Best / Popular Hausa Novels

Hamdah Littafi Na 2 Complete Hausa Novel

Reading file: HAMDAH part 2 complete.txt

Chapter 22 of 35

Munyi tafiya mai nisa jin na gaji nakuma tsayuwa na huta, kana na kuma ci gaba da tafiyar,
wunin ranar haka na wuni ina tafiya idan nagaji da tafiyar duk inda na samu sai na zauna sai dai ban kuma yar da na zauna kan itace ko sunkuru sosai ba guri mai É—an fili nake samu sai na zauna,
a duk inda nayada zango na kwatanta lokaci kawai nake sai na gabatar da sallah.
ko yanzu ma a wani guri mai É—an fili na zauna bayan na idar da sallar isha ganin guri yayi duhu sosai sai hasken farin wata,
ina rungume da Naseem da Nasmah,
cikin tsananin tsoro da kaÉ—uwa na daÉ—a rungume su jin matsi da kukan wasu abubuwa cikin wasu irin muryoyi daban-daban.
idanuna na rumtse ina ambaton sunan Allah,
zuwa can da daÉ—ewa sai na rage jin sautin muryoyin,
a haka dai har gyangyaÉ—i yarika É—an fizgata nayi ta É—an gyangyaÉ—in har gari yawaye...
Washegari ma haka na tashi nayita tafiya in na gaji na huta,
yunwa kishin ruwa zafin rana, zuwa yanzu kam jan kafata kawai nake Nasmah da Naseem sai kuka suke nakuma san suma yunwar ce ke É—awai niya da su.
yunwa da ta addabe ni tafiyar ma da kyar nake iya yin ta
zuwa yanzu kam duk wani
bishiyar da na haÉ—u dashi idan naga yayi min kama da na ci sai na sinka naci.
nayi tafiya har na gaji kafata duk sunyi bororo kaya sun kwakkwar janeni bani kaÉ—ai ba hatta su Naseem da kwarjanin kaya a jikin su dan idan muna tafiyar naga wani abun tsoro zan sa gudu ta sana niyyar hakan zasu faÉ—i ko kuma mu faÉ—i tare haka zan tashi naÉ—a ga su na rarrashe su sai in sunyi shiru muka cigaba da tafiyar...

Tafiyar da bansan ina muka dosa ba tafiyar da har yanzu bata ɓulle dani titi da nake sammanin tana gabana ba,
tafiyar kunci da wahala..
Yau kwanan mu biyar a cikin dajin nan,
nagama galabai ta na susucewa nafita hayyaci na,
yunwa kishin ruwa zafin rana,
baci ba sha ba wanka haka mukayi ta rayuwa acikin dajin nan har na kimanin kwanaki biyar.
a hankali nake jan kafata da ta kumbura ganin dare yayi ina ta É—an sauri dan mufita a cikin sun kurun da muke mu isa É—an sararin da nake hangowa a can a gabana,
da kyar na karaso gun na sauke su Nasmah muka yada zangon mu agun,
rukon su na kyara kan kafata cikin sansanin tausayin su, na zuba musu ido,
sun rame sun dishe sun dawo abun tausayi.
ina nan zaune yunwa ya hanani sakat,
suma sai kananun kuka suke wan da nasan kuma na yunwa ce,
daƙyar na rarrashe su sukayi bacci,
niko kasa yin É—an gyangyaÉ—in da nake yi É—in ma nayi saboda tsabar yunwa,
haka na raba dare ina zaune..
koda gari ya waye kuwa nacigaba da aiki na wato tafiya....

Nayi taganin abubuwa masu razanar wa da firgitarwa idan naga wani abun ma kasa ihu ko niman gudu nake sai dai na rufe idanuna da karfi ina ambaton sunan Allah, nakuma sadakar da cewa rayuwa ta dana Æ´aÆ´ana yazo karshe...
Allah sarki rayuwa dani da Æ´aÆ´ana mun sauya kamanni mun rame mun fita hayyacin mu mun dawo wasu irin abu da kama,
mun dawo tamkar mahaukata,
Zuwa yanzu karfina yagama kare wa É—aukan su yana so yafi karfi na,
idan na É—auke su mukaÉ—an yi tafiya kaÉ—an sai naji numfashi na nayin sama-sama idan na É—an tafi kaÉ—an sai na ajiye su na huta sosai kana mukuma yin gaba.
Yau kimanin sati biyu kenan muke rayuwa acikin dajin da nake mana fatan mutuwa dan na tabbata ita zatafi zame mana hutu da wannan rayuwar.
cikin jan kafa da É—an sauri na nufi bishiyar mangoro danake hangosa can sakanin mu daÉ—an rata dashi,
da sauri narika jan kafata dan rabon da na haÉ—u da bishiyar mangoro ko wani abu mai zaki na kai kwana biyar, sai dai naci Æ´aÆ´an itace mai É—aci ko tsami ko burti.
daƙyar na isa gin din bishiyar ina sauke numfashi da sauri na sauke yaran kasa naɗau san da narika kaɓe mangoron sai da na zubo da su da yawa kana na zauna na tattaro su gaba na,nasunku ya sha ba ko kakkautawa har jikina na ɓari,
ina kallon su Naseem suka É—auka waÉ—an da ke kusa da su, suna ta gwaguya ban ko hanasu ba dan suma nasan kalar yunwar da nake ji shi suke ji.
ina gama sha naji cikina yawani irin murÉ—a wa na kwanta a kasa, na da fe cikin nayita murkususu har da hawaye.
najima zube a kasa ina juyi can naji yaÉ—an sassauta min na mike na É—au kesu muka cigaba da tafiya.....

Kamar mahaukata duk kayan jikin mu yayi matukar datti bazaka iya shaida wani irin kalar kaya bane a jikin mu,sabo da tsabar datti,
nawa kamma duk ya yayyage daga kasa.
tun wannan mangoron da muka sha bamu kuma samun wani abun ciba a hanya ba sai da muka kuma tafiyar kwana biyu,
daga can da nisa sosai na hangi wani katon dutsai mai girma sosai gefe da dutsai É—in wasu bishiyoyi ne ajere,
daga in da nake tsaye ina jiyo wani irin sauti mai kara da kugi mai karfi sosai duk da kuwa ina juyo sa daga can da nesa,
cikin sauri da fatan Allah yasa bishiyar abun cine nakara sauri duk da azaba da zugin da kafafuna keyi,
nanufi gurin dutsai da bishiyoyin nan suke.
duk da dai zuciya ta ciki da zullumi da tsoron jin ina daɗa matso in da kara da ƙugi wato irin sautin gudun ruwa yake,
amma ban fasa nufar in da bishiyoyi da katuwar dutsai É—in nan suke ba,
kuma nan nake jiyo kugi irin kugi mai amon sauti irin na ruwa mai karfi sosai É—in nan.
a sannu narika tafiya ina yi ina huta wa har na iso kusa da dutsai da bishiyoyin nan,
wani irin juyawa da tsara wa kaina yayi hango wani katon kogi mai girman gaske,
cikin É—an É—ar-É—ar na karaso jikin dutsai É—inan wan da can gaban sa kuma katon ruwa ne yana gudu da sautin kugi mai karfin gaske.
koton kogi ne mai girman gaske ko karshen gaɓar sa bana gani, ruwane mai girman gaske ko a TV ban taɓa ganin irin wannan ruwa mai girman gaske haka ba.
gefe da dutsai É—in kuwa wasu bishiyoyi ne lif-lif-lif masu kyau sai dai da yawan bishiyoyin ban san ko bishyar menene bane gasunan da tarin Æ´aÆ´a a jikin su wasu jajaye wasu koraye,
daga cikin bishiyoyin kuwa akwai na mangoro gwaiba dabino kwara kwakwa da kuma tupa,
gasunan kasa-kasa. gindin bishiyoyin kuwa yashine fari soll amalale agurin kamar an share gurin babu ko datti har zuwa bakin gaɓar ruwan.
daga gurin bishiyoyin zuwa bakin gaɓar ruwan da ɗan tazara kaɗan,
kafin ai nihin babban ruwan akwai wani ruwa a É—an gaban bishiyoyin sai dai shi É—an kaÉ—an ne da alama dai ruwan idan yayi yawa yana haurowa har gurin idan ya koma kuma sai ragowar ya tsaya a É—an wannan ramin.
ruwan fari soll kamar babban ruwan kogin nan da yake gudu....

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.