Best / Popular Hausa Novels

Hamdah Littafi Na 2 Complete Hausa Novel

Reading file: HAMDAH part 2 complete.txt

Chapter 25 of 35

Nayi ta yunkurin tashi na kasa da kyar na kai É—aya hannuna na kunce zanin goyon ta kwanta gefe tana cigaba da tsala ihu duk jikin ta ya kwakkwar jane,
hannuna da na faÉ—i a kansa na É—agosa da kyar kana da kyar na iya mike wa zaune.
yayin da hannun da na faÉ—i a kansan ke min wani irin zugi da raÉ—aÉ—i,
da kyar na yunkura na mike ina É—ingishi nazo gun da Naseem yake kife a kasa yana ihu,
na zauna na É—ago shi da É—aya hannuna mai lafiyar,
nashiga kakkaɓe masa jikin sa ina jijji gashi,
shima duk ya kukkuje a.
Nasmah ta rarrafo tana kuka ta zo in da muke na janyo ta na cigaba da rarrashin su,
duk abun da nake cikin dauriya kawai nake dan nima duk jikina a kukkuje yake,zafin raunukan jikina bai kai na hannun da na faÉ—i a kan sa ba.
duk raunukan jikin yaran sai jini yake fidda wa.
rungume su na yi tare da fashewa da kukan azabar da hannuna yake min, ko matsi nayi da hannun sai naji zafin har cikin raina.

Mun jima zaune agurin jin tamkar karamin zafin ake a hankali na lallaɓa da kyar na mike,
na kamo Naseem da hannun na mai lafiyar na É—agoshi da kyar na iya goya shi, dan shi yafi Nasmah jin ciwo.
ina matse idanuna hawaye na zuba cikin jin azaba,
sannan na É—auki Nasmah na rike ta
a ɓarin hannuna mai lafiyar,
gefe na na waiga in da É—ankwali na dana É—aura musu duwatsun wasan su yafaÉ—i can gefe shima na isa na É—au ka da hannuna mai ciwon,
Jin wani irin zugi da hannun yayi min sai na sake É—ankwalin kasa,
na juya ina faÉ—in
"Naseem Nasmah bazan iya É—auka muku abun wasan kuba hannuna yana min ciwo idan na samu wasu zan É—iba muku a hanya".
a sannu na soma tafiya ina É—aga kafata ahankali-ahankali,
sai kuma na tsaya a raina nake faÉ—in
"To yanzu idan na tafi na bar É—ankwali na anan a ina zan samu abun da zan É—aura a kaina idan na cire hijabi na na rufe su Nasmah da shi?".
nayiwa kai na tan bayar,
idanuna na rumtsa nasan idan na É—auka hannuna zai min zafi.
a raina nake ayyana na kunce Duwatsun na zubdasu sai na É—auki É—an kwalina nasan shi bazai min nauyi ba.
na koma in da yake na É—auki É—an kwalin ina kokarin kuncewa nayi nayi na kunce na kasa saboda da hannu mai ciwon ne jin hakan yana daÉ—a kara ramin zugin hannuna ne sai na bari.
na zaunar da Nasmah a kasa Sannan naÉ—an kunce zanin goyo na cusa É—an kwalin sakanin bayana da jikin Naseem,sai na mayar na É—aura,
kana na É—auki Nasmah muka fara tafiya a hankali.
dan yanzu bana iya tafiya da sauri dan duk jikina ciwo yake min ga su Naseem har yanzu suna ta kuka.

Idan muka É—an tafi kaÉ—an sai na sauke su na huta kana muku ma ci gaba,
Abun mamaki munyi tafiya mai nisa amma har lokacin bamu iso in da shanun nan suke ba, daga can saman tudun da muka gangaro da nake hango su banyi zaton zanyi irin wannan tafiya mai ni haka ba kafin na iso su.
a haka dai nayi ta tafiya har na iso kusa da su,
wasu matasa Fulani ne guda biyu suke kiwon shanun,suna tsaye can gefe sai dai na lura basu san da zuwa na gurin ba duk da dai sakanin mu da É—an tazara,
a sannu na isa gindin wata bishiya na zauna kana na sauke su Naseem,
nayita rarrashin su Nasmah har sukayi bacci.
muna nan zaune a gurin har yamma sai sannan makiyayan nan suka fara kaÉ—a shanukan,sunayin gaba,
Ganin haka na mike da sauri na É—auki su Nasmah narika bin bayan su duk inda sukayi ina biye da su,idan suka tsaya na tsaya idan suka cigaba da tafiya nima na bisu.
haka dai mukayi ta tafiya har naji badaÉ—i gashi babu halin nace zan tsaya na huta sutafi su barni,
tafiyar nake ina matsar ƙwalla sabo da tsaɓar gajiya gajikina da ya daɗa kara yin tsami,
muna nan muna tafiya har guri yafara rufawa.
can naga shanun sun tsaya kana a sannu naga sunayin kwana can na hangi bukkoki gefen bukkar cikin wani gurin da a ka zagaye shanun suka shiga, nan makiyayan suka fara É—aure su,
a sannu na karaso gurin sai na tsaya gefe da garken shanun ina ta raba ido,
Fulani mazaunan gurin sunata harkokin su wasu daga kusurwa daban-daban suna ta É—aure shanukan su da alama suma yanzu suka dawo daga kiwo,
numfashi na sauke tare da yin murmushi cikin zubda ƙwalla gani na acikin mutane wan da nagama fidda sammanin yiwuwar hakan,
a hankali na tako na tsaya kusa da garken shanun....

wani dattijo ne yafito daga cikin wani gidan da ke gefe da garken shanun,
kana yashiga cikin shanun cikin girmama wa da ladabi matasan makiyayan nan suka shiga gai dashi cikin girmamawa,ya amsa cikin sakin fuska
kana yashiga tayasu É—aure shanun.
jijjiga Naseem da yake ta musu-musu a bayana nashiga yi dan nasan yagaji ko kuma jikin sa ya masa tsami dan yabugu sosai,ina matse ido hawaye na zuba,
tuni Nasmah ma ta saki kuka, sai na cigaba da gargiza su ina hawaye,
yan da nake girgiza sun hakan yasa hannuna ke girgiza zafi har cikin raina.
da sauri dattijon nan yafito daga cikin garken shanu yana É—an waige-waige da alama dai kukan yaran yaji yasashi fitowa duba da yan da yake ta É—an waige-waige,
nan idanunsa ya sauka kanmu da mamaki yake kallona kana yace
"Ke wanene me kike yi a na?".
yayi maganar idanunsa a kaina cikin hausar sa da bata tsaya ba,
banyi magana ba sai masar ƙwalla nake,
"Ke wanene nace me yasa mi yaron?".
cikin zubda ƙwalla nace
"MunfaÉ—i ne shine yaji ciwo kuma yunwa suke ji".
"Yunwa?".
yafaÉ—a yana kallo na".
na gyaÉ—a kai na alamar Eh, yaÉ—an yi shiru yana kallona,
kana ya kalli su Naseem da Nasmah da kyau sannan yace
"Garin yaya kuka faÉ—i haÉ—arin mota ne ina zaku je??".
yajero min tambayar
nace
"Acan kan tudu muka faÉ—i kuma Yola zamu".
shiru yakumayi alamar nazari kana yajuya tare da faÉ—in
"Kubiyo ni".
ai ko da sauri na bi bayan sa.
ya shiga gidan tun daga bakin kofa yake faÉ—in
"Sumaye Sumaye Sumaye".
wata yarin yar dake zaune a tsakar gidan ta mike tana faÉ—in
"Inna wuro Bappa na kira".
wata dattijo war mata tafito daga cikin bukko da sauri tana amsa kiran sa,
tare da faÉ—in
"Gani nan Malam".
yace
"Zo ga wani bakuwa nan tazo kuma wai yaron ta ya faÉ—i a kasa kuma yana jin yunwa bashi abinci yaci".
tace
"Subhanallahi kawo shi nan mugani garin yaya?".
namatso in da take tana kokarin karɓar Naseem dake ta zandara ihu, garin cirosa sa a bayana sai ta bige min hannun,
yarfe hannun nayi tare da faÉ—in
"Wayyo Allah hannuna".
tace "Ayya Allah kam sansu ke ma hannunka na siwo ne?".
kai na gyaɗa cikin zubda ƙwalla nace
"Eh da muka faÉ—i ne nima na buga hannuna".
kallon yarinyar dake zaune a gefe tayi tace
"Zo Mero kikarɓa mata yaron hannun ta".
yarin yar ta matso da sauri ta karɓi Nasmah,
tace
"La Inna wuro itama taji ciwo".
Inna wuro tace
"Oh wani irin faÉ—uwa ne haka sai kace haÉ—arin mota".
tafaÉ—a tana roko hannuna tare da cigaba da faÉ—in
"Ko dai haÉ—arin mota kukayi ne".
yarfe É—aya hannun nayi nace
"Wayyo Allah na".
Inna wuro tace
"Malam itama ta buga hannun ta inaga tayi targaÉ—e a hannun".
"Nima dai haka nace kamar wan da suka faÉ—i a mota".
yamatso kusa da ni yana faÉ—in
"Naga hannun".
naÉ—ago haka na mika masa yarike yana É—an jujjuyawa,
rumtsa idanuna nayi da karfi ina faÉ—in
"Wayyo Allah wayyo Allah".
yace "Sannu kinyi targaÉ—e ne".
sai ya saki hannun
"Bari nakawo magani nasha maku".
Bappa yafaÉ—a yana shigewa cikin bukko,
ni dai yarfe hannun narika yi ina matsar ƙwalla.
yana shiga yafito da wasu robobin mai guda biyu, ya dawo in da nake.
Inna wuro tayi sauri ta É—auko taburma ta shin fiÉ—a tace na zauna,
na zauna shiko a kan kujera Æ´ar tsuguno ya zauna kana yaruko hannuna yaja yaja yajijjiga shi da É—an karfi, kara na sake cikin jin azaba har cikin kokon zuciya ta, ina shushshure kafafu kasa kamar zan saki fitsari a jikina.
kana yabuÉ—e É—aya daga cikin roban mai daya fito da su ya lakato maganin ciki yashafa min a hannun da tuni yahaÉ—a zufa,kana ya saki hannun yana yimin sannu.
Inna wuro tace
"Sannu zakiji daÉ—i har kiyi bacci".
kai kawai na gyaɗa mata ina matsar ƙwalla, na matsa baya na jingina da jikin garu ina rike da hannun da ɗaya hannuna...
ya karɓi Naseem yashafa masa maganin dake cikin ɗaya robar a duk kanin ciwukan jikin sa,
yana yi yana É—an mammatsa jikin sa har ya gangaro kasan kafar sa ai ko yana rike guiwar kafar sa yakara sautin kukan sa yana kankame jikin sa,
kafar yarike da kyau yaja sai ga kafar tayi kass,
Maganin da yashafa min a hannu yashafa masa a kafar yana faÉ—in
"Gocewar kashi ne".
kana ya mikawa Inna wuro shi ta karɓe shi tana girgiza shi da yi masa sannu,
nan ya karɓi Nasmah itama ya sha fa mata bayan yagama dudduba jikin ta ko itama da buguwa ko gocewar kashin a jikin ta,sai dai ita ba a samu gocewar kashin ba sai dai buguwar kawai...

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.