Best / Popular Hausa Novels

an Daba Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: an_Daba_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 10 of 23

Page 21-22

Cikin dauriya irin ta jaruman mazan nan Dawood yayi gaba yace "ok in kun gama bincikar ɗakin sai ku same ni a falo" Oga Darma ya daka mashi tsawa yace "kan ka ɗaya kuwa?ko ka manta da wa kake magana ne?to Darma ne ko kai ba ka wuce in kwankwaɗa maka azabar ba ina nan a matsayina na DALMA hukunci guda ne nike yi har yanzu bai sauya ba dan haka zo ka bincika min ɗakin da kan ka"Oga Darma ya faɗa ya na sake tamke mummunar fuskar shi,tsayawa Dawood yayi dan ya fi kowa sanin rashin imani na Ogan nasu hukunci guda ya ke shine ya narkar da dalma a rinƙa ɗigawa mutum ita a jiki mafarin ma ake kiran shi da Darma no mutumci.
Ƙofar towel ya buɗe masu yace "ku shiga ku duba"haka ma drower sannan ya yaye zanen bed yace "ku na iya leƙawa ƙarƙashi"ido Leemat ta waro tare da saurin toshe bakinta da taji kuka na shirin kubce mata idonta tuni sun fara zubar da hawaye na tausayin kanta,mutumen da har Dawood ya ji tsoron shi to ina ga ita? period ɗin ta kuwa tsabar tsoro ji take ya na ƙara ɓulɓulowa.

Taɓi Oga Darma yayi yace "da kyau Boss haka ni ke so wannan ya tabbatar min tu es sûr de toi,mu je falo mu yi maganar da ta kawo mu"Dawood bai ce da su uffan ba sai bin bayan su da yayi, Leemat ta sauke sanyayar ajiyar zuciya ganin sun fita.

Bindigogi masu kyau Oga Ya fiddo daga cikin wata bag ya miƙawa Dawood yace "ina son ku fita opération gobe zuwa yamma gomnan Maradi ya ƙi cika alƙawarin shi dan haka ina son ku ƙwamuso min ƴar shi Diya da za ta dawo daga Niamey kar ku bari wannan damar ta wuce ku dan ita kaɗai gare mu,sannan akwai Gift ɗin da ni ke son baka"ya ida maganar ya na murmurshi.
Jujuya bindigar da ta ke mallakin shi yayi dan ta banbanta da sauran yace "to miye na tafiya da bindiga Oga?"Darma yace "saboda tsaro mana duk wanda ya kawo gargada ku halbe shi na san za'a zo ɗaukar ta ne,ga number ta nan na samu ka tabbatar ka kirata ta yadda ta na sauka kai za ta gayawa am ga hoton ta nan cikin enveloppe"kai kawai Dawood ya jinjina, Oga Darma da maƙaraban shi suka fice.
Da sauri ya koma ɗaki ya jawo Leemat wacce ta haɗa uban gumi sai kace wadda ta haɗi kunama,dukan shi ta shiga yi a ƙirji tana kukan shagwaɓa ya sai ƙoƙarin riketa ya ke ta na zillewa "miye haka?ke ki tsaya mana"tace "na ƙi na tsaya ɗin shine ka wani buɗe zanen gadon kenan so kake ya albushure ni"dungure mata yayi yace "rigimama ni ma ƙarfin hali ne nayi saboda ban so a samu akasi in ya ga kamar ina nuƙu-nuƙu tsaf zai gano ni kuma na san ba zai barin ki ba tafiya zai yi da ke"Leemat ta zaro ido ta na shirin komawa ƙarƙashin gado ya riƙe ta yace "ina zaki kuma?"tace "na ɓuya mana sake ni"yace "to ai sun tafi sai kuma gobe su dawo wani aiki ne ya bani" "na mi fah?"Leemat ta tambaya,kasa faɗa mata yayi sai toilet ya shige jin an fara kiran sallah.

Washegari tun da safe kowa ya fito kamar kullum sai dai abun al'ajabi gidan yayi fes an share shi hakan yasa mutane jin daɗi sai dai tsabar mugunta ta Maye yace doli su tisa sharai,yayi hakan ne kuma dan ya turawa Nana baƙin ciki kuma doli da ita aka sake duk da ƙagewar da ƙugunta yayi mata.

Dawood ya kira Arne da Maye ya shaida masu abinda ya kawo Oga Darma,"dan haka ku kasance cikin shiri banda wasa dan akan wannan aikin mutum zai iya rasa ran shi ta ko wane ɓangare"cewar Dawood.
Arne yace "Boss kamar yaya?" Dawood yace "in can suka kama ka ba ka da wani hukunci baya ga kisa nan kuma in ka yi sake yarinyar ba ta shigo hannun ka ba kashe ka za'a yi"cikin jin haushi Maye yace "to shi Oga Darma É—in mi ya hana shi zuwa da kan shi"wani gigitacen mari Dawood ya sauke mashi yace "sai ka kira shi ka shaida mashi"ya na gama faÉ—a ya wuce É—akin shi.

Saurin aje cup É—in hannunta tayi ta nufo shi ta na tambayar shi lafiya?ganin duk ya kunkume fuska,cup É—in ya É—auka ya shanye maltina da ta zuba sannan ya sauke huci.
Shi har ga Allah bai son irin wagga rayuwar da ya ke ciki,amman ya rasa mafita bai san mi zai yi ba balle inda zai nufa.Dogon gemun shi ta ja tace "ustaz ya dai?ko wani ya taɓo min kai?"da sauri ya buɗe ido da mamiki,ta ɗaga gira tace"eh koko ba nawa ba ne?"ya taɓe baki yace "daga wace?kin san ni ne?"ta turo baki tare da juya mashi baya.
Ya gyara zama ƙafar shi ɗaya ƙasa guda kan salon, hannuwan shi ya kurɗa ya zagaye cikinta tare da ɗora kan shi kan kafaɗarta yayin ƙirjin shi ke manne da bayanta.
Lumfashi ya fara sauke mata a kunne ta rumtse ido dan hakan da ya ke yi ya na sa ta cikin wani yanayi,"j'ai peur"ya furta a hankali cikin ƙarancin sauti tace "tsoron mi ?bayan kai ɗin jarumi ne"yace "banda waje ɗaya"tace "ina fah?"yace "wajen da ni ke da rauni domin in ina gun ni kan ji ni sukuku,raggo marar kuzari sai dai alokacin kawai ni ke ji na cikakken namiji"kan Leemat ya ƙulle ta na son juyawa ta fuskance shi sai dai ya ƙwamushe ta sosai.
"Gaya min ni dai"ta faɗa a shagwaɓe yace "no gani a wajen ma ki gane mana"ta na shirin magana taji ya fara lalubarta,lumshe ido tayi ta na jin ta a wani yanayi shi kuwa Dawood sai da ya samu ƴar ƙaramar nutsuwa ya saketa tare da yin baya ya kwanta ya na sauke numfashi,nan barcin wahala ya ɗauke shi.
Cike da tausayi ta ke kallon yanayin shi,tabbas Dawood na da dauriya in ba haka ba ta yaya ga maganin matsalar ka amman ka kasa sha?wani irin matsayi ne Leemat ta bashi a zuciyarta wanda ita kanta ba ta san na minene ba.

Alizza transport voyageurs kanfanin balaguro ne da ke nan jahar Maradi,a sannu matafiyan ke saukowa daga cikin Bus Maye da Arne sanye cikin kayan ƴan kamfanin wato masarar riga da hulla képi.
Diya na fitowa suka nufeta " Hajiya Barka da sauka bado tiket ɗin naki za mu nemo maki kayan ki mu kai maki har mota Oga ne ya samu ga shi can cikin mota"cewar Arne ya na mai nuna mata dalleliyar motar da Dawood ke ciki,ba tare da wani tunani ba ta baiwa Arne tiket ɗin yayinda maye ya rakata har wajen motar da ta ke tunanin ta mutumen da yayi mata text da cewa shi masoyinta ne kuma zai yi mata ba zata a siège domin shi zai ɗaukar ta ya kaita har gida.
Maye ya buɗe mata gidan gaba,ta na shiga ya rufe yayinda Dawood ya shaƙa mata wani hankicin nan barci ya ɗauke ta ba tare da ta ƙarewa fuskar shi kallo ba.
Arne da Maye ba tare da sun ɗauki trollynta ba suka shige mota Dawood ya bata huta,Arne yace "shege Oga wa ya aka yi ma ka yi wannan tunani mai sauƙi haka?"ta madubin da ke gaban mota Dawood ya kalli Arne yace "Ni ne shegen?" "Ayi haƙuri Boss suɓutar baki nayi"cewar Arne.
Maye kuwa cewa yayi "ka san Boss bai son maganar zubda jini shiyasa ya yanke wannan shawarar yo ni na zata da halbi za mu tashi gidan har sai mun ƙwamaso ta"Arne ya ture shi yace "kaji banza su kuma mutanen gun a rasa wanda zai kirawo ƴan sanda?"Maye bai tanka shi ba sai ce ma Dawood da yayi "Boss ya kamata a rage gudun nan tunda mun riga mun ɗaukota"Dawood yace "in kai ba ka da hankali ni ina da shi, lokacin da mu ka fito ba ka ga motocin gidan su sun shiga ba?"ganin an gwasale shi Maye ya ƙi cewa komi.

Bayan magrib Oga Darma ya dawo gidan wanda tuni ya aikawa da gomna da saƙon ƴar shi ta na gun shi,cike da jin daɗi Oga Darma ya tsiyayawa Dawood daji tare da fakar idon shi ya na sa ƙwaya.

"Na ce zan baka Gift to ga shi nan wannan yarinyar ni ke son ka kwana aiki kan ta kar ka raga mata,abinda ya sa na zaɓe ka sanin kai ne ba ka taɓa haraka da mace ba ina son ka sauke gwabrancin ka a kanta sannan ka ɗauko min hotunan ta a yayage"Oga Darma ya faɗi haka ganin baƙin ciki ƙarara kan fuskar Maye.
Dawood zai ce wani abu yaji kan shi na sara mashi yayinda duk wata gaɓa ta jikin shi ke amsar saƙo,gefe guda kuma Diya ce a tuɓe daga ita sai breziya sai pant gashin kanta na ɗigar ruwa saboda wankan da Oga Darma yayi mata da ruwan ƙanƙara.
Cike da tashin hankali Dawood ya miƙe tsaye ya na jin wata masifafar sha'awa ga sandar girman ta fara aikinta,abincinta kawai ta ke nema da hannu Oga Darma yayi masu alama suka fice tare da rufe ɗakin ta baya a lokacin ne kuma masallatai ke kiran sallah magrib.......

Comments and share Please

Jikar Rabo ce 😎
*ÆŠAN DABA*
```love
and
romantic story

``` _MRS SADAUKI_ 💫

*Dedicated* to My Babbar Yaya Nafissa Laouali Rabo🥰

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️

____________________
BISMILLAHI RAHAMANI RAHEEM

*Babu abinda zan ce sai dai Allah bar ƙauna fans na gode sosai da yadda kuke rububin wannan book*🥰🥰🥰

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.