Maradams Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: MAR ADAMS BOOK 3 COMPLETE BY AYSHA BAGUDU.txt
Chapter 8 of 29
Page 10
Maryama tayi shiru tana kallonsa da bayyanane mamaki a saman fuskarta yayinda qirjinta ke wani irin dokawa da sauri sakamakon bakincikin da yayi wa zuciyarta diran makiya ,ahankali ta soma nazarin maganarsa babu abinda yazo cikin kwakwaluwarta sai tozarci so yake ya tozartata baya ga haka babu wanda zai ga zanen data zana bai sa albarka ba had’iye bakincikinta tayi ta d’an saki fuska still kwayar idanunta na kanshi tare da sakin kasalallen murmushi wanda dole tasa mr ata ya lumshe tsumammun idanunshi wad’an da suka wadatu da gashin idanu kamar yadda girarsa take masu kama da wanda yake jin bacci .cikin sanyayyar muryarta mai taushi tace “idan na fahimceka kana son na sake wani kenan?”fuskarsa babu walwala ya lumshe mata ido tare da jinjina mata kai .still shiru tayi tana dubansa shima kallonta yake da kwayar idanunshi yadda yake kallonta ne ke sake d’aga mata hankali domin kallo ne da bata ta’ba cin karo da irinsa ba a tun tsawon rayuwarta.”
“ take tsoron yanayin yadda yake kallonta ya mamaye zuciyarta da gangar jikinta wanda ta rasa a muhallin da zata saka, kallon ne na gargadi ko kuwa na rashin mutunci ne ?”dan baza tace kallon soyayya bane dan matsayi da darajanta basu kai wannan matakin ba a wajen mutun kamarshi “wacece ita ?za dai tafi ajiyesa a muhalin gargadi ne .”tsaki yaja kafin a hankali ya kalli agogon dake d’aure asintsiyar hannunsa yace “mintuna talatin na baki kacal ki canza min “wani ta kalleshi kawai sannan ta motsa lip’s dinta “okay sir !”ta soma taku a natse har ta qaraso kusa dashi bai yi alamun bata hanya ba dan haka muryarta a sanyaye tace”sir ko zan iya wucewa ?”no ! ya bata amsa adake yana had’iye duk wani emotion din da yake ji a gabad’aya ilahirin jikinsa. “fuskarsa babu annuri ya sake sanya kwayar idanunshi cikin nata yana mai nuna mata wajen zama da d’an yatsan hannunsa “ki zauna kiyi anan .”“mamakinsa ya sake kamata .ahankali ta sauke naunayen ajiyar zuciya cike da girmamawa tace “sir kayi hakuri na koma office nayi acan zan fi samun natsuwa “me zai cinyeki anan ?”ya watsa mata tambaya yana mai tsareta da idanunshi”.
Shiru tayi tana nazarin maganarsa komai zai yi cike da gadara da nuna isa yake kamar ba aiki suke akarkashinsa ba shi ya haliccesu , cike da fargaba ta rausayar masa da kwayar idanunta sannan tace “babu kawai banason nayi anan ne “to anan din zakiyi kiyi maza ki fara yana gama fad’ar haka ya soma taku.”dogon hancinta ta d’an hura tana jan tsaki a ranta bata jin zata iya kasancewa daga ita shi ,wannan firgitaccen kallon nasa kad’ai ya isa yasa ta kasa aiwatar da komai dan haka cike da danne tsoronsa ta kai hannunta zata tura kofa fita a matukar tsawace ta jiyo sautin muryarsa “ke bana son iskanci da rainin hankali ko ni saanki ne ?”yayi maganar tamkar bashi yayi ba .”
Jikinta a sanyaye ta juyo tana kallon bayansa kafin ta sadaukar ranta dan bata da yadda zatayi yanayinsa na yau babu sausauci komai zai iya faruwa daita idan tayi masa taurin kai ,gara tayi masa abinda ya bukata kawai ta kama gabanta,ahankali ta soma takowa cikin natsuwa a natse ta qaraso ta zauna akan kujerar daya nuna mata ta zauna tare da zabga tagumi, tana kallonsa ya zaro farar takarda guda d’aya ya d’auki roban da pencil gbdy yake jere aciki ya nufi inda take zaune ya ajiye akan table din gabanta “start!” ya fad’a a dakile sannan ya juya ya wuce ya koma mazauninsa tare da juyar da kanshi gefe yayi kamar bai san da wata halitta zaune ba .”
kallonsa kawai take tana mamakinsa yayinda zuciyarta ke cike da rauni tana jin kamar ta rusa masa kuka, kwatakwata bashi da imani bare tausayi ta kai dubanta ga farar takardar da ajiye mata sannan ta zari pencil d’aya ta rike tare da yin shiru tana tunanin ta inda zata fara ta d’auki tsawon minti goma sannan ta fara ,lokacin daya ga ta maida hankalinta kan aikin daya sakata ne ya juyo da hankalinsa gareta yana kallonta yana jujjuya jikinsa yana jin soyayarta na fixgarsa, domin ji yake matukar bayi saurin killaceta a gidansa ba zai iya rasa ransa akanta sam baya jin dadin yadda yake mata amman yarinyar ce ya fahimci tana da raini shi kuma duk son da yake mata bazai yarda ya d’auki raini ba zai sota hakazalika zai hukuntata idan tayi masa ba daidai ba ” .
bayan kamar minti goma ya mike tsaye maryama taga tahowarsa amman bata d’ago kanta ba dan kwata kwata bata son ko kallonsa a yanzu dan kallonsa zai haddasa mata jin mummunar tsanarsa acikin ranta ,har ya iso inda take zaune ya tsaya akanta yayinda ta tattara dukkanin natsuwarta kan zane da take bata d’ago ba ,har sanda ya janyo kujera gabanta ya zauna tare da ware qafafunsa still bata bar abinda take yi ba .ahankali ya gyara zamansa ya duko da kanshi daidai kanta yana kallon zanen. numfashi ta sauke ta bar abinda take tana jin yadda qirjinta Ke bugawa da karfin gaske sakamakon dab da junan da sukai wanda da zai matso da kujerar kad’an zasu iya had’ewa da juna “ki cigaba da aikinki kada ki ‘bata min lokaci kisa nayi asara .”ya furta cikin wani irin salo da sautin murya hucin bakinsa da numfashinsa na shiga hancinta wanda ya haddasawa tsigar jikinta mikewa “.
“sir ko zaka ..” bata kai ga yin magana suka ji an turo kofar glass din office din an shigo .”sautin muryar ammar dake d’auke da sallama yasa mr ata ya waigo bayansa ido cikin ido suke kallon juna da ammar . ganin ammar bai sa mr ata ya mike ko gyara zamansa a gaban maryama ba illa ma ya cigaba da mata bayanin yadda yake son tayi masa zane da kallo ammar ya bisu yayinda maryama bata masa ba sai gyad’a masa kai tayi tana jin kamar ta fashe da kuka amman ta danne dan muddin ya gane hawayenta shine rauninta ta kad’e a hannunsa “so take ta d’ago su gaisa da oga ammar amman ta kasa dan wata irin faduwar gaba take ji saka makon kusancinta da mr ata gashi yaki mikewa bare ya barta ta samu natsuwa .”
ammar ya koma jikin window office din ya d’an zuge labule kad’an yana hango haraban ma’aikatan dan yasan ko yayiwa ata magana ba lallai ya sauraresa ba .sai da mr ata yayi raayin tashi dan kashi sannan ya mike ya tura hannuwansa duka cikin aljihunsa ya qaraso inda ammar yake tsaye batare da yace masa komai ba “mutumina kana shaa’aninka har kun fara soyayyar ne ?“oh my god sai ka bari taji? ya furta a can qasan makoshi ta yadda idan ba bakinsa ka kalla da kyau ba bazaka fahimci abinda yace ba .”
murmushi ya kwace a saman fuskar ammar “kar dai ka tsaya ‘bata lokaci ?ammar kayi kasa da muryarka mana “okay amman mutumina kayi zafi zafi fa karkaje garin neman gira ka rasa ido kar wani yayi maka shigar sauri a ma’aikatar nan “babu wannan mahalukin a yanzu idan ka ganta da wani to ni ne idan zata só wani to ni ne .”ammar yayi murmushi yana kallon inda maryama take kamar tasan kallonta yake ta d’ago idanunta da suke ta tara hawaye tana dannesu ta saukesu akanshi tana qoqarin motsa bakinta domin gaishe da ammar yayinda ammar din tuni har yayi taku d’aya ya jiyo muryar ata cikin rad’a yana cewa “karkaje !ammar ya tsaya cak yana fuskatarshi “ko me yasa ?”gaisawa kawai zamuyi daita “bana bukata dan nasan halinka byn gaisawa har da rayuwata zaka shiga .”
sanyayyar murmushi ya subuce masa sanda yake hango kishinsa a fili “me kake tunani akaina ?amman dai tunaninka kar yaudareka kasan bazan sota ba ?”ata yayi shiru adaidai lokacin da wayar mr ata ta soma ringing yaja qaramin tsaki yana jin haushi “mutanen nan suna son d’aga min hankali wani tsakin ya sake ja sannan ya kalli inda maryama take yace “Ke ..”tana jinsa tayi masa banza tamkar bataji shi ba “am talking to you ina magana kina jina “.a sheke ta d’ago ta kallesa kwayar idanunta cike da rauni da ‘bacin rai “karki ‘bata min lokaci kin gama “?kamar tayi masa banza sai kuma ta tsinci kanta da ce masa “sauran kad’an na gama ,oga ammar ina kwana ?kina lafiya maryama ya fama da wannan abokin nawa ?numfashi kawai ta fesar “.tana ta’be bakinta ina ruwanta dashi bare tayi fama dashi ta maida kanta ta cigaba da aikinta.”
Ammar ya juya kan ata wanda ya koma mazauninsa shima kujerar dake fuskarsa yaja ya zauna “kai mutumina kabi yarinyar nan ahankali fa “wani abu kaga nayi mata ne da zaka zo min da wata magna ?” ji yadda kake mata magana, kana kallonta kasan bata jin dadin aiki da kai “kar Allah yasa taji ,kana ganin yarinyar nan muguwar yar rainin sense ce kai kaga rashin mutuncin da ta min jiya ace ba ita bace wata ce dabam da yanzu na koreta “me ye tayi maka ?amman bana tunanin maryama tana da matsala nayi aiki daita “nan mr ata ya shiga magana kasa kasa yana koro masa abinda ya faru ai kuwa ammar yayi dariya kamar me “wallahi tayi min daidai haba ai kai din ne baka da kyau shine ka wani tasa diyar mutane gaba kana son firgita masu yarinyar Allah zan fad’a mata ta cigaba da jajurcewa
“tashi mu bar office din nan karka ballo min ruwa .”tare suka mike ata ya zagayo suka fita wanda hakan ya bawa maryama damar aiwatar da aikinta a tsanake .”
Bayan minti goma ya dawo shi kad’ai ya zauna a mazauninsa ya tsarke hannuwansa duka cikin juna ya rike ha’barsa dashi yana kallon zara zaran yatsun hannunta dake kwance tana zane, komai nata dabam ne bai ta’ba ganin halittar data shiga zuciyarsa kamarta ba “kin sace zuciyata ya Allah ka shigar dani zuciyarta da rayuwarta domin na zama abokin rayuwarta na har abada ita dai maryama bata san halin da yake ciki ba ta dukufa kan aikinta.”bayan kamar minti shabiyar ta gama ahankali ta d’ago kanta karaf idanunshi ya tsarke cikin juna wani irin bugawa da karfi qirjinsu yayi take yayi saurin wayancewa “kin gama ne ?”jikinta a sanyaye gabanta na faduwa tayi saurin gyad’a masa kai .”ya mike tsam ya d’auki zanen data fara zanawa ya tako har inda take.”
tana ganin tahowarsa tai saurin mikewa tsaye ta mika masa takardar cike da girmamawa ya kar’ba ya soma dubawa yana taku ahankali ahankali acikin office din yana duba dayan zanen da tayi .gani tayi ya ajiye zanen farko da tayi a daren jiya sannan ya kai d’ayan hannusa ga zanen da tayi yanzu yayi kuci kuci da takardar ya watsa mata “shima wannan bai min ba har gara na farkon zaki iya tafiya sannan ki godewa allah zuwanki ma’aikatan nan ya gyara rayuwata yayi sanadiyyar sauyawata da wani labarin akeyi ba wannan ba akan iskancin da kike min jiya .”ya qarasa fad’a yana tsareta da tsumammun idanunshi ,bata bari ya qara magana ba ta ra’ba ta gefensa har jikinta na gogan nashi sbd kusanci ta wuce zuciyarta tamkar zata kama da wuta kuka ne ke qoqarin kufce mata amman ta danne saboda ganin idanun mutane gabad’aya taji aiki akarkashinsa ya fita ranta tana shiga office dinsu ta zauna tana sauke numfashi.”
maganganunsa suka soma dawo mata wanda ta kasa fahimtar inda suka dosa me yake nufi tana bukatar tasan me yake nufi “ki godewa allah zuwanki ma’aikatan nan ya gyara rayuwata yayi sanadiyyar sauyawata da wani labarin akeyi ba wannan ba akan iskanci da kika min jiya “kamar yaya kenan yake nufi ?wani mummunar abu yake yi mara kyau wanda zuwanta yayi sanadiyyar sauyawarsa ko me ?” to ita a wa kenan data sauyasa ganin kwakwaluwarta na neman daurewa yasa ta kad’a kai tare da yin watsi da maganarsa maimakon cigaba da tunani sai ta janyo jakarta ta fito da kayan aikinta ta fara wani aikin wanda some ta ajiye mata .”
******
Washegari
11:00 dot a office dinsa tayi masa gbdy ma’aikatansa suka dinga shiga office dinsa domin gaishesa a dakike ya dinga amsa masu kwayar idanunshi maryama kawai take son ganin sai dai har lokacin da karfe shabiyu ta buga babu maryama babu alamunta a office dinsa kamar yadda sauran ma’akatansa suka saba shigowa byn sun yi gaisuwa idan akwai aikin da yake bukata ayi masa sai yasa some ta basu mikewa yayi rike da wasu file guda biyu ya fita ya ajiyewa some sannan ya shiga office din da take aiki .”hangota yayi zaune tana aiki ahankali ya zarce inda take yace ta biyosa sannan ya juya ya fice daga office din ya koma office dinsa .”kamar maryama bazata tashi ba amman sai fahimci idanun sultana suna kanta dan haka tá mike ta shiga office dinsa ta samu waje ta tsaya a gabansa fuskarta a had’e tamkar wacce aka aikowa da sakon mutuwa .”
gabansa ne yayi wata mummunar fad’uwar ya tsura mata ido ta bala’i qara shiga ranshi haka yake son mace jajitacciya mai natsuwa da kamewa “manyan ma’aikatana sun shigo domin gaisheni ke me yasa baki shigo ba ko kinfi karfin kizo ki gaishe dani ne ?”ta tsura masa ido kamar tace masa siyanta yayi ko ita bawarsa ce amman sai tace “shigowa gaisheka yana cikin kaidodin aiki a karkashinka ne ?”baya ciki ikona ne yasa hk “okay !ta fad’a tana gyara tsayu warta tana ciza gefen lips dinta alamun bazatayi ba .”
yaji kamar ya fixgota yayi mata muguwar matsar da zai sa ta shiga hankalinta ,ya tsura mata ido kawai har kusan mintuna talatin sannan yace ta dauki file din gabansa “ta kai hannunta ta dauka ta soma dubawa “ kije ki duba page 9 da 10 irin zanen da nake bukatar ne ki natsu Kiyi min aiki mai kyau “amman sir da ka kira wadan da suka fini kwarewa zaka fi samun abinda kake bukata kar nazo nayi maka kace bai maka ba .”ta qarasa fad’a tare da maida file din inda ta d’auka yayi murmushi aciki ranshi yarinyar nan tana son na koya mata hankali tana son nayi mata abinda banyi niyya ba “ki dauka kije kiyi abinda nake so taki d’auka ta cigaba da tsayuwa.”
a tsawace yace “take it and leave me my office”numfashi ta sauke tana yatsunsa fuska ta juya har ta kai bakin kofa yace “ke!” ta tsya batare data juyu ba “awa uku kawai na baki “ta qarasa ficew tana cewa “aikin banza ai dakasani ka bawa wasu sun maka kaga aikin shirme duk wannan abun akan idon some ya faru ta cika da mamaki karo na biyu kenan maryama ke sainsa da mr ata .”Ahankali sultana ta mike zata bar office din sai ga some ta shigo tace “ ina zuwa ?”tayi mata banza “at least ki zauna ki d’an yi wani aiki mana tunda kika zo yau bakiyi aikin komai ba.” sultana ta kalleta a wulakance sannan ta soma magana cikin tsananin fushi “kina hauka ne ? “aiki sai naga dama zanyi dan bama fama da yunwa da tallauci aikin nan ra’ayi ne ko nayi aiki ko kar nayi dole kuma abiyani saboda mahaifiyata tanada karfin iko acikin wannna kamfanin dan haka daga yau ido ne naki akaina dan ko mr ATA bai isa ya koreni daga wannan ma’aikatanr ba dan banyi aiki ba okay.”
Some bata ce mata komai ba har sultana ta qarasa inda maryama take zaune ”uhm Ke dai bagajiya da aiki kamar ba d’azu kikayi wani aikin yanzu kuma kin dukufa yin wani “me ya kawo ni ?”ai aikin ya kawoni kinga dole nayi”sultana tayi shiru can ta cigaba da mgn “duk aikin da mr ATA ya kawo bakya sallakewa ?”taya zan tsallake me ya kawoni idan ba aiki ba kuma dai ai shi din mai gidana ne dole nayi masa duk aiki daya sakani sultana ta cigaba da surutu mara ma’ana “maryama tace “kinga sultana kin dameni ni fa ina son aikina “ ko ma dai menen bazaki ta’ba burge mr ATA ba “banzo dan na burge kowa ba nazo dan nayi aiki ne oky sultana taja tsaki da numfashi sannan ta fita “.
Some ta tsaya akan maryama !tana kiran sunanta “yes ma ta tsaya kusa daita rungume da file “duk cikin masu aiki a kamfanin nan daga manya har kana babu wanda Ke iya maidawa sir magana saboda tsoro amman naga ko kad’an bakijin tsoron komai kina iya mutsu dashi kina iya magana dashi kai tsaye tun shekaranjiya hankalina a tashe yake sai gashi naga sir yayi shiru bai ce komai ba “Eh ! nima nayi tunanin zai ce wani abu sai naga bai ce ba sai abu na gaba nima ina jin tsoronsa kamar kowa “really!?” yes ma !ta fad’a tana sakar mata murmushi “na danne nawa tsoron ko nace so nake na cire tsoronsa dan naga alamar kowa najin tsoronsa shine nake son na cire kaina ya zamo ban dani sannan kuma na rufe damar da zai fad’a min abinda ya ga dama, no chance for him “shiru some tayi tana sauke numfash.”sannan tace “ki dai bi ahankali “okay ma .”
Cikin yanayin na tashin hankali sultan ya shigo office din mr ata yana huci tmkr zaki ya soma magana “yana cewa wai me ka d’auki kanka ne komai kai sai ka nuna wa mutane isa da mallaka , kayi iko akan kowa ,kayi iko akan komai, Ka dinga abu da d’agawa naga alamun so kake ka mallakemu gbdy da kamfanin “mr ata bai ce masa uffan ba illa ya fesar da numfashi mai zafi kana ya mai da jikinsa sosai akan kujera tare da lumshe idanunsa inda sultan ya cigaba da fadar magana son ransa idanunshi ya bude a hankali cikin yanayin tashin hankali ya ci gaba sauraronsa “kamfanin IGA mu suke bawa aiki amman dan rashin godiyar allah irin naka sai da kayi munafurcin da suka kawo maka aiki “ me muka tsare maka me ala dole so kake ka malleke kamfani .”
“Mallakar kamfani kuma na nwa ?ai tun tuni na mallake ,kuma babu wanda ya isa yayi abinda yaga dama matsawar ina cikinsa ,kai kanka kasan nafi karfin na tallata sanaata ga kowa bare IGA “ abu na farko bansan ku kuke masu aiki ba sun bukaci aiki daga gareni kuma nayi masu abinda suke so amman kawai saboda burika kullum ka ci min mutunci ko kayi abinda zan bar kafanin nan ka maye gurbina ka zama MD na wannan ma’aikatar shine zaka zo kana fad’a min mgn kana son matsayina sai dai baka da wannan kokarin sannan baka da talent din sannan daga yau idan kana son ka zo wurina ka dinga amfani da common sense din kafin kazo okay yayi maganar a tsawace .”
“Adam kana wuce gona da iri acikin kamfaninmu ka tattara kwararu masu aiki a wurinka ka hana kowa ya dinga sakasu aiki sai kai kad’ai “mr ata ya kallesa a kaskance jin ya shigo da wata maganar bai kai ga cewa komai ba yaji ana neman izini “ko zan iya shigowa ? aka fad’a daga bakin kofa”kullum kana jin dadin ganinmu cikin damuwa kullum burinka kaga komai namu ya tsaya .” shi dai mr ATA bai ce uffan ba dan daman tuni ya maida idanuwanshi kan system.“daga yanzu zan fad’awa gabadayan family’s dake aiki acikin kafanin nan kada wanda ya sake bin umarninka ko bin wata dokarka acikinmu dan baaajiyemu kayi ba “ maryama taji shiru ba’a bata izini shiga ba tace “sorry sir ! ta juya da sauri ta koma kasancewar taji kamar alamun fad’a “sultan kana damuna alhalin kasan bana son damuwa dan Allah zaka iya tafiya please .”
“Bazan tafi ba sai lokacin dana ga dama dan ba kai kad’ai kake son yin abinda ka dama ba wai har kamar ni zan sa akira min yara zan sakasu aiki suki bin umarnina wai suna maka aiki “rashin tunaninka bazai bari ka fahimci komai ba kai kasani babu wanda zan hana yayi maka aiki sai dai idan suna min aiki amman tunda idanunka yanzu sun dawo Kan ma’aikatan dake karka shina saboda a tunaninka sune nasarata muje ka zabi duk wacce kake son tayi aiki da kai .”wani farinciki ya kama sultan saka makon burinsa ya cika sai dai yaki bayyana hakan dan kar mr ATA ya fahimta ya canza ra’ayinsa dan yasan halinsa .”
Mr ata ya mike ya fito sultan ya biyo bayansa cike da farinciki kai tsaye office din su maryama ya shiga akayi saa duk kusan wadan da yake aiki dasu suna gurin har maryama tunda ya shigo gaban maryama ke fad’uwa sakamakon idanunshi dake kanta “ya numfasa sannan ya soma magana “acikinku wa yake son yayi aiki akarkashin sultan ?gabadaya office din yayi shiru babu wanda yayi magana wanda hakan ya nuna basa bukata ,maryam kam taso tace zatai aiki dashi tunda shi wannan balainsa yayi yawa amman har sanda mr ATA ya gama maganarsa ya shiga wata bata iya cewa komai ba “duk wanda yake bukatar yayi aiki akarkashinsa ya daga hannu? nan ma shiru maryama ta kalli gabadayansu ma’aikatan wurin taga babu alamun akwai wanda Ke bukata dan haka tayi qoqarin daga nata hannun wanda hakan yasa cikin hanzari mr ATA ya cigaba da magana wanda kuma yasan zai kasance akarkashina ya daga hannu ?gabadaya suka daga hannu banda maryama alamun bata tare dashi .”
sultan yaji zafi sosai kenan duk matanka iko da kaidodin da yake masu da balain da hantararsa sun fi bukatar kasance akarkashinsa akan shi lallai sai ya tashi tsaye akan ATA .”wani kallo mr ATA yayi wa maryama ganin har lokacin taki daga hannunta yayinda kowa hannunsa Ke sama d’auke idanunta tayi cikin nashi tana hura hanci “ka gani sultan babu ruwana kawai ni business dina ne agabana bani da burin shiga hakin kowa idan kamfani ne kasan ina dashi masu tarin yawa anan ma ku nake taimakawa da rayuwarku domin idan na barshi barayin cikinku zasu karyar da kamfani qarshe ku dawo kuna bara a wurina which’s very bad .”ya fad’a yana kallonsa a dage ,yanzu ko zaka iya tafiya kasa a nemo maka wasu maaikatan da zasuyi aiki da kai dan wadan nan nawa ne ?”
Tun bai kai ga rufe baki ba maryama tace “sir ko zan iya cewa wani abu ?yayi shiru yana dubanta cikin tsananin fad’uwar gaba yana fargaban bata damar yin mgn d’an bai san me zatace ba hakan nan ya tsinci kanshi cikin tashin hankali da fargaba dan dai shi din miskilin kanshi ne da gabadayansu zasu iya fahimtar yanayin daya shiga “kayi shiru sir ko zan iya cewa wani abu ?ta sake maimaitawa sai daya sauke naunayen ajiyar zuciya a boye sannan yace “yes!.ta rausayar da kwayar idanunta cikin nashi sannan ta bude baki a natse ta soma mgn “sir dayawa daga cikinmu suna jin tsoron su amince da wannan da bansan ko waye shi ba sbd da kai koda kuwa suna só , haka zalika suna jin tsoron suki amincewa da zama kusa da kai duk dai saboda tsananin tsoronka .”sultan ya gyada alamun ya gamsu da maganarta domin daí gsky magana ta tsage ta fad’a kuma ta burgesa sosai kawai ka barshi ya zabi wadan yake so acikinmu .”
gabansa ne yayi wani mummunar faduwa nan take fargaba da tashin hankali da yake ciki ya qaru ya tsura mata tsumammun idanunshi sosai yana jin wani iri a ilahirin jikinsa shi da yake burin matso daita kusa dashi sosai idan ya kasance sultan ya zabeta fa ya zai yi ?muryarsa a kasalance yace “me kika ce ?karka yi kamar baka jita ba alhalin kaji abinda ta fad’a,wannan yarinyar gsky ta fad’a domin ta kawo mana masalaha dan haka zan zabi wadan da nake son suyi aiki akarkashina cewar sultan ,mr ATA bai ce uffan ba illa ya runtse idanunshi qirjinsa na wani irin luguden bugu dan dai itace ta kawo wannan tsarin da wani ne da shi kad’ai yasan irin azabar da zai yi masa amman ko yanzu bazai barta haka ba sai ya hukuntata .”
“Ba wai kai mai wayo ba ,yasan yayi hakan ne dan yasan babu mai zabarsa acikinsu sai gashi acikinsu din dai wata ta kawo masu masalaha sultan yayi mgnr aransa Ahankali ya soma zaba ya nuna surayya da sauri tace “sir ni yanzu haka ina Kan wani aiki ne ban gama ba “shiru tunda na zabeki ki shin ga cikin list, jin hk yasa mr ATA ya bude idanunshi da kyar tare da tsintar kanshi da yin adduar kar ya zabi maryama yayinda maryama ta matsu bai yi pointing dinta ba ya nuna wasu maza guda biyu sannan ya nuna sultana da sauri itama tace “haba yaya me yasa zaka min haka ni dai ka barni nafi son nayi aiki tare da ya Adam .”
Mmn sudais
[8/31, 11:25 AM] Safwan Libiya 2: 💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
BOOK 3
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 12
“Har mr ata ya fito haraban ma’aikatan zuciyarsa tafasa take . da wannan d’acin rai ya qaraso gida duk wani d’aga hannu da securities suke masa bai kalli inda suke ba ,hakan yasa duk suka shiga hankalinsu alokacin da jerin motoncinsa suka paka babu wanda yayi kaud’in isa inda yake dan duk lokacin da yanayinsa yayi haka to gagarumin bala’i ne zai biyo baya.haushinsa ba’a iya kan wanda ya ta’bosa yake tsayawa ba har akan wanda bai da ruwa da tsaki yake saukewa , dan a irin wannan lokacin yake korar mutun daga aiki ko kuma ya bawa mutun hutun satittika.” tun kafin yasa kai cikin babban parlour’n gidan ya soma jiyo hayaniyar mutane sai lokacin ya tuna ashe gobe ne zaayi sunan auta.” a dake ya sanyo kai cikin parlour’n fuskarsa babu digon annuri bai tsaya ba kai tsaye samansa ya nufa batare daya kalli tarin matane dake zaune a parlour’n mami ba, ita kanta mami bai nemita ba sakamakon kansa dake masa mugun sara .
“Ahankali ya zauna akan daya daga cikin kujerun cushions din parlour’n sa kanshi na cigaba da sara gabadaya ya kasa samun natsuwar zuciya da kwanciyar hankali.”ji yayi muddin bai kira maryama ya mata bala’i ba bazai ji dadi aransa ba sannan zuciyarsa bazata samu kwanciyar hankali ba dan haka ya soma neman layinta. shigowar maryama kenan tana yiwa umma sannu da gida inda umma Ke tako wa zuwa inda take tsaye tana tambayarta “yau kin dade a wajen aiki .muryarta a gajiye tace “wallahi wannna boss din namu ne sai ahankali nan ta shiga korowa umma abinda ya faru da yadda suka rabu dashi “ikon allah shi kuma haka nashi tsarin yake ?” “ke dai bari umma mutane na mugun shan wahala a hannunsa amman fa duk da wannan takurawar tasa wai haka suke son aiki akarkashinsa nifa ina ganin zan soma neman wani aikin dan bazan jura ba“Allah ya zaba miki abinda yafi zama alkhairi ko cigaba da aiki akarkashinsa ko samun wani aiki “amen umma “! maryama ta fad’a tana cire jakarta tana qoqarin ajiye jakarta kenan wayarta ta d’auki qara ta d’auka tana duba screan din wayar suann “sir ! ta gani wato sunan mr ATA ne yake yawo a screen din wayar tayi shiru tana jin kamr ta d’auka sai kuma tayi tunanin kar ta d’auaka dan batasan me kiran nashi zai haifar mata ba gara ta sharesa dan haka ta kashe wayar gabad’aya gaban ta na fad’awa ta shige d’akinta .”
Yayinda adaidai wannan lokacin mami na zaune agefen gadonta kusa da maryam tana cewa"haba maryam banason ina ganinki shiru , yawan tunani ko saka damuwa a zuciyarki shin zai miki maganin halin da kike ciki ne? "Jin haka yasa maryama fashe mata da kuka dan daman danne kukan take tana yinsa a cikin ranta “subhallah !”mami ta furta tana riko hannunta cikin nata “haba maryam daga magana meye kuma abun kuka ?”tunanin ne banaso bare ganinki cikin damuwa “akwai abinda aka miki ne kika dawo nan ke kad’ai ki baro yan’uwanki ?cikin muryar kuka maryam ta girgiza mata kai tana saka hanu ta rufe bakinta saboda wani kukan da yake kuma tahu mata suna cikin wannan halin sai ga nana hauwa’u ta shigo bayanta aunty khadija ce rungume da baby da sauri suka qaraso suna tambayar mami “lafiya mami me kuma faru maryam take kuka ? .”
“nan mami ta fad’a masu tsaki aunty khadija tayi sannan ta soma yi mata fada cikin zafin rai “ki zauna kashe kanki abanza ki cuci abinda zaki haifa dan wanda kike damuwa akanshi bai san kina yi ba wai shin dole ne da bazaki rabu dashi da tunaninsa ba ?”a’a khadija banaso haka dame kike son taji ?ke daya kamata ki rarrasheta ki kwantar mata da hankali tunda Kinsan ba'a son tana yawan shiga damuwa da tunani saboda cikin jikinta “.Allah mami maryam din ce da kayan haushi mutumin ko kallon inda take ba yayi bare ya duba situation din da take ciki amman ita kullum cikin damuwa take ,yanzu ki duba kiga kowa tsabgar gabansa yake cikin walwala amman ita ta dawo nan tana damun kanta da tunanin banza da wofi ta qarasa maganar tana jan tsaki sannan ta juya ta fice .”
nana hauwa’u zama tayi kusa daita suka saka maryam a tsakiyarsu .ita kam maryam kuka kawai take dan bata da abinda ya wuce kuka most especially idan ta tuna abubuwan da tayi duk akan adam amman babu abinda yayi tasiri akanshi da kyar suka samu tayi shiru ta share hawayenta tare da zabga tagumi still dai tunanin da basa son tayi shi ta sake lulawa ahankali mami ta dinga mata nasiha .” yayinda mr ata yake can bangarensa bai fito ba sai dai zuwa lokacin yayi wanka ya sauya kaya zuwa na shan iska .”wayarsa ya d’auko ya sake kiran number maryama sai dai amsa daya ake bashi wayar is switch off…..Oh my godness god wai me yake faruwa dani ne? komai ya zama worst a gareni? me ma yarinyar nan ta take nufi dani ?“anya kuwa yarinyar nan bazata haukata ni ba ? wannan shine tambayoyin da ya cigaba dayi a zuciyarsa yana jin zafi mai quna a ransa .”
Zaune yake shiru a parlour’nsa rike da waya layin maryama yake nema amman still a kashe ya duba agogon wayarsa karfe goma ta wuce tsaki yaja “may be tayi baccinta ya furta a fili yana rufe bakinsa aka turo kofar parlour’n aka shigo saurin waiwayowa mr ata yayi,ahankali kuma ya d’auke kanshi yana fesar da iska ganin yaya hisham ne ahankali yaya hisham ya dinga takowa har ya qaraso inda yake ya tsaya gaban Mr ata yana kallonsa kawai, rasa abun cewa yaya hisham yayi saboda yadda yaga fuskar mr ata alokacin tana cikin wani yanayi daya kasa fassarawa ko da ganin haka sai ya samu waje ya zauna ya zuba masa ido kamar yadda yayi masa, a hankali yaya hisham ya saki fuskarsa zuwa yanayin mur mushi, yace” ATA nazo maka da wani albishiri mai dadi mr ata yayi shiru yana kallonsa yana jiran yaji wani irin albishiri ne duk da baya tunanin akwai abinda zai wanke masa zuciya ahalin da yake ciki .”
“babynmu yaci sunan abbanku muhammed tariq ga mamakin yaya hisham murmushin ata ya fara daga yanayinsa sai daya bashi wasu mintuna sannan ya bud'e baki ya cigaba da magana ! Mr ata what this smile ?" wani sabon murmushin ya sake yi cike da tsananin farinciki mara misaltuwa cike da murya Ata Ya furta "ya Allah.! Amman gskiya naji dadin wannan alamarin allah kuma ya raya min ya kuma shirya ma mai sunan babana albarka “Ameen yaya hisham ya furta a fili fuskarsa cike da tsananin murna. yayi mamaki Kwarai da gaske domin bai dauka zai ji dadi har haka ba shikenan fad’a ya qare atsakaninsu a natse ata ya mike ya nufi hanyar fita waje fuskarsa dauke da murmushi yaya hisham ma ya biyosa kai tsaye dakin mami ya shiga anan ya iske mami da yaranta kaf har da maryam zaune .”
Kai tsaye gadon baby ya zarce ya tsaya shiru yana kallon baby kwance cikin showel haka zalika maryam shiru tayi tana kallonsa yana ta’ba qirjinsa yana murmushi kafin yaya hisham ya kai hannu ya d’auki babyn ya kai masa sumbata a goshi ya mika masa ya karbi baby ya nufo wajen mami ya zauna kusa daita “sweetheart!”ya kira sunanta “naam adamcy nah ran my prince ya dade yayi murmushi jin dadi har dimples dinsa ya lotsa “an dade baa min abinda ya faranta raina ba “haka ne kasan baby da shiga rai ai na lura tunda aka haifi yaron nan kake son shi kai ma allah ya baka naka masu albarka shafa fuskar babyn ya cigaba dayi yana murmushi “babana ,my prince ,my averything cikin murmushi ya kalli mami “sunan babana hisham yasa bansan yadda zan misalta farincikina ba.”
nan take fuskar nana hauwa’u data sauran yanuwata ta bayyana tsantsar farinciki daman burinta kenan sunan babanta amman duba ga shi kad’ai iyayensa suka haifa yasa tayi tunanin sunan abbansa zai sa allah sarki ashe ita zai wa suprise
ta kalli yaya hisham tana masa kallo mai dauke da murna da godiya“maryam kuwa ji tayi jikinta yayi mugu mugun sanyi sai taji inama ace nmj zata haifa ba mace ba kai wannnan mutumin ko me zata haifar masa bazai nuna farincikinsa haka ba “ta fad’a a kasan rabata “hisham ya tsallake sunan kowa a dangi yasa na babana bansan yadda zan kwatata murnata ba yau “. hankalin mami gabadaya ta maido kan ata dake zaune rike da baby “lallai wannan abu yayi kyau Allah yayiwa rayuwar ishaq albarka koni naji dadi sosai kuma nasan hajiya zulfa’u ma zataji dadin wannna alamarin kai kowa ma nasan zai ji dadi yaya hisham ya mike ya fita yana dariya byn Kmr second biyar nana hauwa’u ta kwashe kayan baby daaka kawo wa mami tabiyo mijinta d’akin da take jego suka shiga tare ta nufi wordrobe din baby ta bude ta soma qoqarin ajiye kaya .”
Ahankali ya tako zuwa inda take ji tayi kawai ya hadeta da jikinsa ta baya ta juyo a tsorace suka hada ido fuskarsa a sake “meye na wani tsorata bayan kinsan mu kadai ne a dakin “ ?a ganinka bai dace naji tsoro ba?ya daga mata girasa daya lumshe masa idanunta tayi tace “yau ne fa na cika kwana shida da haihuwa “matsota ya sake yi sosai ya hadeta jikinsa “an só !? sai akace kar naji dumin jikin matata ?numfashi ta sauke alokacin da taji ya zame hular kanta ya fara shafa sabon kitson daaka mata kamar wata sokuwa haka ta dawo yayi kamar zai warware mata zani tayi saurin rikewa tana kallonsa ganin yadda ta tsorata ya saki murmushi yana cewa “malama babu abinda zan miki wani naunayen ajiyar zuciya ta sauke “nayi missing dumin jikinki da lip’s dinki bari na rungumeki na rage zafi yana gama fad’ar hk ya hadeta da jikinsa ya kai hannusa ya taro byn kanta ya hade bakinsu waje daya .”
***
Da misalin karfe shad’aya na daren ranar bayan maryamta taga ma komai nata ta dawo parlour’n ta zauna akan kujera hannuta rike da littafin zane tana aikin mr ata duk da tace bazataje aiki gobe ba saboda wulakancisa amman zatayi iyakar qoqarinta taga ta zana masa abinda yake so sai ta mikawa yusura gobe da sassafe ta mika masa ta jima tana zane sai dai bata gama ba acikin biyar uku kawai ta samu damar yi masa a qarshe ta tattara taje ta kwanta washegari karfe bakwai a gidan su yusura tayi mata alokacin yusura na qoqarin futa zuwa aiki bayan maryama sun gaisa da iyayen yusura ta maida hankalinta kanta “ya naga kin biyo ta nan kuma cikin wata irin shiga “?bazani aiki bane yau nazo ne na kawo miki wadan nan zane ki kaiwa mr ata “what ?haba maryama so kike ya tasheni aiki kawai kije ki shirya ki kai masa da kanki ?ai ban gama bane shiyasa nake jin tsoron zuwa ,shine ni zaki tura ni dai gsky Kiyi hakuri gara kije da kanki “yanzu dai bazaki kai masa ba?” gsky ba wai bazan kai masa bane tsoro nake ji maryama ta dauki lokaci tana fama da yusura as ending dai da kyar ta karba da zumar zata bawa madam some sukai sallama
Taron suna akayi a gidan mami mai cike da tsantsar farinciki dan tsabar murna ma mr ata bai je koina ba yayinda duk wanda ya kalli fuskarsa zai san yana cikin farinciki da annashuwa sannan duk wanda yaji sunan da baby yaci sai yayi murna tare da yiwa marigayi alhaji ishaq addua kowa ka kalli fuskarsa farinciki yake banda maryam da gabad’aya tayi wani iri kallo daya zaka mata kasan akwai damuwa atattare da ita duk da mami tana cikin hidima amman hankalinta na kan maryam bini bini zata nemota taga yanayinta ,baby ishaq wanda aka masa lakabi da ashraf ya samu kyaututtuka ta bangaren dabam dabam ta bangaren yan’uwa da kaninsa da kuma bangaren qawayen hajiya zulfa’u dana mami ata ma kyauta yayi masa ta mussaman inda ya bashi takardun gidajensa biyu dake acikin runin gidajensa dake banana estate .”
Zaune maryam take akan kujera a parlour’n umma ta rungume pillow hannuta rike da littafi wanda ya kasance english novel ne tana karantawa domin so take ta cire damuwar mr ata aranta dan tun safe take cikin tashin hankali da fargaba shiyasa ma ta kasa qarasa masa aikinsa dan batasan wainar daake toyawa ba jira take biyar tayi ta kira layin yusura taji ko ta bawa madam some .”knowking din kofa taji ta ajiye littafin hannunta akan kujera da pillow ta mike ta garasa bakin kofa ta bude wata kyakkyawar budurwa ta gani tsaye abakin kofar lokaci daya taji wani mummunar faduwar gaba from know where ya diram mata “ko zan iya shigowa ? budurwar ta tambaya “sunana anifa friend din sadam ko nace tare mukayi karatu dashi haka ma wurin aikinmu daya dashi bana nan nayi tafiya na dawo naji abinda ya samesa”jin haka yasa maryama ta qara sakin fuska sosai tace sannu da zuwa ki shigo daga ciki budurwar ta shigo ta tsaya tana qarewa falon kallo” ya kika tsaya ki zauna mana babu mutsu ta samu waje ta zauna tana cigaba da qarewa falon kallo .”
“Kece matar daya aura “?maryama ta gyda mata kai alamun “eh!allah sarki wai ya wannan alamarin ya kasance ance anemi sadam an rasa amman kuma ke kina raye ?kuma kin cigaba da rayuwa batare da kin cigaba da nemansa ba ko yana raye ko ya mutu?” ya zakice hk ?kin kuwa san irin nemanshi da mukayi ?” munyi iya qaqarinmu ni alokacin bana cikin haiyacina ni dai nasan an binnesa da ransa daga nan kuma bansan komai daya faru ba “okay budurwa ta gyada kanta tana cewa “allah bayyana shi idan yana raye idan kuma ya mutu allah ya jikinsa dan sadam mutumin kirki ne kowa nashi ne sam bashi da matsala banji dadin abinda ya faru dashi ba allah dai yayi masa rahma.”ameen !maryama ta fad’a .”muryarta cike da runi.”
“Amman dai ya kamata kiyi aure zuwa yanzu tunda baya raye .”maryama tayi shiru tana dubanta hakan yasa budurwar tace “am really sorry shawara ce na baki dan naga ke yarinya ce bai dace kice zaki tsaya batawa kanki lokaci ba saboda rayuwa babu tabbas ko yana raye bare baasan a hali da yake ciki ba a mace ne ko a raye “haka ne banji zafin mgnrki ba amman dai na barwa allah komai .”gsky ne kinyi rashin miji mai hakuri da son mutane kai baqarmin sabo mukai dashi ba alokacin muna karatu koda yaushe muna tare har ma mutane suka fara tunanin ko akwai soyayya a tsakaninmu .”
Maryama tayi murmushi kana tace “Amman kuma bai ta’ba bani labari ki ba ?duk wasu abokan karatusa nasani ,haka dayawa abokan aikinsa nasani kece dai gsky ko sunanki ban ta’ba ji ba sai yau shiru budurwar tayi sannan maryama ta cigaba “bari na kira mahaifiyarmu idan zata dawo yanzu ku hadu watakilla ya taba bata labarinki ?” Oh ! bata nan ne ?eh ta dan fita amman bazata jima ba zata dawo zan so naganta dan hasalima akwai abinda ya kawoni saboda akwai aikin project din da muka fara dashi kafin nayi tafiya in fact maryam document din gabadaya suna hannunsa inda zan samu document din gaskiya da zanji dadi sai na qarasa komai idan aka biyani sai nã kawo masa nashi kason tunda tare muka fara .”
“Okay wannan ba matsala bane wani suna ne ajiki sai naje dakinsa na duba miki uhm zakiga sunana da sunanshi maryama ta mike itama budurwar ta mike da sauri “ammm ko zan iya biyoki dan ba lallai ki gane document din ba maryam ta tsaya jim tana mata kallon mamaki kafin tace “tunda akwai suna ai komai zai zo da sauki amman dai muje tayi mata alamar ta biyota da hannunta “maryama tana gaba budurwar data kira kanta da anifa ta biyota basu tsaya akoina ba sai a bakin kofarsa .”
Tsayawa tayi cak qirjinta na bugawa a hankali ta tura kofar dakin ta sanya kafarta daya tana mai jin faduwar gaba tunda aka nemesa aka rasa bata qara shigowa dakin ba ta shigo sosai haka ma anifa abubuwa dayawa sun dawo mata yadda a farko kamar bazai karbi soyayyarta ba daga baya ta juye soyayyar gaskiyar daya dawo yana mata sadaukar wa da yayi a gareta aranar daurin aurensu murmushinsa tabbas matar tayi gsky shi din mutumin kirki ne .”a hankali ta sauke naunayen ajiyar zuciya tana kallon koina a dakin komai nashi yana nan kamar lokacin da yake nan dakin babu dotti da alamun umma na kula da dakin sosai .”
Ahankali suka fara duba wuraren da takardu suke sai dai duk document din da maryama ta nuna mata sai anifa tace bashi bane can ta kalleta “ammmm ko akwai key din wordrobe dinsa a hannunki ?maryama daukowa tayi ta mika mata tare suka bude wani jaka suka gani dan haka suka fito dashi tare suka bude suka fito da takardun ciki gbdy sai dai basu gani ba tarasa yadda zatai can tayi wani tunani dan haka ta kalli maryama “ko zan iya samun ruwa ?ta dafe kanta maryama tayi tana cewa “sorry wallahi na manta ban baki ruwa ba akawo miki juice ko ruwan Kika fi bukata ?kawo min ruwan ma ya isa ok bari naje na kawo miki ta mike ta fita wanda hakan ya bawa budurwa damar kira a waya .”
byn an dauka ta soma magan kasa kasa “na fa duba inda kace amman banga komai ba sai wasu takardun dabam can bangaren data kira akace “ki dai duba da kyau zaki gani anan suke ,wa kika samu a gidan?”
“ wannna sakariyar yarinyar , okay shinkenan naji na daina ta fad’a tana ajiye wayar akan gado ta cigaba da dubawa har tagani naunayen ajiyar zuciya ta sauke da karfi ta dauki abinda ya kawota tana mgnr a fili “ya allah na gode maka da baka bari na sha wahala ba “kin gani ne taji sautin murayar ta cikin waya ?eh ! nagani bari nayi masa kyaywan ajiya ajikina kafin ta dawo ta daga rigarta daman akwai bodyhug data saka domin aiwatar da shirita ta nade takardun ta saka acikin rigarta ta maida rigarta ta sauke da sauri sannan ta cigaba dadduba sauran takardun zuwa sanda maryama ta dawo dakin tana qaqarin mika mata cup din ruwa taji sautin magana “me kik jira ne ?ga ruwa taji muryar maryama a gigice ta dago da sauri ta mike tana duban wayarta da mgn ta fito “kina jina Kiyi sauri mana ina kiranki please “budurwa tayi sauri ta dauki wayar tana rage volume ta gefe “wannan muryar fa ? Maryama ta furta a matukar rikice .”
Mmn sudais
[8/31, 11:25 AM] Safwan Libiya 2: 💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
BOOK 3
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 11
"Ke babu ruwana da wani aiki da kike son Kiyi dashi ku biyoni kawai har ya juya da sauri maryama tace "excuse me sir ! ya juyo ya tsaya a natse yana dubanta "sir ka za’beni ka bar sultana da surayya tunda su suna bukatar aiki dashi ya juyo qare mata kallon tsam yana murmushin mugunta “ai shi baya son wad’an da basa son zama tare da ATA yafi qaunar masu bukatar kasancewa akarkashina fuskarsa a sake yace "bana bukatarki ki barni da wad’an da na za’ba ya fad'a yana sake juyawa lokacin tuni su surayya sunyi hanyar waje .”ta sake qoqarin bud’e bakinta zatayi magana da sauri tayi shiru sakamakon yatsun qafarta da taji mr ata ya take da takalmin kafarsa yana jifanta da wani mugun kallo mai d’auke da gargadi lumshe idanun tayi cikin jin rad’ad’in azaba .”
kallonta mr ata ya cigaba dayi ransa nayi masa quna muryarsa a tsarke yace "wato kin so ya zabeki ba ?ya fad’a yana zabga mata wata katuwar harara tayi shiru tana jin tamkar yana zarar ranta ne dan har lokacin bai dauke qafarsa ba dan mugunta irin tashi ganin idan batayi wani abu ba zai sabauta mata yatsu yasa ta soma kokarin mgn yayi saurin dakatar daita "ki min shiru ana karki ‘bata min lokaci kiyi qoqari ki gama aikin dana baki nonsense girl kawai.”ya qarasa fad’a yana fesar da iska mai zafi daga bakinsa yayinda zuciyarsa ta dinga bugawa da qarfi Ahankali ya dinga saisaita numfashinsa da yayi barazanar daukewa sakamakon wasa da rayuwarsa da maryama taso yi ,shi kad’ai yasa bala’i da zai faru da sultan ya zabita dan dai yasan muddin ya zabeta bazai janye qudirinsa ba shi kuma bazai bar masa ita ba .”
yafi mintuna ashiru yana fama da zuciyarsa batare da yace qala ba yayinda duk wani ma’aikaci dake tsaye a wajen, shi yake kallo fuska cike da tsananin mamaki ”some ya d’auke kwayar idanunshi akan maryama ya maida kanta byn ya kira sunanta "yes sir! ta amsa cike da girmamawa .”ya juya cikin hanzari sectary ta biyosa da sauri maryama kam dukawa tayi tana duba yatsunta ko basu samu matsala ba yayinda sauran ma’aikatan da sultan bai za’besu ba suka shiga murna suna godewa allah domin kuwa aiki akarkashin mr ATA akwai samu ba iya albashi bane kawai duk sati akwai kyauta ta musamman da yakewa ma'aikatansa ."
“Maryama tayi kasa da muryarta sosai tace “na kasa fahimtar me yasa suke bukatar kasancewa da wannan mugun mutumin wallahi ni dai naso sultan ya za’beni na huta da takuramin da yawon kallon da yake min “ maryama ta fad’a tana kallon fuskar yusura dake tsaye kusa daita itama yusura cikin yin kasa da murya tace “ke yanzu da sultan ya zabeki sai kiyi aiki dashi ?sosai kuwa zai fiyye min kwanciyar hankali akan aiki da wannan mugun mutumin “ke ki godewa allah wallahi dama kika fahimci yana kallonki mata nawa ke son ya kallesu bai yi ba ?”wannan matsalarsu ce ni dai wallahi banason wannan kallon yusura tayi murmushi tace ta kai bakinta daidai kunnen maryama “kodai oga ata ya kwasa ne ?tsaki maryama taja tana janye kunnenta bata sake yunkurin cewa komai ba .duk ma’aikatan suka watse suka barta ita kad’ai acikin office tana aiki tana zance zuci sosai tayi ta qoqarin taga ta kammala da aikin daya bata har kusan karfe hud’u bata gama ba wanda zuwa lokacin ma'aikata sun fara watsewa daydaykun mutane ne ke kai kawo ita kuwa tana nan ta dukufa gurin qarasa masa aikinsa ."
a matukar gajiya ta d’ago daga abinda take tare da yin shiru tasa pencil a bakinta tana cizawa fuskata da alamun gajiya “ina ma wannan mutumin zai min uzuri dana wuce gida na qarasa masa a gida tunda baa gobe zaa kar’bi aikin ba dan wallahi na gaji dayawa “.ta fad'a tana lumshe idanunta. bayan Kmr minti biyar ta mike da sauri hannu rike da farar takarda tana tafiya tana duba aikinta ta nufi office din mr ATA har a lokacin yana tare da sectary dinsa suna tautaunawa kai tsaye ta shigo batare da neman izini ba ta soma mgn "sir! "bata kai qa fad’ar abinda ya shigo daita ba taji sautin muryarsa a tsawac"out !tsaye tayi sororo tana dubansa cike da mamaki da jin haushi disgin da yayi mata gabadaya jikinta yayi mugu mugun sanyi ya waigo inda take tsaye rike da farar takarda gbdy ta kasa kwakwaran motsi a waje .”
"nace out dan kin wani tsaya da wad’an banzayen idanun naki kina kallon mutane .”ya fad'a a tsawace bata san sanda ta juya a fusace ba har ta kusan kai bakin glass door din ta sake jin sautin muryarsa " ki koma bakin kofa Kiyi knowking idan an baki izini sai ki shigo “oya leave."wani irin kunya taji ya kamata ta juya tana sauke numfashi da ajiyar zuciya tunda take arayuwarta bata ta’ba jin kunya irin na ranar ba ,har ta kai bakin kofa ta d’an juya baya har lokacin idanunshi na kanta ya hura mata hanci yana watsa mata wani mugun kallo ta sake juyawa a ta bud’e kofar da karfi ta fita .”shi kuma ya koma ya zauna akan kujera ya d’aura kafarsa d’aya akan d’aya yana jujjuyawa bayan kamar second goma tayi knowking tare da cewa “may i coming sir ?”yace yes "coming !
Ta shigo fuskata a had’e tamkar bata ta'ba yin dariya ba idanun ta tsura masa tana mai jin ciwon abinda yayi mata bai kalli inda take tsaye ta hard’e hannuwanta duka a qirji ba bare yaga irin kallon da take masa ,ya mikawa sectary dinsa hannu ta mika masa system dinsa dake rike a hannunta, sosai idanunshi ke Kan system.” maryama ta soma magana daga inda take tsaye "please have a set ya fad'a yana nuna mata wurin zama "ya sake disgata.”
"Inna lillahi ta furta acikin ranta wannan wani irin mutun ne ?gabadaya yanayinta ya sauya ga tsananin gajiya ga yunwa ga tashin hankalinsa ta qaraso ta zauna akan kujerar dake fuskantarshi "sir ban gama qarasa aikin daka bani ba amman ina ganin ..."
“some ! taji ya katseta ta hanyar fad’i haka sectary ta amsa da"yes sir! shiru maryama tayi tana dubansa cike da zallar bakinciki, zuciyarta banda tuttukin bakinciki babu abinda take Tana jin kamar ta mike ta tashi ta bar office din dama ma’aikatar gabadaya bai kulata ba ya cigaba da bawa madam some umarni kallonsu kawai take shi da sectary dinsa fuskarta babu walwala har sanda sectary dinsa ta mika masa wani file ya tsurawa file din ido batare da ya kalleta ba ."yayinda zuwa wannan lokacin zuciyar maryama ta cika da mugun tsoro dan batasan me yake nufi daita ba .”
ahankali taga ya girgiza kai sannan ya kalleta sai dai murmushin mugunta ne kwance akan fuskarsa "ina jinki !?ta mika masa takardar hannunta ya kalla sosai ya kwa’be baki tare da cewa "bai min ba ."bai maka ba ?ya d’age mata girarsa d’aya alamun Eh!me kake nufi sir ?” abinda nake nufi ai kinji baya bukatar na sake maimaitawa tayi shiru tana dubansa qirjinta na dukan tara tara “maryama ! ya kira sunanta cikin wani irin yanayi wanda yasa tsigar jikinta suka mike "yana da kyau ki canza wani kuma a yanzu ya fad'a yana d’auke kansa.” muryarta na rawa tace "okay sir amman me zai hana na tafi gida zuwa gobe sai na qarasa "no! A yau nake bukata leave” ya d’aga mata hannu alamun ya sallameta babu shiri ta fita tun kafin ya sake yanka mata wani sabon wulakanci.”
Bayan fitarta "sectary tace "sir amman gabadaya aikin maryama sunyi kyau "na sani! nasan sunyi kyau but ina bukatar wanda yafi wanda tayi ,”gsky tana da bambamci da sauran masu zane kawai dai tana da matsala ne yana magana yana daddana keyboard zanenta yayi sosai in fact ma ban ta'ba ganin zane mai kyawun nata ba” ya qarasa mgnr yana lumshe ido so yake ya azabtar daita akan kasadar data so masa, yanzu da sultan ya za’beta fa ?ya sake tmbyar kansa yana jin fad’uwar gaba "da komai zai faru sai na dawo daita karkashina ya bawa kansa amsa ."
Tattara kayanta tayi ta dawo office din sectary dan ta gaji da shige da fice ,ta sakê dukufa akan aikita ta bud’e wani takarda ta ajiye tana dubawa ta cigaba da zanen ,tayi zane taga baiyi ba ta dunkule ta yar da takardar ta sake bud’e wani shima haka ta d’aura pencil a bakinta lokacin sultana ta shigo ta wuceta ta shiga office din mr ata "haba yaya me yasa zaka min hk bayan kasan saboda kai na zabi aiki akar kashinka"me zanyi ai yayanki ne shima kuje can ku qarata dan ni ban d’aukeki a matsayin mai aiki ba saboda you're totally nonsense ,duk maganganun da suke maryama tana iya jiyowa sai dai ko d’ago kanta batayi ba .”
waya ya d’aga yayi maganr second goma sannan ya ajiye ya tashi yana tafiya ahankali ya fito har yayi taku biyu kafarsa taci karo da daya daga cikin takardun da marayama ta yar anatse ya kai idanunshi kafin daga baya ya dan ja wondonsa kad’an ya duka tare da dauka ya mike had’e bud’ewa a hankali yana dubawa taga tsayuwarsa amman ko kallonsa batayi ba, ta cigaba da abinda take dan tunaninta ba’a wurinsa yake ba tunanin yadda zata masa abinda yake bukata ta kama gabanta take ."
Ya cigaba da kallo mace ta fara zanawa sanye da kayan weeding ajikinta a hankali ta d’ago tana kallonsa tsaye ya d’aura hannusa d’aya akan kujera ,d’ayan kuma yana rike da takardan ahanakali ta mike tsaye a daidai lokacin ya kalleta cikin sa’a idanunsu ya tsarke ckin juna saurin dauke idanunta tai ta maida Kan aikinta tana tunanin tare da sa pencil abakinta shi kuwa tundaya daura idanunshi akanta bai dauke ba sai daya kai minti talatin "sir sir!! ammm "Nace kice wani abu ne ?shiru tayi kawai tana kallonsa ya maida idanushi kan zanen da take yanzu wani yanayi suka tsinci kansu “set! ta kasa zama Kmr yadda ya bukata ya mika mata hannu alamun ta bashi pencil din hannunta ,babu mutsu ta goge kan pencil din saboda ta sakashi cikin bakinta ta mika masa ya kar’ba ya d’aura akan zenen da take ."
"Me kike qoqarin zanawa anan ?”Abinda ka bukata ne sir “ta bashi amsa anatse cike da kwarewa ya shiga gyara mata yana mata bayanin yadda zatai sun d’auki lokaci yana mata bayani sultan yazo ya wuce kasancewar koina a wurin glass ne duk yadda zaka wuce zaka ga mutun kawai idanunshi ya sauka akansu ya tsaya yana qare masu kallo batare da sun sani ba amamn yaso ace yasan me suke tautaunawa akai sai dai babu damar hakan dan hk ya wuce ya kama gabansa ."
Mr ATA yayi mata gyara sosai kinga yadda zakiyi amman kin tsaya salo da son nuna iyawa alhalin duk nonsense kike zanawa.” yana gama fad’ar haka ya ajiye pencil din hannunsa duk da ya zageta amman fuskarta cike take da farinciki ,tace "kai gaskiya yayi kyau sosai ,ya kad’a kai ai kinga yadda ake yi amman kin damu mutane kin iya zane yanzu kin fahimci ba iya kwarewarki yasa aka nemoki kiyi aiki anan ba ?”ta gyad’a masa kai alamun “”eh!har ya juya ta kirasa "sir! ya juyo yana kallonta a tsanake yana jin wani iri akanta abinda yake ji akanta na dabam ne ,abu ne da bai ta'ba jinsa akan kowace mace ba. abun ne mai tsaya wa arai .”
“Ko zan iya cewa wani abu ? karki ce komai dan bana son jin komai ki zauan ki cigaba da aiki kawai kai ta gyd’a masa shi kuma yasa kai ya wuce ."ta sake zama ta cigaba da aiki bayan kamar second goma ya shigo hannunsa rike da cup biyu d’auke da coffee ya ajiye mata cup d’aya mai d’auke da sunan kamfaninsu sannna ya kalli aikinta ta kallesa “sir dan allah ka bari na tafi gida lokaci ya soma ja hankalin iyayena zai tashi “babu inda zaki sai kin gama min aikina ya sake juyawa rike da nashi cup din yana kur’ba ahankali .”
Sosai tayi concentrate akan aikinta ta sake zaro wata takarda ta cigaba a natse ya fito daga office dinsa zai fita idanunshi ya sauka akanta diret inda take ya nufa ya tsaya yana kallonta yana tsaye sectary dinsa ta qaraso ta tsaya tana cewa” sir ina bukatar ka saka hannunka anan ya cire hannunsa d’aya cikin aljihunsa ya amshi biron hannunta ya saka hannu yana saka hannu amman hankalinsa da idanunshi yana kan maryama ita kanta sectary tana lura dashi tana mamakin yadda ya damu da yarinyar da yadda yake yawon kallonta byn duk ba haka yakewa sauran yammatan dake aiki akarkashin ba ."
Bayan ya gama ta wuce shi kuma ya qarasa kusa da maryama yayi daf daita sosai ,hannunsa d’aya cikin ajihun wondonsa yana duban aikin da take ,jin tsayuwar mutun yasa ta d’ago idanunsu suka tsarke cikin juna suka dinga kallon juna har basa son ko kifta idanunsu da kyar ya iya d’auke idanunshi ya kalli zanen da take "har yanzu kina Kan aikin nan ?"eh ina kai sir kokari nake na qarasa na wuce na tafi gida “yayi shiru yana tunani dan baya son ta wuce abu biyu ne aransa yana son hukuntata ta hanyar ‘bata mata lokaci haka kuma baya son tayi nisa dashi dan yana son akoda yaushe tana kusa dashi yana matukar son ya bayyana mata sirrin dake ranshi amman ya fuskanci yarinyar tana da matukar zafin kai da tsautsauran raayi tare da rainin hankali ,ba lallai lokaci daya ya samu had’in kanta ba ."
Ya kalli zanen sannan ya d’auki pencil yana sake mata bayanin yadda zatai daga can bayansu kuwa sultana ce tsaye tana dubansu ashe bata wuce gida ba idan fa tayi sakaci wannan yarinyar zata yi galaba akan ya Adam zata iya mallake zuciyarsa dan taga gbdy ya maida hankalinsa kanta abinda bata ‘bata gani ba kenan sauraran wata yarinya ko kula da ayyukan ma'aikatan dake kula da kamfanin yayinda a bayan sultana sultan ne ya tsaya yana sauke numfashi "kiyi hattara wannan yarinyar ta kware sosai akan aikinta irinsu ATA yake bukata dan tasan aikinta ni nayi danasani da ban d’auketa ba idan kikayi sake zakiyi loosing opportunities dinki na zuwanki wannan kamfanin domin ki siye zuciyarsa ,ya kamata kiyi duk abinda zakiyi wannan yarinyar ta bar kamfaninan .”
ranta a matukar ‘bace ta juyo tana kallonsa “ kai me yasa bakawa mutun fatan alkhairi sai na tsiya addua ya kamata ka min saboda kasan yadda nake son ya Adam arayuwata bai kamata ka fad'a min hk ba ,ba wai bai kamata ba kawai Kiyi abinda ya dace ba sha shanci ba yana gama fad’ar hk ya juya ya koma office dinsa itama ta juya ."
Mr ATA ya ajiye pecil din hannunsa sannan ya juya ya wuce har yayi taku biyu tace"sir ko zan iya wucewa gida yanzu saboda lokaci ya tafi sosai tayi mgnr tana duba agogon hannunta ya kalleta a natse yace " bake ba barin wurin nan sai kin qarasa aikin nan domin ina bukatarsa karfe bakwai daidai zaa zo akar’ba yana gama fadar haka ya juya ta koma ta zauna hankalinta a matukar tashe tare da saka pencil acikin bakinta can dai taga bata da wani mafutar da ya wuce ta cigaba da aikinta fitsari ta soma ji sosai marayama ta mike tsaye sakamakon marata dake kokarin kulewa ta nufi bayi tana shiga sultana ta qaraso taga yanayin zanenta yayi kyau sosai zane ne da zai d’auki hankali mutun hakan yasa haushi ya kamata lallai sultan yayi gsky idan batayi hattara ba wannna yarinyar zata gama da zuciyar ya Adam dan haka ta d’auki cup din coffe din da mr ATA ya ajiyewa maryama ta juye gbdy akan zanen ta bar wajen da sauri ta koma gefe ta tsaya tana jiran taga me zai faru ."
maryama na dawowa ta iske tashin hankali nan take ta gigice ta dinga kallon zanen tana kuka ta d’auki d’aya daga ciki takardan wani ma har ya fara yagewa tana kallo "waye yayi min hk ?garin yaya haka ta kasance ?cikin haka mr ATA ya shigo sakamakon jin sautin kukanta idanunshi ya sauka akan zanen "what !?ya furta da karfi me ye haka zan gani Ke fa nake jira dan by this time ya kamata ace ina gida "?nima haka na gani na shiga toilet nayi fitsari na dawo na gansu haka "you're very stupid” ya fad'a a zafafe yana duba zanen sultana dake gefe babu abinda take sai murmushin jin dadi tayi Kmr bata gansu ba "amman dai ke anyi dakikiyar yarinya wani irin iskanci ne hk ?garin yaya ma haka ta faru ?”
“Wallahi sir ban san yaakayi ba ni me yasa ma ka kawo coffe tunda ai bance maka zan sha ba ."?ta fad’a cikin muryar kuka ."Okay dan na kawo miki coffe shine ya zama laifi ?“yes dan bana shan coffe bashi da kyau kai ma ka daina sha yana da illa shiyasa ni bana sha "okay zaki gane baki da wayo dan babu inda zaki yau sai kingama min aikina” ya fad'a tsawace tare da juyawa. tabi shi da kallo hawaye na zubo mata bata jin zata iya dan bata san ta inda zata fara ba dan haka ta tattara takurduta ta zuba acikin jakarta ta nufi office dinsa tayi knowking ya bata izini ta shiga yana zaune sectary dinsa na gefensa itama ta gaji sosai amman babu yadda zatai yi tunda mai gidanta bai wuce ba bata da damar wucewa "karki soma kawo min wani uzuri ko bani hakuri ."ya fad’a amatukar fusace .”
"No sir babu daya daga ciki da zanyi nazo na fad’a maka ina son zan wuce gida ya juyo ya kalleta a kaikaice “ na fad'a miki babu inda zaki har sai kingama aikin da na baki a matukar fusace ta soma magan “sir karka manta ni macece ka duba lokaci yanzu ka gani ta kalli agogon hannunta ,gsky ni dare yayi ban saba kai wa dare a waje ba ,yanzu ma nasan hnakalin iyayena na can a tashe ni dai gsky zan wuce ko babu izininka “tana gama fadar hk ta juya da sauri sectary ta shiga kiran sunanta maryama !maryama!! amman ina ko juyowa batayi ba ta cigaba da tafiya.”shiru yayi yana tunani gbdy kwakwa luwarsa ta toshe ya rasa me yake son yayi, shima babu shiri ya mike yayi waje da sauri sectary some ta daga hannunta sama tana cewa "thank you maryama ta fad'a tana tattara kayansa ta fito da sauri ta biyo bayansa .”
Babu yawa ayi hakuri dashi 😭🙏🙏
Mmn sudai[8/31, 11:25 AM] Safwan Libiya 2: 💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
BOOK 3
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.