Hamdah Littafi Na 2 Complete Hausa Novel
Reading file: HAMDAH part 2 complete.txt
Chapter 5 of 35
ido na kurawa cikin layin da nake tsaye a mashigar sa, matasa da magidan ta kowa yana ta haramar tafiya masallaci sallar magriba. Da sauri na sunkuya na janyo akwati na nasoma takawa cikin layin da sauri sosai dan ba karamin tsorata nayi da jin abun da mutumin nan yafaÉ—a min ba,sai dai ina soma tafiyar naji cikina yayi min wani irin murÉ—a yayin da kai na yake mugun sara min.
Na yi tafiya mai É—an nisa sai na zauna kan dakalin kofar wani gida,tare da tafe kai na dake matsa nancin tsaramin, da hannuna É—aya É—aya hannun kuma na dafe cikina, tausayin kai na ya kamani sai kawai na fashe da kuka mara sauti.
cikin muryar kuka nake faÉ—in
"Wayyo Allah cikina kai na wayyo Allah na, innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un²".
wani sabon kuka ne yakuma zuwa min Allah sarki Inna banki a yanzu Allah ya É—auki raina kamar yan da yaÉ—auki nata ba yafiye min wan nan rayuwar.
nayima ina kuka mai matukar kona zuciya kukun da naɗau lokaci mai tsawo batare da nasan lokacin yakure har haka ba,guri yayi shiru bakajin motsin komai sai haushin karnuka da kukan wasu tsuntsaye, na rakuɓe jikin garo na cusa fuskata sakankanin cinyoyi na,an ce bacci ɓarawo ne to ni dai na tabbata duk iya satan sa bazai iya sace ni a wannan irin lokacin ba,ta ya zai sami narasar saceni bayan ina tangare a dandamalin guri wan da a iya ƴan shekaru na ban taɓa mafarkin kasan tuwa a irin hakaba,ban taɓa rayuwa cikin bakin duhu irin haka ba,ina zaune a haka gari yawaye..
nayi al'wala a panpon da ke jikin gidan da nakwana a kofar gidan nayi sallah.
Koda gari yayi haske jama'a suka fara zirga-zirga a kan hanyar duk wan da yazo wucewa sai ya kalleni ganin na zame wa mutane abun kallo dai na mike naja akwati na,
a sannu narika kusawa cikin unguwar haka na rika zaga cikin unguwar idan na gaji sai na sami guri na zauna in na huta sai na mike nacigaba da tafiyar da ban san in da zani ba.
ranar wuni zubur nayi ina haka yunwa kishin ruwa zafin rana sune abokan rayuwata...
Yau kwana na uku a kan layi nake kwana idan nayi ta yawo har dare ya riskeni sai na sami kofar wani gida na rakuɓe gefe a haka zan kwana a zaune,batun yunwa kuwa tarigada ta shiga jikina har ya zamana bana jinta sai dai cikina sai yayi ta murɗeni abun cikina yayi ta motsawa,idan naji kishin kuwa sai na bazama yawon niman kofar gida mai panpo na tara da hannuna nashi,
ina sha kuwa sai nayi hawaye sabo da murÉ—an da cikina zai yi ta min...
Zaune nake akofar wani gidan da nake tunanin a nan yau zan kwana dan yamma tayi sosai ana daf da kiran magriba,
kishin ruwa ne ya dameni tun É—azu sai dai nayi yawo a layin da nashigo yau ban sami wani gida mai panpo a kofar gidan ba,sai dai na fuskanci wannan unguwar na marasa karfi ne dan gine-ginen su ma kaÉ—ai kagani zakasan unguwar talakawa ne.
a hankali na mike na janyo akwakina nacigaba da tafiya ko zan sami ruwa dan ina jin kishin sosai,
ina sharar wata kwana can na hango rijiya mutane na tsaye a kansa anata jan ruwa a cikin sa,
da sauri na nufi gurin dan ruwan da nafi muradi kenan,ina isa gurin na tsaya gefe da wata Æ´ar dattijuwar mata nace
"Dan Allah a sammin ruwa".
matar ta juyo kana tace
"Sha zakiyi ne?".
kai na gyaÉ—a mata tace "Ai ho". wani É—an kara min roba ta janyo ruwan ta zuba ciki tace
"ÆŠauka kisha".
To nace da sauri na É—auka nasoma sha nasha sosai sai da naji cikina ya cika sannan na aje robar tare da yi mata godiya,ta É—au ruwan ta tatafi a hankali naji cikina na É—an murÉ—a min sai dai ba kamar na duk lokacin da na sha ruwan panpo ba,a hankali nasoma tafiya naÉ—an yi nisa da rijiyar kaÉ—an sai na zauna kan wani bulo dake gefen ciyawa jin cikin bai dai na yimin murÉ—a ba.
kai na na cusa sakankanin cinyoyi na inajin yan da cikin ke ci gaba da murÉ—a ni,
da sauri na É—ago kai na jin abu na tafi a kafata,wani irin waro ido nayi cikin firgici da razana ganin maciji a saman kafata,cikin zafin nama na mike tsaye tare da kwalla kara na yarfe kafar da karfi macijin ya faÉ—i can gefe yashige cikin ciyayin dake gurin,
da iya karfina nake ihun ina yarfe kafar....
"Wane ne waye a nan?".
naji murya daga can ana tan baya,cigaba da tan bayar a kayi ana motsawa in da nake,niko sai ihun nake ina tsalle da yarfe ƙafan,
jin an dafa kafaÉ—a na ana faÉ—in
"Subhanallahi Æ´ar nan menene?".
da sauri narike hannun matar da naji tana tan baya na da karfi cikin sananin tsoro nace
"Maciji maciji maciji".
nafaÉ—a da karfi ina cigaba da yarfe kafar,
a kiÉ—ime matar tace
"Ya cije ki ko au da ma kece? me yazaunar dake a nan tun da kinsha ruwan basai kiyi azamar tafiya gida ba, kyazo gidan macizai kizau na ba'azo in da suke Bama ana tare-tare dasu acikin gida bare kinzo nan cikin su,maza zo muje a samiki magani tun kan dafin ya haura miki,wani irin zuwa unguwa ne har guri ya rufa baza'a koma gida ba".
tafaÉ—a tana janyo hannuna,sai lokacin na gane matar itace wacce na roketa ruwa ta bani nasha É—azun nan.
ta janyo hannuna ina É—angala kafar, tana cigaba da faÉ—in
"Dage kiyi sauri muje tun kafin dafin ya haura miki,waÉ—an nan abu ai sai a hankali har gida suke shiga mana dan ma yanzu da sauki muna saka musu magani shine suke É—an yin nesa da gidajen mu".
dai-dai lokacin muka isa kofar wani gida muka shige ciki, murya ta buÉ—e tashiga kwaÉ—a sallama tare da faÉ—in
"Zainabu zainabu matar gidan nan tana nan kuwa".
wata mata tafito daga cikin É—aki tana amsa sallamar tace
"Ina nan, a'a Mama mai awara kece tafe".
Matar da muke tare da ita tace
"Eh,malam Musa na nan kuwa ko har yatafi masallaci?".
Zainabu tace
"Yana nan yanzu yake shirin fita yazaga ne, yauwa gashi ma yafito".
tafaÉ—a tana kallon hanyar bayi,
mutumin da a ka kira da malam Musa ya dube mu yana faÉ—in
"Sannu Mama mai awara ku ne da yammacin nan".
tace
"Eh wlh malam Musa maciji ne ya cije ta dan Allah a sa mata magani kafin ya haura mata".
ya dube ni da har lokacin ina masar kwalla
yace
"To subhanallah garin yaya?".
Mama mai awara tace "Can gefen fadama tabi kasan kuwa kamar gidan su ne".
"Kwarai kuwa Allah yasa ba mugayen bane".
yafaÉ—a yana shige wa cikin É—aki mama mai awara tace
"Amin dai". ni dai ina nan itana masar kwalla ban iya cewa komai ba, matar malam Musa wato Zainabu tashiga tafito da taburma ta shin fiɗa tace muzauna,ba jimawa kuwa malam Musa yafi ɗauke da wata ƴar karamar jaka ya zauna gefen taburman kana yadube Ni yace na miko kafar da yaga ina ta girgiza shi,na mika masa yazuge zip ɗin jakar yaciro kayakin magungunar sa ya zaro wani farin gyale ya gyara zaman sa da kyau ya ɗaura ƙyallen saman kafata kana yaɗauko wani magani acikin kwalba yaɗan ɗiga kan ƙyallen dake kan kafar tawa.
yazubawa ƙyallen ido
sai kuma ya É—ago ya dube ni yace
"An ya nan ne kuwa".
kai na gyaÉ—a da sauri cikin matsar kwalla nace
"Allah nan É—in yahau".
nafaÉ—a ina daÉ—a girgiza kafar dan ji nake kamar har lokacin yana kan kafata,
Maganin yadaÉ—a É—igawa kan gyallen kana ya dubi mama mai awara
yace
"Babu wani alamun dafin maciji a tare da ita gashi nan dai kina gani".
sai ya mai da dubansa gare ni yace
"Amma yaya kikaji da ya sare kin?".
nace "Ganin sa nayi a kan kafata kawai ban san yan da akayi yahau ba".
kai malam Musa ya jinjina kana yayi murmushi da faÉ—in
"Allah ya tai make ki wata kila wucewa zaiyi ke kuma kika tsaya masa takan hanya yabi takafar ki yawuce batare da yasan kina ma gurin ba da taimakon Allah".
mama mai awara ta sauke numfashi da karfi tace
"To Allah ya taimaka ina gama macijiya ce dan su matan basu fiye yin saraba sai sunji matsi".
Zainabu dake gefe tace "Haka ne kam Allah dai ya daÉ—a karewa".
suka amsa da amin nidai ido naketa cirewa cike da tsoro.
mama mai awara ta mike tana yiwa malam Musa godiya tayi wa zainabu sallama tayi waje nabi bayan ta.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.