maryam ta sake damkewa nan suka shiga kokuwa da juna ,har maryama ta samu ta mike tana qoqarin ta zame hannun nadiya ta dake damke da mayafin fuskarta inda wayar dake rike da hannun nadiya ya fadi kasa maryama tabi wayar da kallon mamaki “ai wayar da’akawo mata ne dazu da safe .”
Nadiya ta tsugunna da sauri ta dauka tana mikewa mayafin fuskarta ya zame kafin ta rufe fuskarta tunin maryama tagan fuskarta ,a matukar rikice ta furta sunanta " anifa ! tana rike hannunta dake tsiyayyar da jini wanda adaidai lokacin mr ATA ya soma qoqarin qarasowa inda suke yana kiran “stop !amman ina idanun maryama sun rufewa babu abinda take furtawa sai sunan anifa ki bani wayar nan bazan sakeki ba sai kin bani wayar nan dan bazan bari ki tafi koina ba batare da kin bani wayar nan ba.” ta qarasa mgnr adaidai lokacin da mrs ATA ya qaraso ya rike hannun maryama yana cewa “meye kikeyi haka ko kinyi hauka ne”?” Ka sakar min hannu karka bari ta gudu a matukar fusace ya zare d’ayan hannunta dake rike da nadiya ya hadasu waje daya wanda hakan ya bawa nadiya damar juyawa da sauri maryama ta juyo ta kalli bayan nadiya tana furta "sir sir sir !!! "dan magana ma yaki fitowa daga cikin bakinta tana kokarin fisxgewa daga hannunsa "ke kina hauka ne baki ga jinin a hannunki ba ?ta girgiza masa kai "tana kallon hanyar da nadiya tabi “zakiyi wasa da lafiyarki ne akan shirmen banza ?" rasa yadda zatai dashi yasa kawai ta fashe masa dan wani rikitaccen kuka mai tsananin cin rai tare da zubewa ajikinsa .hannuwansa duka yasa ya tarairayota ya rungumeta tsam ya hadeta da faffafan qirjinsa .”
cikin tsananin tashin hankali ya soma tafiya daita zuwa cikin office dinsa ya zaunar daita akan kujerar hutawarsa ,kuka sosai maryama take tana ciza harshenta da qarfi dan zuciyarta banda zafi alokacin babu abinda take mata “tana son sani me yasa ake kiranta da number anifa “.ya dauki waya ya kira bakin get inda securities suke aiki byn an dauka ya bada umarnin akawo masa hydrogen da cottonwood byn ya gama wayar yayi tsaye rungume da hannun wansa duka a qirjinsa yana dubanta ta kife kanta akan ciyoyinta tana cigaba da kuka wanda babu tantama kuka bakinciki take .”ciza lips dinsa ya dinga yi yana cigaba da kallonta shi a ganinsa gata yayi mata dan idan ya barsu da yarinyar babu tantama maryama zata sha wahala ne domin kuwa yarinyar tafita jiki da shekaru nesa ba kusa ba yana tsaye security ya qaraso bakin kofa yana neman izinin ya fito ya amsa ya juya ya koma cikin office din ya ajiye akan table dinsa sannan ya koma inda take zaune tana kuka .bai mata magana ba ya riko kugunta a hankali ta dago fuskarta shabe shabe da ruwan hawaye ,dayan hannunta da bai da ciwo ya riko zuwa kujerar dake zagaye da table dinsa ya zaunar daita ya kamo hannunta ya daura akan table .”
Ahankali ya bude kwalbar ruwan hydrogen ya zuba acikin cottonwood ya daura akan ciwo "asshhh !ta furta tana jin radadin ciwo,” sorry !ya furta ahankali cike da tausayawa yake goge mata, ajikinta ciwon yake amman ya fita jin radadin zafin "kalli yadda jini yaki zuba ki daina wasa da lafiyarki ,idan baki damu da komai ba ya kamata ki damu da lafiyarki domin shine komai arayuwarki ,ganin wannan jinin dake zuba ajikinki yayi matukar d’aga min hankali sosai amman Ke ko ajikinki why maryama ?yayi maganar kamar zaiyi kuka tare da cigaba da goge mata ciwon .
kwayar idanunta dake cike da ruwan hawaye ta tsura masa tana kallonsa tana jin wani irin sabon tashin hankali na kusantota .”ahankali ya dago tsumam mun idanunshi ya sanya kwayar idanunshi cikin nata gabanta ne ya shiga luguden bugu kamar yadda nashi ke bugawa da sauri ".
“me yasa ka tsaidani sir ?ya sauke numfashi "yace naga anifa amman gashi ban samu damar yimata tarin tambayoyin dake zuciyata ba wallahi da kasan yadda yarinyar nan take da mahimmanci a rayuwata da baka dakatardani ba "culmdown maryama !”ya furta yana cigaba da goge mata jinin ya d’an yagi bandage ya nade mata hannun "babu abinda bazan iya miki ba maryama "ya fad'a yana tsareta da tsumammun idanunshi yayinda hannunsa Ke saman bayan tafin hannunta "zaki iya magana yanzu, fad'a min meye tsakaninki daita "?tayi shiru tana jin zafi mai radadi a hannunta"shirunki ya nuna maryama kice baki da gsky ?ban san yadda zan maka bayani ba dan ba lallai ka fahimceni ba ya lumshe tsumammun idanunshi alamun tayi magana zai fahimceta .”
“ina sauraranki maryama ahankali ta motsa lip’s dinta ta soma magana muryarta da shesheka “tun daga ranar farko da anifa tazo gidanmu amatsayin friend din yaya sadam wacce sukai karatu tare sannan suke aiki tare ,tazo ne akan wasu takardun project da suka fara aiki tare dan haka tana bukatar project ko zan taimaka mata muje dakinsa mu duba banyi mata mutsu ba mukaje , na fita na dawo ina shigowa dakin naji Kmr muryar yaya sadam na fita daga cikin wayarta alokacin ,sannan kwanaki can ina zaune ina aiki da daddare aka kirani da number wayarta akace nazo aiki da wurin sannan shekaranjiya har zuwa yau din nan byn nabi didigin layin wani ya dauka yace min tsintar wayar yayi bayan wani lokaci aka kira wayar ina dauka muryar yaya sadam naji sannan daga by naji muryata babu abinda ta boye masa "yanzu ka fahimci yadda rike wannan matar yake da matukar mahimanci a gurina domin ina da tarin tambayoyin da zan mata sannan me yasa zata shigo har cikin office din da nake aiki ta dauki wayarta wallahi bazan ta'ba samun kwanciyar hankali ba muddin bangata ta amsa min tarin tambayoyina ba ta qarasa mgnr tana sake fashewa da kuka ".
“kina da matsala maryama ko dai kina imagenation ne taya zakiji muryar wanda ya mutu a waya bayan baya duniya ?"no sir ba imagenation nake ba tabbas wannan muryar dana ji muryar sadam ce ko komai ya kasance mafarki ko imagenation agurina wannan gaskiya ne," ni yanzu taya zan fita cikin wannan tashin hankali yanzu a ina zan sake ganin anifa arayuwata ?shikenan kasa na rasata .” shiru yayi na kusan mintuna talatin dan har ta fidda rai zai yi magana sannan taga ya dago kansa yana kallonta zuciyarsa cike da zallar soyayyarta yasani mutumin daya mutu bazai dawo ba imagination kawai take tunda har lokacin tana cikin gigin mutuwarsa ne numfashi ya sauke sannan cike da tausayawa ya soma motsa lip’s dinsa "maryama ki daina kukan nan zan taimakeki kiganta ,”amman me yasa tun safe nake fama dake ki fad'a min damuwarki kika ki ?”
“nasan bazaka fahimceni bane shiyasa "me yasa zakice hk ?”amman ai ni na tamvayeki damuwarki ?” Ta gyad’a masa kai ,ko zan iya tambayarki ?“ta sake gyad’a masa kanta alamun yayi tambayarsa “me yasa kika kasa manta abinda ya faru dake baya ?bazaka fahimci yadda nayi rayuwata bane amman kuma zan iya cewa zaka fahimta ,the situation i have past or the one am going tru at this moment ,my pain’s, my suffering, I don't expect any one can understand me ,and I don't want any one to understand me amman dai nasan ni din yar Adam ce mai numfashi kuma ina yawon addua sir amman nayi facing matsalolin masu tarin yawa arayuwata tun kafin a tsaida maganar aurena da yaya sadam har zuwan sanda ya barni amman kuma duk wannna sai ya zama imagenation ?ko zaka iya fad'a min duk abinda ya faru dani duk imagenation ne ?dan allah ka fad'a min ?”.shiru mr ata yayi batare da yace komai ba yana nazarin maganganunta jin yayi shiru tayi tunanin ko ta ta'ba masa rai ne yasa tace "dan allah ka yafe min akan maganganuna idan kaji babu dadi sir .”still shiru yayi batare da wani dalili ba ina ta fadar maganganu da sam basu dace na fad'a ba na gode sosai da kulawarka sir ta qarasa mgn hawaye na sake turareniya fitowa daga idanunta .”
"Is okay maryama ki goge hawayenki zan nemo miki ita , nadiya sunanta ba anifa ba,zan nemo miki a duk inda take acikin fadin duniyar nan saboda na santa "maryama tayi saurin matsowa kusa dashi har gwiwowinta na gugan nashi "ya akayi kasanta ?sosai kuwa nasata ,amman naji kace nadiya sunanta ba anifa ba “?tabbas nadiya sunanta domin ta ta'ba aiki a daya daga cikin companies dina maganar da nake miki ma yanzu haka ta bukaci aiki da kafanina na auduga “amman ni ce min tayi tare sukai aiki da yaya sadam .”Ta yuwu sunyi aiki da sadam din tare bazan san wannan ba dan ta ta’ba aiki a IA company mahaifinta mai kudi ne sosai tru din wani abokin dad dina na d’auketa aiki a byn ,bata dade tana wani aiki damu ba tace zatai tafiya zuwa qasar amercan idan ta dawo zata sake neman aiki to ina ganin dawowarta ne ta sake tura mana sako neman aiki.”
Ya qarasa maganar yana mugun tsareta da kwayar idanun shi “maryama fad'a min me yasa kike son tsohon mijinki sosai haka ?tayi shiru qirjinta na bugawa fiyye da kaida ,tell me me zakiyi da mutumin da baya raye ?
Mmn sudais[8/31, 11:25 AM] Safwan Libiya 2: 💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
BOOK 3
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 30
Shiru ne ya ratsa office din ,domin kuwa maryama ta kasa bashi amsar tambayarsa ,yadda ba tace masa komai ba haka shima bai sake cewa komai ba har tsawon mintuna shabiyar yana zaune yana kallonta shiru ko bata fad'a masa ya karanci tunani kala kala take acikin zuciyarta ,har ga Allah bata son yasan komai akan rayuwarta, ba dan komai ba sai dan tsare mutuncinta amman kuma idan sanin nashi yana cikin taimakon da zai mata ta samu ganin nadiya bata da option zatayi "maryama !ya kira sunanta da kasalalliyar muryarsa mai tsananin kashe sansar jiki da tsuma zuciyar wanda akayi dominsa"bana maimaita magana d'aya domin kuwa baya daga cikin d'abiata ,amaman akanki kullum sai na aikata haka why ?."still shiru tayi tana nazarin abinda zata fad'a masa wanda zai gamsar dashi "ki amsa min tamabayata akwai abinda zuciyata take bukatar sani" tana can tunanin abinda zata fad'a masa kawai sai taji ya matso ya dawo daf daita sosai yasa hannunsa d'aya ya sake riko hannunta mai ciwo yana kallo "karki ga na damu da son sani kiyi tunanin ina yin shishigi ne acikin abinda bai shafeni ba "no sanin dalilin shine kwanciyar hankalina "."
"maryama a karo na qarshe ki fad'a min me yasa kike son tsohon mijinki sosai ?"ya qarasa maganar yana lumshe tsumammun idanunshi "hallaci ne !"ta fad'a hawaye na zubo mata akan kuncinta, ajiyar zuciya mr ata ya sauke sannan ya bud'e idanunshi sosai akanta yana jin wutar soyayyarta na sake ruruwa acikin zuciyarsa yayinda qaunarta mai zafi ke nacin zuciyarsa, baya qaunar ganin damuwarta bare kuma zubar hawayenta. ya kai hannunsa d'aya ya ciro hanky acikin gaban aljihunsa mai azababben qamshi ya soma share mata hawayen dake gangaro wa akan kuncinta, qamshin turarensa mai sanyi ya cika hancinta ta shaqa ahankali tare da lumshe ido nã second biyu sannan ta bud'e tana kallonsa tana jin wani irin yanayi a gabad'aya ilahirin jikinta ."kasa daina kallonsa tayi dan hk gabad'aya tsigar jikinta suka dinga mikewa tsaye ." kallonta ya sake yi a tsanake yana d'an cizan gefen lip's dinsa ahankali ahankali!!""hallaci mahaifiyarsa tayi min tun kafin nazo cikin duniyar nan ,haka shima yaya sadam yayi min hallacin ,kuma hallacin ne yayi sanadiyyar dasa soyayyarsa mai qarfi acikin zuciyata wanda nake ji muddin ba dashi ba bazan iya qara rayuwa da ko wani namiji ba ."saurin runtse idanushi yayi daga tsura ma marayama idanu da yayi zuciyarsa cigaba da bugawa fiyye da kaida ."
Ahankali yayi baya kad'an da kujera da yake zaune akai yana jin wani irin tattukin bakinciki mai had'e da zazzafan kishi ,ji yayi gabad'aya ya muzanta a gabanta "ashe rashin furta mata soyayyarsa taimako kansa yayi, kuma shine abinda yafi zama alkhairi atare dashi ,shiyasa a kullum manazarta suke cewa duk mutun mai yawon surutu tabbas wata rana sai yayi nadama ,shi kuma mutun shiru shiru kullum cikin nasara yake sakamakon hangen nesan shi "na sani dukkanin rayuwar da nayi abaya rubutaccen qaddara ne ban isa na canzawa kaina ba cike da faduwar gaba ta fara bashi labarin abinda ya faru daita daga kan masu zuwa neman aurenta har zuwa sanda umma ta yanke hukuncin had'a aurenta da yaya sadam da abinda ya faru dasu akan hanyar dawowarsu daga ogun state ta qare maganr tana zubar da kwalla mai zafi tana jin zafi a qirjinta"nasan umma tana rayuwa ne kawai amamn har ta koma ga allah zuciyarta na d'auke da rad'ad'in rashin tilon d'anta wanda nice silar faruwar haka ."
mr ata ya kalleta cike da tsarewa da tausayawa "kin tabbatar a gabanki aka binnesa da ranshi ?"wasu hawaye ne suka sake biyo kuncinta sakamakon tuno da tashin hankalin ,nan take jikinta ya kama rawa tamkar alokacin alamarin ya faru domin kuwa tashin hankali ne da bazata ta'ba mantashi arayuwarta ."
"idan zata manta komai daya faru a past dinta ban da wannan al'amari mai firgici "No !ni ba kuka nace ki min ba "ya fad'a yana dafe kanshi sannan ya sake kai hanky ya goge mata hawaye sai daya tsareta da tsumammun idanunshi sannna ta d'aga masa gira tace "yes a gabana suka haqa rami suka binnesa ta bashi amsa ."ya sauke numfashi yana dora qafarsa d'aya akan nata batare daya san yayi haka ba duk da qafarsa sanye take da safa amamn sai data ji yadda ya sauke wata naunayen ajiyar zuciya wanda tasa hawaye ya gangaro daga idanunta sannan a can qasan makoshi yace "amamnan maryama idan aka yiwa mutun haka me kike tunanin halin da mutun zai shiga?" ko a minti goma né bare an d'auki sama da kwanaki sannna kuma ke karon kanki kin kasa gane inda abun ya faru "?naunauyen ajiyar zuciya ta sauke kana ta motsa labbanta tace "babu tantama mutun bazai rayu ba ." yayi saurin matso da kujerar da yake zaune still tafin qafarsa na saman nata yace "okay anyi haka a gabanki but what are you still waiting "tayi shiru ta kasa cewa komai "mutumin nan baya raye maryama me yasa zaki dinga imagenation dinsa over?"
na sani nasan baya raye amman na rasa dalilin da yasa nake jin kamar yana raye "wallahi bana jin daidai arayuwata sakamakon rashinsa atare damu domin kuwa bani kad'ai nayi rashinsa ba hatta yanuwa gabad'aya sunyi kewarsa amamn basu kai ni ba"tsakninki da allah kina jin soyayyarsa ko tausayin mahaifiyrsa ne ke dawainiya da zuciyarki "?kamar yadda na fad'a maka a farko hallacci ne amamn a yanzu ina son shi har ina jin bazan iya rayuwa da wani namiji ba idan bashi ba I really love him son shi da qaunarsa sun mamayeni ."yayi mata wani irin kallo yana mai jin zafin mgnarta aransa amman sai ya dane tare da d'auke qafarsa akan nata ya juya tare da janyo laptop dinsa gabansa ya soma da daddana laptop din da qarfi a yadda yake operating din laptop din kasan acikin zafi zuciya yake ,yana daddanawa yana fitar da zazzafan numfashi yana jin wani azababben kishi from know where na shigarsa ."
"wato duniya juyi juyi ne yau gareka gobe ga d'an uwarka ,abinda ya baka dariya wata rana shi zai sakaka kuka ,dan girgiza kanshi yayi yana zance zuci wato shi kuma haka qarshen soyyarsa ta zama yana son maso wani ,ina ma mafarkinta ya cigaba da yi da wannan lukutar matseefar da ta samesa .wai kamar shi yau soyayya take kutimememiya dashi haka ?""karkaji komai aranka adam, sannan karka manta ita soyayya allah ne yake sakata acikin zukatan wad'an da yaso ,kuma babu wanda ya isa ya rabata ko kuma ya hana faruwar abinda allah ya had'a kai kanka da kasan haka rayuwar soyayyarka zata zo a qarshe da duk yadda zakayi ka goge shi dakayi amman dake had'in Allah ne har ma yake jin babu abinda zai iya sawa ya juya mata baya ko kuma ya daina sonta dan a yadda yake jin soyayya da qaunar da yake mata babu wani abu a duniyar da zai firgitashi har yaji zai iya hakura daita to kuma ai ita zuciyarta ta tsundu ma acikin tafkin son wani ?"zuciyarsa tayi saurin tunatar dashi "uhm ai kuwa akwai bala'i dan kuwa ta qarfi da qarfafa zai shigar daita tsundum cikin kogin sonshi har ta manta ta ta'ba son wani a duniya yayinda ita kuma maryama sai goge hawaye take wasu na sake gangarowa muryarsa a tsarke yace "kiyi hakuri banyi miki wad'an nan tambayoyin dan na 'bata miki rai ba." karka damu sir dan nima banji komai ba"ni dai ina bukatar nadiya ina son nasan wani abu dan gabadaya a tsorace nake tana bani tsoro matuka bansan me yasa take bibiyar rayuwata ba ."
"nima abinda yaketa bani mamaki Kenan ko me yasa zata shigo har office byn ta rufe fuskarta "na samu wayarta ina ganin akwai abinda yake tare da wayar mai mahimanci ,ta kira taji muryata kuma tana ganin idan batayi hanzari ba zan iya sanin wani abu akanta idan na koma gida dan kwata kwata bana jin dan wayar kawai tazo domin zata iya samun wata wayar kuma tasan bazan tsinci komai da wayar ba tunda a kulle take idan ma nace zanyi flash din wayar dan na bude bazan ga komai ba saboda wayr zata dawo empty akwai dai abinda ta biyo "okay zanga abinda zanyi akai dan dole na nemo nadiya."
" kana ganin zaka iya nemo min ita ?tunda nace miki zanyi zanyi ne" taya kenan ?tana matukar bukatar aiki damu a yanzu zan tura mata sako mun d'auketa aiki ,zanyi qoqari na had'uku sannna akwai binciken da zan yi still akanta in sha allahu .matsa war haduwarki daita zai sa kisamu kwnaciyar hankali I wil try my best ya fad'a yana cigaba da aikinsa maryama ta mike tsaye da kyar tace "na gode sir ni zan wuce gida "."koma ki zauna na gama mu kaiki gida ."haka ta koma ta zauna jiki a sanyaye dan gara ta jirasa din su kai gida ta sake cewa "na gode sosai."bai kulata ba illa ya cigaba da abinda yake ."
Bayan kamar minti shabiyar ya mike ya tattara wayoyinsa ya nufi hanyar fita yana cewa "muje ko".mikewa tayi tabi bayansa yana gaba tana biye dashi har suka sauka qasa yaja ya tsaya tare da zura hannuwansa duka cikin aljihun wondonsa inda masu tsaronsa suka taso da sauri duk suka zagayesa cike da girmamawa ,a natse ya ciro hannunsa daya daga aljihunsa ya soma keyarsa sannan ya soma magana cike da kamewa "a ruwa zai kai ni agege so ku zaku iya wucewa ."iyakar abinda ya fad'a kenan dan bai son ya shiga unguwar da jami'an tsaro."
tana tsaye tana kallonsa ya bud'e gidan baya tayi shiru tana jin mummunar faduwar gaba gabad'aya daga securities din bakin get din har na cikin ma'aikatan da masu tsaronsa babu wanda bai yi mamaki ba dan basu ta'ba ganin haka daga garesa ba har gara ma masu tsaronsa zasu iya cewa suna ganin yana yiwa mahaifiyarsa amman wata mace daban wannan ne farko ."ki bar wannan banzar tunanin naki ki shiga"ya fad'a yana hura hanci jiki a matukar sanyaye ta shiga ta zauna ya maida kofar ya rufe mata sannan ya soma qoqarin zagayawa inda kafin ya qarasa tuni a ruwa ya bud'e masa ya shiga ya zauna yana ware qafafuwansa wanda ya zame masa jiki sannan a ruwa ya shiga mazaunin direba ya tada motar suka nufi get ."
Shiru suna zaune a bayan motan sai driver a ruwa a mazauninshi, haka nan taji hawaye ya ziraro mata a sanda suke hau babban titi , ahankali ta juyar da kanta tana kallon gefen titi tana sheshekan kuka wani dogon tsaki yaja ,tana jinsa kamar zata juya ta kallesa sai kuma ta fasa,ta ci gaba da barin kanta a inda yake ya motsa bakinshi kamar zaice wani abu shima sai kuma ya fasa ya ciro d'aya daga cikin wayoyinsa dake qara mara sauti yanayin yadda taji yayi maganar tasan oga amar ne, bisa dukkan alamu maganar mai mahimanci ne "karka damu dole zan nemeka cikin satin nan "eh duk acikin satin zamuje gurinsa in sha allahu to gsky dai ban gama tantacewa ba, tsarin farko zanbi ko kuwa wani tsarin ne amman dai duk abinda ake ciki zan nemeka sukai sallama kana ya dan tsaya yna kallona"wallahi kukan nan yana maseefar kona min rai ."ya fad'a yana sake jan tsaki mutun yayita kuka baya tunanin halin da mutane zasu shiga” yayi maganar acan qasan makoshinsa ."
shiru tayi tana assessing maganarsa, ta juyo a sukwane taga ita yake kallo fuskashi a hade tamkar wanda aka aikowa da sakon mutuwa ."ahankali ta dauke kanta tare da tsaida hawayenta tana lissafi maganarsa "wallahi kukan nan yana maseefa kona min rai ,mutun yayita kuka baya tunanin halin da mutane zasu shiga "bata gama tunanin makomar maganarsa ba taji ya matso kusa daita sosai tare da daura kanshi akan kafad'anta wanda yasa ta sauke naunayen ajiyar zuciya "please maryama ki daina tunanin matacce haka ."numfashi ta sauke kawai .
bata ankara ba taji ya kamo hannunta mara ciwo cikin nashi "ina son ki daina tunaninsa ,ko zaki min wannan alqarin ?"tun kafin tace wani abu ya cigaba "yes I know you can do it for me "kiyi saboda ni bansan dalili ba maryama bana son ganinki cikin damuwar nan zaki daina tunaninsa " anya kuwa zata iya kuwa? Not thinking of yaya sadam dinta bayan a yanzu bata iya kwana ba tare data yi tunaninsa ba ? "Kullum sweetheart dina tana fad'a min yawon tunani yana illata zuciyar dan adam ta kallesa a tsanake tana sauke numfashi ".
"banason ki illata zuciyarki ko babu komai kina da qarancin shekarun ,kinyi kankatar da zaki jefa rayuwarki cikin over thinking haka .ta sake kallonsa taga har lokacin ita yake kallo sai dai fuskar nan tashi a hade take "nasan daga yau zaki daina ko? ya fad'a yana matse yatsun hannunta cikin nashi sai dai ta girgiza masa kanta ,alamun bazata iya ba, sai ya sake langwabe mata ya dawo kamar wani abun tausayi yana murza tafin hannunta cikin nashi .tayi qoqarin zare hannuta ya damke sosai yace "Please maryama wai mai yasa bakya tausayin kanki ne ?"
yayi mata tambayar yana mata tafiyar tsutsa a tsakiyar hannunta tayi saurin zare hannuna daga nasa tana yarfarwa kamar wadda wuta ta kona saboda wani yanayi da taji ya taso daga hannun nashi zuwa cikin nata, cikin kankanin lokaci ya zagaye dukkanin ilahirin jikinta ,cikin sarkewar murya tace "no sir I can't bazan ta'ba dainawa ba yaya sadam fa jinina ne ko babu aure atsananinmu babban yaya ne a wajena .“ina tabbatar maka idan babu baba gali a raye da yaya sadam yana raye shine ma daurin aurena .da mahaifina da mahaifinsa uwa daya uba daya ta yaya kake tunanin zan iya mantawa da wannan dangantar?"
ahankali ya lumshe mata tsumammun idanunsa yace "shikenan ba’a bukatar ki daina tunaninsa ki cigaba da tunaninsa idan kina só ma kema kije ki haqa rami ki shiga ki binne kanki “kai a ruwa miko min kwalin sigari "sigari kuma ?"ta furta a razane baqar maganar daya fad’a bai mata ciwo ba kamar abinda yake qoqarin aikatawa yanxu .a ruwa ya miko masa tare layter ja ya kar’ba ya bude ya ciro Karan sigari daya ya rike batare daya kai bakinsa ba duk tana kallonsa yayinda idanunta suka sake ciccikowa da ruwan hawaye ya janyo hannuta mara ciwo ya saka layter ciki "kunna min !"ya fad'a yana miko mata sigarin , zaro idanu tayi waje tana dubansa cike da matsanancin mamaki .hankalinsa kwnace yayi mata wannna banzar maganar aiko sai ganin hawaye yayi sharr suna gangaro mata ." numfashi ya sauke sannan ya sake kamo hannunta ya cire layter sa ya kunna sigari ya fara zuka ahankali ahankali hannu ta kai ta toshe hancinta tana tunanin abun yi ita kam tayi data sanin shiga motarsa mutun kamar mai ajanu sam shi baya son zaman lafiya yanzu daga magana me ya kawo batun ta kunna masa sigari ko shan sigari saboda Allah?"yayinda shi kuma ya kai hannu yana shafa goshinsa zuwa keyarsa .”
ahankali ta juyo garesa still hannunta na rufe da hancinta "sir !” ya kalle a d’age da gefen idanunshi “warin abar nan yana damuna "gara ki saba."gara ta saba kuma ?"wannan wace irin banzar magana ce " tayi maganar aranta “zuwa yanzu yaci ace kin fara sabawa da warin sigari "inna ilaihi "ta furta a fili"ita kam ta rasa gane inda maganganunsa suka dosa me yake nufi da hakan kuma?” tunda ya soma zugar sigarinsa bai kalleta ba sai yanzu da ya wani tsareta da tsumammun idanunshi da suka fara canza kala tare da dage mata girarsa d'aya yace "tsoro kike ji ne ?" cike da jin haushi ta fixge sigarin a hannunsa ta manna a gefen hannunta mai ciwo "kina hauka ne ?"
yayi mgnr a firgice yana cigaba da kallon hannun "kasan illar abinda kake yi kuwa ?muna cikin mota kana sha mana wannan qazantar "ka kuwa ma san yadda nake ji idan naga kana shan wannan abar ?"ta qarasa maganar tana juya masa baya sakamakon kukan daya kwace mata ."
ahankali ya kwanto jikinta tare da juyo daita garesa ya sake makale mata ya janyo hannunta ya tsura ma hannun ido "kalli illar da kika yiwa kanki "?gara wannan rad'ad'in akan zafin sigarin da kake sha a gabana "bai san sanda murmushi ya bayyana akan fuskarsa ba sai dai ya gintse yace "marayam kina da rigima "ai kai ne rigimam me ."tayi maganr a kasan ranta tana zabga masa harara."ni kikewa wannan kallon ?tayi shiru tana qoqarin janye jikinta daga nashi “kince na kuwa san yadda kike ji idan ina shan sigari ?kawar da kanta tayi gefe dan bata ma son kallon fuskarsa sai dai ji tayi ya fixgota jikinsa gbdy ta kwanto jikinsa wani irin bugawa zuciyarta tayi ta sauke numfashi tare da tsuke qaramin bakinta tana kallonsa muryarsa can qasan makoshi yace “fada min me kike ji ?"zuciyata na zafi "tayi maganar kmr zatai kuka “amm da ni ina son ki saba daita "akan wani dalili kenan zan saba ?” ni wallahi bana son warinta yana mugun d'aga min hankali bama warinta ba ni d'an sigari ma banason shi a kusa dani "to ya zakiyi dani kenan ?"ya fad'a yana hura hucin numfashi da iskar bakinsa ya qarasa maganar adaidai lokacin da a ruwa yayi magana “yalla’bai mun shigo agege “nan yayi directing dinsa inda zasu sannan ya sake janyo hannuta yana kallo inda ta kona kanta .”
“Karki sake min abinda kikayi min yanzu kalli kiga har kin kona hannunki mutun sam baya abu da tunani yana magana yana hura mata gurin nan take taji ta daina jin rad’ad’i a wajen batare da ‘bata lokaci ba suka iso unguwarsu maryama a ruwa na gama parking maryama ta dauki jakarta tace masa "goodbye sir " yayi murmushi yace "till we meet tomorrow ".da sauri ta bud’e motar ta fita daga motar tana harhada hanya, but she felt as gangar jikina ce ta fito ta bar zuciyata a cikin motar tayi kokarin calming down din zuciyarta kafin ta karasa gida ahankali ta shigo gidansu kai tsye kamar yadda ta saba da part din umma ta fara tayi knowking har sau biyu taji shiru ta kai hannunta da zumar sake knowking taji kofar ta bude "a she ma kofar a bude take ta fad'a tana tura kofar shiga parlour'n babu kowa sai umma ita kadai zaune tayi shiru tana tunanin “lafiya umma ta zauna shiru haka?” tayi mgnr a kasan ranta kana ta tsaya tana kallon hannuta dake nade da bandage tana tunanin ta fad'a mata abinda ya faru yau a office ko tayi shiru kai bai kamata ba hankalinta zai tashi matuka bayan yanzu hankalinta a kwance yake bari mr ata ya gama bincikesa sai na fada mata idan da bukatar haka ta qaraso ta dafata tana kiran sunanta "umma nah ! .”
Umma tayi firgigib ta dawo haiyacinta yace "a'a yaushe kka dawo ban sani ba ?zo ki zauna ki huta kinji diyata ta zagayo daita gabanta ta zaunar daita akan dogon table din dake gabanta tana murmushi "me Ke faruwa ne umma tun jiya na lura bakya cikin farinciki?"meke damunki babu abinda ke damuna kawai dai kaina ke d'an min ciwo umma wannna ba ciwon kai kawai bane akwia abunda ke damunki baki saba boye min komai ba idan kika boye min zanji babu dadi umma dan allah ki fada meke damunki ?nace babu komai bari na kawo miki abinci kici nasan kin gaji dayawa ".umma karki min karya yanzu Kenan bazaki iya fada min damuwarki ba ?Umma ashe zaki iya boyewa diyarki abinda ke damunki ?dan allah ki fada min meke damunki tayi mgnr Kmr zatai kuka "tabbas akwai abinda ke damuna maryama ,mutane basa da amana maryama .”
dana dawo daga ijesha na biya kamfaninmu bread in takaice miki wai dan zaman danayi agida saboda rasuwar sadam ban samu na leka ba idan kika ga barna da gali yayi sai kinyi mamaki nan ta zayyane mata komai da irin matakin data dauka akanshi "tabbas baba yayi kuskure umma daman kuma haka mutane suke kullum cikin Kuskure muke amman kiyi hakuri umma ki bashi wani dama "da wannan damar mutane suke sake kashe mutun kullum ana yi maka ana baka hakuri amman ya zakiyi umma yanuwa ne ki yafe masa umma yanzu wannan matakin da kika dauka akansa idan kika dawo dashi bana tunani zai sake aikata laifin kuma dai kice Kike koyar da na tare dake ,idan mutun yayi maka laifi ka hukunta shi sai kuma ka dawo ka yafe masa “.shike nan na hakura amman saboda ke” maryama ta kwanto jikinta tana murmushin jin dadi tace "na gode sosai umma ina qaunrki .”umma ta shafa gefen fuskata "nima ina sonki maryama "kamar ance ta kalli hannun maryama tace “menene haka a hannunki ?”
Mmn sudais
[8/31, 11:25 AM] Safwan Libiya 2: 💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
BOOK 3
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.