Hamdah Littafi Na 2 Complete Hausa Novel
Reading file: HAMDAH part 2 complete.txt
Chapter 32 of 35
Washegari bayan mun dawo daga masallaci muka tadda an cike mana parlour da breakfast kalolin abinci iri-iri irin na gida Nigeria da kuma irin na nan kasar Saudi,
bayan munci munsha mukayi su wanka, aka kuma É—iban mu da sojoji jama'a sai gamu a fadar Saudi,
Ya ilahi ya lillahi na ga karrama wa naga karamci daga gurin larabawa, gaskiya larabawa akwaisu da karrama wa,
nan da nan ina za'a saka akarika yi da mu tamkar mu wasu ne, anawani kafa-kafa da mu.
Nan da nan aka cike mu da kayan cime-cime irin na larabawa....★
Bayan maganganun da ya gudana sakanin fadar Saudi da jagororin kasar mu da shugaban kasar mu yahaÉ—o mu da su,
nan fadar ta bukaci ganin Diamond É—in,
nan Bappa ya ciro sa cikin lajuhu wan da suke É—aure cikin laida ya mikawa É—aya daga cikin jagororin mu,
kana shikuma ya mikawa wani na kusa da shi sannan shi kuma yamika wa da dukkan alamu hukuma ne, ya karɓa kana ya taka zuwa sakiyar katafaren parlour'n saman table ɗin dake gaban wani farin dattijon balarabe yana zaune cikin kamala da dattako fuskarsa ɗauke da annuri,
ya aje laidar, tare da yin magana cikin harshen larabci.
shugaban shima yayi magana cikin harshen larabci da sauri wani da ke zaune a kasa kusa da kafar sa ya mike ya shinfiÉ—a wani farin gyalle kan table É—in kana yashiga kunce laidar,
ya juye Lu'ulu'u'n kan farin gyallen.
wani dake tsaye taÉ—an can gefe rike da wani É—an karamin a kwati ya maso da sauri tare da buÉ—e É—an karamin a kwatin,
yaciro wani na'ura kana yamaso kusa da table É—in,
ya É—aura na'urar kan Lu'ulu'u'n nan na'urar ta kawo haske tare da bada É—an sauti, idanun mutumin tar a kan na'urar, yaÉ—au mintuna da É—an dama kana yaÉ—ago,
cikin garshen larabci yayiwa wan da nafi tunanin shene shugaban magana,
kai ya jinjina tare da duban mu da murmushi É—auke a kan fuskar sa,kasan cewar bama jin bama jin larabci shima bayajin yaren mu, sai ya juya cikin harshen turanci yake magana,
"To a binciken da akayi yanuna wannan asalin *LU'ULU'U* ne muna tayaku murna".
yafaÉ—a fuskarsa É—auke da yelwataccen murmushi,
ai ko gaba É—aya gurin yakace me da hayaniya kowa yana faÉ—ar albarkacin bakin sa, sai faÉ—i ake wai wanene yasamo Diamond kuma wai a Nigeria.
mutanen saudi suke maganar, nan jagororin mu suka nuna ni, nan aka rika nuna Ni a na faÉ—in nice nasamo diamond É—in, sai kawai nadawo abun kallo, sai nuna ni ake wasu kam ma sai sun zo har kusa dani suna tayani murna,
wasu cikin harshen larabci suke magana sai dai bana fahimtar su gara waÉ—an da suke magana cikin harshen turanci suma É—in dakyar sabo da harshen su yanuna da Larabci turancin nasu da kyar nake iya ganewa.
nawo abun kallo har hotuna sukarin ka É—aukawa dani, wani zaizo kawai yatsaya yaÉ—auki hoto da ni,
mutane suka rika shigowa suka rika kallo na ni da yarana suka rika É—aukar su Naseem da Nasmah,suka rika magana cikin harshen larabci idan suka juya da turanci ne nake É—an fahimtar su,
sukayi ta yabawa yaran da kokari da gararabba da sukayi a bakin ruwa kafin mu samo Diamond É—in,
hatta shugaban sai da ya jinjina min.
nan da nan ya umurta aje banki a kawo kuÉ—i, muna nan zaune har waÉ—an da sukaje kawo kuÉ—in suka dawo aka rika shiga da gana masgo-masgo cike tam-tam da kuÉ—i, aka tarasu a tsakiyar parlour'n.
ido na ware cike da tsananin mamakin ganin yan da ake buÉ—e gana masgo É—in ana ciro kuÉ—i a ciki, kuÉ—i irin na kasar su.
"Sai kace kasa ko kuÉ—in ganye, to me zamuyi da wannan kuÉ—in?".
nafaÉ—a a fili har sai da Mahmoud dake kusa da ni yajuyo ya kalleni,
wasu larabawa ne suka shigo da sallama,in da shi shugaban yayi maga da harshen da muke ganewa wato turanci yake cewa sune masa na farashin Lu'ulu'u, nan suka ƙiyasta kuɗin Lu'ulu'u'n batare da ɓata lokaci ba.
nan da nan aka fara zuba kuÉ—in cikin na'urorin kirga kuÉ—i da suka kai guda goma, wan da duk da su akazo daga banki da kuma ma ai katan bankin. bayan an shafi tsawon awanni ana kirga kuÉ—in
masana farashin Lu'ulu'u' sukayi magana da shugaban,
kuma umurtar su yayi a koma a karo kuÉ—in dan basukai kuÉ—in Lu'ulu'u'n ba,
wannan karon har da zinari aka haÉ—o.
aka rika kirga kuÉ—in duk gana masgon da aka kirga kuÉ—in cikin sa sai a maida kuÉ—in ciki a rufe a kuma zubuta a dadin kuÉ—in cikin sa,haka akayi tayi anayi ana rubutawa.
ni dai ido na zubawa sarautar Allah ni ban ma iya kirga tulin gana masgo É—in da suketa tura kuÉ—i ciki kamar takardu ba,har naji na gaji tamkar nice na'urar dake kirga kuÉ—in, da mutanen da suketa sakawa cikin gana masgo É—in.
bayan da aka gama kirga kuÉ—in a ka jibgesu a sakiyar parlour'n haÉ—e da
gwala-gwalai da sauransu....
Wannan dattijon balaraben da ke bada umurnin duk abun da za'a yi, yayi gyaran murya tare da nuna kuÉ—in kana yasoma magana cikin harshen turanci,
"Wannan shine kuÉ—in Lu'ulu'u'n".
nan kuma ya bukaci a kira masa shugaban kasar Nigeria,
cikin hanzari na kusa da shi yaÉ—aga waya ya danna kiran lambar shugaban kasar Nigeria,kana ya haÉ—a shi da shi,
nan yake sanar masa an ƙiyasta kuɗin Lu'ulu'u'n sannan kuma gashi an kirge shi, nan shugaban kasar mu yabukaci a haɗa shi da Bappa,yace yaya za'ayi da kuɗin,
Bappa yace kawai a sashi a sanunun banki dan bamusan yanda zamuyi da wannan kuÉ—in ba.
shugaban kasar mu ya turo da number account É—in da za'a saka kuÉ—in ciki.
nan shugaban yabada umurnin a tafi da kuÉ—in banki,
nan da nan aka fara fita da kuÉ—in,
a ka kwashe su zuwa banki,
a ka zuba su cikin account ɗin da shugaban kasar mu yabada na bankuna daban-daban.....★
masauki a ka kuma mana acikin masarautar, kwanan mu uku a gurin naga halacci iya halacci, nadawo abun kallo har daga waje ana zuwa kallo na duk wan da yazo kuwa sai yayi hoto da ni.
har nayi kawaye Æ´an matan larabawa Æ´an cikin masarauta.
idan naji suna larabci sai nace su koya min, nace an ya ma kuwa zan iya?, sai suce zan iya babu wuya.....★
Acan cikin garin Bauchi kuwa, zaune Ya SALEEM da Na'ima suke a parlour'n sa........!★
mommyn Twins ce
Suna zaune cikin parlour'n Ya SALEEM,
yayin da shi Ya SALEEM ke zaune saman 1str ya tasa system a gaba yana ta faman latsawa,
Na'ima ko na kwance saman doguwar kujera, lodin yankakkun Apple da kankana da abarbane cikin plt a kan table É—in da ke gaban ta,
daga kwancen take mika hannu cikin plt É—in tana É—ibar yankakkin Apple da kankanar tana kaiwa bakin ta,
yamusa fuska tayi sannan ta mike daƙyar tana cigaba da yamusa fuskar,
sai kuma ta mike da sauri ta nufi toilet dake nan cikin parlour'n, tazubar da yawon da ta tarashi cikin bakin ta kana tajuyo a hankali,
É—agowa Ya SALEEM yayi yana binta da kallo, da kyar take É—aga kafa, tarike kugu da duka hannayenta tana wani tafiya da kyar, ta dawo gurin zaman ta tana wani yamusa fuska,
bin ta da kallo yake har ta zauna ,
zaman sa yaÉ—an gyara yakuma duban ta tare da faÉ—in,
"Amai kika kuma?". cike iya kirsa da makirci takuma yamusa fuska kana tace
"Banyi amai ba amma dai inajin zuciya ta na tashi sai dai nakasa yin aman sai yawu da yabi ya dame ni".
yace "Subhanallah duk kayan zakin da kike ta sha É—in na bai sa kin dai na jin aman ba?".
baki ta yamusa tace
"um to dai gashi ni dai ina jin wannan abun da nake tashan bazai sai da min aman da nake jiba".
"Oh sannu". yafaÉ—a ya juya tare da ci gaba da abun da yake.
ido ta waro a kanshi ganin ya juya cikin ko in kula da damuwar ta ya cigaba da abun da yake, a kasan ranta take faÉ—in
"Idan boka na kan tudu ya kasa juya wannan bahagon halin naka, zan kaika wa wani bokan ya juya min wannan halin ko ohon naka".
cike da kwarewa a makirci ta marairaice fuska cikin shagwaɓe murya tace
"Haba My SALEEM iya abun da zakace min kenan,sannu kawai ai yakama ta kayi wani abu nifa wlh wannan cikin yana damu na, ciki da masafaffen laulayi haka, nifa cikin nan yana bani wahala wlh ni kam gara acire shi kawai na huta".
tayi maganar ne cikin kirsa da son gano yan da yake jin son cikin a ransa.
da sauri ya juyo ya kalleta tare da faÉ—in
"What! azubar fa kikace?".
kai ta gyaɗa cikin shagwaɓa tace
"Wlh ni wannan cikin yadame ni wai ace duk abun da nace baya min daÉ—i, duk abun da naci sai na rikajin zuciya ta na tashi ni,babu abun da zanci naji daÉ—in sa kawai ni dai inaga cire sa shine samun kwanciyar hankali na".
da sauri yace
"Ke bakida hankali ne zakice azubar, cikin ne za'a zubar Na'ima?".
kai ta kawar dan ba haka taso ba, har yanzu takasa gane SALEEM duk asirin ta da makircin ta, har yanzu takasa juyashi yan da take so,
yan da taso tarika juya shi yan da take so sai dai har yanzu bata sami damar hakan ba,
duk wani makircin ta da surkullen ta kuwa,
bata taɓa iya juya SALEEM son ranta.
sai dai wani lokacin takan É—an sami yadda take so daga gurin sa sai dai ba duka yan da take bukata ba.
a yanzu takan É—an sami nuna kuwalar sa a gare ta,
uwa uba bukatar sa yanzu baya barin sa a jikin sa, kullum sai ya sauke sa a mararta, hakan ba kara min da É—i yake mata ba dan yanzu ma da kan sa yake niman ta, akasin da da sai ta nima da kanta.
A son ta tana so ya nuna mata kulawa fiye da kulawar da yake nunawa HAMDAH a da,
sai dai ina duk yan da taso hakan bai samuba, ko kwatan-kwatan yan da yake nuna kulawa da rawan kafa lokacin da HAMDAH take da ciki, da kafin ma samun cikin,
baya yi mata.
system É—in gaban sa yaÉ—an ture kana yamiko hannunsa yaÉ—an shafi gefen fuskarta yana faÉ—in
"Sorry da ma ai an ce duk mai ciki haka take ji har fiye ma da hakan, so hakuri kawai zakiyi har Allah yaraba ku lafiya, yanzu kam ma ai kin kusa hutawa tun da yashiga wata huÉ—u kenan,
kinga ko kin É—au gangarar hutawa tun da an ce wuyan ta ciki yafara kwari ne da zaran yafara girma zaka fara hutawa da laulayi,to kin ga kuwa kin kusa hutawa kenan".
rass. taji gaban kirjin ta ya buga shiru ta É—an yi tare da tafiya cikin tunani a kasan zuciyar ta.
sai kuma da sauri tadawo da kallon ta san sa jin yana faÉ—in
"Wannan cikin dai ina ga shine a ke ciwa mai bin jiki,to ina ga shima yabi jikin ki ne gashi dai har watan sa huÉ—u amma bai fara bayyana ba,wata kila in yafara girma yanuno kansa nan zaki É—an ji daÉ—i".
hannu ta mika taÉ—auki yankakken Apple takai bakin ta tana tauna cikin nuna rashin jin daÉ—in abun da take ci tace
"Ni wlh tsabar wahalar da cikin nan yake bani bansan har yashiga wata huÉ—u ba".
tayi maganar yayin da zuciyar ta ke tunano mata lallai wannan watan ne yayi dai-dai da cikin watan sa huÉ—u kenan.
murmushin gefen baki yayi kana ya mai da idanun sa kan wayar sa da ya É—auka kan hannun kuje rar da yake kai.
sannan yace
"Ai abu na jikin ki ma kina mance kwanakin sa? tun lokacin da na sami labarin cikin nake lissafin sa".
É—an dimm tayi sai kuma tayi saurin kawar da maganar da faÉ—in
"Wlh ni ina jin kwaÉ—ayin gwaten gauta, ina ga abu mai É—an É—aci-É—aci yafi gyara min baki".
"Gwaten gauta kuma to ke meye zakiyi da wani gwaten gauta?".
yayi maganar har lau idanun sa nakan wayar sa.
tace "Allah ni shi nake jin sha'awar na sha zan dai na jin bakina ba daÉ—i, kasan fa tun ranar da Raliya tayi ta kawo min na sha ranar na wuni ban zubda yawu ko amai ba,har nakuma ci abinci lafiyar Allah babu jin rashin daÉ—in nan,
gashi yan zu Raliya batanan tayi tafi bansan yaya zanyi ba,
bansan wama zai yi min in sha ba."
cikin fara gajiya da surutun ta da son sashi yawan magana da take yace
"Kiyi da kan ki mana har sai wani yamiki kafin kisha, tun da ciwon bai kwantar da ke ba kina iya tashi mai zai hana kiyi da kan ki, sai a samo miki gautar kiyi ai,
ko kuma kisa Rufa'ila tayi miki ko sauran ma'aikatan gidan".
yana gama faÉ—a ya mike tsaye yana rufe system É—in sa.
Ido tawaro tace
"Rufa'ila? Rufa'ila'r ce zata yi min girki wlh bazan ci girkin Rufa'ila ba, kawai kasa dai a yimin".
takarashe maganar tana bubbuÉ—e kofofin hanci.
da É—an mamaki yajuyo yakalleta ganin yan da tayi maganar a tsaye kana yace
"To wa kike so ya miki ni kike so naje nayi miki? babu masu girki ne a cikin gidan da sai na nemo masu yi miki?".
ganin yan da ya sauya fuska sai kuma ta shagwaɓe fuska tana faɗin
"A'a kai kuma haba dai kadai sa ayi min dan Allah my SALEEM ina so na sha".
"Wa kenan zan sa yayi mikin?".
yafaÉ—a yana kokarin barin gurin.
da sauri tace
"Dan Allah kayiwa Mamie magana dan nasan ita zatafi iya yin gwaten tun da dai abincin gargajiya ce, ita zatafi yin mai daÉ—i ma dan Allah kayi mata magana sai tayi min".
bai kuma cewa komai ba har ya juya zai bar gurin sai kuma ya ɗago wayar sa ya laluɓo lambar Mamie ya dan na kira.
bayan sun gaisa yaÉ—aura da faÉ—in
"Mamie wai Na'ima ce ke son shan gwaten gauta ko zakiyi mata".
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.