Hamdah Littafi Na 2 Complete Hausa Novel
Reading file: HAMDAH part 2 complete.txt
Chapter 7 of 35
a hankali na kai hannu zan buÉ—e labulen É—akin na fita tace
"da kata,baki da iyaye ajikin bishiya kika fito?".
juyowa nayi ido taf da kwalla nace
"A da ina dasu ayanzu kuma sun yanke alakar da kansu,yanzu ni bani da kowa na karɓi hakan ne abisa umurnin su".
ina kaiwa nan najuya ina kokarin fita tace
"Zo nan kin taɓa jin yan da iyaye sukace sun yanke alakar su da ɗan da suka haifa?,
in ba wani shirin kike son kullawa ba Æ´ar kankanuwa da ke kin iya tsara zance".
wani murmushi nayi wan da yafi kukan da nake ciwo kana na dawo na zauna in da na tashi,dubana tayi da kyau kana tace
"Wacece ke kuma suwaye iyayen naki? da kike shirya musu karyar sun yanke alakar É—a da mahaifa a sakanin ku,sabo da kin kullawa ranki zaki shiga bariki, Allah shi kyau ta wannan rayuwar ba mai É—aure wa bane zai fi miki kyau ki koma gare su ki nimi gafarar su, kirufawa kanki asiri suyi miki aure kije É—akin auren ki asirin ki a rufe,
in ban da zamani ma ai mu a da kamar ki ta isa aure, yanzu ne kawai wai sai yarin ya tagama rika a gida kafin ayi mata aure,
da É—a da dukiya ba'a yi musu mugun ta idan na barki kika fita nasan bagidan zaki koma ba dan haka bazan barki ki fita a gidan nan ba, ni da kai na zan dam kaki hannun iyayen ki,
yanzu dai dare yayi ki kwana gobe idan Allah yakai mu da safe zan kai ki gida da kaina"...
ni dai ban iya cewa komai ba sai sharar kwalla nake,har ta fita a É—akin can takuma dawowa tace nataso na zo,na mike da akwatina nabi bayan ta, É—ayan É—akin da ke jire da nata ta nuna min tace
"Shiga nan É—akin ki kwanta na gyara miki gurin kwan ciya".
nace to,tana tsaye sai da taga nashi ga kafin ta wuce taje ta kulle kofar gida tadawo tashige É—akin ta.
bin É—akin nayi da kallo,katifa ce a kasa da kaÉ—an yafi taburma kauri,sai wasu kayaki da kullin buhunhuna a gefe,sai dai É—akin a share tsaf yake babu ko datti.
a sannu na aje akwati na gefe na zauna kan katifar na janyo pillow da aka naÉ—e shi cikin tsummar zani akayi masa riga da shi,na gyara na kwanta na rufe jikina da hijabi na,
numfashi na sauke lokacin da nakai hakarkari na kan shinfiÉ—i da sunan kwanciya,rabon da na kwanta irin haka yau kwana uku, Allah mai girma yau gani acikin wata rayuwa,
saman É—akin nabi da ido wan da kwano ne kawai rufin sa babu ko silim.
Allah ke nan mai iko mai yin yan da yaso da rayuwar É—an adam,yau nice kwance cikin É—akin da babu gado bare wadaceccen katifa babu hasken wutan lantarki bare AC.
a tunanina kwanciyar da nayi zan sami yin ramuwar baccin da ban yishi ba na kwanaki uku amma me sai naji babu ko ɗigon bacci a ido na,tunani damuwa kunci su suko addabi zuciya ta haka na ta kuka sai daf asuba bacci yasamu nasarar sace ni....★
washegari da safe ina zaune cikin É—akin tashigo
É—auke da kwano da kofi ta dire shi gaba na, hannuna da nayi tagumi da shi na zare kana na gaishe ta ta amsa tace
"Ki karya sai kiyi wanka ga ruwa can na kai miki banÉ—aki bari nagama suya sai mu tafi".
to kawai nace. ta fita na janyo kwano da kofin É—umamen tuwo ne da kunu mai zafi saman murfin kofin kuma awara ne da kosai suma sai turiri suke.
ina gama karya wan na sako hijabi nafito, tana zaune cikin kitchen tana ta suya yayin
yara suka zagaye ta sunata mika kuÉ—i tana zuba musu,har da matasa ma sunata shigo wa siya.
a sannu na shige bayin na É—au tsawon lokaci ina wanke jikina da nake jin nauyin datti a fatata.
koda na fito daga wankan akwa tina na buÉ—e na ciro doguwar riga na material na saka,ina gama sa kayan nazau na kan katifa.
can da jimawa ta shigo da mayafi a kan ta ta dube ni tace
"Taso mu tafi yau wa menene sunan unguwar taku?".
kasa nayi da kai da jikin hawaye ya cika min ido,jin ta kuma mai maita tan bayar sai na É—ago nace
"Ni ba agarin nan nake ba zuwa nayi kuma ni bansan kowa a cikin garin nan ba"...
Da mamaki take kallo na cike da mamaki ta zauna kan É—aya daga cikin É—aurin buhun dake cikin É—akin, ta dube ni da kyau kana tace
"Tanan kika ɓullo kuma?".
kai na jinjina kana
nace "Wlh ni ba ƴar garinnan bace,ban taɓa sanin saba".
kwalla da suka zubo min na share kana nacigaba
"Kada ki mai dani gidan mu domin Abba na yace in nesan ta da su idan na dawo yace bai yafe min ba, bana kuma son ta sana diyya ta naza mo silar barin Ummi na gidan mu,na gwammace nayita yawo cikin duniyar nan har rayuwa ta takare na koma ga mahaliccina".
shiru nayi sakamakon muryata da ta sarke sabo da kuka.
ido Mama mai awara tazuba min,niko a hankali nashiga jan shashsheka.
dakyau ta zuba min ido cikin alhini tace
"Ke ko Æ´ar nan wani irin mummunar laifi kika ai kata haka,har mahaifin ki yayi fushi da ke irin haka?".
kai nashiga girgizawa cikin muryar kuka nashi faÉ—in
"Wlh Allah ban ai kata abun da suka faÉ—a ba, kuma wlh Allah cikin nan nasa ne".
na karasa cikin kuka sosai,
cikin tsananin mamaki tamai da idanunn ta kan cikina dana É—aura hannu kansa,kana ta mike tadawo kusa da ni ta zauna tare da jan hijabi na ta zuba wa cikina ido,
kana tace
"Ba shakka ga ciki nan wanene mai cikin? yanzu Æ´ar nan wannan abu kika ai kata akan yaya iyayen ki bazasuyi fushi dake irin haka ba ciki ciki".
tafaÉ—a tana tafa hannu.
kai nashiga girgiza wa
nace "Wlh ban ai kata zina ba cikin nan na Ya SALEEM ne".
hannuna ta ruko cikin rashin fahim ta tace
"Waye shi É—in ta ya akayi yayi miki ciki to in ba zina ba menene?? kiyiyo ciki a waje kice ba zina kika yi ba to menene sunan shi??".
ta jero min tanbayo yin ida nunta a kai na cike da fargaba da son jin ba'asi.
wasu hawaye masu zafi da kuna na share kana a sannu nashiga bata labarin rayuwa ta,tun daga san da nafara sanin koni waye, har abun da yafaru dani yafito dani daga gida har kuma yau da nake zaune a gaban ta.
kuka sosai nake har numfashi na yana fizga abun da yafaru da rasuwar Inna yadawo min sabo fil a zuciya,cikin muryar shashsheka nace
"Allah ka kashe ni nahuta,kaÉ—auki rayuwa ta ko zuciya ta zata sami sassauci!!!!".
numfashi ta sauke cike da tsananin alhini da al'ajab.
Tace "Akul kidai na faÉ—an haka babu kyau Allah yafiki son kanki, yakan jarabci mutum dan yagwada imanin sa,
hakika mahai fin ki ya yanke hukunci cikin fushi sai dai duk wan da hakan yazo masa rana a saka dole yaji babu daɗe,shi kuma mijin ki ya kama ta yayi tunani ko da a ce hakan yafaru da gaske aure yabashi,amma tun da yace bai amin ce ba bai kuma karɓi cikin ba to shi kenan, ƴaƴa nawa suka rayu batare da uba ba, Allah sauke ki lafiya yataya ki rukon abun da zaki haifa,su kuma waɗan da sukayi ruwa sukayi saki wajen ganin sun ɓata aure, Allah yanuna musu buwayar sa da izzar sa na kwatar wa wanda aka zalinta hakkinsa tun anan duniya,
zaki zauna tare da ni a nan har zuwa lokacin da zuciyar mahaifin ki zai sassauto daga fushin da yayi."
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.