Best / Popular Hausa Novels

Hamdah Littafi Na 2 Complete Hausa Novel

Reading file: HAMDAH part 2 complete.txt

Chapter 6 of 35

Muna fita ta dube ni tace
"Allah ya kare mugayen basu cije kiba,ai wannan mai maganin har wasu garuruwa suna kawo masa jin yan sarar maciji dan shi gada yayi tun iyaye da kakani,idan maciji ya cije ka to da wannan kyallen yake gane kalar macijin da ya sare ka,sai ya baka magani,idan yasaka kyallen dai-dai in da maciji yazuba dafin sa to kyallen zai canza kala yakoma kalar jikin macijin,kinga ai yan da yaÉ—au ra kyallen a fari a farin sa ya É—aga,babu rabon wahala Allah ya kare,
Maza kiyi gida yanzun nan muje na nuna miki hanya mai sauki da zaki fita bakin hanya,jirani a nan na É—auko miki jakar ki".
kai kawai na gyaÉ—a mata yayin da naji wasu zafafan hawaye sun zubo min,yanayin yan da matar take magana yasa ni tuno da Inna ta,
"Allah sarki Inna na tabbata in da kina numfashi bazan taɓa hofanta ba".
Kwalla na kuma share wa lokacin da matar tadawo gaba na tana mika min a kwatina,
tace
"Maza ki tafi gida dare yayi ke bakya tsoron kije gida iyayen ki su miki faÉ—a, Allah ma ya takai ta ai da sai dai a kai ki gida da raunin maciji,
yi sauri muje na nuna miki kinga har na makara markaÉ—en awara nafito É—auka wa shine na jiyo kururuwar ki da yanzu na dafashi har na tsane".

Duk abun da take faÉ—a sama-sama nake jinta wani irin kuna da raÉ—aÉ—i zuciya ta ke min sai sharar kwalla nake.
muna fita gaban rijiyar nan da hannu ta nuna min hanya tace
"Ki mike nan hanyar ta ɓulle har titi Allah bamu alheri".
kai na gyaÉ—a kana a hankali nasoma tafiya,ita kuma tabi ta wani hanyar.
A hankali nake tafiyar idanuna a kasa sai gani nake kamar zan ɗaura kafar kan wani macijin,duk da kuwa guri yafara yin duhu lokacin........!★

Mommyn twins ce

*Masha Allah yau Allah yayi ikon sa na dawo Nagode da addu'o'in ku sosai*🥰

Ina ganin shige war matar cikin wani gida sai na rakuɓe kofar gidan da na iso yanzu,
hawayen tsoro ne suka shiga zuba min a ido shike nan Ni nasan rayuwa ta ta kare yau maciji shi zai yi saniyyar barina duni,tun da kuwa garin su nazo,
wani sassanyar kuka na sake mara sauti nasadakar ma kawai macijin yacije ni na mutu ko zan huta da wannan rayuwar kunci da bakin cikin.
Ji nayi an gasko min toci da sauri na É—ago kai na tare da kare fuskata da hannuna sabo da hasken tocin dake haska min ido.
da sauri takaraso in da nake rike da roba mai É—auke da kullun waken awara a ciki,salati ta doka tana faÉ—in
"Yau naga ikon Allah ƴar nan ashe baki tafi gida ba,kuma zama anan kikayi,hanyar koma wa gida ne ta ɓace miki kokuwa wani laifin kikayi kike tsoron komawa,in ba haka ba mai zaisa kiki komawa gida,ki zauna kina ta rabuɓe-rakuɓe a nan,
yaran zamani ga iya laifi ga tsoron hukunci,tun da kana tsoron hukunci ai sai ka riƙa gujewa ai kata lai fi,to baki tsoron ki karawa kanki wani laifin ni sam banason yaro irin haka to menene am fanin fitowa a gidan da har zaki ki koma wa gidan ki rakuɓe a nan kinata koke-koke, to in bugun naki za ayi bagara ki koma a bige ki ya wuce miki ba, ka zauna ka karawa kanka laifi,ɗauki jakar maza kizo nan".
tafaÉ—a tana dubana.

Tana gaba ina biye da ita muka shige cikin wani É—an ma dai-dai cin gida mai É—auke da É—aki ciki biyu sai kitchen da Kuma banÉ—aki a gefe,
da kaga kidan kasan na talakawa ne sosai sai dai a tsaftace yake babu kazanta ko datti a cikin É—an ma dai-dai cin tsakar gidan.
tanuna min É—aya daga cikin É—akunan tace nashiga,
a kasa kan taburman dake malale cikin É—akin na zauna,
babu jimawa tashigo É—auke da kwano ta direshi gaba na tana faÉ—in
"Ci yanzu muje na rakaki bakin titi kihau abun hawa ki koma gida,
in ban da rashin hankali niyyar guduwa kikayi gaba É—aya a gidan da kika É—au jaka?,
Akul karki kuma wan nan ba ta'adar É—an kirki bane ci maza muje".
wasu zafafan hawaye na share kana da sauri har hannuna na rawa na buÉ—e kwanon,
tuwon jan dawa ne miyar bushashiyar kuɓaiwa,sai tashi da kamshin daddawa yake,
da sauri na sa hannu na soma ci.
ta fita ta kuma dawowa da kofin ruwa ta aje min,kana ta fita taje tasoma tatar kullun da ta É—auko markaÉ—en sa.
cin tuwan nake tamkar na sami nama,yau kwana uku da wuni É—aya kenan rabun da nasa wani abu mai gishiri a bakina.
naci tuwon sosai dan har nakusa cinye wa kana na kara da ruwa,
bayana na jingina da jikin garu tare da yiwa Ubangiji godiya,
a hankali narka jin murÉ—ar da cikina keyi min yana É—an raguwa, yayin da abun cikina da tun jiya da cikin ya murÉ—a ni sai shima naji ya motsa sai ya sauka kasan marana ya dunkule guri guda bai kuma motsawa ba sai yanzu naji yana É—an motsawa da harbawa a hankali...
can an jima matar taÉ—a go labule tace
"Zo kiyi sallah kafin awara ta ta dafu sai muje na rakaki".
"Tom". nace na mike nafito rike da lanta da ke cikin É—akin kasan cewar guri yayi duhu sosai,cikin É—ar-É—ar nashiga bayin nayi sarki nafito kana nayi al'wala na koma É—akin na gabatar da sallar isha,
bayan na idar ina zaune kan sallaya tashigo,ganin da al'wala tare da ita sai na mike nabata sallayar na koma gefe.

Bayan ta idar ta mike ta dube Ni tana faÉ—in
"Taso muje ga dare nata yi ki tabbatar kin koma gida kuma kada kisa ke yin haka
kinaso kishiga fushin iyaye ne fushin su musufa ce yana jefa mutum cikin halaka".
wasu hawaye ne naji sun kuma zubomin
"innalillahi wa'inna'ilaihirra'un".
nashiga nanatawa a raina,shin nima haka zan tabbata da fushin iyaye,shin meyasa iyaye na zasuyi fushi da ni kan abun da ban ai kata ba,me yasa zasu yanke min hukunci kan abun da bana da masaniya a kansa??.
maganar ta naji a sama
"Yau kitashi muje kin tsaya kuka ne,ai har gida zansa mai abun hawan yakai ki, tukunna ma inane gidan ku a wani unguwa kike? dan gobe zanje na tabbatar da kin koma ko baki koma ba,kada ki sake ki kuma laifi kice zaki gudu ni bani son yaro irin haka a ina iyayen ki suke?".
kuka na fashe dashi cikin muryar shashsheka nace
"Ni bani da iyaye bani da komai haka zanyi tabin layi har rayuwa ta ta kare na mutu."
"Zancen banza kai, to tashi ki fita min a gida kije kikare rayuwar naki acan,an ya ma ba yawon duniya kika fito ba?to ita duniya ta ishi kowa riga da wando tun da shi kika zaɓa je kibishi,tashi maza ki fita min a gida ban mayi tunanin ko wacece keba na ɗauko ki na kawo ki har cikin makwanci na,tashi-tashi maza tashi nace".
tafaÉ—a tana nuna min kofa da babbuga hannun ta,
da kyar na mike tsaye ina cigaba da kuka zuciyata nayi min wani irin mugun zafi,
Na rayawa rai na
tabbas idan nafi bakin titi kan kwalbatin da na zauna ranar da nashigo garin nan zan koma, har idan wani yazo yace na bishi zai bani makwanci da abin ci zan bishi,
to menene am fanin rayuwa ta yanzu ratuwa ta bata da wani am fani yanzu.
idanuna na rumtse da karfi jin bugun zuciya ta ya tsanan ta,a duk san da zuciya ta tafara bijiro min da irin waɗan nan tunanin sai magana ta da Inna na karshe yashiga yimin yawo cikin ƙwaƙwalwa,
"kada rayuwa tajuya miki baya ki mance da uban gijin ki".
ƙwaƙwalwa ta tarika amsa kuwwa da wannan kalmar, sai nashiga nanata kalmar innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.