Hamdah Littafi Na 2 Complete Hausa Novel
Reading file: HAMDAH part 2 complete.txt
Chapter 16 of 35
Mommyn twins ce
Ranan Azaune mama ta kwana rike kuma da yaran idan É—aya yayi motsi sai ta aje na hannunta taÉ—au ki É—ayan,
duk san da na farka sai na ganta zaune tausayin ta yakama ni,
na tabbata tun da rana dana fara labour batasa komai a bakinta ba har kuma yanzu, domin gabakinta abushe,
haka tayi-tayi dayaran har gari yawaye.
washegari da safe
Zainabu suka zo da ita da wata makociyar Mama,sukazo mana da abun karyawa niki-niki.
suna rike da yaran a hannunsu kowa sai sanbar ka yake,
Zaunabu data kurawa Æ´a macen ido tace
"Oh ikon Allah jibi waÉ—an nan yara wazai gansu yace tagwaye yara katin-katin dasu kamar haihuwar É—aya,
kai sannu HAMDAH gaskiya kinyi kokari waÉ—an nan kam ai sai dai CS É—in".
murmushi matar da sukazo da ita tayi tace
"Wlh kam yara tabar kallah ga wayo ni dai tun zuwan mu idanun su abuÉ—e suke".
Mama tayi dariya tana faÉ—in
"WaÉ—an nan awaye kazan birni ai tun jiya idanunsu a buÉ—e yake suna jin motsi zasu juya ido gun kamar masu jin magana,
kunga wannan bakyauyiyar kawar tawa idanunta a kan fanka, shi ko angon ido yakurawa kwan wuta".
dariya duk suka saka ai kuwa sai yaran suka shiga raba ido kamar sun san me ake faÉ—a,
Zainabu tace
"Ai kuwa yaran akwai wayo ga yan da suke kokarin juya kai suna jin magana"...
Haka suka yi ta kallon yaran cikin ban sha'awa.
nan mukata hira dasu sai kusan azahar sukatafi.
mama ta rakasu tadawo tana dawowa daga rakiyarsu nadubeta cikin yanayin gajiya da kwanciyar da tun jiya ban motsa daga in da aka kwantar da ni ba,
nace
"Mama dan Allah ki dagani nikam nagaji kokuma injuya gefe".
Mama tace
"Sunce bayanzu ba". dasaura nace
"To Mama kishin ruwa nakeji dan Allah kibani ruwa nasha".
dubana take cikin tausayawa da tsigar rarrashi tace
"Kiyi hakuri HAMDAH su sun fimu sanin dalilin da yasa suka ce kada a baki komai tun da ai kin sune ki kara hakuri dan Allah kibari likitocin suzo tukun".
kai kawai najuya cikin gajiya da kwanciyar guri daya gamugun ƙishin ruwan da nakeji...
karfe
huÉ—u na yamma har lokacin ina nan kwance duk yadda naso Mama ta É—agani ko taban ruwa nasha fir taki.
kuka nasaka mata ina faÉ—in
"Ni dai nagaji nagaji ƙishin ruwa nake ji".
Ido Mama ta zuba min tana jijjiga baby boy É—in dake ta zandara ihu tun É—azu,ta bashi ruwa yafi a kirga da zaran ta cire fida a bakin sa sai ya sa kuka.
Ana cikin haka sai ga É—aya daga cikin
Doctors É—in da sukayi min CS yashigo,
yace
"Mama mai kikayi wa pationt din mu ne haka take kuka".
yafaÉ—a da murmushi yana karaso wa bakin gadon da nake,
Mama tace
"Wallahi tuntini wai so take a ɗaga ta tagaji kuma wai kishin ruwa take ji shine nace tayi haƙuri sai kunzo".
murmushi Dr yakuma cikin kwarewa da iya tafiyar da mara lafiya ya dube ni yace
"Idan zaki iya tashi to tashi".
nayi yunƙurin tashi naji Nakasa sai ji nayi kamar cikina yana buɗewa in da aka min CS ɗin,
ido na matse sai ga hawaye sharr.
Ido yaÉ—an kura min kana yace
"Sorry bari nurse's suzo su tai maka miki".
yafita ba jimawa nurse suka shigo suka É—agani suka goge min jiki suka kimtsa ni,
kana suka cewa mama takawo ruwan zafi kadan a kofi akabani nasha,
sannan sukace na gwada kwanciya da kai na in zan iya,nan ma na kasa,su suka mai dani
suka kwantar dani. sukace wa mama taringa haÉ—a min milo inasha duk bayan awa daya domin zai taimaka
min yakawo min ƙarfi ajikina.
tace to insha'allahu nan suka fita...
Da daddare nurse's É—in suka kuma zuwa,
yanzu kam cewa sukayi na tashi da kai na daƙyar na iya mikewa zaune, bayan sun gama gyara min jikina sukace na kwanta da gefe in zan iya shima nakwanta,
Washegari ma da kaina na tashi nurse's suka gama ai kin su suka fita,
Mama tasa min pillow a baya na na jingina dashi,
bayan nagama shan tea mai zallar milo da Mama ta haÉ—a min,
tadube Ni tana faÉ—in
"To tun da kin koshi kibashi nono yanzu kam kin ga dai tun jiya kuka yake,
ga Æ´ar'uwar sa ma yau ta tashi da kukan, yunwa duk suke ji".
Baki na tura dan tun jiya take ta bina nabashi nono toma ni ta'ina ma zan fara,
miko shi tayi taÉ—aura shi kan cinya ta sai dai bata sake shiba tana rike dashi ta É—an gyara shi ta inda bazai fama min ciwo ba,
tace
"To É—an gyara sai ki bashi"...
yana kama nonon nayi saurin fizge nonon a bakin sa tare da sakin Æ´ar karamar kara,
na yarfe hannu ina faÉ—in
"Wayyo zafi".
ai ko shima sai ya saki kuka yana cusa hannunsa cikin baki,
Mama
tace "Daure ki bashi kinji".
sai da Mama tayi ta lallaɓi na kafin na yarna na maida masa nonon bakin sa ina matse ido harda kwalla.
bayan yasha ta kwantar da shi ta É—auko ta ita ma tasha.
kana tayi musu wanka
nan da nan kuwa sukayi bacci....★
Kwanan mu uku a asibiti kullum sai Zainabu ta ai ko mana da abinci.
zuwa yanzu kam jikina Alhmdllh dan har ina sauka na taka da kaina,
Muna zaune Mama nata jana da hira yayin da take ta yiwa yaran wasa.
Malam musa yashigo da sallama bayan an gaisa yake
tambaya haryanzu baban yaran baisamu isowa bane?
Mama tace
"Eh. a takai ce.
ƙasa nayi da kai na ina wasa da yatsun hannuna yayin danaji wani abu yataso yatokare zuciyata nan take naji ƙwalla yaciko min ido dasauri namai dasu,ta hanyar ambaton sunan Allah a cikin zuciya ta,
Har yanzu mutanen da suke hulÉ—a da Mama basusan ko wacece niba,
har yau Mama bata sanar musu koni wacece ba abun da kaÉ—ai suka sani takuma sanar musu Ni É—iyar kanin tane kuma mijina soja ne yana bakin ai ki haihuwa nazo,
rumtse idanuna nayi yayin da kwallar da naketa mai dasu suka zubo,
nakai hannuna nashare batare da nabari sun gani ba.
Malam Musa yace
"Ayya to Allah yataimaka yaune kwanan su uku ko? yakamata a musu huÉ—uba gashi kuma har yanzu bai samu isowa ba".
da sauri Mama tace
"Haka ne kuma inaga zuwan sa kam ma zai kai har bayan suna ai ko baza'a jira har sai yazo ba za'a yi musu huÉ—u ba,
Malam ayi musu huÉ—u ba kawai, yoo yaushe za'a zauna zaman jiran sa".
Malam musa yace
"To babu damuwa, shin yafaÉ—i sunan daza a sa ma yaranne?".
mama
tace "Eh". takalleni tare da faÉ—in
"Yayama sunan daya faÉ—a miki?".
shiru nayi kaina a kasa,
sai da mama ta kuma mai-maita
tan bayar kana nace
"Idris da Aysha"
tabbas babu sunan da ya dace da yaran face sunan Abbu da Inna, sun nuna min so da kauna da kuma gata. bakuma zan taɓa mancewa da su a rayuwa taba.
Malam Musa yace "Masha Allah yara zasuci manyan suna".
gyara rukon baby boy din dake hannusa yayi kana yazura hannunsa cikin aljuhu yaciro dabino,
Nan yayi Masa huÉ—uba da suna Idris kamar yadda addini yakoyar,
kana ya mikawa Mama shi yace
"Allah yaraya Idris bisa Sunnah".
Mama tace "Amin".
ta kwantar da shi ta dauko baby girl din ta Mika masa Nan ita ma yayi mata huÉ—uba,
kana yamikawa Mama tare da fadin
"Allah yaraya Aysha".
Mama takuma amsawa da Amin Amin,tare da masa godiya.
Nan yayi Mana sallama yatafi.....
Mama ta dubeni da murmushi dason gusar min da damuwar da take hangoshi kan fuska ta, ta kalli yaran tana faÉ—in
"Masha Allah kinwa Inna takwara ne ko wa kanki?".
ta faÉ—a tana murmushi,
ido na tsurawa babyn kana nace
"Wa Inna nayiwa takwara kamar yadda nima naci sunan ta".
dariya Mama tayi tare da lakata hancin babyn tana faÉ—in
"Kaga Aysha É—iyar Aysha kakar Aysha uban giji yaraya ku da imani,
to me za'a rika kiran su yanzu kuma?".
tafaÉ—a tana duba na fuska É—auke da murmushi.
shiru naÉ—an yi alamar nazari zuwa can nace
" *NASEEM DA NASMAH*"
baki Mama ta washe tana faÉ—in
"Iye Ah gaskiya sunan yayi kama dasu".
yanzu kam sai da mama tasani murmushi idanuna a kan yaran ina duba kamar da tace sunan yayi da su....★
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.