Best / Popular Hausa Novels

Hamdah Littafi Na 2 Complete Hausa Novel

Reading file: HAMDAH part 2 complete.txt

Chapter 15 of 35

Nan dillaliya ta caske dubu goma ta bata da fari tace zata cire naira É—ari uku acikin kuÉ—in ta bai wa É—an dakon da zai kai mata katifar gida,
Mama tace dan Allah tai maka kada ta cire ko sisi cikin kuÉ—in ta bita bashi zata bata...

KuÉ—in mama ta haÉ—a da wan da ta ciro a asusu yazamo dubu shashida da É—ari biyar,
É—akin ta bi da kallo babu wani abun da zata kuma É—agawa ta siyar wan da zai bata ko da dubu 2 ne bare yacikita ragowar kuÉ—in,dama katifar ce kaÉ—ai a cikin É—akin sai É—an tarkacen ta da ayan zu take ganin basu da amfani tun da bazata sai dasu su kawo mata kuÉ—i ba.
numfashi ta sauke gaba É—aya hankalin ta na asibiti da halin da HAMDAH take ciki, tasan tana can tana kan shan azaba.
da sauri ta fita ta nufi gidan Malam Musa mai maganin maciji dan suna mutun ci dasu sosai a tsakar gida da sami Zainabu matar malam musa tana al'walan sarllar isha,
bayan sun gaisa
Zainabu ta É—an yi dari tace
"Mama mai awara kin biyo bashin awar ki na shekaran jiya ko? kin ga Wlh kwata-kwata na mance da naci bashin awara sai da na ganki na tuno".
Mama tace
"Wlh Ni ba abun da ya kawo ni ba kenan ai nima na mance da ma kin siyi awara,
rancen kuÉ—i nazo kibani HAMDAH na asibiti za'a yi mata ai ki,kuÉ—in hanuna basu kai wan da ake nima a asibiti ba dan Allah ki ranta min bayan suna in sha Allahu zan biya ki".
salati Zainabu ta saka tamike tsaye tana faÉ—in
"Subhalallahi ayya HAMDAH yan da haihuwar yazo mata kenan Allah sarki yanzu an yi ai kinne?".
Mama tace
"A'a ni ake jira nakai kuÉ—in yanzu sai a mata".
da sauri Zainabu ta shige É—aki tana faÉ—in
"Ikon Allah Allah yabamu da sauki".
tafito rike da kuÉ—i ta mikawa mama tace
"Wlh iyakacin arzikina kenan É—aka da waje wannan dubu huÉ—un gashi malam yafita bare musa ran samun wani abu a gurin shi duk da dai shima naji yau yana kokawa".
Mama ta amshi kuÉ—in tare da faÉ—in
"Wlh hakan ma na gode zan haÉ—a dana hanuna na kai musu suyi mata ai kin kafin gobe na nemo musu cikon".
tajuya da sauri tanufi kofa, Zainabu tabita da addu'a da fatan Allah yasa a yi ai kin a sa'a...

Gida ta koma ta É—auki laidar kayan jariri da take siya da É—ai-É—ai tana ajiye wa idan HAMDAH ta haihu za'asawa abun da ta haifa har na kwana bakwai,wato kala bakwai kenan kayane irin wan da mace da na miji zasu iya sawa,da É—an sauran kayakin bukatu na jariri a talakance.
tafito ta tari abun hawa tanufi asibitin.
ko da ta isa
ta kai musu kuÉ—in ta rokesu da Allah kan suyi mata ai kin idan Allah yakai rai gobe zata kawo musu ciko.
Nan suke sanar mata ai ammayi mata CS É—in sabo da ganin rayuwar ta da abun da ke cikin ta suna cikin haÉ—ari.
wasu nurse's ne guda biyu suka iso in da su Mama suke tsaye da É—aya daga cikin Dr É—in da sukayi wa HAMDAH CS,
É—aya daga cikin nurse É—in tadubi mama tace
"Tun É—azu muketa nemanki Ina kayan babys da sauri mama tamika musu ledan dake hannunta su shige labour room domin su kimtsa babyn.
Mama ta dubi Dr tace
"Likita ya ita mai jegon dai?".
Dr ta juya tashige room É—in dake gefe da labour room tana faÉ—in
"Babu komai in sha Allah har an fito da ita ma tana wannan room É—in".
wuf Mama tayi zatabi bayan ta tayi saurin cewa
"A'a tsaya tukun akwai likitoci a kanta suna ai kin su bari su gama tukun".
tafaÉ—a tana shigewa cikin room É—in.
ajiyar zuciya Mama ta sauke tanayiwa Allah godiya,
taja gefe ta tsaya idanunta akan kofar da akace HAMDAH na ciki.

Bayan wasu Æ´an mintuna likitoci'n suka fito Mama na ganin da sauri ta matso in da suke tana tambayar su ya jikin nata,
sukace zata iya shiga yanzu.
cikin hanzari ta juyo zata shiga cikin room ɗin tajiyo Muryar nurse's ɗin da suka karɓi kayan jariri suna faɗin
"Yauwa mun gama ga baby's É—in".
da sauri ta juyo da mamaki take kallon nurse's É—in dukan su rike da baby,
sai tasa hannu takarbi guda daya na hannun wacce take kusa da ita tajuya zata wuce,
sai É—ayan nurse din tace
"Baki da me taimaka miki ne ga É—ayan fa,
ko kin bar min ne".
tafaÉ—a tana murmushi É—ayar tace
"Ai kuwa nima yaran sun tafi da ni Wlh ni ban taɓa gyara kyawawan baby twin's irin waɗan nan ba kallesu fa wlh ko ƴaƴan turawa bazasu nuna musu komai ba kai ni sai nagama sunfi min ƴaƴan turawan".
da maki Mama ke kallon su da jin abun da suke faÉ—a
tace
"Kuna nufin yanbiyu ne ta haifa duka waÉ—an nan Æ´aÆ´an ta ne?".
tayi maganar cikin matukar mamaki.
dariya sukayi mata ganin yanda take maganar bilhakki,
Nurse É—in ta mika mata É—aya babyn tana faÉ—in
"Duk natane,yauwa na mijin shi aka fara cirowa kafin macen".
rungumar yaran mama tayi a kowani hannunta guda tajuya cikin tsananin farin ciki har da kwalla tanafadin "Alhamdullilahi Allah mun gode maka".
cikin hanzari tashige dakin da aka kai HAMDAH.
dasauri takarasa inda take kwance da yaran a hannunta tana fadin
"HAMDAH bude idon ki kiga abin da kika haifa".
jin Muryar mama yasani buÉ—e idanuna a hankali,
asannu nashiga juya kai na saiji nayi kamar an É—aÉ—É—aure ni,
dasauri mama tamatso kusada ni ta ajiye yaran dake rike a hannunta a gefe na,tana cigaba da faÉ—in
"Allah mai iko kai sannu HAMDAH sannu kinji".
asannu najuyo kaina da kyar kallon yaran da mama ta ajiye a gefe na nayi kana daƙyar nabude baki murya can kasa nace
"Mama waÆ´annan yaranfa?".
sai da ta maso sosai kafin ta iya jin abun da nake faÉ—a,
fuska É—auke da yelwataccen murmushi tace
"Dukkansu nakine".
cikin tsananin farin ciki da murna Mama ta É—ago É—aya daga cikin yaran ta karkato shi saitin fuskanta
tana faÉ—in
"Kalli kyakkyawar mai gidan nan nawa
da sukayi ta baki wuya,ga kawata ma nan".
ido na kurawa jaririn yayin da naji wani irin mummunar faÉ—uwan gaba ya ziyarci zuciyata,
fuskar Ya SALEEM kaÉ—ai nake hangowa kan fuskar jaririn,
idanuna na rumtse da karfi tare da kuma buÉ—e shi kan fuskar jaririn,
mai mugun kama da Ya SALEEM tamkar an tsaga kara.

Mama ta mai da yaron ta kwantar ta É—ago É—ayar tana faÉ—in
"Ga kawata nan tabar kallah masha Allah".
hancin babyn ta lakata tana washe baki da cigaba da faÉ—in
"Ikon Allah wannan girman ciki yayi yawa ashe dai kune kuka baje ciki".
kai na na rausayar gefe da kyar,
jin wasu zafafan hawaye sun zubo min kokarin danne zuciya ta daketa son fama min mikin dake cikin ta nake,
rumtse idanuna da karfi nayi duk yan da naso danne zuciya ta sai da na tuno.
fahimtar yanayin da na shiga yasa Mama tayi ta jana da hira duk da bana ammsa mata da ido kawai nake binta.
haka tayita kokarin gusar min da damuwar da take hangoshi cikin idona,
har sai da taga na saki raina,
har naÉ—an juyo da kaina ina kallon yaran,
Allah mai girma da É—auka wai duk waÉ—an nan Æ´aÆ´an a cikina a ka ciro su.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.