Best / Popular Hausa Novels

Hamdah Littafi Na 2 Complete Hausa Novel

Reading file: HAMDAH part 2 complete.txt

Chapter 18 of 35

Hannu mama ta kuma haÉ—awa tana cigaba da rokon sa da haÉ—a sa da Allah da yi masa magiyar in sha Allahu zata biya sa kuÉ—in a cikin watannan,
yace
"Dai na haÉ—a ni da Allah ki cuce ni,
na dai faÉ—a miki babu bulo É—aya da mijin ki ya É—aura kan ginin gidan nan,
nariga da na gama magana yanzu bani da hannu acikin wannan gidan na nariga da na bada hayan shi,na karɓi kuɗin sa dan haka fita ki basu gida yanzu nasu ne".
yajuya yaso ma tafiya yana cigaba da faÉ—in
"KuÉ—i na da nake bin ki bawai na bar miki bane kuÉ—ina yana nan a kanki kuma zaki biya ni,
na baki sati biyu ki biyani kuÉ—i na idan ba haka ba sai nayi miki rashin Mutun cin da baki tunani,
kin san ni a kan kuÉ—i ko uban waye ma zan iya masa rashin mutunci ko shi mijin naki da muke uba É—aya bai isa yaci kuÉ—i na ba tun da bashi ya nemo min ba."
yayi waje yana cigaba da zazzage bala'i.

Bayan sa Mama tabi tana cigaba da haÉ—a shi da Allah har kofar gida ta bishi,shi ko yaja garen sa yahaye babur É—in sa yayi gaba.
suko mutanen da yazo da su sai shigo wa da kaya suke suna jibgeshi a tsakar gida,
tuni hawaye yafara sauka a ido na, muna tsaye cirko-cirko har suka gama shigo da kayan.
matan suka dubi Mama sukace
"To mun gama shigo da kaya yazu shirya shi cikin É—aki ga gurin yafara rufa wa kar ruwa ya sauko ya jika mana kaya."
da sauri Mama ta dubi matar batare da tace komai ba,
Hannuna Mama tarike tana faÉ—in
"Zo mu fitar da kayan".
cikin zubda kwalla nace
"Mama idan muka fitar da kayan ina zamu kai?".
tace
"Allah bazai hanamu in da zamu kai ba."
Haka mukayi ta fito da kayan mu nuna kai shi can waje kofar gida,
tas muka fito da kayan muka jibgeshi waje duk da dama bawani kayan kirki bane.
muna tsaye a kofar gidan Zainabu ta iso mu hankali tashe tana faÉ—in
"Mama mai awara yanzun nan yaro yazo yace min yaga kuna ta fitar da kaya,
wasu kuma suna shigar wa ciki, Mama da ma tashi zakiyi shine baki faÉ—a mana ba?."
Murmushin yake mama tayi kana tace
"A'a mai gidan ne yazuba Æ´an haya aciki shiyasa muke tashi muma tashin yanzu ne yasa memu bawai tuntini da ma da shi bane".

Ido Zainabu ta waro tare da buga kirji tace
"Ya zuba Æ´an haya a cikin gidan bayan da wasu masu hayan aciki,
ban taɓa ganin haka ba,
ba'a taɓa ɗaga ɗan haya rana a saka batare da an bashi lokaci ba sai an bashi kwanaki ya kama gidan da zai zauna kafin a ɗaga shi,
ba irin wannan É—agawar babu sanar wa ba,
to yanzu ina zakuje Mama kuna da wani gidan da kuka kama ne?".
Mama tace
"Ko É—aya yanzu dai zamu ni mi wani gidan hayan da zamu zauna".
"Gaskiya kam amma wallahi bai kyauta ba ai ba haka ake yi ba ba'a taɓa ɗaga mai zaman haya haka lokaci guda ba,
sai dai a baka lokaci ka kama wani gidan hayan sai ka tashi ba irin haka lokaci guda ba".
Mama kam murmushin karfin hali yacigaba da yi,
Niko hawaye ne kaÉ—ai ke zuba a ido na naka iya furta komai.
Zanabu tace
"Mama ku tattaro kayan kizo muje ga guri yafara rufawa hadari yana kan taso wa".
ta sun kuya tana tattaro kayan tare da cigaba da faÉ—in
"Kuyi sauri kada ruwa yasau, ko kuzo muje kutara su a zauren gidan mu kafin ku sami wani gidan".
Mama tace
"To Zainabu".
nan muka shiga kwashe kayan muna kaiwa gidan Zainabu a zauren gidan ta muka tara kayan gaba É—aya sannan muka shige É—akin ta dan lokacin tuni ruwa ya sauko...

Tun da aka fara ruwan nan bai tsaya ba har yamma,
har Malam Musa yadawo yazo yasa memu a gidan,
koda yaji labarin bai ji daÉ—i ba kwarai yace Alhaji Mamman bai kyau ta ba bahaka ake yi ba,sai dai yasan waye Alhaji Mamman karamin ai kin sa ne yin hakan.
Yacewa Mama bari a É—auke ruwa zai fita yake yataya ta niman gida ko Allah zai sa a samu a yammacin,.
Mama tace ita ma É—in ruwan take jira yaÉ—au ke tafita niman gida.
Gidan malam Musa É—aki É—aya ne tak a gidan shine kuma wan da suke zaune da matar sa a ciki.
dan haka zaure yako ma yaje ya zauna yabar mu acikin É—akin,
gaba ki É—aya Mama a takuri take ganin mai gidan yako ma zaure ya bar mana É—akin.
wasa-wasa ruwan nan bai É—auke ba sai daf magriba,
dan haka Malam Musa yace
Abar niman gidan sai gobe tun da yanzu dare yariga da yayi,
a zaure yakwana yabar mana É—akin...

Washegari da sassafe Mama tafita neman gidan da zamu koma bata dawo ba sai wajen azahar,
tadawo gaba É—aya a galabaice,
a ɓangaren Malam Musa shima bai jima da dawowa daga niman gidan ba,
Muna zaune a É—aki
Zainabu ke tambayar Mama Allah yasa anyi sa a an sami gidan.
numfashi mama ta sauke cike da É—inbin damuwa tace
"Wallahi nagama iya yawo na ban sami gida dai-dai da kuÉ—in hannuna ba duk gidan da naje niman hayar sa gaba É—aya sun fi karfin kuÉ—in hannuna,
azaman yanzu kuma gaskiya masu rangwami sunyi karan ci".
kai Zainabu ta girgiza cike da tausayawa kana tace
"Gaskiya kam yanzu rayuwa tayi tsada Allah yayi mana magani".
Amin muka amsa dashi,
gaba ki É—aya jikina yagama yin sanyi.
Mama ta mike ta nufi zaure in da kayan mu yake can,ganin ta ɓata lokaci bata dawo ba sai na mike na bi bayan ta,
ganin ta nayi tana shirya kaya cikin É—an kari min jaka gaba ki É—aya hankalin ta a tashe,
ta dube ni tare da faÉ—in
"Zanje garin mu HAMDAH kamar dai yan da na taɓa baki labari ni ƴar Yola ne aure ne ya kawo ni nan,
yanzu rabona da Yola shekara 7 kenan zanje ni na dawo in sha Allahu kwana biyu zanyi na dawo,
zan tafi mana da wasu kayayyakin mu zanje na duba kalar yanayin zaman can idan naje nasa mu matsuguni,duk da dai dama muna da gidan gado kamar yadda na taɓa baki labari yanzu dai zanje na duba acikin gidan gadon mu idan akwai ɗakin da zamu zauna,
zan dawo nazo na É—au keki mukoma,
kwana biyu kacal zanyi na dawo sai na É—auke ki mu koma tare".
ta ciro kuÉ—i naira dubu biyu da É—ari biyar ta mika min
tace
"Ga wannan ki rike a gurin ki ko zaki bukaci wani abun,
kin ga suma nan basu da karfin da zasu iya É—awai niyar ku duka duk da bawai jimawa zanyi ba kwana biyu ne ka cal,
Amma ki rike zai iya yi muku amfani,ko zaki ga abun da kike so ko su Naseem da Nasmah sai ki siya musu".
numfashi na sauke
jiki a sanyaye dan Mama ta taɓa bani labarin family'n su
Su biyu ne agun mahaifin su ita da wanta na miji,
lokacin auren ta yayan ta baiso auren da wan da take so ba dan lokacin mahaifinsu ya rasu a haka dai akayi auren sam baya so,
shi yasa ko taje gidan ma bata jin daÉ—i shi yasa takan daÉ—e bataje gidan ba dan ko taje ma baya sauraran ta,
ko da mijin ta yarasu taje amma yaki yabata fuska tazau na agidan,
sai dai ta alakan ta hakan dan gidan nasa ne yanzu sabo da shi yaci gadon gidan,
abun tun yaranta har yanzu tana ta kan fama,
har yakai ga yanzu shi yayan nata yarasu sai dai matar sa ta ari abun ta yafawa kanta,
ta kanainaye gidan tace gida natane da Æ´aÆ´an ta dan haka babu wan da ya isa ya zauna mata a gida.
dan a lokacin da mahaifin su Mama ya rasu yayan ta shi aka basa gadon gidan in da ita aka bata
gadon gonar mahaifin su...
idan taje gidan matar tarika mata wulakanci da gani-gani shi yasa ma shekaran ta 7 bataje ba...

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.