Best / Popular Hausa Novels

Hamdah Littafi Na 2 Complete Hausa Novel

Reading file: HAMDAH part 2 complete.txt

Chapter 4 of 35

Mommyn twins ce

Sauri nake kamar zan tashi sama duk da nafita daga layin unguwar amma hankali na bai kwanta ba,tafiyar nake ina ta waige-waige,sai gani nake kamar Ummi zata biyo ni.
tafiyar kawai nake batare da nasan in da zani ba kokuma sanin in da na nufa ba.
Karar ababen hawa da naji ya karaÉ—e ko ta ina shine ya dawo dani cikin hayyaci na,nayi mamakin ganin in da nake
Duk da kuwa tazarar dake sakanin unguwar mu da in da nake yanzu
wato winte.
Gefen titi na zame nashiga cikin mutanen da nagansu zazzau ne kan bence wasu ko nata harkokin gaban su.yayin da zuciya ta keta azalzala ta ji nake idan naci gaba da jan numfashi acikin garinnan tabbas zuwa anjima numfashi'n kwacewa zaiyi yatafi abun sa.
maganar da naji kusa da nine yasani É—agowa wani É—an yuniyon ne tsaye a kanmu yana faÉ—in
"Yauwa motar ku yanzu kam yacika kowa ya kawo kuÉ—in sa".
gafen da nake ya kalla kana yace
"Ƴan mata ke ma a wannan motar kike?".
tsintar kaina nayi da gyaÉ—a masa kai,yace
"To kawo kuÉ—in ki mota ta cika".
idanuna na mai da kan akwatin da ke gaba na tabbas nasan bana da ko sisi dan ban fita da ko biyar daga gida ba, hasali ma babu abun da na iya É—auka in ba wannan akwatin ba,ganin yanata amsar kuÉ—in mutane sai na kai hannuna kan zip É—in bayan akwatin ina É—an wasa da shi a raina nake faÉ—in
"To ko ince masa yakarɓi akwatin a bakin kuɗin motar ne, Ni har da kayan cikin ma in dai zasu ɗauke Ni suraba ni da garin nan".
yadda nake wasa da zip É—in sai yana É—an zugewa da mamaki nakurawa aljuhun jakar ido ganin bakin kuÉ—i ya baiyana, da sauri na idda zuge zip É—in nazaro kuÉ—in ina juyashi a hannuna naira dubu biyu sabbi dar.
tunanin ta yadda akayi kuÉ—in yashigo cikin a kwatin nake,
nan take na tuno lokacin rasuwar Inna ina zaune a cikin bedroom É—in Ummi taciro kuÉ—i cikin wardrobe zatayi aika kasuwa daga cikin kuÉ—aÉ—en dubu biyu suka zubo,nakwashe ina mika mata tafita da sauri tana faÉ—in na ajiye bari tazo,a lokacin kuwa kasan cewar ina zaune ne kusa da akwatin sai naja zip É—in a kwatin nasaka ciki kan cewar in tashigo zan cire na bata,gaba É—aya nagama mance wa a she dai ban bata ba..

Numfashi na sauke a hankali na furta
"Alhamdulillah".
dai-dai lokacin kuwa É—an yuniyon É—in yake faÉ—in
"Kawo nake".
duka kuÉ—in na mika masa sai naga ya zare dubu É—aya yakai hannu aljuhu yazaro É—ari biyu sai ya haÉ—a da dubu É—ayan nan ya mika min dubu É—aya da É—ari biyu kenan.
karɓa nayi ina juya kuɗin a hannuna "Wato kuɗin motar garin da zasu ɗari takwas kenan?".
nayi tan bayar a raina,
ganin duk wan da yabada kuÉ—i sai ya shige cikin motar dake gaban mu sai nima na mike nashige cikin motar ina rungume da akwatina.
Ina alla-alla motar ta tashi duk da kuwa bansan motar wani gari zata ba ban kuma da mu da duk inda zaije ba ni dai burina nafita a cikin garin nan, bana kaunar na buÉ—e idanuna nakuma ganina cikin garin bana kaunar narika shakar iskar garin naji na tsani garin gaba É—ayan ta.
numfashi na sauke tare da yin hamdala lokacin da motar ta hau kan titin taɗau hanyar fita daga cikin garin......★

★★★

A nan cikin garin Bauchi kuwa,
kan kace me labarin abun da ya faru yakaraÉ—e Æ´an uwa,
su Aunty Jaleela duk sun taho gidan cikin tashin hankali,
Aunty Rafee'at da yanzu isowar su ita da Dr Farooq ko jiran ya dai-dai ta parking batayi ba tafito cikin tsananin tashin hankali tanufi ciki.
Nan ta iske Æ´an gidan dukan su zaune cikin parlour'n Ummi har da wasu Æ´an uwan su,
da sauri tashigo cikin parlour'n cikin muguwar tashin hankali tana faÉ—in
"Ummi ina HAMDAH tatafi ina tasani batasan ko ina ba".
Ummi da har lokacin kwalla basu dai na zuba a idon taba takai hannu ta share wasu zafafan hawaye,bata iya ce komai ba
sai kwallar da ta cigaba da sharewa.
cikin share kwalla goggo Hauwa tace
"Tatafi bamu san in da ta tafi ba".
tafaÉ—a tana sharce hanci.
Kuka Aunty Rafee'at ta sake da karfi cikin muryar kuka sosai tace
"Wlh cikin Ya SALEEM ne wlh cikin sane wlh na shaida HAMDAH bazata taɓa ai kata abun da ake zargin ta ai kata ba".
da sauri
tayi gun Dr Farooq da yanzu yashigo tariko hannunsa tare da faÉ—in
"Wlh Allah cikin nan na Ya SALEEM ne Abba'n Adeel kai shai da ne".
sai kuma tasaki hannunsa tayi gun goggo Hauwa tace
"Goggo Hauwa kema shai da ce Ya SALEEM shine mutum na farko da ya taɓa sanin ta ɗiya mace,wlh na rantse HAMDAH bata ai kata abun da ake zargi ba wlh sharri a ke mata".
takarasa maganar cikin shashsheka..
Aunty Jaleela ma nagefen Ummi takasa cewa komai sai kwallar da take ta share wa,
parlour'n yayi shiru cike da jimami da sautin kukan Aunty Rafee'at......★

Ido na zuba wa hanyar da bansan na wani gari bane,duk tafiyar da motar yake gani nake baya sauri,
munyi tafiyar da yakai na a wa 2,wata matar da take gefe na tabuÉ—e murya tace
"Direba nakusa sauka ni a Narkuta zan sauka".
direban ya amsa mata da to.
tafiya kaÉ—an muka kara muka iso wani gari mai kyau da tsaruwa a dai-dai farkon shiga garin motar ta tsaya direban yace
"Mun iso masu sauka a Narkuta".
kasan cewar Ni ina ta bakin kofa ne yasa dole sai da na sauka kafin matar tafita,
maganar direban naji a sama
"Ƴan mata kema a nan zaki sauka ne".
firgigit na dawo daga tunani da natafi sai kawai na sinci kai na da gyaÉ—a masa kai,
"No wahala"
yafaÉ—a tare da jan motar sa yayi gaba.

ido na baza kan titin kowa na ta harkokin gaban sa,
a sannu na masa gefe kan wani kwalbati da ya kasan ce hanyar shiga wani layi na zau na, tare da aje akwati na a gabana,
yayin da masu a dai-dai ta da mashina suke ta tsayuwa suna tan bayana ina zani,wasu nace musu babu wasu kuma nayi musu shiru.
najima sosai zaune a gurin.
Har guri yafara rufawa yayin da ababen hawa suka yawaita kowa yana kokarin konawa gida,
Ina nan zaune a kan kwalbatin,
shafa cikina da naji yana É—an motsa wa nayi yanzu kam naji ina jin yunwa akasin É—azu da banajin ko É—igon yunwa,duk da wunin yau bansa ko ruwa a baki na ba, dan ko breakfast banyi ba.
a hankali na mike nanufi gurin wata mai sai da abinci da nake hango ta can gefen titin,kuÉ—i na mika mata nace
"Abani abinci".
sai kuma na dubawa kuÉ—in da nake mika mata ido da mamaki ganin naira É—ari biyu ne bayan nasan dubu É—aya da É—ari biyu ne a hannuna,
waige-waigen gefe da gefe na nayi ko dubu É—ayan yafaÉ—i kasa ne amma babu ko alamar sa.
maganar
matar naji tana faÉ—in
"Babu abincin 200".
nace "To abani drink".
ta miko min gora na amsa na juya a hankali hanyar da na bi nabaza ido ko zanga kuÉ—in amma har na'isa in da akwatina yake babu alamar sa,
kurɓa uku zuwa huɗu nayi wa drink ɗin sai naji cikina na murɗa ni sai na rufe gorar,
A sannu na É—ago jin karar mota ta tsaya daf da Ni dai-dai lokacin aka zuge glass É—in motar kasa, wani matashi ne zaune a cikin motar sai busa sigari yake,yayin da wani ke zaune a gefen sa,kai na na kawar da sauri jin hayakin sigarin yana isoni, matashin ya dubi abokin tafiyar nasa yace
"Maye wannan fa ta haÉ—u musala zata rage mana dare sosai".
Kai ya gyaÉ—a cikin cakewa da kayan mayen da yake ta shaka.
matashin ya dubeni yace
"Ya Æ´anmata shigo muje mana mubaki masau ki muhuta kihuta sosai".
yafaɗa yana latso laɓɓan sa,
nan take maganganu Inna da tarika yimin lokacin tana kwance a gadon asibiti suka fara yimin yawo a ƙwaƙwalwa ta.
rumtse idonuna nayi da karfi,sai na
kuma kawar da kai na batare da nako kalle in da suke ba bare na furta wani abun.
É—ayan dake zaune gefen mai zaman banza yaleko tare da É—aga murya yace
"Zazzafa ce fa nawa za'a biya ki?".
nan ma banko juyo ba dan na fahimci Æ´an iska ne inajin É—ayan yana faÉ—in
"Muje gaba akwai irin su, biyu zamu É—iba dan mu huta sosai".
É—ayan kuma yace
"Ta haÉ—u fa duk da tana cikin hijabi".
"Shiyasa take taja mana aji manya masu zaren take so muje kawai".
haka sukayi ta magan ganunsu sukaja motar su sukayi gaba.
numfashi na sauke tare da cigaba da ambaton sunan Allah azuciya ta da nake,
tafiyar su dakamar 5mn wata mota takuma tsayuwa gefe na wannan karon sai da naji gaban kirji na ya faÉ—i,da sauri na juyo jin muryar wan da yake cikin matar
"Shigo na sauke ki a gida mana da alama dai kin rasa abun hawa ne".
saurayi ne shima sai dai baiyi kama da irin waÉ—an can da suka wucen ba yana zaune cikin kamala, murmushi yayi min kana yakuma faÉ—in
"Naga kin jima zaune a nan da alama dai jira kike azo daga gida a É—auke ki in bazaki damu ba muje na sau keki a gidan".
da sauri na girgiza kaina tare da faÉ—in
"A'a Nagode kaje kawai".
kai ya jinjina yadube ni da kyau tare da faÉ—in
"To in ma bazaki shiga motata ba to ina mai baki shawara daki nimi mai abun hawa kihau ki tafi gida".
murmushi yayi cikin maganar da yake kana yaci gaba
"Duk wani wanda yagan ki zaune a nan to zai yi miki kallo irin kallon da waÉ—an can samarin da suka yi miki yanzu suka wuce,gashi dai duk mai tunani idan ya ganki bakiyi kama da irin mata masu tallen kansu ba duk da dai basa da kama,
bai kamata kici gaba da jira a kan wannan hanyar ba dan yana da haÉ—ari sosai,
akwai matasa marasa É—a'a su basa jiran amincewar mace ko kotaso ko kar taso zasu É—auke ta da karfi su kai ta É—aki su kulle idan suka gama kwanakin da zasu yi dake suje su yasar da ke,a irin wannan lokaci suke fitowa, babu kuma wan da ya isa ya dakatar da su domin Æ´aÆ´an manya ne,zai fi miki kyau kitari abin hawa kitafi gida".
ido na waro ina kallon sa har yakai karshen maganar yayin da tsoro ya lulluɓeni sai nashiga gyaɗa masa masa kai,shiko murmushi yakuma kana yace
"Ko za'a bani aron number?".
mikewa tsaye nayi
cike da jin tsoron da ya É—arsa min a zuciya na bashi baya ina ta É—an kalle-kalle.
ina jin sa yakuma maimaita tan bayar sa ganin bani da niyyar amsa shi sai yaja motar sa yayi gaba.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.