Hamdah Littafi Na 2 Complete Hausa Novel
Reading file: HAMDAH part 2 complete.txt
Chapter 17 of 35
Yau Zainabu da kanta takawo mana abincin dare da kuÉ—i naira dubu 5.
nan take cewa Mama malam Musa ne yabata rance,
ranar da tazo niman kuÉ—ine tayi wa malam É—in magana ko yana dashi,
yace
Wlh baya dashi sai yau ya samu shine yabata takawo.
Mama tayi ta mata godiya tace dan Allah tayi masa godiya kuma in sha Allahu zata biya da hannunta da yar dar Allah.
Nan da nan kuwa takai ragowar kuÉ—in da ake binsu a asibitin.
Washegari da safe aka sallame mu....
ranar da muka dawo gida a ranar mama tafara awara,na tausaya mata kwarai,
ranar sai da nayi kuka dan nasan dan ni ta fara sana'ar a yau wan da yakama ta ace hutawa take da É—awai niyar asibitin da ko baccin kirki batayi, sai gashi muna shiga gida tasoma wani ai kin...
ana gobe suna da yamma bayan Mama tayi wa yaran wanka muna zaune ina cin abinci,
Mama na goye da Nasmah yayin da Naseem ke rike a hannunta tanata jijjiga shi, Mama ta dube ni tace
"Wannan mai gidan fa in baiji motsi a bakin sa ba baya gane wa".
fuska na kwaɓe nace
"Mama yanzu fa suka sha".
"To yaro shi ina ruwan sa ciki kawai yasa ni gama dai kiba shi yasha,
ga kawata ma na kan motsi".
Kamar na kurma ihu haka naji,
yanzu suka sha babu jimawa gashi yanzu wai suna nima,
cikin tura baki nace
"Allah kaÉ—an zan basu anjima kuma abasu kunu".
Mama tace
"Kunu kuma?".
nace "Eh". dariya tayi tace
"To shike nan yanzu dai ki basu susha".......
Washegari yakama ranar suna,
da sassafe Mama tayi min wanka kana tayiwa Nasmah da Naseem,
nashirya cikin doguwar riga É—aya daga cikin kayana da nazo dashi tun wancan lokacin yaÉ—an kasa min sabo da ciki sai na ajeshi bana sa shi, shi yana nan har yanzu da É—an sabon tar sa.
É—an ribar awara da tasamu na kwana biyu
da shi tayi cefane ta siyi shin kafa ta haÉ—a da sauran waken kosai suka girka abinci da Zainabu da tun da safe tazo.
da rana makota suka shishshigo,
Mama mai yin biki ne tana da kokarin shiga wa mutane biki, duk wan da take yin biki da su kowa sai da ya kawo mata rigar baby wasu na maza wasu na mata da omo da sabulu har da man shafa wa.
Naseem yasamu kaya kala huÉ—u yayin da Nasmah ma tasamu kala huÉ—u.
da yamma kowa ya watse....
Bayan suna Mama tafara niman kuÉ—i ba kama hannun yaro domin biyan bashin da ake binta,
ba iya sana'ar awara da kosai kaÉ—ai ta tsaya ba har da kayan miya tana sara tana siyar wa,
da duk wani abu na nasa'ar cikin gida da tasan zata sami riba a kansa tana siya ta siyar.
cikin yar dar Allah da ikon sa yadafa mata duk abun da zata taɓa na sana'a sai ta sami riba a kansa...
ranar da muka yi arba'in ranar ta kai wa Zainabu da malam Musa kuÉ—in su,kamar yan da tayi musu alkawarin bayan suna zata biya su takuma jajirce wajen nima har ta samu,
tayi ta musu godiya.....
Tun daga ranar hankalin ta ya kwanta ta kuma mai da hankalin ta wajen kula da Ni da kuma Æ´aÆ´ana,
duk wani ribar da zata samu a kanmu yake kare wa.
yanzu nawar ke garau idan ka ganni bazaka ce CS aka min ba, nakan ji mutane da dama suna cewa jikina mai kyau ne bana da kan jiki.....
Haka mukayi ta lallaɓa rayuwa nakuma daure da juriyar shayar da yaran,sai dai na rame kwarai suko kamar hurasu ake, sunata girma da kuma kara wayo sosai,
lokacin da suka cika wata uku,
Mama ta haÉ—a musu garin kunu na alkama waken suya da gyaÉ—a,
nan ne naÉ—an sami sauki,
da shi muka cigaba da rainon su...
Ranar wata asabar..........!★
Mommyn twins ce
Ranar wata asabar hakan yayi dai-dai da watan su Naseem huÉ—u da sati biyu,
Zaune muke a tsakar gida, ina rike da Naseem a sakiyar kafafuna dan alokacin suke koyon zama.
Mama na goye da Nasmah tana bacci, ita kuma tana ta É—an aikace-aikacen ta.
Sallama mukaji daga bakin kofa da karfi, ba Mama kaÉ—ai ba hatta ni sai da naji wani irin muguwar faÉ—uwar gaba dajin muryar mai sallamar,
yau kusan sati É—aya kenan Alhaji Mamman sai yayi sallama a gidan kullum sai yazo maganar kuÉ—in hayar sa, wan da yanzu ya ninku yazama na shekara biyu da rabi.
takuma sana diyyar mune hakan ya faru kula da Ni da Æ´aÆ´ana shi ya hana ta ajewa Alhaji Mamman kuÉ—in hayar sa,
yunkurin mikewa nashiga yi jin yacigaba da kwaÉ—a sallamar ba ko kakkautawa,
kafin na mike ma ya sako kansa cikin gidan yashigo,
yana faÉ—in
"Fasuma kinsan dai ba gidan mijin ki bane ba,kuma bamu haÉ—a kuÉ—i da ni da shi mun siya ba,
sannan kuma koda ace ma mun haÉ—a kuÉ—i da ni da shi mun siya,
kinsan dai yanzu yariga da ya mutu kuma dole a cire min nawa a ciki,
bare kuma gida gida nane ba nashi ba ko bulo É—aya bai É—aura a kan gidan nan ba,
bare ki zauna kice kina cin gadon sa,
dan haka kifita min a gida yau babu afuwa babu rangwami,
kifita min a gida yau zan saka Æ´an haya acikin gida na,
gasu nan ma munzo tare da su,
ina bukatan kuÉ—i dan sabo da kuÉ—i na tara kafin na gina gidan,
ga Æ´an haya nan mun iso da su ga kayan su can a moto dan haka ki fita kibasu É—aki."
yakaraso ciki yana muzurai tare da cigaba da faÉ—in
"Ganan masu shiga gida sun iso ke kaÉ—ai suke jira kifita kibasu É—aki,
dan yanzu É—akunan gida nasune su sun iya biyan kuÉ—in haka,
sannan kuma
bawai na bar miki kuÉ—in haya da na ke binki na shekara biyu da rabi bane ba,
ina binki bashin su kuma zaki nimo kibiya ni kaya na babu rangwami acikin watannan zaki biya ni in baki bada ta daÉ—i ba zaki biya a hannun hukuma."
Cikin tsananin tashin hankali mara misaltuwa na É—ago Naseem dake hannuna na goya shi,
na mike tsaye yayin da Mama tarika haÉ—e hannayen ta biyu cikin matukar tashin hankali tace
"Dan Allah Yaya kayi hakuri insha'allahu ina nan ina kan tara maka kuÉ—in nan kayi hakuri dan Allah kasan dai yanzu abubuwan sai a hankali,dan Allah
kayi hakuri in sha'Allah zan haÉ—a maka kuÉ—in acikin Æ´an kwana kin nan,
kakara yimin afuwa".
cikin É—aga murya Alhaji Mamman yace
"Dakata dan Allah Ni kin ishe ni kullum ke kenan maganar ki ayi miki afuwa ayi miki rangwami,
wai shin kan kuÉ—in nan in da rangwami da afuwa ake tarashi zai taru ne,
in dai da akwai rangwami acikin tara dukiya da zai taru ne?
nifa kuÉ—i kawai nake bukata,
shi kuma nake son tarawa,
kin san ta yan da akayi na tara kuÉ—i na siyi gidan?,
nifa kuÉ—i kawai nake bukata,
in da ace kin fita tuntini a gidan nan da na tabbata na tara kuÉ—in da yafi abin da ake tunani dan haka ni kifita min agida kawai babu wani rangwami."
fuskarsa yajuya ta bakin kofa ya É—aga murya yana faÉ—in
"Kushigo da kayan Bismillah ga gidan kushigo da su".
kofar da yake kallon na zubawa ido in da naga shima ya fuskanta yana maganar,
wasu mata da Æ´an matasa ne suka fara shigo wa da kaya,
suka ta shigowa da shi suna ajiye wa...
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.