Best / Popular Hausa Novels

Hamdah Littafi Na 2 Complete Hausa Novel

Reading file: HAMDAH part 2 complete.txt

Chapter 3 of 35

Abba ma sai da ya girgiza da jin abun da nafaÉ—a da sauri ya juya yakoma É—aki.
Number Ya SALEEM yakira yace yazo yanzu-yanzu yana niman sa.
a parlour kuwa zaunar dani goggo Hauwa tayi suma suka zazzauna kowa jikin sa yagama sanyi,a hankali naci gaba da kuka na.
batare da ɓata lokaci ba motar sa yashigo gidan
duk muna zaune a parlour har da Abba yayi sallama yashigo,
gefe da Abba yasamu guri yazauna a kasa kana yashiga gai da Abba da su Ummi, Abba ya nisa tare da gyaran murya yace
"SALEEM wai me ke faruwa ne tashigo ta É—agawa mutane hankali da koke-koke da wasu magan ganun da babu daÉ—in ji wai kace ka haramta kanka gare ta da kuma ciki wai ba naka bane ko mene?".
sautin kuka na kuma karawa jin yadda zuciya ta ke tafasa, sawa Abba ya buga min yace
"Zaki rufawa mutane bakine ko sai nazo gun kiyi Mai dalili!".
kai na na jingina da kafar goggo Hauwa ina kukan a hankali.
muskutawa yayi kana yaÉ—an yi kasa da kansa yace.
"Eh Abba gaskiya ne abun da tafaÉ—a".
basu Ummi kaÉ—ai ba hatta Abba sai da ya girgiza, goggo Hauwa ta waro ido tare da buga kirji tace
"Kai SALEEM kan ka É—aya kuwa kasan abun da kake faÉ—a kuwa?".
Abba ya gyara zama kana yace
"To me yafaru da wannan yanke hukunci haka? An san aure abune mai rai wata kila karshen rayuwar sa kenan, shikuma cikin taya akayi yazamo ba naka ba tana da wani mijin bayan kaine??".
Abba yafaÉ—a yana duban sa dason jin ba'asi dan shi kan sa yashiga É—imuwa matuka...

Kafafun sa ya tanƙwashe kana yayi kasa da kansa yace
"Kayi hakuri Abba da abun da zan faÉ—a".
da sauri na É—ago kai na yayin da naji kukan ya tsaya cak na zuba masa ido babu ko kiftawa.
sai ya kuma yin kasa da kansa kana yacigaba da faÉ—in
"Lokacin da nayi tafi
naje nayi wata 1 ranar da na bar garin nan tana cikin yanayin rashin sarki,ranar da na dawo kuma na tadda ta bata da lafiya bayan da na kai ta asibiti kuma likita ya tabbatar da tana É—auke da cikin wata É—aya gatanan kuma ita shai da ce".
YafaÉ—a yana nuna Ni da hannu.
Salati goggo Hauwa ta farka tace
"Amma lallai SALEEM a gaishe ka sabo da haka zakace ka haramta kan ka da ita sannan kuma ciki ba naka ba? zancen banza kenan mata nawa suke da ciki kuma suna jinin al'ada ai ba akan ta aka soma ba in ba ka sani ba kasani".
Maganar sa ce yasa goggo Hauwa yin shiru da nata maganar cikin É—inbin mamaki kowa ke kallon sa
yayin da shiko ya karkata hankalin sa gurin Abba da son bashi amsar tambayar da yakuma yi mishi yanzu kan cewa da yayi mishi "Dalilin ka kenan?".
kan sa ya girgiza kana yace
"Bayan tafiya ta akwai wani wan da yake zuwa gurin ta É—azu ma ai katan gida na suka tabbatar min da haka".
wani irin zabura su Ummi suka yi suka haÉ—a baki wajen cewa
"Wani yake zuwa gurin ta??".
Abba kam hular kansa ya cire yashiga yin fifita da shi,niko ido na daÉ—a kura masa kamar tv...

Zaman sa ya gyara kana yasoma sanar musu duk abun da baba Mai gadi da Habu mai shara da Sani direver suka sanar masa, kana ya É—aura da ganin da Na'ima tace tayi mana a kan gado da wan da Habu shima yace yagani.
salati parlour'n ya kaure da shi tuni hawaye yashiga wanke fuskar Ummi,
cikin takai ci Abba ya dube ni yana faÉ—in
"Abun da zaki saka mana da shi kenan ki ɓata mana family kin tozarta shi tozarci mafi muni me kika nema kika rasa a rayu HAMDAH me muka gaza miki wacce gatace bamu baki ba sakayyar da zaki yi mana kenan!".
kai narika girgizawa hawaye na zuba a idona na buÉ—e baki zanyi magana Abba ya daka min tsawa.
kana ya dubi Ya SALEEM yace
"Tashi ka kaje hukuncin da ka yanke shine dai-dai ta haramta a gare ka kuwa tabbas".
a sannu ya mike yafita da sauri na mike tsaye kamar mai tashin aljanu na bi bayan sa kafin na iso shi har ya isa farfajiyar gida da gudu nasha gaban san sa na ruko hannunsa na É—aura kan cikina cikin muryar kuka da fizgar numfashi na da nake ji kamar zai É—auke, ina kallon fuskarsa nace
"Ya SALEEM Ya SALEEM wlh abun da ke cikin kinan nan naka ne kai ne uban sa, wlh babu wani na mijin da ya taɓa rike koda bakin mayafi nane bare har ya sanni ƴa mace bayan kai Ya SALEEM ɗan kane cikin kane wlh babu wani wan da yake zuwa guri na".
fizge hannunsa yayi kana ya dube ni da kyau yace
"Kada ki sake dan ganta abun da ke cikin ki da Ni ni ba uban sa bane, ke kinsan uban sa ai jeki haifa ki kai masa abunsa in yaso ki kashe shi tun a ciki tun kafin ya fito duniya a san halin da kike ciki, asan wacece ke mutum a fuska kawai,
In dai irin wannan É—an ne zai zamo nawa har abada bana so!".
yana kaiwa nan ya juya yashige motar sa yafice a gidan..

Dur kushewa nayi a gurin ina wani irin kuka mai tsuma rai, na daÉ—e durkushe jin jiri na fisgata na mike da kyar na koma parlour in da su Ummi suke har lokacin Ummi na hawaye sai dai ta kasa furta ko da kalma É—aya ce, goggo Hauwa da Aunty Halima sunyi jugum.
ina saka kafata cikin parlour'n Abba ya takatar da ni da faÉ—in
"Kada ki sake ki tako cikin parlour'n nan maza ki tafi kiyi nesa da mu domin zama da irin ki acikin family tamkar rugujewar ahali ce,
kisani idan zuciya ta tabuga to kece sila kuma bazan taɓa yafe miki ba,bana kaunar nakuma buɗe idanuna na ganki fita min a gida kitafi duk inda zakije amma ki sani ban yarda kije gidan ɗaya daga cikin dangi naba har in dangi nane fita min a gida nace!".
yafaÉ—a cikin karaji baya nashiga ja inajin maganar Abba tamkar saukar ruwan dalma a zuciya ta.
mikewa Ummi tayi hawaye taf idon ta tace
"Ina zataje Abba'n Fauzan ka bata lasisin shiga duniya kenan? bata da in da yafi nan in kuma kace ta tafi to sai dai mutafi tare".
Ummi ta nufo ni tana cigaba da faÉ—in
"ÆŠiyar ka mace zaka jefawa duniya sai dai in mutafi tare".
cikin fushi Abba yace
"Fatima idan kika fita daga cikin parlour'n nan to ki tabbata nayafe ki".
ido na waro cikin tsananin tashin hankali nashiga girgiza kai da karfi nace
"Ummi dan Allah dan Allah karki fita Ummi ki koma na rokeki Abba kayi hakuri ni zan tafi".
ganin tana ta daÉ—a matsoni yasani tahowa da gudu na rungume ta cikin muryar kuka nacigaba da faÉ—in
"Ummi ki koma dan Allah karki fita".
sai kuma na zame jikina da sauri na saka hannuna biyu na share hawaye na nakuma kai hannu kan fuskar ta nashare mata hawaye tare da yin wani murmushi ina duban ta yayin da wasu zafafan hawaye suka zubo min nace
"Ummi duk inda nake a faɗin duniyar nan ko a muce ko a raye addu'ar ki itace zata zame min garkuwa in nazamo silar fitar ki a gidan nan bazan taɓa yafewa kai na ba".
Najuya na dubi su goggo Hauwa da tuni suma hawaye yagama wanke musu fuska na haÉ—e hannaye na biyu nace
"Dan Allah goggo Hauwa Aunty Halima kada kubar Ummi na ta fita dan Allah".
da sauri na juya nafita a cikin parlour'n na É—au jakata dana yar dashi a tsakar gidan da sauri na nufi kofar fita ina waige ko Ummi na biyo ni.
sauri na rika yi har na fita daga layin mu.......!★

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.