Maradams Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: MAR ADAMS BOOK 3 COMPLETE BY AYSHA BAGUDU.txt
Chapter 9 of 29
Page 13
Jikin budurwar na kyarma tace “wani abokin aikina ne wallahi”ta fad’a a rikice tana maida hankalinta ga wayar “kana jina?” okay gani nan zuwa yanzu “daga haka ta kashe wayar gbdy, maryama tayi shiru tare da zuba mata shayayyun idanunta tana kallonta qirjinta na dokowa da qarfi “tabbas wannna muryar da taji yanzu daga cikin wayarta tasanta kuma ba muryar kowa bace face muryar ya sadam dinta ,jikinta a matukar sanyaye ta mika mata cup din ruwa data kawo mata tana cewa”wanan murya kamar ta sadam ?”da sauri budurwar tace “no! d’an dai kina cikin alhinin rashinsa ne kikaji kamar irin nashi ne amman sam sam bashi bane wannna ,tayi maganar a rud’e zufa na karyo mata .”
“kad’an tasha ruwan ta mika mata cup din tana cewa “na gode sosai da kulawarki sai dai ina ganin zan wuce yanzu dan duk na duba banga document din da nake bukata ba “.ta qarasa maganr cike da damuwa akan fuskarta kamar da gaske “shikenan mun rasa komai na project dinmu amman allah yasa ya zame mana alkairi “Ameen! maryama ta amsa mata da haka .”tana jin wani iri a gabad’aya ilahirin jikinta yayinda kallo d’aya zakawa budurwar nan kasan bata cikin natsuwarta ba kamar sanda ta shigo ba, a yanzu a kallon da maryama take mata tamkar mai laifi ce tsaye a gabanta ji tayi kamar kar ta bari ta wuce har sai umma ta dawo sun hadu da juna ,gyaran murya budurwar nan tayi kana tace “maryama ni zan wuce duk da naso na tsaya mu had’u da umma amman wannan kiran da kika ga na amsa na gaugauwa ne ana bukatar gani na yanzu wani aiki ne ya taso amman in sha allahu zan dawo cikin satin nan muga juna da umma .”
Naunayen ajiyar zuciya maryama ta sauke tace “Kamar kin shiga zuciyata tunanin da nake kenan ku had’u da umma amman shikenan sai kin dawo muna zuba ido murmushi ya bayyana akan fuskar budurwa sannan ta soma qoqarin fitowa daga d’aki a tare suka fito .”har bakin part din umma ta rakata inda ta hango baba gali tsaye tare da aunty salma cike da tsinkewar zuciya maryama tai sallama da budurwar ta juyo ta koma bangaren umma kai tsaye dakin ta koma ta maida komai inda yake sannna ta dawo parlour’ madadin ta cigaba da karatunta sai kawai ta kira layin yusura taji yadda ko ta samu damar mikawa madam some zanenta kira d’aya ta d’auka.”
Bangaren baba gali kuwa hankalinsa kacokan ya maida kan aunty salma dake tsaye gefensa yana dubanta”maryama kamar yau bataje aiki ba “uhm ta furta tana dariyar mugunta “ai muddin ina raye kuma malamaina na aiki an dakatar daita kenan dan yadda nida ya’yana bamuji dadin rayuwa ba to wallahi itama bazataji ba muddin ina raye .” baba gali ya gyad’a kai kawai yana gyara tsayuwarsa inda aunty salma ta cigaba da magana “ka duba kaga alamarin yaron nan yusuf gabad’aya ya daina neman inda muke dan ma aikin malam yana tasiri har yanzu ajikinsa ai da dawo zai wajen wannan Shegiyar yarinyar“ai kuwa da ya cucemu kina kallo fa kullum sai na kiran layin mahaifinsa amman magana d’aya ce muyi hakuri .” wannan alamari ya fara damuna matuka dan dai burina auren ya tabbata “kar wannan ya dameka kai dai kayi shiru kawai abunka ka zuba masu ido har zuwa sanda zata fashe “.
“Allah ta wajena akwai shirin da kikeyi kenan akasa ?sosai kuwa shirin kuma babban shiri ne ai na rantse da Allah muddin ya’yana basu fara barin gidan nan zuwa gidan miji ba babu inda maryama zata sai dai bayan raina .”murmushi jin dadi ta subewa baba gali itama aunty salma murmushi take tana kallon fuskar mijinta dake kwance da annuri sosa keya ya hau yi yace “an gaishe da salama uwar gidan gali amman mai zai hana kisa ayi aikin da wannan matar zata damka mana takardun gidan biredin da ma duk wani abu daya zamo mallakin sadam ne .itama murmushi tayi tace “sha kuruminka mijina me kake ci nã baka na zuba ai duk sai sun dawo tafin hannunmu sai yadda mukayi dasu kai dai ka zuba ido kawai zaka sha kallo “an gama ranki shi dade ahaka ya juya ya nufi hanyar fita waje ita kuma ta shige ciki tana zagin maryama da umma .”
Da misalin karfe goma na daren ranar Mr ata yana zaune a tsakiyar gadonsa system ne agabansa yana duba sakonin mutane sai dai duk wani motsi da bugun da zuciyarsa takeyi makale take da tunanin maryama kusan ma yace tunaninta ya hanashi sukuni baya jin zai iya jurar rashinta yau kawai da bai sanyata acikin kwayar idanunshi ba yana jinsa cikin matsi da takura shiru yayi yana cigaba da aikinsa yayinda ahankali maganganunta suke zuwa masa daki daki babu abinda brain dinsa bai kawo masa ba ,wani yayi tsaki wani yayi murmushi yayinda itama .”bangaren maryama itama ta kasa runtsawa tunani muryar da taji d’azu take .”
muryar sai kuwa take mata acikin kunnuwanta dan koda tasanarwa umma zuwan budurwar itama cikin yanayi na tashin hankali ta hauta da fad’a tace ita sam sam bata san wata mai sunan anifa ba mai yasa zata amince daita dan haka karta sake irin wannan ganganci “.
maryama ta qara da sheida mata muryar data ji nan kuma jikin umma yayi sanyi tace “ haba maryama wai mai yasa bazaki manta komai ba dan dai kin saka kulafucinsa aranki ne yasa kike jin kamar yana raye banda abunki mutumin da’aka binne agabanki “amman kuma umma ai babu abinda Allah bazai iya ba “to shikenan tunda kince haka Allah yasa yana raye amman yana raye me yasa bazai dawo garemu ba ?”ta qarasa maganar tana fesar da wani numfashi mai zafi kana ta samu waje ta zauna ta zabga tagumi tare da lumshe idanunta .”maryama tayi wani juyi tana sake lulawa duniyar tunani .”
“idan tayi tunanin rayuwarta da irin kalubalin data fuskanta arayuwarta sai ta dawo tunanin mr ata duk dai ta dan samu natsuwa kadan dan yusura ta sheida mata bai je office yau ba “ko dai taje aiki gobe ne ko zai share bazai ce mata komai ba ?Aa maryama karki je aikin nan gobe?tayiwa kanta gargadi “ karkiyi kuskure zuwa domin kuwa ba qaramin aikinsa bane ya tozartaki kamar yadda saba tozarta duk wanda yaso, ahankali ta sauke numfashi tana kallon inda kayan aikinta yake .”nan ta soma tunanin ko zatayi wani abu koda na awa biyu ne idan ma baza taje aiki gobe ba ta kaiwa yusra da safe kamar yadda tayi yau alabashi sai ta bawa madam some ta bashi.” idan ya nemeta sai taje idan kuma bai nemeta ba shikenan sai ta hakura ta cigaba da zama a gida “.
Bangaren mrs ata ahankali ya cigaba da aikinsa kafin ahankali ya janyo d’aya daga cikin wayoyinsa ya soma neman layin some kira d’aya ta dauka cike da girmamawa tace”barka da dare sir ?”barka ya fad’a tare da yin shiru yana kallon screen din system ya d’auki second goma sannan ya cigaba da motsa lips dinsa “yarinyar nan kuwa ta kammala da ayyukan jiya ?”some tayi shiru cike da jin tsoron sheida masa cewar maryama bata zo aiki ba dan tasan ransa zai yi mugun baci idan yaji amman rashin sheida masa shima zai sa ita kanta ta janyowa kanta gagarumin matsala dan haka gara ta sheida masa muryarta na rawa tace “sir maryama bata zo aiki yau ba amman ta aiko da zane guda uku an kawo “what !? ya furta da d’an karfi nan take zuciyarsa ta fara tafarfasa “wani irin batazo aiki ba ?”batazo ba sir sai dai bansan dalilin rashin zuwanta ba kafin ta sake cewa wani abu taji kit yayi disconnecting din kira ya soma neman layin maryama .”
Maryama na kwance ta soma jin qarar wayarta wanda shine ya dawo daita daga tunanin da take,ta mika hannu ta daga ta kara a kunnenta ba tare data damu da duba mai kiran ba"Assalamu alaikum warahmatullah" muryar nan nata mai daraja da qima a wajensa, muryar nan da yake bawa girma muryar nan da babu tamkarta acikin zuciyarsa
itace ta ratsa dodon kunnensa ji yayi tamkar an cire masa duk wata laka dake jikinsa ta cire wayar a kunnenta ta duba ganin sunansa sai da qirjinta ya buga ta sauke numfashi ta maida wayar ta sake yin wata sallamar tare da yin shiru tana jiran taji yanayin da zai amsa mata sallamarta .sai dai madadin taji ya dawo mata fatan amincin data masa sai taji maganarsa cike da gadara ”ke ni ne na zama abun wulakantawa wajenki ?”
Da sauri ta mike zaune tana cewa no !no sir !! ba haka bane wallalhi bana cikin natsuwa ne shekaranjiya kayi hakuri sir “ba hakuri na kira ki bani “mai ya hanaki zuwa aiki yau ?”shiru tayi zuciyarta cike da tsoro “kaji mutumin da bai je aiki ba ko ina ruwansa da rashin zuwanta ?”am talking to you?”amm uhm “sai kuma tayi shiru ta kasa cewa komai “saboda kin rainani shiyasa kike yin abinda kika ga dama “?ta sake kwantar da muryar da ladabi tamkar tana gabanshi tace “sir ba haka bane ai tsakanina da kai babu raini yau din ne na tashi da matsanancin ciwon kai ko kwayar idanuna bana iya budewa amman kayi hakuri” ta qarasa maganar cikin muryar kasaka kwalla na cika mata idanunta alamun kuka.”
nan take yaji zuciyarsa ta karye idanunshi ya lumshe sannan yace “Allah ya baki lafiya karki manta da sauran aikin dana baki gobe ne za’a zo kar’ba kiyi qoqari kiyi da kyau karki bari a samu wata matsala ko kuskure.” tace “in sha allahu sir gobe karfe tara daidai dashi zaka soma cin karo a office dinka ta fad’a “kiyi make sure bakiyi bacci ba dan ki gama komai kafin 5:30 “ok sir zanyi duk yadda kace “ very good .”wani farinciki ya mamayeta cike da jin dadi tace “thank sir …”yayi shiru yana jin yadda take farinciki wanda yayi sanadiyyar shima ya tsinci kanshi cikin farinciki ya maida jikinsa ya jingina da abun gado ya janyo pillow ya matse a faffad’an qirjinsa yana jin tamkar itace rungume a qirjinsa “.“mr ata !ta kirasa cikin kasalalliyar muryarta mai tsananin kashe jiki da zuciya “tasan bazai amsa mata ba dan haka ta cigaba da magana “nayi maka sallama irin ta addinin muslinci har sau biyu amman baka amsa ba “still shiru yayi mata yana sauke mata numfashinsa a kunnenta “.
“dan allah ka amsa min nima kamin fatan amincin Allah ya tabbata agareni shiru ne ya sake biyowa baya har na tsawon second biyar har ta fitar da rai zai ce wani abu sai ta jiyo sautin sanyayyar muryarsa “wa alaikumussala wa rahmatullah “.ya amsa mata bayan ya sauke ajiyar zuciya. idanunta ta lumshe daga can yana duban kanshi a madubi sai yaga gabadaya ya sauya tamkar bashi ba dan shi kansa ya san baya abubuwa irin na mutane “na gode mr ata na gode da kamin fatan samun amincin Allah agare…” jiya tayi ya katse kiran tun bai ji mai zata qarasa cewa ba .”numfashi ta sauke tana godewa allah daya d’aurata akanshi dan bata d’auka zai sauko haka ba bama ta d’auka zai nemeta ba ta d’auka shikenan sai dai taji an koreta daga aiki .” ta ajiye wayarta akan gado, nan da nan ta duro ta d’auko wata katuwar takardar zane tana dubawa ahankali ta soma aiki har kusan karfe biyun dare tana aikinta .”
yadda batayi bacci ba haka shima bai runtsa ba bini bini zai kirata yaji ko idanunta biyu .”gyangyadi tasoma na alamun bacci da sauri ta dawo haiyacinta “kai bacci ka barni bazanyi ka ba har sai na kammala da ayyukan gabana babu abinda take sai Hamma , bacci ne sosai acikin kwayar idanunta amman haka ta cigaba da zane amman bacci ba’a cin bashinsa sai daya d’auketa bata farka ba sai karfe uku da rabi na dare agigice ta kai idanunta kan agogo ta sauke numfashi tana hamma “wallahi bacci nake ji ta furta cikin muryar bacci tana lumshe kwayar idanunta sannan ta bud’e tana kallon tarin takardun data baje akan gadonta ,dole sai na gama aikin nan kafin na kwanta idan ba haka ba zan had’u da tashin hankali gobe.”
ta mike ta tattara kayan aikinta ta dawo parlour’ ta d’auki remut ta kunna tv wai dan kar bacci ya d’auketa ta cigaba da aikinta amman ina bacci fa yace bai san hakuri ba ai kuwa ya kwasheta akan kujera batare data qarasa aikin ba.”shima bangaren mr ATA kwana yayi yana aiki batare daya runtsa ba haka mami bata runtsa ba, ta shigo ta kawo masa coffee ya amsa batare daya ce komai ba ta juya ta fita ya kai bakinsa yana kur’ba a hankali ya d’auki wayarsa yana neman layinta sai dai wayar na ringing baa d’auka wanda maryama na can tayi nisa cikin baccinta ganin haka ya mike tsaye ya ture system din gabanshi ya shiga zariya hannunsa daya cikin aljihunsa yayinda kunnensa ke manne da waya yana neman layinta “maryama ki d’aga wayar mana amman shiru bata d’auka ba allah dai yasa ba bacci yarinyar nan tayi ba.”?
Tana tsaka da baccinta taga yaya sadam sanye da riga baki yana tafiya a hankali ,yayinda hannunsa daya ke rike da waya dayan hannunsa kuma rike da wata kyakkyawar budurwa suna tafiya cike da annashuwa da farinciki har suka qaraso farm center dake ikeja a long suka tsaya daidai wajen wani katanfarin gidan abinci wanda babu abinda babu naci acikinsa budurwa ta kwanto jikinsa sosai tana zuba masa shagwaba tana nuna masa restaurant kai tsaye suka shiga suka samu waje a vip suka zauna inda ma’aikatan wajen suka qaraso suka mika masu wata takarda da jerin abinci da suke dashi yake zane acikinsa budurwa nan tayi shiru tana kallon hadin salad wanda yaji nama da cocomba ta sake kwantowa jikin yaya sadam ta nuna masa abinda take bukata murmushi ya sakar mata tare da shafa gefen fuskarta ya nunawa maaikacin dake tsaye nan ya tambayesu zasu ci anan ne ko zasu yi takeway .”
Ya sadam ya kalleta tace “zasu wuce dashi dan haha maaikacin ya juya cikin lokacin kankani ya dawo rike da farar leda ya ajiye masu akan table din gabansu yaya sadam ya ciro kudi agaban aljihunsa ya mikawa mutumin sannan ya kalli budurwa da yake tare daita ya kai bakinsa daidai nata zai yi kissing dinta nan maryama ta farka a matukar gigice tana kiran sunansa wanda hakan yasa umma ta farka daga nata baccin ta fito da sauri ta nufi d’akinta sai dai bata ganta ba dan haka ta fito zuwa falo tana kiran sunanta “maryama! maryama !! Kukanta yasa ta qaraso da sauri ta rungumeta tsam ajikinta tana cewa “lafiyaki meke faruwa?”ummah mafarki nayi da yaya sadam tare da wata budurwa allah umma ina ji ajikina yaya sadam bai mutu ba yana raye .”
Umma ta kwantar da kanta a jikinta tana cewa “ idan bai mutu ba maryama mai zai hanashi dawowa gida ?idan bai dawo danke ba ai ya dawo saboda ni mahaifiyarsa dana rage masa a duniya ki cire wannan tunanin cewar bai mutu ba aranki d’an mutuwa kam sadam ya mutu sai dai muyi masa fatan allah ya hada fuskokinmu a aljanna .”shiru maryama tayi tana nazarin maganarta da kuma tunanin yarinyar data zo jiya a matsayin abokiyar aikinsa sannan kuma da sautin muryar dataji irin nasa anya kuwa sadam ya mutu kamar yadda mutane suke tunani?” ita dai tana ji ajikinta bai mutu ba amman zatayi kokari taje farm center gobe .”maza tashi muje ki kwanta ki bar aikin nan haka kya qarasa gobe idan allah ya kai mu mikewa tayi jikinta a matukar sanyaye umma ta tattara duk kayan aikinta suka nufi dakinta ta kwantar daita akan gado itama ta hau ta kwanta tana shafa sumar kanta .”
kasa komawa bacci tayi saboda da zarar ta runtsa idanunta sadam dinta take gani har asuba babu wani baccin daya dauketa .”Kiraye kirayen sallah ta soma ji daga masalatai mabam bamta dan hk ta sauko daga kan gado ta shiga bayi ta dauro alwala ta fito ta isa inda sallaya yake ta d’auka ta shimfida ta soma gabatar da nafil fili haka ma umma washegari qarfe takwas daidai ta shirya cikin doguwar riga yellow ta fito ta bar gida kai tsaye farm certer ta nufa inda ta shiga gidan sai da abincin data gani ta samu waje ta tsaya tana dube dube komai da ta gani a mafarkinta haka tagani azahiri sai dai wurin babu mutane sosai tana tsaye har karfe tara tana zagaya wurin ko Allah zai sa ta gansa sai dai babu shi .”
Jiki a sanyaye ta fito tana dube dube duk inda taga gidan abinci sai ta tsaya ta nuna hotonsa ko sun gansa a wurin jiya sai dai har karfe goma bata samu wanda yace mata yaga koda mai kama dashi ba amman haka ta cigaba da nemansa yayinda mr ATA ke faman kiranta a waya tana danna masa rejecting .”tsaye yake a office yana zariya domin kuwa dai lokacin da masu kar’ban zane yayi kusa gabadaya an gama arrangement din komai maryama kawai ake jira ya sake kiranta adaidai lokacin data nunawa wani mutun hoton sadam yace “zaki dauki kiran ne ko zaki bari naga hoton da kyau ?”sorry please ta fad’a tana saka wayar a flay mood ta mika masa wayar.”
Mmn sudais
[8/31, 11:25 AM] Safwan Libiya 2: 💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
BOOK 3
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 14
Mutumin data mikawa wayar shima dai cewa yayi bai gansa ba hasalima bai ma ta'ba ganin mai kama dashi ba" yana gama fad'ar haka ya mika mata wayar ya shige ya barta tsaye cikin tsananin tashin hankali ita kanta tasan mafarki ba gaskiya bane amman mai yasa zata damu kanta akan mafarki ?"saboda zuciyarki ta kasa hakura da cewar yaya sadam ya mutu ne"ta bawa kanta amsa da haka tana dafe foring head dinta tana cire wayarta a flight mode ." Inda mr ata yake can cikin tsananin damuwa sosai ,a natse ya fito daga office dinsa rike da wayar da yake ta faman neman layin maryama yana bin kowa da wani iri kallo, yayinda kallo daya zaka masa ka tabbatar da cewar baya cikin nutsuwa da walwalarsa duk da daman ba mai sakin fuska bane amman na yau din yafi na sauran lokuta nunawa ."yana cikin wannan halin ya samu kiran gaugawa daga Z&A dan haka ya kalli agogon dake d'aure da tsintsiyar hannunsa shabiyu daidai yanzu ta buga bai koma office dinsa ba ya zarce zuwa qasa direbansa a ruwa da escout dinsa suna ganin fitowarsa duk suka zabura suka mike da sauri aka bud'e masa gidan baya ya shiga ya zauna yana jin wani irin mummunar fad'uwar gaba hannunsa ya kai gwiwar qafarsa yana kad'a qafarsa d'aya yana tunaninta."
tafiyar mintuna ta kawosu Z&A" sanda direba escort dinsa yayi parking atare escout dinsa suka firfito gbdyansu rike da bindiga suka zagayesa inda direbansa a ruwa ya fito da sauri ya bud'e masa kofa ya fito ya nufi ciki har anan ma an fahimci tsananin damuwar da yake ciki ."har yaje ya dawo damuwarsa na nan sai ma ninkuwa da tayi ko cikin kamafanin ranar kowa yasan lallai akwai abinda ke damunsa dan haka kowa ya qara shiga hankalin sa, tun daya hawo saman bai ga alamun maryama ba gabansa ya cigaba dukan tara tara amman ya dake ya samu waje ya zauna ya soma gabatar da ayyukan dake zube akan makeken table dinsa yana mamakin rashin ganinta ."bayan kamar awa biyu da shigowarsa office ya sake duba agogon hannunsa yaga lokaci ya soma tafiya amman babu alamun shigowarta ."
ahankali ya mike ya tura hannunsa d'aya cikin aljihun wondonsa yana taku acikin office din duk wani motsi da zai ji sai ya saita idanushi kan glass door kasancewar ana iya hango duk wanda ya shigo amman sai yaga ba ita bace ,nan fa natsuwarsa ta qara barin gangar jikinsa ya kasa zaune ya kasa tsaye sai kai kawo yake daga cikin office dinsa zuwa wajen office dinsa zuwa office dinsu maryama kunnensa manne da waya yana faman neman numberta tare da sake duba ogagon dake d'aure da tsintsiyar hannunsa sauran mintuna talatin wad'an da zasu zo suga representaition dinsu su qaraso ."
daga sectary dinsa har sauran abokan aikin maryama hankalinsu a matukar tashe yake sakamakon yanayin da mr ATA yake ciki ,".yana tsaye sectary ta qaraso da hanzarinta ta tsaya kusa dashi cike da girmamawa idanunshi ya tsura mata yana son yaji mai zatace masa "sir har yanzu bata qaraso ba dan allah kayi hakuri sir gashi Ina ta kiranta bata d'aga kiran ya lumshe tsumammun idanunshi dan shima layinta yake kira tana shiga bata d'agawa fuskarshi a had'e ya tsare some da kwayar idanunshi kafin a hankali ya motsa labbansa "ina yarinyar data bawa zanen jiya ?" da sauri some tayi baya kad'an ta soma kiran yusura batare da 'bata lokaci ba yusura ta fito daga office dinsu ta bayyana a gabansu cike da girmamawa tana gaishesu idanuwansa masu matuqar tsoratarwa suka sauka akanta gabad'aya yusura ta rud'e "kinyi waya da maryama yau ?"no sir !ta bashi amsa a rude ".
"kirata ko zata d'auka jikinta na rawa ta soma neman layinta"kisa wayar a handsfree "okay sir tayi kamar yadda ya buqata sai dai tana kira ta d'aga muryarta a tsarke tace "yusura !" maryama kina ina ?"da sauri mr ata ya fixge wayar ya soma magana cikin zafin rai "ke kina ne ?"kit yaji ta kashe wayar gbdy "oh shit ya furta yana dafe goshinsa yana fesar da iska mai zafi daga bakinsa yana jan tsaki byn second biyar ya sake tsare yusura da ido "akwai wanda zaki kira a gidansu yanzu domin muji halin da take ciki ?"tayi saurin gyad'a masa kai alamun eh !zufa na karyo mata "ok call !ya fad'a atakaice yana juya bayansa nan da nan ta soma kiran layin umma kira d'aya biyu umma ta d'aga byn sun gaisa ta tmbyeta maryama fa "?ai ta fita tun da sassafe lafiya yusura?"babu komai har yanzu bata qaraso office ba "zata qaraso in sha allahu dan tun sassafe ta bar gidan nan "okay to .ta fad'a tana gyad'a kai cike da tashin hankali ya wucesu zuwa cikin office dinsa da niyyar zama sai dai ya kasa zama bai sani ba tashin hankalin na meye haka na wanda zai zo ne ko kuwa na bai san dalilin rashin zuwan maryama aiki bane ko yace mai tsaidaita ?."
sectary ta biyo shi tana kwantar masa da hankali akan zata zo may be hodop ne ya riketa tunda ance tun da sassafe ta bar gida ya kalli agogon hannunsa a d'age yana cewa " wani irin hodop ne wannan har biyu saura ?yayiwa zuciyarsa tmby," ganin har kusan karfe uku bata shigo ba ya d'auki wayarsa ya shiga neman chief emeka yana kiransa ya d'auka yana cewa "shigowar mu kenan yanzu nake shirin kiranka muna qasa ka turo a hawo damu sama shiru mr ata yayi ya kasa magana yana tunanin me zai ce masa "kayi shiru ko akwai matsala ne ?uhm bari dai a shigo daku "some !"yes sir kisa a shigo da cheeif emeka ita kanta sai data ji mummunar fad'uwar gaba ta fita da hanzari zuwa inda suke ta gasiehesu cike da girmamawa sannna tace su biyota madadin suga an wuce dasu conference hall sai suka ga an nufi office din mr ATA dasu ."
"Have a set !"suka zauna me za'a kawo maku coffee ko juice "?any one !suka bata amsa ta juya da sauri ta fita, hannu mr ATA ya mika masu suka gaisa d'aya bayan d'aya sannna suka fara zantawa akan abinda ya kawosu some ta shigo ta ajiye musu juice ta samu guri ta tsaya kusa da mr ATA."shiru office din ya d'auka baka jin motsin komai sai na saukar numfashinsu har kusan mintuna talatin babu alamun za'a gabatar masu da komai cheeif ameka ya soma mgn "ya kamata ace munyi abinda ya kawomu ".mr ATA ya shafa fuskarsa wannna shine karo na farko da zai nemi wani abu akan wani bil Adam "kayi shiru bayan kasan daga inda muke ?
"Ku dan jira kad'an wacce take aikin akan designs din ne bata samu qarasowa ba amman nasan zata qaraso zuwa nan da mintuna talati "tsaki chef emeka yaja da karfi yana cewa "wannna wani irin kasuwanci ne haka ?"kasan baka kammala aiki ba ka bari muka 'bata lokaci muka zo" ya fad'a yana mikewa tsaye shima mutumin da sukazo tare ya mike da hanzari what can of nonsense is this cheeif emeka ya soma zuba ruwan bala'i ta inda yake shiga bata nan yake fita ba sectary na basu hakuri da qokarin shawo kansu amman suka ki"
Cikin haka taji sautin muryar ata a kausashe "some stop beging them" ya fad'a yana mikewa tsaye ya zagayo daga mazauninsa basu dakatar dashi ba har ya fita ya bar masu office din ."Ko bayan fitarsa hakuri sectary take basu da kyar suka wuce yana ganin wucewarsu ya dawo ya zauna akan kujera yana juyi tare da jin zafin wulakancin da maryama ta janyo masa wanda tunda yake baa ta'ba daga masa murya a office dinsa ba sai yau ."shiru yay yana dogon tunanin abinda ya hanata zuwa wani tunani yayi ya mike zambur ya fito zuwa kasa direbansa na ganinsa ya mike da sauri haka masu tsaronsa sai dai ya datakar dasu ya shiga gida baya direbansa ya maida kofar ya rufe sannan ya zagaya da sauri ya bude gidan gaba ya shiga yana mai tada motar ."
Sai da suka hau Kan titi sosai yace "sir ina muka nufa agege" ya furta yana jan tsaki tunda ya fadi haka bai sake cewa komai ba har suka hau Kan titin da zai kawo mutun zuwa agege direba ya sake tambaya unguwar dasu dake map yake dubawa ".
"Market street"! sunan unguwar ya fad'a a hankali direbansa ya karya kwana zuwa unguwar sai dai inda matsalar take bai san gidansu ba direba ya d'an samu guri ya tsaya yayi parking a gefen titi "sir gamu a market street shiru yayi yana cizan lips dinsa kusan mintuna talatin yana tunanin ta ina zai fara neman gidansu "yarinyar da tabawa zane ce ta fado masa kamata yayi ya taho daita ! some ya soma qoqarin kira,kira daya d'auka tana cewa "sir !"Ki tmbyr min yarinyar nan meye number gidansu maryama ?some tayi shiru cike da mamaki can tayi sauri ta shiga office dinsu yusura kafin ya fara mata maseefa sai dai wayam bata ga yusura ba nan da nan hankalinta ya tashi "sir banga yarinyar ba "gashi nima bansani ba dan James bai ta'ba fad'a min ba kawai dai unguwarsu ya fad'a da sunan maai..."call James ki tmbyesa yanzu karku 'bata min lokaci tace "okay sir ta shiga neman layin James ya d'auka "meye number address din yarinyar nan maryama ?dafe goshinsa yayi dan ya manta amman gidansu bai da bace ana shiga unguwar Kwanar farko gida na d'aya zuwa na biyar zasu ga gida mai kwarababben get baki nan ne gidan "okay tayi saurin discouting din kiran ta sake kiran Mr ATA ."
yana gama jin bayaninta ya katse kiran ya bude mota batare daya bari direbansa ya fito ya bude masa ba ya fito a hankali yana qarewa unguwar kallo tare da zuba hannuwansa duka cikin aljihunsa ."a natse ya dinga takawa yana kallon unguwar Allah yasa ba suyi nisa ba har lokacin suna farkon unguwar baya ya juya ya soma tafiya ganin haka direbansa ya juya Kan mota. wayarsa ya ciro ya soma neman layinta amman har lokacin bata shiga ya sake yin trying yaji still wayar a kashe take cak ya tsaya zuciyarsa na bugawa da karfi adaidai lokacin da idanushi ya sauka akan get din gidansu a natse ya cigaba da takawa acikin qazamin layinsu da dotti yayi masa over over gabansa na faduwa yana tunani mai zurfi tare da sake shiga tashin hankali dan tunda yake baa ta'ba kin d'aukar wayarsa ba ,ko kashe waya saboda dashi ba sai yau ko maza albarka bare ita mace hakazalika bai ta'ba tako qafafuwansa cikin irin wannan uguwa mai cike da dotti ba. da wannna damuwar ya qaraso daf da rubabben get din gidansu sai dai tsayawa yayi cak ya kasa aiwatar da komai "
Kamar ya nufi gidansu kai tsaye yasa ayi masa sallama da iyayenta ko tana da wani layin dabam sai kuma miskilanci ya motsa dan hk ya fasa ,ya juya a fusace ya koma cikin mota ya bawa direban umarnin su wuce ta kan titi capitol suka bi basu koma ta hanyar da suka biyo ta oniwaya ba ,sun danyi tafiya kadan daidai gidan nepa Eldorado ya hango wata kamar ita a tsakiyar titi tana qoqarin zata tsallaka, ware idanuwanshi yayi sosai babu tantama itace "stop !stop !! ya fad'a idanunshi na kanta ta yanka tabi wata kwana tana tafiya tamkar bata da laka ajikinta."ahankali direba ya samu guri a gefen titi yayi parking mr ata ya fito a natse tamkar wanda baya tare da wata damuwa ya tsallaka yabi Kwanar data bi ."
zaune ya hangota ta dafe goshinta tana wani irin Kuka mai ban tausayi hannunta rike da waya tana kallon hoton yaya sadam hawaye na sake gangarowa bisa kuncinta" shikenan na rasaka sadam ."?da gaske ka mutu baka raye ?tana kuka tana furta hakan a fili adaidai lokacin da mr ATA ya qaraso a harzuke ya soma magana cikin zafin rai da zuciya "so kina nan Kin barni cikin tsananin tashin hankali da damuwr rashin sanin halin da kike ciki ?"ya fad'a tsawace da mugun sauri ta zabura ta mike tsaye jikinta na rawa ta zuba masa shayayyun idanunta dake fitar da ruwan hawaye "sir kai ...."Kinsan irin asarar da kikasani wai ke dame kike takama."? yayi saurin tsaidaita " Kinsan yadda kasuwancina yake da matukar mahimanci agurina gabaday na daura raina akan designs dinki nasaka raina nayiwa wanda zaizo ya gani alkwari amman sai kika ki zuwa kuma idan na kiraki sai Kiyi rejecting din kirana me ma kike yi anan ki bani amsa ?"me kike yi anan?" ya qarasa mgnr a tsawace yana kallon cikin kwayar idanunta ."
Nan take jikinta ya kama rawa tsoron da matsanancin firgici ya mamaye dukkanin ilahirin jikinta muryarta cike da in inna ta soma mgn "sir nayi .."Karki fad'a komai bana son jin komai daga bakinki keep quite ya fad'a yana nunata "just keep quite bana son jin komai saboda nasan duk abinda zaki fad'a nonsense ne wai a haka kike son ki zama profetional a ma'aikatan mu?Kinawa mutane iskanci da kika ga dama saboda kina daukar wai dan kin iya designed yasa kike samun aiki cikin sauki ?shiru tayi ta cigaba da kukanta tunda ya hanata cewa komai da bala'i sa byn shine ya tmbyeta ."mutane dayawa suna aiki akarkashinmu kuma dukkaninsu professional ne ban ma san me yasa na baki aikin ba ,it's my mistake ."yayi mgnr yana furza mata iskar bakinsa a fuskarta "kuskurena dana yarda dake yana gama maganar ya juya mata baya yana sauke wani wahalallen numfashi tare da rike kugunsa da hannu daya ."
"Dan allah sir ko zaka bani dama nayi maka bayanin dalilina kuma ina fatan zaka fahimceni "what !?ya furta a matukar tsawace tare da juyowa ya tsura mata tsumammun idanunshi da suka canza kala "what do you want to explain?ke kullum cikin kawo uzuri kike "babu wani uzuri da zan kawo maka"
itama tayi masa magana a tsawace kallonta ya tsaya yi kamar wanda aka dasa shi a gurin "kana son kasan me yasa ban samu zuwa office na kawo maka aikinka ba ?ta tmbayesa hawaye masu zafi na zubo mata muryarta a raunane cike da kuka ta cigaba da magana "jiya ina tsaka da aiki sai bacci ya daukeni acikin baccina nayi mafarkin mijina sadam adaidai farm center ."
"wani mugun kallo ya dauketa dashi tunda ga samanta har kansa ta cikin glass dinsa zuciyarsa na rawa ,nan take ya tsinci kansa cikin wani yanayi mai wuyar misaltuwa wani irin kishi ne ya mamaye zuciyarsa da ilahirin jikinsa qararrawar dake kadawa a qirjinsa ta soma aiki cikin sauri sauri " nayi mafarkin mijina sadam ne kuma daman ni ina ji ajikina yana raye bai mutu ba shine na fito nemansa gashi duk na gama yawo ban samu mutun daya da yace yaga ko mai kama dashi ba ,na ma rasa ya zanyi da rayuwata domin na rasa wanda zai taimaka min ,ina tsananin bukatarsa arayuwata shine mutun nã farko daya tsaya tsayin daga ya jajurce akaina yasoni ya qaunaceni har muka zamo maaurata wanda sanadiyyar aikina muka rasashi zukatanmu na tsananin bukatarsa."tana magana tana kuka tamkar wata zautacciya ni bana son kowa bana son ganin kowa a yanzu sai shi nayi yawo har na gaji ban ..".
"Yanzu dan wannan banzar dalilin ne ya hanaki kammala aikina ?cak ta tsaida maganarta da kukanta ta tsura masa shayayyun idanunta tana kallonsa cike da tsantsar mamaki dan sam batayi tunani zai nuna rashin Imani akanta ba, ya furzar mata numfashi har sai dataji saukarsa a fuskarta "shiyasa nace miki karki fara aiki dani da wannan tunanin naki ,na fad'a miki karki zo min da tarkaen shirme irin haka ko ban fad'a miki ba ?tai shiru tana cigaba da kallonsa "ans..! ya fad'a a matukar fusace kana kallonsa kasan zuciyarsa cike take fal da matsanancin kishi duk wanda zai cigaba da adana abinda ya wuce yana tare da katoton wahala idan bakiyi qoqarin ki cire abinda ya wuce aranki ba zaki qare rayuwarki ne cikin kunci .""amman Ke naga alamun kullum kina son ki mutu da abinda ya wuce arayuwarki ne ."yayi mgnr a tsawace."
" kawai kin batawa mutane lokaci ,sannan kina ta wahalar da kanki kina yawo kawai dan akan mutumin da baya exit a wannan duniyar "wani kallo tayi masa mai dauke da fasara ya kalleta sosai "yes haka nake nufi da yana raye da iwar haka ya dawo gareku amman ina mamaki da wannna dakikiyar kwakwa luwartaki ta kasa fad'a miki gsky ta kasa yarda da ya matu tsura masa ido tayi "yes haka nake nufi ."da yana raye da iwar haka ya dawo gareku kwakwaluwarta ta sake maimaita abinda ya fad'a mata wannna Karan kam wani kallo take masa mai dauke da natsuwa akan maganarsa "kamr fa gsky yake fad'a mata ya kamata ta natsu ta dawo haiyacinta ta cire sadam a duniyarta tunda daman can ba sonshi take ba daga baya ne komai ya sauya agareta take jin wani irin tausayin umma dashi kanshi yaya sadam din har hakan yasa tayi masa kyakkyawan mazauni na musamman a zuciyarta ya zamo zazzafar soyayya ."
"ina mamakin yadda kike yin wasu abubuwan kamar baki zauna a class ba ya kamata ki zama mai dauriya akan komai karki bari rashin wani ya shafi lafiyar ki, kallonsa ta cigaba da yi ."sannan ki sani yau na rasa appotunity dina akanki babu wani mahaluki da yake iya kallon kwayar idanun Adam Tariq abdullahi ya fad'a masa magana amman yau kinsa anyi min ,he happened only because of you ."sheshekar kuka take tana kallonsa cike da tashin hankali "idan zaki manta past din Kiyi ki cigaba da rayuwarki idan bazaki ba wannan matsalarki ce kece zakiyiwa iyayenki da kanki asara dan wanda ya mutu baya dawowa "yana gama maganarsa ta karshe ya juya ya barta tsaye hankalinta a matukar tashe .ahankali ta soma yin kasa har ta zube kasa bisa gwiwayoyinta tana wani irin kuka tana kallon hoton sadam " mr ata bazaka ta'ba fahimtata ba bawai bazan iya manta sadam bane amman it's not easy to me ko dan darajan mahaifiyarsa dole ne na cigaba da son shi a zuciyata ."
Mmn sudais
[8/31, 11:25 AM] Safwan Libiya 2: 💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
BOOK 3
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.